Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta lamushe su,sai ma suka tashi yan tsurut harabar wadace ta take da haske tamkar rana sai ka rantse da Allah rana ce ba dare ba
"Kai jama'a yanzu kamar ba za'a mutu ba?,wannan gidan dai.....inda ni kadai na shigo wlh ihu zan sak na ce gidan yankan kai nazo,kamar ba mutuwa a duniya?"kakarsu fadila hajja gana mahaifiyar abbansu ke wannan santin,su kam me za suyi idan ba dariya ba😂,sai da suka nufi sashen fadilan masu yaba kyau da tsaruwar gidan suka dadu,ginine wanda kaf garin kano baifi ka qirga masu irinsa da hannu ba,ginin part hudu ne sai boys quarters makeken lambu swimming pool gun wasanni kala kala,basketball table tennis,football boxing,tokwand da sauransu baya ga haraba biyu da gidan ke dauke da shi harabar farko dakin mai gadi da parking space take dauke da shi,sun dan tarad da jama'a a gidan acan part din samira suna jira a kawota,ba abinda ke tashi sai kida da yan uwanta suka ware mai barazanar fasa kunnuwa ganin haka hajja gana ta hana su koda guda suyi ta shiga gidanta da addu'o'i bakinta 
"🤔wai ni Allah wannan gida naki fadila idan baka da qarfin imani zai iya saka ka manta Allah "gaba dayasai da hajja gana ta sake sa kowa dariya a gun😂 duk da suma sun lalace ne gun kallon tsaruwar gurin nata falone two in one wanda kan ka shigo main falo akwai varender a farkon sashin sannan ka tadda falon,dukka falukan sun qawatu da kayan qyale qyale na falo babba da qaramim falon kowanne ansa masa abinda falo ke buqata ba abinda aka rage masa,acikin main falon anan daga hannun damanka matattakala ce masu fadi guda hudu zaka taka ka haye gun dining wanda ke daume da wasu hadaddun labulaye masu kacar kacar anan qofar kitchen s dinta take wanda duk wayewarka sai quyancinka ya fito,gaban gun dainin kadan wata yar qoface mai kyau ta glass wadda ke dauke da corridor shimfide da lallausan carfet da hadaddun labulaye dakunan bacci ne guda uku daya furniture ne yan Saudi pink da purple daya dakin kuma yan italia ne ash da pinch yayin da daya dakin kuma aka malaleshi da carfet da manyan tuntuna aka zagayeshi da labulaye masu shegen kyau aka rarrataye mata kayan kaba da kumbuna tamkar jeran qauye sai wani dan gado irin na qauye mai rumfa amma wannan an zamanantar da shi kowanne daki da toilet dinsa sai public toilet dake varender da kuma wani a falo,daga kitchen akwai qofa da zaka zagaua bayan part dinka(ventilation)wanda akayi dan qaramin lambu da wata rumfar bunu sai yar qaramar qorama da aka qirqira da doguwar kujera ta siminti qwaya daya,a falo aka ajiyeta,ido kam ya raja'a da kallom kyawun gidan,sanyi a c da qamshin freshener ya game ko ina ga qamshin sabunta,gidan ya kaure da hayaniyar yammata dake ta zuba santi da yiwa kansu fatan samun koda makamancin wannan gidan ne,

