Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Katseshi daddy London yayi dacewa
"Kafin in bude idona...kabar wajen nan!" Ba musu ya mike yabar wajen yana tafiya ahankali sai kuka yake, daddy London watsawa Ismail wani mugun kallo yayi
"Follow him" ya umarceshi, shima mikewa yayi yabi bayan Aslam, daddy London mikewa yayi ya dawo gaban baby ya jawota jikinshi yana rarrashinta
"Aishan daddy kiyi hakuri...nasan Aslam bai kyauta makiba..kiyafe mashi" baby bata ce komaiba sai kuka, daddy London yacigaba dacewa
"Wannan dalilin yasa koda Aslam bayasonki dole ya aureki...don haka Aslam zaki aura..kiyi hakuri nasan hakan zaifi dacewa" baby kuka kawai take shikuma daddy London sai share mata hawaye yake kawai basu ankaraba sai sukaji kukan baby ya dauke lokacin daya, daddy London na duba fuskanta dake kwanxe kan kirjinshi saiyaga bata numfashi, da sauri ya kalli mom
"Subhanallahi!! Kanwata kirawomin Ismail... Aisha bata numfashi"
[9:44AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 馃挍馃挌鉂ゐ煉燄煉涴煉�
SUNE SANADI
庐zuwairat
5鈨�6鈨�
Aguje mom ta tafi side din Aslam tana kuka, tun ahanya take kiran Ismail, Ismail da Aslam suka fito da gudu, ko inda Aslam yake bata kallaba
"Son please come... Baby ta zata mutu!" Aikam Ismail dagudu yashiga main falo ita kuma mom tabi bayanshi da sauri Aslam ya rike mata, cikin kuka yace
"Mom what's happening?" Mom ko kallonshi batayiba ta fixge hannunta tayi main falo.nan Aslam ya tsaya yana kuka gashi ba daman yashiga cikin. Ismail yana zuwa yaga baby rungume da daddy london, da sauri ya karasa ya amsheta ya kwantar da ita kasa yaduba yaga suma tayi da sauri ya bukaci ya bashi ruwa,, mom ta dauko mashi ruwa daga cikin fridge, dan watsa mata ruwa yayi afuska nan baby ta sake ajiyan zuciya tare da bude idonta ahankali Kara fashewa tayi da kuka, babu Wanda yace mata komai, ahankali ta mike tafada jikin mom tana kuka tana cewa
"Mom ki taimakeni....kar kibari a hadani da yaya Aslam... Kasheni zaiyi...wallahi mommy muguneshi..." Nan Ismail yagane har yanzu daddy London bai janye maganar auren baby da Aslam ba, kusa daita yaje tare da rike kafadanta
"Haba baby.. Kiyi hakuri...ba kyau yiwa iyaye musu...nasan abinda Aslam yayi ba abu bane mai kyau amman karki manta shi dan uwankine kuma kisan hannunka baya rubewa ya yadda...nasan watarana zakiji dadi zabinda iyayenmu sukayi maki" baby batace kalaba sai kuka kawai take, mom rungumeta tayi tana rarrashinta. Daddy London kallonta kawai yake duk tausayinta ya kamashi, bai sake cewa komaiba ya fice daga falon da sauri dad yabi bayanshi yana Kara bashi hakuri amman ko kallonshi baiyiba, abakin kofa suka cikaro da Aslam yana kuka, ko kallonshi basuyiba suka wuce cikin garden, dukda dare yayi amman wurin kal yake saboda hasken fitilu dake wurin. Aslam bayansu yabi, bayan sun zauna yazo gabansu yayi kneeling yana kuka yana cewa
"Daddy am sorry... Don Allah Ku yafemin..." Dukkansu shuru sukayi basu ce mashi komaiba, yafi minti goma agabansu yana kuka kuma yana kneeling basu cemashi kalaba sai daga baya daddy London ya fara cewa
"Aslam...wallahi in ankace in rantse kan bazaka iya aikata irin wannan alfashanba confirm rantsewa zanyi don Sam banyi tunanin kana iya bari shaitan yasami galaba kanka hakaba...abinda nakeson kasani shine, ko kadan kar kabari Aisha takawomin karanka..." Aslam kam yana jin daddy London yace haka ya saki wani sanyanyen ajiyan zuciya ji yayi kaman yatashi ya kwaci shoki gabansu don murna, daddy London yacigaba dacewa
