Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raye ma?
5. Wane ne makashin commissioner mene ne dalilin sa me yasa su Samra suka so a ce su ne suka ga bayansa?
6. Wanene Jaish?
7. Wacece Annabella?
8. Ina Labarin Tamannah ?
9. Ina Labarin mutumin da Ramla ta haɗu da shi harta kusa kaɗesa?, shin Murmushin me ya yi a wancan lokacin?
10. Da gaske aljanu ne a tare da Samra (Lulu) har suke umartatar ta sha jini?
11. Mene ne Labarin Safiyya (Aunty)
12. Mene ne ya faru da Hamraz bayan rabuwar sa da su Umnia
13. Shin Umnia zata sama Nasarar damƙe makashin commissioner?
14. Su waye selfsame da Irshad yake magana a kai kuma zai tafi Katsina saboda su?.....

_Ba'a yi komai ba yanzu labarin ma ya fara with 🔥🔥_

*Mu tara a next page domin samun duka amsoshin tambayoyin ku.*

# RANAR BIYAN BUKATA 🔥
# NAINARH KD NKD'S




*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*

https://chat.whatsapp.com/HWEnklGAjq27nSywL2D130


*Ep-23*


_PRESENT DAY!_


*Washe Gari.*
*9:25 Na safe.*


A hankali take saukowa daga benen hannunta na dama dafe da kanta dake ɗan sara ma ta sakamakon rashin wadataccen bacci da bata samu ta yi ba a daren jiya.
Daga ganin yanayin ta zaka san bata tare da walwala, koda dama ba abin mamaki bane ganinta cikin irin wannan yanayin domin su kansu mutanen gidan, sheda ne a kan kafin dai a ga dariyar Lulu tofa babban abu ne ya faru, ita kanta takan manta rabon da ta yi dariyar, a taƙaice dai idan kaga dariyar ta tofa sai dai idan wani abun na mugunta a kayi to ta yi nan take zagewa ta yi dariya kamar ba gobe.

Fatiyya da yau ta makara bata fita restaurant da wuri ba har su Umma sun tafi sun barta, tana daga Dining Area ita da Maiji suna karin kumallo, yayin da Neina take kitchen ita kuma Ramla tana zaune saman 1 sieter tana duba system tana jiran ƙari sowar Abrad da suka yi waya zai zo sannan su tafi School tare.



Fitowar Neina daga kitchen ke nan tana yarfe hannu ta dubi Lulu da ta ƙari sa saukowa ƙasa fuskarta ɗauke da murmushi take faɗin.


“Samra kin tashi ke nan dama ina shirin taso ki sai kuma gaki.”



Ƙari sawa Lulu ta yi tare da ɗan ma ta side hug ta ce. “Na tashi Neina Barka da safiya, mene ne ya faru kike nema na?.”


“Malam ne ya ƙari so jeki saka mayafi bari na shigo dashi.”

Cewar Neina bayan ta amsa ma ta tana nufar ƙofar fita daga Palon. Gaba ɗaya suka dubeta da mamaki Fatiyya ta ce.


“Malam kuma mai zai yi?.”


Neina tana riƙe da handle na ƙofar palon ta juya tana faɗin Malamin da zai duba ta ne, dama ai already mun yi maganar da Maiji ban sa ni ba kota faɗa ma ita Lulu ɗin.


Kama baki Maiji ta yi tana gimtse dariya dan kuwa bata faɗa wa Lulu ba, domin tasan koda ta faɗa ma ta ba zata yarda ba, shi ya sa taja bakinta ta tsuke.


“Okay! Kice ma kin san da maganar ke nan?.”


Ramla ta tambaya Lulu da take tsaye ba tare da zauna ba, tana nazarin kalaman Neina 'Malam zai zo' to ya yi ma ta uban me?.


Ɗan Murmushi ta yi tana zura ido domin ganin kalan Malamin na kirki ne ko a kasin hakan.


“Nima ban san da maganar ba sai yanzu amma kam babu damuwa ai ya ƙari so ina jira.”


Ta faɗa tana zama saman hannun kujerar.


“Kice yau akwai kallo.”


