Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne,nasirun ya dan sake ranqwafawa yace barkanku da dare hajiya an quni lpy,fadila ce kawai ta amsa samirah kam dauke kai tayi kamar batasan yana yi ba takaici ke cin ranta da dab banzan kishi sai tayi banza da shi
Aliyu ya qare maganar da suke yi da shi da"sai na dawo kaima zaka iya wucewa gida sai gobe insha Allah"nasiru ya dan ja baya yana cewa to yallabai a dawo lpy Allah ya tsare,har ya saoma jan motar ya tsaya ya dannawa nasiru horn ya dawo da sauri yace masa"nasiru kayi qoqarifa gobe ka fita da wuri ka fara zuwa gunsu haruna ka b tabbata a gobe an gama sa kayan duka cikin store qarfe sha biyu zan qaraso insha Allah ,yace to da yarda Allah goben za'a kammala,aliyu yace sai ka wuce gida ka kwanta da wuri don ka samu tashi da wuri Allah ya bamu alkhairi,ya ja motar suka fice
Yanayin tuqinsa salon da fadila bataso ne sau tari sukanyi fada da frida akan haka wato gudun tsiya ne da su,ya iya gudu da keta motoci,motar ta dauki shiru sai sanyin raba dake ratsa kowanansu kowa kuma da abinda zuciyarsa ke saqa masa,a sace fadila ke kallon aliyu ta mirror,fuskar nan ahade tan shaqar qamshin turarensa na chastity sai ta kasa dauke idonta a kansa sonsa na mamayarta,ji take tamkar ta kamoshi ta rungumeshi a qirjinta ko zaiji yadda zuciyarta ke bugawa saboda shi ya tausaya mata,a yanzu ba abinda tane buqata illa soyayyarsa,tana ji ne kamar ta furta masa abinda ke danqare a a zuciyarta ,don kanta ta dauke idonta tana sauke boyayyar ajiyar zuciya
Tafiyar mintina qalilan suka isa katafaren kantinnan na shoprite,ya dauki wayarsa iPhone 6 yayi yan danne danne sannan yayi kira da bai wuce na second goma ba ya maida wayar gefensa ya kashe motar minti ashirin na bayar kada kuma a wuce haka,samirah tace cikin murmushi"ok sweet"ya maida mata da cewa"ok dear"wani dadi ya rufe samiran kamar ta taka rawa💃🏽 domin ta dade bata samu hakam daga gareshi ba duk da tsan ba laifinsa bane ita ta barar da damarta,ta kama hannunsa ta masa kiss sannan ta fice,abinda bata sani ba tuni fadilan ma ta rigata ficewa
Ta kwashi kusan minti goma bata dauki komai ba tana zaune duniyar tunani sai da taga giftawar samiran a inda take sannan ta ankara ta miqe,wani abu ya darsu a zuciyarta,nana da nan ta soma zabar vest ta maza cotton fala qal mai kyau da taushi ta dauki gajerun wanduna dozen sai hand kerchief dozen agoguna na kamfanin gucci uku azurfa biyu takalma hudu budaddu biyu rufaffu biyu sai turarurruka na kamfanin rasasi sai rezar aski ta maza tare da shaving cream na nair,ta daukarwa kanta turaren blue lady sai relaxer,sannan ta amshi mutuminta wato ice cream manya robobi guda hudu,leda biyu aka mata kayan sai tata ledar ta tashi shafal babu wani abun kirki da ta dauka,kayan basu da wani nauyi don haka da kanta ta dauka ta fito,tana kusantar motar gabantana dada faduwa bata ga alamun samira ta dawo ba don haka ta iso motar ta sanya hannu ta bude gidan baya ta zuba ledojin hannunta sam sai ta kasa zama cikin mitar kasancewar aliyun na ciki don haka sai ta tsaya jikin motar ta jingina da ita ta harde hannayanata bisa qirjita tana bin harabar gun da kallo gamida qare masa nazari na yadda matasan yan birni maza da mata keta kara kainar shigowa gun da motocinsu 
Sai fadila ta soma qosawa da tsaiwar gun ganin yadda duk naminin da zai gifta sai ya zuba mata idonsa,taja tsaki tana jin takaicin matsanancin kallo irin na waau mazan,kamar daga sama ta jiyo dakakkiyar muryar Aliyu yana cewa"malama koma.mota ki zauna tun ke bakisan me ya dace ba" a sanyaye ta juya ba tare da ta kalleshi ba ta shige cikin motar zuciyarta na mata quna da jajen yadda aliyu ke mata mu'amala tqmkar wata mara rai kunnuwanta basu taba jiyo mata kyakkyawar kalma daga bakin aliyu ba akanta,zuciyarta ta fara tafasa saidai ta danne bacin ran nata da kiran sunayen Allah,dama ta tsammaci fiye da haka ma daga gurinsa

