Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata khadijatu tana fatan Allah yasa ta yi gadon hali irin na mai asalin sunan,salima dama wannan bai dameta ba ita dama ta rabu da cikin shine agabanta alaqaqai kamar yadda ta laqaba masa

Aka gama wannann ta wuce salima ta sake qirqirar matsala ta biyu wadda ta tunzurashi ta koma jawo igiyar aurensu ta guntule

Mrs muhammad ce👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:48 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*Part 2*

1⃣9⃣&2⃣0⃣

Yadda abun ya faru shine salima sam taqi shayar da iftihal,anty hauwa ita ta gani ta yiwa salima magana cikin nasiha da kuma fadakar da ita illolin dake tattere da qin shayar da yaro nonon uwa indai ba lalura ba mai qarfi wadda zata jawo hakan koda hakan ta faru wasu basu yarda da madarar suna kai dansu ne ga wata wadda suka amincewa halayenta ta shayar musu da yaro balle ita da lafiya lau ne babu wata lalura,qememe salima tayi da ranta taci gaba da dirkawa iftihal baiwar Allah madara ba tare da masaniyar aliyyu ba

Ranar da lamarin ya faru sati biyu ne da yin haihuwar cikin yan suna wata ta sanar da ummi halin da ake ciki don haka ta aiko anty hauwan takanas da roqo da kuma lallashin salima tayi haquri ta shayar da iftihal don abun ya daga hankalin momin tace ko lafiya ce bata da ita tayi magana sai a a samo mata magani cikin tsiwa da rashin kunya salima tace"ita momin ce ta aiko ki?to ki gaya mata babu dan iskan da ya isa ya jawomin abinda zaisa jikina ya lalace lafiyatq qalau saidai tun farko na gayawa ubanta ban shirya haifarta bane,don da na samu dama da tuni tabi rariya ba zata ma zo duniyar ba bare azo ana min iyayin banza da wofi akan...........

Bata qarasa ba taji saukar lafiyayyun mari hagu da dama na kumatunta,da sauri ya daga kai din taga wanda yayi mata irin wannan aika aikar,aliyyu ne tsaye bisa kansa cikin matsanancin fushi fuskarsa tayi jajur😡 abunka da fari huci kawai yake fitarwa kamar wani zaki ya dora da cewa"bansan baki da mutunci ba sai yau ashe ke 'yar iska ce ban sani ba? Mahaifiyata kike fadawa wadannan mugayen kalaman?.....to bari kiji salima.....👉har yau ba'a haifi yarinyar da zata ci mutuncin iyayena ba wallahi duk son da nake mata,yarinyata kuma daga kin bar bata madara indai ni ke aurenki"

Cikin hasala ta miqe tana nuna kanta tace 👆🏼ni ka mara aliyyu?....ni ka mara?,to an fada din yarinya kuma wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata sha min nono ba,ai kana da yan uwa mata kana iya basu ita su shayar maka ko ka samar mata wata uwar ko kuma ka maidata cikinka ka sake haifeta"ya harzuqa matuqa ya daga girarsa yana kallonta "oh haka kika ce! Indai kuwa haka ne baki da wani amfani" "to ba sai ka yiwa tufkar hanci ba"a zafafe ya gyada kai yace "ok,well kije na sake ki saki daya"

Maganar tayi matuqar girgizata tayi zumbur ta miqe ta dangwarar da iftihal da da take riqe a hannunta tace"tafi nono fari ai" ta shige bedroom dinta,yarinyar tamkar kuwa tasan meke faruwa ta tsandare da kuka,ko waiwayo ta bata yi ba,anty hauwa tuni ta qame hannunta aka 🙊🙆🏻saboda sakin da aliyyun yayi

Ta fito dauke da akwati tana shirin fita,sai lokacin anty hauwa ta samu bakin magana "kiyi haquri don Allah ki dauki yarinyar nan"ta juyo a fusace sannan tayi murmushin takaici ta dubi anty hauwa"ai burinku ya cika ko?kuma ina tsammanin kema macace akwai nono a qirjinki kamar nawa to kina iya bata naki"a fusace aliyyu ya sake tasowa da niyyar kai mata wani marin anty hauwa ta tare gabansa

