Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinsa ya zauna ya had'a manyan yatsunsa na hannu guda 2 yana sosa qasan hab'arsa dasu idanunsa a lumshe banda searching babu abinda brain dinsa ke masa lokacin,
ya dan jima zaune agun sannan yaje toilet ya watsawa jikinsa ruwa ya fito yayi shirin barci ya kwanta kan bed knn phone dinsa yayi ringing a zatonsa ko bash ne ma amman yana dubawa sunan blessing ne yafito kan wayar, tsoki yaja ya ajiye wayar danshi yanzu yariga yagama da rufe babinta a garesa dan bazai cigaba da b'atawa iyayensa akan tarayyarsu ba inda basaso indama ace ta yarda ne ta karbi musulnci dada sauqi ma,haka taita kiran wayan sama da mores missed cull amman kota kan wayar bai biba, an dauki tsawon minti 15 sannan wani kiran yasake shigowa dubawa yayi ganin hannat ce ya sashi sake jan wani tsokin tareda kashe wayar tasa ma gaba day'a dan ya fuskanci bawai barinsa zasuyi yaji da damuwar sama ba data hayyacesa.
soyake ya rufe idanun sa ysyi barci koya samu sauqin abun amman Jin yanda cikinsa keyi ne yasashi shafa cikin da hannunsa shi kansa yasan rabonsa da abinci tun na safe shine har yanzu cikin cikinsa dole kuwa yaji cikinsa na kukan yunwa knn.
agogon wayarsa ya duba yaga 10:26 tashi yayi ya fito daga dakin yasauko qasa kai tsaye dining area ya nufa ganin yarinyar yayi zaune akan d'aya daga kujerin wajen wanda hakan ya tabbatar masa da itama yunwar ce ta fito da ita, hakane kuwa ya canka dai-dai dan rabon data sanyawa cikinta wani abinci tun lokacin da dady yai mata maganar amakson koda momy umaimah tazo tai mata maganar ga abinci can dato mah kawai tabita ita momy umaimah tayi tsammani ma tasauko ta debi abincin ta koma dakinta dan wani lokacin haka take daman wato taqi zama dining din saidai ta sauko ta d'ebi nata abincin cikin plate ta koma sama taci acan , saida taji yunwar na katsar tane yanzun mafarin knn ta leqo qasan falon taga bakowa shine tazo ta zauna tadebi abuncin ta fara ci ko six spon batayiba shima ya fito, ganinsa kawai tayi yaja kujera mai pacing dinta ya zauna, har a ranta ta tsorata da ganinsa a lokacin haka tsoron harya bayyana bisa fuskar ta tazaro fararen idanunta waje cikin dabara tafara qoqarin miqewa daga wajen, tsumammun idanunsa ya zuba mata cikin nata da kashedin karta sake ta motsa daga wajen, dauke fuskarta tayi daga garesa tana yamutsa ta kamar bata fahimci abunda yake nufi ba tayi.
plate taga yajawo ya zuba abinci sosai ya faraci idanunsa still su na kanta ita kuwa sai tsakurar abincin take kad'an kad'an dan a mugun takure take jinta a wajen, saida yaci abincin sosai yasha lemo ya goge gefen bakinsa ta teshu paper ita kuwa saurin miqewa tsaye tayi zata bar wajen da sauri yasha gabanta ya tare mata hanyar kanta ta kauda gefe tasake ratsewa masa gudan hanyar ba zato ya finciko hannunta da qarfi saigata saman qirjinsa yasa yatsunsa biyu yadinga mammatse mata lips da qarfi sotake tayi ihu amman babu dama dole tasa ta dunga jujjuya kanta dan azabar zafin datake d'andana daga wajensa, sai kuma hawaye suka biyo baya.
saida yaga lips dunta sunyi jajir kamar na jariri sabuwar haihuwa sannan yasakar mata su babu shiri tayi shirin sulalewa qasa bai bari takai qasan ba yasa hannunsa daya ya dagota ya damqo gashin kanta tareda dago da fuskarta sama dai dai saitin tasa yasakar mata wani killing smiling cikin hucky voice dinsa yace "shutup stupid girl kisani kums tunda har qaddararriyar wahalar qaddarar data sameki har kika amincewa dasu dady akan aurena to ina mai baki shawarar da kiyi gaggawar tanadar maganin ciwowwoka iri iri wanda zakiyi guxurin tafiya dasu qasar da zamu, yana gama fad'an haka ya tureta daga 6arin jikinsa tayi taga taga kamar zata fadi sai kuma dinging table din dake wajen ya tokareta har wani plate din tangaram dake bisa ya fado tuss qasa da qarfi ya fashe, annah dake shirin fitowa daga dakinta danta dauko cazbahar ta data manta nan bisa kujera a falo dazun tunkan ta fito daga dakin suka jiyo tana fad'in "kai waye anan haka da wannan barnar kuma?, haba ay da wani mugun sauri mahabeer ya shige wata 'yar duhuwar surdado mai kwana wacce take gefen dining table dinda suke ya fuxgo ummu hani ta dawo kwance bisa lafiyayyen qirjinsa dayake rigar jikinta tamfar best take mai siririn hannaye sam kuma batta da nauyi amman kuma ba'aze ce mata sharara bace dudda tana sleeping dress ce doguwa.
toshi kuma kayan baccin jikinsa pajamas ce ya daura baikuma daure madauran jikin gaban rigar ba hakan yasa lafiyayyen kwantaccen gashin qirjinsa taji ya tsikarar mata enlargement din mamanninta ga kuma wani irin qaqqarfan riqo dayayiwa arms dinta mai mugun zafi jin azabar ta isheta ne yasa ta wage baki kenan zata rusa masa ihu babu shiri yayi wuf ya danna mata bakinsa cikin nata yariqe lips dinta gam, tayi tayi amman tagaza qwace kanta daga garesa saida ya tabbatar annah takoma dakin ta bayan tagama fad'an na cewa ina amfanin irin kayansu na gayu da tsautsayi Kadan zai fasasu, yana shirin cire bakinsa daga nata ne yaji ta kama lebensa na qasa ta gartsa masa cizo da teeth dinta a firgice ya sake ta tayi sama da gudu shima kuwa ya rufa mata baya da gudu ta shige daki tana qoqarin danna jamlock ne ya sa qarfinsa gaba day'a ya banko qofar dakin nata ya shigo da hannu day'a dan dayan hannun nasa da shine yake kare jinin dake zubo masa daga qasan lebensa data ciza, zaro idanuwa tayi ganin yanda yayo kanta gadan gadan kamar mayunwacin zaki.
jada baya baya ta farayi harta had'a bayanta da jikin qofar toilet dinta ta tsaya tuni idanun ummu hani suka raina fata tahau rarrabasu ba shiri, ganin datai babu sarki sai Allah ne tuni ta had'a hannayenta waje day'a tace ''yaya amakson Pleass and please kayi haquri bazan qara ba"!!,
maganar takeyi amman kuma idanunta a runtse suke gam jikinta na kyarma, dai-dai lokacin mahabeer ya iso gareta tareda damqe kafadunta biyu da hannayen sa yana jijjigata da qarfi tareda dauketa da wani lafiyayyen mari jikake tassss..!!!


*Xexen Fasaha*
f.o.w.
[10/11, 2:48 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

*🌏impacting valuable knowledge and Entertainment*
*is our concern🀝🏻*.

Afuwan fans nayi mantuwa inata sawa hjy laria sunan hjy larai kuyi haquri sunanne kemun maimaitainiya amman ynxu ku riqe da kyau hjy laria take ba hjy larai baπŸ€πŸ»πŸ˜„

*dedicated to mom manal maqociyar q'warsuwar khalilπŸ€ͺ*

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ4⃣0⃣
🌊🌊🌊
idanun ta a runtse suke gam jikinta na kyarma,
dai dai lokacin mahabeer ya iso gareta tareda damqe kafadunta biyu da hannayen sa yana girgza ta da qarfi tareda dauketa da wani lafiyayyen mari jikake tassss,!!! da qarfi ummu hani ta qwalla uban ihu dan jin tsananin yanda azabar zafin marin yayi mata shigar bazata, ingijeta yayi tafada jikin qyauren toilet din saigata cikin toilet tayi qasa warwas tana zaro idanuwa.
ganin datayi ya shafa jikinsa yaji babu belt taga ya nufi inda cazar wayarta ke jone ya fizgota da qarfi yayo kanta, da gudu kuwa ta yunqura ta miqe tsaye ta banko qofar toilet din ta saka lock ta jingina bayanta da jikin qofar tana sauke ajiyar zuciya banda tsinewa mahabeer babu abinda zuciyarta keyi hannunta na bisa kumatunta tana sosawa da akaifu,
da qarfi taji yana dukan qofar yana cewa"ki bude kofan nan wlh nagaya miki, banzar yarinya kamar ke har kin isa ki fiddo mun jini ga jikina?! tana jinsa tayi banza dashi haka yaita dukan qofar amman ko girgiza baiba qofan dole yasashi yayi q'uta tareda yarda kebel din cazar ya bar wajen ya koma d'akinsa ya shiga toilet ya wanko jinin da leben nasa ke zubarwa yasa d'an magani a wajen tareda kwanciya bisa gadon zuciyar sa kamar zata fashe masa kuwa dan baqin ciki, yana cikin wannan halin quncin ne harya samu barci yayi galaba a kansa.
a toilet kuwa saida ummu hani ta tabbatar da fitarsa sama da awa daya sannan ta samu cikin sanda ta fito daga toilet din tayi saurin murzawa qofar key ta dawo ta zauna gefen gado tana qyalqyata dariyar oho dai, danko ba komi tai masa abinda tasan zai kwana cikin baqin ciki shima yau, baqin cikinsa da rashin walwalarsa shine cikar burinta daman, haka ta kwanta cikin farin ciki da annashuwa.
washe gari da safe suna zaune falon qasa itada nabeela da momy harda annah saiga dady mua'zzam sun shigo shida dady Muhammad baffa kaddo na bayansu, nan su annah suka gaiggaisa dasu sannan dady mua'zzam yace
"daman dai akan maganar mahabeer ne da ummu hani shine naje wajen baffan nata nida alhj Muhammad muka gaya masa batun kuma shima cikin ikon Allah yayi wa mahabeer lamunin auren ummu hani, inda dai ita din ta amince kamar yanda ya buqaci jin hakan daga garemu ya fahimci kuma daga ummu hani din har shi mahabeer babu wata matsala a tsakani mafarin kenan annah harya biyomu nan dan yai muku godia sabida gobe ne zasu koma gida inda alhj Muhammad yasamu madadin sa".
annah tace "to baffa mun gode Allah bar zumunci"
baffa yace "mukeda godia annah haqiqa ba mutane da yawa sukeda halinku ba na kyautatawa al'ummar annabi ba, mudai tsakanin mu daku sai godia Allah saka muku da mafificin alheri, "amunn" cewar su.
Alhj Muhammad yace "to baffa gobe insha Allah zamu bika qasarku dan suma sauran dangi da 'yan uwa naku susan da zancen shirye shiryen auren, kuma baffa muna neman alfarma zuwa juma'a mai zuwa ta kasance itace ranar d'aurin aure na yaran sabida tafiyar da zasuyi din dud cikin satin nan take itama" shiru baffa kaddo yayi zuwa can yace "to masha babu komi Allah shi kaimu lokacin darai da lpia".
da "aminn" kowa na wajen ya amsa, duban ummu hani nabeela takeyi wacce tunda aka fara maganar nan bnda wani irin futinannen faduwan gaba babu abunda ke shigar ta kanta na duqe qasa ko qwaqqwaran motsi ma ta kasayi.
baffa yadan jima nan sannan ya koma,haka su dady sukai masa rakiya.
ganin yanda ummu hani take takure yasa momy umaimah taita jansu da fira har saida taga ta dan saki jikinta sannan tace "kuje wajen momy ni'ima ku karbo mun saqo kunji ku 'yan albarka, dato suka amsa tareda miqewa tsaye suka bar falon, suna shiga falon gidan kuwa suka isketa zaune a falon tana kallon tashar sunna tv. gaisheta sukayi suka zauna bayan sun fada mata saqon momyn.
cikin murmushi tace "to twince din umaimah ku jirani kadan ina zuwa,, wata yar qaramar hanya tabi ta wuce bedroom dinta bata jima ba sai gata hannunta daukeda wata leda mai sheqi qarama ta miqawa ummu hani tace "to gashi sai ku kai mata ko, nabeela tace "kai momy kin iya girki, dan wlh tunda na shigo falon nan muke jin qamshi ko ummu hani?
d'an mintsininta ummu hani tayi cikin rad'a tace "kin fiye surutu sister, haka nan ummu hani taji tana tsananin jin kunyar momy ni'ima a yau fiye da kullum ma, ita kanta batasan dalilin ba.
momy ni'ima tace "kaji nabeela Friedrich ce nikeyi nd vegetables kuma nasan yanzu ta ma ida dafuwa ku zauna na zubo muku, da sauri ummu hani tace
"a'a momy munma qoshi ay, nabeela tace "tab sai naci nikam, kuma wlh momy itama tana son Friedrich kawai dai tsirfa ne irin nata, hararar nabeela kawai ummu hani takeyi a boye, momy ni'ima tace ''ah haba 'yata ummu ki saki jikin man kibar d'ari d'ari nanfa gidan kune kema, keda yadace kikawo wani yaci amman keza'ace ana fama dake ma ashe?, sunne kai ummu hani tasa keyi qasa sosai tana sakin murmushi tareda murza zara zaran fararen yatsunta.
tashi momy ni'ima tayi tace "yawwa kokefa amaryar d'ana mahabeer insha Allah, bari na dawo, tana fita ummu hani ta dubi nabeela tace "nashiga uku sister kinji itama tasani ashe?!, nabeela tace "toya sonki sister? aminiyar mah cefa ita d'in taya kuwa zataqi sani? momy na kanta ta buga mata waya ta sanar da ita yarinya dan jia dana fito daga dakinki bayan kin kulle knki toilet din nan to ay nan falo na zauna wajen mah din har naji tana waya ma tana sanarwa mutane bikin harda maman wannan banzar hannat din, waike kin zata mah ta dauki maganar bikin nan naku da sanya? tab agaishe ki to" shiru ummu hani tayi takasa furta komi, momy ni'ima bata dau mintoci ba sai gata ta dawo da qaton plate cikeda abinci wanda yaji tsokokin kaji kota ina ciki sai tashin qamshin dad'i yake, da juns a gefen plate din abuncin kala kala shima tace ''yawwa yarana tom ku sauko yanzun nan ku cinye sa tas kafin na dawo,, ahaka ta fita da kular abincin su baffa danta kai musu suma kamar yanda ta saba kullum.
tana fita nabeela tace "sauko sauko mici sister dan so nike muje gida in gwada miki wani suprise, dubanta ummu hani tayi tace "suprise wane iri kuma knn? murmushi nabeela tayi tace "kedai yi shurunki koma miye kya gani da idanunki, haka suka fara cin abincin suna fira sai ga momy ni'ima ta dawo tace yawwa ku cinye tass saina qara qaro muku ma, zaro idanuwa ummu hani tayi tace "laaaa a'a momy jinake ma cikina ya kusan fashewa dan tsaban cikarsa".
nabeela tace "bawani nan kinji ta momy cikinta fa wlh intaci abinci ko dagowa baiyi shafe zaki gansa kamar ma irin bataci komi ba amman kinji tana cewa wai cikinta zai fashe dan cika... maganar nabeela ta katse jin an banko qofar dakin da qarfi an shigo, wata gajerar mata ce baqa sosai mai uban jiki taci adonta sosai na wani uba uban less ja, ta yafa gyale a saman b'arin kafad'anta tareda kashe kallabi kamar wata 'yar bariki tana tafiya cikin taq'ama jikkarta a sagale ga hannunta tana qwas qwas da takalmanta tana tauna cwingum qas qas a haka ta shigo cikin tsakiyar falon gidan tana harare harare ko sallama batai ba,
Momy ni'ima na ganinta saida taji gabanta ya buga sosai dan yau batasan wane kwandon masifar hjy laria (kishiyarta) tazo sauke mata ba, a hankalin ta bude baki tace "hjy laria sannunki da zuwa ga waje nan ki zauna,,katseta hjy laria tayi cikin masifa da cewa "ke dalla niki rufa min baki haka nan kinibabbiyar mata kawai kinbi kin shanye mun miji sai kin ga dama sannan kike sako mun shi yazo wajena ko? , to wlh bari kiji dud irin asirin da kike zabga masa inada labari kuma wlh ki kuka da kanki kamar yanda nasa akaimun maganin wannan shegiyar 'yar aikin naki indo har can garinsu na tura akaimun maganinta to kema wlh ki kuka da kanki danni ba'a takani a zauna lpia a rayuwa! , tana gama fadin haka ta juya zata bar wajen saita dawo falon da baya kadan ta nuna momy ni'ima da d'an yatsanta manuni tayi mata tas tas dashi tace "kuma wlh in kika kuskura yau banga mijina cikin gida na ba nima saina lafira ya fiki jin dadi banza dangin mayu kawai",, tana kaiwa nan ta fice daga falon harda bugo qofa da qarfi bumm! nabeela ta dubi momy ni'ima tace "momy wannan kuma wacece haka? murmushin takaici momy ni'ima tayi tace "abokiyar zama nace hjy laria, ummu hani tace "to shine take miki haka wannan cin mutuncin momy?
girgiza kai momy ni'ima tayi tace ni ai nasaba da ganin irin haka ummu hani sama da shekara da shekaru kinga kuwa ai yaci ace na saba da halinta ko, shiru sukayi duknsu kowane da abinda zuciyar sa ke saqa masa na gameda rashin mutunci irin na hjy laria.
ganin kamar sun shiga damuwa yasa momy ni'ima ta canza zancen da cewa "kufa cinye abincin nn ko qwara bn son ganinsa a plates dinnan" tayi maganar cikin murmushi, haka suka ci abincin sosai da zasu tafi ta hada musu kayan makeup na sosai sannan suka wuce wajen su mama bintey sun jima can sannan suka dawo gida suka baiwa momy umaima saqon daga ban nabeela taja hannunta suka juya gidansu.
a can kuwa momy ni'ima tana zaune a bedrom dinta tayi tagumi tun bayan sallar azhur da tayi ta fad'a zurfaffan tunani na hjy laria, hankalin ta tashe afili take tambayar mitaiwa inna indo kuma ni ni'imatu? kaiiiiii nashiga 3,
kaddai tanada sa hannu daqin dawowar inna indo gidansu a lokacin? wai ita shin hjy laria da yaushe zata saduda da duniyar ne?, ita sam bata son rigima da tashin hankalin mafarin knn hadda hakan tasa taqi sake zamansu waje guda da ita hjy laria din amman Ashe gudun gara tayi zuwa gidan zago? hakan ma bata tsiraba knn??! tana cikin wannan zurfafan tunanin ne taji an zauna gefenta tareda janye hannayen da tayi tagumi dasu, da sauri ta juya ganin dady Muhammad ne yasata sakin ajiyar zuciya tace "baban boy da yaushe ka shigo ban jika bama?, cikin murmushi yace "kinyi zurfi da tunani daman bazaki san nashigo ba, maganar yake amman can qasan zuciyar sa tabashi cewa qilan babu shakka tunanin danta mahabeer ne abin ya dawo mata shiyasa take wannan tunanin,
dan murnushin qarfin hali ta saki tace "afuwan habibina hankalin yayi balaguro ne shiyasa banji shigowar kaba, muje dining na shirya maka lunch ko, fitowa sukayi falon nanta hau shirya masa abuncin a dining table, saida yaci sosai yayi hamdala nan ya fara jan ta da fira cikin son boye gaskiar abunda ya faru momy ni'ima ta dube shi tace "habibina amman yau dai gidan hjy laria zaka inda daman jian abunda ya hanaka zuwan kamar yanda kasa ba sabida watom masassaran data saukoma lokacin, dady Muhammad yace "hakane amarya ta zanje yau insha allah dudda bn son rabuwa dake dai dai da minti 1 amman dole na haqura na kwatanta adalci a gareku a matsayinku na mata na ku duknku, murmushi momy ni'ima ta dan sakeyi batace komi ba, sai zuwa can tace "hjy laria dinma bata jima da fita ba ay, lokacin datayi wannan maganar dady Muhammad yana qoqarin kiran layin wani abokinsa, nan da nan kuwa ya yanke kiran ya maida hankalin sa kacokam zuwa gareta yace "whatt ni'ima ta? Hjy laria tazo gidan nan fa kikace?! tomi ya kawo ta inda nai mata kashedin zuwan nata nan tuni ba tun yauba, inda nasan zuwanta din ba haifuwar d'a mai ido zai yiba yanda take jarababbar nan,? cikin sauri momy ni'ima tace "a'a kwantar da hankalin ka zuwa tayi kawai muka gaisa kuma ta tafi
babu wani tashin hankalin da tayi mun, abunda yasa ta boye gaskiar abunda ke nan kuwa tasan muddin yasan gskiar sai yaci mutuncin hjy laria sosai fiye da yanda ita din tai mata, ita kuma gashi sam bata son taga tana zama sanadiyyar dazai dinga jin zafin uwar gidansa hjy laria din.
Kallon ta kawai yake amman yasan tadai boye ne kawai amman yasan cewa wlh ko wuqa da varandami aka kawo gabnsa zai iya fadin hjy laria bata shigo gidan nan ta ficesa salin alin ba batareda ta zubar wada ni'ima samfur din nata ba na kalar cin mutun cin nata ba kamar yanda ta saba.
Sharewa kawai yy sukaci gaba da fira dan baison yawan maido magana baya.
anan ne yake shaida mata tafiyarsu Niger din gobe tace "to shiknn AllAh kaiku lpia asamo abinda ake nema kuma"
da amin ya amsa yana fad'in "amma samu ai insha Allah. nabeela da ummu hani ne zaune bisa gadon nabeela a gidansu, duban agogon hannunta ummu hani tayi tace "sister lokaci na tafiya inason tafia gida kada mah taga shirun yayi yawa kuma gashi sai jana da fira kike tun dazun suprise dinma da kike magana akai ya gagara ki gwadamun" tayi maganar tana hararar nabeela din. qyalqyacewa da dariya nabeela tayi tace "kai amaryar yaya amakson kin cika gajen gaquri kam,, hararta ummu hani tasakeyi tace ''mtsss wai dan Allah sister saunawa zan gaya miki kidaina hada ni da wannan azababben mutumen? nabeela tace "taya kuwa zan daina had'aki dashi bayan kun kusan qara jonewa a babban tsibirin ma'aurata taqarashe maganar cikin tsokanarta, fuuuuu ummu hani tayi fushi ta miqe tsaye zata bar dakin da gudu nabeela takamo hannunta 1 tace "afuwan sister inda bakison maganar na daina, qin yadda ummu hani tayi data qara zaman saida nabeela ta shawo kanta da qyar2 sannan ta haqura suka zauna a gefen gadon hannunta nabeela ta daura gefen kuncin ummu hani tace "sister miye yasami fararen kumatun kin nan naki naga yayi ja haka?, tana maganar cikin mamaki tabe baki ummu hani tayi tace "hmm! kad'an daga cikin aikin amakson knn!!, zaro idanuwa nabeela tayi tace "kaddai kice mun shine sila sister? girgiza kai ummu hani tayi tace uhmm to inba shi ba waye kike ganin zaimun haka ne? bama ki kalli lips dina ba knn kikaga yanda yaqara mayar mun dasu ja sosai ba? da sauri nabeela takai hannunta ga lips din nata tace "aikuwa wlh gashi nan har wani pink pink colour yamayar miki dasu kalar nasa kai wannan amarcin nakufa so matching,hararta ummu hani tayi tace "wlh inkika saki na tashi bazan qara zama ba,
rufe bakinta nabeela tayi tace sorry sister na, harararta ummu hani tasa keyi tareda jan wani d'an siririn tsoki,
wardruf nabeela ta bude ta fiddo wasu manya manyan baqaqen ledoji ta dawo saman gadon ta zazzage su dukknsu nan, tace "ga gudummuwata nan sister dan nasan kina son inglesh wears sosai shiyasa na karb'i kud'i wajen dady na isassu tun jiya da dare naje boutique na siyo miki su shine nike cewa zan miki surprise dasu ay".
cikin mamaki dajin dad'i ummu hani tace "kai sister thanks so much wlh amman wannan dud ni day'a basumin yawa ba? cikin murmushi nabeela tace "kinfi qarfin irin haka sau dubun dubbata a wajena sister, kuma basu miki yawa ba kamar yanda kika fad'a , murmushi ummu hani kawai takeyi tana d'aga kayan tace "kai sister kayan nan akwai a tsokani shari'a sosai a cikinsu fa? dan na gama kusan ma dud su sukafi yawa saikace wata wacce zatayi auren soyayya bare in rinqa yiwa hubbyn nawa kwalliya dasu? ,sai nikega irinsu dake yadace saiki dinga yiwa amrinin dinki gayu dasu, girgiza kai nabeela tayi tace
"a'a wlh sister bazan dauka ba dan nikena sawowa snn kuma inada tabbacin cewa zakiji dad'insu kuma zakiga amfaninsu nan gaba,
dan aunty sadiya qanwar momyna tace mu'amala da wad'an nan kayan suna qara jawo hankalin miji akan matarsa inda da sune matan waje har suke nasarar iya cin galaba akan mazanmu,sai nikuma nikega why to muda mike matansu mizai hana muyi fiyeda yanda su nawajen ke musu,?
yamutsa fuskarta ummu hani tayi tace "hmm sister na kenan inda ake soyayyar knn kiketa fad'a ai badai gani ba da wancen farin mugun,, bnda dariya kuwa babu abinda nabeela keyi tace "kai sister yanzu yah mahabeer d'in ne ya koma miki farin mugun knn, cikin tab'e lips tace "yess shifa da knsa sister bawani ba,tayi maganar tana mai mi miqewa tsaye.
murmushi kawai nabeela tayi tana yar dariya tace "hmm Allah kawo muku mafita mudai muna nan nijeria zamu sha labari daga gareku 'yan qasan turai,, tana maganar ne tana mayarda kayan cikin ledarsu.
banza ummu hani tayi mata harta gama suka fito ummu hani taiwa maman nabeela hjy asm'u sai anjima suka fito tareda nabeela saida sukazo bakin gate tabawa ummu hani kayan sannan tace "by sister zan shigo anjima"
a haka ta juya ta koma gida, ita kuma ta ida shiga cikin harabar gate d'in gidan, da sauri ta b'oye jikin wata bishiya maiyawa daga qasanta koriya ce shar, dan hango sa datayi shida bash zaune can wajen swimming pool inda suka saba zama, tarasa ta inda zatabi dole tadinga bin ta bayan bishiyan nan harta isa ga qofar shiga gidan dud abin nan kuwa datake bash na lura da ita tun shigowarta gate din gidan

Please Login or Register in order to submit comment