Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da duk sanda ta kalla yake fusgarta,cikin ranta taje mamakin yadda fareren qwayar idanun sa kar suka rine zuwa ja

Cikin jikinta ta soma jin anya lafiyar aliyyun qalau?,ta kawar da wanna tunanin tana ji a jikinta har yanzu ita aliyyu yake kallo, "na zuba maka ne abincin?" Can qasa ta jiyo shi yace " I don't need",ya maida idanunsa ya lumshe,ta kuma kallon nasa tace "but...." "leave me "ya fada can qasan maqoshinsa cikin katseta,ta ga alamun bai da lafiya ne don haka bata yi zuciya ba tace masa "please ko coffee ne kasha mana" shiru yayi kusan minti uku baice komai ba,hakanne yasa ta gane ya yarda

Ta jawo flask din ta tsiyaya masa rabin cup din sannan ta sake matsowa kadan yadda zataji dadin miqa masa "take it pleas",da qyar ya iya miqewa ya jingina da makarin gadon,ta sake miqa masa yasa hannunsa zai amsa ya hade da hannun nata,kamar bashi ya riqe mata hannu ba bai saka ba bai kuma ce komai ba

Wani shocking take ji ga kuma dumin zazzabin jikinsa da yake ratsa ta itama,sai lokacin ta sake tabbatar da ashe bai da lafiyar,a hankali ya zame mata hannun sannan ya riqe cuo din sosai ya sale maida idonsa yaumshe kamar ba zai sha ba,illar da turaren ke masa nada yawa haka yake rayawa cikin zuciyarsa,ya sashi cikin wani yanayi nason kasacewa tare da ita fiye da tsammaninsa,

Bai damu da dan banzan zafin coffee din ba ya daga kai ya kwankwade tayi saurin amshe cup din ta hada kayan ta maida kitchen ta dawo dauke da cup da gorar ruwa ta dora kan bedside,sai ta tsinci kanta cikin damuwa da cutar yasa duk da bai buda baki yace mata komai game da lalurar tasa ba tasan yana jin jiki,tuni ya kwanta a daya side na gadon ya juya wa ragowat sararin dake bayansa baya

A hankali ta haye gadin gami da debe qafafunta ta maida su saman gadon ta rungume gwiwoyinta da hannayenta tana kallon bayansa,tana iya ganin yadda numfashinsa ke sauka a hankali,jikinta ya soma saki bacci ya kamata batasan sadda ta zame ta kwanta ba

_*2:30 pm*_

Can cikin tsakiyar baccinta taji ayi mata wani irin mugun riqo,nishi take ji cikin kunnuwanta sama sama dumin numfashin na dukan wuyanta,a firgice ta farka amma ta kasa tashi sabida namijin riqon da yayi mata gaba daya ya cukuikuyeta,da qyar ta samu ta juya tana fuskantarsa,murqususu sosai yake yana hada gumi numfashinsa ke fita da sauri da sauri,tuni ta gigice ganin yadda yana yinsa ya sauya gaba daya,ta tashi ta zauna dirshan hannunsa na riqe da cikinsa idanunsa adamqe daya hannun kuma ita ya zagaye da shi,sosai ta rikice babu abinda yake fadi sai *"ya Allah"*

Kimanin minti goma ta shude a haka ta rasa ya zatayi,tunaninta suna da first aid kit a gidan?to koda ma akwai din bazai qyaleta ta tashi ta dauko ba don gaba daya a kanainaye yake ajikinta,dabara ta zo mata da sauri ta miqa hannu ta dauko robar ruwanan da cuo din da dazu ta shigo da su,ta tsiyaya ruwan sannan ta sa bakinta ta tofa masa ayatush shifa ta hada masa da _*allahumma rabbin nas,azhibul ba'asi,wash fi antash shafi,la shifa'u illa shifa'uk,shifa'an la yugadiru saqama*_

Ta dan kalli fuskarsa da tayi ja har yanzu idon ke rufe yana hada gumi "pls can you take it?" Ya dan motsa kadan tasa masa cup din abaki yasha kuwa fiye da rabi

