Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne, idan na ganka sai naji takaici ya cika zuciya ta yanda ka kasa fahimtata, sannan ka kasa yadda dani, ni matar kace da zan iya iya gaya maka abinda ya kamata. Yayi d'an jim yana kallonta, ya san abin da take son fad'a, amman bai son yayi riga malam masallaci, don haka cikin hikima ya fara k'ok'arin kwantar mata da hankali, domin a ganinsa wannan ne lokacin da ya kamata ya rarrarsheta, domin yana ganin kamar ta sauko daga kandokin zuciyar data haye. "Bilkisu ban ta6a tinanin akwai wani abu da zai zo na raina na tozar
Taki ba, kawai dai na kan yi miki uzuri ko nak'i sanar dake abin dana san ina da gaskiya akanshi, wanda na tabbatar gaba ko bana raye zai amfanar dake da 'ya'yana, ki yadda bana yin abin da zai sosa zuciyarki da gangan, ruyuwar nan gajeriya ce idan ka d'auketa da zafi haka zata zo maka, sannan idan ka d'auketa da sanyi ma haka zata zo maka.
Tayi shiru cikin damuwa, ita bata son irin wannan dogon bayanin nasa, domin yana k'ara tabbatar mata da cewar bai sauka daga kan ra'ayinsa ba kenan, ta d'an fara jin haushi amman bata bari ya bayyana ba ta fara magana cikin kwantar da murya da kissa. "amma alhaji ka san Aliyu bai kamata ace ya zamto mijin hanan ba, akwai banbanci da tazara mai yawa a tsakaninsu ta zahiri da ta bad'ini ko. Tana magana tana kallon sa domin ta kula maganin ta ya fara aiki ko bai fara ba.
Alh. Ya gyad'a kai yana d'an murmushi "kamar yanda naga ya miki bilkisu rayuwa ta danganta ga yanda mutum ya d'auketa, sai dai ina son kisani, kuma ki sanya cikinranki. Duk wani mutum da kika gani a duniyar
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(11)
Nan Allah ne ya haliceshi ya kuma bar shi a halin dayake ciki, babu wanda ya san me gobe zata haifa, idan kinajin labarin shugabnnin da suka shugabancin k'asar nan da manyan malaman k'asar nan, da kuma gwabnoni da 'yan majalisu ke har da attajiran kasar nan sai ki ga a bayaba kowanan suba, wasu ma sun rayu cikin tsananin talauci da wahala, amman daga baya suka wamto haka, kinga sanin gobe sai Allah...
"Alhaji misalin daka bayar yana da banbanci da na hanan da aliyu fa. Ta katseshi cikin damuwa, ta hanyar wurga masa wannan tambayar. Bai damuwa da yanda ta katseshi d'in ba domin ya fuskanci tazo da wani salo ne na son sauya masa ra'ayi, wanda ya san haka ba zai yuwa ba har abada, cikin kwantar da murya yaci gaba da bata amsa. "Ban san banbanci dakike nufi ba, kamar yanda na sha gaya miki cewar hakkin aurar da hanan a wuyana ya rataya, ni ya kamata na za6ar mata miji na gari wanda hankalina dana ta zai kwanta har abada, kuma ina son ta auri mijin da bashi da wata tawaya ta zahiri ko ta bad'ini,
Aliyu yana da ilimi yana da asali, yana da sana'ar yi, menene wanda bai cika bana k'a'idojin aure? Ya wurga mata tambayar shima.
