Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bash ya hana mukhatar tafiya saida akayi sallar isha'e sannan yace masa yazo su je gano annah bata lpia,
yai masa qaryar hakan dan so kawai yake suje gidan dan dubun mukhtar ta cika yau a bainar jama'ar gidan ,
shikuwa mukhtar harda wani saurin amsawa da "to" dan muradinsa na son ganin ummu hani.
haka suka shigo motocinsu har suka iso gidan kowa yayi parking ya fito bash ne gaba mukhtar na biye dashi suna shiga kuwa suka iske dady muazzam zaune a falo shida dady Muhammad wanda suka shigo babu jimawa daga masallaci suma,
sai gefe daya annah ce suke zaune ita da momy umaimah suna fira ta 'yan katsina,
sun gaishesu su dady suka amsa kan susake cewa wani abu saiga mahabeer shima ya fito daga ckn kicen hannunsa daukeda gorar ruwan swan lokacin kuwa har bash ya miqe ya isa ga tv ya ciro camera dinnan ya jona da tv daga inda yake tsaye ya juyo wajensu dady mua'zzam yace
"yau dady zaku fahimci gskiar ainahun wanda ya sakarwa mahabeer matarsa dan zallar cin amana irun tasa nikuma nayi dabarunmu harna hillacesa na zurmasa ya bayyana mun gskiar lamarin nikuma shine nazo nima in bayya na muku domun wanke mahabeer daga zargi dan Allah yanzun ku kallo nan kugani,, mukhtar najin haka tuni cikinsa ya bada wani sauti quuuu qulululu, nan take zufa ta karyo masa lokaci daya ga ctv camera ta nuno sa baro baro yana tonawa kansa asiri,, tunkan su dady su gama kallo suka fahimci *gaskiyar lamari*, salati kawai suke da sallallami ay a guje mukhtr ya miqe tsaye zai gudu dawani mugun tsalle ko mahabeer ya damqosa ya gama kansa da bango yafara dukansa jikinsa na ciri kota ina,, tuni ya tadawa mukhtar idanu da hanci da baki suka tashi himmm sai duknsa yake yana fadin "wlh Allah ya isa mukhtar kaci bazan amanata bazan barka ba saina kasheka daqyar su dady suka jnyesa suna basa haquri mukhtar na ganinsa free tuni ya fesa da mugun gudu waje ya fada motarsa shima mahabeer ya futo ya shiga mota ya fuce tuni su dady mua'zzam suma suka biyosu da motarsu dan shawo kan rigimar data auku,
gudu su mahabeer kawai suke fallawa a titi,
cikin tsautsayi kuwa motar mukhtar burki ya qwace masa ya yanki gefen daji motar ta dinga gungurawa dashi ta daki wani bishiya sannan ta tsaya cak,, gaba daya hankalin mahabeer naga inda motar mukhtar din yake bai ankaraba yaji ya ingeji abu dasauri ya maido hankalin sa gabansa ganin wata yar dattijuwa ce ya banke ta zube can gefen titi nan a guje ya taka burki dai dai nan su bash da dady mua'zzam da ddy Muhammad suka iso duknsu lokaci daya, mahabeer ya fito da mugun sauri ya nufi matar nan,
suma su dady Muhammad suka isa inda motar mukhtar yake daqyar suka zaqulosa qafafu sun kakkarye yakasa takasu sai lilo suke suna reto, sai dai talla talla sukai masa suka sashi a motarsu koma numfashi da qyar yake fuddowa suna sakasa mota suka dawo wajen da mahabeer ke zuqunne gaban tsohuwar wacce dadan kullin kayanta a kallabi sai nishi take sama sannan su dady Muhammad sukace "subhanalla sannu dai baba daqyar ta iya amsawa zaki iya tashi kuwa kasa magana tayi wayar hannun dady mua'zzam ya haska a fuskar tsohuwar domim rashin wadataccen hasken dake wajen sosai hankalin dady Muhammad yayi kan tsohuwar cikin tsananin mamaki da razana yace Innalillahe..inna?
wannan ai inna indo ce tshohuwar mai aikina ce wacce muka nema muka rasata tun shekarun baya......



