Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abun ya lalace don Allah mu kula da wannan)


Fadila na satar kallonsa kadan kadan tana kallon yadda ya zubawa yarinyar ido ya lumshe idanunsa daga baya ya budesu ya sumbaci goshin yarinyar sannan ya miqawa mubarak ita yana sake cewa Allah yayi mata albarka,ya amsheta sukai sallama ya shige gida da babyn


Aliyyu ya yafito qasimu dake fitowa fitowa daga gidan hannunsa da robar abinci qasimu ya qaraso hadi da rusunawa aliyyu ya amshi bandir din kudin dake hannun nasiru ya miqawa qasimu yace ka kaiwa maman baby ya zaro 1000 daga aljuhun trouser dinsa ya bashi ya shige motar yabar qasimu nata zuba godiya yare da komawa cikin gidan don sada saqon aliyyu ya bawa nasiru umarni ya tada motar suka bar layin fadila nata satar kallonsa don kiwa dubu dari ce ya bayar a kaiwa babyn




Mrs muhammad ce 👑





📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


2:08 pm. 24/08/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?..
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by masoyiyar buk din wayasan gone..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*Part 2*


1⃣3⃣&1⃣4⃣



Fadila tacigaba da sake2 azuciyarta bata ankaraba taji ana bude get tana dago kaitaga harsun iso gida ashe,parking space ya nufa ya kashe motar,fadila dakekokarin bude motar setaji ya kulle motan ta waiwayo tadubesa suka hada ido tayi saurin dauke kanta zuwa gefe,shiko gogon sebinta ya ke da kallo can yace wai meye kiketa wani bata rai tamasa banza yacigaba damagana ,inatambayarki,kaikidanayine nayi lefi koso kike danabarki kikwana? nan ma shiru yaharzuka cikin tsawa yace wai badakenake maganaba salan wulakanci,

Se asannan fadila tadago kai da fuska cike da hawaye tace wulakanci? wulakanci yawuce wulakantani dakakeyi Wanda haka har matanka suka sami damar gorantamun,Aliyu nayi nadamar aurenka auren bakinciki Inatabbatarma dabadan mahaifinaba dana dade dabarin gidan nan,cikin kuka takemaganar yayin da Aliyun yatsinci kansa da tausayinta Yakuma kasa cewa kome illa binta da kallo.

Fadila tacigaba kodan matanka da ni ba irin su naso nayi kishi dasuba,naso ahadani da wayanda suka San mesukeyi😭 bawadannan da kake kallo amataba nibanga mata anan ba kuma duk ajin naka akan salima da samera yakare ragowar wasu,cikin bacin rai yadakamata tsawa,itako ta dannan motar tabude tafita da gudu tanufi sa shinta,tana shiga tafada kujera setaji ya akayi tayi wadannan magana,setaji kamar bats kyautaba cankuma wani bangaren zuciyarta tacemata garadakika masa haka yasan fa kinsan mekikeyi kuma yasan badan shikike gidanba Dan biyayyar iyayankine,tamike tashiga toilet tayi alwala ta fito ta tada sallar isha dabata samu tayiba.


Can Aliyu kuma kasa futa yayi daga motar jikinsa duk yamutu zuciyarsa ta cunkushe abinda yafi damunsa shine kalmanta datayi kansu samira da salima domin yakaratunawa da yanda yasamu samira adarensu nafarko,sannan Salima bayan rabuwarsu itama ba agida tayi rayuwaba,yadafe kansa karo na farko da naga A S metama na kwalla daya nazurarowa daya bayadaya😰 yace inna lillahi wa inna ilaihirraji un.tabbas jidakai bekama ceniba domin ina tare da wadanda basu cancanci suzama iyayan yayanaba,gashi inakallo se haihuwa ake Wanda akai bikinmu tare duk sun haihu,su naji kowacce tace batashiryaba itakuma wanan yarinyar banashiga harkanta,gashi du k ta gane kome,Aliyu yacigaba da hawaye yana maibakkincikin abubuwa kala kala yadaure ya fita daga mortar jiki akasalance yanufi bangaransa yanashiga ya kulle kofar yabar makullin ajiki sabida bayasan ganin kowa domin koda sunzo sunyi amfani da makullinsu bazebuduba.yashige bedroom yafada gado yacigaba da tunani aranar dai Aliyu beruntsaba Dan maganganun fadila kemasa yawo akwalkwaluwarsa,


Itako fadila cikin nishadi tayi barci domin tafidda wani tabo da kedamun zuciyarta.