Cikin ikon Allah da taimakon ayoyin al qur'ani sai mutsu mutsun da yake ya soma raguwa,riqon tsaurin da yayi mata ya fara sassauta,sai ajiyar zuciya da yakej saki kadan kadan,bata samu sukuni ba sai da taji numfashinsa ya soma daidaita,a hankali jikinsa yayi weak bacci sosai ya daukeshi

Ta saki ajiyar zuciya tana kallin irin yanda ya zagayeta da hannunsa,ta tabbatar da a hayyacinsa yake bazai yi hakan ba,gumin fuskarsa har yanzu da saura,tasa lallausan tafin hannunta tana share masa kadan kadan gami da bin fuskarsa da kallo ganin yadda tayi ja alamun wahala,tayi tayi ta janyeshi daga jikinta cikin dabara saidai abun ya faskara yayi mata nauyi ahaka itama baccin yayi awon gaba da ita

*THIS IS THE BEGINNING OF*............

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻
[10/16, 1:59 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

4⃣5⃣&4⃣6⃣

Yau kam sun makara sosai suka makara don ko sallar daren babu wanda yayi a cikinsu sakamakon bacci da basu samu ba jiya,shi ya fara farkawa ganinta cikin jikinsa ya bashi mamaki,kamar ta san me yake faruwa ta farka itama fuskarsu cikin ta juna,kamar hadin baki da sauri kowa ya janye jikinsa suka miqe a tare,shi ya fara shigewa toilet ita kuma ta shiga na parlour

Ta rigashi idarwa tana zaune tana azkar har ya idar,tana zaune har ya kammala nasa addu'o'insa, tadan waiga kadan tana duben gefansa tace "ina kwana" kamar yadda ta saba ba tare da neman amsa ba tunda ta sani ba masawar zaiyi ba don bai taba amsawa din ba,saidai idan yaga dama ya daga mata hannu kawai,saidai yau ga tarin mamakinta karo na farko sai taji ya amsa da "lafiya",ta sake cewa "ya jiki?" Kai ya daga mata,ta tabe baki ta miqe cikin zuciyarta tana cewa"hmm an ma yi yau abun arziqi" tana kallonsa ya sake komawa gado ya duqunqune

Bai dade da kwanciya ba wayoyinsa dake gefan gadon suka hau ruri,hannu yasa ya debo su bai daga kiran ba hakanan ba tare da ya duba mai kiran ba ya kashesu duka sannan ya maida su kan side drower hadi da jan bargonsa ya sake rufa

🔅🔅🔅🔅🔅

Tana kitchen tana hada breakfast tajiyo muryarshi cikin parlour yana amsa waya,saidai muryan tayi qasa sosai alamun bai cikin jin dadinsa don bata iya jin abinda yake cewa,cikin rarraba hankalinta da takeyi ne ta yanke hannunta da wuqar🔪 da take rarraba kazar da take so tayi masa pepper chicken ba tare da ta sani ba,wuqar ta shigeta sosai don yankan ba qarami bane,zafin ya ratsa ta har cikin qwaqwalwarta batasan sanda ta saki razananniyar qara ba,jini ne sosai ke zuba ta runtse idonta tana jin azabar yankan

Ta bude idonta a hankali suka sauka kansa lokacin da yake shigowa kitchen din cikin sauri,hannun nata da yake digar jini yake bi da kallo,da sauri taga ya ajjiye wayar saman freezer,hannun nata dake digar jini ya riqe yana kalla,wani yarrr fadila ke ji har cikin jininta,shi din ma haka,lallausan tafin hannunta yaso haddasa masa wata sabuwar fitinar cikin jikinsa,yayi saurin sakin tafin hannun nata ya kama tsintsiyar hannun

Janta yayi zuwa gaban sink ya kunna famfo ya tara hannun sannan ya barta gaban famfon ya fice da sauri,cikin 'yan sakanni sai gashi dauke da first aid kit,abunda tayi ta tunanin ina yake jiya,spirit ya fito da shi ya janye hannunta daga famfon ya dangwala a auduga ya soma wanke mata kan yankar,zafi sosai take ji yana ci gaba da ratsata ta runtse ido 😣 tana dan yin baya da hannun,cak ya tsaya da wanke matan da yake don spirit din baya samun inda yake so,fuskarta da idanunta ke rufe ya zubama ido har wani abu yaso shagaltar da shi