Idonta ya fara sauyawa 6acin ranta ya fara bayyana k'arara, domin har muryarta ma ta sauya gaba d'aya. "Akwai abin daya rasa alhaji, bai sami soyayyar hanan ba, bata son shi, bata k'aunarsa kwata-kwata, bai kamata ka tilsta ta auran wanda bata so ba, sannan kamar yanda nake gaya maka, a matsayi da wayewa irin na hanan da karatunta wallahi tafi k'arfin almajiri kamar aliyu, ko ka manta shi yaron gidan kane? Ya kula data fusata kamar yanda yayi tsammanin zai faru tun da farko sai ya k'ada kai yana k'ok'arin lallashinta, domin yana son yau ta fuskanci abinda yake hango musu a gaba. "Kiyi hak'uri ki kwantar da hankalinki bilkisu, inason na miki wata tambaya, shin almajiri ba mutum bane ba? "Mutum ne, amman kowacce kwarya da abokin burminta, na gaya maka kwata-kwata ba sa'an auran hanan bane, kuma idan har ina da mutunci a idonka, sannan ka yadda ni matarka ce da baka da kamata,
(12) kamar yanda ka fad'a don Allah kajanye maganar auran nan. Sai ta fashe da kuka. Ya tsaya yana kallonta cikin mamaki, k'iri-k'iri son zuciya ya sanya matarsa rufe ido akan gaskiya, amman har lokacin bai fitar da ran ganar da ita gaskiya ba, don haka yaci gaba da magana yayinda take ci gaba da kukanta. "Shin bilkisu kin ta6a bincikar wanene mansur? Kin ta6a bincikar halayan sa da mu'amalar sa? Ta kalleshi a fusace "ai wannan ba wani abune da kowa zai gaza sani ba Alhaji, kasan iyayan yaron nan da danginsa, idan ma wani abu aka ce maka yanayi ai k'uruciya ce, da tashi cikin arzik'i da daula, yara irinsu nawa ne da zarar sun yi aure suke gyaruwa, amman irin su Aliyu da sun sami abin da suke so shi kenan, sai iskanci da wulak'anci. Ya gyad'a kai cikin takaici domin ya k'ara tabbatar da har abada matarsa ba zata sauka daga kan ra'ayinta ba, don haka bashi da za6i bayan gaya mata gaskiyar dake ransa. "kamar yanda kika fad'a haka ne, mansur zai iya shiryuwa a gaba, amman banzan iya aura masa 'yata ba tare daya
Shiryu din ba, aliyu shine mijin dana za6awa hanan, ina kuma fatan kiyi hak'uri ki mini biyayya, domin magana ta riga ta k'are, yanzu ma muna tattaunawa domin k'ok'arin fahimtar dake, kin san saura kwanaki k'alilan wannan bikin... Ta kalleshi a fusace "kana son ka tabbatar mini da bani da daraja a idonka kenan ko alhaji?
Cikin zafin rai take maganar idonta naci gaba da zubar da hawaye, ya kad'a kai cikin rashin damuwa da hargaginta. "Ko d'aya ba haka bane, kamar dai yanda na fad'a miki, kiyi hak'uri, bakin alk'amin ya riga ya bushe, insha Allah hanan bata da miji bayan Aliyu. Taji kamar ya soka mata mashi a zuciyarta, abu biyu yake damunta yanda yadage akan abin da yake fad'a, da kuma rashin aikin da maganinta bai yi ba, hakan ya tabbatar mata da duk abin da ta kashe akan mutumin nan tayi a banza, sai ta fice daga d'akin a fusace, alh. Musa yayi ajiyar zuciya cikin damuwa, tabbas ya gaji da wannan hali na matarsa, zuciyarsatana gaya masa abubuwa da dama, amman bai son ya zamto mara adalci, don haka zai bata