"Duk rananda Aisha ta kirani tace ka yi mata wani abu wallahi kaji na rantse sai na raba aurenku...do you understand what am saying" da sauri Aslam yafara daga mashi kai, "you can go" daddy London ya fada mashi, da gudu yabar wajen ya nufi sidenshi direct bedroom dinshi yanufa yawani daka tsallen ya haye kan gado, nan take yanemin rashin lafianshi ya rasa, kwantawa yayi da filo a kijinshi
"Ni da baby zamu zama hubby and wifey...I can't still believe it" juyawa yayi still rike da filon
"Komai halal no haram...ya Allah kasa ba mafarki nakeba..." Kara juyawa yayi ya haye kan filon yana kallonta
"Baby I will love you all your life... Zan zamo maki kowa da komai...I will do anything to make you happy.. I will cherish you.. I will adore you.. We will be the couple of the century.. Many people will envy our love... Yammatan dake group din maryam Salisu da yanmatan ummu maryam page zasuji inama su suka sami irin wannan mijin馃槣" haka ya dinga surutai shikadai kama hin mahaukaci, ya ma mance da mom tace baby batada lafia sai daga baya yatashi ya tafi falo adaidai lokacin Ismail yashigo, dagudu Aslam ya rungumeshi yana cewa
"Yaya thank you... Nagode, Allah ya saka da alkhairi" dan tureshi Ismail yayi yanacewa
"Kasan ka kara dabbanci da dan akuyanci wurin baby ubanka zanshi" dan tsayawa Aslam yayi ya tsosa keyanshi
"Yaya ko bayan munyi aure?" Ya tambayi Ismail, hararanshi Ismail yayi tare da buge mashi keya
"Ban saniba" ya amsa mashi sannan ya sake cewa
"Zamu wuce sai gobe kilan muzo"
"Haba yaya kabari daddy kawai ya tafi mana" galla mashi harara Ismail yayi
"Don ka isheni da surutuko..to ban yardaba kasan I need my space" yafada yana fita daga falon, Aslam binshi yayi yana murmushi suna fita dad yamikawa Aslam mukkulin motan yayi kan yamaidasu gidan daddy London na tukuntawa. Hi
Baby banda kuka babu abinda takeyi don inta tuna za a hadata gida daya da Aslam babu mom babu dad sai hankalinta ya Kara tashi, dukyanda mom taso rarrashinta abin ya faskara, dagabaya mom tatafi daita dakinta tana bata hakuri Amman baby batace komaiba sai kukakawai take, chan saita dan goge hawayenta ta kalli mom
"Mom don Allah in akayi auren Ku barni in zauna nan gidan ...don Allah karku hadani da yaya Aslam cikin gida daya....." Kara rungumeta mom
"Ai baby vani kadai keda iko dakeba" nan fa tafara wani sabon kukan, da kyar mom ta shawo kanta ta yarda ta kwanta, tana kwanciya bacci yayi gaba daita saboda gajiyan kuka, nantake mom ta rufa mata blanket itakuma tashiga bathroom kadancewan adakin mom take, alwala mom ta dauro tafara nafilfilu, don tsintan kanta tayi cikin farin ciki mara misaltuwa.
Dad ma kwana yayi yana nafila yana Asian Allah yasa hukuncin yayanshi ya zama alkhairi ga dukkan zuriansu.
Aslam kam yana dawowa ya Fara duba online yana neman best place for honeymoon, yana gama wannan ya shiga online shopping, duk sexy night gown da skirts, leggings, mini gown din daya gani saiyayi ordering, baigama ba sai wajen 2am, daga shima yayi alwalla yafara nafilfilu yana godewa Allah, bai kwantaba sai bayan sallab subhi.
Wacegari mom tasa aka hada lafiyanyen abinci tasa aka kaiwasu daddy London sannan akajera musu nasu a dinning, baby sai wajen 8am ta tashi kuma da zazzabi da ciwon kai, idanuwanta sun kumbura, mom da kanta tahada mata ruwan wanka sannan tayi sallah mom tahada Mata wani kakkauran tea, da kyar tasha kadan sannan mom ta dauko mata pain reliever daga cikin first aid box taba Tasha sannan ta koma ta kwanta, wasu hawayen na zubowdaga idonta, rufe kanta tayi da bargo tana kukanta ahankali, don sai yanzu takara tabbatar daba mafarki tayiba.