Wata hayaniya da suka ji ta kunno kai gidan ya saka su yin shiru suna sauraron daga ina take?,guda ce da aka cakudata da kirari iri iri hafe da habaice habaice"taka lpy uwar gida sarautar mata,isaahshiyar mace a gidan aliyu maitama ,eh anqi Allah yaso,qaryar mahassada ba zasu iya da ke ba wallahi sama ta yiwa yaro nisa saidai ya tada kai yayi kallo,an buga da ke an barki wlh yarinya ko yar sankin santanbul ce kinfi qarfin ta kara da ke saidai tayi iya nata salon ta haqura,"
hakane ya tabbatar musu masu rakiyar samira ne mama sadiya suka hana kowa fita har suka qaraci ahewarau da shegantakarsu suka shige da ita,zuwa wani lokaci kuma sautin sabon kida na kujerar tsakar gida ya karade gidan tamkar wani club,Allah ya kayuta abinda suka ce kenan 
Qarfe tara aka soma kwashe yammatan ana maida su kafin tara da rabi gidanta babu kowa,kadaici ya kama fadila,tsoro ya cikata,bata jin sautin komai sai hayaniya da kidan yan uwan samirah,zuciyarta tayi rauni sosai tunanin irin zaman da zatayi a gidan take,Aliyunta bai sonta,kishiyarta kuwa salon da ka rakota da ahi ya tabbatqr mata ba zaman lafiya tazo ayi da ita ba,hawaye ya balle mata😭 zuciyarta kaar tayi tsalle ta fito saboda zullumi da radadin da take mata
Horn din motoci ya sake cika gidan,ta daga kanta ta kalli agogon bangon dake falon sha daya na dare ya nuna mata🕚 ba shakka angone da abokansa suka shigo zuciyarta ke gaya mata haka,sannu taji hayaniyar jama'ar na raguwa hakan ya tabbatar mata ana debe su ne tafiya suke,ga tarin mamakinta sai ta jiyo muryar samira na cewa"ku gaida gida na gode Allah ya huta gajiya,ina jiranku gobe da safe,kuma wlh kada ku yarda sai sun vika muku kudin siyan bakin"fadila ta jinjina kai tana cewa cikin zuciyarta lallai ba shakka kowane tsuntsu kukan gidansu yake

Cikin qanqanin lokaci gidan ya sake zama tsit,ba komai cikinsa sai hasken fitilu daya gauraye da kukan tsintsaye da kuma gyare jefi jefi,haka ya sake assasa tsoron dake zuciyar fadila ta runtse idanunta gam😣tana ambaton sunayan Allah hadi da addu'o'in tsari,sannu a hankali taji idanunta da jikinta sun fara nauyi ,gajiyar kwana da kwanaki suka fara sauko mata,taji bata da buqatar komai illa kashingida,ta zame ta dogara gwiwar hannunta a hannun kujerar,tsananin gajiya yasa bacci har ya dauketa bata sani ba💤

ASUBA TA GARI AMARYAR ALY😊😊


Mrs muhammad bello ce 
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:29 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣1⃣

Firgigit ta farka kamar an tasheta,ya zame mata jiki tun a gida assalatun farko take tashi tayi yan nafilfilu kafin assalatu na biyu daga nan idan ta idar tayi baccin mintuna idan tana da lacture ta shiga kitchen ta shirya breakfast,yauma gajiyar bata hanata tashin ba saidai ta sabawa lkcn da ta saba tashi sai kiran a kiran sallah na biyu ta tashi,cikin kasala ta miqe don har yanzu tanajin nauyin jikinta tayi miqa hadi da salati idanunta suka kai kan wata farar leda babba mai dan duhu guda biyu tsoro ya darsu a zuciyarta ta katse miqar a iya saninta sanda zata kwanta babu ledar a gun to ya akai ta samu?cikin sanda ta isa inda ledar take kamar wadda akace za'a kama,saidai tunkan ta bude ledar qamshin turarensa ya ziyarci hancinta,hakanne ya bata amsar tambayarta lallai aliyu shi ya shigo da ledar tayi mamakin yadda har ya shigo ya fita bata sani ba,

Ta bude ledar gasashshiyar kaza ce wadda akai wrapping dinta guda uku sai ice cream da ya gama narkewa saboda an ciroshi daga ma'ajiyarsa sai fresh milk manyan roba har uku,sai yoghurt shima roba uku tayi ajiuar zuciya ta mayar da kayan,kasala ta sake kamata taja da baya ta koma bisa kujerar ta zauna tana aheqar daddadan turarensa tamkar yanzu yake a gun,ta shiga hasashen fuskan aliyun a cikin wadannan awoyin da yake angon mutum biyu,kishi ya taba zuciyarta,tafan bata waau lukuta a zaune ta kasa tabuka komai sannan ta miqe ta lalubi corridor din nan ta zabi bedroom daya ta shiga,tana alwala tana qarewa tsaruwar toilet din kallo,tabbas dole hajja gana tace kamar ba za'a mutu ba,bayan ta idar sa sallar ma tana lazumi dakin taci gaba da bi da kallo tana yaba irin namijin qoqari da iyayenta da yayansu Ahmad suka yi,bata kammala ba wani daddan bacci ya rinjayi idanunta nan bisa dardumar sallarta

