Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwarewar ki da jajircewa ya saki ki binciko gaskiya.”

Ta ƙari sa zancen tana rage girman idanunta sannan ta sakar ma ta murmushi tana jijjiga ƙafa.

Garam kakeji lokacin da Officer ta fita ta bugo ƙofar Interrogation ɗin da ƙarfi, taɓe baki Lulu ta yi irin dai abin bai shalleta ba.


Da ƙarfi Officer tasa hannu tare da watsar da karikitan da ke saman desk ɗin office ɗin ta tana fitar da zazzafan huci na ɓacin rai, ɗan dakata wa ta yi tare da ciro bindigarta gadan-gadan ta nufa ƙofar zata fita, a ka yi Sa'a dai-dai lokacin Kiara ta shigo. Da mugun sauri Kiara ta ƙari sa tare da kwace bindigar tana faɗin.
“Kin rasa tunanin ki ne Officer mene ne kike shirin yi kasheta zakije kiyi?”

A fusace Officer ta bata amsa da faɗin.

“To mene ne amfanin Rayuwar nata bayan ita ɗin Murder ce she's killer sannan ko ban kasheta ba, a gobe za'a zartar mata da hukunci domin na riga dana shigar da ƙarar a kotu kuma gobe za'ayi zama na farko da ƙarshe don kuwa Akwai hujjoji a tare dani.”

Officer Umnia ta ƙari sa maganar tana jinjina ma ta kai alamar tabbatar wa. Yayin da Kiara ta fara yin baya baya cike da tashin hankali take duban Umnia sai kuma ta ce.

“Amma kuwa kin tafka babban kuskure Umnia wanda gyara sa ba zai zama abu mai sauƙi a wurin ki ba, yanzu a kan mutuwar wancan mugun kafirin wanda ya daɗe da fita daga musulunci saboda munanan ayyuka da yake yi, shi ne kika shigar da ‘yar ki ƙara kotu, ɗiyar ‘yar uwanki, amma gaskiya Umnia bakiyi ba, lemme tell you something su dai commissioner da Prof ɗin da kike waɗan nan abubuwan a kan mutuwarsu, to ba mutanen kirki ba ne manyan tantirai ne waɗan da tantirancin su ya wuce duk yadda kike tunani...”

Ganin yadda Officer Umnia take bin ta da kallon rashin fahimta ne yasa Kiara ta kamo hannunta tare da fito da ita waje tana faɗin bari na nuna miki wani abu da baki sani ba.

Wani irin dogon birki Officer Umnia taja tana duban Yarinyar da ta bari a Interrogation amma yanzu gata a waje kuma ƙarin abin ɗaure kan shi ne ba ita ɗaya ba ce tare take da wata Budurwar mai matuƙar kamanni da ita sak. Bama wannnan ne ya sa Umnia a ruɗani ba sai ganin Safiyya Aunty da ta yi tare da Irshad da kuma wasu mutanen da ruɗanin da take ciki bai bari ta gane su ba sai dai ta gane Mannah ɗiyar commissioner wacca take tsaye daga gefe.

A hankali ta fara taka wa domin ƙari sawa wurin ‘yar uwanta Safiyya Aunty bakinta na rawa ta ce.

“Ah'aa Aunty meme nene kike a nan?.”

Ta yi ma ta tambayar tana duban yadda Safiyya Aunty ta riƙe hannun ‘yan matan biyu masu kamanni da juna dukkannin su hawaye suke.

Sha re hawaye Aunty ta yi tare da duban yaran nata sannan ta duba ‘yar uwan nata tana jinjina mata kai.


*BAYAN SHUD'EWAR WASU DAK'IK'U!.*

“To fa kinji ainihin abin da yake faruwa.”


Aunty ta ƙari sa maganar tana duban ‘yar uwan nata Officer Umnia bayan ta gama faɗa ma ta ainihin abin da ke faruwa. ta sanar da ita cewar Lulu da Samara ƴaƴanta ne kuma ba kowa ne mahaifin su ba fa ce Mr Aabdar Dawlah.
Ainihin abin da ya faru shi ne a lokacin da suka iso DSS Headquarter ɗin da Kiara suka fara cin karo a gaggauce Aunty ta faɗa ma ta abin da yake faruwa, ita kuma Kiara da jin hakan shi ne kawai taje ta buɗe Lulu sannan suka iso inda su Auntyn suke dama zuwa lokacin Sanam (Samara) ta farka kuma da ita suka shigo Department ɗin, nan fa a ka tsaya kallon kallo tsakanin Lulu da mutanen especially ma Samara da kuma Aunty, kafin daga bisani ta ƙari sa da gudu ta rungume Auntyn tare da Samara domin kuwa ko zata mutu ta tashi ba zata taɓa manta kamannin Aunty kona Samara ba, a wannan taƙin ne kuma Kiara ta shiga office ɗin Umnia domin sanar da ita abin da ke faruwa, sannan kafin fitowar ta ne Aunty dama Samara suka feɗe ma Lulu ainihin abin da ya yake faruwa, a daidai lokacin da Umnia da Kiara suka fito ita kuma Tamannah ta shigo wurin shi ne ta tsaya ganin wani abin da yake faruwa.