A hankali ta soma jiyo maganganun aliyu dake tsaye jikin mota sai ta tsinci kanta da kasa kunnuwanta cikin qaqanin lokaci ta fuskanci da mace yake hirar,kai tsaye ba zata fassara hirar data soyayya ba amma zaka fuskanci cewa akwai alaqa tsakaninsu ,mai da bayanta kawai tayi ta jingina da makarin kujerar ta lumshe ido tana sauraron bugun da zuciyarta keyi ta dauki tsaqon mintina a haka ba tare da ta tantance halin dabm take ciki ba sai da aka gama zubawa samirah siyayyarta a but qarar rufe buut dinne ya dawo da ita duniyar data Lula
Muryar samira ta karade gun cikin tuhumar aliyu da wace yake waya cikin rashin ladabi bai kulata ba sai da ya gama wayarsa tsab yayi sallama dabwadda yake wayar ya kashe bai ko kalleta ba ya bide side dinsa ya shiga itama cikin sauri ta zagayo tana huci ta shiga itama ta bame qofar yana yiwa motar key ta sake jaddada masa tambayarta "na ce ma da wakake waya?"aliyu bai iya qarya ba don haka kansa tsaye ba tare da shayin komai ba yace"da maman iftihal kin gane?"ba samira da tayi tambayar ba hatta fadila da amsar ta daketa,samira ta hadiye abinda ya taso mata don bin qwaqqwafi ta sake jeho masa wata tambayar daidai sanda motar ta saitu akan kwalta"ro mw kake nufi da yin magana da ita gidanka take nufin dawowa koko ya aka soma?""duk yadda ta kama haka za'ayi"ya mayar mata kansa na kallon kwalta,saiga samirah ta dora hannu aka tana shirin zunduma ihu🙆🏻,da sauri aliyu ya sauka gefan kwalta ya taka birki yace"bari na sauke ki idan kin gama ihun saiki tari mota ki biyo ni tunda lasheki nayi ko kuma satoki nayi"ba tare da ta sauke hannun ba ta hau maganganu bai kulata ba ya figi motar ya koma hanya,fadila kam na baya ji take kamar babu jini a jikinta babu abinfa kunnanata da qwaqwalwarta ke ganewa har suka iso gida ita dai taga ficewar samirah fit kamar walqiya bata ma jira motar ta gaa parking ba don saura kadan ta fadi,ita kam bata da kuzarin yin hakan don haka ta jawo ledar da ta yiwa kanta siyayya tabar wadda ta masa,ta fara tafiya ta jiyo maganar sa abayanta yana tambayar ledar meye ta bari?ta sadda kai qasa😔cikim sanyin murya tace kayanka ne,ya sake damqe rai😠 yacekayana?na sanar da ke ne ina da buqatarsu?"dum dum taji atsakiyar kanta wadda tamkar an buga mata guduma a tsakiyar kanta taji,batasan sanda ta isa sashenta ba ita dai ta tsinci kanta ne kwance bisa carfet din falonta
Aliyu yabi inda ta wuce da kallo ganin bata tanka masa bailla ma ledar hannunta da ta saka ta wuce tana raba hanya,sai yaji wani iri a cikin zuciyarsa yake jin kamar bai yi abu mai kyau ba ya sunkuya ya dauki ledar da ta saki din ya bude mota ya hada da tasan ya wuce sashensa don ko kusa baiyi sha'awar neman samira ba don yasan bazai tainci komai ba illa qarin damuwa da koke kokenta na tsiya,kai tsaye ya wuce bedroom dinsa ya dora ledojin bisa center table din dake gaban gadon ya cire kayansa ya shiga wanka bayan ya fito ya ciro kayan bacci ya feshe su da turare su haka nan jikin sa,ya shimfida sallayarsa yayi shafa'i da wutiri sannan yayi addu'o'insa ya shafa,ya murzawa qofan dakin key yasa hannu zai kashe wutan dakin din kwanciya idanunsa suka fada kan ledojin da ya shigo da su,bayan ya kashe ya koma ya dauki ledojin ya koma saman gado ya kunna fitilar gefan gado ya zazzage kayan dake ledar farko,daya bayan daya yake daga kayan sannu a hankali yake binsu da kallo,sai yaji kayan aun nurgeshi kamar ta san zabinsa,kayan sun masa sosai ya maida su cikin ledarsu,ya jawo tata ledar ya bude wani dan qaramun murmushi ya saki😊hadi da wani abu mai kamar tausayi da ya kamashi,sam list din siyayyar da aka turo masa nata bai kai daya bisa biyar din siyayyar samira ba,ya tashi ya bude dan qaramin pridge din dake dakin ya debe ive cream din ya zuba aciki ya hade ragowar kayan ya dora bisa bedside

