Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai dameshi ba ya riqe hannayen qam qam, "duk abinda kike tuhumata da shi na amince na aikata din,annabimmu ya umarcemu muyi soyayya saisa saisa don zata iya juyewa qiyayya,hakanan ya umarcemu da kada mu zafafa qiyayya don wata rana zata iya zama soyayya,na mance da hakan,na tozarta kyautar da iyayena suka min shi yasa yanzu Allah ke mani hukunci,na manta da cewa *babu wanda yasan gobe sai Allah*,but now fadeelah I identified my mistake,I made so many mistaken,sai dai ki zama mai afuwa yafiya rangwami da sassauci" ta sake zame hannayen nata da sauri ya kama su "I love you.....I love you" "nooooo!" Ta fadi hawaye na zirya a kumatunta, "baka sona aliyyu....bani kake so ba jikina kake soo.....don me yasa da can baka kusance ni ba sai da nayi amfani da wani abun?,don me yasa baka soni ba sai da ka kusanceni?,ina buqatar amsoshin wadan nan tambayoyin aliyu!"ta qarasa fada a dan tsawace wadda kanta bata san ta iya ta ba balle aliyyu da ya zuba mata ido hadi da sakin hannayen ta ba tare da ya sani ba

Kafin yace komai akayi knocking qofar ana fadin "yau kuma me muka samu a office din namu anty fadila ta rufe mana qofa?"cewar fauziyya da yarinyarta dake tayata knocking qofar,kasa motsi fadilan tayi koda na yunqurin goge hawayen ta ne,cikin rashin kuzari ya isa ga qofar ya bude,fauziyya ta kalli fadila da aliyyun tana son tuna inda tasan fuskar,sai ta saki murmushi tana komawa baya "oh...sorry na katse ku ko?,ku gafarceni"ta juya zata wuce tana murmushi"anty fadeelah iman tace a rage kukan nan,duk da ta sani na soyayya ne"aliyu baisan sanda yace "baiwar Allah....don Allah sai ya zama laifi don mutum na tsananin aon matarsa?,don kawai.........

Zumbur tayi tace"ni din ma bance laifi bane"fadilan ta katse shi da sauri,dariya fauziyya ta sake yi ta gyada kai bayan ta gama qare musu kallo"wow,salonsoyayyarku abun sha'awa ne,ya burgeni hakan,well.....koma dai mene ne naga zallar son junanku cikin qwayar idanunku,Allah ya bar soyayya"tayi gaba ta kama hannun iman da tuni tayi gabanta tana ta tsalle tsallenta,ta nufi ofishin da zata kai aikin da taje yi

A sanyaye ya koma gabanta ya tsaya ya zubawa qasan office din ido wanda ke shimfide da terrazzo,a hankali ya saki hannayen nasa,ya tsugunna a gabanta tamkar mai kama ruwa ta yadda zai iya gano fuskarta sosai don kuwa kanta na duqe tana sharar qwalla,"fadeelah" shiru tayi ya sake cewa "fadeelah kin daina sona?" Nan ma shiru "fadeelah kin daina qaunata ko?!" Ya fada cikin dan fusata,a zafafe itama ta mayar masa "amsa kake so kaji?"daga girarsa yayi idanunsa na kanta"yes!" "Na daina sonka bana sonka,kai ada din ma ba sonka nake ba,ban fahimta bane sai yanzu!" Ta fada kanta tsaye ba tare da kawaici ba,lumshe idanunsa yayi yana jin radadin saukar kalaman cikin kunnuwansa kamar ana soka masa mashi,kusan wannan itace kalma mafi muni da yaji wadda ya jima baiji irinta ba,mace ta farko da zuciyarsa ta soma so don radin kanta ta kuma yi mata wani irin kyakkyawar masauki can cikinta tunda Allah ya ginata,irin masaukim da bai taba budewa wata mace koda bakin qofarsa...yau ita ke furata bata sonsa,kalmar da tunda yaje babu wata 'ya mace da ta taba furta masa ita sai ita din,wani daci na kalmar qiyayya da aka gaya masa ke ratsa zuciyarsa

