Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waiwayo tace"ko kasheni zakayi ba zan fasa ba" tadai sake nufar kayan cikin azama a karo na uku,cikin fusata yasa hannu ya janyota baya harsai da ta zube warwas a gun tamkar ya bita ya tattaka haka yake ji,don da namiji ne ya masa haka to yanajin ba shakka sai ya nuna masa qwarin qwanjinsa
Ta sani cewa idan taci gaba da abunda take hukuncin da zai yanke mata ba mai sauqi bane hakan yasa tana daga zaunan ta hau borin kunya cikin surutai da maganganu marasa kan gado daga baya ma da taga ya qi kulata sai ta fashe da kuka
Ko kallo bata isheshi ba ya dinga siban akwatunan bibbiyu bibbiyu ya shigewa da au bangarensa yana gamawa ya rufe qofarsa ya barta a nan,data waiga ta waiga taga ba kowa ba wanda ya gansu sai ta goge idonta ta miqe tana kade zaninta tana wa allah godiya da ba wanda yaga abinda ya faru tana yi tana tsinewa hannatu qanwarta gashinan ta jawo mata asarar akwatinan ma dungurun gum dan ita ta bata shawarar tayi haka
A falon sa ya zube ya dafe kansa hannu bibbiyu yana tsananin jimanta al'amarin to haka mata suke ne basu da hangen nesa ya jima a haka sannan ya tuno bai ma shiga bangaren dayar ba kamar yadda yake ce mata a ransa"itama idan ka shiga wataqila haukan da zata yi maka kenan"wata zuciyar ke gaya masa,ba yadda ka iya tunda itama aqarqashinka take kuma ka shigarwa 'yar uwarta indai adalcin kake son yin
Da sallama ya shiga ta amsa a sanyaye tana zaune ne kan kujera hijabin da tasa ta budewa masu shigo da kaya har yanzu shine a jikinta saidai sabanin da yanzu akwatinan a rufe suke,a fakaice yake dan nazarin falon komai tsaf yake cike da tsafta da qamshi hakanan komai a killace yake a muhallinsa da kyawunsa kamar yau aka jerashi sabanin falon samira da komai ya fita hayyacinsa saboda rashin kulawa duk da dama tsadar kayan ma ba daya bane don iyayenta basu da qarfin iyayen fadilan,kanta na qasa ta dam zamo daga kan kujerar tace ina wuni? Duk da bata sa ran masawarsa ba don bai taba amsa gaisuwarta ba ga mamakinta wannan karon sai taji yace "lpy ga kaya nan abinda babu ko baiyi ba sai ki yi maga ko ki rubuta ta girgiza kai tana cewa๐Ÿ˜” komai yayi mun gode Allah ya qara arziqi" ya lumshe idanunsa don har zuciyarsa ya ji dadin addu'ar "madalla" yace ya zaro bandir na dubu dubu guda uku ya dora saman akwatinan ya juya ya fice sai yaji wani sauqi na radadin da zuciyarsa ke masa addu'ar ta faranta ransa don tunda yake bai taba samun kwatan kwacin wannan ba daga bakin wani abu wai iyali ba
Muje zuwa yanzu aka soma
Mrs muhammad
๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป
12:45 pm 03/11/1437
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
WA YASAN GOBE?