Kwananta biyu kenan tana fama da matsanancin ciwon kai da yaqi saukar mata ta wani rame tunani biyu ne ya addabeta,yiwuwar qara masu abokiyat zama wanda take ganinhaka wabi babban qalube ne da zai qara nisanta ta da aliyu sai kuma raahin sauki na qiyayyar ta da take gani qiri qiri atsakiyar idanun Aliyu

Mrs muhammad ce

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:34 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?.......
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Written by safiyya Abdullahi musa huguma

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶1⃣6⃣

Yauma tana kwance saman carpet ta kanta bisa pillow kwanciyar rub ciki tayi saboda yadda take jin kan nata kamar zai tarwatse doguwar rigar bacci ce a jikinta iya gwiwa,gashin ta yayi dai dai kan pillow din,idanunta runtse suke ciki n haka ta jiyo sallamarsa,ta kadu sosai wanda hakan ya sake haifar mata da wani ciwon ko motsi ta kasa yi bare tayi yunqurin barin falon,tana jinsa har ya qaraso kanta yana sake maimaita sallamarsa,sai dai dif ta kasa amsawa sai wani bari da jikinta yake yi,yasa qafarsa ya dan bigi gefan pillow din da take kai ga zatonsa bacci take saidai nan ma yaji shiru,hakanne ya danso taba tunaninsa,ya sunkuya a hankali yasa hannayensa biyu ya birkitota gaba daya ta dawo rigingine fuskarta cikin tasa saidai idanunta na runtse don wani tsoron ne ya sake mameyeta,hawaye ya gani sharkaf a fuskarta ga wani dan banzan zafi da jikinta ya yi har haqoranta sun fara haduwa da juna"subhanallah😳"aliyu ya fada,surarta gaba daya ta bayyana har baisan sanda ya fadi hakan ba kyakkyawan gashinta ya sauko ya rufe fiye da rabin fuskarta,sai kuma yadda jikinta yayi zafi da yawa da yadda idanunta suka tasa,ya sunkuceta kamar wanda ya dauki tsinken sakace yana laluben bedroom dinta
Saman gadonta ya ajjiyeta ya zuba hannayensa cikin aljihun wadonsa yana kallonta ya rasa mai ya kamata ya yi mata wane taimako ya kamata ya fara bata,don da gaske tanajin jiki rashin lpyr na damunta,a hankali ya bude labbansa yace"relieve ur self and stop d crying "sai da ya kwashi kusan minti biyar sannan yace"already dama baki da lpy?"ta gyada kai ya sake tambaya"meke damunki?"ta nuna masa kanta,bai sake cewa komai ba ya shiga toilet dinta ya hada mata ruwan wanka mai dumi a bathtub sannan ya fito "kishiga ki shirya kanki likita zata zo"daga haka ya fice,ta daddafa bango ta shiga toilet din ta sabe jikinta ta dawo ta saka doguwar riga ta atamfa mai dogon hannu ta fesa body spray ta hade kanta da band qarami ba tare da ta taje shi ba ta koma ta kwanta,bata dade da kwanciya ba taji ana knocking aliyu ne ya tura ya shigo bai dubeta ba taji yana bada umarnin a shigo
