Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubi uncle abban "don Allah salim a naci albarkacin amintaka ina mai baka haquri kan ka sassauta fushinka kan yarona"falon ya dauki shiru na wasu lokuta kamin abban ya saki ajiyar zuciya "naji...naji,abu na farko da zan fara fada shine alhj abbas kai da hajiya amina ku yimin alqawarin babu wanda acikinku zai tursasawa fadila koda ta bayan fage ne kan sai ta koma gidanta ba tare da ita ta yanke hakan ba?" Ba yadda alh salim ya iya don yana tausayama aliyun yace "nayi" ummi ce tayi shiru har sai da hajiya maimuna tace "baki ce komai ba" "nima nayi"itama ta fadi cike da tausayin aliyu

"Abu na biyu,anan gidan fadila zata zauna har sai taji ta amince don radin kanta zata koma,idan yaso naga mara kunyar da zai koreta don ba gidansa bane haka nan ba da qwandalarsa na hada na gina gidana ba"ya fadi yana muzurai,sarai aliyun ya sani da shi abban yake amma sai ya sunkuyar da kansa,saboda shi kam a yanzu kome zasu fadi yaji ya gani kuma ya yarda suyita fadin,ko bulala dukkansu zasu dauka suyita zabgarsa yaji ya amince zai kuma shanye tunda dak an janye batun saki cikin lamarin,uncle abba ya nuna shi da yatsa "saura kuma naga qafarka inda take bare kace zakayi yunqurin takurawa ko tursasa mata sai na saba maka fiye da tsammaninka,tashi ka bawa mutane guri mutumin banza kawai",bashi da zabi illa barin falom kamar yadda abban ya umarcesu ya miqe ya fita bayan ya duqa yace "na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma,Allah kumabya huci zuciyoyinku"yana tafiya yana satar kallonta har yanzu kanta na duqe taqi ma ta dago ya kalli koda fuskarta ne

Sosai uncle abba bayanin dalilin yin wannan hukuncin bayan ya sallami fadilan da anty hauwan,yana sone koda aliyun yayi nadama ya sake sanin darajarta da amfaninta a gunsa kafin ta koma masa,cikin dariya abban ke cewa"haba alhaji ai ba sai kace komai ba,amma dai don Allah a sassautawa yarona haka"dariya duk sukayi,daki aka bawa fadilan kusa da nasu sumayya,amma tace tafiso ta zauna cikin su sumayya,a daren aka kawo mata madaidaicin gado da cupboard irin nasu rabi'ah aka sa mata duka adakin kasancewar dakin qato ne sosai,su suka taya ta shirya kayan suna ta rawar jiki zasu zauna tare,batasan lokacin da su ummunta suka tafi ba sai da anty hauwa ta hauro saman take sanar mata

Cikin daren babu dan qaramin haukan da baiyi ba,kuka ma kasa zuwa masa yayi sai zafi da radadi da zuciyarsa keyi,daurewa kawai yakeyi yana sakar musu jiki don kada ya shiga haqqinsu,wani lokaci idan kewar ta isheshi dakinta yake tafiya yayi bacci cikin bargonta ya kalli hotunanta sannan yake samun relief

(Qalubale a agareku iyayemmu mata har ma da mazan,da kuna ji kuna gani 'ya'ya yenku zasu dinga auri saki,babu kwaba balle hantara,wani lalacewar ma idan anyi sakin wai sai ya kwaso yaran ya kawowa uwar ita ce mai riqe masa kuma tana ziga shi har kina furta gwara da ya saketa,,to ahir din mu domin kuwa kada mu manta mun haifa ko bamu haifa ba an haifa mana,za'a yiwa taki 'yar ko 'yar 'yan uwanki kiji idan da dadi? Ai ko.matar ba ta gari bace akwai matakai da Allah s.w.a yace abi kafin akai ga rabuwar bawai rana tsaka daga an dan saba masa laifin da bai kai ya kawo ba ya karkace ya danqaro saki ba,to wallahi muji tsoron Allah,shi mai sakin dake mahaifiyar me goyon bayansa ina zato a cikin 'ya'yansa ko jikokinki ba za'a rasa mace ba,ya zakuji yayin da aka koro muku ita?,saki yayi yawa musamman acikin al'ummar mu ta hausawa,don Allah mu daure mu gyara ko ma samu gyaruwar al'ummar mu wadda wata tabar barewar tarbiyya daga an saki uwa ne shikenan sai gida ya tarwatse kowane yaro yayi nasa alqibla,babu mao saita siu kan hanya wato uwa ta gari,Allah kasa ku dace mufi qarfin zuciyarmu,ameen)

