Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idar babu aliyyu ba alamunsa,zama tayi kan daddumar jiki a takure,kewa ce sosai ta kamata,ita ba layin qasar cikin wayarta bare tayi kira,a gogon ta sake kalla ya nuna mata qarfe goma da minti biyu,tsoro ya sake shigarta musamman da taji unguwar ya sake yin shiru ba komai ke tashi sai haushin karnuka🐕da keta kai kawo

Dif wutar gidan ta dauke gaba daya,gabanta yayi wani matsanancin bugu yadda duhu ya mamaye gidan ko tafin hannunta bata iya gani,tuni jikinta ya soma rawa ta dunqule guri guda tsoro ya mamayeta haushin karnukan sai take jinsa kamar a qofar gidan

Bata san sanda ta wuntsila tayi bayan kujera ba jin haushin karen a bakin qofar falon hadi da tsaiwar mota wadda aka yiwa full light aka dallare gidan gaba daya daga baya aka kashe,ai bata san sanda ta saki kukan tsoro ba dumin hawayen kawai itama taji,cewa take shikenan na banu,kusan minti biyar sannan ta daina jin motsin karen,zama tayi dabas a qasa hadi da dafe goshinta da tafin hannunta,kuka sosai ta saka,tana bala'in tsoron kare arayuwarta,don duk gidan da zata matuqar suna da kare to komai mutuncin da kuke tafa bar zuwarmuku kenan daman yaya lafiyar kura,yana daya daga cikin abinda yasa bata saba da gidansu aliyyu ba bata zuwa kenan da can suna da karnuka har biyu kafin daga bisani uncle abba yasa aka fita da su

Sam bataji shigowa ba sai takun sawaye ta ji,a guje ta miqe tana neman mafaka a rude ,ji tayi an cafkota cikin duhun,ihu ta bude bakinta da niyyar yi ko da wanda Allah zai sa ya kawo mata dauki sai taji ansa hannu an toshe mata baki dai dai lokacin wutar ta dawo,fuskarsa cikin tata yake kallonta ya zuba mata qwayoyin idanunsa,fuskarta tuni tayi jage jage da hawaye jikinta sai bari yake don sai da wutar ta dawo ta gane ashe tuni har hular kanta ma ta cire saboda tsabar rudewa😂

Ita ta fara janye idanunta hadi da kawar da kanya gefe ganin shi bashi da niyyar janye nasa sexy eyes din da ya zuba mata,qoqarin zame hannunta take har a lokacin kanta na gefe tana kuka mara sauti don iya tsorata ta tsorata,jikinsa a mace yake murus ga gajiyar zirga zirga da ya wuni yana yi tuni rigarshi ma ta saman ya cireta a hannu ya shigo da ita,yaqi sakin hannun nata yayin da yake qara zuba mata wani dafin mai illa ga ruhinta har cikin qwaqwalwarta don baisan me riqe mata hannun ya jawo mata ba,ta kuma rasa me yake yi a tsayen har lokacin don qeya ta juya masa idanunta bai kansa ta kuma qi kallonsa

Gashinta yake kallo dake ta sheqi shigar ta karbeta sosai kamar yasa hannunsa ya shafa gashin saboda sha'awar da ya bashi sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi "zaka jawowa kanka raini" a hankali qamshin turarenta ya ci gaba da sakar masa da gabobi da qyar ya Iya dauke idanunsa yana jan tsaki cikin ransa yana jin haushin kansa

Mrs muhammad ce😘

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻
[10/16, 1:58 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

3⃣7⃣&3⃣8⃣

Ji tayi an janyota baya an zaunar da ita saman kujera ta dago kai suka hada ido fuskarnan tasa kamar dai koda yaushe,ta sunkui da kai hawaye naci gaba da zuba,tana jin tausayin kanta ne cikin zuciyarta soyayyar aliyu ta gama yi mata illa,yana tsayen dai yayin da ya sauke dukka qwayoyin idanun nasa a kanta yana kallonta ita kuma kukanta take haiqan mara sauti lokaci lokaci tana sa tafin hannunta tan rage ruwan hawayen ta hanyar sharesu hadi da jan majina