"a'ah aliyyu kada ka sake dole taji haushi its our fault dont beat her again mu lallabata ta dauki yarinyar dai"cikin harzuqa da tsawa wadda baisan yayi ba yace da anty hauwan"ni👆🏼 ni zan lallabata don ta dauki iftihal god forbid anty"ya fada yana kada kai"ko zata nemi hakan ba zata samu ba"bai san ya sake tura ma salima wani baqincikin ba da sauri ta ja akwatinta ta fice,a sanyaye anty hauwa ta juya ta dauki baiwar Allah iftihal dake nannade cikin showel tana ta tsanyara kuka kamar tasan abunda mamanta ke yi ,sanyata tayi a kafada tana jijjigata tana kallon aliyyu dake zaune saman kujera dafe da kansa idanunsa alumshe jijiyoyin kansa sun fito sunyi rada rada tasan alamun tsananin fushin aliyyu kenan tun yana yaro ,a hankali tana shafa bayanta har yarinyar ayi shiru da yake mai haquri ce bata da rigimako kadan matuqar ta qoshi

Zaman sukayi tamkar na makoki na kusan minti talatin sanann tace"aliyyu tashi mu wuce gida dole su abba suji irin aika aikar da kayi,ya kada ki bayan ya bude idanunsa da suka koma ja ya kalleta"ban yi laifi ba wannan shine hukunci da yafi dacewa da ita,ni nasan me dame salima ta yimin bayan wannn tun alokacin ta cancan ci narabu da ita amma na daure"ya maida kasa kujera yana maida numfashi ya daga mata hannu alamun ta tafi kawai

Ta girgiza ki tace "a'ah bazaiyi na qyaleka ki kadai ba kana cikin irin wannan mood din"ita tayi driving shi kuma ta bashi iftihal din ya riqe,ido sosai ya zuba yana kallon yarinyar tausayinta matuqa ke shigarsa yana tausaya mata na rashin dacen uwa da bata yiba ya rungumeta tsam tsam a qirjinsa cike da qaunarta

Fa babu irin wanda momi bata yi ba tamkar ta ari bakin wasu,kamin abbansa ya dawo ya dora da nashi,ce masa auke ai haquri shine mafita ba saki ba,shi dai uffan bai ce ba don baijin koda salima ta dawo tofa ta rasa shi shi da 'yarsa har abada

To kuma sai aka taki saa ko rashin saa zance ne?uncle abba me ya nuna dattako da kansa ya taka gidansu salima don yin bikonta,qara ra a gabansa abban ta ya nuna masa shifa ba ruwansa bazai tursasawa 'ya 'yansa ba don suna da 'yancin yin duk abinda suka ga ya dace da rayuwarsu,amma zai kira salima atambayeta idan zata koma to,da yake a cikin zafin kanta take a lokacin bata ji kunyar budar ido tace da uncle abba ba itafa ba zata koma ba"abban nat ya kalleshi yace"to kaji mai zaman tac3 bazata iya ba"abba bai sake tofa kanzil ba ya bashi hannu sukayi musabaha ya dawo gida

Lamarin rayuwar gidan nasu yayi matuqar bawa uncle abba mamaki,rayuwar'yancin kai suke irin ta mai jan kunne?ba rayuwa ba irin ta addininmu wadda fiyayyen halitta ya koyar da mu ba?,wanna wane irin masifane da a yanzu muka qaqabawa kanmi?,bayan ya dawo ya sanar da momin yadda sukayi,ita kanta da ake mace abun ya daure mata kai amma kasancewarsu iyaye masu dattako da basu so dansu yayi saki sai ta nemi izini gun uncle abban akan ita ma zata je ko za'a dace"uncle abba bai hanata ba yadda mai akai da mahaifin salima exactly haka akayi da mahaifiyarta don aqidar duka iri guda ce