Jin shiru ya daina sawa ya sanyata bude ido,idonta ya shiga cikin nasa suka hadu,wani magnet ya hadu da qamshin turarenta yaso rikita aliyyu ya manta da abinda yake,amma sai yaso nuna mazantaka ya dake har da qarfin halin kaurara muryarsa "stop it,idan baki buqata zan hada kayana,kau da kai tayi don bazata iya jurar kallon qwayar idanunsa ba,ya duqar da kai yaci gaba da wanke mata daga bisani ya rufe mata da bandage don kada datti ya dinga shiga

Yana maida kayan cikin akwati ta dan motsa labbanta tace "thanks" "for what" ya fadi ba tare da ya dago kai ba bai kuma tsaya da rufe akwatin ba,she became speechless don haka ta zabi yi masa shiru kawai,haka shima bai sake cewa komai ba har ya kammala rufe akwatin ya dauki wayarsa ya fice

Da hannu daya ta qarasa aikin don haka kafin ta kammala duk ta jagwalgwale hannun jinin da ya tsayar mata tuni wani ya soma tsatsatsafowa ta bandejin da ya sa mata,sai da ta gama serving dinsa sannan ya ankara da girkinta ashe ta ci gaba da yi,ya dago ya dubeta tana ta faman hurawa yatsan iskar bakinta,baice mata komai ba ya tashi ya sauka a dining din sai gashi dauke da first aid kit,ta zaro ido cikin tsorata😳 tana tunanin mai kuma zai mata yanzu

Sosai ya riqe hannunta gam tana qoqarin zamewa saboda azabar yadda yake daye bandage din da ya sa mata dazun zai canza mata sabo,sai da ya cire tas ya sake wanke mata ya saka mata sabo sannan ya maida kayansa ya kwashe mai jinin ya sauka da su

Ya dawo ya soma cin abincinsa yana kallonta time to time yadda take ta qwalla "ko da yaushe kina acting kamar baby" hakanan taji ya fada can qasan maqoshinsa,sai da ya kammala cin nasa taga ya ja plate ya zuba mata komai ya tura mata gabanta, "oya" yace hadi da yi mata nuni da plate din da ido fuskarsa a hade,ta dan langabar da kai gefe don bata marmarin cin komai yanzu sai ta tashi a lecture "am ok,na qoshi" kallon nan nasa ya tsareta da shi cikin tsare gida,ta fuskanci hukuntata yake sonyin da ido,tayi saurin janye idanun ta hadi da sake jan plate da cup din gabanta ta soma ci tana yamutsa fuska cikin zuciyarta tana mitar "ya wani tsare mutane sai sunci abinci sai kace wani abbana lokacin da ina gida"

"Good haka abban ke miki saboda baki jin magana kan cin abinci ko?"ya fadi yana fuska a hade yana daga girarsa,da sauri ta dago ta kalleshi batasan sanda tea din da ta kurba a bakinta ya dawo ba,batasan ya akayi yaji abinda take fada ba,anya wannan mutumin ba maye bane?, "am talking to you kin qwalalomin idanunkin nan masu girman tsiya"(lol aliyyu 😜😜😜😜😜) ya fada cikin dan daga murya,kai kawai take girgizawa don babu bakin cewa wani abu,minti biyu tsakani yace "shi yasa kullum store da freezer dinki ke acike kenan basuyin qasa ko?good.....to ni a gidana dole adinga cin abinci.....oya....bismillah ina son naga plate empty"