Sai karfe tara Aslam ya tashi yana wani murmushi jin dadi, wanka yayi ya shirya a cikin wani haddaden English wears sai kamshin turare yake ya tafi main house, yana shiga falo yaga har su mom sun gama breakfast, side din mom yayi don ya gaisheta, yana zuwa bai ga mom ba sai baby kudundune cikin bargo duk idanuwanta sun kumbura, kurawa face dinta ido yayi yana tunanin yanzu kema kin fara jin yanda naji yan kwanakin nan, kurawa lips dinta ido yayi yana kallon, yace cikin ranshi wannan bakin mai shegen tsiwa, mai gama tunani ba mom tafito daga bathroom, da sauri ya dauke kanshi daga kanta, gaida mom yayi ta amsa mashi fuskanta murtuke.

Aranan daddy London ya Kira daddyn baby ya sanar dashi chanjin da yayi, daddyn baby cewa yayi shi baby ba diyarshi bace don haka duk abinda daddyn Aslam yace shine dai2, still aranar da daddy London tare da dad Aslam tare da wasu friends din dad sukaje gidansu sadeeq, iyayen sadeeq basu dauki abinda da zafiba don sun San komai sai in Allah ya yarda, sadeeq kam haukane kawai ke baiyiba amman da abbanshi ya zaunar dashi yayi mashi nasiha sai ya dau hakuri amma acikin zuciyanshi yana tunanin da kyar ya Kara samun macenda zaiso kaman baby.
Yanzu kwana uku Kenan, daddy London yace kar a chanza former wedding date din,so sai auren ya rage kwana 20.
baby duk ta chanza ta rame, sai mom ta zare Mata ido take dan cin abinci, duk abinda mai gyaranta tabata batasha ko yi amfani dashi mom kam tasani amman bata cemata komai.
[9:44AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 馃挍馃挌鉂ゐ煉燄煉氣潳
SUNE SANADI
庐zuwairat
5鈨�7鈨�

Ana sauran sati biyu bikin kayan furniture da kitchen utensils da akayiwa baby order suka iso, gidan da dad yasa aka ginawa Aslam kafin ya dawo daga London aka wuce da kayan, wani irin makeken gida da underground ga swimming pool, in mutu bai saba da shiga irin wanan gidanba sap mutun zai iya bacewa. Kowa da side dinshi, aside din Aslam da akwai wurin baby da kayanta likewise aside din baby da akwai wurin Aslam da kayanshi. Komai na gidan ya hadu, duk kayan sawan da akayiwa baby direct sabon gidan ake wucewa dasu. Kayan dazata sa a wurin wedding events kawai aka kawo gidan cikin wasu manyayen kwalaye. Dad ansan duka contact din Aslam, mom ya hada da nashi ya aika su service providers kaman Mtn, Glo, da sauransu, yan service provider din suka hada wedding invitations da dukan events din dazaayi tare da dress code din dazaayi ako wacce rana suka turawa mutane, sannan aka Kara printing din wani expensive wedding card wanda ke dauke da photo baby agaba saina Aslam abaya akara rabawa manyan kasa.
Yanzu matan Ismail da yarshi sun iso Nigeria. Sai mom dinshi tare da brothers dinshi.
