Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

?"
"Kar kayi fushi commitments ne sukayi min yawa...meke damunka naji muryanka down" shuru dad yayi saida daddy London ya sake tambayanshi sannan ya sanar dashin Aslam ne bashi da lafia ya kuma gayamashi abinda doctor ya fada nan fa hankali Ismail dake zaune kusa da daddynshi ya tashi, nan ya fara kiran number Aslam yana ringing amman bai dagawa. Bayan dad yadawo akasawa Aslam Karin ruwa da allurai cikinta, kafin doctor ya tafi saida ya jaddada masu subawa Aslam kulawa ta musamman.
Baby na zaune kan dinning ita kadai har karfe 9 babu alaman dad da mom, nan taji jikinta yayi sanyi mikewa tayi ta fita waje side din Aslam ta tafi. Afalon ta tsaya tayi sallama mom ta amsa Mata daga bedroom, tsayawa tayi bata shiga cikiba har saida mom tace tashiga cikin, ahankali ta taka ta shiga bedroom din gabanta yana faduwa, tana shiga taga Aslam kwance anayi mashi karan ruwa duk ya chanza kura mashi idotayi bata ankaraba taji hawaye na zubo Mata.

Call dinki yana yimin dadi Zainab Ado madaka Allah ya saka da alkhairi ya tsareki daga sharrin mahassada.馃憦馃挒
[9:43AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 鉂ゐ煉氿煉涴煉熲潳馃挌
SUNE SANADI
庐zuwairat
5鈨�3鈨�

Bata masan hawaye na zubowa kallonshi kawai take, dukda aduniya bata da wanda ta tsana kamanshi amman saita ji tausayinshi ya kamata, Aslam bacci yake amman ba mai dadiba sai juyejuye yake dad ya rike hannunshi da aka sawa drip, mom kuka take har lokacin, dan matsawa kusa dashi tayi
"Sweetheart..." Shuru bai amsaba sai juye2 kawai yake da kanshi, mom takara kiranshi tayi
"Sweetheart..."
"Mom..my" ya amsa mata amman bai bude idoba
"In hada maka tea kasha? " ta tambayeshi, dan girgiza kanshi yayi
"Ba...Zan...Iya..sha...ba..." Aikam nan baby ta fashe da kuka sosai da jin yanda yake magana da kyar, dan karasawa kasudashi tayi tana kuka
"Yaya sorry" Aslam najin muryanta yayi karfin halin bude idonshi Amman bai gani sosai haka yasa ya maidasu ya rufe.
"Mommy ...I ...can't.. See" sabon kuka mom tafara tanacewa
"Bari in kawo maka tea kasha zaka fara gani" shuru yayi bai ce komaiba, mom mikewa tayi da niyyan hada mashi tea da kayan shayin dake side dinshi, baby takowa tayi kusa da mom
"Mommy bari in koma in dafa mashi ruwan tea da kayan yaji ko zaifi sha" babu musu mom ta barta ta tafi. Bayan kaman minti ishirin ta kawo flask da tea cups, hada mashi tea din baby tayi sannan ta mikawa mom, zaunar dashi dad yayi mom tafara bashi tea din, ahankali ya dinga amsa har yasha rabi sannan yace ya koshi, da kanshi ya koma ya kwanta, baby Kara matsawa kusa dashi tayi
"Sannu yaya" kara bude idanuwanshi yayi yafara kallonta gani yayi tayi mashi kyau sosai, rufe idanuwanshi yayi tare da juya Mata baya. Sai wajen karfe shadaya dad yakorasu suje su kwanta, dad wurinshi ya zauna bayan drip din takare dad yacire mashi don doctor ya nuna mashi ta yanda zaiyi in ruwan ya kare, Aslam komawa zaune yayi ya kalli dad
"Daddy" ya Kira dad cikin muryan Mara lafia. Dad kallonshi yayi
"Yes son"
"Daddy please kayimin rai... Kabari...in bar kasan nan...kafin ayi wedding din baby" dad shuru yayi yana kallon Aslam. Aslam yacigaba dacewa
"Dad...in har akayi bikin baby Ina nan gidan nasan da kyar Zan kwana da raina" dad still shuru yayi yana tunanin maganar Aslam, sai yaji dama tilastawa baby auren Aslam yayi amman yanzu ya makara
"Don't worry daddy London zaizo Kano gobe, in zai koma sai Ku tafi tare" cikin ran Aslam cewa yayi duk uban azaban da nake sha bai isa ace za a auramani baby ba? Amman wai bazai iyaba don yafi son baby akaina. Ba kara cewa komaiba sai tunanin yanda zata kasance in daddy London yazo sannan sai adua yake Allah yasa tare da yayanshi suka zo. Komawa yayi ya kwanta bayan dad yabashi magungunanda doctor yace abashi.