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
โ–ถ2โƒฃ2โƒฃ
Ana ya gobe daurin aure su anty hafiza anty hauwa farida sumayya rabi'ah har da rahama suka zo wa fadila,farida ta zube dinkunan da fadila ta bayar aka mata sunyi matuqar kyau da gaske duk da tana da sababbin din kunan ma da bata taba sa su ba,kala ashirin farida ta zabar mata aka dinko su lace biyar atamfa biyar shadda biyar material ma biyar ne,anty hafiza ce ta taho mata da mai gyaran jiki gashi da lalle takanas sai hade haden magunguna namu irin na mata imgantattun na 'ya'yan itace,anty hauwa sai dariya take tana cewa o'o'o fadila 'yar gata to ai ko kece amaryar sai haka,sai dai tayi dariya ta sunkuyar da kanta qasa cike da kunyarnan ta ta,anty hauwa ta zuge jakarta ya fito da littattafai tace ga saqon momi nan,hannu biyu tasa ta amsa tana godiya litttafai ne kusan goma na addu'o'ine da kuma gyara zamantakewar aure,
Zuwansun ya sake debe mata kewa taji dadi nan suka fara tsara yadda za su gudanar da yinin su na gobe wanda ko wacce mace da za'a qarawa abokiyar zama ke gudanarwa,wuni akai ana qalqale mata jiki yayin da su rabi'ah sumayya da rahama suka zage wajen qal canzawa gidan fasali,sune canza labulaye canza carfet goge goge da ahare share duk da komai na fadila tsaf yake sai abinda ba'a rasa ba,cikin qanqanin lokaci kuwa gidan nata ya canza kamar ba shi ba,hatta qamshinsa sai da aka canza kalarsa ya zama na musamman abinka da diyar bare bari
Rahama ke tambayar fadila samirah fa?fadila tace wlh tun safe dai naji tashin motarta amma ban sani ba ko qunshin itama ta tafi "Allah ya kyauta inji anty hauwa ,bayan isha'i komai ya kammala anty hauwa tace zasu wuce sai gobe kuma idan Allah ya kaimu anty hafiza da yake kwana za suyi ita da farida tace"dama kwanciyar ku muka yi maman kausar wlh ,a'ah hafiza na bar yara su daya a gida daga su sai Abbansu wunin yau fa duka?"anty hafiza tace to don Allah ga laila(mai qunshin da ta dauko)ku sauke min ita a dorayi
Suna kan gado duk su ukun sunyi shirin yin bacci hafiza ta zubawa ido dake qoqarin shafa addu'a tace wai yau wa kuka barwa mijin ne?samira fa bata dawo gidannan ba haka kuke masa?"cikikin son rufe sirrinta da son gyara rayuwar aurenta ba tare da taimakon kowa ba tace "girkin samira ne anty bana son neman rigima da tashin hankali me zani in masa tunda ba girkina bane?salin inje mu raba dai abun fada?"daga haka suka qyale zancan
โšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœ
Washegarin aka zo akawa salima jeranta da yake aikin maza ne nan da nan yayi sauri amma akwai wasu daga cikin yan uwanta mata da suka zo da su,girkinsu su fadila sukayi sosai suka zuzzuba a manyan warmers suka aikawa yan uwan salima da wani wasu kuma suka barshi nan cikin kitchen dinta saboda mutane yan uwa da maqota da keta zuwa Allah ya sanya alkhairi har a lokacin sashin samira na kuelle ne alamar bata dawo ba kenan hakan yasa kowa ya shigo gun fadila yake yowa idan suka tambayeta samira sai tace ta tafi gidan qunshi
Ba qaramin kyau fadila ta zuba ba tamakar ita ce amaryar daga wayewar garin zuwa yanzu ta sanya kaya kusan kala takwas kenan har harabar gidan jama'ace don babu laifi yan taru duk da ba wanda suka gayyata
๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”
