Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wulk'antashi gaban abokinsa shine sabo a gareshi, kamar yanda yace zaije gidan kasa zuwa yayi, ya sami guri kawai yayi parking gefn hanya ya kwantar da kujera ya kwanta shiru yana tinani, tabbas da ace Alh. Musa
(21) zai bashi za6i zai gaya masa ya hak'ura da auran hanan, amma yasan hakan ba zai yuwa ba sam. K'arar wayarsa ta farkar dashi daga dogon tinanin da ya shiga, ya d'auka sunan fa'iza ke yawo akan screen din da gaggawa ya d'aga, hakan ya faranta ran Fa'iza. Bai san me ya sanya ya fad'a mata abinda daya fad'aba "fa'iza wacce unguwar kike ne? Shine abin daya fad'a, ya tabbatar 6acin rai ne ya sa kashi fad'i hakan, cikin jin dadi da d'oki take magana daga 6angaranta. "Da gaske zaka zo gurina aliyu? Ina cikin nasarawa g.r.a. Gidanmu yana kan titin tukur road. Ta bashi amsa cikin gaggawa. Yayi yak'e yana cigaba da magana "ki turo mini cikakken addrees, sannan ki zamto cikin shiri, nan da minti goma zan k'araso. Ya kashe wayar yana jiyo ihu da murnar fa'iza daga can, yayi murmushi cikin jin dad'i. Yana kashe wayar kai tsaye ya tayar da motar ya nufi inda fa'iza ta sanar da shi, bai wani sha wahala gane gidan ba, dayake ta turo masa kwatancan a wayarsa, ya isa yana yin horn megadi ya bud'e kofar,
Ya dan shiga da kan motar kad'an, maigadi ya k'araso gurin yana gaisheshi cikin girmamawa. "Barka da zuwa alh. Kaine bak'on haj. Fa'iza ko? Ya amsa da eh, maigadi ya nuna masa inda zah parking, bayan ya kulle k'ofar yayi masa jagora zuwa inda tace ya kai shi. Aliyu ya shiga k'aton falon, da sallama ya sami guri ya zauna, maigadi ya juya ya fita, ya fara k'arewa falon kallo cikin mamaki, bai yi zaton iyayan fa'iza suna da arzik'i haka ba, bai ta6a shiga falo irin wannan ba tun daya ke, ko da yake shi ba mutum ne mai shiga-shige ba, daga yanayin gidan ya tabbatar masa iyayanta ba k'ananan ma su kud'i bane, hotunan dake falon a kafe sun k'ara tabbatar da arzik'in iyaybnta da kuma bokonsu. Bayan minti biyu saiga fa'iza ta fito cikin tsananin kwalliy da jin dad'i, tana masa sannu da zuwa har da tafinta na farin ciki. "oyyo! Oyoyo! Yanda ta fad'i kalmar sai ta bashi dariya har yana gyad'a kai. "Wallahi baki da dama fa'iza, sai kace wani irin yaron nan? Tana dariya tabashi amsa "eh mana ai dole nayi farin ciki
(22) "eh mana ai dole nayi farin ciki da zuwanka, bazan 6oye maka ba aliyu, ban ta6a jin farin ciki a rayuwata kamar wannan ba, kayi suprising d'ina matuk'a, nagode kwarai da gaske. Ya d'an gyad'a kai yana murmushi "kar ki damu ya kamata a ramawa karu aniyarta? Tayi fari da ido cikin jin d'ad'in abin daya fad'a, sannan tayi wani luu da ido tana k'asa da murya. "nayo maka fa gayyar 'yan gidan nan, yanzu zaka gansu. Tana rufe baki suka shigo, dattijuwar mace fara tasanye da glass mdicated wacce tafi kama da tsohuwar 'yar boko ta fito, sai wata matashiya da alamun k'anwar fa'iza ce biye da ita, domin kamar su d'aya, sai kuma wani matashi da bai wuce shekaru shabakwai ba, sai kuma 'yar shekaru sha uku, suka zauna cikin jin dad'i, kafin suyi magana Aliyu ya fara gayar da dattijuwar domin jikinsa ya bashi mahaifiyar fa'iza ce. Haj. Zalaiha tana dariya take magana "yau dai Allah yanuna mini Aliyun da aka jima ana bani labarinsa, sunnunka da zuwa aliyu, ka saki jikinka, ka d'auka nan gidanku ne har abada."
