Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A Waya Din, Kalaman Da Fa'iza Tayi Amfani Dasu Sunyi Matukar Sanyaya Ransa Har Yaji Yasaki Murmushi Batare Da Yasani Ba, Wannan Shine Abin Daya Taimaka Masa Gurin Samun Bacci A Daran Ranar.
RANAR 'DAYA TA 'BARAWO...
K'arfe Bakwai Da Mintina Haj. Bilkisu Ta Kammala Shiryawa Ta 'Dauki Jakarta Tafita, Afalo Taci Karo Da Alh, Musa Yana Hira Da Yaransa Wad'anda Ke Sanye Da Kayan Makaranta A Jikinsu, Alamar Makaranta Za A Kai Su Me Aiki Tashirya Su.
Ganin Haj. Bilkisu Cikin Shirin Ya Bawa Alh. Musa Mamaki, Yabita Da Kallo Har Ta K'arasa
Kusa Dashi. "ina Kwana Alhaji? Tafad'i Lokacin Data Ke Kokarin Karasawa Gurinsa Da Yaran. Yaran Suka Nudta Da Sauri Lokacin Da Alhaji Ke Amsa Gaisuwarta. Takama Hannun Yaran Tana Dan Murmushi Gami Da Kokarin 6oye Damuwar Dake Ranta. "ina Zuwa Haka Da Sassafe Bilkisu? Alh, Musa Ya Tambaye Ta. Ta Dan Yauna A Kusa Dashi Cikin Kissa "tun Asuba Naso Gaya Maka, Sai Dainaga Baka Dawo Da Wuri Ba Tunda Katafi Marallaci, Wallahi Tun Jiya Da Daeare Ulcerta Ta Tashi, Shi Yasa Nakoma 'Dakina Ma Nasha Magani, Amma Abin Yaki Kwanciya, Shine Nakeson Zuwa Asibiti."
Alh, Musa Ya Gyada Kai "ayya Allah Ya Sauke, Nagaya Miki Kidinga Kulawa Bilkisu, Ita Wannan Cutar Kulawa Take Bukata, Yanzu Direba Zai Sauke Yara Sai Ya Kaiki Asibitin Ko? "anya Zan Jirasu, Domin Nasan Talatu Batagama Masu Abincin Launchng Box Din Su, Kawai Zaiyi Dribing Da Kaina Naje, Tunda Banisa. Ta Bashi Amsa. "zaki Iya Kuwa, Yaushe Rabonki Da Tuki, Ga Kuma Yanayin Jikin Naki. Tana Dan Yake Taci Gaba Damagana "haba Alhj. Tukin Dai Shekarata Nawa Inayi, Don Na
(67) Kwana Biyu Banyi Ba Ai Bazai Zama Namanta Yanda Ake Yin Saba."
Yayi Murmushi "shikenan, Allah Yabaki Lfya, Bari Nashiga Dakina Dauko Miki Kudin Kozaki Buk'aci Siyan Wani Wani Abu...
"babu Abinda Zansiya Ka Barsu Kawai, Maganin Zan Amsa A asitin Babu Matsala Kasani, Saina Dawo,. Tana Magana Tana K'okarin Mik'iwa Tsaye. Umar Yafara Rigima "momy Zan Biki Nina. Ta Kama Yaron Tana Lalla6ashi "a'a Asibiti Zanje, Za Ayi Mini Allura, Idan Kuma Kanaso Ayi Maka Shikenan, Da Sauri Yaron Ya Zame Yagudu Gurin Babansa Yana Gyad'a Kai "a'a Nibanason Allura. Hamza Dake Can Gefe Shima Yanuk'e Kafad'a "ni Dama Bance Zan Biki Ba Ko Momy? Gabad'aya Iyayan Suka Saka Dariya, Haj. Bilkisu tayi Hanyar Fita Tana Magana "kunga Nina Tafi, Bazaku Sanya Na Makara Ba. Har Takusa Fita Alh. Musa Ya Kirata "af Bilkisu Bakiji Ba.
Haj. Bilkisu Ta Tsaya Gami Da Waigowa, Tana Jin Takaicin Kiran Da Yayi Mata.