*amun afuwa Mrs Muhammad nayi muki shishshigi amma haka mukeson buk yadawo munakara mikamiki godiya dayabawa Allah yakara basira kidora saga inda natsaya domin zansamu goyon bays amma kitambayi friends sunyarda kidora😀*bye nabarki Lfy Wanda sukaji haushi suyafemin kar azagen nima wlh soyayyar buk din yasa nayi👍🏻

Ba Mrs Muhammad bace👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


[10/16, 1:46 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

1⃣5⃣&1⃣6⃣

Qarfe tara fadila tayi wa iftihal wanka itama ta shirya cikin riga da skert na atamfa a cikin qana nun kayanta ta cirowa iftihal wasu riga da skert dama sun mata kadan jajayene in and top ta raba mata gashinta gida biyu ta tufke mata da ribbon sosai iftihal tayi kyau suka yi break sannan ta soma gyara part dinta kafin ta isa ga na aliyyu don duty dinta ne duk inda ta shiga yarinyar na biye da ita ita ala dole sai ta taya ta aiki sai da fadila ta bata mopping din kayan kallo sanna ta rabu da ita

Fadila ta fito tana goge hannunta da duster bayan ta gama aikin ta iftihal dake ta fama da chocolate tace "anty ina daddy na?"murmushi fadila tayi ta kama kumatunta tace"kwantar da hankalinki 'yar daddy yanzu zaki ga daddy shiga daki bakin gado ki dauko min hijabina"da gudu kuwa ta shiga sai gata da shi a hannu ruwan madara ne iya qugu wanda ya shiga da atamfar jikinta sosai,ta kama hannun iftihal din bayan sun rufe qofan

Tana sa kai falon taji hayaniyar sama sama muryar salima ke a sama,tana tsaye hannayenta harde saman qirji kan aliyyu shi kuma na zaune kan kujera yana sanye da kayan bacci na maza ruwan madara shima hannun nasa harde a qirjinsa😠,shigowar su yasa salima yin dif daga maganar da take yi din gami da sakin fuskarta daga tsukewar da tayi tana dan binsu da kallo(salima akwai duniyanci)sam bata lura da iftihal ba da suka shigo tare sai da yarinyar ta zame hannunta daga na fadila wadda ta shige kitchen ta ruga a guje tayi gun daddynta tana cewa"daddyyyy daddyyyy...."kamar yadda ta saba ta durqusa a agabansa kafin ta haye cinyarsa tana cewa"morning daddy sabahul khair",murmushi ne sosai dauke a fuskarsa wanda bai bayyanar da haqora😊yasa hannu ya dagota yana kallonta yace"sabahun nurrrr my lovely khadija"tayi tsalle ta dane cinyarsa abinta tana wasa da maballan gaban rigar baccinsa tana cewa"daddy tunnjiya nazo da daddare kaqi zuwa na ganka" "wonderful,anan kika kwana ke da wa?""ni da anty fadila tare ma yanzu muka taho"ya daga kansa yana nemanta da idanunsa sai dai tuni ta jima a kitchen bata a gun sai salima dake tsaye ta zubawa 'yar tata ido

Kallonta take tana jin wani alfahari na shigarta tana godewa Allah da bai bata damar rasata ba,wani dadi ne ke cikata ganin gudan jininta ita da halitta mafi soyuwa a gareta wato Aliyyu salim Abdallah maitama,tabbas iftihal abar alfaharinta ce yarinyar bata debo kammaninta ba ko kusa babu wani abu nata data dauko illa farar fata wadda aliyun ma na da ita,kowa ya ganta ya san jinin su ce family din alhaji salim Abdallah maitama ce jininsu ce