(13) lokaci har zuwa lokacin daza ta huce. Bayan haj. Bilkisu ta isa d'akin wayar k'anwarta ta kira tana kuka ta sanar da ita duk abin da ya faru. "nagaya miki alhaji taurin kai ne da shi, duk asirin dazaki yi masa wallahi bazai kama shi ba, mutumin dayake kwana akan sallaya, sannan kullam cikin addu'o'i yake, yanzu kinga nayi asarar kud'ina da lokacina. Tana magana cikin masifa da kuka, duk yanda batula taso kwantar mata da hankali da k'ok'arin nuna mata zasu k'ara bin wata hanyar taki yadda da hakan, daga k'arshe ma kashe wayar, ta zauna kawai a gefen gado tana huci, sai taji kamar an shigo daga bakin k'ofa ta d'aga kanta, hanan ta gani a tsaye tana hawaye, hankalinta ya kara tashi. "ya akayi hanan? Ta wurga mata tambayar, hanan ta fashe da kuka ta k'asa ta fad'a kan cinyarta tana kuka, taci gaba da lallashinta. "ki gaya mini menene ya faru? Me akayi miki kuma? Cikin sheshekar kuka ta fara magana "momy na ji duk abin da ya faru tsakaninki da daddy, na gaya miki daddy ba zai sauya ba idan ya fad'i magana sai
Ta tabbata, ya yazan yi da raina momy na tsani aliyu ban ta6a k'aunarsa ba, ba kuma zan k'aunace shi ba har abada, ki taimaka mini momy, yanzu haka man yayi fishi da ni, ko wayata bai d'agawa kwata-kwata. Tana magana cikin kuka, hankali haj. Bilkisu ya kara tashi ta fara magana tana shafa kan d'iyar ta "tabbas ba zai sauya ba, ba kuma zai janye ba, amman har yanzu muna da sauran dama da lokaci, akwai abin da ya kamata mu k'ara yi, ki kwantar da hankalinki, ba zaki aureshi ba, na tabbatar miki. Hanan ta d'aga kai ta kalili mahaifiyarta cikin mamaki "momy ta yaya? Kin san gidan da aliyu ya koma? Haj. Bilkisu ta tambayeta, hanan ta gyada kai alamar a'a bata sani ba. "kin san gurin dayake sana'a? Da sauri hanan ta d'aga kai alamar eh ta sani.
"tun da kin sani magana ta k"are, idan shi ba maye bane, dole zai fad'a da bikinsa ya fasa auranki, ba zai aure ki ba. Hanan tayi shiru tana kallon mahaifiyarta bata san abin da take nufin aikatawa ba, amman dai ta d'anji sanyi cikin ranta.
Aliyu ya cigaba da shirye-shiryen
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(14) Aliyu ya ci gaba da shirye-shiryen auransa kamar yanda suka kammla magana da baffansa, yaso yaje garinsu da kansa amman lokaci ya kure masa, don haka ta waya suka yi magana da mahaifinsa, ya tabbatar masa saura kwanaki biyu bikin zasu iso shida danginsu, aliyu yaji haka matuk'a, sai dai abin da ya dameshi rashin sanin ina 'yan uwansa auwalu da sabi'u suke, duk wayoyin da aka bashi nasu ya kira basa shiga, daga k'arshe ya tafi kasuwar 'yar lemo ko Allah zai saya dace. Duk da bawani sanin 'yan'uwansa yayi sosai ba sabo da sun d'auki tsahon shekaru rabon dasu had'u, domin tun yana yaro k'arami rabonsa dasu, amman ya san ba zai kasa gane suba, domin kusan dukkansu suna kamancecenina da mahaifinsu ne. Bayan isarsa 'yan lemo yayi ta k'ok'arin neman auwalu amman ya kasa samunsa, domin sunansa kawai yake iya fad'a, har ya yanke k'auna da samunsa sai wani yace shi dai ya taba jin an kira wani abokinsu Zamalo da Auwalu, bai sani ba ko shine, Aliyu yace ya kai shi gurin Zamalo d'in yagani. Kai tsaye suka nufi
Gurin Zamalo, yana zaune gaban teburin lemonsa, ba wani girma bane da tebur d'in ba, domin duk lemon da yake kai bai fi kwando biyu ba, yana zaune cikin rana da hula akansa irin ta kaba saboda zafin rana, Aliyu da mutumin da ya rakoshi suka k'arasa, domin acan bikin hanya yayi parking d'in motarsa, bayan sun gaisa mutumin ya nuna aliyu yana magana. "Wannan ne yake neman wani mai suna auwalu, wai an tabbatar masa da annan yake sana'ar sai da lemo, shi ne nace kamar na ta6a jin wani bak'o da ka yi kwanaki ya kira ka da auwalu ko?