Kusan minti biyar sannan taga ya dora mata handkerchief saman cinyarta qamshin turarensa da yake jikin handkerchief din ya daki hancinta,briefcase dinsa ya dauka ya wuce daki,saman gadon ya fada yayi rigingine yayin da qafafunsa ke qasa hadi da cewa *"ya Allah"*

Lokaci sosai ya bata yana maida numfashi tukun kafin ya miqe ya cire kayan jikinsa ya sanya rigar wanka ya wuce bandaki,ko cikin toilet din ma haka ya dade cikin bathtub kafin ya cude jijinsa ya fito,jallabiyya ya gani saka da short nikker gefan gadon a ajjiye bai kawo komai cikin ransa ba bayan ya tsane jikinsa ya shafa lotion dinsa sannan ta taje soft sumarshi ya feshe jikinsa da designers turarukansa ya jawo kayan ya sanya

Har yanzun tana bisa kujerar saidai yanzu har jingina tayi lokaci lokaci ta na dan saki ajiyar zuciya irin na wanda ya sha kuka,kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa ita kam dama ko sashin da yake bata kalla ba don haushinsa take ji,sai da ya fara zuwa gun makunnin t.v ya kunna ya dauki remote ya qaro volume gidan talabijin dun qasar ne ke labarai ya maida remote din ya wuce dining,da kansa wannan karon yayi serving din kanshi sannan ya soma cin abincin,yaci abincin sosai ba tare d shi kanshi ya san yaci haka ba

Tuni bacci ya dauke ya dauketa kafin ya kammala,ta takure kan kujerar kamar kwanciyar jariri cikin mamansa,ajiyar zuciya take saki kadan kadan cikin baccin,a hankali ya qaraso gabanta ya tsaya bayan ya kammala duk abunda zaiyi,ya zuba hannayensa cikin aljihun short nikker dinsa ya zuba mata ido "sleeping beauty" yaji zuciyarsa na fada,wata sha'awa matsananciya ta taso masa har wani yarrr yaje ji cikin jikinsa,ya tabbata da da salima yazo kai ko samira ce da tuni an wuce gun

Itama ita gani yake kamar bada kaine ya tunkareta tunda dukkansu sun fita shekaru,ta sake jan wata doguwar ajiyar zuciya cikin baccin nata harda juyawa,ya kalli hannunta handkerchief din da ya bata ne duqunqune tsakiyar dogayen yatsunta,karo na farko wani abu mai kama da tausayinta ya ratsa zuciyarsa,ya tuna yadda ta tsorata dazun ya tabbata rashin dawowarsa ne da baiyi da wuri ba da kuma dauke wuta da akayi wanda qarewar kudin wutar su ne daga can company din ya jawo haka,yasa hannunsa ya danyi mata baya da gashinta da keson shigar mata ido

Da sauri ya janye hannunsa kamar wanda wuta ta ja,ya daga kai ya kalli lokaci sha biyu na dare saura minti shida,yasa hannu a ahankali kamar jiya ya zare filon nata,a tsorace kuwa ta tashi don har sai da yasa hannayensa ya tareta don kada ta fado,sai bayan ta nutsune suka hada ido ya janye hannunsa tayi qasa da kanta,tana jin takunsa sanda ya shige bedroom,sai da ta tsaya ta tattare kwanukan ta mada kitchen dare ya riga yayi ga dan Karen tsoro wanda ya hanata gyare gun kamar yadda ta saba

Tamkar jiya yauma kwance yake saman center saidai yau lullube yake da wani qaton lallausan farin bargo ba irin na kan gadon ba,saidai ya debe gaba daya filallukan kamar jiyan blanket din kawai ya bar mata

Again yauma dai sallar ta tarar da shi yana yi saidai ita bayan sallar asuba bata koma bacci ba breakfast ta hada masa don taji da yana waya kamar yana cewa zai fito da wuri zasu Beijing