Fatiyya ta faɗa tana dariya. Ita kuwa Ramla duban Lulu Kawai take yi tasan wani muguntan ta shirya tun da ta ce ya zo kuma bayan bata ma san da maganar ba.


“Laifin ki ne da baki faɗa ma ta ba.”


Ramla ta faɗa tana duban Maiji. Dariya Kawai Maiji ta yi. “Naga koda na faɗa ma ta ba yarda zatayi ba domin ita bata yarda da wasu mutanen ɓoye a tare da ita ba, amma tun da ta amince shi Malamin ya shigo yanzu, mu dai mu zuba ido kawai.”


“Ai kuwa dai musha kallo ba.”


Cewar Fatiyya tana duban mutumin ta Abrad da ya shigo palon da sallama. Ramla ta amsa bata bari ma ya zauna ba ta ce. “Sannu da shanya ni gaba ɗaya na makara saboda jiran ka dana tsaya yi.”

Ta yi maganar tana bin sa da hararar wasa. Shi kuwa idanunsa a kan Lulu ya lura da yanayin da take saboda haka yasan koda ya yi magana Bama kulasa zatayi ba, ya dubi Ramla da ta rufe system dake gabanta tana miƙewa tsaye tare da faɗin.

“Ba dan banaso na kuma makara a kan wanda nayi ba, da sai na tsaya kallon abin da zai faru kuwa. Ko da yake babu damuwa ke Fatiyya idan na zo kya bani labari.”


“Ai kuwa ni kam ba zan tafi ba, ba tare dana saka wani abu a cikina ba, kuma mene ne zai faru da ba kya so kallo ya wuce ki?.”


Abrad ya yi maganar yana ƙari sawa Dining dasu Maiji suke zaune, ya kai hannu tare da buɗe ɗaya daga cikin kulolin dake wurin sai dai babu komai a ciki ya kuma buɗe wata yana zama ita kuma miyar taushe ce a ciki.


Hannu Fatiyya takai tare da buɗe kular dake gabanta ta ciro mulmulen tuwon shinkafa tana faɗin. “Tuwon shinkafa ne a wannan zakaji?.”


“Ah sosai ma kuwa kamar kin san favorite nawa ke nan sass....”


Sauran maganar nasa ne ya maƙale a maƙoshin sa sakamakon tura masa mulmulen tuwon shinkafan gaba ɗaya a bakinsa da Fatiyya ta yi tana Dariyar mugunta. Shi kuwa zare ido kawai yake cikin Azaba na zafin da tuwon shinkafan yake da dashi ya miƙe tsaye yana so ya yi ihu amma ya kasa da kyar ya iya kai hannu ya ciro, ai kuwa wani uban tiriri ne ya fito ta bakin nasa. Gaba ɗaya dubansa suke suna gimtse dariya, Fatiyya da Lulu kuwa tsaban mugunta a fili suke nasu Dariyar.

“Amma Fatiyya baki da kirki fa.”


Cewar Maiji yana saita kanta kar ya gane dariyar da take ɓoyewa.


“Rabu da ita kawai bashi taci kuma zan rama very soon.”😤


Cewar Abrad bayan ya sauke bottle na ruwa da yakai baki wai ko zai dena fitar da tiririn da yake domin zafin gaske mulmulen tuwon shinkafan yake da kuma tsaban ita Fatiyya ɗin ba ƙaunar ganinsa nan ƙalau take ba shi ne ta saka masa a baki.


“Amma kam kasha zafi wannan uban tiriri da ya biyo baya haka.”😃


Ramla ta faɗa tana dubansa tare da ɗan Murmushi. Bai kulata ba sai ma fakar idon Fatiyya da ya yi, ya ɗauki mulmulen tuwon da ya a je saman Plate a lokacin da ya fito da shi daga bakinsa, cusa ma ta a nata bakin ya yi tare da damƙe bakin da hannunsa a dole sai ta cinye. Sai da ya tabbatar ta haɗiye kuwa ganin yadda take zare ido sannan ya cire hannunsa daga saman bakin nata yana dariya.

“Amma dai ka Cuceni wallahi.”


Fatiyya ta faɗa tana raurau da ido bayan ta ɗan dawo hayyacinta domin kusan shaƙeta tuwon ya yi.