"ni Kuwa Kun Yi Waya Da Hanan Jiya? Ya Warga Mata Tambayar Data Bata Tsoro, Sai Ta Dururuce Gaba 'Daya Ta Hau In-ina, A Zatonta
Yasan Me Zataje Tayi. "eh Alhaji Me Kace?
Ganin Yanda Ta Rud'e Lokaci Guda Sai Yayi Tsammanin Ko Zatonta Wani Abu Ne Yasami Hanan Din, Don Haka Cikin Sauri Yace Mata.
"a'a Kinga Bawani Abu Ne Yaru Bafa, Jiya Nayi Nayi Takiran Wayar Mijinta Ne Bata Shiga Ba, Navra Masa Sako Kuma Bai Bani Amsa Ba, Sannan Baije Aiki Ba, Shine Nayi Zaton Ko Kun Yi Waya Ta Gaya Miki Wani Abu Game Dashi? Ta Gyad'a Kai Cikin Sauri Gami Da Fad'in "ko 'Daya Bata Sanar Dani Komai Ba, Bamuyi Waya Da Ita Ba Sam. Ya Girgiza Kai "shikenan, Kije Abinki, Nasan Komai Aci Yau Zai Sanar Dani.
Tafice Da Sauri Gabanta Yana Fad'uwa, Domin Tsammaninta Koya San Wani Abu Game Da Abinda Suke K'ullawa.
Falon Babu Kowa Haj. Bilkisu Tashigo Tana Sallama, Kai Tsaye Tanufi 'Dakin Hanan Jin Ba Amsa Sallamar Ba, Sai Ta Tarar Da Hanan Din Tana Kwance Aka Gado Tana Bacci Har Lokacin Bata Tashi Ba, Ta K'arasa Ta Fara K'okarin Tashinta, Hanan Ta Tashi Tana Mitsike Idonta.
Haj. Bilkisu Ta Dalla Mata Harar Cikin Takaici
"Lallai Hanan Baki Da Hankali, Wato Ke Har
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
Damar Bacci Kika Samu Ko?
Hanan Ta Dan Ta6e Fuska Cikin Damuwa "to Momy Jiya Fa Banyi Bacci Ba...
Haj. Bilkisu Ta 'Daga Mata Ha6u "ya Isa Yanzu Yana Ina Matsiyacin?
Yana Can 6angaransa. Ha6an Tabata Amsa A Takaice.
Haj. Bilkisu Tayi Kwafa Tana Shirin Yin Magana Wayarta Tafara Ringing, Tasanya Hannu Dasauri Cikin Jakararta Ta 'Dauko Wayar Ta Danna Ta Kira A Kunnenta.
"Hello Ya Akai Yi Batula? Daga Can 6angaran Batula Ta Sanar Da Ita Gata Cikin Gidan Hanan 'Din, Haj. Bilkisu Tabata Umarnin Ta Shigo 'Dakin Hanan Kai Tsaye, Bada Jimawa Ba Batula Tashigo 'Dakin Cikin Gaggawa, Tana Shigowa Hankalinta Na Kan Hanan, Tana Kallonta Cikin Tuhuma.
"Hanan Bai Miki Illah Ba Daiko? Hanan Takasa Magana Sai Ta Sunkuyar Da Kanta K'asa Cikin Da Tsananin Kunya,
Batula Taci Gac Da Masifa "shegen K'aton K'auye, Daman Abinda Yajama Yana Sakawa Cikin Ransa Kenan, Shi Yasa Yayi Ta Bin Malamai Har Sai Da Yasammace Mahaifin Ki Ya Aura Masa Ke, Domin Ya Biya Bak'atarsa.
Haj. Bilkisu Ta Amshe Cikin Gaggawa "nima Haka Nace, Amman Wallah
Zan San Yayi Da 'yar Halak, Domin Bazai Cutar Damu A Banza Ba..."
"yanzu Me Kuka Shirya Ne Anty Bilki ? Batula Ta Tambaya A Kufule.
"zuwa Nakenan Kika Shigo Gidan, Ganinta Haka Ne Ya Dan Kwantar Mini Da Hankali, Domin Nayi Tsammanin Zamu Tarar Da Ita Kwance Shame-shame Cikin Jini. Haj. Bilkisu Ta Bata Amsa.