Daga haka ya maida kansa gun wayarsa dake ruri ya fara amsa wayar mr lien,ci take amma sam bata so,da zarar kuma ta tsaya suke hada ido dole take ci gaba da ci,sai gashi taci abinci mai yawa wanda ita kanta ta jima rabon data ci,ta ture plate din tana dan taba cikinta da taji yayi fam tana yatsina fuska yayi mata wani irin qabe qabe babu dadi, "I think u filled your stomach,let me see" ya fadi yana qarashe kashe wayar"qwalalo 😳 ido tayi tana tunanin anya kan aliyyu daya?ciwon cikinsa na jiya kodai ya taba shi?,she dont know why he behaving like dis?,cikin nata zaya ce ta ta yaye rigarta ta nuna masa?,ta dawo cikin hayyacinta lokacin da ya zare mata ido yace "aha show me" ba shiri cikin sanyin jiki ta dage rigar sanyin hadi da shirt din dake ciki,cikinta ya bayyana, ashafe yake tamkar zai hade da bayanta,ya zuba mishi ido,soft skin tata ta bayyana kanta ko ba'a fada maka,wani irin magnet ke fusgarsa,ya dubeta ta tsira mata ido duk a rude take,muryarsa can qasan maqoshinta yace "up" yana ci gaba da kallon cikin,a zaton ta bai gani bane sosai ta dan sake janye masa rigar "up again" ya sake fada,sai ta tsorata don dukka cikin nata ya fito waje da zarar ta sake janye rigar qirjinta(breast) ne zai bayyana

Ganin bata sake dagewarba yasa ya dauje idanunsa daga kallon cikin ya maida qwayar idanun nasa cikin nata,ya karanci ta tsargu don haka sai ya waske ya bata rai hadi da janyo warmer yana budewa gami da cewa "no ni banga yayi full ba,don banga ya daga ba" ta marairaice tuni qwalla har ta cika mata idanu "I swear idan ka qaramin zanyi amai wlh Allah haka cikina yake" da mamaki can qasan ransa ya tsaya da abinda yake din,dama akwai mata masu irin wadannan halittar cikin?,ya riga da ya saba da matansa masu tumbi

Ya koma ya jingina da kujerar da yake kai yana cewa "ok remove dis items,but be careful with your wound,dama neman mafita taje don haka da rawar jiki ta tashi ta soma gyara gun ,cikin kitchen kitchen tafi minti biyar tana dafe da qirjinta idanunta a lumshe kafin yanayinta ya daidaita "me ya sauya shi haka" can qasar zuciyarta take tambayar kanta

*Mrs muhammad ce*

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻
[10/16, 2:00 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

4⃣7⃣&4⃣8⃣

Ta dade kafin ta baro kitchen din har yanzu yana dining area bisa kujera yana danne dannensa a waya,a falon ta tsaya ta jawl computer din ta ta tafi da gidanka(laptop) ta bude tana shirin kunnawa "hey stop" taji ya fadi cikin wata iriyar murya mai kama da ta mai jin kasala,kasaqe tayi tana jira taji mai zaice "shutdown ur system yau ba daukan lecture,kin mance wound dake fingers dinki ne?" Sai ta rasa mai zata ce tana ganin ai hannunta bazai hanata lecture ba koda guda daya zata iya yi,amma da yake mutum ce ba mai son jayayya ba don haka ta kashe din ta koma ta zauna hadi da zubawa sarautar Allah ido

Tana zaune ya shiga ciki yayi wanka ya shiryo cikin kayan sanyi,kan kujerar dining din dai ya koma ya zauna,babu dadewa kuma door bell ta kada,ya dubeta sannan yace "put your hijab" mayafine yafe a jikinta bayan kayan sanyi masu kauri da tasa,nan ma dai bata tanka komai ba ta koma daki ta dauko hijabin,ko da ta dawo su biyu ta tarar shi da doctor yungpho,ta samj kuje daya ta zauna doctor yungpo mutumin china na gaidata cikin harshen turanci

Suna gefanta doctor ya gama duk hwaje gwaje da tambayoyinsa,ya dago yana duban aliyyu "sir,sanyin garin mu na son taba ka gashi kana kwanciya a inda zai iya affecting health dinka,ya kamata ka kula saboda kada yayi maka yawa ya zamarmaka illa" "ok" aliyyun yace, "sannan ciwon cikinka ciwon marasa aurene me yasa ya taso maka a yanzu bayan kana da aure?...." da sauri aliyyun ya katseshi yana satar kallonta duk da kanta baya fuskantar gun amma hankalinta na gurin haka nan kuma ta dago wani abu duk da ya katse doctor din