“Ba wani cuta one one mukayi ai ke kika fara.”

Ya bata amsa yana kai hannu saman Plate dake gabanta ya ɗauki Plantain rolls ya kai baki.


“Gobe kya kuma ma wani mugunta.”


Maiji ta faɗa tana mayar da dubanta zuwa ga ƙofar palon da Neina ta shigo da sallama. Ita kuwa Fatiyya da ta shaƙa batama kulata ba sai ma mayar da duban nata kan Neina ɗin da ta yi.



“Malamin yana can ɗakin baƙi fa, Samra kije can kamar zai fi.”


“Malami kuma wani Malamin ke nan?.”


Abrad ya tambaya da mamaki.


“Wai Malamin da zai duba Lulu ne ya zo.”


Cewar Fatiyya ba tare da ta dubesa ba domin haushin sa take ji abin da ya yi ma ta.


“Abin mamaki dama Lulu bata da lafiya ne?.”


“Ah lafiyar ta Qlau wannan fa daban ne.”


Ramla ta basa amsa a yanzu. Yayin da Neina ta ce. “Malami ne mai cire Aljanu.”


Wannan karon Miƙewa tsaye ya yi yana duban Lulu da ta yi kamar ma bata Palon tana zaune inda take saman hannun kujera.


“Sauri yake yi kin san irin waɗan nan Malaman na addini basu da lokacin kan su yanzu haka ma wani wurin zashi daga nan ma za ki saka mayafi kije.”


“Wai taje ina?.”


“Zuwa wurin sa domin ya duba ta mana.”


“Amma bai kamata taje ita ɗaya ba ko muje kawai.”


“Bar ni kawai bari naje a haka na.”


Ta faɗa tana Miƙewa tsaye ta nufa hanyar da zai sadata da palon baƙin. Da sauri Fatiyya ta miƙe tabi bayan ta shima Abrad bai ma tsaya sauraren abin da Neina take faɗi ba yabi bayansu.



Tsaye ta yi tana duban mutumin da yake a matsayin Malamin da ya ɗan juya baya bata ga fuskarsa ba. Hakan ya sa ta ɗan yi gyaran Murya kaɗan tare da ƙari sa shiga ciki ta zauna saman 1 sieter ba tare da ta dubesa ba, sai dai tana lura da yadda yake ƙare ma ta kallo domin sanye take da Doguwar rigar Bacci mai shara shara kuma mai gajeren Hannu ce, kanta kuma hula ne da bai gama rufe gashin kannata ba. Ita kanta tasan shigar jikinta bai yi ba, amma ta sha re, ganin bai ce komai ba sai wani gyaran Murya da yake ne ya sa ta ce.

“Gani fa.”


Ta faɗa tana duban wani sharɓeɓen Carbi dake hannunsa yana ja. Da sauri ya kau da kansa daga gare ta cikin inda inda na fitar magana ya ce.


“Ma sha Allah! Toh Toh sannu.”



“Ba sannu zakamin ba, koba dubani kazo ba.”


“E haka ne rankin shi daɗe.”


“Kamar na san ka..!”


Gaba ɗaya daga Malamin har ita suka juya suna duban Abrad da ya shigo Palon Fatiyya tana bin sa a baya.


“Kai Yaro baka sanni ba, sai dai idan mai kama da ni, waye kai ma.”


Malamin ya faɗa yana zare ido cikin rashin abin yi, yayin da Abrad yake bin sa da wani Shegen kallo ya ce.


“Ba kai ne Malam Hadi ba?.”


“E shi ne wani abu ne ya faru?.”


Cewar Neina da hankalinta ya kasa nutsuwa ta biyo bayansu.


“Neina wannan Malamin ba Malamin Allah da Annabi ba ne, ya bar gidan nan tun Kafin nayi masa rauni.”


Abrad ya faɗa yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin Malamin da ya fara sharce gumi domin ya gane Abrad sarai. Dama an ce tabarmar kunya da hauka a kan naɗe ta. Tsoron kar ya tona masa asiri ko ya tozarta shi ya sa Malamin faɗin.