Ta dawo daga duniyar tunaninta hadi da miqawa iftihal din hannu alamar ta taho sanda suka hada ido fuskar salima dauke da murmushi,da taga kamar yarinyar bata fahimta ba sai tace"come on baby na come on my dear " yarinyar ta noqe kafada tayi luf jikin mahaifinta kamar mai tsoron ta babu sabo ko kusa tsakaninsu,wani kishi ya kama salima don taga yadda suka shigo da fadila yarinyar a sake take kana ganinsu kasan akwai sabo mai yawa tsakaninsu

Ta sake gwada sa'arta ta miqa mata hannunkaro na biyu tana sake cewa"come on mana mai dear kin manta mominki ne iftihal? Me yasa baki zo guna kin kwana ba ina da chocolate da biscuit da yawa da zan baki"ta sake noqe kafada tace "um um nafison na kwana gun anty fadila she's nice like daddy"sai salima ta maida hannunta ta rungume cikin jin haushi

Aliyyu na ankare amma yayi kamar baiga abinda ke faruwa ba,sai da yaji tana jan qwafa sannan ya tanka mata"duk uwar da bata yi showing mercy akan yaronta ba tayi abandoning duk wasu duty nata akansa no need to deceive her self akan shi zai iya jin qanta ya kuma ji tausayinta"idanunta sun kada sunyi ja kadan take jira ta fara malalar da hawaye tace"aliyyu abinda ya wuce ya riga ya wuce please"ta juya cikin zafin nama ta bar part din nasa kamar zata rushe da kuka

🔱🔱🔱🔱🔱
*TUNA BAYA*👈🏼
🔱🔱🔱🔱🔱

Aliyyu da salima sunyi aure ne irin auren da zaka iya kiransa na soyayya,karatu shi ya fara fitar da aliyyu india cikin garin mumbai dake qasar india,ya karanci fannin kasuwanci da masana'antu ne tun usulinsa,kusan binda ma ya zaunar da shi kenan a qasar bayan kammala karatunsa kafin daga bisani ya soma kai kawo tsakanin nijeria da indian

Tun kafin aliyyu ya kammala degree dinsa na farko yake siyan kaya yana turawa uncle Abba yace a siyar masa tun uncle abban na dariya yana dauka wasa ne abun nasa yakance"alii rigima idan banda abinsa mai ya nema ya rasa da zai takurawa kansa sai ya fara kasuwanci tun kafin ya kammala karatunsa?"shi kama aliyyu ya dage aiko kaya yake tun daga lokacin da uncle abba ya fuskanci son kasuwancin a jininsa yake sai ya qyaleshi ,sai gashi tun kan ya kai ga kammala degree dinsa na biyu ya mallaki kudade masu tarin yawa na qashin kansa tsantsar guminsa,sam yaqi amsar tallafin sisin kwabo dag dukiyar da Allah ya horewa mahaifinsa,kwata kwata aliyyu ba cima zaune bane akwai zuciyar neman na kai tun yana qaraminsa,bai damu da arziqin da mahaifinsa ke da shi ba

Wadannan kudade yaci gaba da juyawa har kawo yanzu matsayin da yake kai na mamallakin companies da share shares a gida nijeria da wadansu maqwaftan qasashen,aliyu ya zamo daya daga cikin matasa masu tarin dukiya mutumne shi da Allah bai bashi dagawar son a san wayeshi ba,yasha gayawa abban nasa tun kafin zuwan wannan lokacin shi yafison yasan ya san zafin neman na kai,sai gashi burinsa ya cika don ya tara dukiyar da shi kansa bai sa ran samun kamarta ba,darajar addu'ar mahaifa riqon gaskiya da amana tausayi da taimakon na qasa su suka kaishi ga wannan matsayin da yake kai

Haduwar su da salima ta kasance ne sanadiyyar hutun qarshen zangon karatu da daliban instute din pashwar suka samu ciki harda,wadanda ba 'yan qasar ba kuma suke da sha'awar zuwa qasashensu hutu nata shirye shiryen zuwa gidan ciki kuwa harda saliman,wasunsu na ahiga kasuwannin dake cikin mumbai don yiwa yan uwa tsaraba