*Xexen Fasaha*
f. o. w.
[10/11, 2:49 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

*🌳impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern🌳*.

*For your only xexen Fasaha novels group, all of you love you so much*❀
🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ5⃣4⃣
🌊🌊🌊
Dukansu mota suka shiga bayan sun sa inna indo itama nan suka nufi asibitin,,
Suna isa aka shigar dasu d'aki nan aka fara dubasu ita inna indo targad'e tayi a yatsa yayinda shi kuma mukhtar aketa q'oq'arin yi masa d'auri a q'afa dan gaba d'aya sun karereye ihun sa dud ya cika wajen sabida d'aurin q'afar da ake masa dan wata futinannen azaba kawai yake sha, ganin haka nan take bash ya d'auki wayarsa yakira baban shi mukhtar d'in babu jimawa kuwa sai gasa yazo saman mashin dinsa shida Mustapa qanen mukhtar din,,
su kuwa su dady mua'zzam suna zaune nan bisa kujeru mahabeer sam yakasa zama har yanzun zallar mamakin abinda mukhtar ya shuka masa kawai yakeyi amman babu komi yaje dan kansa nakasar ma daya samu kadan daga sakamakon wanda aka amincewa mawa knn yayi ha'inci, ya kuma godewa Allah da har gskia ta bayyana yy kuma alfahari da aboki na qwarai irin bash mai hankali da hangen nesa, shiyasa har gaban bash yaje ya zauna ya dafa kafad'arsa ahankali bash ya d'ago ya dubesa su ka yiwa juna wani murmushi, rungume juna sukayi cikin muryarsa mahabeer ke cewa "ngd bash ngd qwarai hak'ika ka cika aboki na gari Allah shi barmu tare,,, ''amunn" cewar bash dafe kansa mahabeer yy bayan ya janye hannunsa daga jikin bash yace "dole ne na dangana d'an iskan nan ga police ma bash dan bazan wai barsa haka ba inna barsa haka banwa kaina adalci ba nikega"
girgiza kai bash yayi sannan kuma yace "kada kayi haka gifted ka barsa haka kodan ma sabida iyayensa ka qyalesa kawai Allah na nan ay"
shuru mahabeer yy dole dai ya haqura badan yaso ba dan babu wata alfarmar da bash zai nema a wajensa bai masa ba, su dady ne suka qaraso wajensu suka zauna nan Dady mua'zzam yace "dudda abinda ya faru mahabeer kayi haquri kada kace zaka daukaka maganar nan dan nasan ka da zuciya kayi haquri sojana kamar yanda Allah ya saka maka ya fito mana da gskiar magana to kayi haq'uri dan lalurar da ke jikinsa ma ta ishesa ishara , taune lips d'insa mahabeer yy yace "naji dady amman kuma wlh narabu dashi har abada bashi ba wajen aiki na,, murmushi dady Muhammad yy yace "daman ai wannan ta rigaya data wuce shi kansa nasan ai kunya ma bazai bari yazo ba"
"hakane kam gskia" cewar dady mua'zzam din shida bash,, duban Dady Muhammad dady mua'zzam yayi yace"amman aboki na naji ka ambaci sunan wannan tsohuwar daman ka Santa ne can da?" girgiza kansa Dady Muhammad yayi sannan yasaki ajiyar zuciya yace "tabbas na santa sani ma na sosai kuwa, itace wacce na taba baka labari mai aikin ni'ima wacce tatafi garinsu tun bayan b'atan mahabeer bamu qara jin labarinta sai yau din-nan fa da dalilin dalili na qaddara data fuddomu har Allah yasa kuma nayi *gam da katar* da ganinta kaga kuwa muddin ni'ima ta ganta nasan ba qaramin dad'i zataji ba a rayuwa dan sun shaqu shaquwa kam bata wasa ba kuma,, kan Dady mua'zzam yace wani abu saiga likita ya fito ya iso wajen yace "zaku iya tafiya gida da ita babar yanzun haka inda ba wani ciwo taji ba shi kuma yaron nan gskia zai yi wuyar yuyuwa koya warke qafafunsa bazasu cigaba da taka doron qasa ba dan gaba day'a qasusuwan sa sun karkarye a hatsarin nan kuma mun debi jininsa dan shima muyi tes....,,,
dakatar dashi mahabeer yy yace "bamune danginsa ba mu kawai iyaka kawosa mukayi ga iyayensa can kaje kai musu wannan bayanin bamu ba" doctor yace "ok i don't know but no problem kwa iya tafiya din kamar yanda nace"
haka su Dady sukayi balance sannan suka fito da inna indo tana fmn d'an d'ingisa q'afar tata har suka shiga mota suka nufi gida.