Wacegari tun da sassafe baby ta ciga kitchen ta hada mashi pepper soup dayaji kayan hadi, bayan tagama sai kuma ta kasa Kai mashi saida mom ta sauko ta cemata Mata
" mom.. ga pepper soup kisa akaiwa yaya" dadi sosai mom taji cikin ranta dukda tana tunanin hakan bazai chanza wani abuba.
"Thank you habibty" mom tace mata sannan ta sa daya daga cikin masu aiki sukai mashi. Mom har ta Kai bakin kofa sannan tajuyo ta kalli baby
"Kin je duba yanda yayanki ya kwana?" Mom ta tambayeta, ahankali ta girgizawa mom Kai alaman Aa
"Maza dauko dankwalinki muje"
"Mommy in tafi mana ahaka tunda kaina a gyaretake,
"To muje" mom tace Mata, binta tayi suka tafi wurin Aslam. Alokacin Aslam na zaune kan gadon ya kishingide da bango yana sanye da gajeren wando da singlet, hannuwanshi rike da juna da ka ganshi kasan tunanin kawai yake, dad ya shiga wanka, da sallama mom ta shiga dakin baby na biye daita
"Sweetheart ya jikinka?" Mom ta tambayeshi amman don tsananin tunani baijitaba
"Sweetheart.." Saida mom ta sake kiranshi sannan yajita, maida idonshi yayi Kansu, karaf sukayi 4eyes da baby nan take baby ta dauke idonta daga kanshi amman shi sai kallonta yake kaman ranan yafara ganinta, haka yacigaba da kallonta har saida mom tayi guarantee muryan sannan ya dauke idanuwanshi dasukayi ja tare da cikowa da hawaye, mom kusa dashi ta matsa
"Sweetie.. Ya jikin?" Ta tambayeshi amman bai amsaba ya maida idanuwanshi kan baby yana yi mata kallon ki tausaya mani, itakam baby irin kallon da yakeyi mata yasa ta kasa gaidashi balle ta nemijin yanda ya kwana, baby dataga kallon baya karewa ta fita daga dakin amman still Aslam bai bar kallon inda ta tsayaba, dafashi mom tayi
"Sweetheart" mom ta kirashi, kallon mom yayi tare da fadawa jikinta yana kuka, mom rungumeshi tayi tana shafa bayanshi
"Haba sweetie.. Meye haka?" Cikin kuka Aslam yace
"Mommy wallahi nasan mutuwa zanyi"
",stop saying that... Babu abinda zai sameka" cikin kuka ya sake cewa
"Mommy ni kadai nasan abinda nakeji cikin zyciyata..mommy azaban yayimin yawa...plea do something before I die of heart attack" mom facewa tayi da kuka tanacewa
"Haba habibi..yanzu ko tunanina da daddynka da sultan bakayi? Mu bakasonmu...yanzu kafison baby akanmu? Har kakecewa zaka mutu don baka sami baby ba?" Cikin kuka Aslam ya fara girgiza kanshi
"Mommy duk duniya bani da kamanku Amman abinda nakeji game da baby sai ya bambanta da abinda nake ji game DA Ku...mommy jinake kaman in bude heart dina in cire son baby in yada don yanzu banayiwa baby kallon kanwa kallon wacce naso takini nakeyi mata..."kuka ne yaci karfinshi, yanayi mom tanayi, yacigab dacewa
"Mommy nasan cewa don abinda nayi matane dakuma bata maku ran danayi yasa tashin farko Allah ya jarabceni da son wacce bata sona" daga kanshi yayi yana kallon fuska mom da fuskanshi da yayi fatafata da hawaye yanacewa
"Mommy ban taba soyayya ba...dan Allah mommy ki yafemin ko Allah zaisa in daina son baby" mommy share hawayen fuskanshi tayi sannan ta maida kanshi kan kirjinta tana shafa kanshi
"Sweetheart kabar fadin haka...na yafe maka..kuma kana iya shiga falona Amman on one condition" da sauri ya sake daga kanshi yana kallon mom