“Fisabilillah an san cin mutunci za'ayi ma mutum shi ne a ka kirasa domin ɓata masa lokaci da suna to shikenan na tafi ma.”


Ya faɗa yana nufar ƙofa fuuu ya fice har yana kusan tuntuɓe.


“Wai meke faru wa ne, a'ina kasan shi ne?.”



Neina ta kuma tambayar ganin yadda malamin ya fita ba'a nutse ba.

“Humph Maƙaryaci ne an taɓa kiransa gidan Uncle ɗina domin duba wata ɗiyar Uncle ɗin nawa da aljanu suka dameta, mutumi ne ya ce a rufe ɗaki daga shi sai ita, a she ba Malamin gaskiya ba ne, kawai ya ari malimtar ne domin cutar mutane.”

“Tofa Tohm Allah ya kyauta gaba.”


Neina ta faɗa tana jinjina lamarin. “Wai ya naga Malamin ya fita ne ko har an gama ruƙiyar?.”


Ramla da Maiji da suka shigo suka tambaya a tare. “Wani an gama ruƙiya ga wanda ya ɓata min budget nan ai tun shigowa ta na lura bana kirki bane naso na ɗan gyara mai saiti gashi wannan ya ɓatamin shiri.”


Cewar Lulu tana Murmushi domin ita kaɗai tasan abin da ta shirya ma Malamin gashi Abrad ya ɓata komai, sai dai ba komai idan halinsa ne zasu kuma haɗuwa, amma kam taso a ce ta ɗan saita masa zama kota sama nishaɗi Sanadin hakan domin yau da dare ne zasu gudanar da aikinsu a kan Prof Bakori Tohm tana buƙatar nishaɗi da walwala kafin lokacin.



“Kai kuwa ya zaka mana haka ai da mun ɗan kwashi nishaɗi domin nasan Lulu ba zata masa da sauƙi ba.”


Cewar Maiji, ita ma Ramla ta amsa da faɗin. “Ai kuwa dai amma ba komai idan halinsa ne ai zai ci gaba kuma zai haɗu da mai maganinsa koda ba Lulu ba.”


Ita dai Lulu Murmushi kawai take yi ta bar Palon domin babu abin da ta tuna sai tuntuɓe da malamin ya kusa yi lokacin da zai fita daga Palon.


“Komai ya wuce kowa ya tafi yin abin da ke gabansa. Allah ya sa mudace kawai domin zamanin ne ya zo da haka ɗaiɗai ku ne daga Malaman suke na gaskiya kuma suke aiki tsakani da Allah.”


“Gaskiya ne wannan Allah dai ya shiga tsakanin na gari da mugu kawai.”


Cewar Maiji, duk suka amsa da Ameen suna barin Palon. “Fatiyya ina ga yau zan biyo restaurant daga school saboda haka ki tana za min abin daɗi kinji Tawan?.”


Cewar Ramla tana duban Fatiyya ɗin. “Yawwa tohm Allah ya kawo ki lafiya, sai dai kar kizo min da wannan mutumin.”


Ta faɗa tana duban Abrad. “Ai kuwa sai na zo sai dai ta fasa zuwa kuwa.”


Ya yi saurin katseta da faɗin hakan.


Zata kuma magana Neina ta riga ta da faɗin. “Ya isa haka nan maza ki saka mayafi ki tafi, ko kuma kawai su rage Miki hanya tun da duk Hanyar ɗaya ce.”



Amsawa Fatiyya ta yi tana ma Abrad Dariyar sai ta ƙara makarar da su sannan ta koma ɗaki ta ɗauko mayafi suka tafi. Yayin da Lulu da Maiji sai kuma Neina a ka barsu a gida.


