Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya suka fito daga office ɗin domin ƙari sawa ward da Mommyn su Mannah take don kaita wurin Malam mahaifin Dr Jamil...

*WANNAN KE NAN.*





*❗💫ZWANDUN MONSTER'S EMPIRE 👊🔥*




Makeken allon dake can sama kafe a cikin ƙaton wurin da ya fi kama da Hall a ka rubuta hakan da manyan launi kuma ja mai silkin baƙi.

Babban hall ɗin cike maƙil da mutane masu neman Duniya yaran shaitaan waɗan da suka rungume duniyar da kyale kyale dake cikin ta hannu bibbiyu maza da mata baƙaƙe da farare har da ma jajaye. Ko'ina hayaniya ce ke tashi sama sama a ciki kowa faɗin albarkacin bakinsa yake sakamakon yau ne rana ta cika da Shugaban ƙungiyar gaba ɗayan ta da har yau banda shugaba na biyu da a ka kashe kaf cikin members na ƙungiyar babu wanda ya taɓa ganinsa sunansa dai a bakin kowa shi ne JEZIM A.k.a The Shaytaan. (Wa'iyazubillah🤧)

Yau ne Rana da shugaba ya yanke a kan bayyana sabon shugaba na biyu ta yi.


Lokaci guda tamkar giftawar walƙiya komai da ke motsi a wurin da kowa duka mutanen wurin suka yi tsit shiru kakeji Sakamakon takarda da tsuntsaye suka wurgo daga sama da sauri wani ɗan aljani da ya koma sifar Aku irin mai magana ɗin nan, ya ƙari sa tare da ɗaukar takardar dake a nannaɗe ya buɗe tare da fara karantawa a zahiri kamar haka....🌚


*Domin sanin yadda zata kaya mu haɗu a episode na gaba....⚔️🔥😂👊*


Share Fisabilillah ❤️👏



*🔥 RANAR BIYAN BUƘATA 🔥*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

_Perfectly Pen's ✊_

. . Nainarh KD Nkd's . . . ✍️
07067953066.

https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20

_Don't forgot to follow my WhatsApp channel 👏❤️_
.
E. 30.


“A bisa duba da cancantar matsayi da a ka yi, kai tsaye an naɗa Sanam a matsayin sabuwar shugaba ta biyu a ƙungiya, kuma nan da kwanaki biyu za'a gudanar da gagarumin shagali na munar samun sabuwar shugaba ta biyu a ƙungiyar Zwandun Monster's. Sannan a ranar ne za'a bata kambi na shaidar zama shugaba ta biyu a wannan ƙungiyar...”

Daga haka rubutun ya ƙare, Akun ya koma wurin da yake bayan ya naɗe takardar, yayin da gaba ɗaya Hall dake maƙare da mutane mabanbanta daga sassa daban daban na faɗin Duniya ya ɗauki wani irin hargitsi da hayaniya na mutanen dake ciki kowa faɗar albarkacin bakinsa yake, cike da tsananin mamaki na jin wacce a ka naɗa matsayin sabuwar shugaba wato Sanam yarinyar da ko shekaru Biyar ba'a cika ba da kawo ta ƙungiyar, e mana kawota tun da tana cikin halin jinya a ka kawo ta, sai da ta shafe wata da watanni sannan ta warware sai dai fa ta manta gaba ɗaya bayanta, bi ma'ana memory nata ya goge ta manta sunanta da komai nata a wancan lokacin. Shi ne yanzu kuma za'a bata ragamar shugaba ta biyu a ƙungiyar. Lallai da bala'i...🔥 Domin kuwa old members na ƙungiyar sam sun ƙi aminta da wannan lamarin.