falo suka shiga gaba day'a nan suka taras dasu annah har la okacin suna tare kenan amn wannan karon harda ummu hani zaune gefe daya tana riqe da baby manal cikin jiknta,
amman kuma dud jikinta yai mata sanyi jin wai mukhtar abokin mahabeer ne yajaza wannan rigimar,,
kai duniya ina zaki damu gskiya tai qaranci mutane babu tabbas sai d'ai d'aya na Allah.
zaunar da inna indo mahabeer yayi, duknsu suna qara mata sannu,
su annah sai kallon rashin sani dai suke mata,,
da sauri kuwa dady Muhammad ya juya ya fice daga falon bai jimaba sai gasa sun dawo shida momy ni'ima,
ai momy ni'ima na arba da inna indo kamar yanda dady Muhammad ya fad'a da sauri ta isa inda take suka riqe juna suna tsananin murna da farinciki dudda tsufan da inna indo ta qarayi amman hakan bai hana momy ni'ima shaida taba nan taken,
momy ni'ima tace cikin hawaye "inna indo ashe munada rabon sake ganawa? inna indo ina kika shige ne? babu inda bamuje nemanki ba amman shuru gashi kuma bamusan garinku ba tun muna nema har muka haqura,, inna indo tana qoqarin bude baki tayi mgn
sai kuma akaga ta fashe da kuka tana cewa "Alhamdulilla nagode Allah ni indo Aisha daban mutu ba batareda na gamu da mutanen nan na fad'a musu inda amanar su take ba, o'ni na gode Allah jalla wa azza,, zuba mata idanuwa kawai Dady Muhammad yayi shida momy ni'ima.
d'agowa tayi ta dubi momy ni'ima tace
"uwar d'aki na yau zan fayyace muku *sirrin b'oye* wanda ya jima da b'oyuwa sama da shekaru kusan nawa,,
shin kokunsan cewa d'anku mahabeer yana raye bai mutu ba kuwa?
cikin wata iriyar azababben razana suka fara magana dady Muhammad yace "inna indo mi...mim... mikike son cewa haka ne?
gyad'a kai tayi tace
"tabbas kuwa kamar yanda dai kukaji na fad'a muku haka ne, cikin wata muguwar futinannen bugun zuciya momy ni'ima tace "wa.. wa ya d'auke mana shi ne to inna dan Allah?!
sannan kuma yana ina yanzun?