*( Mu dai kam Abrad baka kyauta mana ba sam 🙂 ai da ka bari Lulu ta gyara masa zama ko ya ya ne😤 mu ma ai ma sama nishaɗi 😅)*


_____
_Assalamu Alaikum WarahamatuLlahi Wabarakatuhu My people Ina godiya matuƙa da Addu'o'in ku a gareni, kuma ina baku haƙuri na jina kwana biyu Shiru a ka yi sammakon rashin lafiya da na ɗan yi shi ya sa bana samu na yi typing ɗin, amma yanzu in sha Allah naji sauƙi komai ya daidaita zaku ci gaba da samun update a kai a kai in sha Allah, masu son magana dani zaku iya tuntuɓata ta wannan lambar (08081129487) na gode Nainarh ce ✍️😍_
___

*A daure a yi comment da share da kuma like mutanen amana 😍 👍🙏🤍*



*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Ep-24*



*B.U.F Restaurant, Abuja.*


*Mahbubullah POV.*

*5:30 Na Yamma.*

Baƙar motar ƙirar Camry ta faka. Ba'a ɗauki lokaci ba driven ya fito daga Gidan gaba da hanzari ya ƙari sa tare da buɗewa Boss ɗin nasa ƙofar gidan baya cike da girmamawa. Sai da a ka ɗauki kusan sakanni da buɗewa sannan ƙafarsa dake rufe cikin comfortable Black leather oxford shoe with white socks ya zuro ta waje kafin daga bisani ya fito gaba ɗayansa Kyakyawa da shi ajin farko sanye cikin modern fit suit maroon color. Tafiya ya fara sannu a hankali ya shiga ciki tare da ƙari sawa wurin da ya saba zama a duk lokacin da ya zo restaurant ɗin sannan ya zauna. Idan ka kallesa yadda fuskarsa take a matuƙar kame ga kuma Glass dake idanunsa ba za kayi zaton yasan da zaman wasu mutane ba a restaurant ɗin. Sai dai komai dake faruwa a daidai lokacin kuma cikin restaurant da mutanen ciki yana an kare da kowa kuma idanunsa suna a Kallon ta da kuma lura da abin da take yi tun shigowar sa Wurin.


“Sannu da ƙoƙari Fatiyya wannan kayan maƙulashe haka duk nawa ne ni ɗaya?.”


Ramla ta faɗa a lokacin da ta ɗauki pan pizza ta kai baki tana kallon Fatiyya da ta jide ma ta kayan kwalam da maƙulashen a saman table da take zaune.

Fatiyya tana dariya ta ce. “E mana ai naki ne duka ki cinye ban da wannan dan ba da shi na bada ba ke naɗai ne kawai.” 😌


Ta faɗa tana gallawa Abrad dake zaune gefe yana shafa waya harara kamar yadda ta saba. Kuma ta yi maganar ne tana ƙoƙarin kai lomar pancake a baki. Sai dai wuffff taji an wafce ko kafin ta yi wani yunƙuri ya kai baki ya gutsira tare da bin ta murmushin ƙeta yana kashe ma ta ido.
Dariya Ramla ta yi zatayi magana a daidai lokacin kuma idanunta suka yi tozali da kyakyawar fuskarsa, duk da cewa bata ga kwayar idanunsa ba amma ƙwaƙwalwarta ta iya tuno ma ta a inda ta san shi ko a ce ta taɓa ganin sa.

Ba tare da jiran komai ba ta ɗa ga masa hannu tana Murmushi dan kuwa haka kawai taji ya dace ta yi masa magana kuma ba komai ne ya bata gwarin gwiwa ba sai Murmushi da taga ya yi ma ta alamun shima ɗin ya gane ta.


Da mamakin ta sai gani ta yi ya miƙe tare da ƙari sowa wurin cikin wannan dai kamilalliyar muryar tasa ya ce.

“Zan iya zama kuwa?.”


Ta ɗa ga masa kai ba tare da ta ɗauke idanunta daga kansa ba.

“Wannan kallon fa ko dai kinayi ne domin ganin wurin da kika min rauni a wancan Ranar ya warke ne ko a'a?.”😂


Ya faɗa lokacin da ya zauna ya miƙawa Abrad Hannu suka yi misabaha.


Ramla ta ɗan saita kanta ganin ta ɗan kwafsa ta ce. “Ohmm.” Kawai sannan ta kuma cewa. “Kamar akwai sanayya tsakanin ku?.”

Ta tambaya ganin alamar kamar shi ɗin da Abrad sun san juna. Abrad ne ya bata amsa da faɗin. “E amma sanayyar ba sosai ba, ke fa a'ina kika san sa?.” Ya yi ma ta tambayar yana kallon ta, sai dai tun kafin ita ta bada amsa shi ya riga ta da faɗin. “Waya take yi alhalin tana tuƙi har ta kusa kaɗeni bata sa ni ba, shi ne dalilin haɗuwar tamu.”