Hasken rana da ya soma shigowa ta window yana taba fuskarta shi ya farkar da ita,da addu'ar tashi daga bacci ta miqe a bakinta ta dubi agogon dake ajjiye kan bedside ya nuna mata goma da minti sha biyar na safe batayi mamakin awanni data shafe ba tana baccin ba,toilet ta shiga ta kunna water heater dake manne a kusurwar bandakin cikin mintina qalilan ruwan ya tafasa ta kunna shower ta daidaita zafinsu ta shige kwamin wankan🛀🏼,tsaf ta shirya cikin atamfa mai zanan manyan ganye mai kalolin pink da ja sai light blue,dinkin da ita atamfar kanta tayi.masifar karabarta duk da ba wani make up tayi ba hoda ce kawai sai man lebe da kwalli,dinkin ya lafe mata sai kayi tsammanin fitted gown ce daurinta yayi das wanda ya awa gashinta damar kwanciya bisa dokin wuyanta

Ta fito falo ta kwashe siyayyar jiya ta kaisu kitchen,tsayawa tayi kallon kitchen din tana jinjina kai da dan guntun murmushi akan fuskarta😊ba shakka ummi tasan tsarinta game da kitchen kuma ta san maitar kitchen irin tata don haka ta cika mata ahi da dukkan wani nau'i na kayan amfanin kitchen babu ce kawai babu,abun nema ya samu nan ta bata lokaci gun tsara da shirya kitchen dinta yadda take muradi,tana tsaka da aikin ta jiyo ringing din wayarta wadda ita sam ma ta mance da ita ta fito galin tana laluben inda take,tsakiyar filalluka ta hangota tasa hannu ta dahota tana duba mai kiran garida ta gani tayi yar dariya sannan ya daga hadi da sallama,muryar farida a qasa ta amsa fadila tace lafiyanki qalau kuwa?"ta masa mata da "hmmmm,ai dole ki ce min lpy qalau tunda ke naji miryarki garau da ke "fadila da bata fuskanceta ba tace"kamar yaya? Wani abu ya faru ne a gida?"farida ta sake ajiyar zuciya tace"mubarak bashi da tausayi Allah sister fadila jiya kada kiso kiga rashin imanin da ya gwadan,anty hafiza tasan haka amma ta dinga dirka mana magani"fadila data dau haske a zancan nata tace"to Allah ya kyauta""wlh kin ga na kasa tashi sister"ta fada cikim karyewar murya,wani yarrr fadila taji tausayinta da tsoro suka kamata tace"ai ke likita ce saiki kula da kanki Allah ya bada lpy"tace"amin na gode ina ya Aliyu"
"Baya nan"
Cikin sauri farida tace "kada dai ace samira kika miqawa uwargidan bayan ke aka fara daurawa aure kuma ke aka fara kaiwa?"
Fadila cikin son abar zancan tace"ban sani ba 'yar jarida kije ki fara jinyar kanki tukun idan kin warke sai kiji amsa"ta katse wayar,jikinta yayi sanyi sosai a salube ta zauna agefan kujerar,ashe har faahin matsayinta ma sai da aka mata?ita idan banda yanzun ma bata san itace gaba da samiran ba tasa hannayanta biyu ta dafe kanta cikin wani irin yanayi da ta kasa tantance ame take?,ganin ba mafita yasa ta koma kitchen taci gana da gyare gyarenta zuciyarta cike fak da tunani,

