Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ya kunna kallo yana yi, amman shi kansa ya san hankalinsa bai kan kallon kwata-kwata, lokacin yayi taja har zuwa kusan karfe d'aya na rana, bai yi karin safe ba ga kuma rana tayi, yaga kamata ya samarwa kansa abin da zaici, don haka ya mik'e tsam ya fita ya nufi
Kicin d'in gidan, tunda ya tare a gidan ya saba da dafa indomie ko kawai yaci idan yana jin yunwa, yanzu ma haka yayi niyyar yi. Kicin d'in babu kowa, akwai alamun ba ayi amfanin da komai ba, don haka ya kunna gas-cooker ya d'ora abinda yake buk'ata ya kammala ya koma falo ya zauna ya faraci, sai dai rabin hankalinsa yana kan kofar d'akin ko zai ga fitowar hanan amman shiru ko motsin ta bai ji ba. A 6angaran hanan, tun da ta tashi tayi sallar asuba ta k'ara komawa bacci, kasancewar tana cikin gajiya ya sanya ko motsi bata yi ba sai da rana ta take bacci har ya ishe ta, ta mik'e tana mik'a, kallon agogo ta fara wanda ya nuna k'arfe d'aya saura, tayi shiru akan gado cikin damuwa, domin tabbas ta fara jin yunwa, ta mik'e ta shiga bandaki tayi wanka ta sanya doguwar riga ta zauna tana sak'a abinda ya kamata ta yi yanzu, ta san yunwar da take ji bata iya hak'uri da ita ba, amman bata zo gidan domin tayi girki ba, kuma ta san bata isa tace zata fita haka ba tare da tasanar da Aliyu ba, abin da ba isa ba
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(31) domin mahaifinta zai iya jin ta fita d'in yau, daga k'arshe ta yanke shawarar shiga kicin taga menene a ciki. Ta mik'ie tsam tayi hanyar fita babu ko d'ankwali akanta sai gashinta data gyara ya sauka wuyanta kasancewar bata san kan gidan ba ya sanya bata san ta ina ya kamata ta bi taje kicin d'in ba, ta tsinci kanta ta yi kicibis da aliyu zaune a falo yana cikin abinci, gabanta ya fad'i har tayi shirin juyawa da gudu domin bata yi tsammanin akwai mutum a gurin ba, sai dai tayi k'ok'arin dakewa ta tsaya. Cikin damuwa ya kalleta yana fad'in "sorry! Abin da ya fad'a d'in ne ya dawo ita hayyacinta, tayi tsaki ta wuce kai tsaye ta nufi wani gurin data ke tsammanin nan ne kicin d'in, ya bita da kallo gabansa yana ci gaba da fad'uwa, bai san dalilin da ya sanya duk lokacin daya ga hanan sai yaji gabansa yana fad'uwa ba, shi dai ya san ba tsoranta yake ji ba, amman ta kan yi masa kwarjini matuk'a. Ya dinga jin kamar ya tashi ya lek'a ya ga me takeyi, amman ya san hakan bazai yuwu ba. Bayan ta shiga kicin ta
Tsaya shiru cikin damuwa tana k'arewa kicin d'in kallo, babu laifi ya burgeta yanda aka tsara kicin d'in, koda yake tasan kusan komai anty barka ta shirya, shi ya sanya ya kasance haka, ta fara bud'e lokokin kicin d'in, akwai komai na buk'atar da za ta dafa, ta bud'e farji shima akwai na buk'atar dazata dafa, ta bud'e farji shima akwai komai, ga kaji nan ga kuma kayan miya kala-kala, abin da yazo ranta shine waye ya saka wad'an nan kayan, aliyu ne ko kuma babanta ne cikin kayan gara, komai dai wanene tana buk'atar abin da zataci. Cikin gaggawa ta had'a kaza da supergetti tayi jallop ta nufi hanyar fita, sai data tsaya tayi lissafin hanyoyin da ta biyo, sannan ta gane ta ina ya kamata ta koma batare da taga aliyu ba, tayi sai kuwa tayi lissafin dai-dai ta wuce d'aki abinta.