Wannan shi ne dalilin cecekucen domin kowa ya gama sadaƙarwa da bari a kan tsakanin mutane ukun nan wato Mr Aabdar Dawlah da Alhaji Haashir sai kuma Alhaji Umair Ubaydullah a cikinsu dole ne za'a zaɓa ɗaya a naɗa matsayin sabon shugaba na biyu duba da irin gudummawar da suka bawa ƙungiyar shekara da shekaru sun yi ma ta hidima wanda wannan lokacin ne suke saka rai da samun sakamakon hidimar da suka ma ta, ta hanyar naɗa ɗaya daga cikin su matsayin sabon shugaba na biyu wanda har hakan ya haddasa ƴar gwarya-gwaryar rashin fahimta a tsakanin su domin kowa a cikinsu so yake ya zama shi ne za'a naɗa matsayin sabon shugaba na biyu a ƙungiyar, wanda hakan zai zama shi ne ticket na haɗuwar sa da shugaba na farko wato JEZIM wanda hakan shi ne burin ko wane member dake a ƙungiyar Zwandun Monster's...🔥👊



....
Su uku ne a cikin Ɗakin kowa babu abin da yake sai sakin numfashi cike da ɓacin rai na abin da ya faru a yau, shi ne suka a je ƴar gabar da ta shiga tsakaninsu dalilin son zama shugaba na biyu da kowannen su keyi bayan wannan hukunci da a ka yanke daga sama.
Sun taru ne a yanzu su ukun a wannan Ɗakin nasu na shawara da suka saba tattaunawa lokaci zuwa lokaci domin neman mafita. Sai da suka shafe aƙalla awa guda a hakan ba tare da kowa ya ce komai ba, kan su ya ɗau zafi neman mafita kawai hajaran majaran suke a halin yanzu domin ba zata taɓa saɓuwa ba wai bindiga a ruwa, ace suna ji suna gani yarinyar da su ne sanadiyar shigarta ƙungiyar shi ne yanzu za'a naɗa ta matsayin shugaba ta biyu yarinyar da ba uwar abin da take tsinanawa ƙungiyar ko jini bata taɓa sha ba, abin da za'a ce tana bawa ƙungiyar gudunmawa shi ne ta fannin na'ura kwararriya ce ta ƙarshe fannin sanin kan na'ura ko wacca kala ce kuma tantiriyar mai kaifin basira ce duk wani tsara tsare na ƙungiyar ƙarƙashin ta yake gudana tana bada gudunmawa ta hanyar ɗauke hankalin jami'ai ko sauran mutanen daga kan ƙungiyar shi ya sa har yau shekara da shekaru ba'a ankara da ƙungiyar ba duk ɓatar da take yi, sai kwana kwanan nan da abubuwa suka fara rincaɓewa, yanzu haka da a ka yi zaman nan har a ka bata muƙamin bata ma a wurin domin ba kowanne taro na ƙungiyar take halarta ba...


Doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya fara safa da marwa yaje ya dawo hannayensa maƙale a bayansa cikin rashin abin yi sai can ya ce.

“Abin yi shi ne kawai mu kawar da ita muddun munaso kujerar shugabancin ƙungiyar ta kasance hannun ɗaya daga cikin mu tofa sai mun fara kawar da ita dama ai mune silar zuwanta ƙungiyar a shekaru huɗu baya idan bazaku manta ba lokacin da Prof Bakori ya zama silar komai....”


Alhaji Haashir ya ƙari sa maganar yana duban ƴan uwan neman Duniyar nasa. Gaba ɗaya suka yi shiru suna nazarin maganar sa, an rasa mai magana, sai can shima Mr Aabdar Dawlah ya ce.

“Hakan shi ne daidai kawai dama ai mune muka kawo ta yanzu kuma tun da ta kawo cikas a cikar Burin mu kawai muyi gefe da ita dama tana bamu ciwon kai tabi ta mamaye komai da ko'ina cikin shekaru huɗu ta yi ƙaurin suna, ƙungiya kowa ya san da zamanta, mu da muka kawo ta kuma muka daɗe muna ma ƙungiyar hidima ba'a gama sanin mu ba kamar ita.”

Ya kai ƙarshen maganar yana cizon yatsa cike da takaicin ta, ita ba Sanam yarinyar da sune suka yi silar shigowarta ƙungiyar amma yanzu nema take ta zame musu ƙarfen ƙafa.

“Yadai Alhaji Umair kayi shiru bakace komai ba kodai hukuncin da muke yanke a kanta bai maka ba?.”