Da azahar baqi suka soma zuwa mata sallama din komawa gidajensu yan maiduguri ne da yan gwambe,zuwa qarfe uku suka tafi sai su rumasa'u sa'adah minah rahama da hafsah duk cousins dinta ne rumaisa tace'?"wai ke ya ne?"fadila ta kalleta da alamun tambaya ,sa'adah ta karbi zancan "gidan farida muka fara zuwa tana can kwance mubarak nata hidima amma ke gaki dungur gur a zaune"fadila ta juya idanunta🙄tace"lallai yarannan"da yake ta basu tazarar yan kwanaki ta Dora"kuce kawai uawon sa'ido yau kuka fito ko"dukkansu suka sheqe da dariya😄,suka ce"to ai gwara kafin mu wuce muga lamira sun daidaita " tace"to Allah ya qara muku himmar sa'ido"ta fada tana shirin shigewa toilet rahama tace"to ai sai ki kira mana angon mana mu gani ko shi aka dorawa jinyar"ta jiyo ta harareta tace"baki isa ba kuma kwa qaraci zaman gulmarku ku tattara yammatan qafafunku ku koma inda kuka fito"suka sake aheqe mata da dariya😂,ita kuwa ta shige toilet din tana fadi a ranta"koni bancin arziqin samun ganinshi ba rabonku da ganinsa tun a dinner to nima hakan take"

La'asar gidan ba kowa duk sun yoye sun mata yan gyare gyaren da suka ga ya dace na game da jere da yan goge goge sukayi sallama cike da kewa tabi kowaccensu da dan dasheshan turare,turaren wuta ta zuba a bin turare mai amfani da wutar lantarki ta daidaita sanyin a.c falon yayi wani dadi qamshi da sanyi auka hafe guri guda,turare na musamman da hajja gana ta musu da kanta kuma ya tsumu sosai don ya jima a ajjiye ta musu tanadinsa,don haka qamshin har farfajiyar gidan,wajajen biyar ta sake gyara fuskarta ta feshe jikinta da turarurruka don dama babdaga baya ba fadila gun qamshi ta gabatar da la'asar da ta kufce mata,tana linke sallayarta tana ci gaba da jiyo hayaniyar dangin samira don tun farkawarta da safe wajan goma da rabi ta fara jin zuwansu,ta gama ta koma falo ta kama mbc bollywood dan ta samu ta debe mata kewa,kafin takai ga zama kan kujerar taji ana knocking din qofarta,ta nufi qofar tana cewa "waye?"saidai shiru ba'a amsa ba,don haka tasa hannu ta bude idanunta a waje don ganin waye,a subhanallah,ta fadi a zuciyarta saida bugun zuciyarta 💓ya dadu sosai fiye da qima,Aliyu ne tsaye a bakin qofar yana sanye cikin wani lallausan farin yadi qal(tissue),yadin nada shara shara don hakka hatta farar vest dinsa kana iya hangota,dinkin yarbawa aka masa(boda)iya gwiwa da dogon wando yana sanye da baqin takalmi idanunsa saye da farin gilashinsa na qa'ida kansa ba hula sai kwantacciyar sumarsa kamar mai sa mata relaxer saidai natural ce haka sumarsa take,qamshin turarensa ke dukan fuskarta,tsintar muryarsa tayi yana cewa"su bar maka a nan ka dinga daukowa kana ahigowa da su"hakan yasa ta tabbatar bashi kadai bane,tayi niyyar yin sauri ta koma ciki don ba hijabi a jikinta saidai ta kasa moysa qafafunta,sai jan jiki da tayi ta rakube a bayan qofa,nasiru n yake shigowa da kayan abinci duk wani dangin abunci da nasha na har ya kammala shigewa da su tsaf aliyi na tsaye tsakiyar falon hannayansa zube cikin aljihunsa yana facing qofar store yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,ta haka fadila ta morewa kallonsa ba tare da ya sani ba,ingarman namiji ne wanda siffar qarfi ta bayyana atare da shi bayansa kawai ka kalla zaka fassara hakan,nasiru ya fito yana kade hannayansa ya dan russauna yace"yallabai na gama"yana qoqarin zaro kudi a aljihunsa yace"yauwa ya miqa masa kudin yace"raguna zaka samo guda biyu ka biyaau su gyara komai su wanke acan ka duba motar zuwa kasuwa ka tafi a ita""to yallabai"ya fada yana shirin wucewa"nasir"aliyu ya kirashi a aladabce ya juyo yana amsawa"ka biya ta gidan gona su gyara kaji ka taho da su""an gama sir"cewar nasiru ya fice da sauri