Zamalo ya kalli aliyu cikin tuhuma yana gyad'a kai "eh haka ne, yaya aka yi? Aliyu ya k'ura masa ido, duk da wahala da talauci sun sanya auwalu yin bak'i amman bai kasa gano kamanninsu ba, domin ko ta tsaho da rashin jiki zai iya gane danginsu, balleshi daman auwal yafi kowa tsaho a gidansu, yana tsammanin hakan ne yasanya suke kiransa da zamalo, yayi dan murmushi yana fad'in. "Kasan malam Beld'o na garin sam6auna? Mamaki ya cika fuskar zamalo yayi 'yar dariya "wacce irin tambayace
(15) wannan bawan Allah, yaya zaka ambaci sunan mahaifina kana kuma tambayar wai na sanshi, to na sanshi mahaifina ne. Aliyu yayi dariya cikin jin dad'i yana fad'in "to ai nima mahaifina nane, ni k'aninka nd Aliyu dan wajan inna sumaye... Kafin ya k'arasa magana auwal ya mik'e cikin sauri da zumud'i yana salati cikin jin dad'i. Haka ne wallahi sai da ka fad'a sannan kamanninka suka dawo mini gaba d'aya, wallahi dan uwana ne malam buba, k'ani nane, daman kwanaki can dana je gida aka sanar dani kaje, kuma akace mini anan garin kake kai ma, kai amman naji dad'in ganinka aliyu."
Yanda yake magana cikin murna da zumud'i ya faranta ran aliyu, ya dinga kiran mutane yana nuna musu aliyu cewar k'aninsa ne, su kuma mutanen kallon aliyun suke cikin mamaki, ashe zamalo yana da d'an uwa haka mai kud'h, sai da suka gama gaisawa da mutane sanan suka ke6e guri daya. Auwal ya kalli aliyu cikin jin dad'i yana magana "Allah mai iko, mun rayu gari d'aya amman bamu ta6a ganin juna ba aliyu, wannan shi ne kad'an daga illar
Almajiranci yayiwa rayiwarmu, yanzu da mun tashi gari d'aya ai bazan gan ka na kasa gane kaba. Aliyu ya gyad'a kai yana magana "hakane, Allah ya k'addara mana wannan rayuwar, amman mungode masa da ya k'ara had'amu guri d'aya, tintini nake ta neman had'uwa daku, Allah bai yi ba sai yanzu. "ka kyauta aliyu, an bani labarin irin rayuwar da kayi tajin dadi fiye damu, kayi sa'ar rayuwa ka godewa Allah, kalleka babu wanda zai yaea cewar kai d'anuwa nane, amman naji dad'i da ka nemeni. Ya d'an fara hawaye yana gogewa cikin damuwa aliyu yafara magana cikin kwantar masa da hankali. "Kayi hak'uri, mugodewa Allah ma daya barmu cikin rayuwarmu mai inganci, amman kana da labarin Sabi'u ko?
Cikin sauri ya amshe "sosai ma kuwa, ai kusan unguwarmu d'aya, domin babu nisa daga gidansa zuwa nawa, kwanaki ma daya ya kasa biyan kud'in haya nan gidana ya dawo shi da iya lansa, har sai da suka samu suka biya. Duk da nima d'in daki biyu kacal na iya kamawa." aliyu ya gyad'a kai cikin farin ciki da jin dad'i, babu abinda yake so
(16) kamar 'yan uwansa. 'Ko zamuje mu gaisa da iyalin naku, sannan shima na sanar da shi maganar bikin nawa, domin yanzu saura kwanaki tara bikin. "kace aure zaka yi Maisango, kai amma naji dad'in wannan maganar, Allah ya sanya alkairi, ai sai muje d'in, daman na kusa tashi, domin yamma ta kawo jiki, muje na tattara kayan nawa saimu wuce. Bayan Auwalu yagama tattara kayansa suka nufi gurin motar aliyu, mamaki ya kamashi dayaga motar aliyu, ya shiga cikin yana ta santi da sambatu, tun da yake bai ta6a shiga irin motar ba, to a ina zai shiga, suna tafe a hanya suna ta hira cikin jin dad'i suna baiwa juna labarinsu, aliyu ya fuskanci 'yanuwansa sun sha wahalar rayuwa kuma suna kan sha ma, sai dai inda yaji dad'i da dukkan suna da ilimi sosai na k'ura'ani domin auwalu ya gaya masa sunyi sauka sannan sun rubuce all'ura'ani da kansu, sabi'u nema yaso lalacewa amman cikin ikon Allah ya shiryu bayan yayi aure. Suna isa kofar gidan aliyu yayi parking, auwalu yace bri ya shiga ya sanar da mutan gidan su gyara,