Likitace sanye da kayan aiki,aliyu dama bai lamunci hurda da likita namiji ba akan matsalar iyalinsa tun usuli tun maman iftihal doctor sa'adah itace family doctor dinsa ta qware sosai akan aikinta tasan me take tamakar mayya haka take akan cuta da maganinta,da sallama ta shigo farar macace dirarriya wadda aqalla shekarunta ba zasu haura talatin da biyar zuwa arba'in ba doctor sa'adatu akwai ta da fara'a don.mawuyacine kaga fuskarta babu murmushi yanzun ma da fara'ar a fuskarta suka gaisa da fadila tana mata sannu yayin da Aliyu ya jawo dresaing chair dinta ya zauna hadi da zaro wayarsa ya soma danne danne,doctor sa'adah ta ajjiye kayan aikinta a gefan gadon ta fara fito da su tana tsokanar fadila"Allah dai yasa qaruwa muka samu madam😃"kunya ta kama fadila don a haife doctor ta haifeta,ta dan saci kallonsa sai ta ga ma sam hankalinsa bai kansu 
Cikin qwarewa ta soma aikinta tana gwaje gwajen tana hada mata da tambayoyi,tambayoyinta har suka so rikita fadila domin tamakar doctor na son karanto zuciyarta ne ,fadila tayi ajiyar zuciya lkcn da doctor ta tsagaita da tambayoyin ta zauna a gefan gado yadda zata iya fuskantar aliyun sosai tace"gsky a.s maitama damuwa ce fal a zuciyar madam wadda itace musabbabin wannan ciwon nata wanda Allah ya gani da ace tana fa qaramin ciki da tuni tayi miscarriage dinsa,aliyu ya maida wayar sannan ya kalli😒sa'adatu ba tare da yace komai ba tasan bazaiyi maganar ba don ba komai yake bada amsarsa ba saboda haka sai kawai ta dora da bayaninta"ya kamata ka binciki abinda ya sanyata damuwa mai yawa haka,ya dauke idanunsa daga kan likita yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yace"doctor iya sanina bata da wata matsala amma gaki gata ai u can ask her"ya dago kyawawan idanunsa masu tafiya da zuciyoyin miliyoyin 'yammata ya zubesu fes bisa fuskar fadila,tayi gaggawar yin qasa da kanta don kada tana fama da kanta ya baro mata wani aikin,tasan cewar a yadda take jinta dinnan matuqar ta yadda suka hada idanu to la shakka qaryarta ta qare domin daga shi har sa'adah ba zasu sja wahalar gano mai ke dawainiya da zuciyarta ba"meye damuwarki?,ya furta cikin dakakkiyar murya ba tare da ya dauke idonsa a kanta ba ,da zata iya ba shakka da tace masa kaine!,kishinka da qaunarka aliyyu sune damuwata!!!,sai fainkash ko kusa bata jin zata iya,abinda take jin zata iya kuma ahi yafi dacewar tayi din shine shiru kuma shi tayi din
Shiru din kuwa ya ratsa dakin doctor sa'adah tace"mai tama ba haka ake ba,it can be d screat ne she dnt wanna share it with another person so ka bari idan na tafi ta gaya ma a nutse"ta qarasa maganar tana yago pepper daga memonta mai tambarin asibitinta a jiki ta soma rubutu bayan ta kammala ta ajjiye takardar kusa da fadila da har yau kanta ke sunkuye tace"to madam Allah ya qara sauqi but pls kiyi qoqarin rage damuwa"kai ta daga ta mata godiya,sa'adah ta kalli aliyyu tace ga magungunan da za'a siya mata a nemo.yanzu ta soma sha zata samu relief insha Allah amma ta dan ci wani abu before ta sha din,ta miqe tana hada kayanta tqna musu salllama aliyu yace"thanks sa'adah a gaida yara


Mrs muhammad ce

📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wa yasan gobe?