*WANNAN KE NAN!.*


“Allahu mai iko Annabi mai dubun daraja, yanzu wannan rikitaccen lamarin da ko'a hasashe ba'ayi tunanin afkuwarsa ba gashi ya kasance ya faru mene ne mafita, ƙarin ruɗanin kuma shi ne Mr Aabdar Dawlah shi ne mahaifin Samra da Samara.”


Officer Umnia ita ke wannan maganar cikin taraddadi.

Taɓe baki Samara ta yi tare da faɗin.

”Tsoro kike kar muji babu daɗi a kan nan bada daɗe wa ba zai girba abin da ya daɗe yana shuka wa ko? Ai karma ki damu kanki a kan mu domin mutuwarsa ba zai ƙara mana ko rage mana komai ba da can ma ai da Bamu san uban mu yana raye ba muna nan daram balle kuma yanzu da gaskiyar Komai ta bayyana.”

Gaba ɗaya duban Samara suke yi da jin abin da take faɗa kuma da alamu tun daga ƙasar zuciyarta maganganun suke fitowa.
Ƙarar saƙon da ya shigo wayar Mahbub ne ya ja hankalinsu gaba ɗaya.

Ya saki wani killer smile bayan ya gama karantawa tare da duban Samara ya ce.

“Everything is done, ƙarshen azzalumai yazo.”

Ta saki kyakkyawar murmushi tare da jinjina masa kai tana faɗin.

“Good job Oga.”

Sannan ta dubesu gaba ɗaya tana faɗin.

“Ina ga fa komai ya ƙare domin Babban kifin tare da muƙarraman sa sun shiga hannu.”

“Kamar ya ya ban gane ba me kuke nufi?.”

Cewar Lulu cikin rashin fahimta.


Mahbub ya ce.

“Bari nayi muku bayani, tawagar bincike ta musamman na turawa address na waɗan nan mutane uku Alhaji Haashir Mr Aabdar Dawlah da kuma Alhaji Umair Ubaydullah kuma duka sun shiga hannu sannan shima shugaban nasu ma'ana mai jan ragamar nasu wato Jaish Jezim Inkiya Shaytaan an kama sa sannan a halin yanzu Zwandun Monster's ya zama labari domin kuwa fusatattun Jami'an sun ƙona sansanin nasu gaba ɗaya.”


Gaba ɗaya da tsananin mamaki tare da farin ciki ta wani ɓangare yayin da kuma wani ɓangaren cike da al'ajabi suke duban sa.

“Ina da Tambaya. Wai shin Barrister Mahbub kai wanene? Sorry fa na kasa yadda kawai a matsayin ka na Barrister kake duk waɗan nan abubuwan.”


Ramla ce ta yi maganar, ya dubeta tare da murmushi sannan ya ce.


“Yarinya mai basira, tabbas ni ɗin Barrister ne a baya amma a yanzu ni ne jagora ko nace kwararren Jami'in bincike na sirri maki fikira a tawaga ta musamman na binciken manyan miyagun Laifuka matakin farko a ƙasa.”

Babbar magana!

“Yanzu kana nufin kai jami'in sirri ne ke nan?.”

Cewar Umnia, ya yi murmushi tare da faɗin.

“Ai ba ni kaɗai ba ma har da Samara ita ɗin mataimakiyata ce ita ma jami'a ce da a ke ji da ita.”

Fuskokin kowa na wurin ɗauke da farin ciki da kuma mamaki suke duban Samara, sai dai kafin su kai ga magana, Kiara ta shigo counseling room ɗin da suke ciki tare da Tamannah ta shigo tana faɗin.

“Ga ƙarin hujja fa kun samu.”


Ta yi maganar tana musu nuni da Tamannah sannan ta yi ma ta alamun ta faɗa abin da yake tafe da ita.