inna indo tace
"in bazaki manta ba aranar da aka dauke mahabeer nazo miki da magana kan cewa kisa ido sosai akan d'anki dan bn yarda da takun saqar hjy laria ba amman sai kikace a'a ga tunaniki na ta gyaru alhalin ni aranar naji abinda naji gameda suna son sace sa suje su kashe sa dan baqin cikin ita hjy laria din bata haihu ba,,
inna indo na fad'in haka momy ni'ima ta kife wajen ta fashe da kuka tana dukan jikinta tana fad'in "minayi miki ne haka hjy laria da kika tsaneni kika rusan farinciki na? miqewa tsaye tayi zata fice da sauri dady Muhammad ya tarota tafara qoqarin qwacewa tana kuka take cewa "nika wlh ka rabu dani sai naje ta fiddo mum dud inda yaro na yake,, saida qyal yashawo kanta sannan ta dawo ta zauna tana cigaba da kuka, su kuwa su dady mua'zzam gaba day'a sun cika da al'ajabi kan abubuwan da suke ta faruwa dasu haka kamar almara.
inna indo ta dubi momy ni'ima tace "ki sauraran da kyau uwar d'aki na yanzu koda kinje wajen hjy laria batasan inda yaro yake ba nice nan nasan inda yake danni ce nayi ceton rai na d'okesa nabar gidan dashi a ga6ar lokacin da suke neman cimma mummunan burinsu ni kuma na daukesa na kaisa inda nasan za'a basa cikkayiar kariya da kuma kulawa kamar kowane yaro.
kamo hannuwanta momy ni'ima tayi tana share hawaye tace "Alhamdulilla inna indo dan Allah to ina yarona kika kaisa wlh kin tado min tshohon miki na jinake zuciya na kamar zata fashe tsabar duka da take mun yanzun haka"
inna indo tace "bai hannuna tun lokacin dana daukesa nabar gida dashi na kaisa gidan marayu a nan na badasa nace musu zan dawo nan ba da jimawa ba in karb'esa, to koda na dawo gida naga anata bid'arsa ganin ynda hankalin ku ya tashi nikuma shiyasa nakasa jurar ganin hakan shiyasa a lokacin na fake da cewa zan tafi gida dan ban jurar rashin yaron kusa dani ku kuma sai kuka sauko kuka dinga tausana kan kada in tafi ammam dudda haka na dage akan dai lallai lallai inason zuwa gida gano babana da bai lpia nayi hakanne ni kuma dan in tafi in barku nadan wani lokaci in yaso sai daga baya in dawo in fad'a muku gskia lamarin da yasa nai hakan danku d'auki mataki to sai kuma gashi kuma dai a wansheka ren da naje gidan namu da daddare muna kwance kawai naji an daukeni an tura cikin wani qaton buhu an qulle an tafi dani an ajiye wani waje wlh nan naji ansa itace manya manya anata fmn dukana ina qulle cikin buhun tun ina iya kuka da motsi harta kai ga na gaza ko motsa hannuna haka mutanen da ban san ko su suwaye ba suka tafi suka barni jin wani day'a daga cikinsu nacewa dayan daga gani na mutu inda ga jini nan na fitowa a buhun kuma na daina motsi ma,
wlh bansan inda kaina yake ba sai dai farkawa nayi na ganni a gida ashe da gari ya waye nan maqotan mu suka kwance buhun da nike ciki ganin nice yasasu suka gigice a rude suka kirawo babana suka shigar dani ciki,
haka babana yaita mun magani tsawon shekara da shekaru dayake dud gab'ban jikina babu inda basu nakasa ba, wlh sai a hankali nafara iya zama harta kai ta kawo ina miqewa baba na na koya mun tatata harna fara d'an daddogara wa da kaina da sanda, da tafiyar tayi qwari nakuma samu lpia sai na bawa baba na labarin abunda ya faru dakuma yanda na dauki jinjirin naku shine a lokacin na nuna masa inason in zo nan birni wajenku in kaiku ku dauko yaronku a lokacin shikuma yace a'a bazai yarda in zo ba dan bai son nima ya rasani inda ni day'a ce a wajensa dan ya tsorata matuqa da labarin dana basa na hjy laria gani yake in na koma na fadi gskia kamar nima zata sa a nemi kashe nine,
to nikuma dole na haqura dan bn iya sa'insa ba da baba na ba tun ina 'yar qaramata bare yanzun da mnyanta ta kama ni,, haka na haqura naita kulawa da babana dayake ya tsufa sosai kuma, lokacin kusan komi na rayuwa nike masa hatta ciyarwa nike surho da aikatau in dinga ciyar dashi dan 'yan uwanmu ba kulawa suke damu ba inda bamu dashi wai.
