Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata.
"Macuci azzalimi! Ban yafe maka ba, fyad'e zaka mini eye!
Yanda take maganar da kukan datake yi ya tayar da hankalinsa matuk'a, ya fara k'okarin bata hakuri, amma bata kula shi ba ta shige d'akinta da gudu tana cigaba da kuka. Aliyu ya zauna shiru akan kujera ya dafe kansa cikin damuwa, tabbas shigewa hanan da yake yi shine ya haifar masa da wannan matsalar, domin yawan ganin ta cikin shigar datake yi babbar matsala ce gare shi. Ya kamta ya k'aurace mata, tabbas idan har yana ganinta gabansa komai zai iya faruwa, don iyakacin hak'urin dazai iya akanta ya k'are, sai yaji hawayen tausayin kansa na zubo masa, ya jima da gane ya fara son maso wani da hausawa kecewa k'oshin wahala. Hanan data shiga d'aki ta fad'a gado tayi shiru tinani, ba ta ta6a yi mata irin abin da Aliyu yayi mata ba, mansur yayi mata wani abu amman ba irin wannan bane, ta dinga tuno abin cikin ranta, tana son ta mantawa ta kasa, sai dai tana ganin kamar taci
(49)
Amanar Mansur k'arara, don haka ta nufi band'aki da sauri tana ta wanke bakinta, ta kasa daina jin da sauri tana ta wanke bakinta, ta kasa daina jin abin da aliyu yayi mata cikin bakinta, tana jin kamar yana amfani da abin da ake kira man kamshin baki, koma daimenene ta tabbatar ya cuceta kawai, domin ta kwana cikin damuwar abin daya faru gareta.
A 6angaran Aliyu abin daya faru ya k'ara haddasa masa wata wutar gobarar soyayyar hanan cikin ransa, sai dai yana mamakin kan sa da dalilin dayasa ya aikata hakan, shi ba halin sa bane hak'ewa mace, da-dai ne abin da ta fad'a nazai yi mata fyad'e, ya kasa goguwa cikin zuciyarsa. Washegari daya tashi sai yaji yana jin kunyar hanan, don haka bai iya zuwa d'akinta ba ya bar mata sak'on takadda ya wuce kawai, tayi alk'awarin ta daina karanta sak'nsa don haka ko daya ajiye sai ta d'auk'a kawai ta wurga shara, domin haushin sa take ji a yanzu.
Maigadi da insu sun fuskanci irin zaman da iyayan gidansu keyi, musamman inusa wanda da yake kusa da hanan,
Domin shitake aike ko ina idan tana buk'atar wani abu, amma fad'an daya fi k'arfin ka sai ka mayar dashi wasa inji masu iya magana. Sun yi kwanaki uku a haka, cikin na hud'u wanda ya kasance ranakun hutu yayi shirin tafiya ganin iyayansa, bai san hanan bata karanta abin daya rabuta mata ba, don haka ya ajiye sak'on ya tafi ne kawai ba tare da yasanar da ita ba.
Inusa ne ya taya shi shigar da kayansa cikin mota, yayi sallama dasu ya wuce, ya cika motarsa da tsaraba ya nufi k'auyansu, a 6angaran hanan ta cika mak'il yau tayi niyyar amayar da abin dake ranta na rashin mutunci ga aliyu, domin tasan dole yau zai zauna a gidan tunda babu aiki, sai dai har rana ta fito bataga gilmawarsa ba, ta dinga jin kamar ta shiga har d'akinsa ta k'are masa, sai dai zuciyarta ta bata shawarar kar ta shiga tace ci gaba da jiran ya fito ne. Har dare yayi babu alamunsa, hankalinta ya d'an fara tashi akan rashin ganinsa, sai kuma a lokacin taga dacewar ta karanta takardar daya bari taji ko menne a ciki, ta nufi shara da sauri,
(50)
Kusan duka takaddun da ta yadda ta d'auko ta fara karantawa, data farko tafara wacce ya fara bata hak'uri akan abin daya faru, saitaji wani irin cikin ranta, sai kuma ta yau data tayar mata da hankali, domin tunda take bata ta6a kwana a gidan ita d'aya ba, yau gashi zata kwana, sai taji kamar ta fasa kuka da ihu, saboda tana da tsoro matuk'a. Taji kamar tace Inusa ya shigo ya kwana a falo, amma hakan bai kamata ba, ta hak'ura ta shige d'aki da gaggawa ta kullo k'ofar d'akin, ta shige cikin bargo, sai a yaune ta gano zaman aliyu a cikin gidan yana da amfani.
Sumaye da mal. Beld'o sa sun yi murna da zuwansa, musamman da yake yaje musu da tsarabar daya saba, kamar kullum sun jima suna hira da mahaifiyarsa cikin d'akinta tana masa tambayoyi kala-kala, har tazo kan wacce ta bashi mamakin da ya kasa amsawa.
"Maisango anya kuwa matar nan taka tana k'aunar ka, ban ta6a jin ko da muryarta ba, bata ta6a tinanin ta gayar dani ko sau d'aya ba, tabbas na kula akwai wani abu dake boye mini maisango."
Yayi shiru cikin damuwa, kansa yana k'asa, ya san halin mahaifiyarsa macece mai tinani da sauri gano abubuwa, ya sanya gaji abubuwa da dama a gurinta, maganar ya 6oye mata wani abu game da auransa ma bai taso ba, sai dai ba komai zai iya gaya mata ba, ya gyara zama yana tinanin ta ina ya kamata ya fara. Ta k'ura masa ido kawai tana jiran jin abin da zai fad'a, ya d'aga ido ya kalleta cikin damuwa sannan ya fara maga. "Inna banine wanda hanan take k'auna ba, tana da saurayin da suka jima suna soyayya, ni na d'auketa a matsayin k'anwata ya gano wanda take so d'in bai kamata ta aure shi ba, yaro ne dan masu hali, sai ya bani umarnin auran hanan, tun kafin ayi auran bata so na, har zuwa yanzu da aka yi, amma ima ta k'ok'arin ganin ta hak'ura ta amince dani inna..." yayi shiru domin bai san me zai k'ara akai ba kuma, sumaye ta gyad'a kai tana fad'in. "na san za a rina, amman abin da nake roko agareka shi ne ka rik'e yarinyar nan da amana, doke zaka fuskanci damuwa, amman ka dinga tuna abin da mahaifinta yayi
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(51)
Maka a duk lokacin data yi maka wani laifi. Tayi d'an jim sannan ta k'ara kallonsa cikin zargiri" ina son kaga ya mini tsakani da Allah kana son hanan maisango?
Ya kalli mahaifiyarsa maganar ta bashi dariya, yana magana cikin murmushi. "Inna kinga wani abu ne da yayi kama da hakan? Cikin dariya take magana itama "eh mana, tun da kazo kana tayin maganarta, har kana cewa, hanan d'in tana kama da autata maryama ko ba haka ba?
Aliyu ya sosa k'eya yana dariya "kai inna, nace dai kawai zan tafi da maryam din kice..." da gaggawa ta d'aga hannu "a'a bazan baka d'iyata ba sam, gwara ma kar ka saka rai. Tana magana tana dariya, daga nan suka sauya wata hirar, hirar yawanci ta danginsu da 'yau'uwansa, sai da suka raba dare suna hira sannan ya nufi inda yake kwanciya, d'akine da ya gyara shi musamman saboda saukarsa, domin bai son ya dinga kwana a d'akin babansa kona k'annensa.
Washegari ma bai yi shirin tafiya ba sai yamma, idan yazo garin bai son rabuwa da mahaifiyarsa da 'yan uwansa, musamman idan aka had'u
Ana hira, wannan abun shike tayarwa da lanto hankali, duk da yanzu ta hak'ura ta fara zubar da makaman yak'in ta, saboda yanda aliyu ya yayiwa yaranta nisa, kuma suna gaya mata irin taimakon da yake musu acan.
Lokacin da ya shirya zai tafi ne Abubakar ya fito daga d'akinsa d'auke da kayan sa wai tare zasu tafi, domin yana son ya fara karatun boko shima, mahaifinsa ya goya masa baya da hakan, aliyu bai shiryawa tafiyar ba, amma babu yanda ya iya dole ya amince yace su tafi d'in, mahaifiyarsa ta fuskanci hakan a tattare da shi, sai dai bata damar yin magana domin mahaifinsa ya ringa ya yanke hukunci, don haka suka yi sallama kawai. Aliyu ya cikasu da alkairin ya daya saba, har da lanto suka wuce cikin mota.
Hanan bata raina kanta ba sai da aliyu bata gidan, ta tabbatar tana cikin matsala yau, da kasa bacci tayi, sai dai bacci 6arawo da ya d'auke ta, yau kam har kuka tayi da taga k'arfe tara ta wuce bai dawo gidan ba, gashi ita ba lambar wayarsa ne da ita ba balle taji ko zai dawo yau, ko tana da ita d'in ma
(52)
Bazata iya kiransa ba, ta shige d'aki ta dinga kuka, tana jin kamar ta kira mahaifiyarta ta gaya mata abin dake furuwa, amman ta gaza, sai kawai ta kudundune kamar jiya. Tana cikin bargo taji kamar alamar mota ta shigo gidan, ta mik'e cikin sauri tana lek'a wundon, sai ta hango aliyu ne ke k'ok'arin tsayar da motar, tayi ajiyar zuciya cikin jin dad'in abin da ya faru, ta koma ta zauna a gefen gadonta tana yuwa kanta dariya. Aliyu kai tsaye sashin bak'i ya kai Abubakar, ya siya masa abinci sannan sun biya gurin jiont d'in su ya amsar masa abubuwan sha da snack, ya nuna masa komai da yanda zai yi amfani dashi, abubakar yayi murna matuk'a, domin dasu akazo d'aurin aure, yaji dad'in zaman gurin nan, gashi yanzu zama na shi d'aya, cikin farin ciki yake. Aliyu ya nufi cikin gida kai tsayd bayan yagama da abubakar, Yana shiga falon yayi ajiyar zuciya cikin jin dad'i, sai yaji kamar ya shiga aljanna, ya tabbatar gidan nan yanzu ya zamto cikin jikinsa da 6angaransa gaba d'aya, ya cire takalminsa ya nufi d'akinsa
Kai tsaye, sai yaji ya kamata ya duba hanan yaga halin datake ciki, domin sai bayan ya tafi ya gano yayi kuskure da bai amshi lambar wayarta koda a gurin wani bane, don bai kamata ace har ya kwana baffansa ya kamata ya amsa, amman da kunya ya kira shi yace masa ya bashi lambar matarsa, matar da suka jima guri d'aya tare.
Ya tura k'ofar ya shiga, tana gefen gado a zaune, da kyar ta iya amsa sallamar da yayi ta k'ara kwar da kanta, yaji wani farin ciki ya sauka a zuciyarsa saboda ganin fuskarta kawai, yayi d'an murmushi yana mata magana.
"Barka da gida hajiya, kiyi hak'uri bani da lambarki ne shi ya sanya ban kira ba... "Kaga don Allah fita kabani guri! Ta fad'a cikin gatsali, maganar ta masa ciwo, sai dai ya nunu bai damu ba, yaci gaba da magana. "kar ki damu, yanzu zan fita, ina son tabbatar da lafiyarki k'alaune, Allah ya tashi mu lafiya. Ya fice da gaggawa ta bishi da tsaki gami da yarfa masa magana "iska tana wahalar da mai kayan kara." ta juya ta kwanta akan gado, a ranta tabbas taji dad'in dawowarsa,
(53)
Domin yau zata yi bacci cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
Da safe aliyu ya shirya yayi shirin fita, sai yaga dacewar ya gabatar da abubakar ga hanan, bai kamata ace yana gidan basu san juna ba, koda me zata yi masa ya kamata tasan da wani a gidan, don haka ya isa d'akinta yana kwankwasa mata k'ofa, ko kulashi bata yi balle ta bud'e, yana jin motsinta abin da ya tabbatar masa tana cikin d'akin. Don haka ya fara magana daga inda yake tsaye "daman ina son sanar dake muna da bak'o ne, jiya dana je garinmu na taho da k'anina, so zai iya taimaka miki idan kina buk'atar wani abu.
Bata kulashi ba har yagama suruntansa ya wuce, taja tsaki kawai cikin ranta tana fad'in, haka dai za a cika mini gida da 'yan k'auye.
Sai wajan k'arfe goma ta fito falo ta zauna, bayan ta samarwa kanta abin dazata ci, abubakar ya shigo falon yana sallama, abin da ya baiwa hanan mamaki bai wuce ganin matashin saurayin ya durk'usa har k'asa yana gayar da ita ba, ya burgeta kwarai da gaske, gata daman da son girma,
Sai ta amsa cikin sakin fuska, har ta d'ora da tambayarsa ya sami abinci kuwa yaci, yace mata akwai sauran wanda yayansa ya rage masa, amman sai tace bari ta kawo masa sauran wanda ta rage na karin safe, ta kawo masa yana tambayarta ko da wani abu da zai yi mata, abin da tafi buk'ata a yanzu shine wankin kayanta, domin bata da wani mai aikin dazai yi mata, domin bata yadda da tsaftar inusa ba, don haka takasa bashi wankin ta, ta tambayarshi ya iya wanki da guga, da sauri ya amsa mata da eh ya iya, taje ta had'o masa.
Kafin aliyu ya dawo
Abubakar yayi mata wanki da gugarta, abin da ya kara burgeta da shi shine yanda ya saki jiki da ita, babu wanda zai yi tsammanin daga k'auye ya fito, domin ya san komai na rayuwa, koda yake ya gaya mata shi yana jin rediyo sosai, sannan ta kula shi d'an gayu ne gashi kykyakwa, domin nesa ba kusa ba yafi aliyu kyau don haka cikin k'ank'anin lokaci suka saba, sai taji ta sami abokin hira domin ta gaji da zaman gidan daman ita d'aya. Lokacin da Aliyu ya dawo da takeaway
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(54) a hannunsa ya nufi d'akin abobakar ya tarar da shi yana kallo ya mik'a masa abin da ya siyo, gami da wayancewa da cewar matar gidan bata jin dad'i ne shi ya sanya ba zai samu abinci yanzu ba sai an kwana biyu, sai yaji yaron yana sanar da shi ai ta bashi abinci yaci ya k'oshi, mamaki ya kama aliyu ya fara tambayarsa yaya aka yi, ya sanar da shi komai, ran aliyu yayi fari, domin yaji dad'in hakan data yi masa. Zuwan abubakar ya sanya aliyu sake salon ajiyewa hanan kud'in cefane, domin yanzu ta hak'ura tana d'auka, domin kud'in hannunta sun k'are, gashi ba ta isa ta tambayi babanta ba, data yi masa waya tana buk'ata kud'i sai yace tambayi mijinta, domin shine ya kamata yabata kud'i, a ranar ya yiwa aliyu kyautar kudi a ofis a zaton shi ko ba shi da kudi ne. Kyautar ta bai baiwa aliyu mamaki, amman daya ke alh. Musa kamar uaba yake gurin aliyu ya gaya masa dalilin kyautar, kunya ta cika aliyu, don haka bayan ya koma gida har d'aki ya same ta. Kamar yanda tasaba daga amsa sallama bata k'ara ce masa komai
Hakan tayi masa, yabi ta da kallo tana shafa mai a gaban madubi, tsigar jikinsa ta dinga ta shi, amma ya san ko ya yafi kuturu naci nan gani nan bari, don haka ya fara fad'in abin daya kawo shi. "Hanan ban ji dad'i dakika tambayi baffa kud'i ba, don Allah duk abin da kike buk'ata ki tambaye ni, idan ma bazaki tambaya ba, k'ofar d'akina a bud'e yake, kawai loka da zaki jawo ta bud'e side ki d'auki abin da kike buk'ata. Har yagama bata tanka masa ba, ya ajiye mata dubu gamsin, cikin kud'in da mahaifinta ya bashi dubu d'ari, ya sakai ya fice, ya ga alamar kamar ta yadda. Yana fita ta d'auki kud'in tana surutai, wai kud'in ubanta ne ko taci babu abin kunya. Tun daga wannan lokacin ya koma ajiye mata kudin cikin d'akin ta idan ya shigo ganinta da safe maimako dubu biyu sai yake ajiye mata dubu uku, sannan yana yi mata ta cefane da siyayyar komai ya sanya a firji da sito. Ba a jima ba abubakar ya zamto d'an aiken hanan, da farko tana had'a shi da inusa ne, daga k'arshe daya san gari shi kad'ai ma yake zuwa.