Ya juyo yayo tattaki har zuwa bakin qofa,fadila ta saci kallonsa sai taga hankalinsa na waje,cikin sanyin jiki da sanyin mutya tace masa"ina wuni"yqdan kalli sashin da take ya kauda kai,cikin wata dakakkiyar murya yace"kada ki qara zama haka bayan kin san cewa ba ni kadai bane,in kunne yaji......"tace"to"har yasa qafarsa awaje yadan dawo da baya ba tare da ya dubeta ba yave"qarfe takwas ki sameni a gefena"to ta sake cewa,"shikenan babu abinda kike da buqata?"ya fada yana duba agogon hannunsa,"babu"tace
"Ok ki duba saman kujerarki"kawai yace yasa kai ya qarasa barin sashin aransa yana cewa"ta wani labe sai kace wadda ake kora"

Hannayansa harde bisa qirjinsa yake bin harabar gidan da kallo ,ko ta ina dangin samirah ne kamar wani sabon bikin suke sakewa,ba bainda auke illa aikin dafa abinci da kade kade,shiba wannan ne damuwarsa ba hayaniya ce baiso sam ko kadan,musamman wannan lokavi da tun daren jiya zuciyarsa ke a cunkushe,lamarin na taba ransa sosai yanayin da ya samu samira a daren jiya tun daren bacci ya qauracewa idanunsa,yaja siririn tsaki a ransa yace"wai duk haka matan suke ne?"bashi da mai bashi amsar tambayarsa don haka ya nufi sashensa

Damuwa ita ta haddasa masa gajiya da kasala ya zauna bisa kujera ya miqe duka qafafunsa kan kujerar ya hardesu yasa hannunsa na dama yana shafar sumar shi,tunani ya masa yawa ya rasa da wanne zai fara,yana a haka yaji knocking kafin ya nada izini har ta shigo,tafiya take tana wani karairaya kamar mai ahirin tsinkewa ta kafa masa ido tana murmushi,sam ko kusa bata burgeshi ba hasalima wani tsanarta da baqinta yake gani,ta haue kujerar da yake kai kamar zata koma cikinsa"sweet aly ina ka shiga tunda ka kawo kayan abinci ka fice"ya dauke kansa yana qoqarin janye jikinsa yace"na koma kasuwa ne"
Ta dan bata fuska ganin yadda yake nuna kamar yana qanqyaminta tace"haba sweet wai meke damunka tun daren jiya fa ma lura da sauyawarka,bayan wannan lokacimmu ne da ya kamat ace mun moreshi,pls kada ka bari wani dan qanqanin abu ya tarwatsa mana jin dadin wannan lokaci da muka dade muna tanadin zuwansakada ka lalata mana suitable moments dimmu"kallon da ya watsa mata shi ya firgitata ya kira sunanta da wata murya da ta qara razanata
"Kin dade da wargaza farincikin wannan lokaci tuntuni da hannunki"ta dan zaro ido cikin duniyanci😳 tace "kamar ya wai me ya faru?"ganin tana shirin raina masa wayi yasa ya.miqe gami da jan tsaki yace"ni zaki mawa silly question irin wannan?"ta kama gefan rigarsa tana shirin kecewa da kukan kirsa tave"din Allah ka gayamin me na maka?",ransa tafasa da suya kawai yake,ya dawo da baya yana huci ya ranqwafo kanta tamkar maiahirin fadowa kan nata har tana jiyo hucin numfashinsa,ya ware sexy eyes dinsa soaai a kanta wadanda bata san suna da girma ba haka miuyarsa a shaqe yace"u mean bakisan kinyi loosing virginity dinki ba,u did not know u r not a virgin!! A ina kika bada kanki samirah!!!"ya qaraahe cikin qaraji saboda wani kishi dake sukarsa,