Mr Aabdar Dawlah ya tambaya ganin yadda Alhaji Umair ɗin ya yi shiru yana sauraren su ba tare da ce musu komai ba.


Ya saki wata bazawarar dariya yana dubansu gaba ɗaya sannan ya fara magana.

“Ku yanzu a ganin ku kawai dan kun yanke zaku kawai da ita daga dogon Duniyar sai hakan ta kasance?.”

Ya yi musu tambayar yana dubansu bai dena murmushi ba hannunsa a baki kamar yaro, a zahiri zaka ɗauka dariya yake domin nishaɗi, amma a baɗini tafarfasa da raya muggan abubuwa da dama wannan bak'ar zuciyar tasa take.

Ciki rashin fahimta suke dubansa kafin Alhaji Haashir ya ce.

“Da gudu ma ko kana tunanin akwai abin da zai hana faruwar hakan?.”


Ya kuma darawa sannan ya ce.

“Sosai ma kodai kun manta wacece ita ce a halin yanzu?. Bari na tuna muku, matsayin shugaba ta biyu take wanda hakan ke nufin basirarta da ƙwaƙwalwarta da wayon ta da duk wani motsin ta zai riɓanya sama da baya sakamakon manyan baƙaƙen aljanu da zasu kasance tare da ita domin bata ko wani irin taimako da take buƙata..”


Gaba ɗaya shiru suka yi cikin rashin abin yi jin bayanan sa. Kafin Mr Aabdar Dawlah ya saki wata muguwar dariya ya ce.

“To ai idan an san wata ba'a san wata ba, ai ba kai tsaye zamu yi ma ta abin da zamuyi ba, ta bayan gida zamu bi da siyasa har mu samu muyi nasara a kan ta, ko dai kun manta a Duniyar kimiyya muke yanzu?.”

Ya ƙari sa maganar yana kuma sakin wata shu'umar dariya yana kuma dubansu.

“Mr Aabdar Dawlah Abokina shegen kaya faɗa mana mene ne plan naka a kan ta?.”

Cewar Alhaji Umair yana sakin dariyar shima.

“Ku matso kuji domin abin sirri ne.”

Ya faɗa yana musu alama da hannu a kan su matso. Ai kuwa ba musu suka ƙari sa tare da haɗe kai wuri ɗaya suka yi zobe, nan yake sanar da su mummunar shirin da ya shirya wanda zai yi ajalin Sanam. Gaba ɗaya sun gamsu da maganar nasa ɗari bisa ɗari nan suka ci gaba da shirya hanyar da zasu bi wurin ganin sun hallaka Rayuwar Sanam sun ɓatar da ita daga tunanin kowa an gama da babinta. Sun yi ma kan su alƙawarin ba za su ƙara magana a kan ko wanene a cikinsu zai zama shugaba na biyu ba, har sai sun fara gamawa da babin Sanam tukunna. Sai dai fa kowannen su akwai mummunar ƙudiri da yake ayyana wa a zuciyarsa kuma ya ɓoye, a haka dai taron nasu ya tashi a kan zasu shirya haɗuwa da ita kuma a lokacin ne zasu gudanar da mummunar ƙudirin nasu a kan ta...🔥


_/Duk fa wannan abu ya faru ne a Ranar da Lulu ta yi ma waɗan Samari dukan mutuwa./_




*. . 24 Hour's Later. .*



*LULU POV.*


Bata bari motar da ta kawo su hospital ɗin Ramla da ta tuƙo ta gama dai-dai parking ba, Lulun ta fito da saurin ta domin ta gaji da kallon harara da Maiji ke ma ta, ita kuma taƙi magana. Tafiya ta fara bayan fitowarta daga motar sai dai shan gabanta da Maiji ta yi shi ne abin da ya dakatar da ita daga tafiyar da take yi, magana Maiji ta fara tana dubanta muryarta da alamar fusata da lamarin Lulun.