Magunguna doctor yungpo ya bashi yana shirin hade kayansa aliyyu yace ya bashi pain killers" ya hada masa duk cikin magungunan,fitarsa babu dadewa aliyyu yasa ta bashi ruwa yasha magungunansa,tamiqa masa ita kuma ta wuce kitchen da zummar dora abincin rana tunda taga alamun da qyar idan yau zaya fita

Sai tsintar aliyyun kawai tayi cikin kitchen din ya damqota yayo waje da ita,saman kujera ya zaunar da ita yana ware mata sexy eyes dinsa kamar wata qaramar yarinya "idan kika sake jangwale ciwonki I will wash it again budewa zanyi in sake wankewa no pity ok?" Tayi qasa da kanta tana kallon yatsan nata mai ciwon,muryarta so cool tace "lunch zan hada mana ne" "we don't need" ya fadi yana juyawa "wo hoho Aliyyu.......Aliyyu...." fadila ke fada cikin zuciyarta,ya sata hutun dole kenan?....... Babu karatu babu girki?.....fine" ta fadi tare da yin kwanciyarta saman three sitter

Wunin ranar tana zaune ita dai sai gani tayi an kada qararrawa da rana an kawo musu lunch hakanan da daddare,coffee kawai ta faki idonsa ta hada,shima tana dire masa ta bar bedroom din don kada yace zai mata fada,sai da ta kintaci kamar yayi bacci sannan ta koma,cikin sanda ta salallaba ta hau daya side din tana jan bargon zata rufa taji ance "good" ta zaro ido tana shirin sake jin mai fada,jin yayi shiru bai sake cewa komai ya sanyata jan bargo ta lulluba tana addu'o'inta cikin zuciyarta tana yiwa kanta dariya,wato ita mai wayo taqi shigowa ta gudu sai yayi barci ashe idanunsa biyu,ta saki ajiyar zuciya wadda ba don kwanciyar kai da qafa sukayi ba da zai iya jiyota

Yafi awa biyu yana yaqi da zuciyarsa,qamshin turarenta ke ban banta masa tunani,ya rasa wace iriyar masifa ce,sosai ya san yana cikin wani hali amma baisan me yasa ta sanadiyyarta yake samun kansa cikin wannan halin ba,sunsha zama haka shi da salima idan ta masa laifi don ya hukuntata,suna daukan tsawon lokaci a haka ba tare da kuma ya damu ba,saidai ita ta gaji ta hanyar gyara laifin da kuma bashi haquri,ya runtse ido,da qarfi yake son tilastawa kansa sai yayi bacci,da qyar wani wahalallen bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba da shi

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Kwana uku tayi babu cas babu as,duk abinda ta dauka zata yi sai yace "stop it,hatta da shara kuwa kawai akan dan yatsanta guda daya,saidai ta faki idonsa ta kimtsa inda taga bai dace ace ana barshi haka ba,da zarar kuwa yazo yaga alamun hakan zai zuba mata ido wanda ta fassara shi da *eyes punishment*,sai ta sunkui da kanta kawai ta wuce sum-sum-sum ta bar gun,kwana biyu yana gida yana jinya babu inda ya fita,sai a rana ta ukun ya koma kan ayyukansa

Sosai itama ta rungumi karatunta tana jin dadinshi matuqa ta bashi mahimmanci mai matuqar tasiri don ta sani zai sake jawo mata qwarewa da kuma daukaka ta fannin aikinta,hakanan tana sake samun goyon baya da qwarin gwiwa daga gidajen rediyoyin da take mu'amala da su,su kansu ko yaushe suna fadi mata yadda sukayi missing aikace aikacenta masu cike da inganci da juriya

🔱🔱🔱🔱🔱🔱🔱🔱
_*SANADI*_
🔱🔱🔱🔱🔱🔱🔱🔱

Cikin nasarori masu tarin yawa dukkan wani shirye shiryen bikin bude kamfanin suka kammala,cikin watansu na uku da sati na uku a qasar ta sin,wanda cikin lissafin da fadika keyi kwanaki goma daka iya zuwa a gaba koma sati guda wato next week zasu iya komowa gida,tun sati uku da suka gabata ta kammala naga coarse din ta kuma fita da sakamako mafi kyau duk cikin daliban