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Washegari maqociyar ta ta hannun hagu mr lin ta shigo mata 'yar asalin qasar china dince tana da yara uku,sosai fadila taji dadin kulawar da ta nuna mata sun dan jima suna taba hira har daya mqociyar tata ta shigo,sunanta nadiyya 'yar asalin alqahira ce sai fadila tafi farinciki da nadiyya fiye da mr lin saboda addini da suka hada duk da cewar itama mai kirki ce,saidai ita nadiya yaronta daya mashkur sai mai gidanta abdul-basid karatu ne ya rabosu da qasarsu,sunyi hirarsu da ita sosai cikin harshen larabci don ta nan bangaren ma ba'abar fadilan a baya ba

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Rayuwa aqasar da baka da kowa ba wanda ka sani bata fiya dadi ba ba kamar idan kana qasarka ta gado ba,to hakanne ya kasance ga fadila da zarar aliyyu ya fita ta kammala aikace aikacenta sai ta koma kan waya ko computer ta duba saqonni,idan ta gaji sai ta sanya hijabinta ta dawo balcony ta zauna tana kallon masu shige da fice,duk da cewa unguwa ce da bata da yalwar jama'a amma ba'a rasa masu wucewa jefi-jefi har wasunsu kan tsaya suyi mata magana ganinta baqar fata mutanen qasar mutane ne masu so da girmama baqo hadi da mutunta shi

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

A irin wannan ne ranar bayan ta kammla aikinta da wuri ta hau social media dinta ta gaji ta dawo balcony kamar yadda ta saba,saidai yau da gobe sai Allah sai zaman nan din ma ya gundireta,wasu 'yammata su uku ta gani sunzo wucewa dukkaninsu akan kekuna suna tafe ajere suna hirarsu abinsu🚴,sai taji tana da sha'awar zaga koda layin sune zuwa qarshensa

Cikin zumudin tunanin da tayi ta zqro wayarta ta dan yima aliyyu text, _*please zan dan fita qarshen layi*_

Mrs muhammad ce👑

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*

3⃣9⃣&4⃣0⃣

Ta kalmashe wayar a hannunta bayan ta tabbatar saqon ya je,ta miqe ta saya qofar don bata damu da sai ta kulle ba ta san qasa ce mai cike da tsaro

A hankali take ratsa layukan duk da dan banzan sanyin dake bugarta amma yanayin yayi mata dadi sosai,tana tafiya tana cilla hannayenta gaba da baya fuskarta qunshe da murmushi ,unguwar ta burgeta matuqa babu yawan jama'a tunda dama can ita bata son hayaniya,sai yara jefi jefi dake wasa wasu cikin balcony dinsu wasu kuma a qogar gida duk wasannin nasu baya wuce tseran keke da buga qwallo(football)

Abinda ta lura da shi shine su kamar ma sanyin bai damesu ba ba mamki ko don qasarau ce sun saba,har ta fita daga layin da shiga second street bata sani ba,yara ta gani su hudu babbar ciki ba zata wuce shekaru tara ba ma bi mata ba zata wuce takwas ba ta ukun kuma ba ta gaza uku qaramar ce mai alamun biyu amma da yake yanayin qasarsu ya bam banta da namu buka buka da su masha Allah,ball suke bugawa suka bugo mata saidai a qafarta ta sauka basu sameta ba

Babbar cikinsun ce ta fara lura da wadda suka bugawan ta tabo mai bi matan tana mata rada akunne tana kallon fadila duk sai suka juyo suna kallonta,fadika ta sunkuya ta dauki ball din ta nufi inda suke fuskarta dauke da murmushi suma murmushin suke saboda ganin baquwa,ta ajjiye ball din agabanta tabuga ta ta tafi gabansu ai kuwa suka hau ysalle da murna suka dawo mata da ita,duk da bata jin yarensu amma ta gane dadin hakan sukeji

A nan gurin yaran ta bata lokaci sosai ba tare da ta sani ba,yaran sun sake sosai da ita nan ta hada su dukkaninsu ta shige tsakiyar su tayi musu hotuna,suka shige gidajensu suna daga mata hannu,sai alokacin ta duba gari taga ya soma duhu hankalinta a taahe ta juya ta soma laluben hanya garin haka sukayi kacibus da mutumin nata (kare)shaf ta manta kare baya son gudu don a rude take tuni ta takure ta sheqa a guje shi kuwa ganin haka ya rufa mata baya