“Wai Lulu mene ne kike nufi ne me ya sa kika ƙi kulani sannan me ya sa kika yi ma Irshad haka kin san damuwar da ya shiga a kan ki kuwa?. Sannan kin zo kin daki waɗan can samarin kin yi musu illah kuma babban tashin hankalin har da Yaron Mr Aabdar Dawlah a cikinsu wai bakya tunani ne a kan abin da zai biyo baya baki damu da rayuwar ki ba kwata kwata?.”

Maiji ta ƙari sa maganar tana dubanta tare da tambayarta duka a cikin ɗa ga murya take maganar yayin da Lulu ta yi shiru tare da harɗe hannu bibbiyu tana sauraren ta har sai da taji ta yi shiru alamar ta kai aya. Sannan Lulu ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe baki da niyyar magana, sai dai kuma me?. Maganar da suka jiyo ta bayansu shi ne dalilin hanata faɗar abin da ta yi niyya.

“Ta ya ya kuwa zata damuwa da kanta bayan ta kasance Killer oh I mean murder wacca kisa bata ɗauke sa a bakin komai ba?.”


Gaba ɗaya su biyun har da ma Ramla da Neina da suka ƙari so wurin a yanzu suka juya suna kallon mai maganar.

Officer Umnia ce tsaye sanye cikin baƙaƙen kaya nata na aiki da gaban rigar dake jikinta a ka rubuta D.S.S da manyan baƙi launin fari.

Tafiya ya fara har sai da ta ƙari sa gaban Lulu sannan ta dakata tare da ciro handcuff ta nufa hannun Lulu tana faɗin.

“Yu're under arrest.”


Da ƙarfi gaba ɗaya su ukun Neina da Maiji sai kuma Ramla suka maimaita abin da ta faɗa bayan ta saka ma Lulu ankwar a hannu. “Under arrest kuma?.”

Cikin tashin hankali Maiji ta ƙara da faɗin.

“A kan wani laifi zaki kamata kafin nan ma ina shaidar da zai tabbatar keɗin jami'a ce?.”

Officer Umnia ta dubeta tana Male baki tare da sakin wani lalataccen murmushi ta kuma duban jami'an dake tare da ita, kana ta ciro I.d ɗin ta nuna ma ta.


“Ina fata hakan ya wadatar sannan da kike tambayar wani laifi ta yi, bani da zarafin faɗa muku komai gaba ɗaya a yanzu sai dai ku biyo ni D.s.s headquarter domin sanin dalilin, ina fata kunsan address ɗin?.”


Ta faɗa tana mayar da baƙin Glass nata da ta cire sannan taja hannun Lulu suka ƙari sa mota, Lulu ta shiga ciki ba tare da gardama ba.


“Kar ki damu babu abin da suka isa su yi miki kinji Samra zamu fitar da ke da iznin Allah.”


Cewar Neina da ta ƙari sa wurin motar a kiɗime suda suka zo asibiti duba yarinyar da Lulu ta taimakawa a jiya gashi an ƙare da kamata ko garin ya ya wannan lamarin ya kasance?.


(Shi ne abin tambayar????🥲🙂🤐)


Officer Umnia da ta buɗe murfin mota zata shiga gidan gaba ta juyo tare da duban Neina da ta yi maganar, ta girgiza kai sannan ta ce.

“Mu jami'ai ne ba makasa irin ta ba, saboda haka ki kwantar da hankalin ki ba zamuyi ma ta komai ba, muddun ta amsa laifukan ta.”


Tana gama faɗar hakan ta shiga motar. Yayin da ta bar su tsai tsaye cikin tashin hankali da rashin madogara ita Ramla ma har ta fara hawaye dan ta sadaƙar gadar zare kawai wani ya ƙulla musu gashi yanzu an kama Lulu. Maiji ma daurewa kawai take yi amma ji take kamar ta fasa ihu ko ta samu zuciyarta ta dena tafarfasa da take yi. Haka take ma ta ɓangaren Neina cikin matuƙar tashin hankali take sai dai ta yi matuƙar ƙoƙari wurin ɓoye hakan don kar su taru su zama ɗaya, yanzu mafita zasu nema ba wai lokacin kuka ne yanzun ba dole ma Lulu ta fito kuma a yau idan ta ce yau e yau ɗin take nufi bi ma'ana kota halin ƙaƙa....🔥


_Wai mene ne ke faruwa nene? Garin yaya hakan ta kasance? Kuna da buƙatar fita daga wannan ruɗanin ko? To yana da kyau mu koma 24 hour's back domin gane ainihin mafarin lamarin._



*. .24 Hour's Back. .*



*-100, Lake Chad Crescent, Maitama, Abuja, Nigeria.*


*Umnia POV.*


“Larai saukar yaushe kuma aina zata ma kin manta damu ne daga zuwa duban gida.”