▶1⃣7⃣

Fitarta da yan mintina aliyu ya dauki pepper din maganin ya fice ba tare daya ce mata kanzil ba,shima ba dadewa da fitar tasa wayarta dake qarqashin pillow ta dau tsuwwa alamun shigowar kira,a kasalance ta daga wayar tana duba mai kiran sister farida ce ta daga hadi da yin sallama farida tayi dan jim sannan tace sister ya naji muryarki ta canza ne?fadila cikin muryar marasa loy ta masa mata wlh bani da lpy ne farida ya gida ya kuma mubarak?cikin yar qaramar dariya farida tace duk muna lpy sister ko ta samu ne?,samuwa kamarbyaya? Ta tambayeta,farida tayi qasa da murya tace ian nufin fa juna biyu,ta dan basar tace abinda kika bugo ki tambaya kenan?,a'ah anty dama ina ceqa ne gibe ki duba haya ina nan zuwa harda result dinki tun last week ya samu,duk da bata jin da lafiya hakan ya mata dadi sosai har ta nuna zumudi,jin bata da lpy yasa farida qyaleta akan sai tazo goben,ta amsa don dama kantabhar ya soma sarawa ta maida kanta saman pillow ta kwantar tana addu'ar Allah yasa ta samu damar aiki
Ya shigo hannayensa biyu riqe da ledoji ya shigo ya zubesu kan bedside ya maida hannayanaa aljihu kamar kullum,ji tayi kamar ya cika mata dakin wani kwarjininsa ya cika mata gu jikinta yayi sanyi tanajin kamar ko hannuta ba zata iya dagawa ba ta shiga satar kallinsa duk fa batayi niyyar yin hakan ba zuciyarta ce ta tursasata kansa na qasa ne yana kallon carfet kamar mai nazari,sai ya mata kyau sosai fuskarana fes kama ganinta kasan tasan hutu tabbas maza irin aliyu sai ka tara dari zaka samu biyu cikinsu ga tsawo da qaqqarfan gangar jiki mai murdadden damtse mai cike da qarfi faffadan qirji mai cike gargasa wadda ta bayyana har hannayensa yana da jiki amma ba zaka kirashi mai qiba ba domin tsawonsa ya shanye ta,kusan ko yaushe fuskarsa a haka take ba fara'a sam don ita a iya saninta da shi bata taba ganin haqoransa ba,
Saura qiris ya kamata tana satar kallonsa tayi gaggawar janye idanunta daga kanshi a hankali taji yace dazun na tambayeki meye damuwarmk yanzun ma na maimaita karo na biyu"shiru ta sake yi.masa hakan yasa ya kausasa.murya yana sake tambayarta,cikin cool voice dinta tace babu komai,ya dago kamar zai kalleta sai kuma ya lumshe ido ya budesu kan.ledojin da ya shigo da su sannan yace idan tashin hankalinki da damuwarki sun ta'allaqa ne kema kan dawowar maman iftihal to kiyi saurin taimakawa kanki ki nemi sassuci a gun zuciyar ki don zata dawo ne amatsayin mata ta karo na biyu ba wata baquwa bace......sannan ki bawa zuciyar dai taki again shawara da kada ta cika kanta da damuwoyi masu yawa tun yanzun......ya danja fasali sanna ya miqa hannunsa ga wayarta dake gefanta abinka da giant tuni hannun yakai ba tare da ya hau gadon ba ya lallatsa sannan ya ajjiye mata yace"ga abinci nan da magunguna ki sha,then ga number ta if there is any problem contact me"daga haka ya juya ya fita ba tare da Saura ron komai ba
Sai abun ya zamewa fadila wani iri ta jima akwancen kafin ta samu damar miqewa zuciyarta na qarfafa mata gwiwa ta tashi ta taimaki kan nata kamar yadda aliyu ya shawarceta,tq shiga toilet tayi fitsari sannan ta daura alwala wai ko zata ji sauqin zugin dq zuciyarta ke mata,ta dawo bakin gadon ta bude ledojin daya magunguna ne a ciki daya kuma gasashshiya,ta dinga zare tsokar tana ci zuciyar ta dauke da addu'o'in samun sauqin daga quncin zuciya(inda Allah ya taimaki fadila kenan bata mantawa da add'a duk irin situation din da take ciki,muyi koyi da ita yan uwa domin hatta qaddara babu abinda yake tareta sai add'u'a,mu dinga tuna Allah a yayin da muke cikin jin dadi da walwala sai Allah ya tuna da mu lokacin da mu kuma muke cikin qunci da neman taimakonsa wannan fadar annabi ce s.a.w,kai ta addu'a da sannu Allah zai isar maka,take note pls!)jin naman take kamar magani mai daci haka taci gabada dannashi har tqji kamar zata yi amai,ta balli.maganin adadin yadda aka rubuta tasha sanna ta dan zauna na mintina don abincin ya fada mata sanna ta ja pillow ta kwanta,cikin ikon Allah ta dinga jin sassuci a zuciyarta,ta jawo wayarta sai taji tana qamshin aliyu ta soma duba contact dinta taga number din da yace yasa mata ai kuwa a rukunin A taci karo da sunansa full name dinsa ya saka mata ta bude numbers din tana qare musu kallo suma special ne don cikin taqaitattun daqiqu zaka iya haddacesu,(mrs muhammad nace ko na sato muku numbers din A.s maitama ne cikin wayar fadilan?to gasu 0803344.......😜😜 to naqi don naga wata har tana saurin kwafa ba ruwana ku da fadila😜)ta zuba musu ido kamar tana son ganin fuskar mamallakin numbobin da ta gaji da kanta ta rufe wayar ta maida ta qarqashin filon ta lumshe idonta tana maida numfashi cikin zuciyarta ta soma tilawar suratu yusuf tana yi tana bin labarin annabi yusuf din da Allah s.w.a ke bayarwa cikin surar,zuciyarta ta mata sanyi damuwarta ta ragu sosai lallai Allah yayi gaskiya da yace(ala bi zikrillahi tadma'innal qulub/ku saurara da ambaton Allah ne kadai☝🏼 zukata ke samun nutsuwa)