Yau wedding din sauran kwana 13, amma Aslam bai Kara saka baby a idoba, rabonshi daita tun ranan da ganta kwance side din mom, kuma ko yazo dinning baya ganinta, Aslam kam yanzu ya murmuje kaman bashi bane kwance rai hannun Allah yan kwanakin bayaba. Duk ya Kira abokanshi wanyanda ke Spain da wayanda ke London sai wayanda yafara masters dasu a b.u.k, wasu cewa suke ai sunga invitation. Yana kwance cikin natsuwa sai Allah Allah yake ranar daurin aurensu yazo, sai yaji karan cigowan motoci mikewa yayi yaduba, saiya ga motan Ismail ne, sai kuma ga wata motan abayan wannan motan kuma sai wata bus, DA sauri ya fito, Ismail na gama parking shikuma yana isowa wurinsu.Ismail ne yafito tare da matanshi da diyarshi da sauri Aslam ya isa garesu ya amshi diyar, dayan motan kuma mommy Ismail ce tare da kanin Ismail aliyu sai autansu wanda ke age mate din Aslam yusif,daman yasan sun zo amman basu ga junansuba da sauri yaje ya rungumi mom dinsu hannunshi rike da Fina diyar Ismail
"Big boy...naji dadi sosai dazakayi aure...Allah yayi maka albarka" mom dinsu Ismail ya fada, aliyu Wanda ke dan shekara 38 aduniya ya dan tabe baki yana cewa
"Haba mom miye abin jin dadi dan karamin yaro kaman Aslam ace zai sa kanshi cikin commitment" hararanshi mom tayi batace komaiba, sakin mom yayi yaje suka rungumi juna da Yusuf, Yusuf cewa yayi
"Dan uwa kayi auran nan ka bamu labarin yanda akeji don friends dina cewa suke marriage sucks" dariya sukayi sannan Aslam ya gaisa da Matan Ismail, suna cikin gaisawa mom tafito. Da sauri suka rungumi juna da mommy Ismail. Kaya aka fara fidowa cikin bus din ana wucewa dasu main house. Tare suka wuce falo, mommy Ismail cewa tayi
"Sister Ina amaryan take" Aslam dadi yaji don mugun son ganinta yake, dariya mom tayi tare da kiran number baby dukda cikin ranta batason su ganta don duk ta rame.
Bayan baby ta gama waya da mom ta mike jiki babu kwari don yanzu ta gaji da kuka, duk kamaninta ya chanza kaman ba itaba, kawai zaman da zasuyi da Aslam take tunanin, ahankali ta mike ta tafi falo, tana tafiya iska na kadata, tun tana stairs Aslam ke kallonta, shi kanshi ya tausaya mata don ta chanza sosai duktayi sanyi kaman baitaba. Sai yaji inama zai iya hakuri da ita. Kanta kasa ta shiga cikin falon, gaidasu tayi, sai yaba kyanta ake, Yusuf kallon mom dinshi yayi
"Mommy ni ma Ku neman min irin baby a family dinmu in aura" ya fada babu alaman wasa tattare dashi, baby gefen mom ta zauna kanta kasa, bata daga kai ba balle ta kalle Aslam amman tasan yana gurin saboda kamshin turarenshi, Aslam kam banda kallonta babu abinda yakeyi. Mommy Ismail ta nunawa mommy Aslam kayan da Aslam da baby zasu sa aduk events din da zasuyi, kasancewan mommy Ismail ta dauki nauyin hakan. Basu bude kayanba amman da ganin irin kwalayen kasan kayane masu tsada da kyau. Ismail kallon matanshi yayi
"Habibty ki tafi da sister ta upstairs kiyi mata kyalliya za a daukesu prewedding pictures" kallonsu mommy Aslam tayi
"Pre wedding pictures kuma?..bai makaraba" dan girgiza kai Ismail yayi
"Gaskiya anty bai makaraba...ya zaayi ashe baby da Aslam zasuyi aure babu pre wedding pictures?" gaban baby Fara faduwa yayi, Aslam kam Sam baisan abunda akecewa ba cos kwata2 hankalishi baya jikinshi, Yusuf kallon Aslam yayi
"Bros irin wannan kallon haka?" Da sauri Aslam ya kauda kanshi yana murmushi, matan Ismail mikewa tayi ta nufi baby ta daga, baby kallon ki taimakeni tayiwa mom, itakuma mom tayi mata kallon kiyi hakuri suka bar falon, mom din Ismail tasa akabi bayansu da cosmetickit tare da kayan da baby zatasa. Ismail kallon Aslam yayi
"Go and get dress...the photographa is on his way" shima Aslam mikewa yayi Yusuf shima yabi bayanshi, ismail yasa yusuf ya dauki wani park na kayan maza suka tafi side din Aslam, shima Ismail bayansu yabi shi kuma miskilin aliyu balance yayi kan cushion sai danne2 yake awaya. Mom da mommy Ismail side din mom sukayi suna hiran bayan saduwa. Aslam wanka ya sake yi, sannan ya bude kwalin kayan wasu tsadaddun Cristiano febian six piece suit ne aciki
"Wooow" ya aslam fada yana dauko dan bow tie dike saman kayan, without wasting of time Ismail da Yusuf suka taimaka mashi yayi dressing, da ka ganshi sai Kara rantse dan queen of England ne don yanayin shiganshi kaman nayan sarautan turawa. Aslam kallon Ismail yayi
"Yaya how do I look"
"So cute" ya amsa mashi, ya sake cewa
"To yaya Ina kasamo Wanda zaiyi mana pictures din?"