Aliyu yayi murmushi yana fad'in "nagode hajiya. Sauran yaran suka gaidashi, ya amsa cikin jin dad'in yanda aka girmamashi da karramashi, sun d'an tattauna da haj. Zaliha ta tambayeshi inda yake aiki sannan ta mik'e suka bar gurin, bayan sun tafi fa'iza ta kalleshi tana dariya. "kayi hak'uri da tambayar momy kasan tsohuwar 'yar jarida ce, tayi aiki B.B.C yanzu haka kuma itace shugabr 'yan jarida mata na k'asa, tana da gidan rediyon kanta wato nishad'i F.M, itace managing director. Aliyu yayi murmushi "banji komai ba fa'iza bayan farin ciki, na jima banga mace irin mahaifiyarki mai faran-faran da sakin fuska ba, family d'inku ya burgeni, ya nuna mini kuna k'aunar juna kwarai da garke." Fa'iza tayi dariya "haka ne, ko sau d'ya mutum yazo gidan nan zai fahimci haka, ba mu dayawa mu shida ne 'ya'yan gidan, baban mu shine tshon grand kaddy na jahar nan, yanzu kuma yana matsayin babc cikin majilasar alk'alai ta k'asa, sai babban yayanmu yaya sulaiman doctor ne, amman yana k'asar waje acan yake aiki, sai mai bi masa
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(23) sai yaya nura da ya rasu yana karatu waje, sai kuma ni, sai nabila dake gab da kammala digirinta a jami'ar Ahmad Billo sai kuma salis daya kamla secondry scholl, sai salima autar momy dake Jss 2. Aliyu yayi dariya yana gyad'a kai "kin iya bayar da labari, amma baki gaya mini naki karatun ba, kin yi tsallake ko? Ta d'an bud'e hannu tana dariya "haka ne to ni dai banyi wani karatu ba, domin master ne kawai da ni, akan tsumi da tanadi sai na sami aiki da jaha, yanzu haka ni 'yar ma'aikaciyace. Aliyu ya fashe da dariya yana nuna ta da hannu "wato fa'iza kina da balaga ta iya magana, ko mutum zai kwana yana hira dake bazai k'osa ba. Kafin ta kai ga yin magana me aikin ta fara shigo da manyan fulasai na abinci akan katon farinti, ta ajiye su akan wani karamin tebur na tangaran, fa'iza ta fara k'ok'arin zuba masa tana ci gaba da jan shi da hira, yana jin dad'in hirarta, domin hakan ya mantar da shi duk wani hali da yake ciki na damuwar da hanan ta saka shi, ya biye ta, hakan ya bashi damar cin abinci me yawa,
Ya jima bai ci abinci kamar haka ba, har ya kammala bai gaji da hirar fa'iza ba. Ta kalleshi cikin zolaya tana magana "yanzu ina son ka bani labarin 'yan matakanka aliyu. Maganar bata zo masa a bazata bb, domin ya jima da gano fa'iza tana son shi, ba zai ce bai sonta ba, domin ya jima tana burge shi amma kai tsaye ba ta6a jin soyayyarta cikin ransa ba, ya gyara zama yana kallonta cikin murmushi, ya san abin da zai gaya mata ba zai mata dad'i ba, amman gwara ya sanar da ita gaskiya. "Ummh! 'yan matana suna da yawa, amma idan nace miki saura sati d'aya auren zaki yadda? Ta kalleshi cikin tsananin mamaki da fad'uwar gaba, gaba d'aya sai ta d'auke wuta ta kasa yin magana. Yaji tausayinta ya cika ransa, sai dai bai bari ta gane ba yaci gaba da magana "yaya ki kayi shiru ko baki yadda ba? Tayi k'ok'arin dakewa da shanye damuwarta tana d'an yak'e "eh zan yadda mana, domin na kula kai aliyu wani mutum ne jarumi mai magana d'aya, baka fad'in wani abu da ba haka yake ba, ko da zai sosa zuciyar mutum..."