“Ai kuwa dai gashi wancan Ranar mun rabu ban san naka sunan ba.”


Ramla ce ta yi maganar yanzu tana duban Fatiyya da ta dawo wurin riƙe da madaidaicin tray mai ɗauke da bottle na ruwa a kai. A je gefen sa tana faɗin. “Ai ni nayi fushi ma Yah Mahabub kwana biyu ka manta damu.”

A yarda ta yi maganar zaka fahimci cewa Akwai shaƙuwa da tafi kama dana Ƙanwa da Yayanta a tsakanin su.


Ramla ta saki baki tana dubansa shi da Fatiyya ɗin. Again ita ma Fatiyya ta san shi ke nan?. “Mahbub...” Ta maimaita sunan da ta ji Fatiyya ta faɗa tana dubansu fuska ɗauke da murmushi da yafi kama dana yaƙe.


“Sorry Ƙanwa ta kwana biyu bana a garin shi ya sa bana zuwa ya kike yasu Umma fatan ana samun customers sosai sosai?.”
Ya faɗa yana shafa kanta. “Ai duk muna Lafiya, fatan kaima ka dawo lafiya?.”

Cewar Fatiyya. “Alhamdulillah Ƙanwa ta amma fa ya kamata ki yiwa Auntyn ki bayani na kinga yadda take binki da kallon tuhuma.”😃
Ya faɗa yana buɗe bottle na ruwan da ta kawo masa dama haka suka saba tun wasu watanni baya yake zuwa restaurant ɗin idan ya zo sai dai ya sha ruwa kawai kuma ya biya kuɗi kamar wanda yaci wani abun, tun basa amsa har dai suka saba da zarar yazo ma sun san mene ne yake buƙata, ruwa kawai sai dai ya yi ta danna waya idan ya gama ya a je kuɗi ya tafi ana hakan har Fatiyya da ta kasance mai saurin sabo da mutane yawan sakin fuskar da yake da shi ga kowa ya sa suka saba yake kiranta da ƙanwarsa ita kuma ta kirasa da Yah Mahabub.


“Ai Bama sai tayimin bayani ba, na gane komai wato dai mai siya da siyarwa ne a ka sama shaƙuwa tsakani.”


“Ai kuwa kin cinka daidai.”

Cewar Fatiyya tana dariya.....


___

*Irshad POV.*


Kamar yadda ya tsara washe gari ƙarfe sha biyu na Rana a Katsina ta yi masa, sai dai yaje a rashin Sa'a tare da samun mummunar labarin da ya Girgiza tunaninsa na cewar wannan gidan marayun ya daɗe da rushewa kuma bayan hakan abubuwa da dama sun faru a taƙaice ma su marayun dake a gidan duk basa nan kowa ya kama kansa. Duk da cewa ya san za'a rina domin tsawon shekaru huɗu ke nan amma bai yi tunanin wannan labari zai samu ba. Hakan bai masa Bama sai da ya bincika iya yadda zai iya a kan ko zai sama bayani na wurin da a ka mayar da marayun, amma bai sami komai ba, gashi abin haushi ko pictures nasu bashi dashi duk ya bar su a gida balle ace za'a iya gane inda suke ta hanyar pictures ɗin. Jiki ba gwari ya dawo Abuja duk ya shiga damuwa da takaicin kansa na watsar dasu tsawon lokaci da ya yi bai tashi tunawa da su ba sai yanzu gashi bai san ma ta inda zai fara da neman su ba, Burin sa bai wuce a ce suna raye ba. Haka dai wannan Ranar ta kasance masa duk babu walwala. Washe gari ma haka ya tashi gajiyar jiya bata sake sa ba.


*10:56 na safe.*


Ya shiga Palon Aunty da ta sama sallama tun jiya da Yamma a ka dawo da ita gida kuma ta warware tas dama damuwa ce silar summa da ta yi.