Cikinsu harda salima su hudu ne ita sai wata qawarta 'yar nijeria sa'adiyya abikan karatunta biyu 'yan qasar data nemi rakiyarsu don qasarsu ce sun fita sanin kan farashin kayayyakin shruti da arohi,sun ahiga shagon a sanda aliyyu ke ciki yana zaune kan daya daga cikin kujerun dake ajjiye a shagon suna lissafi ne shi da mai mai shagon kan wasu kaya da aliyyun ya sara a gunsu alokacin tun kafin ya bude kamfaninsa

Abu na farko da ya fara kama jan hankalinta game da aliyyun shine baiwar tsantsar kyau da Allah ya bashi da daddadan sauti ,abu na biyu ya bata mamaki jin yadda yake hira tar tar da indiyanci tamkar haifaffen can,tunda suka shigo shagon daga kallon farko na amsa sallama bai sake duban sashin da suke ba ya mai da kai yaci gaba da abinda ya kawoshi shagon

Ita din ma azahiri idan ka kalleta sai kayi tsammanin hankalinta bai kansa saidai duk siyayyar da take yi kusan qani abun ma bata san me zatayi da shi ba data dauke shi don hankalinta na kan alin

Tuni ya kammala abinda yake yayi sallama da raja ya wuce,sanda yake fita ashagon garin karkatawa ya wuce taga silmiyowar wani abu daga aljihun trouser dinsa ma baya amma bata zaci wani abu mai muhimmanci bane sai da ta sake matsowa ta sa idonta sosai sannan taga ashe wata 'yar kyakkyawar wallet ce ,da sauri tasa hannunta ta bude ciki,rupees(kudin india) ne masu yawa aciki a miqe,sai dan qaramin hotonsa wato passport,sai kuma wasu kati guda uku biyu na wasu shaguna dayan an rubuta *adishwar garment* shagon na cikin *janta cloth market hawkers plaza*ta maida shi ta duba dayan shi kuma na shagon *ajmeri fashion* shagon shi kuma na *hazarat abbas road Samuel street*,duk cikinsu babu shagon da ta taba zuwa tunaninta na kan yadda Atayi masa da wallet da kuma yadda zata sake samun damar hanawa da shi,tana duba kati na uku uku na dauke da sunan hotel din da ya sauka haka jikinta ya bata tunda su muta nene da komai ka siya ko kayi mu'amalar ciniki da shi sai sun baka rasit ko card nasu,tasan hotel din tunda takan ziyarci cikinsa lokaci bayan lokaci nan kusa da makarantarsu yake

Ta maida duka kayan ciki tana sauke ajiyar zuciya,bayan sun kammala siyayyar suka koma cikin makaranta,da daddare ta canza shiga irin tamu ta hausawa atamfa ce saidai dinkin riga da skert ne tayi kwalliya sosai a fuskarta,ba wata tafiya ce mai nisa sosai ba tsakaninsu don haka irin keken nan nasu ta hau ya qarasa da ita,bata sha wahalar samunsa ba saidai da yake hotel ne na manyan mutane akwai tsaro sosai da kuma tsari duk magiyarta basu yarda sun bata number din room din ba sai da sika kirashi suka sanar masa,duk da yayi mamakin mai neman nasa kuma sunce mace yace a bata number din baisan me ya kawota ba ko da taimakon da zai iya bata

Ku biyo
Mrs muhammad👑😘

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:47 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

1⃣7⃣&1⃣8⃣

Sai da tayi knocking sama da sau biyar sannan aka bude mata,fuskarta ta wadatu da murmushi😃 yayin da tasa take a tsuke😠 kamar hadari,"sannu ko?"tace da shi cikin fara'a"yauwa sannu" ya fadi adan dake yayi bake bake abakin qofar babu wata hanya bare ta sa ran shiga ciki don ko kalan labulen bakin qofan ba zata tantancewa ba,cikin qosawa ya gyara tsaiwarsa ganin tayi shiru yace "I hope lafiya dai ko?"ta sake yin murmushi a karo na biyu ya zaro wallet din daga cikin yar purse👛 dinta dake damqe a tafin hannunta sannan ta dubeshi tace"wannan ka yar dazun a mall din paras mahal collection"ta miqa masa tana dan murmushi,ya sa hannu ya amsa yana cewa"thank you verry much"ya juya yana qoqarin mai da qofarsa ya rufe

Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar cewa"haaabaaa haabaa malam babu ko goron tsintuwa?😊" a qagauce ya dakata ya juyo yana cewa"nawa kike buqata?"t saki wani mayaudarin murmushi"ba kudi nake so ka bani ba,kawai passport nake so na cikin wallet naka sai kuma phone number dinka shikenan abunda nake buqata🤗"

Girgiza kai yayi hadi"it can't ki zabi wani abun dai daban banda wadannan"ta kanne ido daya😉 tace"ni su din dai nake so"kafewa yayi kai da fata bazai bata ba"i told you ba zaki samu ba"itama kafewa tayi akan shi take so indai alherin da tayi masa yake son rama mata,daya lura tana da yawan taurin kai sai ya bude wallet din ya zaro rupee dubu daya kwatan kwacin kudin nijeria a yanzu naira dubu hamsin ya ajjiye mata saman qafarta ya juya karo na biyu yana shirin sake rufe qofarsa

Ta tabbatar idan ya subuce mata a yanzu mawuya cine ta sake samun dama kwatan kwacin wannan don haka cikin zadin nama ta tattara kalmomin"idan kamin haka baka min adalci ba zaka kashe min gwiwa ne na aikata aikin alkhairi,ni bana buqatar kudinka

Da haka ta kashe masa gwiwa don bazaiso ta zama mara kirki ba ta sanadinsa ya sani idan har hakan ta faru yana da tagomashi a agun Allah,dole ba dan yaso ba ya bude wallet din ya bata passport din hadi da karanto mata numbobinsa ta kwafe tsaf bisa wayarta tayi serving,tun daga lokacin hotonsa shi ya zama abokinta da zarar ta kadaice shi take sawa a gaba tayi ta kallo,kyan Aliyyu na qayatar da salima ya tafi da imaninta 100%

Takan bata lokaci tana gurin kiransa amma ba zai daga ba,ta jure hakan ba tayi zuciya ba tana ci gana da kiransa,yau da gobe tafi qarfin wasa har takai da idan ta kirashi sau goma zaoyi qoqari ya daga mata ko sau daya ne shima daga gaisuwa bai bari a wuce haka,an halicci zuciya abisa son mai kyautata mata to hakan yake don kuwa kulawa sosai salima ke nunawa aliyyun mutum ne dama da bai taba budurwa ba samun hakan yasa ta shiga cusa masa ra'a yinta sannu a hankali har ya minta da ita ya bada amannar zata zama abokiyar rayuwarsa

Asalin salima 'yan katsina ne mahaifanta,yan boko ne na bugawa a jarida irin mutanen nan ne da ake cewa"yan boko aqida"wato ga karatun bokon ga kuma bin duk wasu aqidu nasu, bokon suke da gaske babu sirkin addini ko kada cikin mu'amalar rayuwarsu ta yau da gobe bokon kawai akasa agaba shine madubi,hakan yasa tun a nijeria salima ke alalace don babu kwaba balle hantara da zarar kin kai shekaru goma sha takwas a gidansu to kina da yancin yin komai da kika ga dama,iyayenta na da arziqi daidai gwargwado don su suka dau nauyin karatunta ta fita indian

Mutum daya ne salima ta yarda da shi ta sallama masa jikinta a nijeria suke harkarsu duk da tana bawa wanda taga dama kanta yayi tabe tabensa don a cewarta ita babbar harka take,sai kuma zuwanta india ne wani abokin karatunta rahul,shima din tunda ta hadu da aliyyu tayi mishi fata fata sukayi handing over don kuwa tunda ta ga aliyyun tayi amanna ta samu kalar namijin da take so ya zama miji a gareta ya hada komai hundred percent

