Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bude ya fara karantawa.
Kai har kana da arzikin da zaka iya ciyar da ni, ka sani banzo gidanka da sunan zama ba, gwara ma ka sake lale!.
Wannan shine abinda aka rubuta jikin takardar, da harshen turanci tayi rubutun.
Ya tsaya shiru cikin damuwa yana karewa takardar kallo, sai ya mayar da ita ya ajiye kawai, bai taba kudin ba ya barsu nan, cikin ransa yana jin ciwo mai zafi, yaushe zai samu girma da daraja ne a wajen Hanan, wannan tunanin shine yayi masa jagora a daran har zuwa baccinsa.
Kwanaki sukayi ta ja kullum sai Aliyu ya ajiye mata dubu 2 ita kuma bata tabawa har kudin suka taru da yawa a gurin, a ranta tana mamakin taurin rai da karfin hali irin na Aliyu, yayin da shi kuma yake jinjinawa girman kai da isarta.
Ya saba da cin abincin hotal da rabin rayuwa awaje musamman a joint dinsu, sunusi bai cika damunsa da sanin komai nasa ba, tunda bai sanar dashi ba shima bai damu da lallai sai ya sani ba, sai dai zuwa wannan lokacin shakuwarsu da fa,iza tayi nisa sosai, bata shakkar kiransa a waya kowanne lokaci, domin bai taba hanata ba, takasa gane irin zaman auren da yakeyi da matarsa.
41.
Amma bata da fuskar tambayarsa, sai dai tana ji kamar matar tasa ba wayayyiya bace, duk da ba wata magana data taba shiga tsakaninta da shi na matarsa, duk sanda ta sako maganar iyalinsa zai sauya hirar, idan ta matsa ma sai yayi fushi don haka ta tattara ta watsar da maganar kamar yadda taga yafi bukata.
Yau ya dawo da wasu kasuna masu kyau daya siyo, bayan yagama abinda zaiyi ya dawo falon ya zauna ya fara kokarin kunna kayan kallo, sai dai abinda ya bashi mamaki bai wuce ganin babu kudin nan akan tebur din da suke tara su ba, ya tsaya shiru yana kallon tebur din cikin fargaba, amma sai ya share ya koma ya zauna ya fara kallonsa, yana zama wayarsa tayi kara, kiran fa,iza ne dan haka da gaggawa ya daga cikin murmushi.
Haba hajiya nayi fishi, yau kwana da yini kenan fa baki kirani ba.
Daga bangaren fa,iza tayi murmushi kamar yana ganinta tana fadin.
Wallahi baka da dama Aliyu wato ni banyi fushi ba sai kai tunda muke ka taba kirana? Idan zamu shekara ban kira ba fa bazaka kirani ba, shikenan ni ban iya fushi ba sai kai ko?
Yayi yar dariya irin ta mazan duniya yana fadin, kuma fa hakane tuba nake, yanzun dai yaya kike ya su momy?
Sunanan lafiya kullum sakonta a gaisheka, ina fatan dai kananan lafiya?
Lafiya lau, yaya aiki da komai da komai, ina missing muryarki fa......
Ta fashe da dariya har ya tayata cikin kwarkwasa ta tambayeshi Like seriously?
Eh mana, kin san ban fadin abinda bashi naji a cikin raina ba, na saba da muryarki da gaske nake, kawai bansan maiyasa bana kiranki ba........
Dai dai lokacin hanan ta fito daga cikin daki a fusace tana huci akwai kudi a hannunta dami guda, ta kalleshi cikin takaici da bakin ciki da sauri yayi magana.
Zan kiraki anjima fa,iza, ya kashe wayar kafin ta bashi amsa.
Ran fa,iza yadan sosu ta fara kula idan matarsa ta iso kusa da shi ne yake sauri ya kashe wayarta kafin suyi sallama.