“Madam dama nazo ne domin na dakatar da bincike a kan mutuwar mahaifina da kuke yi domin yanzu nasan ainihin waye shi, shi ɗin ba kowa ba ne fa ce tantirin ƙasurgumin mai laifi lamba ɗaya, sanadin ciwon da mahaifiyar mu take ne na gano wannan gaskiyar domin kuwa ya bada jininta ne a ƙungiyar matsafa da yake, shi ne yanzu bayan mutuwarsa suke ƙoƙarin ganin sun kwashe jinin nata da ya basu, sai dai basu sama nasarar hakan ba domin Dr Abdallah ya haɗa mu da malamin addini na gaskiya kuma a halin yanzu mahaifiyar mu ta sama lafiya shirya shiryen barin ƙasar ma muke domin ci gaba da zaman mu cikinta ba zai yiwu ba, bayan tonuwar asirin ainihin wanene mahaifin mu, shi ya sa nazo na a janye binciken da a ke yi.”

Tana gama faɗar hakan ba tare da ta kuma mintina goma cikakku ba ta bar Headquarter ɗin bayan an gama jajanta lamarin.


A wannan Ranar dai abubuwa da yawa sun faru na daɗi da a ka sin hakan finally dai su Lulu sun haɗu da Auntyn su mahaifiyar su kuma gaskiya ta bayyana azzalumai zasu karɓa hukunci na abin da suka daɗe suna aikatawa tun da sun shiga hannu kuma a gobe za'ayi zaman kotu domin yanke musu hukunci, dama ƙarshen alawa ƙasa, ai ina ga ko'a nan labari ya yi ƙare su Lulu suke da nasara domin gwagwarmayar su ka yi, bai tashi a banza ba, sai dai fa zan so jin ƙarshen waɗan nan azzaluman.🔥🙇


★. .


Washe gari court Shari'a ta kai Shari'a an fafata tsakanin kwararrun lauyoyin da na waɗan da a ke ƙara da kuma lauyoyin gwamnati domin kuwa gwamnati ita ta ɗauki nauyin shari'ar kasancewar Mahbub da Samara jami'ai na gwamnati shi ya sa lamarin ya kasance hakan, Neina tana zaune gefanta kuwa ɗiyarta ce wato Mienal wacca tun a jiyan suka gano gaskiyar zancen a lokacin da Hamraz ya kira Umnia ya sanar da ita abin da yake faruwa a taƙaice dai tun a jiya Neina ta haɗu da ɗiyarta kuma suka gaskata juna sun sha kuka sosai.
Ana tsaka da shari'ar ne kuma wani abin mamaki ya ƙara faruwa ta hanyar bayyanar wata budurwa mai suna Ariana (Ina tunanin kun gane ta ba, wacce suka haɗu da Irshad a lens journey da ya tafi a sri Lanka, bayan dawowarsa kuma yake yawan tunani a kan ta! tofa ita ce wannan.)
Ariana Salis Mamman shi ne cikakken sunanta, mahaifinta Salis Mamman mai muƙamin President of Journalism, shi ne shugaban dukkanin ƴan jarida na ƙasar nan a kwanakin baya wani Babban yaron sa ya fara bincike a kan wani sanannen attajiri nan ne ya gano ainihin true color na Alhaji Umair Ubaydullah a lokacin kuma yana cikin su tsundum kuma sun gane shi ɗin ɗan jarida ne wannan ne ya sa suka yi masa mummunan kisa, sai dai basu sama hujjojin da yake a kan miyagun laifukan Alhaji Umair Ubaydullah ɗin ba domin ya riga da ya turawa shugaban sa P. Salis Mamman wannan dalilin ya sa a wani dare suka afka gidan P. Salis Mamman da yake zaune a Borno State domin asalin ɗan can ne sun sama nasarar kashe shi da matarsa sai dai ɗiyarsu Ariana ta gudu basu samu sun kasheta ba kuma sannan da waɗan nan hujjojin ta gudu.
Sai kuma gata a yau ta bayyana a kotu kuma ta miƙawa kotu waɗan nan hujjoji.
Dama a rayuwa komai ya yi farko tofa ƙarshen sa na zuwa, shi ya sa a ke so a koda yaushe mutum ya kasance cikin aikata abin da ya kasance na daidai kuma Alkhairi kuma komai mutum zai yi ya yi domin Allah ya tuna akwai Ranar hisabi.
Daga ƙarshe dai waɗan nan azzalumai an yanke musu hukuncin kisa ta Hanyar rataya yayin da shi shugaban nasu likitoci suka tabbatar da cewa yana da taɓin hankali domin dama duk mutum mai hankali ba zai aikata abin da ya yi ba, sai dai cutar ta samesa ne sakamakon abin da mahaifin sa ya aikata ta hanyar kashe mahaifiyarsa a gabansa tun daga nan ƙwaƙwalwarsa ta taɓu ga kuma abubuwan da suka biyo baya a Rayuwarsa, har yazo matakin da yake a yanzu.
Wannan dalilin ya sa kotu mai adalci ta yanke masa ɗaurin rai da rai a gidan kaso. Kuma ta raba aure dake tsakaninsa da Annabella ɗiyar Mr Aabdar Dawlah domin ita ta buƙaci hakan.
Alhamdullilah kowa ya yi farin ciki da wannan lamarin ya kasance, Aunty da yaranta sun ci gaba rayuwa mai inganci cikin ƙaunar juna yayin da Samara ta kasance Jami'ar sirri, ita kuma Officer Umnia ta yi matuƙar ƙoƙari yayin da sai da ta tabbatar da Samra wato Queen Lulu ta mu ta zama cikakkiyar Jami'ar DSS.✊
Alhamdullilah ma sha Allah bayan wani lokaci aure ya gudana tsakanin Mahbub da Samara da kuma Samra (Lulu) da Irshad.