To fa makaranta na labari yanzu muka soma shigarsa kuci gaba da jumurin bina insha Allah zamu cimma gaci😊

Dumbin godiyata a gareku
Mrs muhammad ce

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻........
[10/16, 12:35 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wa yasan gobe?

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶1⃣8⃣

Washegari misalin sha biyu na rana tana kitchen tana tafasa ruwan lipton so take ta dan sha ko zai warware mata ciki don tun tashinta yau ba abinda ta iya ci,muryar farida taji tana qwali mata kira da gudu ta fito suka rungume juna suna dariyar farincikin ganin juna😄,farida ta dan janye fadila daga jikinta tana cewa sister yi a hankali kada ki mana asarar baby,fadila ta ballamata harara tace"wai ke wa ya baki wannan labarin qanzon kuregen?farida tace bayan mun gama waya jiya da ke da daddare rabi'ah ta kira ni take gayan again,fadila na qoqarin komawa kitchen din tace uhm sai ki zauna ai kiyi ta jiran cikin,farida tayi dariya ta bita,maimakon daba lipton sai ruwan zafin ya koma na girki,suna yi suna casar hira,suka kammala suka zuzzzuba su a warmers suka wanke kwanukan hadi da gyara kitchen din

Wash! Inji farida bayan ta zauna fadila ta kalleta tace kin canza sister fa sosai kinga qibar da kika fara yi?farida tayi murmushi tace ke dai bari ya fadila ina tsammanin ciki ne fa?,fuskarta cike da fara'a 😄tace ke dan Allah,tace wlh da jibi ko gobe mubarak ya matsa sai naje an min test wai kada na jawo masa asara cikin rashin sani ni sai naga kamar ba shi ba,kasala kawai fa nake da yawan bacci,fadila tace,a'ah nima fa ina bayan mubarak sister kije a dubakin meye amfanin zaman haka,kina likita ai kinfi kowa sanin alfanun abin,tace insha Allahu gobe zamu je