ana haka wataran na wayi gari ran baffa na yayi halinsa naci kuka harna gode Allah haka nai ta binsa da addu'a, ni day'a naci gaba da zama a gida dan 'yan uwa babu wnda ya yarda naje na zauna a gidansa,, nikuma shine nayi qudarin koda zan mutu saina zo nan birni na fad'a muku boyayyen zan cen nan, dan haka yau da safe nai sallama da yan uwa akan cewa zanyi dan tattaki haka na hau mota natafo saida magrib na iso nan garin nakuma je can tsohon gidan naku nagamu da maigadi yace hjy laria din bata nan nace masa wajen hjy ni'ima nazo ay daman nan yace kun tashi har yaimun kwatancen inda kuka koma to kuma akan hanya tane ta tafowa nan gidan har na qetaro titi kenan wannan hatsarin ya ritsa dani to kunji yanda abun yake"
kowa ya tausayawa rayuwar innah indo anan falon momy ni'ima ta dage akan sai sunje gidan marayun amman dady Muhammad ya hana yace su haqurarwa zuwa gobe in AllAh ya kai da rai da lpia dan yanzun dare yayi har 12 ta wuce.
dole ta haqura suka barsa sai goben. daren ranar daga dady Muhammad har momy ni'ima babu wanda barci ya ga idonsa dan farinciki dakuma q'aguwa gari ya waye kosa sa d'ansu a ido suma abun shekara da shekaru.
wanshekare tun qarfe takwas na safe dukkan kafatanin iyalen mua'zzam saraki sune suka raka su dady Muhammad zuwa gidan marayun tun akan hanya ganin gidan marayun da aka dosa yasa gaban su dady mua'zzam dana mm umaimah fara dokawa kuwa suma, basu qara tsinkewa ba saida suka shiga office dinda rabonsu dasuka shigesa sama da shekaru knn tun randa sukazo aka basu jinjiri basu qara zamnsa ba inba yau ba, nan annah ta basu cikakken bayanin itace wacce takawo ajiyar yaro a shekarun baya.....
nanta warware ma mutumin komi da lalurin daya hana ta dawo karbar yaron kan kari sa6anin yanda tai musu magana akai na zata dawo karbarsa nan bada jimawa ba in komi ya lafa .
dudda tsufa da annah ta qara sosai amman hakan mlm mukhtar bai hanasa gane itace wacce ta kawo mahabeer ba a rud'e @ shekarun baya ba,, nan ya aika nani tazo itama yai mata bayanin kowacece aiko itama nan ta gane inna indo nan aka d'auko littafin da suke sa dud wani history na yaron dake cikin gidan dakuma wand suka kar6esa ,,a hankali cikin nutsuwa mlm mukhtar ya dago kai ya dubi su Dady mua'zzam ya kuma dubi Dady Muhammad,
girgiza kai yayi snn yayi dan Murmushi yace "Alhamdulilla aboki ya rainarwa dansa d'a knn? kai masha Allah,, cikin rashin fahimta dady Muhammad yace "ah nifa bn gane ba mlm mukhtar? kan mlm mukhtar ya ce wani abu tuni har dady mua'zzam ya katsesa da cewa "hmm nasan daman komin kuwa daren dadewa gskia zatayi halinta, shuruya danyi sannan yace "haj Muhammad kamar ynda mlm mukhtar yace aboki yayi rainon d'an abokinsa to haka abun yake dan ni dama tunda naga mun shigo gidan nan kuma mun shigo office din nan nasan magana ta qare... nan dady mua'zzam ya fad'a musu ynda sukazo suka karbi dan nasu mahabeer a lokacin,
yana gama fad'an hakan ya juya ya dubi mahabeer daya daskare a wajen jin abinda ke wakana kamar a mafarki,, dafa kafadarsa dady mua'zzam yayi yace "sojana komi kaji hakane dan tabbas ranar wanka ba'a b'oyen cibi dadyn ka Muhammad da momyn ka ni'ima sune asalin iyayenka ba muba kamar dai yanda kaji komi an maga warwaresa yanzu a gabanku"
dady mua'zzam yaqarashe maganar tareda share qwallar data zubo masa sannan ya miqe tsaye ya kamo hannun mahabeer ya kaisa ya zaunar gabansu dady Muhammad da momy ni'ima yace ga d'anku nan ya dawo hannunku kamar yanda muka d'au alqawari wato idan iyayensa suka bayyana zamu miq'asa garesu"
mamaki kawai ummu hani keyi momy ni'ima kuwa tsabar farinciki kamar ta zuba ruwa qasa tasha daman yanzun ashe kenan mahabeer dansu ne?