🔅🔅🔅🔅🔅

Sosai ta koma bakin aikinta don uncle abba yace babu mai hanata,babu yadda aliyyu ya iya haka ya zubawa sarautar Allah ido,ina ma yaga bakin magana koda yana da ta cewar?,don ko yazo gidan iyakacinsa parlour ko kallon upstairs inda dakunan baccinsu yake momi ta shiga balla masa harara kenan,haka zatayi kicin kicin da fuska har sai ya gaji da muzurai ya qara gaba

Ita kuwa uwar tafiyar tun daga lokacin da akayi hukuncin bao sake sanyata cikin idonsa ba,har addu'a yake Allah ya hadasu amma daidai da gilmawarta Allah baisa ya gani ba,tana sane ta sani,matuqar taji muryarsa to babu ita babu fitowa tana qule cikin daki ko kitchen idan a qasa take har sai ya bar cikin gidan

🔅🔅🔅🔅🔅

Da yammacine suna zaune cikin parlour ita da sumayya da rabi'ah,momi bata nan ta tafi dubiyar yayanta da baya jin dadi alh datti ita da iftihal suka wuce,gidan sai su ukun,lokaci lokaci rabi'ah naeqa kitchen ta duba abincin dare da ta daura sumayya kuma na tsefewa fadila calabar din da take kanta,saboda tsawo da santsin gashi da hannu suke tsifar,yayin da fadila ta jawo wasu fuskarta tana tayata,wani film da suke masifar ao suke kallo a m.b.c bollywood,na soyayya ne sosai,jarumin film din na musu kama da aliyyu sosai hatta da halayya,don haka wani lokacin ma ya aliyu suke kiransa duk sanda aka sako film din,suna son film din don haka idan ana kallonsa ko hira ba'ayi,saidai idan anzo wani gun daya burgesu,

A hankali aliyyun ya turo qofar falon with confidence don tun a gate ya tambaya aka sanar masaomin bata nan,basu ga shigowarsa ba sai sumayya kawai don rabi'ah na kitchen duba girkinta,fadila kuwa gashin da ya rufe mata fuska da yadda film din ya yafi da hankalinta sosai yasa sam bata lura ba

Sumayya ta bude baki zata yi masa sannu da zuwa ya dora yatsansa kan labbansa,gum kuwa tayi shiru,ya bata umarni na gaba da ido alamun ta tashi a hankali ta haye samansu,ba musu kuwa cikin sada ta haura saman,gurbin da sumayyan ta tashi nan ya maye,harda dan jawota ya jinginar jikin gwiwoyinsa,fadila uwar 'yan son jiki kuwa ya jingina abunta harda cewa"yauwa sumayya dama baya na ya gaji,calabar ko ashirin bata kai ba amma taqi tsefuwa ta dadin rai?"baice uffan ba ya kama jelar kitson ya soma tsefe mata kamar yadda yaga sumayyan nayi,ita kuma bata damu da rashin amsawar sumayyan ba ta bayar duk film din ne ya dauki hankalinta,rabi'ah ce ta fito da sauri daga kitchen din don kada tayi missing wani gurin,turus tayi ganin aliyyun a gun da sumayya tasan ta bari,itama yatsan ya dora mata kan lips nashi,yayi mata nuni da ido kan ta koma kitchen,nan ne ma fadilan taga giftawar komawan rabi'an kitchen din "rabi'ah za'a wuce gun da kike son kalla fa" "ina zuwa anty ban qarasa hada miyar bane"

Gaba daya ya shagala,wani irin farinciki ke ratsa shi,santsi kyau da qyallin gashin ya hanashi ganin wahalar tsifar,sai gashi sun kusa gamawa saura guda daya,yana ankare da yadda take bawa film din muhimmanci,murmushi kawai take zubawa hadi da sakw gyara zama,sai da aka zo wani gu da yayi masifar qayatar da ita ta saki murmushi tana cewa "hmmmm......soyayya" ta dan waigo tana cewa"don Allah sumayya basu burgeki ba yadda....."kasaqarasa maganar tayi ganin aliyyu zaune dare dare saman kujerar yaa mata tsifa,to sumayya ce ta rikide ta zama shi ko idanunta ke mata gizo?.......