Motar kamfanin ta ajjiye aliyun a qofar gida yayi sallama da su yana jaddadawa wanda ke gaban motar su tabbatar gobe early in d morning sun kawo engines din nan an qarasa kafasu agurarensu,ya amsa masa cikin girmamawa,suka ja moyar shi kuma ya juya ya shige gidan

Qwan lantarkin na kashe yasa hannu ya kunna haske ya gauraye falon,neat yake kamar ko yauahe cike da qamshi ya jefa rigar samansa da ya cire hade da jakarsa kan kujera shima ya zauna,a gajiye yake tubus ya soma zare takalminsa da safarsa sannan ya kalli inda ta saba ajjiye masa ruwa da lemo wandayake fara sha da zarar ya dawo,wayam babu sai abincinsa dake jere saman dining,yanmiqe ya bude freezer wanda basu kunnata sosai yanzu saboda yanayin sanyin garin ya ciro ruwan roba,ko cup bai nema ba ya balle murfin ya kafa kai sai da yasha kusan fiye da rabi sannn ya maida ya rufe

Bedroom ya nufa don yin wanka hadi da alwala cikin zuciyarsa yana mamakin rashin jin motsi ko yaya cikin gidan,mamakinsa ya dadu ganin babu ita a dakin ya bude toilet babu ruwan wankansa wanda ya riga ya saba ya tadda shi yana jiransa,tunaninsa sai ya tafi ga ko tana kitchen,ya nannade hannun rigarsa ya daura alwala idan yayi sallar daga baya yayi wankan tunda yau bai samu ruwan ba,har ya shimfida abun sallah zai tayar sai kuma ya fasa zuciyars ta kasa samun nutsuwa,sai yakejin wani irin rashin ganinta amma sai ya alaqanta hakan da sabawa da yayi da ganin nataidan ya dawo

Kitchen din ya nufa kai tsaye bata nan,wani dim yaji zuciyarsa ta harba💓,ya riga ya sani tunda auke da ita bata taba fita koda qofar gida ne ba tate da izininsa ba,a hanzarce ya koma bedroom inda ya ajjiye wayarsa saman madubi call logs ya shiga da sauri da sauri yana dubawa dinta ko Allah zaisa yaci karo da number dinta,tsaf ya gama bincikensa bai ganta ba,ya saki ajiyar zuciya hankalimsa amatuqar tashe,sai sannan ne ma idonsa ya kai kan 'yar qaramar envelope dake maqale saman wayarsa wanda ke nuni akwai sabon saqo a wayarsa,

Har zai maida wauar aljihu sai ya fasa ya jawo saman wayar ya shiga gun sms,numbers ne guda biyu daya ba suna daya kuma ta mr jake ne,yana gama karanta tex din ya tabbatar ita ta turo masa shi baisan sanda ya juya ba ya zira silifas ya fita a sukwane ,da sauri yake daddanna numbobin jumong daya daga cikin direbobin kamfaninsa wadanda suka fi kusa da unguwar da auke ciki yave ya kawo masa mota yanzu yanzu,bai iya ysayawa jiran mitar ba ya fita da qafafunsa yana ji ajikinsa cewa hanyar dawowa ta rasa

A hanzarce yake tafiya,kasancewarsa giant ma'abicin kuzari sai gashi yayi tafiya mai dama kafin isowar jumong din

Ta waiwayo cikin gudun dai bata fasa ba taqin dake tsakaninta da karen dan kadan ne,ta saddaqar cewa ta gama yawo,tuni tayi surrender ta tsaya cak lokacin da taga ya daka tsalle tana jiran taji ya yago ta,qyam tayi jinin jikinta adaskare,rungumeta taji anyi yayin da qamshin turarensa ya mamaye mata hancinta,tsawq taji ya daka wa karen ta bude idanunta ahankali yayin da dumin jikinsa ke ratsata,sum sum taga karen ya juya cikin sassarfa ya bar gun,sai da ya bace alayin sannan ya juyo ya kalli qwayar idanunta,idanunsa fal da fushi sai huci yake,hannunta ya fincika ya bude bayan motar ya sanyata sannan shima ya shiga jumong ya tada motar