A 6angaran aliyu tun da ta shiga kicin yayi zaune cikin tinanin, yana daga nan ya fara jiyo k'amshin girki ya cika gidan, har yana had'iyar yawu daga inda yake zaune, yana jin alamun tafiyarta ta d'ayan falon alamar ta nufi d'akinta,
(32) ya mik'e cikin sand'a yana lek'eta amma bai ganta ba, sai ya shiga kicin d'in, abin da ya bashi mamaki shine babu komai cikin tukunyar abincin data dafa, kawai alamun iyakacin wanda zata ci kawai ta dafa, yayi d'an murmushi ko babu komai yaji dad'in hakan ma datayi. Sun Wuni a gidan amman kowanne yana 6angaransa, kusan kwanki biyu da suka kwashe a haka suka yi su babu wanda ke neman wani, kwanne yana shashin sa, aliyu bai fita sai ya tabbatar yaji motsin ta a cikin gidan. Abin da ta fara yi tun farko tayi girkinta iyakacin cikinta shi taci gaba dayi, shi kuwa cikin kwanakin biyu nan sai dai ya dafa indomie yaci, a yammacin kwanaki na biyun ne yaga dacewar ya d'an fita ya zagaya gari, yana tsaka da shiri wayarsa tayi k'ara, sunan Fa'iza ke yawo akan screen din, gaba d'aya ya manta da ita, ya koma ya zauna a gefen gado yana murmushi ya d'aga kiran na ta, acan 6angaranta tama dariya ta fara fad'in. "Tuba nake ango, Allah ya sanya ban shiga lokacin amarya ba? Yana dariya yace "ko d'aya, amarya tana can
6angaranta nima ina nawa?
Tayi ajiyar zuciya tana d'an dariya "har naji dad'i, daman cewa nayi bari na ta6a gayen nan, tun da ya shige dags ciki ya manta da kowa. Maganar ta bishi dariya har da kyakyatawa abinda ya bata dariya itama tana tambayarsa me yake yiwa dariya. Cikin dariyar ya fara magana "wallahi biki da dama fa'iza, ke babu wuya kin zaro zance? Tana jin wani farin ciki yana shigarta tace "to yaya na iya, kai d'in ne hukama ce sai da lallashi, yanzu yau she zaka shigo ne mu gana, ko sai amarya ta bayar da dama?
Yayi d'an jim bai son ta gano wacece matarsa da irin zaman da yake yi domin yana ganin wani abu ne da ya shafi rayuwarsa, don haka cikin zolaya yace mata "eh ki bari sai na nemi izininta tukunna. Ai kuwa ta k'uta kwarai da abin da ya fad'a amma da yake 'yar siyasace sai ta basar tana fad'in "shike nan, idan ta bayar da dama sai azo a ganni ko? "Kar ki damu, zan zo soon. Ya bata amsa, sannan ya nemi zai kirata anjima, domin yaga ga kiran sunusi ya fara shigowa, ba domin taso bata kashe wayar,
(33) domin zatonta ko amaryarsa ce ta fito shi ya sanya ya nemi kashe kiranta. Yana kashewa ya kira sunusi, daga can 6angaran sunusi ya fashe da dariya yana tsokanarsa. "Shegen sama kuma kai shike nan, ba a jin d'uriyarka, kace madam ta iya kiwo, komai zam-zam." ya 6ata ran wasa yana fad'in "kaga bana son shak'iyaci, da saka ido, kasan ni yanzu ba tsaranka bane ko? Ya kamata a dinga girmama manya. Sunusi ya fashe da dariya har da kwarewa, aliyu ya kashe wayar kawai yana dariya, ya k'arasa shiryawa ya nufi hanyar fita kai tsaye. Motarsa ce kawai a harabar gidan, yayi mamakin dalilin da ya sanya ba a kawowa hanan motar ta ba, bai san menene dalili ba, gashi kuma bai isa ya tambaya ba, ya shige motarsa bayan sun gaisa da maigadi da inusa yaron gidan ya tayar da motar. Daga can inda hanan take kwance akan gadonta tana chatting, ranta a 6ace, domin mansur yana ta mata magana amman ta kasa ce masa komai, don ta san illar da hakan zai mata, ta jiyo k'arar tashin mota, da sauri ta miki ta lek'a ta wundo,
Sai ta hango aliyu ne ke shirin fita, ranta ya k'ara 6aci, wato ita ya ajiye a gida shi zai fice yawonsa, tana tsaye har ya fice daga cikin gidan maigadi ya kullo k'ofa, ta koma ta zauna shiru damuwa tacika ta, ita fa yanzu ta zamto kamar ba mutum mai galihu ba, sag hawaye ya fara zubowa daga idonta, bata san ta ya y zata fara tinkarar aliyu ba, don tana ganin bai isa ta kula shi ba balle har tayi masa magana, duk da ya zama dole tayi wani abu wanda zai zama yana ta6a ransa wanda hakan ne zai bashi damar tanka mata, ta fara tinani abin da tasan aliyu ba yaso tun tasowarta cikgn rayuwarta. Tasan aliyu mutun ne mara son hayaniya da damuwa, sannan bai son irin shigar da take yi ta k'ananan kaya, lokcin tana yarinya ya kan yi mata fad'a ko ya kora ta gida akan ta sake kaya, akan hakan sun sha rikici da mahaifiyarta wanda watarana saida tayi masa gargad'i mai zafi bayan ta girma musamman lokacin data dawo daga k'asar waje idan tayi shigar baiy iya ko kallon ida take, wannan sune abubuwan daya kamata fara tak'ala
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(33) Wannan sune abubuwan da ya kamata ta fara takala domin 6akata ransa. Kai tsaye Aliyu Jiont d'insu ya wuce, duk sanda ya shiga gurin yana murnar ganin yanda suke ci gaba, basa rabo da maziyarta yan gayu, koda take suma suna k'ok'arin k'awata gurin kullum, ya gaisa da ma'aikats sannan ya wuce ofis d'insu ksi tsaye, bubu kowa gurin ma a kulle yake sai yayi amfani da mukullin hannunsa ya bude, ys shiga ya zauna ya fara duba computer d'in da suke ajiye lissafinsu. Bai jima ba saiga Sunusi ya shigo yana zolayarsa yana dariya "Kace kana hanya babban yaya, kaga yanda kayi wani frsh kuwa? Aliyu ya 6ats rai yana magana "Kags malam kar ka raina mini wayo, waye baban Yaya? "Au har ka manta abin da kace mini na dinga girmama manya yanzu? Aliyu ya fashe da dariya ya bashi hannun suka tafa suna dariya, Sunusi ya zauna a kusa da shi yana 'yar dariya. "Yaya Madam ne? Yayi dan yake bai son tuna komai "Tana nana lafiya. Yaya Joint d'in dai bubu wata matsala ko? Ya karasa maganar da sako wani zancen yanda zai manatar da Sunusi waccan maganar ta farko. "Gashi nan dai za ace, amman yanzu haka daga wani guri nake, daman ko baka zo ba zan kira ka a eaya. Aliyu ya gyara zama yana kallonsa "Ina jinka me yafaru? "Ina ganin bai kamata ace mun dogara ga wannan business d'in kawai ba, duk da akwai wani aiki da kake yi a gefe, amman ina ganin mu kalli future d'in mu a gaba, wannan gurin yayi ne, kuma lokacine, akwai lokacin da duk abinda muka yi ma saba zaiyi tashen da yake da yake yi yanz yanzuu ba, don haka nake gani me zai hana mu kama wani abun danban kuma? Aliyu ya gyd'a kai alamun gamsuwa da maganar sunusi sannan ya fara magana "Najima da wannan tinanin cikin raina sunusi, amma ka wace sa'a kake ganin zamu fara kenan?
"Yanzu haka daga gurin wani abokina Isma'il nake, tare mukai yi secondry dashi, bsi sami damar ci gaba da karatu ba sai yanzu yake yi part time, ssna'ar mahaifinsa ya gada siyar da taya, shine yake cemin daza a ssmi jari a hannuna koni da kaina na dinga shigo da tayar amma ta hannu wacce ake kawowa daga legas ba k'aramin samu za ayi ba, shima rashin jarine ya hannshi harkar, ya mini bayani akwai samu sosai a cikin harkar. Sliyu yayi shuru yana tinani sannan yace "Sunusi kasan sana'sr yanzu tana buk'atar jari, mu kuma ba wani kud'i ne damu a k'asa ba. "Haka ne, saidai yanda ya mini bayani idan muna da dubu dari bayar zamu iya farawa, na san kud'in da muke sarving sun kusa kaiwa d'i uku da wani abu yanzu haka, kaga akwai yuwuwar mu fara d'in ko? Aliyu ya gyad'a kai yana fad'in "Haka ne, nima akwai wasu kudi cikin accont dina, ina zaton sunkai kusand'ari biyu da hamsin, idan kun gama magana sai ka tuntu6eni muga yaya za ayi. Daga nan suka sauya darasin hira tasu da wata, duk yanda Sunusi yaso jin wani abu daga @6ngararn Aliyu akan zaman sa da Hanan bai samu damar hakan ba, don shi mutum ne me zurfin da k'okarin rik'e sirrinsa mutuk'a, sai wajan shad'ayAn dare sannan ya fara k'ok'arin barin gurin. Tun hanan tana zaune a falo tana jiransa, domin tayi d'amarar fara tsiyRta a daran yau, har bacci ya d'auke ta a kan kujera, yayi parking ya shigo palon bsta san yashigo ba, ya mayar da k'ofar ya rufe sai ya hangota kwance akan kujera, gabansa ya fad'di ya ya tsaya ya k'ura mata Ido ar
(34) kyar cikin wani irn yanayi da bai taba ganinta a haka ba, ya kasa d'auke idonsa daga kanta, har saida tayi d'an juyi kamar zata farka, sai yayi wuf ya nufi d'akinsa cikin sauri da damuwa. bayan ys shiga d'akin ya zauna shuru ysns tinanin yanayin dayaga Hanan, tabbas sai yau ya tabbatar da cikar surarta, wani irin abu kamar mayan k'arfe ya dinga fisgarsa, ammanl yasan bai isa ya k'arasata gareta ba, don hska ya shiga band'aki kawai ya d'auro alwala ya fara sallah. Hanan tana tsaka da bacci taji kamar ana tashinta, ta farka tana kallon agogon bango wanda yanuna k'arfe d'aya na dare, fargaba da mamaki suka cikata, tasan dai Aliyu ya shgo tini, domin ta k'ara tabbatarwa sai ta lek'a waje ta hango motarsa tana nan ajiye, taja dogon tsaki ta wuce d'akinta, bata san irin yanda yazo ya tararda ita ba, amman ai gobe ma rana ce ta ayyana cikin ranta. washegari bayan a dawo daga sallar Asuba yana kwance a kan gadonsa, bacci ya fara d'aukarshi irin baccin nan na safe mai dad'i, sai jiyo karar kid'a kamar a cikin kansa,, ya tashi firgigit cikin matuk'ar mamaki yana kalle-kalle, kai ya jiyo k'arar dsga babban falonsu take, don haka yanufi can kai tsaye. Abin daya bashi mamaki bai wuce ganin talabijin a kunne an kure sifiku dake gefen irin wanda ake kira da theater, ya isa ya kashe talabijin d'in domin bai son k'arar, sai dai sbin da ya k'ara bashi mamaki bai wuce ganin Hanan ta fito daga cikin d'aki da gaggawa kamar wacce ta manta wani abu ba, ba, da sauri. kai ye tsaye talabijin d'in ta k'ara kunna ta ta k'ure kid'an fiye dana farko, ya kalleta cikin mamaki, saiyaga ta nufi kujera ta zauna ta d'ora k'sfa d'aya kan d'aya tana karkard'awa, ya k'are mats kallo sanye da kayan bacci har lokacin, sai kawai ya kad'a kai ya nufi komawa ciki, sai dai bugun k'ofar da akeyi ya sanya shi dakatawa. . ya nufi k'ofar d'akin da gaggawa ya lek'a a, sai yaga Inusa nr, ya kalle shi cikin slamun tambaya, Inusa ya gaishe shi sannan ya fara magana.