Cikin lokaci qanqani salima ta dage a tada maganar aure don kuwa tsoron take kada ta rasa aliyyun saboda tana ganin yadda mata jinsin qabilu kala kala dake indian mazauna can yan asalin indian da kuma baqin haure ke kara kaina akansa abunda ya sauqaqa abun ma babu fara'a ma bisa fuskarsa ko yaushe tana daure ne tamau balle kice zaki kawo masa wargi

Bai damu ba suka koma gida nijeria aka gama komai sannn ya dauko ta suka dawo indian saboda business dinsa ita kuma ta samu ta kammala karatunta,dole salima ta yakice duk wani abokin shashancinta saboda matsananciyar qauna da take ma aliyyun

Ba qaramin tashin hankali aliyun ya shiga ba yadda ya sameta ba budurwa ba duk da bai san ya budurwar take ba hakanan tasha stitches duk don ta matse,yafi aqalla sama da wata abun ma dukansa amma kasancewar sa mutum mai tsananin kishi da baijin zai iya auren mace ya saketa wani ya aureta yasa ya qyaleta,bugu da qari tsantsar qauna da take masa tamkar ta fidda ranta ta bashi,yayi imanin idan ya rabu da ita mawuyaci ne taci gaba da rayuwa parfectly

Cikakkiyar kulawa aliyyu ya dinga samu sosai daga farkon aurensu duk da ya fuskanci qalubale da dama na wasu ayyuka na cikin gida wanda ya zama dole kowacce *cikakkiyar mace* ta iya su,kama da girki zuwa tsaftace gida amma sai yayi haquri da hakan yake koya mata wasu abubuwan da niyyar idan sundawo gida nijeria zai turata makarantar koyon irin wadannan abubuwan

Abu na farko da ya fara kawo babbar baraka a zamantakewarsu wanda shi ya zama sila kuma sanadiyyar barkewar alaqar dake tsakaninsu shine,wata uku da yin aurensu ta soma rashin lpy,tuni suka yiwa mumbai general hospital tsinke sabodancita take sosai ,ba bata lokaci likita ya fara aikinsa cikin dan taqaitaccen lokaci sakamako ya bayyana sun samu qaruwa Allah ya albarkaceta da samun juna biyu

Ba qaramin tashi hankali da razana aliyyu ya tsinkaya ba kan fuskar salima shi da ya tsammaci ganin farinciki,tun acikin asibitin take kuka wi wi har suka iso gida,duk da ya kawo abubuwa da dama cikin ranta game da kukan da take sai dai ya hani zuciyarsa da yanke hukunci bisa zato da zargi,don ya tabbatar ya matsa mata da tambayar mekw faruwa? Bata yi qasa agwiwa ba kuwa budar bakinta tashin farko ta ce masa"gaskiya darling ban shirya haihuwa ba yanzu babu abinda ke cikinta banda wahala da tsofar da mutum,just shekarata ma nawa da zan fara shiga rayuwar raino da wahalar 'ya'ya?,am just 25 fa"ta qaraahe maganar idanunta na malalo da hawaye

Da fari ua dauka rashin fahimta ne saboda boko da ya dabai baye rayuwarsu don haka sai ta ma bashi dariya ya murmusa idanunsa akanta yace"that's my salima,wannan tunanin naki fake ne it's not real,haihuwa ai ni'imace daga Allah wanda kudi ko mulki ko wata isa basu isa su baka ita ba,tsufa kuma ai lokacine,idan yazo babu abinda ke tareshi,bama haka ba idan kika ga haihuwa tasa mace tsufa ya danganta ko daga gareta ne rashin gyara ko kuma daga yanayin kulawar da take samu daga mijinta,ke kam baki da wannan matsalar ko daya,come on baby dont bother your self kinji,I promise I wil be with you cikin ko wanne irin yanayi"

Wannan duk baiwa salima ba tun aliyyu na rarrashinta har ya gaji ya sanya mata idanu,daga qarahe ma ganin ya zuba mata idanu sai tayi tsammanin ko ya haqura ne gaba daya?,sai kuwa ta fito masa da aniyarta na son zub da cikin wai ko don ta samu taci gaba da yin karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tunda tana final year dinta watanni kadan suka rage mata zata fuskanci exams