Batula Tak'ara Kallon Hanan Cikin Damuwa Sannan Ta Kalli Haj. Balkisu "anty Bilki Nifa Wallahi Dazaki Ji Shawarata Da Yau Konace Yanzu Zamu Kashe Auran Na Mutafi Da Yarinyar Nan, D6in Yayi Abinda Ya Cancanci A Tsinka Igiyoyinsa Gaba Daya."
"Haka Yakamata Da Ace Babu Alhaji, Amma Yanzu Duk Abin Damuka Aikata Kin San Kaina Zai Dawo, Yaron Nan Zai Iya Sanar Dashi. Haj. Bilkisu Ta Bata Amsa Cikin Damuwa.
Suka Yi Jugum-jugum Cikin Tunanin Abin Da Ya Kamata Ace Sun Yi.
Aliyu Ya Kanala Shiryawa Tun Bayan Da Ya Idan Da Sallar Asuba Yana Kan sallaya Yana Lazimi, Sai Da Yaga Gari Yawaye Sa6an Yatashi Ya Shirya, Sai Dai Ransa Yana Cikin Da Damuwa, Domin Bai San Mai Zai Sanar Da Sirikinsa Idan Ya Tambayeshi
Tambayeshi Dalilin Kin Zuwansa Aiki Ba, Dakuma Kashe Wayoyinsa Da Yayi Jiya Ba, Duk Daya Tanadarawa Kansa Abinda Zai Fad'a Din Anan Yana Jin Kamar Bai Gamsu Da Hakan Ba, Sai Dai Bashi Da Mafita. Ya Dauki Makukin Motarsa Da Jakarsa Yanufi Hanyar Fita Kai Tsaye, Bayan Ya Isa Falon Ya Tsaya Turus Cikin Sak'awa Da Kwancewa, Bai Son Ya Fita Batare Daya San Halin Da Hanan Take Ciki Ba, Domin Yanaji A Ransa A Duk Sanda Yatuna Da Amanar Da Mahaifinta Yake Fad'in Ya Bashi Tata, Hakan Yasanya Yaji Zuciyarsa Tadake Yaije Yaganta, Don Bai Kamata Ya Fita Batare Daya San Halin Datake Ciki Ba, Ko Zata Zage Shi Taci Masa Mutunci Ne Kamar Yanda Tasa Ba, Don Haka Kai Tsaye Ya Nufi Hanyar Sashin Nata. Haj. Bilkisu Da Batula Ke Magana Dai-dai Lokacin Da Aliyu Yasako Kansa. "ni Aganina Anty Bilki Mafara Kaita Asibiti Ayi Mata Waikin Ciki, Domin Cilifa Zai Iya Sh4a Jikinta."
Wannan Ce Maganar Data Fara Dukan Kunnensa, Ya Tsaya Turus Cikin Tsoro Da Fargaba, Saiyaji Abin Kamar Cikin Mafarki Ba Gaske Ba Kafin Yagama Tantance Abinba
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(68) Kafin Ya Gama Tantance Abin Daya Kamata Yayi Ya Kuma Jiyo Muryar Haj. Bilkisu Na Bayar Da Amsa. "tabbas Haka Ya Kamata, D6in Komin Zai Iya Faruwa.
Sai Yaji Ya Kasa Hak'uri, Bai Yaea Da Gaske Maganganun Daga 'Dakin Hanan Suke Fitowa Ba, Idan Ma Daga Nan Ne Tabbas Aljanune Keyi Ba Mutane Ba, Don Haka Ya Kutsa Kansa Kai Tsaye Cikin 'Dakin Gami Dayin Sallama, Bayan Ya Tura Kofar 'Dakin. Abin Da Yafaru Tsakaninsu A Iya Kiransa Da Kici6is, Domin Kowa Yaga Kowanne Batare Da Tsananin Ganin Nasa Ba, 6angaran Haj. Bilkisu Da Batula Kawar Dakansu Kawai Sukayi, Haj. Bilkisu Najin Kamar Ta Kalli Aliyu A Karon Farko Ta Zage Shi Ta Uwa Ta Uba, Amma Tasan Batada Lokacin Yin Hakan Gareshe, Domin A Ganinta Bai Kai Tayi Masa Hakan Ba, Batula Kuwa Huci Take Yi Tana Jin Kamar Ta Rufe Shi Da Duka. Aliyu Ya 'Dan Rankwafa Cikin Ladabi Yafara K'ok'arin Gaishe Su "momy Ina Kwanaku?