(42)
Hanan tana jin zafin wannan halin dayake mata, domin tana ganin kamar wani izgigalanci ne, da zai zauna yana waya da mata a falonta, amman yanzu kam ba wannan ne ya kawo ta ba, don haka ta fara aiwatar da abin da ya kawota, kudin dake hannunta ta watsa masa a fuskarsa, kud'in suka zube a jikinsa da tsakiyar d'akin, ya kalleta cikin mamaki, karon farko da zai fara yi mata magana kenan. "kina da hankali hanan, yaya zaki dinga watsar da kud'i haka?
Ta dalla masa harara cikin 6acin rai "ina son nuna maka kai suka dama ne, domin ni kasan d'iyar arzik'ice a cikinsu na tashi, don haka baka da kud'in da zaka burgeni dasu, don haka ina gargad'inka daga yau ka daina 6ata mini falo da wasu k'azaman canjin ka, sannan ka sanya a ranka ba wai nazo zama gidan nan bane, lokacina na gab da cika! Tajiya da gaggawa tabar gurin ya bita da kallo, maganganunta masu zafi a gurinsa amman babu yanda zai yi, kamar yanda mahaifinta ya buk'aci ya k'ara hak'uri shine kawai abin da zaici gaba dayi, don haka ya tsugunna ya fara
Tattara kud'in yana tarawa guri guda, amman cikin ransa akwai abin da bai sauya ba. Washegari da safe da ya tashi ya ajiye mata kud'in kamar yanda ya saba ajiyewa da takardar sak'o ya fice abinsa, tana tashi kamar kullum taci karo da kud'in yau har da k'arin takarda, takaici ya cikata, bata ta6a ganin mutum irin Aliy ba, a fusace ta fara d'aukar takardar tana karantawa.
"Kamar yanda kika fad'a tabbas haka ne, na san bani da kud'in da zan iya baki, sai dai ki sani shi aure yafi komai daraja, don haka ko da kin fi kowa arzk'iki a wannan duniyar ni ne dai mijinki, ni ne zan ciyar dake, don haka ki d'auk'a abin dana ke yi ba, a'a ina yi domin sauke nauyin ki da yake kaina."
Ta jima bata karanta sak'on daya k'ona mata rai kamar wannan ba, wato shi saboda tsabar ya isa ma, ba zai gaya mata da bakinsa ba sai dai ya rabuta mata cikin takadda, ta yayyaga takardar ta watsar da ita ta koma ta zauna tana huci da tinanin abin daya kamata tayi masa. Koda ya dawo da daddare har d'akinsa tabi shi wannan karon,
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(43)
Wanda shine karo na farko da fara shiga d'akinsa, ta tsaya daga bakin k'ofa tana rik'e da k'ugu, lokacin yana cire kayansa daga shi sai singileti ya waiga yana kallon ta cikin mamaki, ta d'an ji nauyin yanda ta ganshi, amman da yake rashin kunya ya kawo ta ta fara zazzage masa, ta gaya masa maganganu marasa dad'i amman bai ce mata ko k'ala ba.
Abin dake bak'anta mata rai, ta rasa yanda aliyu ya d'auki kansa, wannan shine dalilin dake sanya ta k'ara jin haushin sa, tana ganin rashin maganar da yake mata kamar raini ne ko kuma nuna isa, shi kuma yana k'ok'arin hana kansa magana ne domin bai gaya mata abin da zai 6ata mata rai kwata-kwata, ko ya sanya shi fusata yayi mata abin da bai shirya ba, har ta kammala bala'inta ta wuce bai kula ta ba, ta fice tana huce.
Data shiga d'akinta sai ta fad'a gado ta fashe da kuka, bata san yaya za tayi da Aliyu ba, yana neman ya mayar da ita mahaukaciya gaba d'aya ma, ta jima tana kuka, sai taji sak'o ya fara shigowa wayarta, ta san ba kowa bane sai mansur,
Sai ta k'ara fashewa da kukan takaici. Washegari ranar asabar ne babu aiki, don haka aliyu yayi zamansa cikin d'aki yana ta aiki a computer d'insa, watan k'arfe shabiyu da rabi warshi ta fara k'ara, sunan alh. Musa ke yawo akan scren d'in don haka ya d'auki wayar da sauri yana gaisheshi cikin ladabi, alh. Musa ya sanar da shi yana k'ofar gidansa, da sauri aliyu ya mik'e ya nufi hanyar fita, yana sanye da jallabiya a jikinsa. Cikin ladabi ya durkusa har k'asa ya gayar da shi, sannan yayi masajagora zuwa cikin gidan, ya bashi gurin zama a falo cikin jin dad'i ya fara gaisheshi, alh. Musa yana kallonsa kawai cikin tausayawa, ramar da yaga yayi ta fara damunsa, amman sai ya fara tambayarsa.
"Ioa matar taka ne? Da sauri aliyu ya mik'e kamar irin suna wani shirin nan yana magana "tana d'aki, ina tsammanin bata tashi daga bacci ba, amman bari na kirawota. Sai ya nufi d'akin hanan kai tsaye. Sanda ya isa k'ofar d'akin ya d'an tsaya cikin damuwa, don tunda yake a gidan bai ko ta6a kusanto k'ofar d'akinta ba balle
(44) har ya kai shi ga shiga ciki ba, yau dai dolen sa ya shiga, ya tura k'ofar a hankali sai yayi sa'a bata ta shi ba. Tana kwance akan gado daga ita sai doguwar shima tana chatting a wayar, taji an turo k'ofar d'ak'inta, sai ta mik'e a gigice cikin tsoro domin ta san babu mai shigo mata d'aki, ga makinta sai ta ga aliyu ne cikin fargaba yana tsaye, masifa da bala'i suka cika ranta ta kalleshi shek'ek'e cikin futsara tana magana. "malam lafiya, me ya kawo ka d'akina, koka shigo kwartanci ne? Maganar a daki ran sa, amman sai yay murmushi yana yin k'asa da murya "kiyi magana a hankali kar ya jiyo ki, baffane yazo gaishemu, yana can a falo, don Allah kar ki nuna masa akwai matsala a tsakaninmu hanan, bana son abin da zai tayar da hankalinsa, idan yatafi zaki iya yi mini komin, amman yanzu dai kar kiyi abin da zai gane." Doguwar maganar da yayi ta bata mamaki matuk'a, tunda ta tare a gidan, yau ce ranar daya ta6a yi mata magana irin haka mai tsaho, ta yi tsaki kamar bata damu da duk abin da yace ba tana fad'in.
"Kaga malam fita mini daga d'aki, kaje ka gaya masa ganin nan zuwa, ina kuma gargad'inka da shiga harkata, don babu ruwanka da yanda zanyi magana da mahaifina. Kamar zai k'ara yi magana amma yanda ta nuna masa hanyar k'ofa da alamun ya fita ya sanya yafice da gaggawa, ta mayar da k'ofar d'akin ta rufe tana tsaki sannan ta tsaya cikin tinanin dalilin zuwan babanta gidan, sai tayi sauri ta fara shiryawa. Abin daya tayarwa da alh. Musa hankali bai wuce ganin ramar hanan tafi ta aliyu ba, daga ganinta bata cikin kwanciyar hankali, hakan ya saukar masa da fishin dayazo da shi gidan, domin ya fuskaci gaba d'ayansu suna cikin wani haki na tsananin damuwa daya kamta ace an basu lokaci, don haka maikon fad'a sai ya kama yi mata nasha, tunda ta sunkuya da kanta k'asa ba tace komai ba sai hawaye da take yi kawai a ranta tana jin da zata iya rok'on babanta ya taimaka ya baiwa aliyu izinin sakinta da hakanne kad'ai mafita gareta, amman baza ta iyaba, don haka tana sauraransa ne kawai.
"Na san naniki abinda bai kamata ba
(45)
Hanan kamar yanda kikeji cikin ranki, amma ki sani ni ya kamata na zabar miki mijin daya dace dake, me addini, na za6ar miki aliyu wanda nake fatan ganin rayuwarki ta ginu tayi kyau da shi, do haka ina mai miki nasiha daki bi mijinki, ki rik'e auranki da girmamawa, watarana ko bana raye zaki tina dani hanan. Yajima yana yiwa hanan nasiha, aliyu yana kallonsu, cikin ransa yana jin kamar hanan ta d'auki nasihar mahaifinta musamman yanda yaga tana ta goge idonta alamar tana hawaye, sai da ya jima sannan ya fara k'ok'arin mik'ewa tsaye, aliyu ma ya mik'e da sauri yana kallonta cikin idonsa duk da gabansa yana fad'uwa amman bai hanashi fad'in abinda yayi niyyar fad'a ba. "Hanan ba a kawo wa baffa ruwa da lemo c, ki had'o masa da abinci mana. Hanan ta mik'e da sauri kamar gaske tana fad'in "eh haka ne, dady bari na kawo maka ruwa ko? Alh. Musa ya k'arasa mik'ewa yana kard'a kai gami da fad'in "yanzu bazan ci abincin gidan ku ba, don yanayinku ya nuna koku kanku baku ci kun k'oshi ba, idan kun yi kumari zanci
Watarana, sai anjima." maganar sa mai harshan damo ce, aliyu ya fahimci mai yake nufi, ita dai hanan murmushi kawai tayi ta rakashi har k'ofar fita daga falon tana masa a dawo lafiya, aliyu kuwa har gaban motarsa ya raka shi, alh. Musa ya jiyu ya kalleshi jim sannan ya fara magana. "Aliyu ko baka gaya mini ba nasan baka jin dad'in zaman aure da hanan, domin na fahimci babu wata alak'a ta kusa ko ta nesa tsakaninka da ita, sai dai ina son ka sani bata da kowa a wannan gidan sai kai d'aya, kai ne komai nata, kaci gaba da hak'uri da ita, amman dole ka saki jiki kayi k'ok'arin sabawa da kai domin kaine komai nata a yanzu, kai ne kuma a gaba da ita, irin zaman daka za6a shi zakuyi, dule sai ka k'ara dagewa akan baya, na baka amanarta." Jikin Aliyu yayi sanyi da kalaman sirikinsa, ya jima bai maganar da ta ratsa shi irin wannan ba, don haka cikin damuwa ya fara mara magana. "Insha Allah baffa zan kiyaye da hakan." Alh. Musa yayi murmushi ya shi ya shiga motarsa "nagode Allah yayi maka albarka. Aliyu ya mayar da
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(46)
Kofar motar ya rufe yana amsawa da amin, sai dayaga tashin motar sannan ya koma cikin gidan, ya zauna a falo shiru kaman sirikinsa na dawo masa a rai, tabbas bai rik'e amanar hanan yanda ya kamata ba, ya watsar da ita, ba haka ya dace ya zauna da ita ba, ko da tana zaginsa ya kamata ace ya sauke nauyin dake kansa, yaji dole zai yi abin da zai sauke mata hak'k'in ta, ko da ita baza ta bashi nasa hak'k'in ba. Ya fara tinanin abin da ya zamto hak'k'in hanan daya kamata ya sauke akansa, amanar da baffansa yace masa ya bashi ta ta tayar da hankalinsa matuk'a.
Ya wuni sukuku a gidan, bai fita ko inaba yana ta sak'awa da kwancewa, har dare yana zaune a falo. Hanan idan zata wuce sau dubu ta koma sau dubu sai tayi masa tsaki, bai damu da hakan ba, har sai da yayi shirin kwanciya bayan ya kulle ko ina na gidan sannan ya nufi d'akinta kai tsaye, tana kwance akan gado tana waya da mahaifiyarta suna labarin zuwan mahaifinta.
Haj. Bilkisu na k'ara izta "babu ruwana da dalilin zuwansa, domin bazai sauya komai na
K'udirinmu ba, ke dai na gaya miki, ki matsa masa, zuwa yanzu zaman ki ya fara nisa, ya isa haka, kina magana da mansur d'in a waya ko?
Cikin sauri tace "a'a momy bana yi, sau d'aya na ta6a bashi amsa a chat shima cewa nayi ya k'ara mini lokaci, yayi hak'uri ya daina mini magana..."
"Sai yace me? Haj. Bilkisu ta tambaya da sauri. "bai k'ara ce min komai ba har yau momy, hakan yana damuna sosai. Amma kin san mansur ba hak'uri, idan na bashi fuska gidan nan ma zai iya zuwa.
"ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru na tabbatar miki mansur yana k'aunarki, naji labarin irin halin daya shiga bayan bikin ki, ance har yanzu bai dawo cikin hayyacinsa ba, ki ci gaba da k'ok'arin ganin bayan auran nan."
Ta gyara kwanciyar tana gyad'a kai "momy zan yi..." Sallamar da akayi daga bakin k'ofa ta katse mata magana, ta waiga da sauri ta kalli aliyu tsaye a bakin k'ofa, gabanta ya fad'i ta kasa cewa komai. "Yaya aka yi? Naji kinyi shiru, menene? Haj. Bilkisu tayi mata magana daga 6angaranta, cikin k'uk'uni tana
(47) tana hararar Aliyu tayi magana. "shine ya shigo... "Shi kuma? Me ya kawo shi d'akin ki? Haj. Bilkisu ta katse ta cikin karaji. "ban sani ba nima momy, bari zan kira ki..." "Kafin ki kirani d'in, ki tabbatar kin gaya masa mara dad'i, domin ban son ya miki siddabarin da zaki kasa tantance fari da bak'i kamar mahaifinki. To kawai tace sannan ta kashe wayar tana kallon aliyu dake tsaye yana sauraranta, aliyu ya k'arasa shigowa cikin d'akin yana magana k'asa-k'asa. "Kiyi hakuri idan na takura miki... Ta d'aga masa hannu da sauri gacnta yana ci gaba da fad'uwa "kaga malam me ya kawo ka d'akina a daran nan? Lafiya? Tana magana tana nufarsa cikin rashin kunya da fitsara, bai damu da hakan ba, yana k'ok'arin dai-daita fad'uwar gabansa ne kawai, don haka cikin dakiya yace. "kiyi hakuri ba wani abu ya kawo ni ba, ina son tabbatar da baki da wata matsala ne..." ta katsae shi da gaggawa "matsala? Ai kaine babbar matsalata, mutum sai kace maye! Bai k'ara ce mata komai ba ya fice da gaggawa daga d'akin,
Ta bishi da tsaki da masifa shi dai bai dawo ba ta zauna agefen gado tana goge gumi kamar wacce tayi tseren gudu saboda masifa, sai ta rasa meya kamata ta fassara hakan, kiran da wayar tayi ya sanya ta d'auka da gaggawa kiran mahaifiyarta ne.
Tun daga wannan rana, kowacce safiya da kowanne dare sai aliyu ya shiga yaga lafiyar hanan sannan zai fita ko ya kwata, tun tana gaya masa maganganu idan ya shiga, har ya zamto bata ko kallonsa, wanda shi hakan ya fi ma komai dad'i, zai gama maganar sa ya fice batace masa komai ba. Abin da Aliyu ya fara fahimta shine ya fara damuwa da lamarin hanan, ya zamto ganinta kawai kan sanya shi jin sanyi cikin ransa, ya yadda wannan fad'uwar gaban da yake yi akan ta ba komai bane illa soyayyar, A yanzu ya yadda da maganar da abokinsa sunusi ke gaya masa, sai dai yasan kowanne irin so zai yiwa hanan ya tashi a banza, domin ya tabbatar ita bata da mik'iyi bayan shi.
Tun abin yana damunsa cikin ransa, har ya fara damuwa a fili, don haka ya duk'ufa da addu'a akan zamansa,
A yanzu ya tabbatar komai zai iya faruwa da shi ba zai iya rabuwa da hanan ba, ya kula ko masifa take yi burgeshi take yi, musamman idan tayi shigar dake sanya shi kallon ta babu k'akkautawa, sai dai ya k'i yadda ya nuna mata hakan a zahiri. A 6angaran hanan duk wani abu da zata yi wanda zai tunzura shi, amman a banza, ta kula kamar tana k'ara iza shine ma, daga k'arshe wata shawara tazo ranta, don haka ta k'udiri aniyar aiwatar da ita. Yau yana zaune a falo ya dawo daga aiki yana kallo ta fito cikin shigar k'ananan kaya ta gyara kanta, ya bita da kallo cikin damuwa, sai ta zauna ta kalleshi ya kawar da kansa da sauri cikin fad'uwar gaba, sai ta daddana wayar dake hannunta kara a kunnenta ta fara magana cikin kissa da dariya.