Tuni ya sayi injina masu kyau ya aiko da su gida ta container din max air wanda na wasu kamfanoni ne da yakeson budewa idan ya dawo gida a kano cikin rukunin kamfanoni dake sharada industrial area

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Tsaye take a kitchen sauri sauri take ta kammala girkinta saboda yau tayi late sosai,sanye taje cikin trouser na mata sai rigar sanyi in and top ta saqa ce irin saqar turawa,yar cikin har gwiwa take mai gajeran hannu ta saman ce iya qugu mai dogon hannu,wuyan rigar yankan *V* shape ne,ta taje baqi sidik din gashinta mai sheqi ta sake shi ya sauka gadon bayanta,kanta na saye da hular sanyi na mata mai wadda a jikinta yaje saqale da teddy's qananu,shigar dark pink tayi tayi masifar yin kyau kamar wata black American

Hankalinta sosai yayi gaba,ta bada duk wani attention nata kan girkinta don hatta dan siririn mayafinta da tadan yafa da hular kansu sun zame don haka ko shigowarsa bata ji ba,fresh milk shi din ma ya shigo dauka hade da ruwa don busy din da tayi yau ya sanya ta mance bata ajjiye masa ba yadda ta saba,wani strong abu yaja hankalinsa sosai game da ita,sai ya koma jikin freezer din ya jingina ya harde hannayensa saman qirjinsa kamar yadda ya harde qafafunsa yana bin duk wani moments nata da kallo

Sosai ta tsorata lokacin da ta juyo zata dauki ragowar markadaddun kayan miyan da ta sanya a fridge saboda ganin mutum a tsaye unexpected,tsananin tsoro ya kamata tayi baya zata qwalla qara don rudewa ma bata barta ta kalli fuskarsa ba sai kuma ta taka bawon doya ta zame tana shirin shan qasa saboda santsin tiles da doyar ga kuma ruwa

Gaba daya taji ya rungumeta tsam cikin jikinsa yayi hada bakinsa da nata don hanata yin ihun,zaro ido tayi,cikin yan sakanni ya soma kashe mata jiki saboda yadda yake sarrafa bakinsa cikin nata tamkar ya samu sweet qamshin turarenta na dada ingizashi,cikin lokaci qanqani ya soma burkice mata har ya fara bata tsoro duk da ita din ma tana cikin shauqin abinda yake matan,wannan shine karo na farko da ta soma hada jikinta da wani da namiji a rayuwarta

Caraf tayi qarfin halin riqe hannunsa jin yana qoqarin shiga wani fage,sai lokacin da ta hada hannuntabda nasan sannan ya soma dawowa saitinsa,cak ya tsaya da abinda yake yi din,cikin sauri ta 6ashi daga jikinsa tana maida botiran rigarta hadi da maida gashinta baya wanda tuni ya hautsine,kunyan da tsoro suka hanata tsaiwa ina zata boye?,bedroom nasu ne su biyu duka,kitchen gashi a ciki,gudu gudu sauri sauri ta nufi qofar ventilation da niyyar ficewa

"Hey you" taji aliyyu wanda ke jingine jikin kantar kitchen yana maida numfashi yace "cak ta tsaya ita bata qarasa ficewa ba hakanan bata juyo ba "duba girkinki it burns",sai a lokacin ta tuna doyarta data dora

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻
[10/16, 2:02 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺







*part 2*




4⃣9⃣&5⃣0⃣





Verry slowly ta juyo kanta a qasa ta kashe gas din ta sulale ta fice ya bita da ido,sirrintacciyar ajiyar zuciya ya saki jikinsa a mace ya juya ya dauki abinda ya kawoshi