Babu Wanda Yace Masa Ko K'ala, Balle Yayi Tsammanin Zasu Ce Masa Wani Abu, Sai K'ara Kawar Da Kawunansu Ma Dasuka Yi, Hanan Ce Kawai Taja Dogon Tsaki
Yajima Kansa A K'asa Yana sauraran Ko Zasu Ce Wani Wani Abu Amma Shiru, Ya Kar Yin Magana Karo Na Biyu. "ayi Hakuri Momy Tabbas..."
Haj. Bilkisu Tayi Magana A Karon Farko Cikin Kufula "kaga Dm Allah Wuce Ka Bani Guri!
Yaji Maganar Ta Kamar Dukan Guduma Cikin Tsikiyar Kansa, Ya Dinga Jin Wata Juwa Na Neman Kayar Dashi, Ya Kuma Jiyo Tsakin Hanan Karo Na Biyu, Don Haka Yayi Gahawar Barin 'Dakin Batare Daya K'ara Sanin Abin Da Zai Yi Ba.
Batula Ta 'Dauka Cikin 6acin Rai "amma Lallai Yaron Nan 'Dan Iska Ne Anty Bilki, Wallahi Banda Bai Isa Komai Ba Da Yau Naga Yagama Rigar Mutunci, Shege 'Dakiki Jahili Kawai, Banda K'aeara Irin Ta Aure Menene Had'in Hanan Da Almajiri, Yaron Damun Riga Mun San Asalinsa Da Bamu San Shi Bane Zaiyi Mana Haka."
Ta Inda Tashiga Batanan Take Fita Ba Kamar Zata Ci Babu, Hanan Ta Kalleta Karon Farko Sai Taji Kalaman Da Aka Gayawa Aliyu Sun Yi Girma Matula, Domin Abubuwan Da Antyn Nata Ke Fad'a Yayi Yawa, Ta Kuma Tabbatar Aliyu Yajiyo Wasu, Domin Tun Bai Gama Fita Daga 'Dakin Ba Tafara
Sai Taji Tausayinsa Ya Cika Ranta.
Haj. Bilkisu Ta Katseta Cikin Sauri Ganin Tak'i Daina Mitar "haba Batula, Da Wanda Ya Isa Ya Kamata Ayi Magana Bada Sakarai Irin Wannan Ba! Ki Rabuda Shi Kawai, Muyi Abinda Ya Kawo Mu."
Aliyu Bayan Ya Shiga Motarsa Sai Ya Kifa Kansa Akan Sitiyari, Karo Na Farko Yaji Hawaye Yazubo Masa Akan Kuncinsa, Me Yasanya Hanan Da Iyayan Ta Ke Wulak'antashi Haka Ne, Shin Shi Ba Mutum Bane Ba, Me Yasa Suka Kasa Yadda Da Abinda Allah Ya K'addara Tsakaninsu, Wani Tuk'ik'i Yana Cigaba Dacin Ransa Yana Jin Kamar Ya Fasa Ihu Ya Huta. Kwankwasa Glass Din Motar Da Akayi Ne Ya Sanya Ya 'Daga Kanshi Da Sauri, A Tsammaninsa Wata Daga Cikinsu Ce Tadawo Domin Cigaba Da Cin Mutucinsa, Sai Dai Ganin Abubakar Kaninsa A Tsaye Ya Bashi Mamaki Matuk'a, Ya Sauke Glass Din Motar Da Sauri Yana K'okarin K'ak'aro Murmushi Akan Fuskarsa.
Abubakar Yaya, Kana Lafiya? Yaron Ya Fahimci Yayansa Yana Cikin Matsala, Amma Abinda Ya Kula Bayason Yasanar Dashi Komai, Don Haka Ya Fara Magana Kai Tsaye.
"yaya Lafiya
Jiya Daga Kai Har Anty Banga Kowa Ba?
Tambayar Tazo Masa A Bazata, Don Haka Cikin K'ok'arin Dakewa Yaci Gaba Damagana "lafiya Abubakar, Yaya Makarantar Ba Zaka Shiga Bane Yau?