Umnia ta ƙari sa maganar tana saukowa daga benen cike da mamakin ganin Larai tsohuwar amintacciyar mai aikinsu da watannin baya ta tafi ƙauyen su domin ganin gida tun daga lokacin kuma basu ƙara jin ɗuriyarta ba sai yau shi ne dalilin mamakin Umnia.


“Ai Yallaɓiya abubuwa ne da dama suka faru bayan komawata gida shi ne dalilin da ya sa kikaji ni shiru duk waɗan nan watannin.”


Matashiyar Dattijuwar matar da Umnia ta kira da Larai ta faɗa hakan tana ɗan murmushi.


Cike da kulawa Umnia ta dubeta sannan ta dubi agogon dake maƙale a tsintsiyar hannunta ganin ta makara da yawa ya sa ta ce.

“To Allah ya shige mana gaba a al'amurra gashi kin zo mutuniyar taki wato Bittu bata nan Daddyn ta ya fita kai ta school nasan ma yana hanya ni yanzu zan wuce ki huta kawai na Ranar yau.”

Ta faɗa sannan ta yi gaba bayan Larai ta amsa ta tana godiya.


Mota Umnia ta shiga driver yaja direct su wuce headquarter na D.s.s koda isarsu sauri sauri take tafiyar domin yau kam ta makara haɗuwa suka yi da Kiara suka tsaya gaisawa Kiara ta ci gaba da faɗin.


“Ai kuwa kina da baƙuwa tun ɗazu tazo ta ce wurin ki tazo ɗiyar Prof Bakori ce wai tazo ne domin bada information a kan mutuwar mahaifin nata.”


Da jin abin da Kiara ta faɗa yasa Umnia faɗin.

“Okay tana ina yanzu?.”

Ta tambaya da sauri.

“Ga ta can ma.”


Cewar Kiara tana ma ta nuni da inda budurwar take tsaye.

“Okay sai mun haɗu zuwa anjima bari na ƙari sa naji da mai tazo.”


Cewar Umnia sannan ta nufa inda Budurwar take da yake dab da Office ɗin ta ne shi ya sa ta ce ma Budurwar su shiga ciki.


🔥🔥🔥





*🔥 RANAR BIYAN BUƘATA 🔥*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

. . Nainarh KD Nkd's . . . ✍️
07067953066.

_Perfectly Pen's ✊_

.https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20


_Don't Forget To Follow My What'ssapp Channel_👏🤍
_
E. 31.

“Madan nazo ne domin bada information a kan mutuwar mahaifina Prof Bakori.”


Budurwar mai suna Jalilah ta faɗa bayan ta zauna a kujerar Office ɗin officer Umnia ɗin suna fuskantar juna.

“Wani irin information ne a tare dake?.”

Officer Umnia ta tambaya cike da kulawa.

“Nasan fuskar ɗaya daga cikin mutanen da suka zo gidan mu a wancan daren, saboda haka zan yi muku bayanin ta nasan zai taimaka muku.”

Budurwar ta kuma faɗa tana duban officer Umnia ɗin domin ita Burin ta bai wuce a kan a kamo waɗan mutane da suka zo gidan su ba a wancan daren har suka yi sanadiyar mutuwar mahaifin ta duk da taji daga bakinsa na munanan abubuwa da ya aikata, amma a hakan ta toshe kunne ita dai a hukunta waɗan da su ka zama dalilin mutuwarsa. Domin ita ƙaramin tunanin ta shi ne ai da'ace wancan daren Ranar basu zo musu gida sun titsiye mahaifin nata Prof Bakori har ya faɗa musu komai ba, ai da bai mutu ba, saboda haka ita a nata ƙaramin tunanin sune silar mutuwarsa.