"Wani dan abokin dad ne ya kirawominshi mukayi magana ance celebrity photographer ne wai yaiya hoto sosai" shi kam Yusuf kurawa Aslam Ido yayi for a while sannan yace
"Amman irin wannan weird marriage din baayinshi a London" Aslam ya amsa mashi dacewa
"Kamanya weird marriage?"
"Ai you are getting married to your sister duk matan duniya karasa wacce zaka aura sai sister ka?" Daria Aslam da Ismail sukayi sannan Ismail yace
"Ai it's not haram..kuma ai dazun naji kanacewa Kaima anema maka irin baby kuma kace a family" daria suka sajeki, maigadi ya bude get wani haddaden motane da bus suka shigo
"Yauwa yazo"inji Ismail. Ismail fita yayi suka gaisa da mai photo. Sannan yasa yaranshi dake cikin bus suka fito da wasu kujeru na alfarma guda biyu suka jira acikin garden.
Abangaren baby kam matan Ismail sata tayi tayi wanka ta gyara mata gashin kanta sosai sannan ta zaunar daita kan kujeran mirror ta fara tsara Mata kwalliya saidai ana kwalliyan hawaye na batawa saida ta zaunar daita tabata hakuri dukda batasan sanadin kukantaba sannan ta samu aka yi mata kwalliyan. Suna gama kwalliyan ta bude wani kwali Wanda aka rubuta valantino ajikinshi, wasu golden sapphire gown tafiddo tasaka mata sai golden Gucci shoes sai ta dora mata wani tiara irin na princess kanta, duk inda ta zagaya zakaga shining saboda wasu classic stones dake jikin kayan. Bayan sun gama suka sauko falo amman baby taki fita waje duk yanda matar Ismail tayi kin fita tayi, alokacin su Aslam sunfi minti talatin da fitowa suna jiran fitowansu, Ismail kiran matanshi yayi sai take sanardashi sun gama suna falo ya gayawa Aslam yazo ya tafi da matanshi. Ismail cewa yayi Aslam yaje su taho da baby suna falo, yana shiga falon matan Ismail tafita waje tana cewa what a perfect match, hangota yayi tamkar jaririyan wata, dan kusa daita yaje
"Habibty let's go" bata kalleshiba ta makale mashi kafada
"Ban zuwa" tafada a tsiwace. Tsaya kallonta yayi ya murmushi
"Baki dai zuwa ko?..to ba komai ai nan da few days za a kawoki gidana kuma nima zan rama..." Da sauri ta katseshi
"Yaya...in naje photo... Bazakayi min komaiba?" Dan shuumin murmushi ya saki sannan yace
"Indai har kikayi behaving kanki, kikayi duk abinda akasaki ko nasaki har aka gama wedding dinmu nayi maki alkawarin bazanyi maki komaiba har saikin nemeni da kanki..." Dan kallonshi tayi suka hada ido ya kashe mata ido daya, sai tafara kokarin kuka
"I know you are joking" cikin ranshi yace ashe kinsan it's impossible, a zahiri yace
"No am not.. Kuma naga matan nan dake dora miki magani tabar dorawa...to indai banga tashigaba da dorawaba bazan kyalekiba" cikin ranta tace kunji wannan tantirin dan iskan, yaxigaba dacewa
"Did you hear what I said?" A hanjali ta gyada mashi Kai