"zan Shiga, Yanzu Nake K'ok'arin Shiriyawa Natafi Ma. Abubakar Ya Bashi Amsa. Yazura Hannu Cikin Aljihunsa Yazaro Kud'i Ya Mik'awa Abubakar 'Din. "amshi Wannan Karike A Hannunka, Idan Ba Yi Abinci A Gidan Ba Sai Kaje Ka Sami Takeaway Ka Siya, Kaji Ko?
Abubakar Ya Gyd'a Kai Alamar To, Sannan Yaja Da Baya Yana Godiya, Aliyu Ya 'Daga Masa Hannu Alamar Babu Komai, Sannan Yayiwa Motarsa Wuta Yanufi Hanyar Fita.
Abubakar Yabi Yayansa Da Kallo, Tausayi Yayan Nasa Ya Cika Ransa, Kowa Zai So Yasami Rayuwa Irin Ta Yayansa, Anan Wanda Yasan Halin Da Yake Ciki A Gidansa Zaiji Tausayinsa, A Haka Idan Kagan Shi Ba Zaka Yi Tsammanin Yana Da Matsala Ba, Sai Kamtso Kusa Dashi Sannan Zakagane Hakan, Tabbas Yana Tausayawa Yayansa.
Aliyu Da Yashiga Kamfaninsu Ofis 'Din Su Kai Tsaye Yawuce, Yana Shiga Ya Kullo Kan Shi Ya Kifa Kai Kan Tebur, So Yake
Zuciyar Shi Ta Sanar Dashi Abinda Ya Kamata Yayi Wanda Zai Samarwa Kansa Mafita Amman Ya Kasa, Duk Abin Dayazo Masa, Zaiyi Ji 'Daya 6angaran Zuciyarsa Ya Sanar Dashi Wannan Fa Hanan Ce 'Diyar Baffansa, Sannan Waccan Kuma Haj. Bilkisu Ce Matar Baffansa, Kome Sukayi Masa Bazai Iya Tozartasu Ba, Wannan Ya Sanya Har Ya Kammala Tinaninsa Bai Sami Mafita Ba, Ganim Zai 6ata Masa Lokaci Yasanya Ya Fara Aikinsa.
Bai Jima Da Farawa Ba Yaji An Kwankwasa K'ofarsa, Da Gahawa Ya Mik'e Domin Bud'e K'ofar, Da Alh. Musa Ya Ci Karo, Cikin Girmamawa Yara K'ok'arin Gaisheshi Alh. Musa Ya Amsa Yana K'are Masa Kallo, A Ransa Ya Gam Akwai Wani Abu Dake Damun Aliyu.
"Aliyu Lafiya Jiya Ka Kashe Wayoyinka, Kuma Bakazo Ofis Ba?
Aliyu Ya Sunkuyar Da Kansa Domin Bai Son Ya Had'a Ido Da Baffansa, Don Kar Yagane Halin Dayake Ciki. Baffa Banji Dad'i Bane, Sai Kuma Nasha'afa Ban Kunnu Wayoyin Ba "ayya, Amma Dai Kaje Kaga Likita Ko? Domin Bai Kamata Mutum Yazauna Da Rashin Lafya Ba
"Naje Baff. Aliyu Ya Bashi Amsa. Alh. Musa Ya Gyad'a Kai
Gami Da K'ok'arin Fita Yana Magana.
"Allah Ya K'ara Lafiya, Kar Kara Kashe Wayar Ka Irin Haka.
"Insha Allahu Baffa." Ya Bashi Amsa Dai-dai Lokacin Da Ya Kanala Fita.
Aliyu Yayi Ajiyar Zuciya Gami Da K'ok'arin Komawa Ya Zauna Akan Kujeransa Jikinsa Yayi Sanyi K'alau, Bai San Me Zai Faru A Gidansa Ba, Kalaman Anty Batula Sun Fi Tsayawa Cikin Ransa, Yanzu Ashe Hanan Zata Iya Samun Ciki, Amman Kuma Zasuje Ayi Mata Wankin Ciki Domin Lalata Komenene Ya Shiga Mahaifarta, Idan Har Suka Aikata Haka Tabbas Sun Zalunce Shi.