Da jin abin da budurwar ta faɗa ai kuwa nan da nan officer Umnia ta yi waya ba'a ɗauki lokaci ba mai zane ya ƙari so nan ya tasa Jalilah ta fara zayyano masa yadda fuskar wannan budurwar ɗaya daga cikin mutanen da suka je gidan su a wancan dare. Dalilin da ya sa Jalilah ta gane fuskar ɗaya daga cikinsu, shi ne a lokacin da Aminullah ya cire face mask dake fuskar budurwar bashi kaɗai ba hatta ita ma taga fuskar budurwar kuma a fahimtar da ta yi ma lamarin, da alama ita ce shugaba ma wannan shi ne.


A lokacin da mai zanen ya gama zane fuskar da Jalilah ta siffanta masa. Kuma da yake shi ɗin kwararre ne wurin zane sai ya zo daidai ba'a samu matsala ba. A lokacin tsayawa Umnia ta yi a gaban zanen tana kallon fuskar budurwar da a ka zana.

Nan da nan ta tara jami'ai kwararru a ka shiga bincike a kan inda za'a gane ina ita wannan budurwar da a ka zana take. Da yake jami'an nata sun horu ta fannin aikinsu kuma kwararrun masana na'ura ne su ɗin shi ya sa ba'a ɗauki dogon lokaci ba suka gano ainihin wacece wannan budurwar ta na'urorinsu masu ƙwaƙwalwa da kuma bayani a kan ta duk da ba yadda suke so suka samu ba sannan a lokacin da suka gano ainihin daidai wurin da take a wannan taƙin ne officer Umnia ta ɗiba jami'an ta domin case yazo ƙarshe nan suka dumfami address ɗin wurin da take ta hanyar amfani da map har suka cimma ta daga nan komai da ya faru ya biyo baya...


*Present Day. . .*


Suna nan tsaye curko curko cikin rashin madogara sai ga wata mota maroon color ƙirar companyn Kia ta shigo hospital ɗin kai da ganin yadda mai motar ya shigo a sukwane kasan ba lafiya ba. Fitowa Mahbub ya yi da saurin sa ya ƙari sa wurin da suke tsaye curko curko. Ramla da ganin sa ya bata mamaki domin ta tuna sa ta sha re hawaye lokacin da ya ƙari so yana faɗin.

“Allah ya sa ban makara ba ina Lulu take?.”

Cike da tsananin mamaki gaba ɗaya suke dubansa jin abin da ya ce.

“Kamar ya ya Allah ya sa baka makara ba, sannan kasan Lulu ne a'ina kuma waye kai?.”

Maiji da take iya wuya ta jero masa tambayoyin tana dubansa.

Shafa kai ya yi yana lumshe ido sannan ya buɗe alamu dai sun tabbatar ya makara ke nan, sam bai so hakan ba, da ƙarfi ya kai ma iska naushi idanunsa sun yi jajur. “Me ya sa hakan take faruwa?.”

Ya yi tambayar a fili kuma da ƙarfi kai daga jin muryarsa kasan a fusace yake daidai wannan gaɓar.


“Bawan Allah ko zamu iya sanin wanene kai da dalilin da yasa kake neman Samra.”

Neina ta yi masa tambayar cikin sanyin murya tana dubansa. Yayin da ya ɗa go ya kalle ta at the first time ya gane matar ita ce tsohuwar matar abin harinsa wato dai Alhaji Haashir, duk da cewa bai taɓa ganinta a zahiri ba sai a hoto amma ya gane ta. A hankali ya furta.

“Labarin mai tsawo ne.”


Daidai lokacin kuma motar Irshad da ta shigo hospital ɗin ya ƙari sa wurin tsaye curko curko, tare da parking a gefe, sannan ya fito shi da wata mata da basu san ta ba, abin da yake a zahiri shi ne, Maiji tana da lambar Irshad jiya ta karɓa to ɗazu ya kirata bayan da jami'an nan suka tafi da Lulu sai take faɗa masa abin da yake faruwa.


“Ina take?.”


Irshad da ya ƙari so wurin a sukwane ya tambaya yana dubansu.

“Jami'ai sun tafi da ita zuwa headquarter nasu.”


Maiji ta basa amsa don kuwa yanzu ba wani ɓoye ɓoye komai ya caɓe.


“Pooh wai mene ne yake faruwa ne wacece kake nema?.”


Aunty dake tsaye gefansa ta tambaya tana cikin ruɗi dan ta kasa gane komai ita da ya tuƙo ta domin zuwa wurin Umnia don akwai Magana mai muhimmanci da suka fara jiya ta waya basu ƙari sa ba shi ne ita kuma ta kasa jure har sai Umnia ta tashi daga wurin aiki sannan ta je su ƙari she maganar, to shi ne fa Auntyn ta nema Irshad da ya yi driving nata zuwa D.s.s headquarter ɗin suna a hanya ne bayan ya kira Maiji take faɗa masa abin yake faruwa shi ne fa kai tsaye ya yo hospital ɗin da ita.



“Zan yi miki bayani daga baya Aunty Labarin da tsayi, babu lokaci a yanzu.”


Ya faɗa yana ƙoƙarin kiran lambar Umnia bayan ya ciro wayarsa a trouser pocket nasa.

“Me kake ƙoƙarin yi ne Irshad ka barta kawai domin a halin yanzu Rayuwarta yana cikin hatsari zaman ta a can shi ne tsirarta zuwa nan da wani ɗan lokaci.”


Galala Irshad ya yi yana duban Mahbub da ya yi maganar sai kuma ya daure cikin muryarsa da a yanzu in'inar ta ragu da kaso 75% cikin 100% ya ce.

“Saboda me kace Rayuwarta tana a hatsari?. Wai menene yake faruwa ne can you All explain to me, what is really happening?.”

Ya yi musu tambayar da ƙarfi cikin wata iriyar murya da batayi ko kama da tasa ba, yana kuma dubansu gaba ɗaya.

“Su kan su yanzu basa cikin nutsuwar da zasu yi maka bayani domin suma ba komai suka sani ba ko nace suke ganewa ba a yanzu domin suna cikin ruɗani a kan ta yadda jami'ai suka sama information har suka kama ɗaya daga cikin tawagar su wato Lulu, amma bari nayi maka bayani.”


Mahbub ya kuma faɗa yayin da gaba ɗaya suke dubansa da tsananin mamaki an ma rasa mai tanka masa har ya fara magana kamar haka.

“Dalilin da ya sa nace Rayuwar ita Lulu yana a hatsari shi ne samarin da ta yi ma duka har da rauni a jiya cikinsu akwai yaron Mr Aabdar Dawlah ina tunanin kunsan shi domin ba ɓoyayyen Mutum ba ne a ƙasar nan baki ɗaya. Ta yi ma yaron nasa mai suna David babbar illa a gabansa wannan dalilin ya sa Mr Aabdar Dawlah ya fusata har yake ƙoƙarin aikata wani abu da ka iya zama nadama nan gaba a garesa bayan gaskiya ta bayyana, ya saka an fara farautar Rayuwarta a yanzu haka, sai a ka yi katari jami'ai sun tafi da ita shi ya sa nake tunanin wata ƙila zata fi samun tsaro a hannunsu.”


Gaba ɗaya kansu ya kulle da jin bayanan sa maimakon fahimtar sa sai ma ƙara shiga ruɗani da wasunsu suka yi. Ita kuwa Aunty daga jin sunan da ya ambata, nan take cikinta ya yi wani irin hautsinewa gabanta ya yi mummunar bugawa da ƙarfin da ya sa sai da ta kusa kifawa ƙasa cikin tsananin firgici da tashin hankali.
Da bala'in sauri Neina dake tsaye dab da ita, ta tarota tana ma ta sannu.
Yayin da ita kuwa Aunty babu sunan da ke

Please Login or Register in order to submit comment