35.
Inusa ya gaishe shi sannan ya fara magana.
Oga naji karar talabijin ta cika gidan ne nayi tsammanin ko ba kwa kusa ne.
Da gaggawa ya bashi amsa muna ciki jeka kawai karka damu.
Kallon da yaron ya masa kafin ya tafi ya dan bashi kunya, domin ya nuna masa kamar akwai matsala a karar,amma ya ya iya,ya koma ciki da gaggawa, kallo daya ya kara yiwa hanan tana kada kai tana bin wakar ya nufi dakinsa da gaggawa,abinda ya iya shine ya turo kofarsa ya rufe bam amma duk da haka yana cigaba da jiyo sautin kidan .
Ba haka taso ba taso ace ya biye mata ko yayi magana amma hakan ma ya mata dadi domin ya nuna mata ransa ya baci matuka.
Duk yanda yaso ya jure ya gaza, sai yaji kamar ya koma aikinsa, sai dai sati guda aka bashi hutu amma tabbas bazai iya zama cikin hayaniyar nan ba
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
36.
Amma tabbas bazai iya zama cikin hayaniyar nan ba sai kansa ya buga, dan haka da gaggawa ya shirya ya fice daga gidan, tana can dakinta bata ma san ya fita ba sai da taji karar motarsa, tayi tsaki cikin bacin rai sannan ta fito falon ta kashe.
Yayi ta yawo agari baisan inda yakamata ya nufa ba, yasan ko yaje joint dinsu yanzu basu bude ba, don haka sai yasamu waje ya ajiye motarsa ya kwantar da kujera ya kwanta kawai, ransa yaso ya baci domin ya kula kamar da gayya ta aikata masa abinda ta aikata din.
Bai koma gidan ba sai wajen sha biyu da rabi, sai da ya tsaya awani gidan abinci yaci ya koshi sannan ya nufi gida, yaji dadi sanda ya tsayar da motarsa yaji gidan shiru babu karar sautin, ya lallaba ya nufi cikin gidan sai dai abinda ya tayar masa da hankali yana kama kofar zai bude yaji sautin kidan ya karade gidan, ya tsaya shiru cikin damuwa, ya fuskanci sai yana gidan take kunna kidan, da zarar ya fita sai ta kashe ya jima yana sakawa da kwancewa ita kuwa tana zaune tana jiransa domin taji karar tsayuwar motarsa.
Yayi kamar ya koma da baya amma sai ya baiwa kansa wata shawara idan har hanan ta gano yana gujewa abinda ta fara yi masa to babu ranar da zata daina, gwara ya nuna mata bai damu ba watakila hakan zai sanya ta daina din, don haka ya bude kofar kawai ya shiga tana zaune akan kujera tana kallo amman da alama hankalinta ba akan kallon yake ba, domin sautin yayi yawa, ya samu guri ya zauna yana kallonta, sai yaji gabansa ya fara faduwa saboda shigar dake jikinta.
Ita kuwa abin mamaki ya bata, batason ko kallon inda yake amma ta tabbatar yana zaune yana kallonta sai taja dogon tsaki ta kawar da kanta, shi kuwa samun guri yayi ya zauna sosai , sai ma ya juya ya kwanta akan kujera ya kurawa talabijin din ido sosai yana kallo alamar film din yana birgeshi har ya fara ambata hakan a fili.