Bai ce mata uffan ba kamar yadda bai sake kallonta ba idanunsa na bisa titi har yanzu kana ganin fuskarsa kasan cikin fushi yake,kuka take kanta na qasa ita kanta ta rasa kukan kuma na mene tunda Allah ya taimaketa,sai da suka qaraso gidan sannan ta tabbatar aahe tafiya tayi mai yawa bata sani ba irin haka?

Ya bude side dinsa ya fito sannan ya bude nata ya damqo hannunta ya fito da ita,jumong nata cewa"gudnyt sir" amma baibi ta kansa ba,saman kujerar ya cillat yana huci,shi kansa bai san me yasa yake jin wani fushi ba don ta bata hakanan yake jin wani tashin hankali da bai ganta ba,cikin jikinsa yake ji kamar *ZATA IYA GUDUWA* wataran tace zata barashi,

Saman kujerar ya dora qafarsa yayin da ya sauke dayar a qasa yana tsayw gabanta,kukanta har yanzu take ci gaba da yi harda dan sautin sheshsheqa,hankalinsa gaba daya ya rabu biyu ,hukunci sosai yake son yayi mata saboda kada ta sake fita har ta bace agaba,yayin da qamshin turarenta keta rarŕaba masa hankali,ya kasa komai kukanta na ci gaba da shiga kunnuwansa,hannu ya dunquke ya daki kujerar da suke kai "keep quiet"ya fadu cikin tsawa,hannu tasa ta rufe bakin nata hawaye naci gaba da silalowa🙊,ya dage girarsà yana fadin"kiwa mutane laifi kuma ki sasu a gaba kina masu kuka?ko don kinga bakinki yafi nawa iya kuka?"ya qarashe maganar da sigar tambaya

Ita dai babu abinda tace,kusan minti biyar shiru ya ratsa falon hawayenta naci gaba da silalowa shi kuma yan ci gaba da kallonta yana jin 2ani abu kamar ya zaqe da yawa why?,a hankali ya juya yana barin gurin hadi da cewa "silly girl"

Abincin da bai iya ciba kenan a ranar ita da kanta kuma sai taji bubu dadi,koma mene tasan batan ta ne ya bata masa rai shi kuma ya jawo mishi,da bacci ya dauketa ma kan kujera da asuba anan ta farka ta ganta bai tashe ta ba kenan

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻


[10/16, 1:59 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

4⃣1⃣&4⃣2⃣

Kwana uku tsakani tana zaune ya kawo mata foam🗞,gefan ta ya ajjiye bata san na mene ba sai da ta bude sannan ta duba sosai ta gani ashe na wata instute ce, sabon corse ne kan aikin jarida zasu fara wata uku ne kacal za'a kammala,daga qarfe goma na safe zuwa daya na rana,zaka iya attending classes dinsu kokuma ka dauki lecture din online kana daga gida

Tsalle ta dinga yi cikin murna bata san aliyyu na tsaye ba qofar kitchen ashe ita ya zubama ido,a hankali suka hada ido tayi saurin komawa ta zauna kunya ta kamata shi kuma ya ya dauke kai ya shige kitchen din,a nutse ta dinga cike foam din har ta kammala da maida cikin envelop

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Sosai fadila ta soma jin dadin karatunta duk da online take daukan lecture ko yaushe tana gaban computer din ta,koda ta kammala daukan lecture sai tayi zamanta tayi ta research,tun daga lokacin da abin ya faru itama bata sake gigin fita ba,iyakacinta gidan nadiyya ita din ma ba sosai don gidan mr lin ma sau daya ta taba leqa mata,sai dai su turo mata yaransu suyita taya ta hira don ma bata gane yaren nasu tafi hira da mashkur don ya iya yarensu na larabci sosai