Sai yaga bashi da wani mataki da zai dauka saboda haka itama ta dandani makamancin wannan dacin koma wanda ya fishi,saidai yana son tabbatatwa da kansa da gaskene bata sonsa?,ya bude idanunsa ya zubesu fes a kanta har yanzu kanta na qasa tana share qwalla,"fadeelah!" Ya kirata cikin wata iriyar murya,bata amsa ba hakanan bata kalleshi ba,ta sani babu abunda bai so irin shirun nata "fadeeelahhhh!"ya fada cikim qaraji,bata sanda ta dago kai suka hada ido ba,da sauri tayk qoqarin maida kan nata amma sai ya fita hanzari,da sauri ya riqe habarta ya dago kan nata........

*note*:don Allah masu caccanza numbers na novel dina na roqeku ku daina🙏🏻,sai nayi typing sai acanza tsarin number a dinga rikitarmin da makaranta na to gaskiya bana so,idan kuma aka ci gaba to ba shakka zanyi Allah ya isa,sannan na samu wata kuma tana samin number din wayarta cikin typing dina,to itama na roqeta ta bari,idan bata ji ba zan kai qararta gurin Allah,don kuwa yana gaggawar amsa addu'ar wanda aka zalunta,ku barmin novel dina yadda na tsara,kuma kuyi naku ba wanda ya hanaku,Allah yasa mu dace🙏🏻

*Mrs muhammad ce*👑

📘📘📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 2:13 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

1⃣5⃣&1⃣6⃣

Da sauri ya riqe habarta ya dago kanta,"ki kalli qwayar idona ki gaya min baki sona,I promised zan bace daga rayuwarki kamar yadda kikamin alqawari kema!" Ta sani qwarai aliyyun kaifi daya ne,yana aikata duk abinda ya furta komai tsananinsa,tashin hankali da tsantsar rigima da take hangowa yanzun a qwayar idanun aliyyun ba kadan bane,ko bama haka din ba tana jin ko kanta za'a sanya gabas a dora mata wuqa ba zata iya kallon qwayar idanunsa tace bata sonshi ba,ita kanta ma tasan ta yima kanta qarya koda ta fadi hakan,wannan ma wasa ne

Ko motsi kasawa tayi don tasan abinda yake buqata din ba qaramin girma ke da shi ba a gunta, "uhummm.....am waiting,tell me fadeelah.....tell me baki sona kamar yadda kika fada dazun"shirun dai ta kuma yi din bata da abun cewa,yasa yatsunsa ya sake dago fuskarta ta sosai still dai taqi yarda su hada idanun"fadeelah ni na sani kina sona,kina qaunata,amma me yasa ba zaki yafe min ba?me yasa ba zaki manta komai ba?,if u are nt willing to forgive someone,then you don't truly love them,fadeelah silence the mind and hear the heart,ina sonki fadeelah ina sonki har bansan adadi ba"cikin murya dake nuna alamun karaya ta dago kan nata ba tare da ta dubeshi ba ta dawo da tambayarta ta dazu "na gaya ma baka sona aliyu jikina kake so!" Cikin rudu ya sake kamo hannayen nata da ta sabule ya riqe gam "wa ya gaya miki hakane fadeelah?,who told you?" "Ni na gani da idona,baka soni ba aliyyu sai da kwanta da ni?" Bai son wanna kalmar da taje furtawa

bai san sanda ya zauna dirshan ba qasan office din,"wallahi Allah fadeelah idan ba tare muka fara son juja ba to da kadan kika rigani,wani kurman so nake miki fadeelah ki yarda da ni ba tare da ni kaina na sani ba,zuciyata na sonki ba tare da nasan hakan ba,na sani......kuma na zaci haka dama zaki zaci cewa jikinki nake so,saboda ban tashi sanar dake ina sonki ba sai a wannan gabar,bani da kalmar da zan kare kaina da ita,amm abu daya ne zai tabbatar miki da gaskiya ta,abun kuwa shine....ki amince ki dawo gidana fadeelah wannan shi zaisa ki tantance wanne irin so nake miki,zaki gane za kuma ki fahimci ba wani abu daya nake kwadayi tare da ke ba....a'a....kedin gaba dayanki nake qauna nake so fadeelah,na miki alqawarin baza sake taba koda yatsanki ba har sai kin nutsu kin amince da soyayyar da nake miki

"Fadeelah na sani ni da bakina nace miki bana sonki amma wallahi Allah shine shaida ba haqiqanin abinda ke zuciyata ba kenan,ban taba jin qinki a zuciyata ba dai dai da qwayar zarra,wallahi fadeelah da bana sonki bazan aurenki har na iya zama da ke ba,bana iya zama da abunda zuciyata ke qinsa,mata nawa ke sona?mata nawa aka kawo min a take na qisu?,amma fadeelah na amince na aureki na zauna qarqashin inuwa guda dake.....nake ci daga abincin da hannayenki suka sarrafa shi....nake buri da muradin sha daga abunda hannunki ya hada,nake kuma kwanciya bigire daya dake qarqashin rufin kwanon daki guda"

"Fadeelah.....kalli qwayar idanuna na tabbata sun isa amsa a gareki,ban iya qarya ba fadeelah,amma karo na farko da na fara yinta a rayuwata,na bugi qirji nace bana sonki bayan nasan ba haka bane,nace bazan soki ba koda wata rana ne bayan *bansan gobe ba,ba wanda yasan gobe sai Allah*,gashi yau wata ranar tazo ta riskeni ta qaryatani......kuma nima na qaryata kaina da kaina"yayi shiru idanunsa na kanta yana maida numfashi

Gaba daya ya gama da ita,ya lalata mata dukkanin tunaninta,ya tarwatsa duk wani mummunan tunani zato da tsammani da a da take da shi a kansa,maimakon haka ma sai wata sabuwar qauna da soyayya tasa dake ratsata har jinin jikinta,ahankali take fasa qashi tana malala har zuwa bargonta,jinta take kamar ba'a duniyarmu take ba,abinda ta jima ta jima tana bege da yaqin samu gashi yau a gabanta,yau ga aliyyu zaune dirshan a gabanta,yauga aliyyu zaune ya zamo kalar tausayin a qasan qafafunta,bayan babu abinda ya rasa a rayuwarsa soyayyarta kawai yake nema,aliyyun nan dake bata tsoro,aliyun nan dake da girman kai aji da kuma kwarjini yaushi yake roqon soyayyarta?,to itakam idan bata sallama ba tayi haqurin ai ta yiwa Allah butulci,me take nema dama idan ba wannan din ba?,tasan wasu daga halayensa sarai kamar yadda kowa ya shaideshi bai iya qarya ba....shi din kaifi daya ne da ko gaskiyarsa ba zata faranta maka ba hakan bai dameshi ba

Cikin cool voice da wani irin kunya da nauyi kanta a qas tace "na yafe maka,komai ya wuce "lumshe idanunsa yayi wani sanyi na kwara cikin ransa,ji yake kamar an masa gafara da bushara da aljanna,me yafi so dadi?,me yafi qauna faranta rai?,amma duk da haka yana neman qarin bayani,ya bude idanunsa ya sake matsowa jikin gwiwoyinta,"fadeelah kalmomin da zan miki godiya da su na tabbata sunyi kadan,bani da su saidai na kwatanta yin hakan don bani da abunda zan iya saka miki da shi,na gode na gode Allah ya miki sakamako da aljanna,but I need more fadeelah I need more,please tell me kina sona kina qaunata kuma zaki koma gida na"kafin tace komai aka sake knocking,da sauri ta daga kai ta kalleshi "please ka tashi daga qasa ka koma kan kujera,za'a iya shigowa a ganka a haka fa" ya noqe kafada ko matsawa baiyi ba yana ci gaba da kallonta "no,I don't care ko waye ma zai ganni a haka,a gaban fadeelah ta nake kuma ta cancanci komai har ma fiye da hakan,idan tana sone ma na kwanta ta dinga taka gadon baya na tana tafiya am ready if I can make her happy"dariya ce ta subuce mata tasa tafin hannunta tana qunshe bakin,ya kalli qwayar idanunta da suka sake yin kyau da 'yar ragowar qwalla aciki wadda tasa shi ya koma kamar oily eyes ya dage girarsa "oh,kina tantama ne?,let me show you"tuni ya soma qoqarin ruf da ciki a qasan,batasan lokacin da ta kama hannunshu ba tana qoqarin hanashi ba"no haidar,I trusted you"yabi hannayen nasu da kallo yadda ta riqe masa hannu da tattausan hannunta,ganin yana kallon yadda ta riqe shin sai kunya ta kamata tayj saurin janye hannun hadi da yin qasa da kanta tana murmushi,shima murmushin yake sannan ya nufi bakin qofar ya bude,fauziyya ce har ya dawo tace cikin fara'a "ina fatan kun kammala ban sake katse ku ba karo na biyu duk da takaddu kawai na shigo diba zan wuce gida"yasa hannu ya dauki baby iman dake ta miqa masa hannu taba masa dariya tamkar dama can ta sanshi ya soma mata wasa,baice mata komai ba sai hanya da ya bata yace"bismillah"