*Mrs muhammad ce*👑

📘📘📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 2:12 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

1⃣1⃣&1⃣2⃣

Sai da yasa bakinsa ya hure mata idon sannan ta dawo hayyacinta,da hanzari ta miqe sannan kuma a guje tayi sama tamkar wadda taga dodo,binta shima yayi a hanzarce yana kiran ta tsaya,ganin da gaske take ba tsayawa zata yi din ba ya sanya shi cafkota a matattakalar qarshe,cak ya dagata yayi dakinsu rabi'an da take son shigewa,cikin sauri sumayya dake zaune saman dressing chair ta fito ta bar musu dakin

Tsakiyar gado ya direta sai haki suke dukkansu saboda gudun da suka kwasa a step din benan bugu da qari yadda zuciyar kowannensu ke bugawa,sun zubawa junansu ido cirko cirko da su kamar zakaru,a hankali yake hawowa gadon yayin da ta soma ja da baya har ya qureta,suka sake zubawa juna ido,shi nashi na tsantsar so da qaunace da suke sake huruwa cikin zuciyarsa take kuma aika saqonni zuwa sassan jikinsa,yayin da nata kuma na jin haushi tsoro da fargaba ne don bata manta wannan dare ba,kasa jurewa yayi sai da ya miqa hannunsa ya janyota ta fado jikinsa ya matseta gam a qirjinsa

Cikin fusata haushi da mamakin aliyyun ta soma tureshi,saidai ko motsi baiyi ba don qarfin ba daya bane,a hankali ya soma sinsinar wuyanta cikin kunnuwanta zuwa gashin kanta,ya dago fuskarta a hankali ya tura harshensa cikin bakinta,tsotsa yake sosai tamkar wanda ya samu sweet yayin da ita kuma take turje turje hadi da yunqurin tureshi daga jikinta saidai sam ma shi baisan tana yi ba,ganin duk iya qoqarinta ta kasa barin jikinsa sai ta fashe da kuka,hawayen da ya gangaro fuskarta ya taba nashi fuskar shi ya ankarar da shi,ya zare bakinsa daga nashi ba tare daya bari ta bar jikin nasa ba,kukanta take sosai yayin da ya zuba mata ido,gaba daya ya marairaice ya koma kalar tausayi " *fadeelahhhhh*"ya kira sunanta cikin wani irin yanayi tamkar mai rada,da sauri ta dago kanta ta kalleshi don wannan shine karo na farko da ta taba jin sunanta a abakinsa, "fadeelah" ya sake kiran nata ta sake itama kallon nasa "please fadeelah forgive me,I know I hurt you I break your heart,babu wanda ya wuce kuskure,fadeelah I love you more than words can say,I can't do without you,na kamu da soyayyarki,pls kada,pls kada kice zaki hukuntani da tarin laifuffuka na,if bazaki iya yafemin ba ma na amince kiyimin kowanne irin hukunci zan dauka,amma bazan iya jure rashin ki ba"

"Haka aliyyu ya shahara da yaudara?,haka aliyu yake?,taya mutumin da ya qika ya kuma sanar maka bazai taba sonka ba yanzun yace yana sonka?,bazai taba yiwuwa ba it can't"ta fadi hakan cikin zuciyarta tana girgiza kai,tayi wani kukan kura ta shammaceshi ta fusge daga jikinsa,jikinsa ya riga da ya mutu shi yasa ta samu nasarar qwacewar,tana yunqurin sauka shi kuma yana yunqurin sake cafkota aka turo qofar dakin,tuni fadila tayi amfani da wannan damar ta shige toilet "qaniyarka,qaniyarka nace" cewar momi dake watsowa aliyyu daquwa,sunkuyar da kansa yayi qasa yana Tsakiyar gadon da tuni ya bedsheet dinsa ya yamutse,ta qaraso cikin dakin tana riqe da murfin qofar dakin da daya hannun ta nunawa aliyyu waje "zo ka fice ka bawa mutane guri mara kunya,ka keta idanun qannenka ka biyota har kan gadonta" "kai momi kamar ba mata ta ba"ya fadi hakan cikin zuciyarsa yana ficewa daga dakin

Momi ta qarasa bakin qofar toilet din ta qwanqwasa tana cewa "fito" fadilan kanta a sunkuye kunya da takaici na sakadarta ta fito,momin ta dafa kafadarta tace "ko wani bak gaya min ba na sani kina son ali,muma kuma bamu taba fatan aurenku ya rabu ba har a qiyama,munyi hakanne don ya sake sanin darajarki da qimarka ta yadda ko nan gana bazai sake wasarere da lamuranki ba,ki samu yi duk mai yiwuwa ki tabbatar da soyayyarki cikin zuciyarsa kin fahimceni?" Cikin gamsuwa ta gyada kai tana yabawa momin ta yadda son kai bai rufe mata ido ba,bata duba cewa aliyyu danta bane bare ta bari tana gani a cutar da ita ba,qaunar momin da qimarta suka dadu cikin zuciyarta

*_1:30 am_*

Qarfe daya da rabi na talatainin dare fadila na kwance rub da ciki tsakiyar gadon ta,gaba daya ta rasa bacci cikin idanun nata,duk juyin da zatayi qamshin turaren aliyyu take ji daga bakinta har kayan jikinta,har kaya ta sauya amma a banza man kare don bata daina ji din ba,tana kallon yadda su sumayya ke baccinsu hankali kwance sai take jin dama ita dince su,basu da wata damuwa,wayarta dake gefan pillow dinta ta soma haske wanda ke nuna alamun kira ne ke shigowa,cikin mamakinta daga wayra tana duban kiran baquwar numbace,ta zubawa kiran ido har ya katse,ba'a fasa kiran nata ba har sai da ta tashi da missed call bakwai ana takwas dinne ta yanke shawarar dagawa ko wani abunne ya faru,ta danna ok ta kara a kunannta tayi shiru ba tare da tace komai ba

"Bakiyi bacci ba fadeelah?" Ya tambaya cikin wata iriyan sassanyar murya wadda har sai data sanya fadila runtse idanun ta,tana jin qaunarsa na yawo cikin jinin jikinta,shiru tayi masa har ya qara cewa "me ya hanaki yun bacci a irin wannan lokacin fadeelah?" Nan ma shirun ta sake yi masa,saidai ita kadai tasan yadda take ni'imtuwa da jin muryarsa mai tsada "nasan kika jina fadeelah,kuma bana tantama abunda ya hanani bacci shi ya hanaki....,sau da qauna ne ke dawainiya damu baki daya,tunaninki shi ya hanani sakat kamar yadda na san cewa tunani na shi ya hana miki yin bacci,da zaki ganni a yanayin da nake ciki zaki tausayamin,da zan iya ciro zuciyata kiga dumbin qaunar ki da ta cikata fadeelah da nayi,na tabbata da sai kin min addu'ar Allah ya rage min,jin shirun yayi yawa yasa yace "hello,are you there?" Ya duba phone dinshi tana nan bata yi hanging up ba,ya sake maida wayar kunnensa yana cewa "please fadeelah say something ko zan samu relief,am sorry fadeelah and I said it really" tsananin mamaki ne ya mamaye fadila,shin da gaske ne ba mafarki take ba aliyyun ne kuwa?aliyyu salim maitama? Aliyyunta?,mafarkinta na kullum,burin zuciyarta,shike gaya mata wadan nan tsadaddun kalamai?....kalaman da ta dauki tsawon shekaru tana dakon jinsu?irin qaunar da ta jima tana lalubenta daga gun aliyyun,shin da gaske ne a yanzu ta samesu?,eh...yes ta samesu but he didn't deserve ya samu amsarta a arha har irin haka,now its her turned,its her field to play her game.....

Muryarsa ta tsinto cikin sanyi yana cewa"fadeelah I know you gave me happiness and I gave you a reason to cray,u gave me your care and I stabbed you from behind,am sorry for having given you nothing in return for you having given me everything am sorry kiyi haquri....." kasa jure ci gaba da jin kalamansa tayi,tasani ko iya wannan ya isheta,ta samu qauna daga gun aliyyun,ta samu soyayyarshi,ya kawo mata kansa yana begging dinta ta bashi soyayyarta.....,tuni ta katse wayar wani dadi na nuqurqusarta,ta sani tabbas zai kuma gwada kiranta saboda haka ta kashe wayar gaba daya,cikin zaqi da gardin kalaman da aliyu ya kasheta da su bacci yayi awon gaba da ita tamkar dama au take jiran ji,bacci ne mai cike da mafarkan aliyyun a yanayi daban daban,shi kam tsai yayi da wayar a hannunsa cike da al'ajabin yaushi mace ke kashe wa waya?,tabbas ya sake yarda fadilan tana da wani matsayi da babu wata 'ya mace da ta kama koda gefanta

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tunda ta kashe wayar bata kunnata ba sai washegari sha daya na safe tana shirin tafiya office sha daya na safe,cikin shadda take pinch sai maiqo take dinkin doguwar riga aka mata,cif cif rigar tayi mata kamar a jikinta aka dinkota,ta bude sosai daga qasa rigar,tana cikin yafa orange mayafinta sumayya na koda kyawun da tayi"wallahi anty kyawunki na daban ne Allah kuwa ba don wai nayi ziga ba,ko bakiyi kwalliya ba kyanki fitowa yake,zanso yaya yaga wannan kwalliyar"

Harararta fadilan tayi"ke dai kin shiga tara,tuni rabi'ah ta dade a school ke kin zauna kanzagi kinqi fita,to bazai ga kwalliyar ba,sumayyan ta qyalqyale da dariya hadda kwanciya saman gadon"wallahi anty kiyi a hankali kada amiki qwace don har yau yayin ya aliyyu ake ba'a dena ba,kullum Allah ne da kullum wallahj dai ya fatattaki 'yammata,kada ki dauka qananu,a'a wlh anty hadaddu masu ji da kansu 'ya'yan manya kuma",fadila ta tabe baki kishi na cin ranta duk datasa haka dinne amma sai tace "dawar wani karkarar wani abincin wani kuma gubar wani"ta dauki wayarta dake gefan sumayyan zata fice sumayyan nata sheqa dariya,text ne taji ya shigo hakan ya sanyata dakatawa daga yunqurin fitar da takeyi,number din da aliyyu ya kirata ne jiya

Tun shidan safe saqon ya shigo "if u can't see the tears in my eyes,I beg you feel the pain in my heart....fadeelah na rantse I will do anything and everything just to take away all d hurt that you feel,please na roqeki give me and let me set thing straight,am sorry once again fadeela and I love you I really love you...."gaba daya ya zare mata dukkan kuzarinta,jikinta ya saki,maimakon fita sai ta koma bakin gado ta zauna,sumayya daketa leqen wayar tana qumshe dariya tace "anty lafiya dai ko?" Ta saki ajiyar zuciya gami da dauke idonta daga kan screen din wayar "lafiya lau me kika gani?"sumayya ta kada kai tana cewa "gani nayi kin shirya zaki fita kin dawo kin zauna,jiya kuma fa anty naga cikin dare baki yi bacci ba ko" hararar fadila ta sake aika mata tana kada kai cikin zuciyarta tana cewa "lallai na yarda ba qaramin illa soyayyar aliyyu ta yimin ba,a fili sai kuma tace "naji to sai kuma akayi yaya?" Ta fada tana ci gaba da jifanta da hararar wasa,miqewa summayan tayi tana ci gaba da qunshe dariyarta tace "k'n,uhmmmm,a'ah anty ni bance komai ba daga wannan,amma dai anty kiyi a hankali saboda yayammu gwarzo ne kuma gwani ne,he is hero,zai iya saaaaaace zuciyarki ba tare da kin sani ba"