Farida ta janyo jakarta ta bude ta miqawa fadila takardunta,cikin zumudi ta buda tana duba result din ba abinda bakinta ke fada sai alhamdulillah,domin kuwa yayi kyau fiye da yadda ta tsammata cikin farinciki tace da farida"burina na gaba farida inga na soma aikin media shine burina tun ina qarama"murmushi ta sakar mata tace"kwantar da hankalinki ya ahmad yana can yana miki wannan aikin don kuwa freedom da express tuni sun karbi takardunki jira yake kawai yaji daga garesu,wani farincikin da qaunar yan uwanta ya sake kamata
Tana toilet tana wanka ta bar farida a afalo tana kallin arewa 24 suna haska maimaicin shirin boyle bitmesin wato kyautata rayuwa da yake jiya tace tayi missing bacci ya dauketa bata kalla ba,ta jiyo hayaniya sama sama ta tsinci dai muryar anty hauwa din haka a gurguje ta gama tana fitowa ta shirya kanta cikin shigar doguwar rigace ta shadda wadda aka mata paint work mai tasadar orange ce akayi mata kwalliyar light blue,body spary kawai ta fesa ta daura dankwalinta ta debo magungunanta wadanda zata sha da rana ta fito falon,rabi'ah ce da sumayya da anty hauwa,cikin fara'a suka gaisa suka mata sannu da jiki"tace ai na samu sauqi ina momy da iftihal mutuniyata,anty hauwa tace suna gida gurin momyn nace ne ba da wanda zanzo duk har su kausar suna gunta muhammad ma tunda ba nono yake sha ba acan na barshi don suna zamu wuce dqga nan wata maqwafciyata ce ta haihu to kuma da yake haihuwar ta danzo da matsala a gidan su take acqn za suyi taron,tace eh Allah ya qara mata lpy,amin inji anty hauwa
Nan suka shiga hira abinsu minti talatin suka miqe suna shirin tafiya fadila dake ta qoqarin zuba musu abincin tace anty ga abinci don Allah ku tsaya kuci,anty hauwa tace bayan lemo da cake da kika cika mana ciki da shi alhamdulillah wlh,rabi'ah tace nikam anti fa na fasa rakiyar nan gidan sunan kuce da maman hidaya ina mata barka na taho anjima farida ta saukeni a hanya,sumayya tace"dama na sani anti ba rakaki zata yi ba ina ji tana cewa yau ana rana da yawa nasan dama daga nan gidan ba inda zata dara"aishikenan muje mu gaisa da samirah sai.mu wuce,inji anty hauwa,sumayya ta coge😒sannan tace a'ah anty nikam zan jiraki cikin mota ki shiga ki fito tayi saurin yin gaba damma kafa antin ta tsayar da ita,fadila tace "baki kyauta ba sumayya idan kika wuce baki gaidata ba"rabi'ah dake zaune tace wlh anty ko nice ba zan je ba,farida dake ta faman cin abincinta abunta tace qyalesu sister mai daki shi yawan inda yake masa yoyo✋🏻,ai kuwa dai sister farida sai.kaje kayi ta bugu taqi budewa gashi fa kana kallo ta tana kalloka qiri qiri,bayan kuma ta bude sai tayi.bake bake a bakin qofa ta tsare ka da ido tana wani ce maka meye?kamar wanda kazo maula gurinta,duk suka kwashe da diyar yadda rabi'ah ta gwada yadda samiran keyi banda fadila da ta dan murmusa gami da girgiza kai tana mamakin halayya irinta samirah
Biyar da rabi farida ta dauki rabi'ah suka tafi suma sashen sai ya dawo sai ita kadai ta so ta yiwa farida zancan dawowar maman iftihal sai kuma taga mai hakan zai dadeta da shi iyaka

Please Login or Register in order to submit comment