Yana ji tana tsokanar fadila haddi da yi mata sallama "yau dai ban sani ba ko anan office din zaku kwana ke da ogan" cikin murmushi ta mayar mata "a haba fauziyya,gida za muyi yanzu muma"ya sauke mata iman hadi da zurawa yarinyar five thousand cikin awarwarayenta dake hannunta,yaro ba wayo sai kallon kudin take gami da qoqarin zarosu tana ganinsu kamar abun wasa ne,yana ta murmushi son yara na dada kamashi,fauziyya ta masa godiya,shi ba ma'abocin son ayi masa godiya bane don yayi kyauta don haka baice komai ba ya dauke kansa ya maida kan fadeelah dake qoqarin miqewa don hada kan komatsanta da niyyar tafiya gida,wani jiri ya debeta duhu ya gilma idanunta tayi baya luuuu zata fadi,cikin zafin nama ya qaraso gareta ya mata kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa yace "subhanallah",fauziyya dake yunqurin jan qofar ta dakata gami da juyowa "sannu fadila jirin ne dai?" Da mamaki a fuskarsa ya kalli fauziyyan "dama jiri take yi?"
"Wallahi tunda ta dawo aiki take fama da shi,kullum haka take yi,matuqar tayi dogon zama ko zirga zirga,nayi zaton ma ta gaya maka,don nayi nayi da ita taje taga likita sam taqi,don ko jiya sai da na dan riqeta na wasu mintina sannan ta zama normal"
"Thank you" yace ya maida idanunsa kan fadilan wadda ta sake cusa kanta cikin qirjinsa tana shaqar daddadan qamshin da jikinsa keyi,dadi qamshin ke mata sosau kamar su dawwama ahaka haka take ji,maidata yayi ya zaunar saman kujerar ya hada mata dukkan takardun da take buqata din cikin hand bag dinta ya dauka sannan ya zo ya miqar da ita ya rungumeta ta kafadarsa yadda zasu iya tafiya a hakan

*ku yimin afuwa makarata rashin chargy*👏🏻👏🏻

*Mrs muhammad ce*👑

📘📘📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 2:14 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3*👈🏼

1⃣7⃣&1⃣8⃣

Ganin ya nufi qofa alamun ficewa za suyi ya sanya fadila zaro ido "a haka zamu fita?"
Ya dubeta "yes ko yayi miki kadan na daukeki ne?"
Ta kuma zaro ido cikin marairaicewa tace "no,please ka cika ni ka ban jakar,ai na daina jin jirin zan iya tafiya da qafata"
Girgiza kai shima yayi"no,bazan iya barinki ba,bazan bari kisha wahala ba indai ina tare da ke,ko ki bari mu tafi a haka ko na daukeki gana daya na kaiki har cikin motar"
Ta san halin aliyun kadan ne daga aikinsa,zai iya aikatawa ba tare da yaji ko dar ba,tilas tayi shiru suka fita tana sunne kai

Motarsa taga ya nufa da ita,ta dago da kanta tana ce masa "amma da ka bari tunda a motata na zo sai na koma aciki ko?kada momi ko uncle abba su gammu tare"
Ya tabe baki sannan ya saki dan qaramin murmushi dake qayata fuskarsa "kada su gammu tare?,so what?,ai ni dama haka nake so,kinga daga nan sai su tarkata min mata ta mu koma inda muka fi wayo"murmushi ta saki ta maida kanta don dariya aliyun ya bata,ya bude mata gidan gaba kusa da shi sai da ta shiga ya dan kwantar mata da kujerar ya sumbaci goshinta duk tana kallonshi "ki zauna a haka don bani so a ganemin ke a hanya"murmushi kawai tayi cikin jin kunya,cikin zuciyarta tana cewa"idan banda abun sa wa zaya ganni mota duk baqin glass"ya zagaya nasa bangaren ya bude yana shirin shiga

Wasu 'yammata su uku suka fito daga reception,daya daga cikinsu ta finciko hannun dayar tana nuna mata aliyyu,damar da ta jima tana neman kena taga aliyun don haka ta jawo hannunta ta rakota har bakin qofar motar,yana shirin sanya qafarsa yaji ance "ranka ya dade ya kai kyakkyawa" kusan ha saba jin irin wadannan babatun abakin 'yammata saboda haka bai juyo ba sai da ya shiga motar ya rufe qofar sannan yayi qasa da glass din,fuskarsa a yamutse kamar ya ga kashi yake kallonta,yayin da ita kuma ta harde hannaye ta zuba masa ido tamkar mayya tana zabga murmushin neman shiga "kina da matsala da ni ne?",cikin murmushin tace "yes,babba ma kuwa"aliyu ya fasa kunna motar da yake qoqarin yi da dayan hannun nasa ya dogara hannun jikin murfin motar yana shafa sumarshi hadi da tsareta da ido,ya sani sarai qarya take don yaci karo da mata irinta sunfi dari

Sai yayi mata kwarjini domin shi din ba kalar wasa bane,ba tare da ya sake tambayar tata ba ita da kata cikin diriricewa tace "zuciyata ka sace min ne,kuma na jima ina jiran rana irim wannan da zan sanar da kai"fadila dake kashingide cikin motar kalaman suka shiga kunnuwanta,amma sai taga meye nata tunda ba'asa da ita ba,bari taga ya drama din zata kaya,sake kallonta aliyu yqyi cikin raini "ke! Ki shiga hankalinki,ni ba sa'an wasanki bane,bana son shashancin banza" yaja tsaki yana shirin tada motar ya kunnata ya fara dan janta yana duna inda zaiyi ribas,"ko baka sona ni ina sonka wallahi kuma suna na mansurah"ya leqa kansa ta window "sai ki bada himma ko,stupid" "Iove you idan baka soni ba bazaka hanani in soka ba aliyyu salim kuma sai na aureka na shigo gidanka"zuciyar 'yan maza ta motsa ya tsani mata masu naci irinta haka,niyyarsa ya fice yayi maganinta ta kama hannunsa dariya na shirin subuce mata "haba sonka fa tace tana yi ba qinka ba,masoyi ai yafi maqiyi meye laifinta?" Tana gama fada dariyar ta kubce mata

Qyal qyala dariyarta take sosai,cak ya tsaya yana kallonta,kyawunta ne ya fito sosai,tuni ya mance da wasu ya shagala da kallonta,ita kam bata ma lura ba dariyarta take har da toshe baki,a hankali ya kai yatsansa lobawar nan ta tsakiyar habarta da ta dauki hankalinsa sannan ta farga ita yake kallo,ta yi qoqarin gintse dariyar ta janye fuskarta a kunyace,ajiyar zuciya ya saki kana ya tada motar,tuni ya manta da wata halitta wai ita mansura,fadila ce ma idanunta suka kai gun tayi sakato a tsaye tq zuba musu ido ita mansuran sai lokacin ta kula bashi kadai bane cikin motar,tamkar ta fashe da kuka takaici ya cikata,'yar rakiyar tata kam dariya take ta qyalqyala mata"ai na gaya miki mansura,banda abunki ki duba fa kanki ki dube shi ki dubi kuma wadda suke cikin motar tare,wanda yake da kamar wannan ai baki isheshi kallo ba,ke babu lallaima ko a 'yar aiki ya daukeki indai zaki hada kanki da wada suke tare din nan" ashar ta lailayo ta dirka wa qawar,ita kuwa tayi gaba ta fice abunta