Pillow dake kan gadon ta jawo ta jefi sumayyan da shi tana cewa "ban guri mara kunya" gocewa tayi ta fice da gudu tana dariya,sake mai da kanta fadila tayi kan saqon taa sake karantawa,ba shakka aliyyu shu'umi ne,so yake ta qarfi da yaji ya wargaza mata duk wasu makaman yaqinta,ya shirya tunkararta da duk wasu makamansa wanda tana tsammanin indai haka ne mawuyacine ta iya kubuta daga kaifinsu,duk ya kashe mata jiki kamar yadda ya saba ta qarfin tuwo ta gayyato dauriya sannan ta samu ta fita,ta tadda momi da sumayyan a falo,ta yiwa momin sallama,sumayya tace "a dawo lafiya anty.....momi dama inason baki labarin abinda na gani dazu,wata soyayya ake mai fada fada aciki"ya fada tana satar kallon fadila dake qoqarin ficewa daga falon fuskarta dauke da murmushi,a sace fadilan ta watsa mata harara mai nufin gargadi a fakaice ta qarasa ficewa,sumayyan nata qyatunta tace "na fasa anty kada ki hanani kudin ankon"..........

*Mrs muhammad ce*👑

📘📘📚📚✍🏻✍🏻✍🏻


[10/16, 2:13 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

1⃣3⃣&1⃣4⃣

Qarfe hudu dai dai ta kammala sallar la'asar dinta a masallacin mata da nan cikin gidan radiyon,ta goge kyakkyawar fuskarta da hoda,ta murza dan qaramin turarenta na (asaal brush perfume)wanda bata rabo da shi cikin jakarta saboda dadin qamshinsa gashi kuma qaramine baya da cika guri,ta saba jakarta bisa kafada sannan ta dauki wayarta ta nufi office dinsu don ci gaba da aikin takaddun programme dinta na gobe da ta baro ta taho yin salla

Ta tura qofar ta shiga kasancewar babu kowa ciki fauziyya ta tafi yiwo wani aiki a a ministry of education shi yasa bata damu da yin wani sallama ba,

Taja takardun gabanta bayan ta zauna ta dora daga inda ta tsaya,sosai yanayin tsarin programme din na gobe ke burgeta muhawarar da za'a tafka cikin shirin,lokaci lokaci takan saki murmushi gami da gyada kai,hakanan cikin jikinta ta dinga jin tamkar ana kallonta,cak ta tsaida rubutun,kan ta kai ga yin komai an zuro hannu an zare takaddun,tabi hannun da kallo har zuwa fuskar wanda ya gabatar da aikin,aliyyu ne tsaye qyam a agaban teburin nata,sanye yake da shadda ruwan madara(milk colour) dinkin yarbawa,rigar iyakacinta gwiwa hakanan hannun rigar shima gajere ne iya gwiwar hannu,sai manyan aljihu gefe da gefe,wandon dogo ne,kanshi babu hula sai kyakkyawar sumarshi dake cike da gayu da tsafta,idanunsa na saye da gilashin nan nasa fari qal wanda tana iya hango fararen qwayoyin idanunsa dake zube fes a kanta

Kallonta yake sosai ba tare da yace komai ba,da azama ta miqe hadi da ture kujerar da take kai baya,tasa hannu zata dauki jakarta gami da qoqarin ficewa daga tsakanin table din,taku uku yayi ya tsare mata hanyar ficewar,baya tayi da sauri saboda ganin yadda yayi gab da ita kamar mai shirin fadowa jikinta,ganin ta sake yin baya ya sanya shi sake shigowa cikin shima,da haka har ya danganeta da bango,sosai take jin fitan numfashinsa wanda ke cakude da qamshin turarensa

Ya dage sai ya sanya qwayar idanunsa cikin nata,saidai sam taqi yarda hakan ya faru,lumshe idanunsa yayi gami da nufar bakinta kai tsaye yana mai kwadayin tsotsar tattausan lips dinta,tuni ta gano manufarsa ta sunkuya ta qasan table din ta zille,bai san hakan ya faru ba sai da ya jishi ya dangane da bango,da sauri ya bude idanunshi,can ya hangota har ta dora hannunta kan handle,cikin zafin nama irin na cikakken da namiji ya haura ta saman table din don sai yafi masa sauri,taku hudu ya isa gareta,lokacin tuni har ta sanya qafarta waje

Jawota yayi har sai da ta fado jikinsa uasa hannayensa ya rungumeta,da qarfin tuwo take son qwatar kanta saidai hakan ya gagara,batasan wani yazo gilmawa ya gansun a hakan saboda qimar da take da ita agun dukka ma'aikatan gidan ba zata so hakan ya faru ba,ta kuma kasa bude baki balle tace ya saketa sai kawai hawaye ya balle mata,Allah ya taimaketa sai ua dauketa cak ya dawo da ita cikin office din hadi da murza masa maqulli ya kullesu

Kujera ya janyo ya dora ta akai yana maida numfashi,tsaye ya sake yi a kanta ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sake qare mata kallo kai kace ranar ya soma ganinta,ita kuwa tana zaune sai qananun hawaye take,ya sake taku biyu ya matso gabanta cikin wata iriyar cool voice yace da ita "fadeelah pls stop craying,I can't take it anymore,I know shirun wanda aka ma laifi yake nufi...I know,ki hukuntani kawai fadeelah kimin hukuncin da kike jij shi zai sa temper din da kike ji game da ni zai tafi,zan iya dauka,nasan duka girman laifi na ne ya jawomin,amma fadeelah kinja bakinki kinyi shiru,kinqi cewa komai kwata kwata why?,please(ya hade tafukan hannayensa)ko zagina ne kiyi fadeelah indai zakiyi magana indai kuma hakan shi kadai ne hanyar da zai saki ki huce,ko duka na ne ma kike so kiyi indai shine zai saki ki huce am ready fadeelah"

Ko daga kai ta kalleshi bata yi ba balle yasa ran zata ce wani abun,hakan take masa ko wani lokaci,ya tsani shirun nan nata,yana ci masa tuwo a qwarya,ya fuskanci babu ta yadda za'ayi su fuskanci juna babu ta yadda za'ayi ya samu abinda yake buqata matuqar ya barta taci gaba da yin shirun bayan kullum bai cikin nutsuwarshi duk ta sanadiyyarta....duk ta sanadiyyar qaunar da yake mata,bayan kk yaushe bashi da wani muradi sai nata,ta riga da ta gama kashe masa jiki da qwayoyin sonta da bai taba tsammanin akwai kalarsu a duniyarmu ba,banda time to time yana ganinta da yana tsammanin tuni ya dade da zaucewa,yana tare da ragowar matansa amma ita yake gani,zaici abinci amma sai ua bude hotonta cikin wayarsaa fakaice yana kalla ko da su salima na gun sanna zai samu ya iya ci

A yau dai yaci alwashin ba zaya qyaleta ba sai yaji ta bakinta,bazai barta ba sai anyita ta qare,ya jawo daya kujerar ya zauna a gabanta gwiwarsa na manne da tata,yayi mata kane kane ya hanata ta ko motsa duk lokacin da tayi yunquri sai ya maidata ya zaunar,idanunsa sun kada jajur "I promised ko da yau zamu kwana anan indai bakice komai ba na shiryawa hakan,ni ko ke babu inda wani zaya motsa,u stole my happiness any moment in my life am feeling am lonely,ina jin na rasa komai na rayuwata,why me yasa ba zaki yafemin ba?"

"Na sani I let you down,I made you frown,na sani I dont deserve forgiveness,but I want you to see the depth in my apology just listen to mu heart,it has been torn apart broken,but it still beats for you,ina sonki fadeelah ina sonki!!!.....

"Baka sona! stop saying it aliyyu,already ka riga ka gayamin *baka sona baza ka soni ba ko anan gaba kada nayi tsammanin zaka soni*,ka manta aliyu?..ka manta?,duk wanda yace baya sonka da safe ya dawo da yamma yace yana sonka he does not mean what he said,yana nufin wani abu ne na daban ba son ka ba

Sak yayi yana kallonta,bai taba tsammanin tana da baki har haka ba,but....at least yaji dadi...yaji dadi da yau ta bakinta ya gaya masa wani abu da ta qunshe cikin zuciyarta game da shi,don haka yana ganin dama ce ta samu gareshi,hannayenta ya kamo tana qoqarin zamewa,hakan

Please Login or Register in order to submit comment