(23) tayi d'an jim kamar baza taci gaba da magana ba, amma ta dake taci gaba. "ina taya wacce ta sameka a matsayin miji murna, yaya sunanta? Irin yanda take magama ya nuna masa abin da take ji a cikin zuciyarta, sai yaji tausayinta ya k'ara kama shi amman bai son ta gano, gwara ta saba hakan, cikin dariya yace. "Sunanta bai kai naki dad'i ba, canki. Hakan da yayi ya sanya taji sanyi cikin ranta, da yace sunanta bai kai na ta dad'i ba, don haka ta d'an saki rai tana karkatar da kai. "ban yadda ba, amman bari na canka, sunanta zahra, kaga yafi sunana dad'i ko? Ya gyad'a kai "ina baki canka ba sunan ta Hanan. Tayi luu da ido "hanan, hummm? Sunan mai dad'i ne, gaskiya ya fi nawa dad'i, me yasa baka ta6a gaya min wannan labarin ba aliyu? Ta karasa maganar da tuhumar sa. "Saboda lokacin da yakamata muyi maganar baiyi ba sai yanzu. Ya bata amsa kai tsaye. Ta gyad'a kai tana d'an cije lebe "haka ne, sai dai ina fatan hanan zata iya bani damar ko gaisawa na dinga yi da kai ko? "Baki da matsala akan haka fa'iza,
Kina da muhimmanci a gurina a yanzu, ina jinki kamar jinina. Wannan sune kalamai mafi dad'i da ya gaya mata tun bayan furta kalaman auransa, sai kawai taji komai ya wuce a ranta, domin tana son Aliyu. Koda mata hud'u ne da shi bazata iya daina son sa ba, balle mace d'aya ce, ta d'an yi malejin damuwarta suka ci gaba da hira, har zuwa sanda ya mik'e da zummar tafiya, ta rakashi har gurin motarsa suna hira, sai dataga fitar sannan ta koma cikin gida cike da damuwa. Kai tsaye d'akin mahaifiyarta ta nufa cikin damuwa, haj. Zaliha tana zaune a gefen gado da computer akan cinyarta tana danne-danne, ta shiga ta d'aga kai ta kalleta cikin mamaki. "Ya akayi Fa'iza, yaya naga ranki a 6ace, nayi tsammanim yau ranar farin ciki ce a gareki? Fa'iza ta zauna kusa da mahaifiyarta tayi shiru cikin damuwa, sai hawaye ya fara zubowa daga idonta. "Momi ni ma nayi tsammanin hakan ne, sai labarin da Aliyu ya gaya mini ya tayar mini da hankali, wai auransa saura sati guda... Haj. Zaliha ta dafe k'irji cikin damuwa tana salati da
(24)
Salallami. "Amma garin yaya hakan ya faru fa'iza? Bai son kine daman? "Ban sani ba momy, amman alamu sun nuna yana k'aunata, ya kuma k'ara jajjadami mini da bakinsa, sai dai ina zaton na hd'u da shi lokacin da bai dace c, ina nufin na had'u da shi lokacin da yake gab da aure, ya yazan yi momy? Tayi nairai-narai kamar zata rushe da kuka, haj zaliha ta rik'o hannunta tana rarrashinta. "Tabbas naso ace Aliyu saurayine dake zaki auri abinki ke d'aya, domin tunda na ganshi naji ya kwanta mini cikin raina, yafi mubarak komai, baki ta6a saurayin mai nutsuwa da kamalarsa c, ga kuma kyau da cikar haiba, zan so ace ya zamto sirikina domin daga ganinshi za a sami zuri'ia mai albarka da shi, don haka ina goyan bayan kici gaba da sayayya da shi, idan ya kasance mijinki ne babu komai kece a matsayin matarsa ta biyu, zaminin da mace zata tsaya tana cewa sai ita d'aya zata zauna a idan mijinta ya wuce fa'iza, mun shigo zamanin da mata ke buk'atar mazajan aure nutsatsu irinsu Aliyu, wanda kuma sun yi wuya,
Kici gaba da son aliyu, kibi duk hanyar daza ki zamto matar sa ko ta biyu ce." Fa'iza ta gyad'a kai cikin murmushi da jin dad'i "amma momy cki ganin idan yayi aure matarsa za ta raba ni da shi? "ko d'aya bana ganin haka, da ace zata iya rabaki da shi da yanzu ya kamata, domin duk macen da bata kama mijinta a waje ta hanashi kallon wata ko zuwa gurin ta kafin aure ba, da wuya bayan aure ta katangeshi ga hakan." Farin ciki ya cika fa'iza cikin murna take fad'in "Nagode Momy, shi yasa nake k'ara sonki wallahi." sukayi dariya gabad'ayansu cikin jin dad'i. Daga 6angaran Alh. Musa da Aliyu sun ci gaba da gudanar da harkar bikinsu yanda ya kamata, domin aliyu ya gayyaci duk wani mutum da ya ta6a sani zuwa d'aurin auransa, domin yana son farantawa baffansa rai. "yan'uwansa dake garin da matansu da yaran su har d'inki yayi musu kusan kala uku uku, domin burinsa bai wuce ganin sun fita fes ba suma. Haj. Bilki da hanan sun yi duk abin da zasu iya sai dai a banza, saura kwanaki uku ya rage yanzu biki har yan'uwan aliyu
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(25) har 'yan uwan aliyu sun iso, babu mahaifiyarsa sai abokiyar zamanta, da matan 'yan uwansa maza dake garin, kamar yanda aka tsara gidan, can 6angaran saukar baki ya kai su, nan kad'ai suka gani amman sun cika da murna da farin ciki, babansa da 'yan uwansa sun yi ta satin gidan da mamakin irin daular da Aliyu yake ciki, shikam babu abin da yake so illah idan ya dawo daga gurin aiki yazauna a cikinsu ayi ta hira cikin jin dad'i. Lanto da yaranta mata dake aure d'aki d'aya aka basu, sai kuma sauran dangi suma suka d'auki d'aya, wuni suke yi hirar gidan da sha'awar shi. Salame har sambav take tana fad'in ita wallahi da za a barta anan zamanta zatayi, domin bata sha'awar komawa garinsu, lanto tace ai ba ita kad'ai ba ko itama ta samu dama, zama zatayi, don da ace auwalu ko sabi'u ke da wannan babu abinda zai mayar da ita k'auye kwata-kwata, haka suke wuni hira da santin gidan. Saura kwana biyu d'aurin aure, aliyu yana k'ok'arin parkin din motarsa kiran fa'iza ya shigo cikin wayarsa, ya sami guri ya tsaya
Sannan ya d'aga kiran yana murmushi. "ka zama busy ango, ina ta lissafi jibi ne abin ko? Abin da ta fara gaya masa kenan. Yayi dariya cikin jin dad'in yanda ta damu da shi yana fad'in "yaya akayi kika rik'e lissafin fa'iza? Tana dariya ta bashi amsa "yaya kuwa ba zan rike ba, yanzu ma kira ne domin sanar da kai ina son na shiya fati, idan har amarya bazata damu ba. Gabansa ya fad'i, lallai fa'iza bata san irin auran dazai yi ba da batayi wannan maganar ba, amma sai ya daure yace mata. "Kinga ba nason bidi'a, amaryata ustaziyya ce bata son fati. Yanda ya fad'i maganar batji dad'i ba, amman dai ta fara sabawa da halin aliyu, don haka ta wayance tana fad'in. "Shike nan tun da ba a buk'atar gudummawata, a fad'a mini abin da ake buk'atar nayi. Cikin dariyar yaci gaba da magana "kiyi adda'u kawai ya isa." shi kenan zan yi, bari na barka naga kamar kana kusa da amarya ne, ko kuma kana gab da isa gurinta, don na kula baka son maganar ma, sai da safe." yaji babu dad'i, sai dai hakan shine gaskiyar abinda ya kamata
(26) yayi mata, ya kashe wayar sannan ya nufi cikin gidan kai tsaye. Ya sami 'yan uwansa ana ta hidimar biki, dad'i ya cika ransa, ashe shima zai ga irin wannan ranar zai ga 'yan uwansa fal sun cika gida. A can gidan alh. Musa ma biki ya kankama domin yan uwansa dana haj. Bilkisu sun cika gida ana ta hidima, duk yanda haj. Bilkisu taso nunawa hakan ya gagara, dole ta saki jiki ta fara hidama da mutane, domin gidan ya cika mak'il, anyi jeren kaya na gani na fad'a, alh. Musa yayiwa hannan kaya irin wanda ake yayi, komai ake yayi a wannan lokacin sai da aka saka a gidan, gidan 6angare biyu ne, amman wancan d'aya ba a kammala shi ba, sai kuma 6angaran baki, sashinta manyan falo ne biyu da d'akunan bacci guda uku, sai k'aton kicin, ko ina sai da aka cika shi da kayan alatu, masu jere sun koma gida suna ta santin gidan sosai. A 6angaran hannan ko tsakar gida bata fitowa balle a sanya ran zata yi waniabu, duk masu gyaran jiki da magungunan mata da suka zo gidan bata kalli ko d'ayaba, idan aka matsamata da magana ma
Sai ta saka kuka, don haka dole aka tattara aka watar, daran ranar daza a d'aura auranta da Aliyu ne kiran waya ya shigo wayarta, mamaki y kamata domin kiran Mansur ne cikin rawar jiki da murna ta d'auki wayar, kusan sati biyu ke nan mansur ya kashe wayarsa, ta rasa yanda zata same shi, ta tura sak'o babu adadi amman bai ta6a dawo mata da amsa ba. Cikin farin ciki ta fara magana "haba my man, yaya zaka mini haka, kasan halin dana shiga sabo da rashin ka kuwa?
Mansur yana zaune akan kujera, cikin 6acin rai yake matuk'a, tun ranar da hanan ta bar gidansa, ko k'ofar gida bai fita sai dare ya raba, sai ya kulle kansa cikin gida yayi ta shaye-shaye ya kashe wayoyinsa gaba d'aya, iyayansa kawai ya turawa sak'on yayi tafiya, don kar hankalinsu ya tashi, sai yau ya kunnata. "Me zan miki hanan? Me kike so na miki? Ya tambaye ta cikin sanyin muryar daya k'ara tayar mata da hankali, tabbasa tana son mansur iyakacin soyayya. Cikin rawar baki taci gaba da magana "kayi hak'uri man, kai kad'ai kawai nake so,
(27) wallahi ban ta6a son aliyu ba, ka yadda da hakan." Nb yadda Hanan, kin san daga gobe shi kenan kin zama matarsa, kin rabu dani, bazan k'ara ganinki ba har abada? Yana magana kamar zai fasa kuka. Waye ya gaya maka haka? Ta bashi amsa cikin gaggawa, ta d'ora cikin sauri "na yadda zan auri aliyu, amma wallahi har abada ba zai sami abin da yake buk'ata daga gareni ba, sannan kamar yanda momy ta sanar dani zan je gidansa na wani lokaci ne, ka ka kasance cikin shiri daga nan zuw wata guda domin iyakacin kwanakin dazan yi a gidan ke nan da dawo maka, kai ne mijina uban 'ya'yana. Wannan labarin ya d'an faranta ran mansur har ya sanya shi mik'ewa zaune yana d 'an murmushi "da gaske haka momy tace miki hanan? Ya tambaya cikin sambatun mayen buguwa. "Haka tace min, na kuma yi maka alk'awarin yanda na shiga gidan aliyu haka zan fito maka, ka kwantar da hankalinka masoyina. Yanda take magana cikin kwantar da murya ya bashi kwarin gwiwa kwarai da gaske, har ya dinga jin kamar daga an d'aura auran gobe shike nan komai
Ya wuce, sun jima suna hira tsakaninsu ta jin dad'i da soyayya, basu san dare yayi ba sai da bacci yaci k'arfin idanunsu sannan suka kwanta.
ALLAH YAYI AURE DA MARA KWABO Wannan shine karin magana dayafi dacewa da auran Aliyu da Hanan, domin duk gaba da k'iyayyar da aka nunwa auran sai da aka d'aurashi, auran daya tara d'umbin jama'a, duk da aliyu yana cikin damuwa akan auran, amman ganin d'inbin jama'ar da suka taru gurin auransu ya sanya ya dinga jin wani abu kamar bashi ba, 'yan uwansa murna har kunne, haka nan alh. musa yana jin kamar bashi ba da sauran ranar farin ciki bayan wannan, an d'auran aure cikin farin ciki da jin dad'i.
ana gamawa aka fara fito da takeaway daga cikin gida kala kala mutane suka fara ci, ma su busar algaita da marok'a suka shiga aikinsu suma. a wannan ranar ne babar yayarsu haj. bilkisu haj. barka ta matsawa hanan akan dole tayi kwalliya, babu yanda zatayi domin tana shakkar aunty nata don haka ta hak'ura 'yayanta sune suka yi mata kwalliya, da kyar ta fito tsakar gidan tana cin
Like · React · Reply · Report · 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(28) da kyar ta fito tsakar gidan tana tacin magani ana d'aukar hotuna. Aliyu bai yi niyyar shiga cikin gidan ba, domin yana tsoro gamonsa da uwar matarsa da ita matar, alh. Musa yace masa yazo su shiga cikin gida su gaisa da mutane. Yana shia idon sa kan amaryarsa ya fad'a, kwalliya da akayiwa hanan ta amsheta matuk'a, duk da ranta a 6ace yake bata ko dariya amman tayi kyau, ita kam kallo daya tayi masa ta d'auke kanta domin ko ganin sa bata k'aunar yi. Alh. Musa ne ya kamo hannun aliyu suka tsaya aka d'aukesu hoto shida hanan wacce taso gudu amma yayar mahaifiyarta hanata motsawa, aka yi ta musu hotuna kala-kala, bayan alh. Ya wuce nan ma tace kowa ya fita aka yi hoto daga Aliyu sai Hanan, hanan tana jin kamar ta had'iyi zuciya ta mutu ta huta, sai dai yaya ta iya. Bayan gama hoto aliyu ya fara zagaya dangi yana gaishesu, sai dai abin daya tayar masa da hankali bai wuce k'in amsa gaisuwar sa da haj. Bilkisu tayi ba, yana shigowa falonta yana durk'usawa yana fara gaishesu ta mik'ik'e tsam tabar gurin,
Jikinsa yayi sanyi haka ya ashi ya fita, wannan shi ne abin da yasare masa farincikinsa na ranar. Duk da babu wani shirin biki ko shagali da za a yi bayan d'aurin auran, haj. Bilkisu ta cika da mamaki sanda suka ji sak'on alh. Musa na cewar amarya ta shirya anjima zaikaita d'akin mijinta, tun daga sannan hanan afara kuka, a son samunta babu wani abu da za tayi na shiri, dole antinta a sanyata gaba tayi wanka ta shirya. Bayan an gama shirya ta anty batula tazo ta kama hannun hanan ta nufi wani d'aki da ita, daga ita sai haj. Bilkisu cikin d'akin, suna shiga suka dase k'ofar garam, hanan ta rushe da kuka cikin bak'in ciki. "don Allah ki daina kuka, d'aura auranki da aliyu ba yana nufin kin zamata sa bane fa, sau nawa ana d'aura auren da ake so da k'auna ma ya watse balle na ku auran kiyayya. Anty batula ke fad'in haka. Haj. Bilkisu tayi kwafa tana fad'in "ki gaya mata dai, tuntini abin da nake gaya mata kenan, ta kwantar da hankalinta, rayuwar auranta a hannunta take, idan kika so a daran yau zaki murkusheta
(29)ki karheta hanan." hanan ta d'an rage kukan da take yi, anty batula taci gaba da magana "ki naji ko? Kamar yanda muka gaya miki, rayuwar auranki daci gabanta yana hannunki, don haka kar ki sake ki bar wannan aure ya shiru ko ina, da kin shiga sati guda yayi yiwa ki gaggawa dawowa gidan nan da takardar sakinki, kar kuma ki yadda da saki d'aya sai ya baki uku, wanda hakan shi zai baki damar auran wanda kike so, kin ji ko? Sun jima suna mata hud'uba kala-kala sai da alh. Musa ya shigo harabar gidan yana neman amarya sannan suka fito da ita, bai kula kowa ba ya kama hannun hannun hanan suka yi hanyar fita hanan tana kuka cikin karaji, a motarsa ya saka ta, sai haj. Barka da ya d'auka ta zauna a bayan motar, sauran motocin 'yan kai amarya suka rufa musu baya. Sai daya kai hannan har cikin d'akinta, ya jima yana mata nasha sannan ya fito daga cikin d'akin, sai dai babu wani abu da hanan ta d'auka a duk abin da ya fad'a mata, fatanta kawai ya fita ya bata guri, haka suma 'yan kawo amaryar suka kammala dabdalarsu
Suka watse, har dangin mijin da suka dinga leken d'akunan cikin murna da jin dad'i.
Sai da kowa ya watse sannan aliyu ya shigo gidan shi d'aya, kai tsaye 6angaransa ya nufa, yana kallon k'ofar d'akin hanan a kulle, ko da a bud'e take babu abin da zai kai shi balle ya gan ta a kulle, ya kalle, ya kad'a kai ya nufi d'akin da ya zamto na shi ya kullo k'ofa, sai dai yayi ta jiyi yana ganin kamar abin da yayi bai kamata ba, amma yana tsoron abin da zai biyo baya ne, domin bai son 'yan uwansa su san halin da yake ciki da matarsa, duk da gidan yanzu ya rage sai mata kawai, domin mazan ana daura aure ya samar musu mota ya biya kud'i suka yi sallama suka wuce garinsu, wad'an dake garin kuma suka wuce gidajansu. Hanan ta kwanta cikin bak'in ciki da kuka, kamar zata amayar da idanuwanta don kuka, bacci 6arawo ne ya lalla6o yayi gaba da ita. Da sassafe aliyu ya samarwa 'yan'uwansa mota, ya saka su aciki, sun yi ta son ganin amarya amman yace musu bata tashi ba, dole haka suka hak'ura suka tafi bayan ya salleme kowa
(30) sai daya bata d'ari biyar-biyar bayan kud'in motar daya biya, Allah yasa yana da sauran kud'i a hannunsa da abokansa suka dinga bashi gudummawa, sai dayaga tashinsu sannan hankalinsa ya kwanta. Ya umarci maigadi da wani yaro mai gyara masa fulawa dasu gyar 6angaran bak'in gac d'aya, sannan ya koma gida. Lokacin da ya shiga babban falon gidan ya tsaya shiru cikin damuwa, a ransa yana ganin bai kamata ace ya kwana har gari ya waye rana ta d'aga batare da yaga halin da hanan take ciki ba, a k'asan ransa yana shakkar abin da zai biyu biyo baya, domin ya duk abin da yayi sai ya tina gargad'inta garesi. Zuciyar dake bashi shawarar shareta tafi k'arfi don haka ya wuce d'akinsa kai tsaye, bai san me ya kamata yayi ba, bai jin dad'in komai, don

Please Login or Register in order to submit comment