(55)
Duk inda take son aikenshi zaije, domin yaro shi wayayye, daga maigadi har hanan suna jin dad'in zamansa cikin gidan, domin sun sami abokin tattaunawa, a 6angaran aliyu yana ta k'ok'arin samar masa makarantane da zai d'ora karatunsa, ya sami wani malam a SAS sun gama magana yace akaishi yayi masa intervew ya gani, cikin sa a ana yi akaga dacewar saka shi aji biyar na makarantar gaba da sakandire, domin ya haddace kur'ani zuwa yanzu, da wasu littattafan, ga shi ya iya rubutun boko da karatunsa, hakan ya faranta ran aliyu matuk'a.
Matar sabi'u da matar auwal sun damu akan son zuwa gidan aliyu, daga k'arshe dai suka had'o kai suka taho gidan dayake tun biki sun san gidan. Da farko hanan bata gane su ba, sai daga baya da suka yi mata bayani, ta amshe su hannu biyu, domin suma cikin mutuntawa suka gayar da ita, ta kira abubakar ya siyo musu lemo domin na gidan lokacin ya k'are. Bayan da dawo suka zauna tare suna ta hira, da yake hanan tana neman 'yan hira ya sanya taji dad'in zuwansu, anan suka wuni,
Su kuma yanda suka wuni ci wancan ci wancan ne ya zaunar dasu, dazasu tafi ta had'a musu goma ta arzik'i, har da sabbin atamfofi turmi biyu-biyu, domin yanayinsu ya bata tausayi ganin kayan jikinsu, ga shi kowacce da k'aramin goyo ba kula, sannan tabasu kyautar dubu biyar-biyar, wannan abin c k'aramin dad'i ya musu ba, suka tafi suna ta godiya. Aliyu bai san da zuwan su c kwata kwata, sai da yayyan nasa suka kira shi d'aya bayan d'aya suna masa godiya, mamaki ya kamashi, amman ya amsa musu dato kawai, bayan sun gama waya ya nufi d'akin Abubakar. Ya tarar dashi yana karatu, ya fara tambayar sa ya akan zuwan matan yayyan nasa, abubakar yayi masa bayanin komai, dad'i yaci ka ran aliyu, tabbas hanan bata k'aunar sa yasani, sai dai yanda take mutunta 'yan'uwansa ya sanya tasami daraja mai girma a gurinsa, ya kuma gono ko shi datake wulak'antawa saboda d'abi'ace da babar ta d'ora ta akai, amman akwai jinin tausayi a jikin ta irin na mahaifinta.
KWANAKI SUN JA
Kanaki sun ja har watanni biyar sun wuce babu wani abu
(56)
Da ya faru da hanan ke fata, kullum mahaifiyarta cikin hura mata wuta take yi, sai dai tana mata bayanin halin da ake ciki. Don tun ranar da abin nan ya faru bata k'ara k'ok'arin kiran wayar mansur a gaban aliyu ba, daman randa ta kira ma k'arya ta kira salon ta 6ata masa rai, sai dai ta kula hakan ya kusa kaitaga dani sani don haka ta sake taku, babu abin da bata yiwa aliyu ba amma a banza, yanzu ko kulata ma ya dai na yi, sabgar gabansa kawai yakeyi, ta kuma kasa cire maganar mansur cikin ranta. Yau tayi manyan bak'i domin k'awayanta ne suka yi mata waya yau zasu zo su wunar mata, taji dad'in hakan domin tajima rabonta dasu, dukkansu basu san da magar auranta ba, sai bayan anyi sannan sukaji, sun kirata suna yi mata ciwon bakin ta sanar dasu bafa son auran take yi ba, don tana neman hanyar da zai 6alle ne ma, kasancewar Fadila ce babbar k'awarta kuma bata gari, sai cikin satin ta dawo daga inda take karatu, ta had'o kan k'awayan kowa mata ziyara. Lokacin da suka shigo suka dinga ihu da tsallen murnar
Had'uwa da juna, domin su biyu basu k'asar ma cikin satin suka dawo, aka zauna aka fara hira cikin jin dad'i da walwala. Fadila ce ta fara tambayar hanan cikin mamaki "k'awata don Allah da gaske ko da wasa kike mana, nifa sanda kika sanar dani a waya wai ba man kika aura ba najima ina mamaki, na dinga jin kamar na zama tsuntsuwa na dawo naga ni, garin yaya kika amince da hakan, waye ne kika aura ne ma? Hanan ta 6ata fuska sun ta6o mata abin dake mata k'aik'ayi, ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar dasu cikin takaici.
Fadila ta kuma zaro ido cikin mamki tana fad'in "ba dai gayen nan da kika cewa almajirn gidanku aka aura miki ba?
Hanan ta k'uta kamar zatayi kuka tana fad'in "shifa, ai daddy ya gama dani, amma ina kan hanyar mayar da rayuwata yanda take a baya." zahra'u ta tambaya da sauri "kamar yaya? Hanan ta kalle ta tana bata amsa "kamar ta auran man dina mana, wannan shine kawai burina. Suka fashe da dariya sannan suka ci gaba da hira, hanan ta kira abubakar domin ya siyo musu snacks,
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(57) Domin yasan duk wani gurin masu kayan dad'in da take siya, suka ci gaba da hira cikin jin dad'i. Bayan Abubakar ya shigo ya gaishesu ya amshi sak'on ya fice, suka bishi da kallo, Amina ta d'an
ta dan ta6a cinyar hanan kin gulma. "wannan kuma kyak-kyawan matashin inakika samo shi k'awata? Hanan ta ta6e baki "k'aninsa ne, daga k'auyensu ya kawo shi... zahra'u ta katse ta da gaggawa "wai kina
nufin had'ad'd'an yaron nan d'an k'auye ne, babu alama, ni wallahi ya burgeni matuk'a, daya kai shekaruna ai dana shiga daga ciki. suka yi dariya suka tafa suna shewa. fadila ta kalli k'awayan tana
magana. "ai abin da baku sani ba, mijin da take kushewar kamar su d'aya da wannan din, kai yama fi wannan had'uwa, shi fa yanda kasan twince brother dinta haka suke. hanan ta d'aka mata duka a cinya,
ta fasa ihu suna dariyar tsokana. "Allah....idan kika bari na sanar da man yankan k'aunar da kike masa zai daina kuka ki, ko chatting dinki zai dai na replying. Fadila ta ta6e fuska "tosai me, wallahi
k'awata ina baki shawarar zama da mijinki, a zamanin nan ba kowacce mace ke sa'ar samun mijin irin haka ba. Hanan ta k'ara 6ata fuska "don Allah kar ki 6ata mini rai Fadila. Fadila ta d'aga hannu.
(58) "Shike nan Allah ya baki hak'uri. sai suka sauya wata hirar, suna ta tuna baya suna shewa cikin jin dad'i, aka turo k'ofar falon aka shigo Aliyu ya d'an tsaya turus yana kallonsu cikin mamaki,
sai ya fara yak'e. "kuyi hakuri ban san da muna da bak'i ba, sannunku da zuwa. gabad'aya suka amsa da amin, ya fara k'ok'arin cire takalminsa, suka dinga satar kallonsa, ranar yayi shigar k'ananan
kaya ne, jeans a jikinsa, sai shet mai dogon hannu, ya gyara kansa sai walk'iya yake yi, akwai jakar brifcase rik'e a hannunsa. ya gama cire takalimin ya k'arasa ya zauna a jujera yana kallonsu yan
Yana kallonsu yana dan murmushi, Hanan sai tsaki take tana kawar da kanta, bai kula da hakan ba yafar gaisawa dasu. mutun d'aya yasani a cikinsu Fadila donhaka ita kawai ya ambata, bayan sun gama
gaisawa ya mik'e ya nufi d'akinsa, suka k'ara binsa da kallo cikn mamaki baki bud'e, yana shigewa, Zahra'u ta matso cikin gulma tana k'asa da murya. "Hanan wai wannan ne kike cewa an miki auran dole
da shi don Allah? Fadila ta ta6e baki "shine, don Allah menene makusa a jikin gayen nan, mutum kamar shi yayi kansa. Zahrau ta banka zagi tana wani dafe k'irji tana kallon hanan. billahillazi ina mai
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(59)
Billahillazi Ina Mai Tabbatar Miki. Idan Kika Bari Gayan Nan Ya Kubuce Miki Kin Yi Asara. Kinaganin Mutum A Tsaye Cikakken Namiji. Wallahi Wannan Yafi Manj 'Dinki K6ai. Sai Dai Ya Nuuna Masa Fari Da Kud'i Kawai...
Aimana Ma Ta Amshe "tabbas Gayen Nan Ya Had'u. Ni Irinsa nake Nema Ruwa Ajallo. Ina Ma Ace Na Sami Miji Kamar Wa6an? Hanan Ta K'ara Kufula Ganin Yanda K'awayanta Suka Rud'e Gaba 'Daya. Cikin Bacin Rai Tafara Magana,
"ai Sai Kije Kigaya Masa Kina Son Sa Aimana. Ni Kuwa Kinga Ko A K'afa Aka D'aura Mini Shi Zan Yakice Na Yadda. Wallah Kun Bani Mamaki. Gabad'aya Idonku Ya Rufe. Kun Mata Waye Man. Kun Manta Irinj Had'uwarsa. Ko Makoho Ya Shafa Yasan Akwai Banbanci Tsakanin Wannan Mutumin Da Mamn 'Dina, Fadila Ta Amshe "tabbas Akwai Banbanci. Wallahi Soyayya Ce Kawai Ta Rufe Miki Ido. Amman Wannan Shine Right Husban 'din Ki Hanan. Kin Sanj Halin Man... Hanan Ta d'aga Mata Hannu "idan Har Kun Zo Domin Ku 6ata Mini Raine Ya Isa Haka. Nayi Iyakacin Hak'uri Da Zanyi Fa,
Sun Kula Ta K'ulu, Idota Kuma
Ya Rufe Da Mansur Don Haka Suka Bata Hakuri Suka Cigaba Da Wata Hirar, Amma Dukkansu Hankalinsu Yana Kanj K'ofar D'akin Aliyu. Ana Kiran Sallah Sai Gashi Yaa Fito Sanye Da Dagowar Riga. Ya K'ara Gaisuwa Dasu Sannan Ya Fice. Suka Bishi Da Kallo Cikin Ajiyar Zuciya. Hanan Ta K'ara K'ulawa,
"wai Menene Haka Don Allah? Zahra'u Ta Amshe Da Sauri "sorry K'awa Kawai Ina Son Gano Makusa Jikin Gayan Nan Ne, Hanan Taja Tsaki Bata Yi Magana Ba, A Daddafe Ta Biye Musu Suka Cigab Da Hira Har Suka Yi Sallama Suka Tafi, Bayan Tafiyarsu Ta Shige 'daki Tana Kaiwa Da Komowa Cikin Takaici, Bata San Me Mutane Suke Gani Jikin Aliyu Da Yake Burgesu Ba, Ko Domin Basu San Shi Ba Tun Farko, Ita Kam Tasan Kowaye Shi. Ta Kuma San Asalinsa, Dabata San Shi Ba Shine Zai Iya Rud'arta Da Abubuwa Da Suke Fad'a. Sai Take Jin Haushi Da Takaicinsa Yana K'ara Shigarta, Domin Ta Kula Mutane Suna Neman Su Raba Mata Hankali Biyu Akansa,

Please Login or Register in order to submit comment