Saidai ita an samu dan bambanci kasancewar salima tafara saukowa har ta fara kewar aliyun sai mamarta tace wa momi saidai aliyyun yazo da kansa,nan momi ta saka shi gaba akan lallai lallai ya shirya yaje,shi dai kullum yana binta ne da to don kuwa ya riga ya gama yankewa ransa cewq ko itace autar mata yq haqure mata don gaa daya ta qarasa ficewa fit daga ransa,bata da wani abu a yanzu da zata burgeshi da shi

Ganin momi ta soma tsanantawa a al'amarin sai ya soma shirin komawa indiyarshi ba tare da sanin kowa ba bai so ba ba kuma a son ranshi ba don baiso yayi nisa da yarinyarshi sai da ya kammala ne suka sani,momin taso ta hana abba yayi mata magana aka ta tsagaita hakanan da Maganar dole sai salima ta dawo idan da rabo zaman bai qare ba zata dawo ne,aliyyu mai tsananin biyayya ne bashi da tarin kunne akan duk wani umarni da iyaensa suka bashi,yana dai da zurfin ciki ne da nauyin baki,tun yana yaro idan suk ce yayi abu ya kafe baiyi ba to yanada dalilinsa ne mai qwari wanda sai daga qarshe idan suka bincika sai suga lallai yana da gaskiya

Momi ta gamsu da bayanin abban ta kuma yiwa aliyyun fatan alkhairi da samun dacewa,aliyyu ya bar nijeria 🛫cike da kewa da qaunar 'yar diyar tashi tsoka daya a miya khadijatul iftihal,ya tanadar mata duk wani abu da zata buqata daki guda ya ware mata yajibge mata komai hatta da ruwa da zata sha ya tanadar mata bai bari ya dorawa kowa wahalarta ba harda kayan banza ma da wofi wanda bata buqatarsa,hakanan ya bude mata account duk wata yana saka kudi a ciki yace da momin aje a cira ayi mata abinda tale da buqata,to kawai take cewa kamar yadda uncle abba ya umarceta don shi tuni ya karbe ragamar komai din kudin da aliyyun keta aikin turowa uncle abba yace abarshi cikin account din ta amfanesu idan ta mallaki hankalin kanta

Wata shida kacal salima taji ajikinta qaunar aliyyu da yarinyarta tamkar zata zautata cikin begensu take kwana take tashi,yayin d iftihal ke cikin walwala da samun gamsashshiyar kulawa gata da soyayya ta qannen uba kakanni na gun uba da kuma dangainsa,tayi bulbul abinta madarar dai ita taci gaba da karba don itama taqi nonon kowa zakaran da Allah ya nufa da cara sai gashi cuta mai taba yaro bata taba samun yarinyar ba don ko haqori tashi sukayi suka ganta da shi ya soma fitowa,ga wayo a gunta gane mutane da kaifin basira

Shekara daya da rabi salima ta kasa daurewa,ido ta rufe ta soma neman aliyyun,saidai ya riga ya toshe duk wata kafa da zata sada shi da ita,sai daga baya ta samu labarin ya koma india,ba bata lokaci tayi visa ta bishi don zamanta da aliyyu ta samu dukiya sosai kasancewarsa mai sakin hannu shi yasa hatta zaman gidansu take jin bai mata ba

Acan din ma bata sameshi da wuri ba don ya canza gari ma gaba daya sun zauna a mumbai ne shi kuma ya koma new Delhi taci wuya ka su hadun saidai haduwar tasun mabata haifar mata da d'a mai ido ba,kaca kaca yayi mat irin wanda bata tsammani ba ya kuma jamata kunne da idan har ta sake suka kuma hada hanya sai ya wulaqantata,ta samshi qwarai idan ya fusata baida dadi iya kuma qurewa ta sani ta qureshin don haka bashiri ta tattara ta dawo nijeria ba tare da ta cimma nasara ba

Aliyyu bai waiwayi nijeria ba sai bayn shekaru uku cike da nasarori da budi masu tarin yawa wadanda bai taba tsammatar samunsu ba,company nasa ya bude babba acan hadi da qulla harkokin kasuwanci kala daban daban da wasu manyan kamfanonin,yazoya taras salima naci gaba da bibiyar rayuwarsu shida yarsa taqi aure sam duk wadata tsaya da shi sai taga ba namiji bane ganinsa take kamar mace yar uwarta taqi sauraron kowa da komai,itace kira saqonni na email sms duk wata kafa da ta samu ya rabu da duk wasu layukansa saboda ita amma ya rasa yadda take samun sababbi,sunzo don a basu iftihal yafi sau hamsin tun yana india suke da muradin haka ya gaya masu su da iftihal saidai su ganota daga nesa don bata buqatarsu


🔱 🔱🔱🔱🔱🔱
*samira*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱

Shekarunsa hudu da dawowa ya hadu da samira gun bikin abokin kasuwancinsa,tunda ta qyalla ido a kansa ta qwallafa ranta,ta rasa ta inda zata samu shiga domin kuwa baida walwala ko sakin fuska shi yasa take fargabar tunkararsa,da yake tare yake ta hidimar bikin abokin nasa da iftihal dinsata lura da yadda yake ta nan nan da yarinyar ta samu kuma information kanncewa 'yarsa ve da yake tsananin qauna sai itama ta jata ajiki sosai tattali take nuna mata kamar babu gobe,shikam mai son wanda ke son iftihal dinsa ne don haka ya sakar ma samira duk da ya ja jikinsa sosai da fari saboda yakan tuna yadda ta kasance masa a baya tsakaninsa da salima

Itama tazo akan gaba don lokacinne tsananin ya sake aure ya masa yawa a gida ahi kuma a zahitin gaskiya a wannan lokacin bai da time na duba mace,ganin ya samu maison iftihal dinsa yasa ya amince daga qarahe ne ma momi ke masa albishir din itafa ba zata bashi iftihal ba donnta riga tazo kenan,ba yadda ya iya duk da son da yake wa yarinyar tasa

Sai da salima ta gasu sosai fiye da tsammaninta wanda tadinga jelen kamun qafa da momi da abban da a baya ta watsawa qasa a ido kullum tana cikin gidantana magiya sannan ta samu dawowa gidanta,gidan da ta tarar ya kubce mata har wasu biyun sun samu mazauni cikinsa,ya ta iya da ranta son da take masa yasa bata ji wani abu ba tayi zamanta duk da a baya tana daga cikin matan dake iqirarin basu ba kishiya don ba zasu iya zama tare da ita ba

🔱🔱🔱🔱🔱🔱
*_dawowa labari_*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱

Washegari tun qarfe tara fadila ke shirin fita suna,tayi wanka ta shirya tsaf cikin shadda dinkin doguwar riga ne yasha aiki daga sama har qasa butter colour ta debi wadanda zata sauya a can kala biyu ne da tayi musu anko ita da faridan zasu sa tare ta shirya iftihal cikin itama doguwar rigar yan kanti wadda ajiya ta bada aka siyo mata hade take da takalminta da ribbons dinta red ce in and top ta tsaya mata iya qauri takalmin boot ne na yara fari qal tayi ma gashin yarinyar ado da fararen ribbon tayi kayu matuqa kasancewar yarinuar mai yalwar gashi mai tsawo da santsi

Hat ta tada motarta iftihal ta hango abban nata ta balle murfin motar ta fice aguje,bayan ta duqa ta gaidashi ya dauketa yana wulla ta a sama shiko nauyi bata yi masa"cewar fadila cikin ranta tana satar kallonsu,tana ganin iftihal na nuno mishi ita,ya juyo ya kalleta suka hada ido tayi maza ta sunkui da kai don kada qwayar idanunsu ta hadu ya saka mata dafin da ya saba jefa maya cikin zuciyarta na qarin qaunarsa,"verry neat ya fada sannan ya dauke kai"iftihal ta leqa fuskarsa "daddy munyi kyau kuwa"yayi kissing kumatunta yace kinyi kyau sosai my dear"tadan bata fuska tace "anty na fa?"yayi yar qaramar murmushi yace "both of you""thank you daddy"ya sauketa bayan ya sake kissing dinta tana daga masa hannu ta zura aguje ta dawo cikin motar tana dariya

Mrs muhammad ce👑😘

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:50 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

2⃣1⃣&2⃣2⃣

Fadila tayi murmushi sannan ta tada mota iftihal tace "anty Abba yace munyi kyau wai na zama 'yar gatan anty ni 'yar gatanki ce wai anty?"ta shafa kanta da daya hannun nata tana murmushi tace"iftihal ke 'yar gata na ce mana"

Minti arba'in suka qarasa gidan da yake safiya ce babu yawaitar mutane sai 'yan uwa na jiki sosai,su hajja gana(kakarsu ta gun uba) umma a'i anty hafiza rumaisa da sauran 'yan uwa na nesa da na kusa,Fadila ta fada jikin hajja gana tana cewa bari na more cinyar 'yar tsohuwa" hajja gana ta sa dariya da yake sunfi shiri da Fadila fiye da farida"more abinki kafin kema Allah ya kawo miki masu more taki"murmushi fadilan tayi sannan suka soma gaisawa da yan uwan hajjar na tambayarta mai gidan tace lpy lau yana ma gaisheki

Kafin azahar gidan ya tumbatsa da jama'a,ko ta ina,bayan azahar kuma da kadan sai ga family din aliyyu momi ce kawai banda ita,cikin bedroom din farida sukayi zamansu anata karbar baqi

Rabi'ah ta kalli fadila lokacin da take canza kaya su anty hauwa na sallah tace "ni dai anty idan kuka tafi chinan nan qana nan kaya kawai nike son tsarabata"fadila ta dago ta dubeta bayan ta gama zuge zif din rigarta tace"wace china kuma rabi'ah"dariya rabi'an tayi"kai anty ko baki son asan zaki ne?"cikin rashin fahimta take dubanta tana qoqarin daura dankwalinta"wai wa yace miki zani china rabi'ah?"ta sake qyalqyalewa da dariya tace"tun last week fa yaya aliyyu ya gaya ma momi an gama ginin sabon company dinsa da zai bude zai wuce china cikin satin nan ke da shi,shekaran jiya kuma sai ga shi ma da visa dinku a hannu ta fito jibi zaku tashi da daddare amma anty kice baki sani ba?😀"

A badini zancen yayi matuqar kidima fadila ya daketa sosai amma sai ta dake don kada ta bada satar amsa ta qago murmushin yaqe"kinsan halin yayanku akwai lafiyar miskilanci dazun dai yake cemin idan na dawo zai min wani albishir to ina tsammanin shine"sumayya da a lokacin ta sallame sallarta tace "har Allah Allah nake na idar kinga haukan da salima ta dinga yi wai da ita za'a tafi?"su sumayya suka kwashe da dariya rabi'ah tace"qara fa ta kawo gun momi sai gata tayi tsuru tsuru da ya aliyyu yake fadin babu abinda suka iya ba inda zai je da su su zamar masa nauyi"sumayya ta dora "qarshe ma momi da yake zayyano mata matsalarsu kunya ce ta isheta ta bar falon ba shiri tace suje gida su shirya kansu mu dai bamusan ya aka qare ba bata sake tada zancen ba ma"anty hauwa tace"ku kuma gaku sarakan gulma ba,kwaci qaniyarku da ya kamaku kuna labe ai"

Duka wunin ranar bunda ke cin zuciyar fadila kenan zancan tafiyar yayi masifar daga mata hankali,sai ta rasa nutsuwarta gaba daya,lokaci lokaci qwalla kan taru a idonta ta faki idon mutane ta matse ta,gaba daya sai kuzarinta ya ragu,Allah Allah take su kebe da farida,bata tsammani alkhairi aliyyu ke nufi da tafiyarsa da ita,nufinsa ma fa kenan gaba daya tabar aikinta da take masifar so ta kuma fara jin dadinsa yake kuma debe mata kewa?sam ba zata iya wannan tsari nasa ba

Sai bayan sallar isha'i ta samu nasarar tadda farida cikin bedroom dinta zaune gefan gado tana canzawa baby da taci sunan maman mubarak wato(aisha humaira)pampers ta zauna itama a gefan gadon tana duban pampers din da faridan me sawa humairar ,da fara'a farida ta juyo a fuskarta tana duban fadila zata dan tsokaneta sai fara'ar ta janye sakamakon qwalla da ta gani tana bin kumatun fadila tayi hanzarin sauke humaira da ta aza akafadarta tana cewa"lafiya sister?"tamkar ma ta tunzurata sai hawayen suka dadu

Tafin hannunta take sawa tana share su da nufin tsaidasu saidai turereniyar fitowa ma suke abinsu,sai da farida tasa hannayenta ta kamo hannayen fadilan ta sa cikin nata sannan ta sake tambayarta,da qyar kuma cikin muryar kuka fadila ta bude bakinta tace"yanzu tsakani da Allah abinda aliyyu kemin yana kyautawa?"tayi tambayar wasu hawayen sabbi na shirin sake zubowa,farida ta sake fuskantarta a dan kidime tace"meke faruwa sister me ya miki?"ta girgiza kanta cike da damuwa"wai china zai dauke ni mu tafi har kuma na tsawon wata hudu

Sai farida ta sake ta hadi da sakin dariya tana tafa hannu"🤔yanzu sister fadila wannan abun farincikin kikewa kuka kamar wata teddy?"fadila ta katseta"ba zaki fahimta ba farida kwata kwata wata na nawa da soma aikina?"farida ta sake dubanta"😏aikin banza sister fadila,ga inda zaki samu aljannarki kike zancan wani aiki"sake girgiza kai fadila tayi"still farida baki fahimceni ba,zan gaya miki abunda babu wanda yasan yana faruwa sai ke,har yau sister aliyyu bai sona,aliyyu bai qauna ta kalma mai dadi bata taba hada ni da shi ba kallon arziqi bai taba shiga tsakanin mu ba amfani na daya agunsa shara da girke girke tamakar wata 'yar aikinsa tun muna kusa da iyaye kenan tun muna qasarmu kena ina ga nabishi can wata uwa duniya mai kuma kike zaton zai faru a ni?"

Ga mamakin fadila sai taga farida tayi murmushi mai kaa da dariya sai fadila ta saki baki tana binta da kallo tan tsammanin farida bata damu da halin da zata tsinci kanta ba kenan ko yaya?,sai da ta gama dariyarta sannan tace"☺👏🏻bravo! bravo! bravo!,wallahi aliyyu yayi miki gata ba da qarami ba"zaro ido fadilan tayi har ya mamakin bai sake ta ba😳,ganin haka yasa farida ta kama kafadar fadila ta sake juyowa da ita ta fuskanceta sosai,ganin yadda fadilan ta tsure sai ya sake bawa farida dariya daga baya kuma sai ta dawo serious dinta ganin kallon sakarcin da fadila ke mata,ta kuma kama hannunta sannan tace"ni na gano abinda qila ke baki gano ba,kuma ba zaki gano shi ba yanzu,sister duk abin ya aliyyu koya nuna ko kada ya nuna ko ya yarda ko kada ya yarda kina da muhammanci da wani tasiri a rayuwarsa komai qanqantarsa koda kuwa ya qaryata hakan da bakinsa,sister a iya hangena da tunani na na fuskanci cewa don kada ya aliyyu yayi missing girkinki ne baya so yayi nesa da abincinki wanda yasan zaiyi wuya ya samu kamarsa nima shaida ce"ta qarashe maganar cikin sigar tsokana wadda ta zame mata jiki