Can Wajan Rana Yana Ta Aiki Yana K'ok'arin Mantar Da Kanshi Komai Dake Faruwa A Gidansa, Amma Yakasa, Idan Abin Yatafi Can Kuma Sai Ya Dawo Masa Haka Yakusa Wuni, Sai Wayarsa Tana Kira, Ya 'Dauka Ya Duba, Sunan Fa'iza Yagani Akan Wayar, Ya 'Dauka Yana Murmumushi Ya Kara A Kunnensa,
"Tubanake Yi. Abinda Yafara Furtawa Kenan. Fa'iza Tayi Murmushi Daga Can 6angaranta Tana Magana. "Laifin Me Kayi Kake Tub?
Ya Gyara Zama Cikin Jin Dad'i Yana Ci Gaba Da Magana "nidai Nace Tubu Nake, Idan Kuma Ana Buk'atar
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
Tone-tone Ne To?
Tafashe Da Dariya "Allah Aliyu Kana Da Wayo, To Bari Nayi Magana 'Daya Yanzu Idan Nace Yau Ina Rok'on Ayi Dinner A Gidanmu Bazan Yiwa Madam Laifi Ba?
Yaji Wani Abu Yatsaya Cikin Ransa Me Yasa Fa'iza Tadamu Dashi Har Haka Ne, Shirun Da Yayi Ya Fad'ar Mata Da Gaba Har Ta Magantu.
"Zan Yiwa Madam Laifi Kenan Ko? Maganaq Fa'iza Ta Katse Masa Tinanin Daya Shiga.
Da Sauri Yace Mata "A'a Ko 'Daya, Kawai Ina Tinanin Irin Yanda Kika Damu Dani Ne Fa'iza. Bai San Lokacin Da Maganar Ta Fito Daga Bakin Sa Ba.
A 6angaran Fa'iza Sai Taji Maganar Kamar Albishir Da Gidan Aljanna Don Haka Ta Fashe Da Dariya Cikin Jin Dad'i.
"Watak'ila Haka Ne Watak'ila Ba Haka Bane Ba, Sai Anjima."
Tana Gama Fad'in Haka Takashe Wayar Ta, Yayi 'an Murmushi Sannan Ya Kalli Wayarsa, Sai Yaji Zuciyarsa Na Fad'in. Dama Ace Haka Hanan Ke Kulawa Dashi Da K'aunarsa, Idan Hakan Ta Tabbata Yagama Samun 'Daukan Jin Dad'in Duniya Sai Da Kuma Ya Bukaci Cikawa Da Imani.
Bai Tashi Daga Ofis Ba Sai Wajan K'arfe Bawai Na Dare Don Haka Daga Can
Gidansu Fa'iza Kawai Ya Nufa, Duk Dayaso Yakoma Gida Yayi Wanka Ya Sauya Kaya, Amma Fargabar Abinda Zai Tarar A Gidan Yasanya Ya Hak'ura, Dm Yasan Balallai Ne Ace Sirikan Nasa Sun Bar Gidan Ba. Yana Shiga Unguwar Ana Ta Kiraye-kirayen Sallar Magariba, Don Haka Yasami Masallaci Ya Tsaya Yayi Sallah Sa6an Ya K'arasa Gidan, Lokcin Da Yayi Mata Waya Yace Yana Harbar Gidansu Taji Kamar Ta Shid'e Don Dad'i, Cikin Gaggawa Tafito Taja Gorance Shi Zuwa 'Dakin Saukar Bak'insu.
Yanayin Kwalliyar Da Tayi Ya Amshese Ta, Ta K'ayatar Dashi, Bakinta Yak'i Rufuwa Tamkar Gomar Auduga, Don Haka Ya Kalleta Cikin Murmushi Yana Tambayar.
"Hala Wani Abun Ne Yafaru Dayasa Ki Farin Ciki Fiye Da Kullum Ko Fa'iza?
Ta Kad'a Idonu Cikin Kissa Sannan Tafara Magana "akwai Wani Abu Dazai Sanya Ni Farin Ciki A Wannan Duniyar Bayan Kai Aliyu, Kaine Kawai, Domin Ban Yi Zaton Zaka Amshi Gayyata Ta Kai Tsaye Ba, Sai Gashi Ka Amsa, Kaga Dole Nayi Farin Ciki Ko?