Tamkar sirikinta haka ya koma mata gaba daya taqi koda kallonsa a haka ta zuba masa abinci ta miqa masa taja kujera ta zauna tana wasa da nata abincin sai jagwalgwalashi take da spoon baice da ita komai ba har kammala nasa,sai da ta miqe tana shirin hade kwanukan ta maida kitchen taji yace "baki isa ba sit and eat" ya tabo mata abinda taqi jini wato ace taci abinci,ta langabar da kai cike da fargabar ya za'a yi ta iya cin abinci yanzu?,ita hasalima tun abin nan da ya mata dazu taji cikinta ya cike amma taga ma shi ko ajikinsa tamkar bashi yayi ba,tamkar ba aliyyun nan ba kamar kullum canza shi akeyi



Da qyar tayi spoon biyar ta fara yunqurin amai "stop don't vomit,go" hakan dama takeson ji saboda haka da sauri ta kwashe kayan ta maida su,sai ta kasa zama afalon tayi komawarta daki tayi shirin kwanciyarta ta nade abinta a gado duk da a lokacin bata jin wani bacci,a hankali ta dinga tuna yanayin da suka kasance dazu da aliyun moments din yaqi bacewa daga kwanyarta,unforgettable ta fadi hakan a hankali can qasa,sai kuma wani murmushi ya subuce mata ta cusa kanta tsakiyar filo tana jin kunyar kanta da kanta,qaunar aliyun take ji na sake linkuwa cikin ranta,wannan shine karo na farko da suka taba body contact yana cikin saninsa,ta dinga tuna yanayin qamshi da laushin jikinsa,kamar yadda shi dinma yana zaune a falon ya kasa hasala komai ga ayyukansa nan a gabansa amma ya kasa koda sa password ya bude computer din bare akai ga batun yin aiki,tun barci ma fisgarta a hankali har mai nauyin ya saceta



A hankali ta soma ware idanunta saboda jinta da tayi tamkar tana rungume jikin mutum,qamshinsa ne ya bata amsar,a hankali zuciyarta ta tsananta bugu💓 sosai ta gwada yunqurin miqewa saidai ina ya zagayeta ne da hannayensa,ta tsammaci bacci yake ko magagin bacci ne ya sashi yin hakan saidai sanda ta sake yunqurin zare jikinta karo na biyu sai taji shi cikin soft voice can qasan maqoshinsa yace "relax,relax,am not going to do anything with you....just am feeling like am going to froze,I need to warmth my body ar you clear?" Bata ce komai ba ta maida kanta ta kwantar idanunta kan ribbon da hular sanyinta dake watse a gefe da alama shi ya zare mata su don kanshi ya tura cikin gashin yana saukar mata da dumin numfashinsa tsakiyar kanta



Ta lumshe idanunta sanda ya sake janta jikinsa sosai ya nutsa zara zaran yatsunsa tsakiyar gashin nata yana sake sheqar daddadan qamshin turaren gashi data ke fesawa kanta wanda ya cakude da na jikinta yana rarraba masa hankali,turarenda bai taba jinsa kan matansa ba,hucin numfashinsa da ta ji ya dawo sauka bisa dokin wuyanta shi ya sake rikita ta,cikin rawar murya tace "a....a....am" tsayawa yayi cak "is there any trouble?" "N....noo" bata san sanda bakinta ya fadi hakan ba,sake matseta yayi cikin faffadan qirjinsa a hankali dumin jikkunansu ya soma ratsasu,sanyin nan mai ratsa qashi ya ragu matuqa,a hankali takejin wani calmness da bata jin irinsa ba na shigarta,hakanan 2ani daddadan barci mai cike da nutsuwa ya saceta



Ya saki ajiyar xuciya jin saukar numafshinta alamun bacci ya dauketa,ya ciro daya hannunsa yana sake shafa gashin,sam ya kasa daurewa gashinta na burgeshi matuqa kasancewarsa mai son gashi,yaci gaba da shafa shi yana jin dadin santsinsa cikin tafin hannunsa har shima nasa daddadan baccin yayi gaba da shi cike da mafarkai kala kala

🔅🔅🔅🔅🔅

A hankali ta bude idanunta tadan juya bayanta ba kowa sai qarar saukar ruwa da taji cikin toilet,qarfe biyar na asuba,ta zubawa qofar toilet din ido lokacin da

Please Login or Register in order to submit comment