Tuqi yake amma gaba daya kaf hankalinsa na kanta,duk second biyar zuwa goma sai ya juyo ya kalleta,sai daga baya ta lura da hakan "please ka maida kanka gun driving,kaga muna kan titi ne"ta fada idonta na kallon kan titi,gani tayi yayi gefan titi a hankali ya gangara gefan kwalta yayi parking din motar sannan ya kashe ta,ta juyo ta dan dubeshi don bin ba'asin abunda suka tsaya yi din,amma sai ta kasa furta komai saboda wani mayen kallo da yaje binta da shi wanda ya haddasa mata jin wata matsananciyar kunya mai kashe jiki,ya sake raunata mata zuciya da gangar jikinta da wani kurman saqon soyayya mai zafi,bata san sanda ta maidq bayanta jikin kujerar ba ta lafe hadi da langabar da kanta gefen kafadarta hagunta

A hankali yasa hannunsa ya juyo da fuskarta zuwa gareshi, "no,kada kimin rowar fuskarki baby na,barni in more abuna" bata ce komai ba sai dan qaramin murmushi da ta saki wanda ya sake shagaltar da aliyyu,sannu a ahankali ta dora qwayar idanunta cikin nasa tana morewa kallon aliyyun,rana ta farko da hakan ta soma kasancewa tsakaninsu,dukkaninsu kallon so qauna aminci da yarda suke wa junansu

A hankali ya soma motsa labbansa da yakejin suna mishi nauyi still idanun nasa na cikin nata yace "please,tell me kina sina baby nah"ta dan lumshe idanun nata tana jin wani shauqi cikin zuciya da gangar jikinta sannan ta sake budesu ta watsa su cikin idon aliyun "bau wasu kalmomi da zasu iya bayyana abinda nake ji cikin zuciyata, I love you more than I did yesterday,and I will love you more tomorrow than I do today,kai na fara so kuma kai zanci gaba da so har qarshen rayuwata,inaji a jikina an halicceni ne kawai saboda kai" jinsa yake tamkar yana yawo a sararin samaniya,yana jin tamakar su dawwama a gun tana ci gaba da bayyana masa irin qaunar da take masa da sweet voice dinta

Karo na farko da fadeelah taga dariya mai cakude da murmushi cike da nishadi kwance bisa fuskar aliyyun,har yanzu idanun nasu na manne dana juna "is what I see in your eyes true or the mirror?"gyada kai tayi tana mai bashi tabbaci "its true,da gaskene miji na" "really?" Ya sake tambayarta "yes its real"ta amsa masa tana sake bashi tabbaci,hannayenta ya kamo ya matse cikin nasa tafin hannun,"please ina neman alfarma guda daya" gyada kai tayi alamun tana saurarensa,ya sake matsowa kusa da itan har suna shaqar numfashin juna yana murza tattausan tafin hannunta "ina roqonki fadeelah if u reprimand me hug me and give me bliss and let it to be a loving touch,please na roqeki kada ki sake yin nisa da ni,kada ki kuma barina,kada ki kuma raba ruhina da naki,kimin alqawari fadeelah na,are you promised to do it?"ta gyada kai tana murmushi "yes I promise you" "good and I promise you too....I will never do it again,all I want is to see you smile forever not just for a while...." ya rungumeta tsam yana fadin"am sorry I will never hurt you again" "ya wuce wallahi ya wuce,Allah ma muna masa laifi ya yafe mana"