Yayi DanJim Yana Tinanin Irin Amsar Daya Kamata Yabata, Dai-dai Lokacin Masu Hidimar
Gidan Suka Fara Shigowa Da Kayan Abinci Kala-kala, Bayan Sun Gaisheshi Cikin Girmamawa Suka Fice Daga Falon, Fa'iza Ta Fara K'ok'arin Zuba Masa. Bai Yi K'asa A Gwiwa Gurin Kwasar Garar Ba, Domin Yana Cike Da Tsananin Yunwa, Yajima Bai Ci Abinci Mai Dad'i Irin Haka Ba, Yana Ci Tana Jan Shi Da Hira, Hakan Yasanya Yasami Sakewar Dayaci Abincin Mai Yawa, Gami Da Kayan Tand'e-tand'e. Ya Jingina Da Kujera Bayan Cikinsa Ya Cika Yana Kallonta Yana Murmushi "Hanan Kin Cika Mini Ciki Da Yawa.
Ta Kalleshi Da Wani Duc Daya Ya Bayyana Kishi K'arar Cikin Fuskarta, Sai A Lokacin Ya Tuna Da Abin Daya Kira Ta Hanan, Tabbas Hanan Ce Cikin Ransa, Da Abubuwa Biyu Jin Dad'i Da Kuma 6acin Rai, Sai Ya K'ar Gyara Zama Yana Yak'e.
"Tuba Nake Fa'iza..."
Tag'aga Masa Hannu Da Sauri "bafa Laifi Kayi Ba, Domin Lokacin Tane Na Shiga, Mu Bar Maganar Kawai."
Yanda Ta Bashi Amsa Ya Tabbatar Masa Da Bataji Dad'i Ba Har Cikin Ranta, Amman Dayake Ta Iya Siyasa Take K'okarin Dakewa.
Yarasa Me Zai Kuma Fara Gaya Mata, Domin Yana Buk'atar Ta Koma
Walwalarta Kamar Baya, Dm Haka Ya Fara Yi Mata Zancen Wani Saurayinta Daya Ta6a Ganinsu Tare Cikin Mota.
"Ina Mutumin Ne Fa'iza? Ta Kalleshi Da Gaggawa Gami Da Bayyana Mamaki Akan Fuskarta "mutumin Kuma, Wanne Kenan? Ta Tambaya Cikin Fargaba,
Yasami Gangara Don Haka Yak'ara Gyara Zama Yana Murmushi "wannan Saurayin Naki 'Dangayu, Mai Farar Anaconda 'Din Nan."
Sai Tafashe Da Dariya, Domin Ta Tuno Abin Da Yafaru Lokacin Da Aliyun Ya Gansu Yayi A Magana, Saurayin Nata Kabir Yana Bala'in Smta Kuma Tak'i Bashi Had'in Kai, Don Haka Lokacin Da Aliyu Zo Yaga Hankalin Ta Yayi Kansa Sai Yafara Masifa Da Zage-zage, Dayake Aliyun Ba Mai Son Rigima Bane Yad'aga Masa Hannu Gami Da Fad'in.
"Kaga Malam Ni Fa Yayanta Ne, Kuci Gaba Da Zancanku. Kafin Ya Bashi Ammsa Ya Yiwa Motarsa Wuta Ya Bar Gurin, Duk Da Fa'iza Bataso Tafiyar Tasa Ba, Domin Ziyarar Daya Kawo Mata Ta Bazata Ce, Amma Sai Daya Bata Dariya Yanda Ya Nuna Jin Tsorarsa K'arar A Fili. Ya Dinga Kallonta Tana Dariya Sannan Ya Tanka "wai Me Yabiki Dariya Ne, Daga
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(69) Daga Ambatar Saurayinki, Na Kula Yana Bala'in Sonki Fa."
Ta 'Dan Rage Darege Dariyar Sa6an Ta Kalleshi "Irin Yanda Lokaci 'Daya Ka Firgita Daya Fara Maganane Idan Na Tuna Yake Bani Dariya, Ko Kafin Kiftawa Da Bismillah Ka 6ace Daga Gurin Gaba Daya, Ka Tafi Ka Bar Shi Yana Ta Mitga, Wai Be Yadda Da Abinda Ka Fad'a Ba, Kishin Tsiya Ne Dashi, Gashi Kuma Ya Kasa Samun Sa'ar Soyayyata."