"Then let's go Mrs Aslam" dan hararanshi tayi ta wusiyan idon sannan ta shige gaba yabi bayanta suna fita mai photo ya farayi musu kirari yana daukansu photo
"
[9:44AM, 22/05/2017] 馃挒@lh@ji馃挒: 鉂ゐ煉氿煉涴煉熲潳馃挍
SUNE SANADI
庐zuwairat
5鈨�8鈨�

Hotuna suka sha kala2, mom da mommy Ismail suna saman bene suna kallon photo shoot din, mommy Ismail ji take inama aliyu ne zaiyi aure mai hoton yace su sake kaya nanfa baby ta Kama kuka wai cikinta keyi mata ciwo, Aslam yasan karya take, Ismail kallon yanda take kuka yayi sannan yace ta tafi, tafiyanta mai jan hankalin mai kallon ba kaman Aslam ta farayi dukkansu suka bita da kallo, tana shigewa Yusuf ya kalli Ismail
"Yaya nima wallahi Ku nemamin kamanta a cikin family" naushi Aslam ya kai mashi yana daria
"Kar ka Kara kallon princess dina" Matan Ismail da batajin Hausa kasancewan ita balarabiya ce ta fara daria
"Aslam is jealous" daria suka sakeyi sannan Yusif ya sakecewa
"Forget about him Anty... Zanga ta yanda zai hanani kallon kanwata" Aslam bai tanka mashiba yabar wajen yana kokarin kunce bowtie din dake wuyanshi. Baby tana shiga cikin ta kwanta tana kuka
"Please ya Allah...help me..banason Aslam... Please somebody help" haka ta shigaba da kuka tana dukan filo kaman tana dukan Aslam. Sai wajen karfe hudu su Ismail suka koma. Around 5pm yan decorations suka zo, sukayi decorating ko Ina da gidan, duk Wanda zai shigo farfajiyan gidan yasan suna da occasion.
Bayan Aslam da dad sun dawo daga masjid sallan ishai, Aslam har yayi side dinshi dad ya kalleshi
"Aslam meet me inside" yana kaiwa nan ya nufi ciki tare da shiga side dinshi, Aslam fasa shiga side dinshi yayi yabi bayan dad. Da sallama ya shiga falon dad, dad ya amsa mashi tare da nuna mashi kujeran dake kallon nashi, Aslam zam yayi yana kallon dad
"Aslam.." Yakira shi
"Na'am" Aslam ya amsa mashi sanna dad yacigaba dacewa
"Son...inason kasani Aisha amanace na baka...ko kadan ban yarda ka takura Mata..
Kasan baby bata sonka amman aka sata auranka..so ka rubuta in har ta kawomin karanka raba aurenku zanyi...did you understand what I just said?" Ahankali ya gyadawa dad kai, dad tacigaba dacewa
"Kar kayi abinda zai kawo matsala tsakanina da yan uwana...kanajina?" Kai Aslam yakara gyadawa dad, dad wasu document yadauko
"Take this," ya mikawa Aslam sannan yacigaba dacewa
"Wannan document din gidan da nagina maka ne...take it as a wedding gift" dan murmushi Aslam yayi
"Dad na gode..Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen" dad yace sannan ya cigaba dacewa
"Kuma ka shirya sati daya bayan wedding din zaka fara aiki a company dina na"
"Ok dad" Aslam yace amman cikin ranshi ba haka yasoba donshi bai ki abashi shekara daya ba. Dad ya Kara cewa
"And ka shirya zuwa gobe ka koma chan gidan" Kai ya gyadawa dad amman shi baiso hakaba, shawarwari dad yacigaba da bawa Aslam sannan daga baya yaje ya kwanta.