ashe sonda take masa har cikin ranta ba banza ba son d'a da uwa ne? sujada kawai tayi qasa tana cigaba da yiwa Allah kirari da godia.
kuka kawai momy umaimah ta fashe dashi aiko da sauri mahabeer yayo kanta ya rungume gefen jikinta yana zybda hawaye shima ganin abun zaiyi yawa yasa su dady mua'zzam da Muhammad sukayi bankwana da su mlm mukhtar bayan sunyi abinda ya dace sannan suka dunguma sukayo gida nan aka zazzauna falo annah kam kasa cewa komi tai itama dan a boye take goge hawayen fuskarta dan sabo kam yafi qarfin wasa bare nasu sabon da mahabeer tun abun yana jinjiri gashi yanzun harya girma yazama cikakken mutum dole ne kuwa suyi kuka.
nan falon ya d'auki shiru saidaga bisani dady Muhammad ya dauki wayarsa ya bugawa hjy laria yace komi takeyi tazo nan gidan alhj mua'zzam abokinsa yana jiranta yanzu yanzun.
ba'a jimaba kuwa sai gata ta shigo falon gidan itada qanwarta hjy safia. wajen zama suka samu suka zauna ta tsorata kuwa hjy laria sosai ganin irin wani wulaqantaccen kallo da dady Muhammad din yake aika mata dashi.
dady Muhammad ya nuna mata inna indo yace "kokin shaida wannan baiwar Allahn? sai da hjy laria ta qare mata kallo sosai sannan ta dafe qirji da hannuwa bibbiyu tace "na shiga ukku ni hjy laria daman indo kina raye su goga sukace sun kasheki? daura hannuwa tayi bibbiyu saman kai jin da tayi subutar baki dan rudewa,
dady Muhammad yace "kaicon ki muguwar mata to d'ana mahabeer da kikai burin kashewa to Allah ya nufa bai mutu ba gashi nan zaune daram a gabanki a raye cikin rayawa ta Ubangiji Allah" yayi maganar yana nuna mata mahabeer dake zaune kansa na masa mugun ciwo da sara,, sannan yace "kuma billahel azeemu koki fadan gskia ko yanzun nan kijiki prison dan wlh d.p.o. zaki gani yanzun nan ganin idanunki yatasa mun qeyarki gaba kuma wlh har duniya ta nad'e ba zaki fito ba a gidan jarin din ba zakita zama har kita girbe mugun irinki da kika dad'e kina shukawa saiki zauna can kita cin amfanin girbin naki har illa masha,
fashewa tayi da wani kukan dantasan komi yace tofa saiya aikata inka layance masa gskiar da ya nemi ji wajenka dan kaifi day'a ne shi tasan da hakan kuma tuni shiyasa dud iskancinta batayi a gaban idanunsa ko, a tsorace tace "ka yafemun alhj wlh zan fadi gskia wlh dud sherri shedan ne ne,, daka mata tsawa alhj Muhammad yy yace "karkice mun wani shedan ne hjy laria wlh kema muguwar shedaniyar kanki ce nasan da hakan tuntuni qyaleki kawai nikeyi dan haka maza imun maganar ynda kika shirya sauran shi tuggun naki ina sauraronki.