Aliyu Ya Girgiza Kai Cikin Yanayin Murmushi
"Amma Fani Banga Aibun Sa Ba, Meyasa Bazaki So Shi Ba Fa'iza?
Maganar Tazo Mata Kamar Kwad'a Guduma Cikin Tsohon Gyan6o, Lokaci Guda Fa'ar Dake Fuskarta Ta 'Dauke, Ta Kawar Da Kanta Gefe Takasa Magana, Ya K'ura Mata Ido, Yasan Abin Dake Ranta Amma Bai Son Ta Yadda Hakan Ne, Yafison Ta 'Dauke Shi A Matsayin Dan'Uwa, Shi Ya Sanya Duk Wata Hanya Da Zai Nuna Mata Wani Cu Wai Shi Soyayya Yana Kauce Masa.
Jin Yayi Shiru Bai Kara Yin Magana Ba Ta Waiga Ta Kalleshi Tafara Magana Cikin Damuwa "Aliyu Da Gaske Kake Abin Daka Fad'a, Ko Kuma Tsokana Ta Kake Yi?
Ya Kasa Amsa Mata Tambayar,
Domin Bai San Me Yakamata Yace Ba, Saboda Ta Tsare Shi Da Idanuwanta Wanda Ke Nuna Abin Dake Damunta Karara Har Cikin Zuciyarta, Jin Ya Kasa Magana Yasa Taci Gaba Damagana Bayan Ta Sunkuyar Da Kanta.
"Yau Daman Nayi Niyyar Gaya Maka Abin Da Ke Cikin Raina, Ko Da Zaka Gujeni, Nagaji Da Jiran Lokacin Dazaka Gane Ina K'aunarka, Duk Dana San Ka Jima Dagane Hakan, Amma Kak'i Yadda Ka Amince, Ban Ta6a Son Namiji Kamar Kab, Ban Ta6a Yin Soyayya Irin Taka Ba, Inason Ka Aliyu Ko Ba Zaka Ta6a K'aunata Ba,
Ta 'Daga Ido Ta Kalleshi Idonta Yana Zubar Da Hawaye, Hakan Ya Karya Zuciyarsa Gab Daya, Sai Yaji Tausauyinta Yacika Zuciyarsa, Koda Bai Son Fa'iza Bazai Ce Baijin Wani Abu Game Da Itaba, Duk Sanda Yaji Muryarta Yana Samun Nutsuwa Da Nishid'i, Sannan Idan Ya Kalleta Tana Faranta Masa Rai Fiya Da Matarsa. Ya Tabbatar Hakan Shine Soyayya, Sai Dai Bashi Da Damar Yin Soyayya Da Wata, Domin Bazai Iya Kallon Baffansa Yace Masa Zai Auri Wata Ya Had'ata Da 'Diyarsa Ba, Don Haka Yau Zai Gaya Mata Gaskiyar Abin Dake Ransa.
"kiyi Hak'uri Fa'iza, Tabbas Vn Randa Na Fara Ganinki Na Fahimci Akwai Wani Abu Cikin Ranki Game Dani, Kuma Bazan 6oye Min Komai Ba,
Kin Tsaya Cikin Raina, Har Inajin Ki Kamar Jinana, Kamar 'yar'uwata...
Yayi Shiru, Tayi Tsuru Tana Kallonsa, Ba Wannan Kalman Take Buk'atar Ya Fad'a Ba, Amman Sai Tayi Kurum Tana Sauraransa, Fatanta Yafurta Abinda Take Buk'utar Ji 'Din.
Ya Kwar Dakansa Gefe Domin Abin Zai Gaya Mata Mai Zafi Ne, Sannan Yaci Gaba Da Magana. Bazan Iya Had'a Hanan Da Kowacce Mace Ba, Bazan Iya Yin Komai Gariki Bayan Na Zauna Muyi Hira Ba Kawai, Fa'iza Kiyi Hak'uri."
KASH! MUHA'DU A AKASHI NA HU'DU
IDAN ALLAH YA KAIMU GOBE ZAMU DORA AKASHI NA HU'DUN

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment