Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Banza tayi dashi batace komaiba
"I said repeat what you said!" Ya daka mata tsawa, baki ta tabe ko gizau tace
"Zan koma England... Kuma da baby zani..." Karkada kai daddy baby yayi sannan yace
"Dare me.." Yana kaiwa nan yafice daga dakin.

Wacegari Wanda yakama Friday wasu yan family din mom suka Fara shigowa garin kano.
Abangaren su Aslam kam tun wayewan gari wasu daga cikin friends dinshi suke kiranshi kan waazin dazaayi kasancewan waazin ya kasu kashi biyu daya na baby da friends dinta Wanda zaayi agidan dad Aslam sai dayan na Aslam da friends dinshi Wanda zaayi a Sheraton hotel. Tunda wuri Aslam tare da Yusuf da Mahmud suka shirya don zuwa ansan kayan da aka kawo na wurin mom.

Abangaren daddy baby kam gari na wayewa ya tafi gidan daddy London don sam bai dauki maganar maami serious ba. Yana fita itama tafito da traveling bag dinta sai Yusriyya bayanta don umar da Maryam cewa sukayi basu zuwa sai angama bikin baby basu san baby take shirin daukaba, batace masu komaiba ta barsu tayi tafiyanta. Adaidai gidansu Aslam tayi parking, fita tayi ta umarci Yusriyya data jirata acikin mota. Tana shiga falo taga ba kowa kasancewan wasu daga cikin yanuwan mom dasuka zo suna wani bangaren da aka tanada saboda baki, wayanta ta dauka takira mom ta sanar daita cewa tana falo tana jiranta duk yanda mom ta roketa tashigo ciki ki tayi, tun anan mom tasan cewa akwai matsala, mom na saukowa ta kalleta
"Haba sister saiki ki shigowa? Kaman ke bakuwace? " maami batace komai ba sai dan murmushi tayi. Mom zata Kira mai aiki takawo Mata abinsha amman maami tace abarshi sannan ta gyara zamanta tafara cewa
"Sister don Allah kar ki dauki abinda zanyi dazafi...gaskiya bazan Iya jurewa ganin anyiwa Aisha auran doleba...don haka zan tafi da baby inyaso nan gaba inda rabon Aslam ne mijinta sai ayi auren" tunda tafara magana mom tafajin faduwan gaba amman tana cewa zata tafi da baby mom tafaraji kaman numfashinta zai dauke, da kyar ta daure tace
"Sister.. Halin da baby take ciki yana damuna nima amma ba yanda zanyi...don son dakike yiwa manzon rahama kar ki daukemin baby...wallahi banajin son Aslam cikin raina kaman yanda nakejin son baby cikin zuciyata...please" ta karashe magananta muryanta na rawa kaman zatayi kuka, maami mikewa tayi takoma kusa da mom tare da dafa kafadanta
"Sister kiyi hakuri..in har bantafi da baby ba, babu abinda zai hana ayimata wannan auren kuma hankalina bazai kwantaba..so nayimiki alkawarin Zan maido maki yarki unkomai ya lafa" mom kuka tafariyi itakuma maami sai rarrashinta. Suna cikin haka su Aslam suka shigo falon, da sauri mom ta daga Kai ta kallesu tana cewa
"Please ku bata hakuri kar ta tafi da baby na..." Tafada tana kuka, Aslam najin abinda tace yaji kafafunsa sun kasa daukanshi nan inda yake ya zauna kasan tiles. Yusuf kam da sauri yakoma waje yakira daddyshi yasanar dashi abinda kefaruwa, yakoma cikin kaman bai Kira kowaba. Mom goge hawayenta tayi takira baby awaya tace mata ta shirya ta fito. Aslam hada kai yayi da gwaiwa yana kuka Yusuf da Mahmud na rarrashinshi, bayan kaman minti ashirin baby ta sauko cikin wasu tsadandun swiss atampa peach, tana zuwa maami ta mike
"Let's go" tace mata atakaice, baby kallon mom dake kuka tana kallonta tayi, Aslam daga kanshi yayi yana kallonta, ahankali ta taka taje wajen mom, rungume mom tayi itama mom ta rungumeta tana cewan