Wani kuka ta rushe masa da ahi harda dora hannu a ka🙆🏻 kasancewar tasan halinsa baisan kuka ko da na yaro ne qarami yanzu zai dameshi,gunji take sosai hakan yasa temper dinsa ta fara raguwa,ya koma da baya ya zauna sosai,ta qasqantar da kanta tamkar wadda zata masa sujjada ta muzanta sosai,ta tsara masa qaryar fyade aka mata tun tana qanqanuwa"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"ya dinga mabata ahankali har yaji zuciyarsa ta fara sanyi duk da wani bangaren na zuciyarsa ya kasa gasgata labarinta,ya amince haka qaddararsa take,shi kam ya sani bai taba koda kusantar zina ba bare ya aikata ta amma Allah ya jarabceshi da samun mata har biyu da suka zo masa babu budurci,harda matarshi ta fari

"Ya isa,is ok "yace da ita,"hakan baza ta sake faruwa ba"yaci alwashin hakan,ta ruqunqumeshi tqna ta zuba godiya xikin zuciuarta tana godewa allah da asirinta baitonu ba don bazata iya jure rashin aliyu ba,baiga alamun tayi wanka ba don haka ya tambayeta,ai kuwa ta narke murya tave"na manta yadda ka koyan jiya da daddare"cike da madaukakin mamaki yake kallonta mace yar kimanin 25yrs amma ace bata iya wankan janaba ba ya koya mata ta kasa daukewa ?tun asubar jiya kuma tana zaune da janaba ajikinta bata damu ba to ina ga ban sallah kuma?ya jin jina kai yana hamgo girman aikin da ya sameshi,duk kuma yawan yanuwanta da sukazo a rasa wanda zai kwatanta mata harkar gabansu kawai suke,ya fuskanceta sosai ya sake koya mata ,nan toilet dinsa yasa ta shiga bai barta ta fita ba sai da yaga ta kammal ta kuma rama dukkan sallolin dake kanta

Tofa masu karatu muje zuwa

Mrs muhammad bello

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:30 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣2⃣

Har magariba fadila na bisa kujerar ta kasa tashi,kudin da ya jiye mata na gefanta tafa ce ta dubu dubu guda biyu,tasa hannu ta sake juya kudin a karo na barkatai "nafi buqatarka Aliyu fiye da kudinnan fiye da komai ma,me zaniyi da kudi"ta raya haka a ranta,kiran sallar magariba da aka qwalo a masallacin qarshen layin shi ya kawo qarshen zaman dirshan din da take,wanka ta soma dama ita gwanar sa ce don wani lokacin farida kan tsokaneta da agwagwa sarkin wanka ta hado da alwala bayan ta fito ta sa hijab ta gabatar da magrib sannan ta zauna tana azkar tana kuma jiran kiran isha'i
Minti arba'in tsakani ta jiyo kiran isha'in saboda haka ta tashi ta bada ita ta kammala da addu'oi ta shafa sannan ta isa madubinta dake cike da kayan kwalliya,kwalliya ta yi mai qayatarwa bata hauka ba mai cika fuska da yake ba baya bace gurin kyau sai kayi tsammanin bata lokaci tayi gurin yinta ta amsheta sosai ta kuma dave da yanayinta,ta bude duk sif dinta ta zuba mata ido tana tunanin wanne kaya zata saka?,hankali take shafa su har hannunta ya kai kan wani material
Pink ne mai adon dark blue da dark green din zare da golden sai wasu dutsuna da aka caba ado da su masu sheqi suma golden colour,dinkin doguwar riga ne da mayafinsa material din yake zuwa,yana da sulbi da taushi ba santsi ba yana shaking kadan a jiki don haka da tasa sai yabi jikinta ya lafe ya kuma haska kyakkyawar chaculet din fatarta fashion na dutse ta dan madaidaici ta maqala a kunnenta sai siririyar sarqarsa data lafe a dogon wuyanta sai zobe blue shima qwaya daya da ta saka a yatsan tsakiuar hannunta,ta shafe jikinta da tutaren asaal da ahlamul arab tame suka gauraya suka bada wani daddadan qamshi mai sanyi ta zura plate shoe pink ta dau mayafin kayan ta nade kanta da shi
Sannu ahankali tame ratsa gidan sai yanzu ta qarewa gidan kallo ita kam ya burgeta tsarin sosai,tamkar kana turai,ta sauke ajiuar zuciya sanda zuciyarta ta raya mata dama ita da Aliyunta ne kadai ke rayuwa cikin gidan rayuwa kuma irinta soyayya

cikin takun nutsuwa ta nufi qofar da zata sadata da bangaran nasa ido ta saki tana kallon ko ina,tako ina bangaran nasa yafi naau kyau da tsaruwa sosai,tun daga varender dinsa take jiyo sassanyan qamshinsa,ta shiga falon a nitse falone da ya tafi da gaba daya tunaninta tamkar gadar shugaban qasa,haduwarsa da tsaruwarsa tafi gaban kwatance