"Haba man na gaya maka fa...
Aliyu ya kalleta cikin mamaki, bai ta6a sanin yana da kishi kamar haka ba, tabbas hanan ta kawo inda bazai iya jurewa ba, bai son kojin sunan mansur a bakin wani balle matarsa, cikin masifa ya fara magana ganin taci gaba da abinda take yi.
"Hanan baki da hankali, yaya kina matar aure kike waya da wani, kinsan haramcin hakan kuwa? Hanan bata kalleshi ba taci gaba da maganarta cikin wayar, sai ya mik'e da sauri a fusace yana huci ya nufeta, bai yi wata-wata ba ya warce wayar hannunta, hanan ta kalleshi cikin tsananin mamakin abin da ya aikata tana huci take kallonsa. "lafiya menene kuma had'ina da kai malam? "Ni ba sakarai bane, zan iya jure komai akan ki amman bazan yaea ki raina mini wayo, ki karya mini darajar aure ba!
Tamik'e tana dariya ta tafa hannu "lallai su aure manya, kai yanzu har kana tak'ama da auran naka akayi na dole ba da son zuciyar kowa ba, to bari na gaya maka idan har ka sanyawa ranka cigaba da zama dani wallahi zaka fuskanci fiye da haka ma, dan haka bani wayata!
Tamik'a masa hannu, ya dalla mata harara bai yi magana ba, ta k'ara fusata. "malam nace kabani wayata ko! Ta na magana cikin izgili.
Yayi yak'e yana magana "hanan ki gane wani abu shi aure ba abin wasa bane ba..." kawai sai ta mik'a hannu wai zata k'wace wayar avious comments…
Zeinab Abdoul-karim
(20) almar yana cikin tsananin 6acin rai, amman jarumta da dakiya irin nasa ya sanya ya k'ak'aro murmushi yana magana. "ban ta6a damuwa da abin da Hanan ko mahaifiyarta suke mini ba, dukkan abin shukemini na 6acin rai, karamcin da mahaifinta yayi mini ya maye shi. Haka ne, amman baka ganin ya kamata ka sanar da mahaifinta wannan maganar domin ya d'auki mataki akai, bai kamata ace tana biyoka har gurin aikinka tana maka irin wannan cin mutunci ba, gaskiya bayan sanin alk'ar dake tsakaninka da yarinyar nan babu abin da zai hana na maketa? Aliyu ya k'ara yin murmushi yana d'aga kafad'a "ni kuma ban ji komai ba, na san hanan tana cikin bakin ciki da 6acin rai, tana son ta fesar da abinda ke damunta, don haka nine mutumin da ya kamata ta tunkara domin hucewa, amman nasan ba zata huce ba har abada, domin auranta bub gudu bubu ja da baya, maganar na sanar da mahaifinta kuma nayi alkawari har abada hakan bazai faru ba, babu wani abu da zata mini da bazan jure ba, kar ka damu abokina. Ya mik'e tsaye yana dan gyara
Ringarsa "zan wuce gida, akwai wasu shirye-shirye danake son yi a daran yau. "Kafin sunusi ya kai ga cewa wani abu aliyu ya fice da gaggawa cikin yanayin 6acin rai, sunusi ya bishi da kallo a ransa yana jin bakin ciki. Shi fa da shine zai baiwa Alh. Musa hakuri ne kawai ya auri wata, gayen da mata kala kala-kala ke k'aunarsa masu kud'i da yangayu, har da 'yayan manya k'aunarsa suke yi, zai tsaya wannan yarinyar na 6ata masa rai, da ace aliyu yana biyewa matan da ke nuna suna son shi ma da bai fi haka ba, bai mantawa watarana siyayya sukaje shoprite suka had'u da wata had'ad'iyar yarinya ta nuna tana sonsa ya basar da ita, daga k'arshe ya gano yarinyar d'iyar sanatace, da ya gayawa Aliyu yace sai me?
Abin da hanan ta masa ba sabo bane cikin abin data saba yi masa, sai dai zuwanta gurin sa'anarsa da wulk'antashi gaban abokinsa shine sabo a gareshi, kamar yanda yace zaije gidan kasa zuwa yayi, ya sami guri kawai yayi parking gefn hanya ya kwantar da kujera ya kwanta shiru yana tinani, tabbas da ace Alh. Musa
(21) zai bashi za6i zai gaya masa ya hak'ura da auran hanan, amma yasan hakan ba zai yuwa ba sam. K'arar wayarsa ta farkar dashi daga dogon tinanin da ya shiga, ya d'auka sunan fa'iza ke yawo akan screen din da gaggawa ya d'aga, hakan ya faranta ran Fa'iza. Bai san me ya sanya ya fad'a mata abinda daya fad'aba "fa'iza wacce unguwar kike ne? Shine abin daya fad'a, ya tabbatar 6acin rai ne ya sa kashi fad'i hakan, cikin jin dadi da d'oki take magana daga 6angaranta. "Da gaske zaka zo gurina aliyu? Ina cikin nasarawa g.r.a. Gidanmu yana kan titin tukur road. Ta bashi amsa cikin gaggawa. Yayi yak'e yana cigaba da magana "ki turo mini cikakken addrees, sannan ki zamto cikin shiri, nan da minti goma zan k'araso. Ya kashe wayar yana jiyo ihu da murnar fa'iza daga can, yayi murmushi cikin jin dad'i. Yana kashe wayar kai tsaye ya tayar da motar ya nufi inda fa'iza ta sanar da shi, bai wani sha wahala gane gidan ba, dayake ta turo masa kwatancan a wayarsa, ya isa yana yin horn megadi ya bud'e kofar,
Ya dan shiga da kan motar kad'an, maigadi ya k'araso gurin yana gaisheshi cikin girmamawa. "Barka da zuwa alh. Kaine bak'on haj. Fa'iza ko? Ya amsa da eh, maigadi ya nuna masa inda zah parking, bayan ya kulle k
[10/29, 5:59 AM] H Inna🧕🏼: Zeinab Abdoul-karim
(48)
Kawai sai ta mik'a hannu wai zata k'waci wayar wayar a hannunsa, da gaske tak'ok'arin kokawa da shi, abin ya bashi mamaki har tana wani hak'oro ita mai k'arfi, ya kaita jikin bango ya matseta, ta fito da ido cikin damuwa tana ci gaba da yunk'urin kwacewa, sai ya sanya wayar cikin aljihunsa ya had'a hannuwanta ya rik'e su katamau a bayan ta, suka k'urawa juna ido, wani irin abu ya dinga yawo tun daga kan Aliyu har zuwa yatsan k'afarsa.
Ya kasa jurewa sai kawai ya kai bakinsa cikin na hanan, tabbas ya gano yana buk'atar matarsa, ta fara k'ok'arin gocewa gami da yank'urin ganin ta kwaci kanta sai dai ya rik'e katamau, a yaune ta tabbatar da aliyu k'ark'arfane, sai da ata dai na yunk'urin kwatar kanta ba, shi kuwa ya tafi wata duniya da ban, bai ta6a samun haka gawata mace ba cikin rayuwarsa sai hanan, komai yana shirin kwance masa yaji an taka k'afarsa da k'arfi sai a sannan ya dawo hayyacinsa, ya janye bakinsa da sauri, sai ya kula itace ta taka shi da k'afarta, yana sakinta tana fashewa da kuka sosai
Tana ta tofar da miyau daga bakinta, alamar zata ta tofar da sumbar da yayi

Please Login or Register in order to submit comment