37.
Ta kalleshi cikin takaici kamar zata yi masa magana amma girman kai da ji da kanta da takeyi ya hanata, sai kawai ta mike da sauri ta kashe talabijin din tayi hanyar dakinta.
Ya bita da kallo cikin murmushi a fili kasan ransa kuwa wani irin faduwar gaba yakeji ya koma ya kwanta akan kujerar ya lumshe idonsa.
Wannan shine ya kawo karshen kunna masa kida da takeyi bayan haka babu komai daya taba shiga tsakaninsu koda gaisuwa kuwa.
ZAMAN YAN MARINA.
Zaman da sukeyi yafi kama da ka kirashi da zaman yan marina wato kowa da inda ya sanya gabansa don gaisuwa ko magana bata taba shiga tsakaninsu ba har akayi sati guda wannan abin ya fara damun Aliyu, domin yanayinsa ya sauya ya rame matuka, duk da yana kokarin boye damuwarsa amma ta bayyana akan fuskarsa.
Don haka ranar da yakamata ya koma aiki nayi ya dinga jin wani karsashi da dadi, da sassafe ya shirya ya fice daga gidan, sai dai zuciyarsa tana fada masa irin zaman da suke bai kamata ba, domin ko babu komai hanan a karkashinsa take ynzu, don haka tana da hakki akansa wanda yakamata ace ya sauke mata koda ita bata sauke nata hakkin dake kanta ba.
Ya zauna ya rubuta mata wasika mai layi uku a takadda ya hada da naira dubu biyu ya ajiye a tebur din falon ya dora remote akai ya tabbatar idan ta fito zata gani yayi ficewarsa.
Tana bacci kwata kwata batasan ya fita ba don haka koda ta farka tayi tsammanin yana gidan sai da ta kammala shirinta sannan ta fita falon sai ta hango takarda an dora remote da kudi akai, mamaki ya kamata da karasa ta dauka ta bude takardar ta fara karantawa.
38.
"Salam Hanan ya gida, yau na koma ofis, dan haka ga kudi nan ko akwai wani abu da zaki bukata, Aliyu".
Wannan shine abinda ya rubuta cikin takardar, wani malolo ya iso kirjinta ta tokare, me wannan gayen ke nufi, shi yanzu har yana da kudin da zai iya bata wai ko zatayi wani abu, taji kamar ta cinnawa kudin wuta amman hakan bazai huce mata takaicinta ba, ta nufi daki da gaggawa ta dauko biro da takarda ta bashi amsa ta nannade yadda ya ajiye agurin ta ajiye itama ta koma dakinta ta zauna tana huci.
Can ta dauko wayarta ta daddanna ta kara akunnenta a fusace tana jiran a daga.
Haj. bilkisu ta daga daga can bangaren tana magana Hanan ya akayi ne?
Momy gayen nan ya rainamin wayo, wai har ni zaice ya ajiyewa kudin cefane?
Tabbas kam wuyansa ya isa yanka, kome na sama ya ci balle ya baiwa na kasa, karki taba kudinsa domin kinfi karfinsu.
Ban taba ba ai momy, ta baiwa mahaifiyarta amsa.
Cikin damuwa haj bilkisu ta cigaba da magana
Yaya har yanzu babu wani cigaba ne Hanan? Kinga fa sati guda kenan fa, kinsan yaron nan idan ba kiyi da gaske ba bazai taba sakinki ba fa.
Damuwar hanan ta karu ta kada kai tana magana.
Wallahi momy ko kallo bai isheni ba balle yasamu wata magana mai dadi, sai dai na kula hakan bai taba damunsa ba, sabgarsa kawai yake yi, yau fa ban ma san ya fita ba, gaskiya na gaji da zaman nan ni ma yakamata na fara aiki a ofis din daddy gaskiya momy, sannan har yanzu ba,a kawomin motata ba bansan me daddy ke nufi da hakan ba.
Haj. Bilkisu ta kuma kufula tana magana.
Ki bar baban nan naki Hanan, yana shirin kasheni da raina, wai da na masa maganar kai miki motarki sai yace ba kya bukatar mota yanzu domin duk inda zaki mijinki zai kai ki tunda yana da abin hawa, idan lokacin da yakamata akai miki yayi ba sai na masa magana ba da kansa zai kai miki............
Momy wai haka daman yake nufi?Hanan ta katse mahaifiyarta cikin bacin rai tana magana.
39.
Hanan ta katse mahaifiyarta cikin bacin rai tana magana.
Anya kuwa daddy yana kaunata motar tawa ma bazai bani ba wallahi hakan bazai yiwu ba.........
Sai ta fashe da kukan takaici, haj. Bilkisu ta fara rarrashinta.
Kinga ya isa kiyi hakuri na gaya miki ki kwantar da hankalinki, da mun samu kin rabu da auren nan aai shikenan, mota dai a gidan mansur sai kin rasa wacce zaki hau, ki barshi yagama komai, kallonsa kawai nake, amma kinsan wani abu Hnan?
Cikin damuwa ta amsa da a,a momy.
Dolenki fa sai kin fara yiwa yaron nan magana koda kuwa zaginsa zkiyi, ni nafi so ma ki fara neman ya rabu da ke, idan kuma kina da wani abu da zakiyi ya fusata shi hakan nake bukata ni, haj. Bilkisu ta bukata.
Momy ni fa ko kallonsa bana son yi wallahi.
Hanan ta bata amsa cikin shagwaba.
To ya za,ayi dole ai sai kin rintse ido sannan zamu kai ga abinda muke son kaiwa, ki daure kinji ko?
Shikenan momy, ta baiwa mahaifiyarta amsa, sun jima suna sakawa da kwancewa akan maganar auren.
A can ofis Aliyu yayi kokarin ganinya nuna babu wani abu da yake damunsa, duk da kowa ya kalleshi yasan bai cikin cikakkiyar nutsuwa, sanda suka kebe da Alh. musa gabansa yayi ta faduwa, domin bai son yayi masa maganar Hanan ko yanayin zamansu kwata kwata, sai yayi sa,a baiyi masa din ba sai maganar aiki kawai sukayi suka bar maganar anan, haka ya cigaba da aikinsa har aka tashi daga aiki, sai dai yau ya dan sami sassaucin damuwa, domin ko babu komai yasamu abokan tattaunawa.
Bayan an tashi ya fara hada kayansa ya nufi motarsa yana kokarin shiga yaji an kira sunansa daga bayansa ko bai waiga ba yasan sirikinsa ne don haka cikin ladabi ya waiga yana amsawa.
Alh. musa ya karaso kusa da shi yana murmushi yana magana.
Ango duk ka rame kamar ba sabon ango ba? Abinda ya fara fada kenan, Aliyu ya sunkuyar da kansa kasa cikin ransa yana fadin shikenan an yanka ta tashi, amma sai yaji Alh, musa ya sauya magana da nasiha.
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
40.
Nasan zaka fuskanci matsala mai girma da Hanan a yanzu, amma idan kayi hakuri watarana komai zai wuce zai zama tarihi kaji ko?
Aliyu ya daga kai da sauri yana fadin.
Insha Allah baffa karka damu.
Alh. musa ya dafa kafadarsa yana dan jijjigawa alamar jinjina, Nagode Aliyu.
Kafin Aliyu ya kara yin magana ya nufi motarsa da sauri ya shige, Aliyu ya danyi jim cikin damuwa, ya jima bai ga mutum irin Alh. musa ba cikin rayuwarsa.
Bayan ya isa gida abinda ya fara cin karo da shi a falon gidan shine kudin daya ajiye, mamaki ya kamashi, domin yasan indai ta fito falon nan dole zata ga kudin, amma takardar daya bari sai yaga ba ita bace ba, hakan ya bashi damar daukar sabuwar domin yaga menene a ciki, ya

Please Login or Register in order to submit comment