Tana tsaye ne ta ɗan durƙusa kaɗan tana sakama junior takalmi ta ɗa go tare da dubansa tana amsa sallamar nasa. Yayin da ya ƙari sa shiga ya zauna saman Sofa. Bayan sun gaisa Aunty ta dubesa cike da kulawa ganin idanunsa sun yi jajur alamar bacci bai ishesa ba ta ce.

“Pooh kana lafiya kuwa an ya zaka iya zuwa Mining Company ɗin kuwa naga kamar bakajin daɗi ko dai na kira Dr ya duba ka?.”


Kallon ta yake yana ɗan lumshe ido, a har kullum yana Alfahari da kasancewar sa mata a wurin Mahaifin sa kuma mai nuna kulawa a garesa sam bata gajiya da hidima da shi, kuma duk da cewa ba zata haifesa ba amma a matsayin ɗa ta ɗauke sa kuma yana girmama ta bisa ƙaunar da take masa. Ya ɗan Girgiza kai.


“Nope it's okay, ba sai yazo ba...”


Ya faɗa yana kuma lumshe ido daga ƙarshe ma ya ɓige da kwanciya saman doguwar kujerar.


Aunty ta dubesa tana faɗin. “Tohm shikenan tun da kace hakan amma dai fita Company sai dai idan ka warware.”

Ta faɗa bawai dan ta fasa kiran Dr ɗin ba, a yadda taga yanayin sa tasan daurewa kawai yake yi kasancewar sa mutum mai zurfin ciki...



__

*Umnia POV.*


*11:55 na safe.*


Bata jin daɗi amma haka take daurewa kuma ta taho Headquarter kafin ta ƙari so sai da ta biya ta duba jikin Safiyya Aunty sannan ta taho. Yanzu ma tana zaune ne a office ɗin ta, ta kuma ɗa go kanta ta dubi Budurwar dake zaune cikin office ɗin da ta zo wai a kan mutuwar mahaifin ta commissioner domin jin yadda binciken yake wakana. Wannan ne karo na farko da wani daga Ahalin commissioner ya zo musu a kan maganar binciken mutuwar saboda haka sauke ajiyar zuciya ta yi, tare da faɗin. “Har yanzu muna iyakar bakin ƙoƙarin mu a kan binciken kuma muna dab da kama mai laifin a hannu ku bimu da fatan Nasara kawai.”

Ƙarishe maganar nata ya yi daidai da shigowar kira a wayar Tamannah dake zaune tana sauraren ta hakan ya sa bata gama jin abin da take faɗa ba. Ta ɗa ga wayar tana sauraren Mulaika da ta kirata gefe guda kuma tana Murmushi ta tuna abin da ta yi ma Mulaika ɗin a Birthday party da ta shirya.

“Autyn Mannah kina ina ne, jikin Mommy ya tashi yanzu haka muna asibiti kiyi sauri kizo yanzu, jini take zubar wa sosai su kansu Likitocin sun kasa gane mene ne ainihin abin da yake damunta.”


Miƙewa tsaye ta yi hankali a matuƙar tashe take faɗin. “Garin ya ya? Yanzu kuna wani Asibitin ne? Ki turomin address ɗin. I'm on my way...”


Ta ƙari sa maganar tare da katse kiran ta dubi Officer tana faɗin. “Madam zan tafi kawai Mommyna bata jin daɗi idan babu damuwa zan kiraki kawai mu ƙarishe maganar.”

Umnia ta amsa ma ta sannan ta fita sauri sauri....


🔥

*Ko wane ne Mahabub?*
*Mene ne yake faruwa da Mommyn su Tamannah?.*
*Allah Sarki our Pooh (Dimple Perfect) Dole kayi zazzaɓi na rashin ganin selfsame naka....😭*
*Gaskiya Officer ya kama ki yunƙura fa mun ƙosa musan wanene Makashin commissioner da kuma dalilin sa🌚*
*Ko mene ne zai faru gaba????.*
*KU MUJE ZUWA KAWAI SANNAN MU HAƊU A NEXT PAGE JIBI IN SHA ALLAH DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA🔥🔥🔥*


*_Helloooo..! Kwana biyu an jini shiru za'a ce wannan lafiya. Lafiyar

Please Login or Register in order to submit comment