Rayuwarsu ta ci gaba da gudana cikin farin ciki da ƙaunar juna, finally mahaifiyar Irshad ta dawo gare sa kuma ta nema yafiya na sharesa da ta yi, kuma ya yafe ma ta bayan tataburza da ta ɗiba da shi, kuma asirin Mummy Abida ya tonu a wata Rana da take shirin sakama mijinta Alhaji Khalil I Khalil guba dan yaci ya mutu, a cewarta dama can saboda dukiyarsa ta auresa sai dai bata taɓa haihuwa da shi ba domin Abdallah da Abrad yaran ƴan uwansa ne suke a hannunsa, shi ya sa take ƙoƙarin kashe sa ta kwace Dukiyarsa, sai kuma gashi asiri ya tonu, ai kuwa a wurin ba tare da jiran komai ba ya rattaɓa ma ta saki har uku kuma ya fattataketa ta bar masa gida dama ƙarshen alawa ƙasa. Ta ɓangaren Ramla ma ta koma ga danginta kuma sun yi farin ciki da komawarta garesu sannan sun dangana na rashin Yazan da suka yi, sai dai ta wani ɓangaren sun ji daɗi sun kuma yi farin ciki tun da azzaluman sun sama hukuncin da ya dace dasu dama zalunci baya taɓa kafuwa na bar abada na ɗan lokaci ne dama kuma daga ƙarshen ƙarshe ko da koda yaushe ƙarshen alawa ƙasa...!


~HAPPY ENDING 👏💯~

ALHAMDULLILAH!


*To duka duka dai anan wannan labarin na RANAR BIYAN BUƘATA wanda hausawa suke cewa Rai ba'a bakin komai ba, yazo ƙarshe.*


*Ina fata gaba ɗaya zamu ɗauki darussan dake ciki sannan mu watsar da mummunan abubuwan da ke ciki, Labarin gaba ɗaya ya ginu ne a kan fansa da kuma neman adalci, sannan kuma da zalunci, kamar dai yadda mahaifin Jaish ya kashe mahaifiyar Jaish ɗin a gaban idanun Jaish ɗin baya da haka kuma matar daya ƙara aura wato Clara ita kuma take gana masa nata salon azabtar war ta hanyar yi masa barazana da wuƙa a kan kawai sai ya kira ta da Mama alhalin saboda a aureta a ka kashe mahaifiyarsa a gaban idon sa ku duba fa, baya da hakan suka ci gaba da yin abubuwan da basu dace ba a gabansa da haka ya yi sanadiyar taɓa ƙwaƙwalwarsa har a ka wayi gari ya kashe su, daga nan kuma mai makon abin ya tsaya iya nan, a'a sai a ka sama a kasi shima Uncle ɗin nasa ba mutum ne mai tsoron Allah ba ya yi amfani da wannan damar ta hanyar mayar da Jaish ɗin ƙasurgumin ɗan ta'adda, kuma abin da zai ƙara baku mamakin shi ne bai fa haɗa Jaish da iyalansa ba duk da cewa Jaish ɗin tamkar ɗa yake a wurinsa. Ta ɓangaren su Lulu ma maraici da kuma fyaɗe da a ka yi ma mahaifiyar su har ta haifesu shi ne abin da ya jefa Rayuwarsu gaba ɗaya a garari har ita ma Samara Prof Bakori ya sama Nasara a kan ta.

Allah ya sa mu amfana da abin da Labarin yake tafe da shi, Allah kuma ya haɗa mu A littafina mai zuwa nan bada jimawa ba mai suna *BA TABBAS.* Ina fata zaku ci gaba da bibiyar alƙamina. Nainarh KD Nkd's.✍️


Salma Ahmad Isah ba zan manta dake ba Tawan ina miƙo gaisuwa tare da fatan Alkhairi a gareki.🍬💯💘



# RANAR BIYAN BUƘATA
Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba
END
BY
# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
# Nainarh KD Nkd's
Thu, Aug, 1, 2024!
Proudly.💪✍️






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment