Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyauta muddin kika bani dad'in ni'ima irin taki na kwankwad'a"
yayi maganar yana kashe mata idanu da lashe gefen bakinsa irin na cikakkun 'yan duniyar nan,,
a haukace ummu hani ta juyo cikin tsananin takaici dama ga baqin cikin irin muguntar da mahabeer ya gama rad'ad'a mata bata gama shanyewa ba shi kuma yazo gaba ya tusata yana mata maganganun iskancinsa akai,
ai batareda ta san lokacin data d'aga hannunta ta wani yarfawa doctor lurwan wani qwaqqwaran maruka biyu ras bisa kumatukansa masu rai da lpia kuwa, cikin kuka take fad'i
"d'an iskan likita kawai ka matsawa rayuwata?? Mina tsare maka ne? Wai ku dud maza haka kuke ne bakuda imani ne?? koni kaga alamun irin kace watsattsiya?? dazaka tusani gaba da munanan kalamnka wanda badon shi aka kawoni cikin asibitin nan taku ba,??
cikin tsabar takaici tayi shiru ta dafe kanta sannan ta dago tana kallon sa hawaye na zubo mata,,, dud a cikin hausarta da bata fita sosai taci gaba da cewa
"in kuma danshi kake ganin an kawoni bari naje na fadawa wanda ya kawoni din saika qara maimaita masa bitar magungunan daka gama cemin asai mani su insha yanzun,,,,,"!!!
da wani irin azababben sauri doctor lurwan ya zube gabanta tareda kama kunnuwansa bayan yasaki kumatunsa daga radadin zafafan marukan da suka gama ratsa masa kwanya, qwarai yayi mamakin ynda ta iya fidda hannu ta zabga masa wannan marukan, dama haka take da zuciya yarinyar?
yanzu in har ya kuskura taje ta fadawa yalla6ai mahabeer ai ya rigaya da sanin kashin sa ya gama bushewa tuni, wataqila ma hakan na iya janyo masa yayi ta aikin sa.
mafarin knn ya zube gaban ummu hani yana tuba yana ahi da rantsuwar cewa ya daina mata kalar maganganun insha Allah,,,, ya dade a zube kasa gabanta saida yaji ta tsayar da kukan nata sannan ya tashi ya koma ya zauna ko fuskarta ma ya gagara iya sake kallo, a haka yace
"na gode madam ummu hani da ahin ki gareni,, harara ta zabga masa taqi cewa masa komi,, ciga yayi da cewa "amman ban san mike damun kiba madam???
saida ta sake watsa masa harara sannan ta fada masa yanda takejin qafafun nata na matan,,,
nan yayi nazari sosai a gameda yanda tai masa maganar ya fallo wata farar takarda kenan da zummar rubuta mata magungunan da yadace tasha da wnda zata shafa bisa qafafun yaji an turo qofan office din nasa an shigo,
afusace ya dago da zummar ganin waye haka ya shigo masa office ba excuse kuma?? ganin wnda ya shigo dinne yasashi ya koma yayi laqwas,
mahabeer ne ya shigo office din wnda shi kansa samun kansa yayi da fitowa daga motan nasa ya dawo cikin asibitin, anan wata sister budurwa ta gamu dashi mai shegen surutun tsiya da rawan kai sai faman wani kwarkwasa take masa dan kaf fad'in garin nasu babu yarinyar dabata shaida ganin wannan kyakkyawan fuskar guy din mahabeer mua'zzam saraki ba a akwatin television da jaridu ba,,,
Jikinta har rawa yake ganin gata gashi kurkusa nan tahau cewa "am yallabai patient dinka ka dawowa ne?
ko kallonta baiba amman kuma matuqa gaya yanason sanin halinda yarinyar ke ciki mafarin knn daya kasa zaune waje day'a a cikin motan nasa da ya koma ya zauna,
shi dama can tun asalin fari yaji yatsani doctor lurwan shine musabbabin ma dawowar tasa cikin asibitin dan ganin anyi komi a gabnsa saboda tsare lpiar 'yar amanar momyn tasa,,, shiyasa ma har ya iya tambayar ita sister din cikin gimtsewan fuskar tasa da huscy voice nasa yana sake jan ajin sa cikin izzarsa batareda ya ko kalli inda take tsaye ba, shima dan yana buqatar sanin inda yarinyar take ne shiyasa yace
"emm, , tana ina ne???
har wani lumshe idanuwa sister nadiya take sannan ta ce "ay tana office din doctor lurwan ne yana m.....
tunkan ta ida maganar tata yayi gaba abinsa inda yaji amsar da yake son ji to mizai tsaya jira???? da gudu sister nadeeya ta bisa har tana haki ganin Yana niyyar 6acewa ganinta a yanda yake dogon taqin nan nasa na isassun maza,,
tace
"waitt!!,, waitt"!!,, yalla6ai please ,,,!!
tsayawa yayi cak ya dubeta yace "wani abun??
da sauri ta kauda fuskarta daga tasa ganin yanda idanunsa suke cike da wani sirri wanda ta kasa fassara sa ma, tadaiji idanunta sun kasa iya jurar kallon nasa ne,, fiddo phone dinta tayi a aljihun farar riganta ta sistoci tace ''dan Allah in bazaka damu ba muyi selfie mana ko guda day'a ne yalla6ai ,,,"
shiru yayi mata tareda bin wayar da kallo a zuciyar sa yace waisu matan nan almost dinsu basuda kamun kaine komi?
Ya tsani mace da rashin halayen kamewa sam 2,, shiyasa har gobe a tsarin burinsa babu auren hausa fulani,, ita kuwa kallon sa take da fatan Allah sa handsome dinnan ya amunce mata suyi selfie din nan tare kota samu na dorawa a instagram da twitter da face book gamida whatsapp dan ta ciri tuta wajen friends dinta na ganinta da mai farin jini a cikin al'umma manya da qananu,
yaro da kudi abokin manya knn,,
ga kyau ga yaran banki baja baja,, wani Murmushi tayi tace ''please and please yalla6ai accept me my requesting,,, hard'e arms dinsa yayi a chest dinsa ya dubeta sosai sannan yace
"i don't need it,, banda buqatar hakan ok??"
daga haka yayi wucewarsa itako ta saki baki ta bisa da kallo sai daga bisani itama ta juya tabar wurin cikeda sanyin gwiwar ta, fuskar mahabeer mua'zzam saraki ne fall ta mamaye mata zucirya ta,,, wata zuciyar tata ke cewa Allah sarki nadeeya kema kinji abinda dud kowace budurwa keji gameda shi knn muddin tayi tozali dashi tuni take kwaye masa,
farin jini garesa kamar yashi,,,...inji sister fauziyya itama.
shi kuwa gogan naku tsuka yaja abinsa, a haka har ya iso qofan office din doctor lurwan din excuse dinma a ciki ciki yayi sa mafarin knn sukaga shigowar tasa kamar daga sama.
waje ya samu ya zuna tareda harde legs nasa, lap under lap haka yayi zaman nasa ko kallon ummu hani baima sake yi ba tun kallon farkon da yayi mata tun shigowar sa office din, duban doctor lurwan yayi yace
"yaya doctor hope komi normal ???,,,
Cikin sauri sauri da tsoro 2 doctor lurwan ya fara magana da cewa "e..ehh everything it's normal yallabm6ai,,, gama takardar da za'a siyo mata medicine daya kamata tafara sha, yayi maganar yana satar kallon ummu hani dan gani yake kamar zata budi baki ne ta fadawa yalla6ai mahabeer din maganganun da yayi mata na banza., shiyasa gabansa ke dukan tamanin da uku uku a lokacin.
Baima san ita Ummu hani ba daga shi har mahabeer din bata tasu take ba hankalin ta gaba day'a naga su baffanta dabata je wajensu ba yau, kamar yanda ta saba, kuma tasan suma suna cen hankalin su na knta,, karbar takardar mahabeer yayi ya dan duba sannan yace
''ok,,"
duban ummu hani yayi bayan ya rubutawa doctor lurwan check ya basa yace
''oya oya muje inada abinyi,,"
gaba yayi itama tabiyosa a baya Babu abinda take aikawa bayansa dashi illa hararar.
suna dura harabar gidan momy umaimah da annah suka tarbata shikuwa juya kan motan yayi yabar gidan,, haka momy umaimah taita kulawa da ummu hani har tsawon sati sannan qafafun suka sace sakamakon magunguna datake sha,,
da wata safiyan lahadi dataje wajen su baffa kuwa ta fad'a musu ciwon nata har fad'a baffa yayi mata akan taqi bari a gaya musun,
ai koba komi sayi mata addu'a.
duqar da kanta tayi qasa tace "kuyi haquri baffa banason hankalin ku ya tashi ne shiyasa."
son 'yar tasu ya qara tasiri sosai a zuqatansu har kullum suna godia ga Allah daya basu nutsatssiyar yarinya day'a tamkar da 1000.
tajima nan wajen su sai wajen 11 sannan ta dawo gida,,
falo ta dan kwanta da zummar kan lokacin girki yayi ta tashi ta dora musu.
da yake annah ta tafi katsina jia dacen zata tafi wajenta suyi fira.
motsin fitowar momy umaimah taji daga kichen hannunta daukeda cup,, tana ganin ummu tace
''yawwa ummu na kin dawo knn??"
"eh mah bnjima bama ay d dawowa"
"yawwa to taso ki kar6i cofee dinnan ki kaiwa mahabeer Yana can saman sa,, ban san hawa benan nan saboda cikin nan wlh nauyi ne dashi ina nishi ina komi nake samu na hau sa",,
Karba tayi tana fad'in to mah sannu,,
''Yawwa ummu na nagode"
harta fara tafiya momy umaimah tace
''af na manta ummu koma kitchen ki dauko masa tea spon dinsa ki had'a masa dashi kikai ni zan shiga ciki na warwatsa ruwa yanzun zan fito insha Allah "
"to mah,,"
wucewa momy umaimah tayi dakinta ita kuma ummu hani ta shiga kitchen din kai tsaye inda ake ajiye roban yaji da gishiri ta dosa,, taji dadi sosai da cofee din ya kasance mai duhu ne, dan haka ta samu tarugu jawur ta hada da gishiri da tasshi harda citta da karamfani ta zuba ruwa kadan a ciki ta hadesu ta tace, sannan ruwan data tace din ta juyesu cikin cofee din nasa tasa spon ta jujjuya tana sakin Murmushi sannan ta dauko cup din ta fito ta haye samansa ta tura dakin tareda sallamarta,,
jin motsin ruwa a toliet ya tabbatar mata da yana bath ne,, qwarai taji dad'in hakan shiyasa tayi saurin ajiye masa cofee din ta fice daga dakin nasa ta koma falo tai kwanciyar ta tareda lumshe idanun ta tana bitar suratul Muhammad a cikin zuciyar ta cikin jin dad'i,,
koda ya fito daga wankan cikin sauri yake komi dan sunyi dasu bash zasu hadu after 25 mint's zasu zo gidan,,
saida ya sanya kayansa jan T-shirt ne da farin wando jeans, sumar kan nan nasa sai qyalli take ta ko ina zubda qamshin perfume yake, shi mutum ne mai son qamshi a rayuwar sa.
gashine kwance lub lub a fatar jikinsa dukansa,,hakama sajen fuskar sa ba qaramin qara qawata kyakkyawar fuskar tasa yayi ba gwanin sha'awa abin,,,
sai dai fuskar nan datake a tsuke tamm, amman hakan ma datayi ba qaramin qara kyau yayi ba, girarsa har wani tudu tudu tayi sabida tsaban yawanta da cikarta black sosai kamar an d'ora masa ita a seti,
pressing cap dinsa fara ya daura a kai sannan ya zauna gefen bed dinsa ya d'auko laptop dinsa ya d'ora a laps dinsa yana duba wani message da yake tunanin shigowar sa tun safiyan yau,,
tsoki yaja tareda rufe laptop din ganin har yanzu basu turo accepting nasu ba, ,,
(requsting ne ya tura a can wata school dake London akan qara ilimi kan hanyar haqo mai ta hanyar hadin gwiwa dasu turawan,, wanda dama sune suka bude school din suka fara yada manufofinsu akai ga sauran qasashen duniya wanda yasa yanzun haka school din Saura wata 5 ta fara aiki,
dady mua'zzam ne sukayi maganar dashi jia akan ya tuntuba yaji koda sauran gurbi na karbar dalibai a cikinta in bai cike ba, ta hnyar tura musu message nason shiga school din, instead dady mua'zzam yaje sai shi mahabeer din yaje,,
suna son yin hakan ne dan sauqin samun farashin mai ya wadatu a cikin alu'mma ta nigeria a ko'ina, da sauqi mai rahusa.
hannu ya miqa ya d'auki cofee din knn wayar sa tahau ringing baibi ta kan wayar ba dan hankalin sa tafi da ynda yaji copee din na qamshin wasu abubuwan masu dadi yau,, mafarin knn ya q'agu dajin son dandanon sa a cikin bakinsa,, ya kafa kai tareda yiwa copee din wata kyakkyawar zuq'a,,
tsananin zafin copee dinne dawani hatsabibin dandano na wani mahaukacin yaji yaji ya gauraye masa dukkan illahirin qwalwar kansa,, tuni ya shaqi copee din ba dai dai ba ba shiri yasaki cup din qasa tareda duqewa Yana sakin wani uba uban tari da atishawa kala2, kansa yaji Yana jujjuya masa kamar wanda yasha q'waya, ba shiri yasa hannayensa ya riqe kansa da qarfi tuni idanunsa suka dinga yoyo da hancinsa hawaye faca faca a fuskarsa yanda kasan an vude fanfon mono,, Gabaki day'a bakinsa ya mutu mururus, nan yayi baya saman gado yafada dafe da cikinsa dayaji shima yana jujjuya masa,,kukan ainahi yake son yi amman abin ya faskara dan wata azabar tafi gaban wata...


*Xexen fassha*
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿3⃣5⃣
🌊🌊🌊
*H* awaye ne sabbi suketa shatata yana daga a idanunsa, kwance yake ya mimmiqe kamar gawa yana faman hucin numfarfashi,
tari kuwa yayi har yaji babu dad'i gamida atishawa,
banda ciwo babu abinda qirjinsa ke masa kuma a halin yanzu kamar zai 6alle daga jikinsa ya fad'o yakeji sabida suyan radadin zafin.
ya kwashi sama da minti arba'in sannan yasamu tarin ya lafa masa da atishawan,,,
lamo yayi bisa gado jikinsa yayi laqwas Kamar wanda yayi gudun wuce sa'a ya gaji liqis banda numfashi babu abunda yake sake saki,,
lokaci day'a yaji gumi na kwararo masa a kowane ga6a na sassan jikinsa,
tashi yayi ya koma toilet ya cire dukkan kayansa ya sake yo wani sabon wankan ya canza kaya ya tsaya gaban mirrow yana kallon yanda idanunsa sukayi jazirrr dasu har yanzu basu washe ba tukun,
Maganezian ya d'auko yasha ba jimawa yaji qirjinsa yabar zafin da yake masan,
tunani zuciyar sa ta zurfafa yi nayaya akayi yau momy tai masa wannan hadin na lahira kurkusa??
Lallaikm ya leqota ya dawo,,
sakin numfashi yayi yace a fili "momy na nasan matsala aka samu inda ba haka kika saba mun ba,,
haka ya sauko falo adai dai lokacin ne momy umaimah ta fito itama daga d'akinta ta dubesa ganin yanda idanun sa sukayi jazurrr yasata saurin matsowa garesa tana shafa fuskarsa take fad'in "0h ya ilahee mahabeer na! mine ya yasamu idanun ka haka ne suka kad'a sukayi ja ne em?!!
Ummu hani dake lafe cikin kujera tana jinsu farin ciki ne fal cikin zuciyar ta na jin ynda haqarta tayi saurin cimma ruwa na gameda tarkon data d'anawa shugaban mamuguntan gidan, shafa wajen saman maqoshinsa yayi zuwa kwantaccen sajensa ynda yake jin suna masa tsabar zunga har yanzu, kamar yanzu ne yasha abin yakeji,,,
sam yaji bai iya cewa sabida coffee dinta ne daya sha ya tsinci kansa a cikin wanna halin,
a hankali ya saki numfashi gamida d'agowa ya dubeta yace "haka nan naji idanuna namun ciwo momy,, amman kada kidamu zuwa anjima nasan zasu washe insha Allah" qwarai sosai taji tayi matuqar tausaya masa cikin karayan zuciya tace
"Allah shi yarda mahabeer na, amman in anjiman yayi naga idon bai sauya kalan saba gskia dole kaje kaga likitan ido hospital"
a zuciyar ummu hani kuwa cewa tasakeyi ''ni dama ya makancen wlh danaji dad'i sai inga dawane iriyar idon ne zaiyi kalla yayi muguntar mun,, miqewa tayi da zummar fita harabar gidan cen inda ta saba zawa wajen kayan games sai lokacin nema suka lura da ita cikin falon,,
karaf idanunsa ya fad'a cikin nata kanya fidda nasa tayi saurin janye nata idanun tareda sakar masa wata malalaciyar Murmushi wnda yarasa gane ma'anarsa, ita kuwa tayine dan murnar datake cikin ranta fal na ramakon da tayi a sauqaqe.
musamman data ga ynda idanun nasa sukayi jaaaa kamar gauta.
Momy umaimah tace
"ashe daman ummu kina nan falo?,,
cikin sunne kai ummu hani tace
"eh mah yanzun waje ma nikeson dan zuwa wajen inda kayan games din can suke ne"
"ok to shiknn"
cewar momy umaimah.
ummu hani kuwa wucewarta tayi abinta tana faman qunshe dariyar ta.
shikuwa ya rakata da harara tareda kyabe bakinsa kamar yaga abin qyama, shi ta idonsa ma yake ba ita ba musamman ynda yaji suna masa qaiqayi shikuwa ya bada himma wajen murtsukasu da hankicerf din hannun sa, har saida momy umaimah tace ya daina sa wa idon hannu dan hannu shima dafi ne sannan ya haqura ya janye badon yaso ba.
nan ya zauna suna fira da momy saida wayar su bash ta shigo alamun sun iso suna waje sannan yabar momyn shima ya fice wajen,,,
nan bakin ruwa ya taradda mukhtar da bash,
zama yayi sannan sukaba junansu tafi,, bash yabisa da kallo a fuska sannan yace
"kai gifted lpia kuwa idanunka ja haka miya faru ne?? Mukhtar yace
"to nima dai Wlh abinda nike shirin fad'a knn?
Shafa fuskarsa mahabeer yayi zuwa saman idanunsa ya dan yi yaqe Wanda yafi kuka ciwo kad'an sannan yace
"ciwo suke min ne naji a lokaci day'a,, but zasuyi normal insha Allah,
yayi saurin canza maganar da cewa
"inasu Masu'd ne da imran???,,
mukhtar yace
"kai kada dai basu fad'a maka komawarsu cenya ba dan ida had'a masters degree dinsu na final year din nan gaba day'a dai ko??
cikin mamaki mahabeer yabar sake murzar idanun nasa daya komayi batareda ya tuno mgnr momy ba, danshi yama mnta shaf har ga Allah idanun nasa ba qaramin qaiqayi suke cigaba dayi masa ba, shiyasa da hankicerf din hannunsa yaketa murza yanajin dan sauqi sauqi,
sannan ya dubesu yace
"basu fad'an ba, gskia,amman anyi 'yan iskan guys nan wlh,, yaushe ne suka wucen?
Bash yace
"jirgin yamma sukabi jia"
yamutsa fuskar sa yayi yace "may be phone nawa it's switchoff ne tym din, mukhtar yace "nowender dan gskia munyi dasu zasu kirakan dan suma tafiyar ne yazo musu qurarren lokaci,,
yaci gaba da cewa on sturday zamu fara programs na bikina fa shine maganar ma data sa muka hadu nn knn?
Bash yace
"dadyn nata ya dawo knn?,
Mukhtar yace
"ya dawo jia da daddare daga tafiyan nasa, kasan aida tuni angama bikin ma dandai kawai an jirkinta ne ya dawon tofa shine
sai jian yakirani naje anan yace mucigaba da shiri netx week"
bash yace "wow wow kace zamu barje gumunmu lokaci yazo.
"kai dai bari kawai danma baban nata full sunna ne, dayaga fatittikan da zamuyi wlh cewa yayi family and freands kawai za'ayi bai son fate fate"
''ai qwamma dayai maka hakan,
kaji tsohon kirki wlh ya burgeni mani,, cewar mahabeer yana daga kishingiden sa yana sake murzan ido,,
Harara mukhatar ya jefa masa gamida cewa "dan baqin ciki dama haka kk so ai dan kada kaje mata su taya,
yaci gaba da cewa alhamis ne partyn ya kama ranar Friday ne daurin auren,,,Bash yabawa mukhtar hannu suka sake kashewa bash yace
"kai mutumina kace dai an gwanci d zafi zafi,,, mukhtar yace ''toya sanku em?, Kuma in kun gune ku yunqura mana,,
dariya sukayi dukkansu yayinda mahabeer kuwa shi Murmushi kadai ya dan saki,,mukhtar yace "yawwa gifted wai ina balarabiyan gidan nan ne,? Cikin halin ko in kula mahabeer yayi shiru abinsa dan sarai ya jisa kuma yasan wacce yake magana akai bai wuce waccen fitsararriyar yarinyar ba wacce sam baison yaga ana shigo da ita cikim lamurransa shiyasa ya share mukhtar din yayi kamar ma bai jisa ba,,, saida mukhtar din ya qara cewa.
"Kaifa dan iska ne wlh gifted kanaji ina magana kai shiru,,,
Harara mahabeer ya sakar masa da jan idanun sa sannan yace "in gidan baqon kane sai in gani, kaje ka nemota man inka matsu, zakazo ka ritsani da tambaya kamar kaban ajiyan ta?
to kaida matan suka dama saikaje ai,, mukhtar ya kanne ido day'a yace "auu haka ma zakace kaga dan iska??? sharesa mahabeer yasakeyi yaqima tanka masa saima duban bash da yayi yace "bash jiya fa realmadrki ta wuce barsalona da ci daya da rabi,
kaiya kaga wasan??
Tsoki mikhtar yayi tareda ture kujerar sa ya miqe tsaye ya shige cikin gidan,,
da harara mahabeer ya rakasa jiyayi Bash yace kai wasa fa yayi zafi jia ai wlh mutumina naso ace muna tare muka kalli wasan da bansan irin ihun da zan sake maimaita kwatsatsawa ba kamar na ranar nan, wnda har annah taji ta ta fito, dan ita a zatonta wani abun ne ya faru,,
ya qarashe yin maganar yana kyalkyata dariya na tuno dramar ranar suda annah ynda ta kasance,,
Wani sbn murmushi mahabeer ya saki yace
"hmmm ranar ai munsha fad'a daga tshohuwar nan,, shiru yayi yace i missing you annah,
bash yace "Kaddai ta koma kt?
Girgiza kai yayi yace "tatafi jia nina kaita ma, amman cikin satin nan zanje na dawo da ita,, d'an tsuka yayi yace "danma ta matsa da sai taje taga dangi aida saita haqura da xirga xirgar nan haka jikinta zaiyi mata ciwo,,"
Bash yace "annah ai badai son zumunci ba,,,,, zaman mukhar ne wajen ya sashi canza maganar tasa da cewa har kaje ka ganota knn ka dawo?
Dubnsu mukhtar yayi yace "ban sani ba ko kun aike nine? Nida na tambayeku inda take kunban amsa ne koko bare kuji nawa amsar nima?
Mahabeer yace
"dakata mlm ina fatan dai wannan maganganun naka bada niba a ciki ko? Danban tambayeka ba bare,,
banza mukhtar yayi dasu saida ya kunna tabarsa sannan ya fara zuqan abinsa ya dubi mahabeer din yace "ban sani ba dan iska kawai,,
Kwashewa musu da dariya bash yayi yace "Kudai ba qananu 'yan iska bane wlh,,,
sharesa shima mahabeer yayi yaci gaba da firan qwallansa shida bash yayinda mukhtar ya juya musu q'eya yana bawa sararin samaniya feshin hayaqin tabansa,,
Karaf yayi arba da ummu hani wacce tagaji da wasan kayan gamez din ta fito daga wajen ta shigewarta cikin gida,, tunawa da yayi a shigar sa daxun gidan iske momy umaima yayi falon zaune tana kallo wnda shi yaso ace yarinyar ce yayi karo da ita koyaji dad'i amman saiya fake da xuwa yayi ya gaishe da ita momyn,, ahaka yataso yadawo wajen nasu.
ganin yanda mukhtar yake bin hanyar shiga gidan da kallo har wani leqawa yake da kansa yasa suma su mahabeer kai dubnsu wajen,,
Tsoki mahabeer yaja ya dauke kansa daga wajen.
Saida ta wuce sannan ya dawo ya zauna bash yace "wlh kaji haushi mukhtar, kana shirun amarcewa amman kana kalle wa 'yar mutane kyawu? kaje ka kalli na amaryar ka man,, ida zuqe sigarinsa yayi yayar sannan ya miqe tsaye yace nabarku lpia 'yan sa ido kawai, yayi maganar yana kallon agogon sa,, dariya bash yayi yace billahil axeem nasan culub zakaje ynxu dan iskan qarya kawai,,
wlh kazo ka rufawa kanka asiri mukhtar kaga zakayi aure, wlh kabar wannan shedantar da kk yi kodan gobenka yayi kyau,,
gaba mukhtar yayi yana fad'in ''inkai keda goben ka hana taimun kyau dan iskan nan,,, ahaka yashige motar sa ya fuce.
girgiza kai bash yayi yace
"Kai ka sani matsalan kane kuma gskia dai ce bamai hanamu fad'an ta kotai dad'i kokar tayiwa mutum dadi wlh, yanzud duniyar nan da kafadawa mutum gskiyarka babu wuya saiya barka? Yakoma yanama wani kallo na daban kamar maqiyinsa gifted??
Mike damun mutane ne sake for god!!??,,
mahabeer kuwa tun kan mukhtar yabar wajen yana gefe baice musu komi ba kamar baima jinsu amman yanajin komi shirun dai yayi musu dan baida buqatar magantuwa a maganar,
dan jiyake maganar tasu ma hawar masa kai yake,,,
saifa yanzu da shi bash din yake masa wannan tambayoyin, Yana shirin basa amsa ne yaji wayarsa tayi ringing,,yana kallonta har ya katse batareda ya daga ba dan sunan bleesing ne akai yasan kan maganar zuwan dayace zaiyi ne yau kuma yana sane sharewa kawai yayi baiyi niyyar zuwan ba, haka nan ma yaji itama yanajin haushinta. kashe wayar ma yayi gaba dayanta sukaci gaba da firansa da bash anan wajen,
Allah ya temakesa ma bakinsa yabar zafin shine ma qarin nutsuwan tasa.
a washe garin ranar ne momy umaimh taja ummu hani sukaje kasuwa itada tai mata siyayyan kayan sawa isassu, hadda su baffanta taimawa suma, kayan make up dasu English wears gyalulu suma duta sayawa ummu hani din, daga nan wajen Tailor suka nufa tai masa bayanin yanda takeson dinkunan na ummu hani din su su kasance na zamani sosai sosai.
daga nan suka dawo gida, gidan momy ni'ima suka shiga,
har wajensu baffa ummu hani taja momy umaima sukaje ta gaishesu cikin girmamawa tabasu kyautar dinkakkun kayan data siyo musu suma.
har bakin gate ummu hani taje ta kirawo baffa shima yaga kayan.
nan sukaita godia suna jinjina alherai irin na mutanen wanda fa d'azu d'azun nan shima mua'zzam saraki daya shigo gidan wajen alhj Muhammad baffa na zaune bakin get yayi masa kyautar dubu hamsin,
haka jia shima alhj Muhammad yabasa dubu d'ari wai albashinsa dud yawansu fa??? shikuwa wane irin mutanen kirki ne Allah

Please Login or Register in order to submit comment