Tsawon mintina yana rungume da ita yaqi sakinta,ita din ma dadin hakan take ji sosai,don ba zata yaudari kanta ba sosai tayi missing soft skin nashi,tayi missing scent nashi masu dadi,kai komai nashi ma tayi missing dinsa,sai gashi lokaci guda Allah ya maido mata da shi da kuma abunda bata taba tsammanin ba ma,duk da ta sani addu'a bata faduwa qasa banza dama,kuma lallai wani jinkirin alkhairi ne,sai da taga lokaci na qoqarin qwace musu gashi bai da niyyar sakinta bare ya tada motar su tafi "lokaci na tafiya fa,kada momy taga ban dawo on time ba"ya dagota yana kallonta"sai kice mata kin sha'afa ne kina tare da lovely husband dinki"ta rufe fuskarta da tafin hannunta "momin zan cema haka?"ya dage girarsa "yes kinga sai tace tattara kayanki kibi mijinki,kinga fine komai yayi kyau ko?",sai ta maida jikinta kan kujerarta tana murmushi qasa qasa,qamshin turarensa da ya manne a mayafinta yana sake yi mata dadi tamkar yau ta sanshi

Kusan sai da suka tsaya sau kusan uku kafin sukai gida,kallonta yake ne yaqi maida kanshi yayi tuqin,idan tayi masa qorafin hakan sai ya yace "gaskiya gaskiya bazai iya tuqi baya kallonta ba,saidai a haqura da tuqin idan ya gama kallon nata sa tafi,lokacin da suka isa gida tuni anata tada iqama,tana qoqarin ficewa daga motar ya kamo hannayenta,ta dan fiddo da idanunta tana kallonsa,ta shagwabe fuska kamar zata yi masa kuka " please ka sakemin hannu muna cikim gida ne fa yanzun,it can be possible wani ya fito ya gan mu a....." kanta qarasa tuni ya janyota jikinsa daidai lokacin uncle abba ya fito daga cikin gidan hannunsa dauke da carbi da alamu masallaci zashi

Sarai ya gansu amma sai ya dauke kai tamkar bai kula da su agun ba,farinciki yaji sosai cikin zuciyarsa "alhamdulillah"kawai yaje fadi cikin ransa,bisa dukkan alamu sun sasanta kansu kenan,yanzu yake ji a zuciyarsa zai iya maida fadilan gidan aliyyu,don duka alamu sun nuna na qauna da soyayyar da suke ma juna,fadila ce ta soma ganin abban lokacin har ya basu baya,ta zare jikinta da sauri tana gyara yafen mayafinta zuciyarta na bugawa tace "innalillahi" aliyu ya kalleta"lafiya baby?"
Uncle abba ta nuna masa da yatsa tuni idanunta suka cicciko da qwalla "ya ganmu wallahi,sai da nace ka bari ka bari fa"

Dariya ya saki cikin nishadi "to mene ne?,kinga addu'ata ta karbu kenan,kuma ma baby naga da mijinki ya ganki fa mene na rudewa har irin haka?" Ya jawo hannunta yana goge mata qwallar da ta soma gangaro mata "calm down my unique,don't cry again,kin gama kuka a duniya ai matuqar ina tare da ke,I will never let your tears to fall down again.....muje ma raka ki ciki"sai taga tunda abba ma ya riga ya gansu a dazun don rakata ma cikin gida ba komai bane,abun kunyar dai an riga an gama tafka shi,tayi tayi da shi ya bata jakarta ta riqe yaqi yace sai ya kaita har ciki,sai da yace idan ma ta fiya matsawa zai goyata ne ya kaita har cikin gidan,tasan kadan ne daga aikinsa,tilas ta bar masa tayi gaba yana take mata baya......

*Mrs muhammad ce*👑

📚📚📘📘✍🏻✍🏻
[10/16, 2:15 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

1⃣9⃣&2⃣0⃣

Ai kuwa sukayi kyakkyawan gani cikin parlour,momi ce da iftihal dukkansu suna zaune kan kujera sanye da hijabi da alama sallah suka idar,karatun qur'ani iftihal keyi da ka momi na gyara mata kura kurenta,kallo momin ta bisu da shi daga bisani sai kuma ta dauke kanta tamkar bata gansu ba,ya miqawa fadila jakarta da take ta Allah Allah ta bar falon kunya gaba daya ta rufeta,gogan harda hadawa da hannunta lokacin da zai miqa matan,ta zame hannun nata da sauri ta haye sama inda dakinsu yake,ya wani bita da kallo ko kunya baiji ba,sai da ta qare hawa sannan ya janye idonsa ya

Please Login or Register in order to submit comment