cikin rudaddiyar murya hjy laria tace "lokacin da muke tsara zamu dauke jinjirin domin muje mu kashe sa kawai sai mukaga alamun mutum ta bakin qofa a wajen, na tura safiyya taje taga waye tana fita taga indo ce a wajen tsaye sai taga indo din tayi saurin wucewa jin motsin zaa fito knn,, nikuma koda ta fada mun hakan na tabbatar da cewa lallaikm taji sirrinmu mafarun knn na ajiye qudurina na sace yaron da niyyar saina koyawa indo din hankali sannan in dawo ga yaron, katsam naji labarin babu yaro daga baya naji ance itama indo din ta koma garinsu nan nasa akaimun binciken garin da indo take da zama da kuma gidansu, ba'a jimaba muka gano hakan kuwa shiyasa natura aka saceta akaimata duka dan kawai in huce hushina to wannan shune gskiar mgn dan Allah alhj ka yafe mun bazan qara ba na tuba nabi allah nabi ka".
girgiza kansa Dady Muhammad yayi yace "ina takuma q'are gskia ta fito bori kuma yakar boka wlh harga wllah hjy laria bazan cigaba da jurar munanan halayenki ba dan haka kije na jnye
sauran igiyar aurena akanki inda daman nata b'a yimiki 2 a baya ynxun ga dayanki nn na cika miki" ai da gudu hjy laria ta kwasa tayi waje tana kururuwa da fadin "Allah ya isa bata yafe ba an cuceta kuma dukiya ce tayagi iyakar rabonta danmi inya saketa aiba shine autan maza ba" ahaka safiyya tajasu suka tafi sai tsinewa indo suke ganinsu itace dud ta jaza musu wannan masifar to'an saketa hankalinsu ay ya kwanta matsiyatan itada ni'ima din.
tun a hnya ta kira masu kwashe kaya dan tayi alq'awari ko kwana daya bazata qara gidan saba tabar masa tsiyatakunsa yazo yayi dud yadda zaiyi dashi "munafikin shima", cewar qanwarta safiyan.
acan kuwa dady Muhammad ya dubi Dady mua'zzam yace "kada ku damu abokina mahabeer dan mu ne mu duka dan haka har yanzun hannunku yake dan ko babu ranmu kai mai riqe mana shine, burunmu yacika inda mun gansa da ransa bawai ya salwanta ba, dan haka kada kuji komi zaici gaba da zama hannunku inda dud ana tare",, dasauri mahabeer ya rungume dady Muhammad cikin murna hakama yaje wajen momynsa ni'ima ya matse hannuwanta ya kwantar da kansa a bayanta yanajin wani farinciki idanunsa na sauka ana annah ya dage mata gira ta yi Murmushi tace "ja'irin gske kaiko? dariya duka falon sukayi momy umaimah da ni'ima sukace "kai annah keda jikan naki" Murmushi annah tayi tace''a'a nabar muku kuyita kaya" daga haka ta shige dakinta nan dady Muhammad yace
"to hj mua'zzam yaushe diyar tamu zata tare gidanta? Murmushi Dady mua'zzam yy yace "ko gobe yy ko? Inda yagama komi na gidan nasa anan bayanmu gidan yake".
da sauri momy umaimah tace "a'a nuree abamu sati daya sabida mu shirya yar tamu muma kam,, murmushi su dady kawai sukayi suka cigaba da firarsu ta abubuwan da suka faru a rayuwar tasu duniya kenan. yayinda mahabeer yafaki idanun su dady ya

Please Login or Register in order to submit comment