Qarfe sha daya da rabi na rana aka daura auren Aliyyu salim maitama da salima tukur Abubakar,kasancewar gidansu salima na na unguwar dake daura da g.r.a ne yasa yanuwan fadila na jiki da suka halacci daurin auren suka dinga zuwa ana gaisawa suna tafiya ciki kuwa harda abbanta da muhammad da ya ahmad taji dadin zuwan hakan kuma ya faranta mata ranta don tun da aka daura aurenta rabonta da taga abban nata kuma shima yaune zuwansa na farko gidan nata,ya mata nasiha sosai da ta qara mata nutsuwa ta kuma sata kuka ta sake tabbatar da cewa ba qaramin zumunci bane tsakanin abban nata da uncle abba mahaifin aliyyu tabbas babu abinda zata wa abban ta aduniyar nan fiye da ta jure zaman aure da aliyyu,anan suka bar mata muhammad zuwa yamma abban zai turo a daukeshi
Qarfe sha biyu da rabi ta sake wanka ta sanya wani Swiss lace pink ne mai dan turuwa kadan sai kore aka masa da ratsin silver din zare sai manyan dutsina masu walqiya sarqarta abun hannu da dankunne mayafi da takalmi duk silver ne dinkin riga da skert aka mata skert din eight pieces ya bude daga qasa sosai ,yayi matuqar karbarta ya haska chaculet din fatarta gashinta mai tsawo da santsi da baqi ya sha parking da pink and green din ribbom sai ya kwanta a bayanta sai sheqi yake tayi daurinta das wanda ya ta qasansa gashin nata ya fito,ta dauki turare tana fesawa taji ana kiranta maqotanta sun shigo kuma wasu na nemanta a harabar gidan saurin da take yasa ta manta bata dauki mayafi ba,suka gaisa da baqin tasa aka kawo.musu abinci sannan ta qarasa harabar gidan, nasiru ne da wasu mutane suke neman gun jibge abincin da ake ta shigowa da su,ta nuna musu store dinsu dake harabar gidan ta farko kusa da parking space
Tana shirin shigewa ciki motocin suka soma danno kai suna parking daya bayan daya,bata fuskanci su waye a ciki ba sai da suka cika harabar gun dukkaninsu cikin fararen kaya suke,Aliyyu ta hango a tsakiyarsu fuskarsa nata fitar da wani annuri cikin wata rantsatstsaiyar shadda babbar riga da yar ciki sai wando zata iua cewa bata taba ganinsa da irin wanna shigar ba ya qara wani kyau da kwarjini sosai ta shagala da kallonsa har suka hada ido
Haushi ne da takaici suka cika shi ganin yadda tayi kwalliya kuma ta fito har kusa da get a haka na tare da tayi lullubi ba,yayi mata kallon nan nasa data tsana wanda ya saba yi mata hakan yasa ta tuna a uadda ta fito fa tayi saurin shigewa cikin jama'a ta bacewa ganinsa
Tana zaune cikin baqinta sumayya ta shigo tace anty kije inji yaya sai taji maganar banbarakwai gabanta kuma ya fadi tace yana ina?yana cikin garden,dakinta ta shiga ta sake fesa turare sannan ta lulluba mayafinta,tunda ta nufo lambun zuciyarta ke dukan uku uku a haka har ta cimmasa,yana tsaye ya goya hannunsa a baya ya juyawa qofar shigowar baya,batasan yadda akayi ya gane ta shigo ba don gurin gaba daya grass carfet ne bare tace yaji takun tafiyarta ne sai ji tayi yayi gayaran murya gayaran muryan sai ya zamo kamar ya mata luguden guduma a qirjinta๐Ÿ”จ,me ya fito dake harabar gida babu lullubi?shiru tayi muryarta na dan rawa tace ka.....kay......kayi haquri"ya dan dauke wuta na dan lokaci kana ya juyo da azama kar mai shirin waftar wani abu,hakan ya sa tayi tsammanin duka zai kawo mata tayi baya da sauri cikin tsautsayi ta taka wani dutse sai kuwa ta tadeta tayi baya luuu zuciyarta na bugawa da sauri don ta gama saddaqarwa sai ya sha qasa,sai kuma ta jita jikin mutum aliyu ne ya sa singalalin hannunsa ya tallafeta ta bude idonta data lumshe tana jiran ta jita ta sha qasa sai ga idonta cikin nasa,ya tsuke mata fuska ๐Ÿ˜ kana yace meye haka tashi" tayi azamar zare jikintata tana cewa kayi haquri,sai ya harde hannunsa aqirji ganin yadda duk tabi ta duburburce yabi gashinta wanda ya bi wuyanta ya dawo kafadar ta ta dama da kallo lace din ya zauanar mata caras cas yabi lafiyayyar fatarta chaculet,ya dan dauke kansa yabi gefansa da kallo yana jan tsaki a fili
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
WA YASAN GOBE?
โ–ถ2โƒฃ3โƒฃ
Sai da ya gama shan qamshinsa sannan yace ina da baqi dame dame kuke da shi a kitchen?cikin dai rawar muryar tace akwai sinasir masa funkaso da miya fried rice sai white rice da miya,ya danyi shiru sanna yace cikin sweet a bamu sinasir da masa sai a hado da white rice tace to har ta juya yace hey! Tadan waigo idonta na kallon qasa yace idan min kawo kiyi knocking kawai ki barsu a bakin qofa ta gyada kai ta wuce
Bayan isha'i gidan ua dade ba mowa sai anty hafiza da farida suma suna gama kintsa mata ko ina suka turare shi sannan sukai haramar tafiya,godiya ta musu mai yawa su kuma suka cikata da nasiha ta rakosu tana bawa naty saqo don allah ki kawo min yan biyu tunda kika kaisu gida yaye anty minqi karbosu tace yayanku ma mita yake amma shekaran jiya munyi waya da mama sun kusa dawowa insha allah da haka suka rabu ta dawo ta koma bedroom dinta ta hada ruwan wanka wanda ya wadata da turarukan wanka,bayan ta fito ta shirya kanta ckin wani lafiyayyen material kalar qwanduwar qwai wanda aka masa ado da qyalli silver da ratsin fari kadan kadan ,shima yana daya daga ckikim dinkunan da aka kawo mata jiya riga ne da skert amma wadannan sun kamata sun muma fito da shep din ta sosai,tana gyara kayan kwalliyar dake kan madubin nata ne taji gudar yan kawo amarya jikinta ya saki ta zauna bisa dressing chair
Tana kwance bisa kujerar qaramin falonta agogon bango ya kada qararrwar qarfe goma tayi ajiyar zuciya ta gayar kwanciyarta goma da ashirin da biyu qarar intercome ta tada ita daga bangaren aliyu ne hakan yasa ta fahimci hadasu yake sonyi kamar yadda al'ada ta tanadar gabanta ya tsanata faduwarsa๐Ÿ’”,cikin nutsuwa ta sake feshe jikinta da turare turare ta lulluba mayafi a lallausan gashin kanta wanda bata daura dankwali ba
Da sallama ta tura qofar falin nasasu biyun ne suka amsa amaryar na tsaye gaban fridge tana ciro ruwan roba da lemo yayin da gogan ke hakimce bisa kujera two sitter shigar jikinsa ta yanzu ta babbanta da ta dazu duk da dai babbar riga ce yanzu ma a jikinsa ta shadda milk colour ya ajiye babbar rigar a hannun kujerar da yake kai,salima ta dan zubawa fadila ido na yan sakanni sannan ta dauke kai ta dauki plate saman fridge din ta dora kayan fadila ta samu one sitter dake gefansu ta zauna ,saluma ta janyi centre table dan madaidaici gaban aliyun ta dora masata tsiyaya ya masa ta jiye ta koma kusa da shi kan kunerar da yake kai ta zauna,fadila ta saukar da idanunta qasa tana cewa cikin ranta "ni kadaice bani da irin wanna damar me yasa why Aliyu?,na kusa samota na kusa da qarfin zuciyata insha Allah" muryarsa ta jiyo yana fadin kefa mume jira ko?,shiru na yan mintina sanna ya qara cewa"yayi miki kyau" ya ajiye wayar ,saluma tace kawai ka qyale ta ni na gaji bacci nake so nayi,fadila ta dago kai suka hada ido sai kuma kowacce ta dan saki fuskarta fadila tace sannu amaryarmu"itama da dan murmushin a fuskarta tace sannu kuna lpy"a taqaice fadila ta amsa mata da" lau"ta dan saci kallonsa shi lemonsa ma yake kurba idonsa na kan qofa
Banko qofar akayi aka shigo samirah ce sanye da baqar doguwar riga babu ko alamar hida bisa fuskarta sai dan kwalun atamfa da ta dauro a kanta wanda tayi masa daurin ture kaga tsiya,ta kama qugu tana cuno baki gaba tace da aliyu "gani" wani banzan kallo ya jefeta da shi sanna yace "ga gurin zama nan ko ina idan kuma bai miki ba.....ya nuna mata qofa da hannu๐Ÿ‘‰๏ฟฝ,sai da ta qarewa ko ina kallo sanna ta nufi kujerar da aliyun ke kai kusa dashi a daya side din ta dora qafa daya kan daya tana girgizata harara salima ta makawa samirah itama kuwa batayi jinkiri gun ramawa ba,taja tsaki sanna taci gaba da jijjiga qafarta,hara rarta aliyu yayi ya kalli qafar da take jijjigawa ta fuskanci abinda yame nufi kuma tasan ba magana zai.mata ba don haka ta sake zumbura bakinta sannan ta sauke qafar tata
Godiya ya far yiwa Allah sanna ya dora dukkaninku a qarqashin iko na kume kuma tsarin Allah ne shi ya tsara hakan kamar yadda yame da ikon tsara rayuwar ko wane bawa nasa to ma gode masa akan duk yadda yayi da tawa rayuwar "daganan ya dora da yi musu gargadi da jan kunne sannan ya tunasar dasu tsarinsa na zama a bangarensa mai girki ta biyoshi"salima ta kanne masa ido tave" dear ani dama na nasan da wanna tsarin naka tuntuni saidai kawai ya zamto kamar tunasarwa a gareni"murmushin shima ya mayar mata yace "yes"
Zuciya ta kawowa samirah iya wuya sai da ta tanka" a banza ai wai talaka ya girmi sarki dolen mutum yanzu shinr qarami ko yaqi ko ya so"cikin fusata salima tace "๐Ÿ‘‰๏ฟฝke nifa ba dake nake ba,ban gayyatar irinku a zancena don ni idan banda qaddara ba ma baki kai matsayin ma ki zama kishiya ta ba wlh don ko yar wanke wanken gidammu ta fiki kwarjini sai kuwa samira ta nuna ta da yatsa tace"๐Ÿ‘‰๏ฟฝdon kutumar uban mutum ya qara gaba mana don ni duwa wuce dole ne a zauna da ni zama daram wlh "sai suka so su kacame
Cikin wata gigitacciyar tsawa aliyu ya dakatar da su sannan yace kowacce ta bace masa agun ba zasu haddasa masa ciwon kai ba haka kawai"salima ta miqe ta shige bedroom dinsa samira kuwa ta fice tana gungunin a qyaleta wlh taci uwar mata,ita kuwa fadila abun nasu tsorata ta yayi don bata taba ganin fadan kishiyoyi ba hasaluma ma ba'a taba yiwa umminta kishiya ba gidansu daga ita sai farida sai muhammad ko a tsakaninsu ba fada suke ba don haka tun ma kafin ya kammala bada umarni su fice din ita tuni ta riga su fita yana juya lamarina ranta
Ransa abace ya shiga dakin duk yadda taso lallashinsa yayi banza da ita ta san halinsa tun ba yau ba kuma bata manta da shi din ba don haka da taga yayi banza da ita yana shirin shiga wankร  sai ta qyaleshi sai da ya fito yana shirin kwanciya sanna ta langabe a jikinsa tana bashi haquri,ya dan kalleta ya basar sannan yace matuqar kika ce haka zaki dinga biye mata kunayi a cikin gidana to na rantse babu wadda zan saurarawa acikinku,idan banda raini ma a gabana? Ta sake marairaicewa tana cewa "Allah na lura ita wannan kanta na hayaqi ne da kamar dayar ce da babu ruwana da ita,su auremin mijin kuma suce bazanyi kishi ba" shi sai a lokacinne ma ya tuna da fadila baima san sanda ta fice a dakin ba donsanda yake musu jawabin ka ta na sunkuye ne sai ya tuna rana shigen irin wanna da ya hadasu ita da samirah ba wanda ta kula a ranar ma ahi ko samiran harta wuce" ya kauda wannan yace mata" am telling uh indai kina son zama da ni cikin kwanciyar hankali" "baza'a qara ba dear"
Ganin yadda yaqi sakin jiki da ita yasa ta dinga masa wasu abubuwa wanda suka sa ala dole ya ajjiye fushinsa abinka da dama wanda yake cikin wani hali nan ya bada kai bori ya hau aka tuno da tsohuwar zuma don salima dama idanunta a goge take ta wannnan bangaren to haka shima aliyyun yake dalilin da yasa saliman ma ta kasa auren kowa kenan tayita naci har sai data dawo masa
Mrs muhammad
๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
WA YASAN GOBE?.......