Tun da motar ta shigo unguwar yara suka fara kallmta, domin unguwace ta talakawa matuk'a domin gidajan haya ma sunfi yawa cikin unguwar, bayan wani lokaci auwalu ya dawo cikin rawar jiki yana masa magana ya shiga, aliyu ya sa kai ya shiga. Gida ne babba mai d'akuna da yawa, domin d'akunan gidan sun kusa goma, ga mata nan kwacce a k'ofar d'akinta, wasu na girkin dare wasu na sauran ayyuka, haka suka dinga ratse su suna wucewa, cikin ran aliyu godiya yake yi kawai ga Alla daya ingata rayuwarsa, domin daga ganin gidan da yayansa ke zane ya tabbatar yana cikin rayuwa mai wahala, wai kuma anan shi yafi wancan ma rufin asiri. Bayan sun shiga d'akin damuwa ta k'ara bayyana aransa, domin ko ledar tsakar d'aki babu a d'akin, sai gado kawai lamba wan na katako da sif a gefe k'arama, laraba matar auwalu tana d'auke da ciki ga yara k'anana da manya, suna zazaune cikin murna da jin dad'i, suka gaisa da aliyun, matar ta rasa inda zata saka ranta saboda murna, wai xannan k'anin mijinta ne, ta kawo masa ruwa a kwanon sha,
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(17) tana tajan shi da hira, aliyu ya saki jiki suka yi hira sosai sannan ya buk'aci su k'asa gidan sabi'u don magariba na kawo jiki, suka mik'e yayi sallama da iylin, ya baiwa dukkan yaran kowanne dubu d'aya-d'aya, sannan ya baiwa Laraba dubu biyar. Suka amsa suna ta murna da jindad'i gami da masa addu'a, tunda take bata ta6a rik'e k'i kamar wannan ba, to duka jarin mijinata nawa yake da zata rik'e kud'i mai yawan hakan, suka yi tamasa godiya har suka raka shi bakin k'ofar gida. Yaran sai ihu da murna suke yi, musamman masu wayon, bayan sun fita mutan gida suka taru akan lbara suna tayata murna da jin dad'in kud'in data samu, ta amshe kud'in hannun yaran gaba d'aya, tana fad'in sai babansu ya dawo tukunna, wasu zasu fara rigima ta had'asu da naira goma-goma, sai gashi ta tashi da dubu goma shabiyu, domin yaran su bakwai ne. Farin ciki ya cika zuciyar auwalu, musamman kyautar da aliyu yayiwa iyalinsa, tabbas suna cikin tsananin talauci da wahala, amman yasan wannan kyautar ta sanya matarsa ta samu jarin
Sa'ana ko yayane. A gidan sabi'u sun yi sa'a yana dawowa daga kasuwa suna shiga, kasancewar sabi'u dako yake yi yanayinsa yafi na yayansa wahala da tsufa, haka nan ma gidan da yake haya ya tsufa sosai, gashi gidan k'asa ne, sai dai bai kai wancan yawan mata ba, wannan su biyar ne, bayan sun shiga d'akin hankalin aliyu ya k'ara tashi, domin shi ko arzik'in gadon ma babu a d'akinsa, sai katifa ajiye a k'asa da k'ullin kaya cikin buhunna, shima matarsa tana da kirki, amman shi yaransa ukune. Lokacin dayaji aliyu ne d'an'uwansa yayi kamar ya shid'e don dad'i, ya dinga kiran matarsa da ke tsalar gida tana hura wutar tuwo, ta shigo da gaggawa, ya nuna mata Aliyu yana fad'in.