"Please habibty don't go" kuka tafarayi tana Kara rungume mom. Ahankali maami tajata tamike ,sukafara tafiya nan kukan Aslam dana mom ya karu, har sun kar bakin kofa baby tajuyo tana kallon mom, nan tafara kokarin kwace hannunta amman maami tariketa gam tsalle2 tafarayi tana kuka tana cewan
"Maami...kiyi hakuri..ban zuwa...ki barni wajen mommy na..." Still kokarin kwace hannunta take amman maami tajata tana cewa
"Stop being silly... Let's go" da sauri Mahmud yarike mata dayan hannun yanacewa
"Maami dan Allah kiyi hakuri ki gyaleta tunda tace..."maami katseshi tayi dacewa
" kai...sakammata hannun" Mahmud kin tsaki yayi don yasancewa Yusuf ya Kira parents dinsu
"Maami please kiyi hakuri...Please" yakara cewa yana rike da hannun baby, itakama baby sai kuka take tanacewa
"Maami kiyi hakuri karki tafi dani...yanzu inason..auren..inason...yaya..as..." Bata karasaba sukaji an bude kofan falo, gabankin dayansu suka juya sai ga daddy London, daddy KSA, daddy Aslam sai daddy baby, fuskan daddy baby kaman fuskan horror saboda yanda ranshi ya baci. Dukkansu basu ce komai ba suka wuce cikin falo da sauri maami ta saki hannun baby, shima Mahmud hannunta ya saki, da gudu baby ta fada jikin mom tana cigaba da kuka. Daddy baby hannu yasa cikin aljihunshi ya debo kudinda baisan iyakansuba sannan yace
"Yaya..ga kudin sadakin Aisha... A daura masu auren yanzu!!!" Daddy London ansan kudin yayi, yayi counting dinsu yaga 48k without wasting of time daddy London ya daura auren Aisha da Aslam kan sadakin dubu arbain da takwas.

Duk Wanda yaji dadin page dinnan yayi DAB ingani. Nidai ganawa馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃槣
[9:54AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 鉂ゐ煉氿煉涴煉燄煉涴煉�
SUNE SANADI
庐zuwairat
6鈨�2鈨�

Aslam kam kaman mafarki yake don har munsunan kanshi yayi don tabbatar daba mafarki yakeba, har lokacin yana zaune kasan tiles. Baby kankame mom yayi tayi tamkar za a kwaceta sai kuka take mara sauti at the same time gabanta da harbawa da sauri,
"Yaya kawai a tafi daita gidan mujinta kawai sai inga iskanci..." Inji daddy baby, daddy London daga mashi hannu yayi, baby Kara rike mom tayi gam,
"Ku bamu wuri" daddy london yafada. Ahankali Aslam yamike yana maijin wani irin farinciki acikin zuciyanshi. Ko kayan dasuka zo dauka bai tuna ba yayi hanyar waje Yusuf da Mahmud suka bi bayanshi, tafiya kawai yake batare dayasan inda zashiba, hanyan bakin gate yakama maimako don tsananin farinciki, Mahmud da Yusuf suka kalli junansu tare da tafawa da karfi suna daria sannan Mahmud
"Angon baby kadawo nan ga motanmu chan inkuma akasa zaka saboda farinciki sai muji" sai lokacin ya tuna da mota zasu. Yusuf kyalkyale da daria yayi yana cewa
"Ka kyaleshi kasan ko cewa yayi duk rananda aka daura mashi aure da baby zai take garin Kano da kafa?" Aslam kam jinsu kawai yake amman shi tunanin dayake daban, tunanin yanzu baby ta zama mallakinshi kawai yake, yanzu yazama mujin aisha..donshi haryanzu gani yake kaman bada
gaske baneba. Gaban mota yazo ya tsaya amman tunani ya hanashi bude kofa, Yusuf yazo kusa dashi yarike kafadanshi yadan maidashi gefe sannan yabude mota yaturashi cikin kaman wani mara lafia, Mahmud sai cewa yake
"Ango bada kanka asare kaje gida kace yafadi" Yusuf yaja mota suka bar gidan Aslam sai murmushi yake kaman anyi mashi albishir da gidan aljanna. Duk yanda Mahmud da Yusuf suke zolayanshi ko kallonsu baiyiba balle ya tanka masu.
Su Aslam na fita mom da baby suka hau upstairs. Daddy London fada yayiwa maami sosai inda maami ta nemi maigidanta ya yafemata saboda ta ketara umarninshi. Nan ya yafe Mata donshi har cikin ranshi baijidadin yanda baby takomaba haka yasa baiga laifin maamiba dayawa. Haka suka yanke hukunci za a shigaba da shagalin buki sannan zaasu karayi wani daurin auren saboda bakin dazasuzo.
Aranan akayi waazi, amarya tasha kyau harta gaji amman banda hawaye babu abinda takeyi. Suma Aslam suna chan a Sheraton hotel suna chan waazi inda babban malamin kabeer gombe yayi masu waazi, Aslam mamaki yayi dayaga sadeeq donshi sam baiyi tunanin zaizo ba, sai wajen magrib aka gama waazi. Aslam neman yafiyan sadeeq yayi kan irin rashin mutuncin da ya dinga yimasa, nan sadeeq yacemashi inda bai yafemasa ba da bazaizo ba. Har rungumejuna sukayi.
Abangaren baby kam ana gama waazi suka koma dakinta da kawayenta harda amira kanwar Mahmud. Mai gyaranta takawo Mata magani tasha amman taki ammasa, matan batace komaiba don tasaba cos tun rananda akace Aslam zata aura tabarshan maganin. Matan side din mom ta nufa, da sallamanta tashiga cikin, mom da wasu sisters dinta na zaune, gefe kuma mommy London ce sai mommy KSA. Hajiya ummi guri tasamu gusa da mom ta zauna sannan tace
"Hajiya gaskiya inajin tafiya zanyi tunda zama a bashi da amfani" mom kallonta tayi
"To ya akayi kuma?" Mom ta tambayeta
"Wallahi Hajiya baby batashan Maganin nan...dazunma nabata amman taki amsa" hajiya ummi tafada
"Shine bazaki ci uwartaba?" Inji mommy London tafadi hakan, mikewa tayi tana kallon Hajiya ummi
"Muje ki kaini wajenta " hajiya ummi mikewa tayi tafita mommy London da mommy KSA nabiye daita har suka isa dakin baby, fada kwando2 suka dingayiwa baby, baby sai kuka take tana basu hakuri nan suka sata yimasu alkawarin shan maganinta kai ta gyada masu alaman eh. Nan Hajiya ummi ta kawo Mata ta shanyeshi duka.
Around 8:00 Aslam ya kira number baby for the first time, don tunda ya sake Mata Sim card ya dauki number ta amma bai taba dailing number taba sai yau, ringing yake amman baa daukaba har ta tsinke, Kara dialing number yayi, yafara ringing kaman sau hudu sannan ta dauka, cikin muryan Wanda bai dade da gama kukaba tace be
"Hello" Aslam lumshe idanuwa yayi don yanda muryanta yayi mashi zaki kaman yau yafara jinta
"Hello" takara cewa, sai lokacin Aslam yace
"Amaryata how are you?" da sauri baby tacire wayan daga kunnenta tana kallon wayan, Aslam yakara cewa
"Aslam's bride" baby kurawa wayan idotayi not saying a word, Aslam yakara. Cewa
"Haba my wife,..ina yimiki magana baki amsamin ko?...no problem Zan Rama" kuka baby tafarayi, Aslam lumshe ido yayi sannan yace
"Wai my bride baki gajiya da kukane?" Ya tambayeta, dukda wayan ba kunnenta yakeba tanajin abinda yake cewa, Aslam yacigaba dacewa
"Kinci abinci?.." Ya sake tambayanta, baby hararan wayan tayi tana tunanin shi ta abinci yake dan iska, Aslam yace
"Kinsan wallahi inayimiki magana baki bani amsa ranki zai baci don Ina iya gayawa daddy London yasa akawomin matata yau...kuma kinsan ina iyawa" nan fa kukan baby takaru, Aslam sauraron kukanta kawai yake, yafi minti biyar yana sauraron muryanta saiyaji kaman yaje har gidansu ya dauketa ya rarrasheta
"Aisha..please stop crying... Kinsan am not a bad husband" kukanta Kara volume yayi tana tunanin wai selfish Aslam good husband gaskiya saidai agarin da babu mazan kirki Aslam ya kashe murya kaman namaijin bacci yacigaba dacewq
"Sweety it's because of the way I force myself on you before right?" Baby bata amsa mashiba sai kukanta kawai take yacigaba dacewa
"Am sorry.. Ki yafemin...in aka kawoki kici ubana har saikinji zuciyanki ya huce" baby batace komaiba donta san bata isa tace zataci ubanshiba don ko kadan bai daukan raini. Kukanta kawai take, cikin sanyin murya Aslam yace
"Good night... I love you" ya katse wayanshi ya koma falon, yana komawa falo Mahmud ya kalleshi yace
"Ango yanzu bazamuyi bachelor eve din bako tunda yanzu Kai ba saurayibane"
"Ai wallahi saimunyi" inji Yusuf, Aslam kam baice komaiba sai murmushi kawai yake don yasan bazasu gane irin farincikin dayake cikiba. Baby kam sai tunani take wai yanzu ita Matan aurece kuma wai Matan Aslam kuka takara fashewa dashi tana tsoron irin zaman dazasuyi dashi sai adua take Allah yasa kowa da side dinshi.

Wacegari yakama asabar, aranan akayi mothers day a commercial hotel inda su dad sukayi fathers day a Sheraton hotel. Aranan aka kawo wata makekiyan banner Wanda ke dauke hotunan Aslam da baby aka lika a gidan. Aranar lahadi sukayi kauyawa party, tun karfen biyu akeyiwa baby kwalliya sai wata da aka dauka don daukar video coverage sai dauka take, kwalliyan yan kauye akayi Mata, sai aka daure mata atampa sai rigan swiss lace sai dankwallin wata atampa daban, tayi kyau sosai. Shima Aslam yana Chan yana dressing shima sai daukanshi ake. Karfe hudu suka tafi wajen gari, sukasha shagalinsu, Aslam kam banda kallon matanshi babu abinda yakeyi. Sadeeq ma sai kallon Yusriyya yake don kammaninsu da baby tabaci. Sai bayan ishai suka dawo gida. Ranar Monday sukayi bride and groom football inda team din Aslam sukaci team din amarya 3:1. Ranar Tuesday sukayi pick and obey party. Abubuwa kala2 aka rubuta cikin paper duk abinda ka chanko to sai kayishi ko kuma a anshi dubu hamsin hannunka ko kuma su amshe maka waya inya kai dubu hamsin, sannan akaidansu kayan jikin mutun sai kudinshi ya kai dubu 70.

Please manage let's continue tomorrow inshaAllah.
[9:54AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 馃挍馃挌鉂ゐ煉燄煉氿煉�
SUNE SANADI
庐zuwairat
6鈨�3鈨�

Aranar Tuesday din dazaayi pick and obey party, baby blue flowy gown aka sa mata sannan aka daura mata light pink head sai vail mai sharara shima pink tun tana shirya ake daukanta video kaman kullum tana fitowa mutane dake falo suka dau guda, fuskan baby daure babu alaman farncikin tattare daita.
Shima Aslam yana chan yasha blue jeans da jacket masu tsadan gaske, motoci take as suka rakashi zuwa inda ake party wayanda duk friends ne. Abakin hotel din da akwai guards Wanda su zasu tantance Wanda ya chanchanta ya shiga da wayanda bazasu shigaba wato marasa gate pass da wayanda kayan jikinsu bai kai tsadan 70k ba. Jamaa kyan wurin da guys da yammatan dake gurin bazai faduba, don duk guys da budurwqn dazaka gani mai ji da kanshine cos yayan manyan mutane, sai bayan hour daya baby da wasu friends dinta suka iso wurin, nan wayanda basu san baby ba suka dinga mamakin kyanta, yammata kuma suna jin Aslam bai sami class dinshiba don anasu tunanin tayiwa Aslam karanta. Tana shiga hall din duk suka mike tsaye yammata sai gulma suke. Kanta kasa amman fuskanta babu alaman faranciki daka ganta kasan dole yasa tazo wurin. Mc sai kirari yakeyi mata, wurin da aka tanada Mata kusa da Aslam ta zauna batare data kalli inda yakeba. Ahankali tadan juya takalleshi sukayi 4 eyes ta galla mashi harara tare da tabe baki, duk Wanda ke wurin ya lura da abinda tayi Aslam ma yayi mamakin rashin kunyanta gaban mutane, baby kam da shawaran Yusriyya take amfani. Baa bata lokaciba mc yafara bawa Aslam kwandon linkakun papers hannu yasa ya dauki daya, mc yace yakara daya tunda shine ango, Kara dauka yayi sannan mc ya mikawa baby ta dauki nata, wani irin mugun kallo ta watsa mashi, Aslam hannunta ya Kama ya matsa yatsunta da karfi, da sauri ta daga kai ta kalleshi suka hada ido ya murtuke fuska sannan yace ahankali
"Pick it now" ba musu ta dauki daya, mc yakara cewa ta Kara daya ta dauka tana hararanshi har lokacin Aslam bai saki hannuntaba, saida tafara jan hannunta sannan ya saki hannunta. Bayan nan mc ya mikawa kowa na cikin hall din, saida aka kammala sannan ya ajiye basket din ya dauki lasipica ya koma gefen Aslam ya amshi takardanshi, yabude saiya ga anrubuta
"Ask me anything" mc kallon jamaa yayi ya nuna masu duka suka dau shewa sannan mc ya kalli Aslam yace
"Me kafiso ajikin matanka?" Gaban baby ne yafara bugawa don tasan Aslam bashi da kunya. Aslam kallon baby yayi from head to toe yana shafa sajenshi ahankali sannan yace
"Her boobs" dukan wurin suka dauki ihu baby kam kaman ta nutse don kunya, mc amsan dayan paper yayi yabude yaga anrubuta
"Tell us how you feel about your partner " Aslam ya amshi microphone yafara cewa
"My partner is everything to me...wit kohout her my world is over" aka dauki tafi, sannan mc yakoma wajen baby ya amshi papers dinta, ya bude na farkon yaga
" kiss your partner" mc yafada da karfi duka suka dauki ihu suna cewa
"Kiss...kiss...kiss...." Suka dinga fada amman baby ko side dinshi bata kallaba balle tayi niyyan yin abinda suke cewa, ihu suka cigaba dayi. Aslam dan matsawa kusa daita yayi yarike mata kafada tare da juyar data ta fuskanceshi sannan yace
"Kiss me" baby fara kokarin kuka tayi, Aslam ya hade rai kaman bashiba, ya kwantar da murya yace
"Kar ki sake kiyimin kuka..and kiss me now ko kuma kinsan sauran" dukda Yusriyya tace ta bar soronshi Amman sanin halinshi yasa ta dan mikar da wuyanta har saida bakinta yakai dai2 bakinshi ta dan shafa bakinta kan nashi sannan ta kauda kanta tare da dan goge bakinta, mc ya karbi dayan paper hannunta yaga an rubuta
"What character did you love about your partner" baby ta suke fuska sannan tace
"Gaskiya bashi da halinda nakeso" kowa kallon juna suka farayi Aslam kaman ya nutse don bakinciki. Hade fuska yayi, haka suka cigaba da shakiyancisu, Aslam kam babu abinda yakeyi sai hakon baby.
The following day which is Wednesday akayi kunshi wurinsu Aslam kuma friends dinshi sukayi mashi party bankwana da rayuwan samartaka wato bachelor eve. Aranar Thursday sukayi Arabian night inda amarya ta saka Arabian gown black sai ango yasa white jallabiya sai yanmata sunsa pink Arabian gown tare da short blue himar sai dukkan guys sun sa jallabiya. Fadin irin kyansu is a waste of time don banda walkiya babu abinda wurin yake, Aslam bai wani sakarwa baby fuskaba don haryanzu bai manta disgin datayi mashiba. Itama baby fuskanta babu walwala.
Ranar Friday aka Kara daura auren Aslam DA Aisha kan sadakin 150k, daurin auren daya samu hallatan manyan mutanen gida da waje.
Ranar asabar akayi yinin biki, gidansu Aslam ba wurin saka kafa saboda jamaa. Still a ranan akayi reception, amarya Tasha wani expensive lace golden sai head ja ango yasha babban riga white da brown hula sunyi kyau sosai. Yan high table sunsha kyau don fadin sunayensu zai iya cinye dukan page din, ankon wurin ya kasu kashi2, tsaya fadin yanda akayi reception din is a waste of time amman dukwanda yasan dream wedding haka yake. Suna dawowa daga wurin reception akawuce daita gidan daddy London nan taga daddy KSA, dad Aslam sai daddynta waazi da nasiha sukayi mata sosai banda kuka babu abinda takeyi daganan aka kaita wajen maami, itama nasiha tayi Mata amman daga baya tafashe da kuka don ganin yanda baby ke kuk脿. Gida aka maidata gurin mom, mom itama fashewa tayi da kuka tana rungume daita, sai mommy London da yanuwan maami suka dinga yimata nasiha Amman ko jinsu batayi sai kukanta kawai take, wani draman saida akazo daukanta don kaita gidan mijinta. Baby kuka take tana cewa
"Mommy kigaya masu kar su tafi dani gidan yaya Aslam... Mom dan Allah kar kibari su rabani dake please" mom kuka kawai take tana tunanin irin zaman da Aslam da baby zasuyi, baby rigan mom tarike gam tana kuka wai kar tabari su tafi daita, da kyar aka kwaceta daga jikin mom tana ihu kaman wacce malaiku zasu kai wuta. Har wajen mota aka kaita akarufe mata fuska da mayafi amman ta yadda gyalen tayi waje da gudu aka kamota aka sakata cikin mota sai gidan Aslam. Mutane baki suka bude don girman gidan, baby kin fita tayi. Da kyar wata yayan maami ta banbarota daga cikin mota. Tundaga bakin kofan side dinta aka suba wasu red rose flower har Cikin falonta, wasu candles masu kamshi aka kunna ta koina a dakin,dayan dagacikin bedroom din aka kaita, shima dakin da gadon tamkar anyi masu decoration don daga kan gadon har kasa flowers ne. Wajen karfe 10 kowa ya tafi yarage daga maryam, Yusriyya, baba asmau sai amira, baby sai kuka take har muryanta baya fita, Yusriyya sai fada takeyi mata tana cewa
"Wannan kukan banza dakikeyi zaisa ya rainaki, nasha gaya miki karki bari mutum yagane kina tsoronsa amman bakijin...rubbish" maryam hararan yusriya tayi.
Around 10:20 Aslam dasu Mahmud duka suka shigo gidan, Aslam babban riganshi ya cire ya mikawa Yusuf sannan yace
"Gashi ka ajiyemin cikin wardrobe dina....good night" Yusuf kallon mamaki yayi mashi
"Bazamu rakaka dakin amaryaba?" Harara Aslam ya watsa Mashi sannan yace
"Ubame zakayi awurin matata"?" Dariya Mahmud yayi
"Kai kyaleshi muje...yagagara yasa baby kuka...please brother kabi ahankali kar zumudi yasa ka balla kanwarka" Aslam tabe mashi baki yayi acikin ranshi yana bakicikin fyaden dayayiwa baby.
[10:05AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 馃挍馃挌鉂ゐ煉熲潳馃挍
SUNE SANADI
庐zuwairat
6鈨�4鈨�

Ahankali yabude kofa yashiga falo yabi koina da kallo wani irin farinciki ya ziyarci zuciyanci
"Wai yqnzu baby tana cikin gidan nan kuma as my wife... Alhamdulillah" daya daga cikin bedroom din side dinta yakalla yaga ba kowa, bedroom din tsakiya ya bude fuskanshi dauke dawani irin murmushin jindadi. Yana budewa ya murtuke fuska da yaga su Maryam
"Me kuke jira anan?" Ya tambayi maryam don bai lura da baba Asmau ba. Maryam sunkuyar da kanta kasa tayi, kallon baby data hada Kai da gwaiwa tana kuka yayi don wani sabon kuka tafara dataji muryanshi. Sake kallonsu yayi
"Baku jina ne?" Ya Kara tambayansu. Baba Asmau ce tace
" saurayina ai nan zamu kwana" sai lokacin Aslam ya lura daita, dan girgiza Kai Aslam yayi
"Gaskiya baba kuzo driver ya maidaku gida" ya fada muryanshi babu alaman wasa. Yusriyya kallon agogon hannunta tayi sannan tace
"Yanzu fa karfe 10:30 gaskiyan kabari mu kwana anan" tafada muryanta babu alaman tsoro. Wani irin mugun harara ya watsa Mata
"Uwar mara kunya ko karfe biyun darene tafiya zakuyi...na baku minti 3 kufita" baba Asmau baki tarike dukda tasan kadan daga cikin halin rashin kunya shi kenan. Hannu yasa cikin aljihunshi yana kallon baby da sai kuka take kaman ranta zai fita, amira da maryam mikewa sukayi sannan baba Asmau da Yusriyya suka mike, baby daga kanta tayi da kumburarun idanuwanta ta kallesu, da sauri ta sauka daga kan gado tarike kafafun baba Asmau tana kuka tana basu hakuri kar su tafi, still Aslam kallonta kawai yake, maryam ma fashewa tayi da kuka ta bar dakin amira tabi bayanta, Yusriyya ma fita tayi harta Kai bakin kofa sannan ta dawo ta durkusa gaban baby ta sa bakinta cikin kunnen baby tace
"Ki kulle kofanki" Aslam na tsaye yana kallonsu Amman baiji abinda ta gaya mataba but yasan ba abun arziki baneba, Yusriyya tazo wucewa ya rike gashin kanta tacikin mayafin kanta
"What did you tell her?" Yusriyya ko gizau batayi ba ta daure fuska sannan tace
"See me see wonders...ni da kanwata bazanyi Mata maganaba...please free my hair" Kara rike gashinta yayi
"Daman ina hakonki don ban manta abinda kikayimin kwanaki bayaba..To Wallahi in baki kiyayeni ba saina ci ubanki kuma gidan nan yagagareki shigowa...idiot, get out of my house" yana kaiwa nan ya wullata falo itakuma tabi bayanshi da harara, baba Asmau kasa tafiya tayi don yanda baby tarike kafafuwanta gam, Aslam ya karasa wurinsu, cikin wani irin husky voice yace
"Ki sakar mata kafa ta tafi" baby daga kanta tayi wasa mashi harara da red eyes dinta sannan tace
"Ban saki" tafada cikin muryanta da baya fita sosai saboda yanda ya shake, Aslam kallon baba Asmau yayi
"Wai baba baku gaya mata ba a yiwa miji gardama ba?" Sai yaji baby tace
"Sai anyi gardaman" tafada cikin tsiwa kallon bakinta yayi yaga yanda take ji dafada saiya saki murmushi, dukawa yayi ya kwace hannunta daga kafan baba Asmau, baba Asmau najin kafanta free tayi waje da sauri, baby kokarin kwace kanta take amman takasa, Aslam kam kuramata ido yayi kaman bai taba ganintaba, hannushi daya yarike hannayenta biyu dashi sannan ya rike kugunta da dayan hannun, baby sabon kuka tafara
"Yaya dan Allah kayi hakuri...remember kayimin alkawarin bazaka kusanceniba..." Tafada tana cigaba da kuka. Dan dariya yayi sannan yace
"Ni?...yaushe nayi miki wannan alkawarin?" Cikin kuka tace
"Lokacin da muke falon dad ko.." Dariya yakara yi
"Kin mance cewa nayi inki yarda kin aureni bazan kusancekiba"
"To ba gashi na aurekaba?"
"Ai bake kika yardaba daddy London yasaki" yafada tare da sakin hannuwanta, hawayenta ya goge mata amman wasu zubowa suke Aslam yacigaba dacewa
"Wifey inban kusancekiba, wa Zan kusanta..kuma nasan nan gaba ke da kanki zaki dinga yadani kinacewa mijina raggone" da sauri baby tace
"Wallahi bazan gayawa kowaba" daria Aslam yakari don yadda bby ke magana gashi da kyar muryanta kefita. Kara goge mata hawaye yayi sannan yace
"Angle muje muci abinci sai muyi wanka mu kwanta barci" baby girgiza mashi Kai tayi
"Nayi wanka...kuma banajin yunwa" sakin kugunta yayi yafara cewa
"Ki baryimin gardama inba hakaba bazan daga maki wayan beautiful legs dinaba balle ki shiga aljanna" cikin kuka baby tace
"Ba sai kasami aljannanba....angaya maka azzalumai suna shiga aljanna...? Bayan hannunshi yasa yadan buge mata baki ammam bada karfiba, baby rike gurin tayi tana kuka tana cewa
"Mugu..." Bata karasaba yarike mata hannu yace
" muje muci abinci sai in nuna maki mugunta " aikam nan hankalin baby yakara tashi sai kuka kawai take tanacewa
"Kayi hakuri...nidai bada Kai nakeba"
"Naji" kawai yace yana rike da hannunta sukayi falo, baby lokarin kwace hannunta kawai take amman yariketa gam. Suna zuwa

Please Login or Register in order to submit comment