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
โ–ถ2โƒฃ4โƒฃ
Cikin kwanakin amarci kawai ake ta ballewa a gidan ,salima wayayyar gaske ce ko da wani lokaci tana manne da A.s maitama samira kuwa ta kasa tsaida hankalinta gu guda,yiwa salima itada da aliyyu labe kuwa ya zamo.mata kamar ibada mintina kadan sai ka hangota tana ta safa da marwa tsakanin sashenta da na Aliyu,fadila baiwar Allah lissafinta yafi ga kwanakin da zata soma shiga office da kuma ranar da zata zamo itace ranar girki a gareta
Kwana uku kenan da tarewar salima fadila ta soma zuwa aikinta ya kama ranar laraba,shiga tayi ta hausawa atamfa ce dinkin riga da zani wadatattu yayin da tayi lullubi har kanta cikin yalwataccen mayafi komai nata cikin kamala yake da nutsuwa haka nan halittarta take kamar wata babbar mace duk da shekarun nata qana na ne,ta bude sabuwar motarta fara qal wadda bata taba shigarta ba saiyau,ta zauna a sit din zaman driver ta kunnata ta wana ta sosai sanna ta sauke hannunta daga kan key din ta hada tafukanta ta soma addu'a๐Ÿ™๐Ÿป,sai da ta gama tana shirin tasar motar ta tuna da hand bag dinta data manto kan gadon ta da sauri ta bude motar ta koma ciki
A hanyar dawowa ne sukayi kacibus da shi kasancewar ta gefansa ne zata wuce din sai tayi tsammanim bai ganta ba don haka ta dauke kanta cikin sauri ta wuce don ta kusa makara ta ajjiye jakar a asit din baya tasa hannu zata kunna motar taji an janye hannun gami da zare key din ta daga kai tq bishi da kallo bai ko kalleta ba ya zagayo sit din mai zaman banza dake kusa da ita ya zauna sosai sannan ya maida qofar ya rufe,ta dan sunkui da kanta๐Ÿ˜” ya dan kalleta sannan ya basar don ya lura kamar al'adarta ce hakan,ya tabe baki cikin muryar nan tasa ta isassun maza mai cike da izza ya soma ce mata"ko banza a qarqashin mulki da ikona kike saboda haka u must obeying my statute and order if kina son aikinki,ya dan qara tsuke fuska ๐Ÿ˜ duk da yawancin lokuta haka fuskar take ya dage kafadunsa sannan yace" I don't know why aka wani tsiri yin aikin bayan ban gaza komai a gidana ba......
Ya dan sha qamshi sannan ya dora firstly ya zama dole kanki shiga ta kamala idan kin tashi fita,sannan ban lamunce da yawace yawace abu na gaba kada ki kuskura na ganki da number din wani qato a waya ko receiving calls ba and d last one kuma mafi girma wanda zai iya causing loosing din aikinki mu'amala da maza,kada ki dauki damar da na baki na fita aiki lasisi ne da na baki da zaki dinga ganin kina da right na yin duk abunda kika ga dama,take note๐Ÿ‘‰,yana qoqarin ficewa tace insha Allahu zan kiyaye"duk da ranta a abace yake da irun dokokim da yake kafa mata da ita a karan kanta ai tasan ya kamata,baice komai ba ya cilla mata key din yaja qofar ya fice ya tafi abunsa,ta miqa hannunta ta rufo qofar sannan tabi bayansa da kallo yanayin yadda yake taku kamar zabar masa inda zai taka ake,ranta babu dadi ta ja motar ta fice a gidan ,yanayin motar yana da dadin tuqi hakan ya taimaka mata wajan dawo mata da walwalarta,a hankali temper dinta take sauka sai ta dora da fadin la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalim cikim zuciyarta,da haka har ta qarasa gidan radiyon freedom don can ta tafi sha'awa amma duk da haka akwai wasu privet ayyuka da zata dinga yi da express radio din
Yanayin yadda ta samu karbuwa ya sake sa mata interest akan aikin sosai,su biyu ne kawai a office din ita da wata fauziyya kusan za tayi sa'a da fadilan amma ita nada yarinya daya iman,fauziyya shekararta uku da soma aiki da tashar,sosai fadila taji dadin samun fauziyya da tayi wayayya mai faran faran da son jama'a duk da ita miskila ce,wunin ranar tayi shine tare da managing director da wasu ma'aikatan tana arranging din ayyukanta ciki harda tsara sabin shirin da suka qirqiro wanda za'a fara gabatar da shi a asabuwar shekara wanda itace mai gabatar da shirin da taimakon fauziyya ta sake fuskantar yadda abubuwa suke duk da dama tasan da wasu lokacin attachment dinta
Kwana biyu tayi tana tsara komai ta mai da kanta busy sosai ta hana kanta sukuni hakan yasa bata da wani lokaci na tunani ,da ta koma gida tayi wanka tayi sallah sai ta samarwa kanta abunci simple ta ci sai kwanciya idan da wuri ta dawo kuma takan yi tilawar alqur'ani tunda dama ta jima da kammala haddarsa tun lokacin da tayi candy,idan ta gama taga tana da wani lokcin sai ta dauki wani aiki da zai taimaketa a office ta yi ko tayi amfani da laptop dinta tayi research na wasu abubuwan masu muhimmanci,a rana ta uku ne da taga komai ya kammala ta nemi hutu na kwana biyu ba wani matsala suka bata tunda dama bata soma gabatar da ayyukan ba cikin shirye shirye dai take,tayi hakanne don a lissafinta ya bata yau itace zata karbi girki ,kuma dama tuni ta shiryawa zuwan ranar
Da wuri ta koma gida ruwa kawai ta watsa ta zura doguwar riga har qasa mai hannun shimi ruwan hoda ta saka,ta taje dogon gashinta ta daureshi da ribbom shima ruwan hodar ne,farin hijabi ta saka wanda iyakacin qirjinta kawai ya rufe,ta wuce locker dinta ta lalubi inda ta adana muqullan da bata amfani da su ta debesu gaba daya ta zira farin silifas na fata ta fito,a falonta ta soma tsayawa ta bude fridge ta dauki lemon chi exotic nectar na pineapple da yayi sanyi sosai ta sha ta maida sauran ta rufe sashen nata,
TO FADILA SAI INA?๐Ÿค”

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
โ–ถ2โƒฃ5โƒฃ
Kai tsaye sashen Aliyyu ta nufa gabanta na dan faduwa kadan kadan har ta isa qofan,addu'a fal bakinta ta ke sanya muqullan daya bayan daya take gwadasu har ta dace da na qofar,ta tura babbar qofar ta shiga sanyin a.c ne da daddadan turaren aliyyu ne yayi mata maraba,ta dan lumshe ido kadan sannan ta waresu sosai kamar mai neman wani abu,a hankali take bin kowane sashi na falon da kallo tabbas yana buqatar gyara,bata shakka cewa har bedroom dinsa

Please Login or Register in order to submit comment