"Kingan shi ko, k'anina ne, jininmu d'aya. Itama ta gyayar da aliyu cikin jin dad'i, sun jima suna hirar duniya da rayuwarsu, da aliyu zai tafi itama matar sabi'u ya bata dubu biyar yaranta dubu d'ai-d'ai, tayi murna da farin ciki. Bayan sun fita waje aliyu yae zaije dasu ya siya musu wayoyi domin su dinga gaisawa suna saninhalin dajuna keciki
(18) babu musu suka shiga motar, wani babban shago siyar da waya na unguwar ya siya musu amman k'aramar waya ya siya musu da bata wuce dubu biyar-biyar ba, godiya suka dinga yi tun da basu ta6a rik'e wayar da tsadarta ya kai haka ba, sai dai su siya ta hannu daba ta wuce dubu biyu ba, itama idan buk'ata tatashi su siyar da ita, har da layi da komai ya sai musu sannan ya mayar dasu k'ofar gidan auwalu, ya basu dubu goma-goma. Sun yi murma matuk'a da gaske, suka dinga godiya da sanya masa albarka, ya kuma sanar dasu maganar bikinsa sannan suka yi sallama. Aliyu yana tafiya cikin mota idonsa yana zubar da hawaye, ta yaya zai manta alkhairin da alh. Musa zayi masa, da yanzu shima rayuwarsa irin ta 'yan uwansa ce, haka ya k'arasa joint d'in su. Tun da ya shiga sunusi ke kallonsa har ya gaji ya tambayeshi abinda ke damunsa, bai 6oyewa sunusi komai ba ya sanar dashi duk abin da ya faru. Ya d'ora da cewar "sunusi da yanzu nima haka nake ko? Sunusi yayi murmushi ya dafa kafad'arsa yana fad'in "duk yanda Allah
Ya shiryawa bawa rayuwarsa haka zata kasance, ko baka had'u da alh. Musa ba Allah ya k'addara rayuwar bazata yi garari kamar ta 'yan'uwanka ba, kaci gaba da yiwa Allah godiya kawai. Ya gyad'a kai yana fad'in "haka ne, kullum cikin gode masa nakeyi. Sunusi ya sauya hirar da tambayarsa "wai abokina yaya shirye-shiryen bikin, kana ta rabon katin d'aurin aure amman banga kana manganar fati ba. "Aliyu ya kai masa dukun wasa yana fad'in "wallahi zan fasa maka baki, ka mayar dani kamar wani sakarai ko, auran da ake lalla6awa ayi...
Banko k'ofar ofis d'insu da akayi ya sanya su yin shiru, suka waiga gaba d'aya suka kalli k'ofar, hanan ce ta shigo cikin shigar data saba ta k'ananan kaya da k'aramin gyale akanta, gaban Aliyu ya fad'i, yaji wani irin abu ya soki ransa ya kasa magana. Sunusi ne yayi k'arfin halin yin magana "sannu da zuwa..."
Hanan ta d'aga masa hannu da sauri "kaga ba wannan ya kawo ni ba, rik'e gaisuwarka? Sunusi ya kalli Aliyu cikin damuwa sai ya nufi hanyar fita da gaggawa, amman Hanan ta babbake
(19) k'ofar da sauri tana cigaba da yin magana. "ya kamata ka zamto a garin nan domin zamowa shida ko gaba. Suka kalli juna cikin mamakin abin da ta fad'a, bata damu da halin da suka shiga ba, tace gaba da magana. "Na san kana da labarin abinda ke shirin faruwa tsakanin da wa6an! Ta nuna Aliyu da hannunta, sannan taci gaba da magana. "tunda mahaifina ya sanar dashi zai aura masa ni bai ta6a damuwa da sanin yaya na d'auki maganar ba, to ina son yau yasani, babu hannuna cikin wannan aure, kamar yanda na sha gaya masa na tsane shi, yau ma zan k'ara gaya masa, bana k'aunarsa na tsaneshi, na tsani duk wani abu da ya shafeshi sannan zan yi iyakacin k'ok'arin ganin ban zamo abar da ake fatan na zamto gare shi ba. "idan kuma na gaza har aka d'aura auran, to ina mai yi masa albishir da rayuwa mafi muni da tsananin wahala, don haka zaka iya bashi shawarar k'ok'arin sanar da mahaifina bai buk'atar aurena, domin na kula ya asirance ahaifina bai jin maganar kowa sai tashi. Aliyu ya waro ido cikin damuwa ya kasa magana,
Amman maganar hanan ta k'arshe ta daki zuciyarsa, mai yasa suke masa wannan kallom ne ita da mahaifiyarta.