Ta nuna fadila da yatsa 👉�sannan ta dora ke zaki canza wannan manufar ke zaki sauyata da kanki,ke zaki canza wa aliyyu wannan lafazin nasa na bazai soki ba har abada ki qaryata lafazin nasa ta hanyar nuna masa ba wanda *_yasan gobe_* sai Allah,sosai ta gamsu da maganar farida dari bisa dari kaso sittin cikin dari na damuwarta ya tafi,ta jinjina kai hadi da sakin ajiyar zuciya sannan tace"batun aikina fa sister?" "So easy"inji farida ta gada tana murmushi😊"k8na iya daukar excuse a gurinsu ki musu bayani tafiyar gaggawa ce ta sameki zuwa china zaki ajiye aiki amma da manufar zaki je course ne na wata hudu,idan hakan bai samu ba su barki a matsayin wakiliuarsu ta qasar china ta tsawon wata hudu" "great sister!"fadila ta fada cike da farinciki,tabbas dan uwa na gari dadi ne da ahi gashi xikin 'yan mintina qalilan ta warware mata damuwarta,ta rungume faridan tana cewa"thank you sister ya barmu tare ya raya mana humaira"tace "amin Allah yasa kema ki samo mana tsarabar dan china nan da wata tara ko goma mu dauki sabon baby " dariya sosai ta bawa fadila tana jinta ne kawai

Sanda ta dawo gida yana zaune cikin balcony dinsa,tayi maza ta dauke kai gami da qara sauri don ta shige shi

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Washegari qarfe 6:40 pm ta dawo daga aiki sun gama settling komai da managing director na express da freedom sai damuwarta ta sake raguwa qwarai da gaske,tana toilet din falo tana wanka taji moysi kadan kadan a falonta,da sauri ta kammala tana son taga waye don a bude tabar bangaren nata,kacibus sukayi da shi tsaye yake tsakiyar falon yana sanye da kufta dark coffee wadda tasha aikin sarauta sai hukarsa baqa abinka da fari sai yayi matuqar kyau kyansa da jaskensa ya sake fitowa shigar ta amshe shi sosai fadila ta lumshe idonta tana jin wani abu na zagaya jikinta"ki shirya na kaiki gida ki masu sallama,gobe zamu bi jirgin yamma insha allah zamu wuce china"duk maganar nan da yake idonsa na kan wayarsa dake hannun hagunsa damansa kuma cup ne cike da maltina mai sanyi🍺,ta dan langabe kai kamar bata ji mai yace din ba"ina zamu je?""kaiki zanyi na siyar"ya fada yana ci gaba da danne dannensa ta faki idonsa ta manna masa harar ta zagayeshi ta wuce zuwa bedroom

A sanyaye ta kammala shirinta cikin atamfa dinkin riga da zan8 simple style hakanan fadila take bata fiya son abimda ya cika ado da yawa ko daukan hankalin jama'a ba yadda take bata da hayaniua haka dabi'unta suke saidai idan ta so,ta lullube kanta da wadataccen mayafi kalar kayan,ta jawo locker dintabta debo kudaden da suke ciki ire iren kudaden da aliyyun ke basu ne duk qarashen wata da kuma na cefane acewarsa tunda komai suna da shi a ajjiye hatta magi ba zasu buqata ba ta watsa su cikin jakar sannan ta rataya ta ta fito,yana zaune a mazaunin driver tasan bata isa ta shiga baya ba ko ya shiga zai maidoto ne gaba don haka ta bude gaban ta zauna,yadan kalleta hadi da dauke kai ya daga glassan motar gaba daya samà ya rufe su ruf hadi da kunna a.c,wani irin tuqi yake slowly tamkar baza'aje ba tayi tsammani zaiyi irin tuqin nan nasa mai gudun tsiya,a hankali suke ratsa titi nan har suka qaraso cikin anguwarsu fadila

Muje zuwa masu karatu🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻

Mrs muhammad ce👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:50 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

2⃣3⃣&2⃣4⃣

A qofar gidansu yayi parking,bata ce masa komai ba kamar yadda bai tsinka mata ba,ta bude murfin motar ta nufi bakin get din gidan cikin doki ta dan tsaya suka gaisa da malam mai bude masu qofa idan zasu shige da motarsu

Parlour din babu kowa sai qamshin fresher da ya gauraye da na girki ,murmushi fadilan tayi kai tsaye ta nufi kitchen

Please Login or Register in order to submit comment