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Zaman garin yanzun bai fiya takurata ba sosai tun lokacin da ta fara daukan lecture dinta,sosai computer din ta sake zama abokiyarta shi kansa uban tafiyar ya lura da yadda gaba daya walwalarta ta koma kan laptop dinta,haka nan sai ya soma jin haushin computer din gani yake kamar ta tsare masa wani abu da ya rasa mene shi gaba daya bata da wani sukuni sai ta zauna a gabanta

Shi yasa wani lokacin da zarar yaga ta dauko da niyyar yin karatu sai ya tsiro wani aikin na babu gaira babu dalili,cikin zuciyarsa yake gulmar "reading like machine"karatu kamar ranta,(hmmm kaji fa gwano baijin warin jikinsa shi da yake wuni zirga zirga da kai kawon bude company dinsa)

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Kamar kullum yauma tara daidai ta kammala dukkanin ayyukanta sabida goma zata zauna lacture,tana sanye cikin kayan sanyi na turawa ta yane kanta da dan qaramin hijabi fari tas iya kafada,shigar orange and white 🔶⚪tayi sai ta haska chocolate colour skin dinta,tana tsaye a dining area tana zuba masa farfesun kan rago cikin plate ta hada masa tea cikin cup☕ don ya dan sarara kafin ya fito

Taa cikin rufe flask dinne taji takun tahowarsa ,a dabarance ta saci kallonsa ta gefan ido cikin rashin sa'a ya kamata,da sauri ta dauke idonta ya qaraso dining din ya jawo kujera daya ya zauna hadi da dora briefcase dinsa a dayar ya ajjiye wayarsa kusa da cup din tea📱☕,itama kujerar ta ja ta zauna kamar yadda yakeso kenan idan zaici abinci(🙄🙄🙄 hmmmm)

Ta sake satar kallonsa a karo na biyu suka sake hada ido "hold on ur sight"ya fada yana kai cup din bakinshi,sai ta danji kunya ta kamata duk da shi din ma tasan satar kallon nata yayi har suka hada idon,tsakanin jiya da shekaran jiya zuwa yau gani take mood dinshi ya canza,duk da dama bawai mai fara'a ne ba amma taga sauyi cikin walwalarsa da kuzarinsa,hakanan ayyukan da yake tahowa da su yayi ta lodawa cikin laptop dinsa ya ragu sosai

Haka nan cin abincinsa ya ragu daga kusan kaso saba'in cikin dari,cikin ranta take ganin bata da wani matsayi gurinsa bare tayi gigin binciken meke damunsa,kamar yadda ta zata kuwa tea din kawai ya shanye ya miqe yana rataye jakarsa ya kuma ajjiye mata yuan 100 kamar yadda ya saba,a hankali yake saukowa daga daga step din dining area din kamar mara laka

Tuni qamshinta yayi masa rugu rugu da gangar jiki da kuma zuciyarsa,babu abinda yake buqata a yanzun idan ba mace ba koda samira ya samu ayanzun zai iya maleji da ita,har sai da ya fice sannan ya kauda kanta daga kallonsa ta maida idonta kan table din inda ta hada kayan break,tea kawai itama ta iya hadawa ta sha ta kwashe kayan ta gyara gun takai kitchen ta wanke ta dawo kan computer dinta don yin karatun

Qarfe daya da mintina goma sha biyar ta kammala ta rufe laptop din,ta danyi miqa irin ta gajiya tana yar hamma,ta jawo wayarta ta dan duba saqonninta na watsapp na tsawon minti arba'in sannan ta sauka,sallah ta soma yi don biyu tayi sannan ta kwaba alkubus don shi ta shirya yi yau

Tana tsaka da aikin nadiya ta shigo nan ta zuba ido tana mamakin me fadilan ke hadawa haka?,dariya fadila tayi tace irin abincimmu ne

Sai qarfe uku nadiyan ta tafi fadilan ta rakota bakin qofa tana gaya mata idan ta gama zata ta turo mashkur ya karba mata taci taji,ta saye qofar falon ta koma kitchen din fara aikinta,ta kammala komai da wuri ta gyara gurin ta koma bedroom don daura alwalar sallar la'asar don har tana qoqarin subuce mata