Hanan ta k'ara kallm Aliyu cikin 6acin rai tana cigaba da magana "kasan kai matsiyacine ba d'an kowa ba, don haka kaje ka nemi mace irinka, gigin ganin na zama matarka saboda son zuciya ba zai haifar maka d'a mai ido ba, wannan shine gargad'in dazan yi maka, kayi gudun fanfalaki na fita daga cikin rayuwata, kafin ka yi nadamar da bazaka dai naba har abada!
Tana kaiwa nan ta juya a fusace ta fice daga ofis d'in, suka bita da kallo, hankalin sunusi ya tasnusi ya tashi matuk'a ya yadda hanan bata da kunya, amman bai yi zaton rashin kunyarta ta kai haka ba, aliyu kuwa komawa yayi ya zauna akan kujera ja6ar cikin damuwa kamar zai fasa kuka yake ji, babu abin da ya sunusi ya dafa kafad'arsa cikin lallasih yana magana. "ka yi hak'uri abokina, ka d'auka wannan itace jarabawar rayuwarka, babu wani mumini dazai zauna haka batare da Allah ya jarabeshi ba. Aliyu ya d'aga kai ya kalleshi idonsa ya k'ada yayi jajir
Like · React · Reply · Report
[10/29, 5:52 AM] H Inna🧕🏼: vious comments…
Zeinab Abdoul-karim
(20) almar yana cikin tsananin 6acin rai, amman jarumta da dakiya irin nasa ya sanya ya k'ak'aro murmushi yana magana. "ban ta6a damuwa da abin da Hanan ko mahaifiyarta suke mini ba, dukkan abin shukemini na 6acin rai, karamcin da mahaifinta yayi mini ya maye shi. Haka ne, amman baka ganin ya kamata ka sanar da mahaifinta wannan maganar domin ya d'auki mataki akai, bai kamata ace tana biyoka har gurin aikinka tana maka irin wannan cin mutunci ba, gaskiya bayan sanin alk'ar dake tsakaninka da yarinyar nan babu abin da zai hana na maketa? Aliyu ya k'ara yin murmushi yana d'aga kafad'a "ni kuma ban ji komai ba, na san hanan tana cikin bakin ciki da 6acin rai, tana son ta fesar da abinda ke damunta, don haka nine mutumin da ya kamata ta tunkara domin hucewa, amman nasan ba zata huce ba har abada, domin auranta bub gudu bubu ja da baya, maganar na sanar da mahaifinta kuma nayi alkawari har abada hakan bazai faru ba, babu wani abu da zata mini da bazan jure ba, kar ka damu abokina. Ya mik'e tsaye yana dan gyara
Ringarsa "zan wuce gida, akwai wasu shirye-shirye danake son yi a daran yau. "Kafin sunusi ya kai ga cewa wani abu aliyu ya fice da gaggawa cikin yanayin 6acin rai, sunusi ya bishi da kallo a ransa yana jin bakin ciki. Shi fa da shine zai baiwa Alh. Musa hakuri ne kawai ya auri wata, gayen da mata kala kala-kala ke k'aunarsa masu kud'i da yangayu, har da 'yayan manya k'aunarsa suke yi, zai tsaya wannan yarinyar na 6ata masa rai, da ace aliyu yana biyewa matan da ke nuna suna son shi ma da bai fi haka ba, bai mantawa watarana siyayya sukaje shoprite suka had'u da wata had'ad'iyar yarinya ta nuna tana sonsa ya basar da ita, daga k'arshe ya gano yarinyar d'iyar sanatace, da ya gayawa Aliyu yace sai me?
Abin da hanan ta masa ba sabo bane cikin abin data saba yi masa, sai dai zuwanta gurin sa'anarsa da

Please Login or Register in order to submit comment