A ranar taga bacin ran aliyyu irin wanda bata taba ganin irinsa ba,yayi mata kaca kaca ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba ya mata jan kunne mai zafi akan kada ma ta yarda koda mistake wani abu ya samu cikinsa bazai lamunta ba bare kuma intentionally,ta tsorata ainun amma duk da haka ta kafe ta turje akan bata ga abunda zai sata zam da cikin ba tunda bata so ai ba'a dole shi kuma yace zai mata dolen kuma zata gani,kamar ta haqura amma zugar qawaye na sake tunzurata,cikin rikici ta dinga rainon cikin ji take kamar tasa hannu ta fisgo abinda ke cikin ta jefar ta huta,wani takunkumi ya kafa mata ya hanata fita ko ina hakanan ya hanaduk wani mai zuwa zuwa gurinta,makaranta ma shike daukarta ya kaita ya kuma tsaya a bakin inda da zata dau lecture din har sai ta kammala ya daukota ya maidota gida ya kuma kulleta sannan ya fice sabgoginsa

Da wannan rikici ta kammla karatunta yayi clearing din komai nasa ya dawo Nigeria shi da ita gaba daya sai dai idan wani abu ya kamashi na yaje indian sai ya tasata agaba suje tare su dawo tare don kada ma ya barta tsautsayi ya gifta tayi abinda ranta ke raua mata,don baijin idan ta aikata hakan zai iya qyaleta ko ya daga mata qafa,

Ita kuwa ta samu sake rigima harda mara dalili yinta salima take dom dai taga duk ya dora burinsa kan cikin,ya zuba mata ido ne saboda albarkacin yaronshi da take dauke da shi gashi mai tausayi ne qwarai da gaske kan mace mai ciki,hakanan tsakiyar dare sai ta tashi ta zauna ta kuma taahi aliyyun suyi kwanan zaune ta kuma kwana tana rusa masa kuka da ihu ita wai cikin ya dameta ya hanata sakewa

Cikin haka ne ranar wata juma'a aliyyubya fito a masallaci aka masa waya asibitin doctor sa'adah yazo salima ta haihu,yayi matiqar mamaki don kuwa cikin watansa takwas da sati biyu kuma lafiyar Allah ya fita ya barta a gidan babu wasu alamun naquda tare da ita don baccinta ma take shirga,baiyi qasa agwiwa ba ya isa asibitin cike da murna doki da koma mamaki,yana zuwa ya samu qarin bayanin zuwa tayi aka turo naqudar ta qarfin tsiya wai ta gaji da zaman cikin ajikinta don lafiyarta lau ta iso asibitin,yayi fada sosai don sunga doctor sa'adah bata nan ne da ko bakin salima zai cire don roqo bazata yi mata ba har sai da yarda da kuma izinin aliyyun

Ransa yayi mummunan baci saidai yana yin tozali da santaleliyar baby girl din da Allah yayi masa kyautarsa sai farin ciki ya mamaye gurbin bacin ransa tuni yama mance da abunda ya faru,sak kamammin family dinsu tayo ya rungume yarinyar tsam tsam a qirjinsa qaunarta na mamaye jinin jikinsa,ya dinga kissing din yarinyar da tofeta da addu'o'in tsari kala kala,tuni gidansu ya cika da yan uwa mominsa farin ciki tamkar akan yarinyar ta fara jika,duk wani uatsina da salima keyi da daga kai ita da yam uwanta hakan bai dami yan uwan aliyyu ba domin su gadon arziqi ne ba taka shi sukayi suka haye ba rana tsaka,harkar girma kawai sukeyi

Suna akayi na tserewa sa'a,yarinya tayi albarka sosai don daga salima jar aliyyin babu wanda bai ga hakan ba,khadijatu shine sunan da ya mominsa ta zaba mata don abba ya bawa zabi shi kuma yace ya bawa momin ta zabawa kishiyarta sunan da kanta tayi murmushi tace ta

Please Login or Register in order to submit comment