Turus ta ja ta tsaya ta kuma saki baki,jakarsa da rigar suit dinsa na watse saman sofa shi kuma na kwance saman gado ko takalmin qafarsa bai tube ba,cikin mamaki take satar kallonsa tana mamakin yaushe ya shigo gidan don ko alamunsa bata ji ba,kuma ma mainya dawo da shi gida a wannan lokacin

Rabawa tayi ta shige toilet ta dauro alwalar ta fito ta dauki abun sallarta ta koma falo,bayan ta idar ta koma saman kujera ta zauna sai dai hankalinta ya kasu rabi na kan t.v rabi na bakin qofar bedroom din don har yanzu bata ji motsinsa ba

Hankalinta ne ya gaza kwanciya cikin sanda ta miqe ta tura qofar tana leqen saman gadon,har yanzu a kwance yake kamar yadda ta barshi,ta qarasa bude qofar gaba daya a hankali cikin sanda ta qarasa bakin gadon ta duqa ta kama qafarsa a hankali ta zame masa takalman bai motsa ba har ta gama cire masa sai tayi tsammanin bacci yake ta sabule masa socks din ta cusa cikin takalmin ta kwashe su ta maida su muhallinsu

Ta juya zata fice ta sake waiwayowa kalleshi idanunsa na lumshe kan hancinsa yayi wani ja irin na farin mutum kamar an murza gun,ta kauda kai ta fice daga dakin,duk abinda take yana kallonta idanunsa biyu,matsanancin zazzabi da yake ji da ciwon ciki mai azaba wanda ya jima rabonsa da shi shi ya hanashi koda yin motsi,yasan yadda ciwon cikinsa yake idan ya kamashi baya masa ta dadi,sai yaji dadin yadda ta sake dawowa ta dubashin ganin bai fito ba,ya tabbata kasa nutsuwa tayi da rashin ganin bai fito din ba

Sai da ta shigo daura alwalar sallar magariba sannan ta ganshi zaune kan abun sallah a side din gado duk da bata ga fuskarsa ba kansa na aduqe,ta sake wucewa tayi alwalar

Qarfe tara na dare zaman falon ya gundireta ita daya kamar mayya,sabo mugun abune zaman da sukeyi tare duk dare shi ya sanyata kewa ganin yau babu shi duk da ba wani zaman da za'a fadeshi bane kowa harkar gabansa yake duk da da zarar daya yayi wani motsi mai qarfi zaka ga hankalin dayan yayo kansa

Sai da ta hada masa coffee ta hada harda abincin cikin babban tray guda daya don har lokacin bai ko leqo koda falon ba bare yaci abincin nasa,ta dauka bayan ta gama shirin kwanciyar ta cikin night gown riga da wando ne wandon har qasa rigar iya gwiwa cotton ne very soft sai hijabi saboda sanyi

*Mrs muhammad ce*
👑😘

📚📚📝📝✍🏻✍🏻✍🏻

3:54 pm 5/09/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*

4⃣3⃣&4⃣4⃣

Ta ajjiye tray din kan bed side tana tunanin ina ne makwancinta yau kuma?,saboda aliyyu na kwancene a kai crossing gadon,bata jin kuma zata iya kwanciyar qasa yadda shi yakeyi domin matsanancin sanyin garin ya girmi qashinta,ta kuma kallinsa karo na biyu yana duqun qune cikin bargo gaba dayan jikinsa kansa ne kawai a waje

Sai ta rasa ta yadda zata tada shi tafi qarfin minti goma ahaka kafin dabara ta zo mata,gyaran murya ta taqarqare ta ja har aai da maqogwaronta yayi mata zafi,a hankali ya bude idonsa ya zubesu fes kan fuskarta tsakiyar qwayar idonta,fadila ce ta soma janye nata qwayar idon tana jin wani magnet na fusgarta,tabbas ba don aliyyu mutum bane zata iya cewa wani mayen qarfene cikin idonunsa

Please Login or Register in order to submit comment