Wacegari yaje wurin mom,yayi Mata bayanin yanda sukayi da dad, advice mom takara zaunar dashi tabashi don harcewa tayi inya musgunawa baby bata yafeba, sai tunani maiyasa basu tunanin halinda shi zai shiga in ya kyale baby tayi abinda ta gandama. Sallama yayi da mom sannan yakoma side dinshi ya Kira Yusuf yagaya mashi zai koma sabon gida, nan yusuf yace yajirashi su tafi tare. relaxing yayi tare da bude Facebook dinshi nan yafara ganin yanda irin comment da like da akeyiwa pre wedding pictures dinsu, murmushi yayi yakoma instargram nan ma comments da likes ne kaman hauka. Bayan kaman hour daya da rabi Yusuf yazo sannan suka wuce, address din da dad yabashi sukabi sannan suka isa bakin gate din makeken gidan "woooooow" kawai Yusuf ke cewa, Aslam fita yayi daga cikin motan ya bude kofan ya shiga ciki don ya bude gate, ji yayi wani nacewa
"Kai...Kai ..waye" juyawa Aslam yayi ya kalli Wanda yayi maganan shima mutumin Aslam yake kallon
"Waye Kai?" Ya tsake tambayan Aslam, Aslam kallon head to toe yayi mashi sannan yace
"Ni sunana Aslam... Kai" Aslam bai gama maganaba, mutum Wanda zaiyi tsaran Ismail ya Fara cewa
"Sannu da zuwa...sunana saminu kuma ni ke gadin gidan nan" gaisawa sukayi yana mai girmama Aslam, bude musu gate yayi sannan suka shiga gidan. Both Aslam da Yusuf mamakin gidan sukayi dukda sun saba da manyan gidaje amman gidan ya balain burgesu. Key Aslam yasa yabude hanyan falon
"Kaiiii..this place is paradise on earth" Yusuf ya fada, dan murmushin jindadi yayi, suka Fara zagaya gidan komai normal. Aslam gani yayi dukkan wardrobe din gidan cike da kayanshi dana baby sannan kowanne kitchen cike da kayan abinci, kowane kofa da abinda akarubuta, Aslam kallon Yusuf yayi
"Guy gaskiya gidan nan yayi min yawa..kazo mu zauna kafin akawomin princess dina" dan daria Yusuf yayi
"Ai baka isaba...wato in ankawo maka baby saika korani ko?"
"Da tare zamu zauna da kai?"
"Ni bance Ku zauna daniba amman nima yanzu bazan zauna da kaiba" dan tabe baki Aslam yayi
"Kada Allah yasa ka zauna...ai sai inbika family house dinku" daria Yusuf yayi sannan yace
"Zan zauna da Kai sai muyi bachelor eve dinka anan..daman su Mahmud muke jira kuma sunce gobe zasu iso" cikin farin ciki Aslam yace
"Rantse...cos dazu da safe munyi call dashi kuma bai gayaminba"
"Ai he said he wants to surprise you... Nima gulma nayi" dadi sosai Aslam yaji
"Kai am happy wallahi"
"Sannan gobe family dinsu baby zasu zo suma..don naji ance sisters din baby sun fita kyau" daria Aslam yayi sosai har da rike ciki
"Uban wa yafi baby kyau cikinsu...MARYAM ko yusra" hararanshi Yusuf yayi
"Ai dole kace haka tunda baby ta sace maka zuciya" haka suka cigaba da hiransu suna zolayan juna.
Wacegari mutane Saudi suka iso wato daddy KSA da yayanshi Ahmed, Mahmud Wanda ke saran Aslam da Yusuf sai autansu amira wacce ke age mate din baby. Daddy KSA shine kanin daddy London sannan daddy Aslam sai daddy baby su hudu iyayensu suka haifa, suna mugun kaunar junansu don da kyar kaji Kansu.
Aranar dasu dad KSA suka iso daga Saudi, ranar iyayen baby suka iso daga England tare da yayyan baby umar, MARYAM sai Yusriyya, kowannensu gidanshi na kano ya sauka sannan kowa yakawo gudunmowa mai tsoka wanda in a auren talakawane yaisa a aurar da yara biyar da gudumowar mutun daya,
Bayansu parents din baby sun huta, daddy baby ya tafi gurin daddy London donsu gaisa, sannan mommy baby tare dasu maryam suka kaman hanyan gidansu Aslam.
Gara sosai mom tasa aka hada masu dontasan da zuwansu, around 5pm suka iso, cikin murna da kaunar juna mom da mommy baby suka tarbi juna, gaisawa sukayi da junansu cikin So da kauna, bayan su zauna MARYAM da Yusriyya suka fara kalle2 ko zasu ga baby Amman basu gantaba, MARYAM kallon mom tayi
"mommy ina baby take.. Ban gantaba?" Daria mom tayi
"Kin gagara kiga little sister ko...bari in kirata.."
",no mommy.. Ki nunamin dakinta sai inje" mom kwantanta Mata dakin baby tayi maryam da yusra suka tafi upstairs shikuma umar na zaune.
Abakin kofan baby suka kwankwasa, baby dake zaune gaban mirror

Please Login or Register in order to submit comment