Idanunta suka sauka kanta tana hakimce kan kujera tana fuskantar t.v tana sanye ne da riga body huge da wando na jeans wadanda suka mata dam dam,ta baza kitson attachment din da aka jibga mata aka har gadon baya,fara ce sosai don har wani kore da yalo gefe da gefan fuskarta yake tabbacin kaso saba'in cikin dari na farin nata ya qara shi ne da man kanti,tana da jiki amma ba can ba da alama nan gaba kadan ta samu hutu zata narja qiba ne,tabbas ba don farin da ta aro daga kanti ba kana mata kallon farko zaka saka ta a sahun muna na amma sai farin ya boye kaso hamsim cikin dari na munin nata

Fadila ta sake jadda da sallamarta a karo na biyu sai Aliyu ne dake zaune bisa step kan dining ya amsa yayin da samira tayi saurin dago idanunta tana kallon mai shigowar idanunta suka fada kan fadila wani faduwar gaba taji amma ta maze don bata son fadilan ta fuskanci ta razana da ganin da ta mata,maimakon haka ma sai ta mata wani kallon raini na sama da qasa sannan ta janye idanunta ba tare da tace kanzil ba

Bata ma lura da kallon ba tana qarasowa cikin falon ta yiwa kanta matsugunni bisa tattausan carfet din da ya malale dakinta jingina jikinta da kujerar dake bayanta,wani abu ke tsunkular zuciyarta game da kishi duk da ta godewa Allah da ta tarar samirah bata fita da komai ba sai farar fata don ta tsammaci aliyu zai so matar da ta fi samira ne ba kamar samiran ba cikin ranta take cewa lallai so hana ganin laifi,to ganin samiran ko sashen da take bata kalla bayasa itama ta dauke mata kai sai ma ta zaro wayarta ta shiga latse latse

To shima Aliyun sai da ya kammala abinda yake ya shiga bedroom dinsa ya dan jima sannan ya fito ya samu kujera daya ya zauna ai kuwa tsam samira ta bar gurinta ta dawo jikinsa ta lafe kamar mai shirin komawa cikin sa ta gefan ido take satar kallonsu wani abu mai daci na damunta,amma a haka idan ka kalleta sai ka rantse da Allah batasan Allah yayi ruwansu ba don bata fasa danne danne a wayarta ba

Da bismillah ya fara yayi salati ga fiyayyen halitta yaja dogayan addu'oi wandabhar samira ta fara nuna masa tafa gaji,fadila ita mamakin yadfa Aliyu ke zuba addu'a take tamakar ba daga bakinsa suke ba(hmmm fadila kenan bakisan waye Aliyu bane😜)ya kammala sannan ha shafa,ina godiya ga Allah bisa ni'imomi da ya yimin a rayuwata tun daga haihuwata har kawo yau,ya kalli samira yace ga abokiyar zama nan Allah ya qaddara tare zan aureku sai kj zauna lpy bana buqatar hayaniya ko tashin hankali a gidana kowacce ta kama kanta ta tsaya inda Allah ya ajjiyeshi....
Ya dan sarara sannan yace idan da mai magana bismillah ya koma ya jingina da kujera yana jiran cewarsu,samira ta saci kallon fadila tana jiran taga zata tanka sai taga ma Sam idanunta bai kansu ta aza su ne bisa carfet,ta gayara zama cikin iyayi da kisisina tana kuma yatsuna 😏 tace"to nidai bana son shishshigi kuma bana son raini ehe.....kuma kowa ya kwana lpy shi yaso,sweet banji kayi rabon kwana ba?"ya daga kafada yace"its un 2 u ai"tayi wani

Please Login or Register in order to submit comment