"I will do anything to earn your trust again mom"
"Zaka yimin alkawarin baxaka kara taba macen da ba matankaba komin rintsi "
"Wallahi nayimiki qlkawarin bazan Kara taba wata maceba"
"Then clean your face ka gayamin inda keyi maka ciwo" goge fuskanshi yayi amman still hawaye na zuba kaman mace
"Mommy heart dina ne keyimin ciwo"
"Sorry Allah zaibaka lafia kaji?" Gyadawa mom Kai yayi, da ka ganshi sai ka rantse dan yarone nan kam dan shekara 32 ne
"Tashi muje in zuba maka pepper soup dinda baby ta dafa maka" kallon mamaki yayiwa mom
"Mom yauce baby ta Iya dafa abinci?" Dan daria mom tayi
"Yanzu ake koya Mata" wani kukan takaici yafara yi wai yanzu baby taiya girki kuma bashi zata dinga yiwaba, yanzu duk wayan nan abubuwan saboda za a aurar daita ga sadeeq ne, kaman ya hadiye zuciya don bakin ciki
"Mom banci"
"Stop crying, muje kaci kadan kafin doctor yazo" Kara girgiza kanshi yayi
"Mom bazanci ba ki hada min tea kawai insha"
"Aa habibi, muje kaci kadan sai in hada maka tea ka dora" da kyar mom tashawo kanshi ya yarda yaje can dinning, bayan mom ta zuba mashi pepper soup din ta hada mashi tea mai kauri, spoon yasa yafara Kai ferfesun baki, shuru yayi yana tauna naman ahankali, dagowa Yayi ya kalli mom
"Mommy waye ke koyawa baby girki?" Ya tambayeta,
"Sweetheart yayi dadi KO?" Bai amsa ba yana maijin haushin kanshi
" wasu yan eatry ne muka dauko su koyamata" mom ta gaya mashi, Kara fashewa yayi da kuka yana cewa
" mom na chuchi kaina
"Haba sweetheart meyasa kake son kuka kaman mace ne?"
" mommy bari inyi ko Zan sami sauki cikin raina" ahaka yayi breakfast yana hawaye mom kuma ta biye mashi sai lallashin shi take.
Wajen karfe biyu daddy London suka shigo garin Kano direct gidanshi dake tukuntawa ya wuce Amman Ismail hanashi zama yayi wai dole su tafi ganin jikin Aslam. Daddy London kiran dad yayi yace mashi yasa drivern shi ya zo ya daukeshi daga gidanshi. Without wasting of time driver ya tafi daukosu.
Mom sa masu aiki tayi suka cika dinning da abinci kala2, around karfe biyar su daddylondon suka iso gidan, dad da mom suka taresu, Aslam kam baisan sun iso gidanba don yana bacci, direct main falo aka kaisu Amman Ismail sai kalle2 yake don ganin Aslam, baby saukowa tayi daga upstairs, Ismail kallonta yayi cikin ranshi yana cewa ai dole Lil brother yake samun heart attack sabode ke irin wannan haduwan haka?, daddy London budewa baby hannuwa yayi baby ta fada jikinshi
"Aisha ke kika girma haka? " daria tayi tare da rufe fuskanta, shikam Ismail daure fuska yayi don Allah kadai yasan yanda yake jin haushinta. Gaidashi tayi amman sai ya kauda kanshi gefe kaman baijiba su dad da mom sun ga abinda yayi amman sai suka basar. Wajen dinning aka kaisu daddy London tambayan jikin Aslam yayi dad yace DA sauki yana bacci, Ismail kin zama yayi wai shi sai ya fara ganin Aslam, side din Aslam aka Nuna mashi ya tafi wurinshi, afalo ya ga Aslam kaman ba Aslam din dasuka rabu few months back ba, da sauri Ismail ya karasa wurinshi ya zauna gaban kujeran da Aslam ke kwance sama. Shafa gefen fuskanshi Ismail yayi, nan Aslam ya bude idonshi sukayi four eyes da sauri Aslam ya tashi ya rungume Ismail yana kuka
[9:43AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 馃挌鉂ゐ煉涴煉熲潳馃挌
SUNE SANADI
庐zuwairat
5鈨�4鈨�

Ismail rungumeshi yayi yana shafa bayanshi
"Lil brother ina keyi maka ciwo ka lalace haka" cikin kuka Aslam yace
"Yaya kirjina keyimin ciwo...yaya tunda Kai doctor ne don Allah ka taimaka ka cire min heart dina kar in mutu" "stop saying that... Wai cin har yanzu baby batasan itace SANADI wanna ciwon takaba"
"Yaya ta sani amman shi don't give a hute if I die" murtuke fuska Ismail yayi
"Amman this girl is heartless... Wai shin uban waye Wanda takeso da bazata hakura saboda halin daka ciga sabida itaba ?" Shuru Aslam yayi baice komaiba yacigaba da kuka,
"Common stop crying like a girl...kalli yanda idanuwanka suka rine sabida kuka"
"Yaya kukan nan yana sani samun nutsuwa cikin zuciyata"
"Naji amman ka daina kuka haka nan..ina magungunan da kake sha?" Mikewa Aslam yayi da kyar ya ciga bedroom dinshi ya dauko magungunanshi ya kawowa Ismail, dubasu yayi daya bayan daya sannan yace
"the medicine are OK ammam da akwai wasu dazan kara maka so kaje ka shirya mu shiga cikin gari mu sayosu tunda kafini sanin gari" ba musu Aslam ya koma cikin bedroom dinshi ya sanya black jeans da v neck polo. Har sun fito waje Aslam ya kalli Ismail
"Yaya bari inje in gaida daddy kafin mu tafi"
"OK to mutafi" suka tafi falo tare har lokacin dukansu na zaune kan dinning harda baby, sultan kuma yana zaune kan cinyan daddy London. Suna shiga daddy London ya daga Kai ya kalleshi, mamakine kwaance kan fuskanshi don raman da Aslam yayi. Gaishe shi Aslam yayi ya amsa sannan yace
"Kaikam Aslam me yaja maka irin wayannan illness din kana yaronka?" Aslam sunkuyar da kansa kasa yayi baice komaiba. Itakam baby ganin irin kallon da Ismail yakeyi mata yasa ta mike ta tafi upstairs.
"Yanzu ina zaku?" Dad ya tambayesu,
"wasu medicine din zamu karo " Ismail ya amsawa dad
"To sai kun dawo" dad yace masu, sai suka wuce, daddy London daina cin abincin yayi yakalli dad
"We need to talk" yacewa dad
"When?" Dad ya tambayeshi
"Now" daddy London ya amsa mashi
"Ka gama cin abincinka mana" dad yace mashi. Daddy London bai saurareshiba ya mike tare da saba sultan a kafadanshi yayi hanyar waje. Dad bayanshi yabi itakuma mom tasa aka gyara dinning. Daddy London wuri ya samu ya zauna acikin garden, shima dad kara sowa yayi ya zauna kusa da wanshi. Daddy London kallon dad yayi
"Meke damun Aslam? Cos nasan haka nan yaro kaman ci bazai yi developing ulcer, hawan jini da ciwon zuciyaba"
"To ya zanyi rashin lafia ne kawai" dad ya amsa mashi daddy London kallon rashin yarda yayi mashi
"Da akwai abinda ya haddasa masa wayan nan ciwokan so shinake so ka fadamin" shuru dad yayi for a while sannan yace
" wai baby yake so itakuma baby tace batasonshi tana da Wanda takeso shine ya kasa daukan hakuri..." Daddy London ya katse shi dacewa
"Wane irin magana kake fadi haka?...baby ta chanchanci ta zabawa kanta miji ko Kai ya kamata ka zabamata miji...kunjimin zancen banza, kamanka Ashe bakasan abinda yakamata kayiba?"
"Ai yaya banason in sata tashiga wani hali" afusace daddy London yace
"To shi Aslam yakamata ya shiga wani haliko? Tunda shi ba haihuwanshi akayiba" dad shuru yayi na dan lokaci sannan yace
"Kasan mutane na iya cewa don bani na haifetaba yasa nakeson yi son zuciya nasan watarana Aslam zai manta da sonta" ran daddy London Kara baci yayi
"Wane irin maganan ban a kakeyi haka...mu ina ruwan family dinmu da abinda mutane zasuce..kuma uban waye ke baisan kai ka raini Aisha ba...barima in tambayeka, halinda da Aslam yashiga bai nuna maka son gaskiya yakeyiwa Aisha ba?...anyway bari in bar wasting time dina da kai...anjuma Zan gayawa baby na yanke hukunci hadata aure da Aslam inyaso saitacemin batasonshi" nan fa gaban dad ya Fara faduwa don bayason wanshi yasan ainahin dalilin dayasa baby batason Aslam
"Yaya nidai aganina da kabarta ta auri wanda take so"
"In ban isa da yarankaba ai sai ka hanani" daddy London na kaiwa nan yamike ya bar dad azaune wurin. Dad sai tunanin me zai biyo baya in har abinda Aslam yayiwa baby ya fara tonuwa cikin family dinsu.
Su Aslam basu dawo daga cikin gariba sai bayan magrib. Suna parking Aslam hanyar side dinshi yayi yana tafiya ahankali, Ismail kallonshi yayi
"Lil brother Ina zaka kuma?" Ismail ya tambayeshi
"Yaya inason idan kwantane kafin lokacin sallan ishai yayi"
"To abinci fa?" Aslam dan bata fuska yayi sannan yace
"Yaya bazan iyaciba" Ismail bai karacewa komaiba ya shiga main house shikuma Aslam ya shiga side dinshi ya kwanta kan doguwar sofa yana tunanin yanzu bikin baby bai wuce less than wata dayaba.
Bayan ismail ya shiga falo yaga babu kowa ya tambayi side din mom aka nuna mashi, yana shiga falonta itakuma mom tafito daga bedroom dinta. Kara gaisawa sukayi sannan Ismail yacewa mom
"Anty please kisa baby ta kawomin abinci side din Aslam" mom amsa mashi tayi da ok, mikewa yayi ya koma ita kuma mom kiran baby tayi awaya ta fada mata takaiwa su yayanta abinci a side din Aslam. Nan gaban baby ya Fara faduwa don duk tsoron Aslam da take tafi tsoron Ismail gashi ba daman tayiwa mom gardama, haka ta mike ta tafi kitchen ta jira abinci cikin katon tray ta nufi side dinshi, tana zuwa gaban wurin ta tsaya gabanta na faduwa sosai tafi minti biyar awajen sannan ta saduda ta shiga ciki, sallama tayi Amman babu Wanda ya amsa Mata haka yasa tsoro ya Kara kamata, gaida Ismail da kallon CNN tayi ya amsa ciki2 ko kallon inda take baiyiba, bata kalli Aslam ba don idonshi rufe suke amman yanajin muryanta ya budesu yana kallonta, itakuma kan dinning tafara jera abinci. Ismail kallonshi yayi
"Lil brother tashi kaci abinci" ba musu ya tashi zaune yana kallon baby dake jeran abinci, tana gamawa ta juya zata fita Ismail ya juya ya kalleta
"Baby zo nan" yakira nan ta tako zuwa kusa dashi jikinta sai rawa yake
"Wa kikeso ya bashi abinci?....ko baki ganin bashi da lafiyaba" cikinta na rawa tace
"Na...Sani"
"Then kije kiyi feeding dinshi" ya fada mata atakaice batare daya kalletaba balle yasan reaction dinta
[9:43AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 馃挌鉂ゐ煉涴煉熲潳馃挌
SUNE SANADI
庐zuwairat
5鈨�5鈨�

Ismail mikewa yayi ya tafi kan dinning ya zauna ita kuma baby kamewa tayi waje daya, shi kuma Aslam zubawa baby ido yayi don yaga reaction dinta, bayan Ismail yayi balance kan dinning ya daga Kai ya kalleta fuskanshi babu alaman wasa
"Bakijin abinda nace makine ?...koni kikeso in bashi abincin?" Asanyanye baby ta girgiza mashi kai
" then kar ki bari abinci ya huce..kar ki manta ba lafia gareshiba"still tsaye tayi ta kasa daga kafanta, hawaye na taruwa a idonta
"Uncle..." Zatayi magana sai tayi shuru, Ismail kallonta yayi
"Na'am" ya amsa mata, baby shuru tayi batace komaiba, Ismail ya sake cewa
"Kinsan in abincin nan ya huce sairanki ya baci...kinajina?" Da saura ta gyada mashi kai, shikam Aslam kallonta yake tamkar mirror, ahankali baby ta taka zuwa kan dinning ta zuba abinci cikin plate sannan ta zuba drink cikin cup ta dawo gaban Aslam ta durkusa, Aslam kam sai kallonta yake baya kiftawa, ahankali ta dauki chokali ta debo abinci zata kai bakinshi, har chokalin ya Kai bakinshi bai saniba saboda hankalishi baya kusa dashi, itama da Kai tayi ta kalleshi cikin idonshi, ido cikin ido suka dinga kallon juna ,baby sai taji gabanta na faduwa da sauri ta dauke kanta, Ismail sai kallonsu yake yana tunanin wow ban taba ganin wayanda sukayi matching kaman Aslam da baby ba, sake kallonsu yayi yasake cewa yarinya kina sonshi amman taurin kai ya hanaki kinashi daman. Baby maida chokalin tayi saboda hannunta dayayi sanyi shikuma kallonta ya hanashi bude baki balle ya ci abincin. Kara diba abincin tayi ta Kai bakinshi hannunta sai kyarma yake at the same time idanuwanta shike da kwalla, ahankali ya maida idanuwanshi kan hannunta dake rike da spoon din sai lokacin ya bude bakinshi kadan ta zuba mashi abinci lumshe idanuwanshi yayi ya cin abinci ahankali. Shokali uku yaci ya dauki drink ya sha, Kara debo abincin tayi ta Kai bakinshi amman saiya girgiza mata Kai
"Na koshi" batace komaiba ta maida cokalin, Ismail kallonsu yayi
"Ka cinye dukan abinci" Ismail ya umarceshi
"Yaya na koshi"
"Kai banason gardama" kallon baby Ismail yayi
"Ki cigaba da bashi" ba musu ta shigaba da bashi har ya cinye sauran kadan sannan yace
"Yaya ina Kara abincin nan amai zanyi" saifa lokacin Ismail ya sallami baby. Bayan few minutes suka tafi masjid suna dawowa Aslam da Ismail har su nufi side din Aslam daddy London dake bayansu yakira Aslam da Ismail yace masu suje main falo yanason ganinsu, nanfa gaban Aslam yafara disco, suna zuwa falo suka tadda dad, mom da daddy London, Ismail wuri yasamu kan cushion ya zauna shikuma Aslam ya sami wuri yazauna, mom kam adua take Allah yasa lafia cos batasan dalilin tara su din da akayiba, daddy London kallonta mom yayi
"Kanwata ki kiramin Aisha awaya" ba musu ta dauki wayanta ta kirata.baby kam lokacin ta fito daga wanka tana shafa mai mom ta kirata. Mom nacewa tazo main falo gabanta yafara faduwa amman hakan bai hanata gama shafanta tare da shafa turarukan da mai gyaranta ta bata ta dinga shafawa. Don anata tunanin mom ce kawsi ke kiranta, saida ta gama sannan ta saka rigan bacci mai wando da riga ta tafi kasa, tana sauka falon ya bade da kamshi, tana ganin kowa zaune gabanta ya Kara faduwa gefen mom ta zauna, Aslam daga Kai yayi ya kalleta yana mamakin irin turaren da take shafawa. Daddy London kallon Ismail yayi
"Son bude mamu wannan taron da adua" Ismail adua yayi duksuka shafa sannan daddy London yafara cewa g
"Nasan baku san dalilin dayasa na tara ku ananba...Aslam da aisha, dukanku yayanane kuma bazanyi maku hukuncin da bai dace dakuba...so without wasting of time na yanke hukunci hada ku aure!" Nan take Aslam ya daga Kai yana kalle2, mom itama kallon mamaki takeyiwa dad, shikam Ismail wani irin ajiyan zuciya ya sake inda itakuma ji tayi kaman numfashita zai dauke, shuru kowa yayi babu mai cewa Kala sai kukan baby dayafara tashi, tun tana controlling kanta kar kukan ya fito amman ta kasa ta fara kukan sosai tana yarfe hannuwa, kallonta kawai kowa yake harda Ismail daya hade rai
"Ke!..kukan uban me kikeyi haka..." Ismail ya Dhaka mata tsawa
"Ka kyaleta in ban isa daita ba sai ta gayamin" daddy London ya fada afusace, baby Kama bakinta tayi da hannunta amma still bata bar kukaba , Aslam kam gani yake kaman marfaki yake donshi sam bai yarda cewa shi zai auri baby ba. Baby kam ganin dad da mom basu ce komaiba yasa ta kwanta kasa tana rolling kaman yanda ta sabayi aikam nan Ismail yayi kanta, afusace dad Aslam ya dakawa Ismail tsawa
"Don't you dare touch her" Ismail komawa yayi ya zauna yana huci
"Uncle kalli fa yanda take kuka kaman ance kasheta za a yi" Ismail ya fadi haka. Baby cikin kuka sosai tafara cewa
"Daddy wallahi banasonshi...mugune...azzalumi..." Afusace Ismail yakara mikewa daddy London daka mashi tsawa yayi yazauna sannan yajuya ya kalli dad Aslam
"Ayuba wane irin tarbiya kayiwa baby da bata ganin girman manya?" Dad goge zufan goshinshi yayi sannan yace
"Ba rashin tarbiya baneba, she has her reasons" daddy London bai saurari dad Aslam ba yajuya wajen baby
"Aisha, nasan har yanzu bakisan abinda ake nufi da soba don haka wannan ba matsala bane...sannan kice Aslam mugune azzalumine, me yayi maki dakika bashi wayan nan sunayen" baby batace komaiba sai kuka kawai take, falon tsit bakajin komai sai kukan baby, Aslam sai kallonta kawai yake kuma sai tunanin abinda zafaru next yake. Dad yace
"Yaya kayi hakuri kar ka ga laifin Aisha, shi Aslam ya bata kanshi wurinta hi" Ismail ne yayi saurin cewa
"Amman uncle ai komai yana wucewa abu kusan shekara biyar Amman wannan muguwar yarinyan ta kasa yafe abinda yayi Mata...this girl is very mean" ya karashe magananshi yana nuna baby da dan yatsa. Mamakine yakama dad da mom, suna tunanin ashe Ismail yasan abinda yafaru. Shikam daddy London sai kalle2 yake don yagane inda magana Ismail ya dosa amman bai ganeba, Ismail yacigaba dacewa
"Uncle har mutum ana kashewa kuma Wanda ya hallicemu ya yafemana amman wannan yarinyan ta kasa yafe abinda Allah ya kaddara?..." Daddylondon ya katseshi dacewa
"Wane magana kakeyi haka? ...uban meye yayi Mata!!? " nanfa Aslam ya fara kuka sai kallo yakoma kanshi, kuka yake sosai mai ban tausayi don ita baby dan tsararawa tayi tana sauraronshi, daddy London kallonshi yayi
"Wane irin sakarcin banza ne wannan...meye abin kuka anan?" Ya tambayi Aslam sannan ya kalli Ismail
"Kai kuma meyayi mata " Ismail shuru yayi baice komaiba, dad Aslam kam gabanshi sai faduwa yake, mom kuma hawaye kawai take, uban gayyan banda kuka babu abinda yakeyi. Daddy London kallon dad yayi
"Menene yayi mata???" Ya sake tambayansu amman babu Wanda ya sami courage din bashi amsa, still daddy London tambayansu yayi sai sukaji Aslam cikin kuka yace
"I....raped her" daddy London kalle2 yafara ko zai sami Wanda zaice masa karyane amman sai yaga kuwa ya sadda kanshi kasa, Ismail ne yayi karfin halin cewa
"An dade da wannan abun fa...."
"Shut up!!!" Daddy London ya daka mashi wani irin rikittan tsawa, yanayin fuskanshi ya chanza sannan ya juyawajen dad
",when did this happen?" Ya tambayi dad
"Shekara biyar da suka wuce" dad ya amsa masa a sanyanye, shuru daddy London yayi for a while sannan yace
"Kuma ni ban chanchanci ku fadamin ba" dad kallon daddy London yayi sannan yace
"Yaya kayi hakuri ...abun kunyan ne yayi mani nauyin fadi" shuru kowa yayi, babu abinda kake ji sai kukan baby dana Aslam, mom ma hawaye take, cikin kuka Aslam yasake cewa
"Daddy... I'm sorry..."

Please Login or Register in order to submit comment