Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta yi ƙaranci shi ya sa kukajini Shiru. Now am back kuma in Allah ya yarda baku ƙara jina shiru. Zaku ci gaba da samun update a kai a kai sai dai ban yi alƙawarin Kullum ba, amma zan dage na dinga yi muku long idan kuna buƙatar long page naga ruwan Comments da zai tabbatar da cewa lallai kunaso._*


*A Daure a yi abin wato comment da like da Share ✊✨🔥 🙌 Domin a ƙara min gwarin gwiwa ta hanyar ci gaba da kawo muku wannan daddaɗan labari....*

# RANAR BIYAN BUKATA
# NAINARH KD NKD'S
# 07079793782
👆👆 Wannan lambar ta ita za'a sameni a halin yanzu. Domin ɗayar lambar tawa mutanen nawa what'sapp sun kuma rufe wa 🥲 sai kuma idan sun buɗe 😃 Ban da kira Dan Allah. Idan ta kama sai an yi kira dole ga wannan lambar ita ce official number tana on duty everyday (08081129487).


Nkd's ce✍️


*. . . PERFECTLY PEN'S. . .*

*🔥 RANAR BIYAN BUƘATA 🔥*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

. . Nainarh KD Nkd's ce . . . ✍️
07067953066.


https://chat.whatsapp.com/HWEnklGAjq27nSywL2D130


E . 25.


★¡★
Dare ya tsala, shiru kakeji ko'ina, gari shiru, a daidai wannan lokaci da dare ya raba ko wani mutum zaka samesa ne a gidansa cikin iyalan sa, yayin da daren ya kasance lokaci na huta ga wasu, wasu kuma suka mayar da shi lokaci ne da suke Kaɗaita suna ibada domin tanadar ma kansu kyakkyawar masauki Ranar gobe ƙiyama, yayin da kuma ta wani ɓangaren ba haka yake ba a wurin wasu mutanen domin sun mayar da daren lokaci ne da suke Kaɗaita su baje hajarsu tacin kasuwa na neman Duniya kota halin ƙaƙa kuma koda mene ne zai faru su dai kawai su sama Duniya a tafin hannunsu domin a ganin su ai *RANAR BIYAN BUƘATA* _Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba_ shi ya sa suke cin karansu babu babbaka basu san cewa ba, a kowani lokaci na Rayuwa mutuwa tana iya riskarsu. (Allah ya sa mu cika da imani 😭.)
A tsakiyar daren tawagar masu neman ADALCI da suka bada Rayuwar su domin ganin sun sama adalci na abin da a ka yi musu da ma wanda ake ma sauran al'umma, suka yi ma gidan Prof Bakori tsinke.
TAU! kakeji ƙarar fashewar ƙaramin bomp ɗin da ta saka jikin ƙofar, daidai lokacin kuma ƙofar ta faɗi ƙasa a tarwatse sanadiyar bomp ɗin da ya tarwatsa ta, wanda ƙarar fashewar sa ne ya yi sanadiyar tashin Prof Bakori da yake cikin Bacci a Ɗakinsa ya tashi a gigice yana zare ido sai dai kafin ya gama tantance mai ke faruwa wasu mutane dake sanye cikin baƙaƙen kaya da suka fi kama da na patrol suka shigo Ɗakin fuskokinsu a rufe gaba ɗaya. Jikinsa ne ya ɗauki rawa sanadin hancin bindigar da ɗaya daga cikin mutanen da suka shigo ya ɗaura masa a baki. Zare ido kawai yake babu bakin magana gefe guda yana ƙoƙarin tashin Matarsa dake Bacci hankalin ta kwance a gefe domin a ganinsa idan ma kashe sa waɗan nan mutanen masu kama da mala'ikun ɗaukar rai suka zo suyi sai dai su tafi tare da ita don ba zata saɓu ba bingida a ruwa a ce ya mutu shi kaɗai.🤨
Wani gigitaccen mari ɗayan kakkauran mutumin ya kifa masa a gefen kuncinsa, dandanan kuwa fuskar ta kumbura abin ka da jikin hutu, tsananin zafin azaba da ya ziyarce sa ya sa shi wagale gaba ɗaya Muryar sa ya saki wata firgitacciyar ƙara da ta yi sanadin farkawar Matarsa a firgice tana karanto duk addu'ar da ta zo bakinta domin yadda taji ƙarar ta yi tunanin ‘yan fashi ne suka yo musu zuwan bazata cikin dare, ilai kuwa bata gama buɗe ido ba taci karo da mutane tsai tsaye cikin baƙaƙen kaya riƙe bindigu. Ai kuwa nan take cikinta ya yi wani irin hautsinewa tsaban tsoro da tashin hankali har gudawa taji ta kusan yi a wando.😂
Amma a hakan cikin ƙarfin hali tattaro gaba ɗaya jarumtarta ta tattara wuri guda ta buɗe Muryar ta dake a shaƙe tsaban tsoron dake cinta da kyar ta iya faɗin.
“Shshsttssimm mun shiga uku ‘yan fashi ne.”!
Ta ƙari she da kyar kuma da in’ina. Sai dai tun kafin ta ƙari sa taji an fashe da wata uwar dariya a mai firgitarwa sannan mai dariyar wacca da alama mace ce ta ce. ”Just Relax mana Mrs Bakori waɗan nan ubanin ‘yan fashi ne a gaban ku, kin gane ko?.”

Ta faɗa tana ɗan ƙara girman idanunta da suke masifar tsoratar da Mrs Bakori saboda yadda yanayin su suke dole ne ma ta tsorata balle kuma cikin dare a irin wannan lokacin sannan kuma a bazata.
Ai kuwa jiki na rawa Mrs Bakori ta amsa da cewa. “E e e Wallahi na gane ranki shi daɗe.”
Ɗauke idanunta ta yi a kan Mrs Bakori sannan ta dubi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare ta ce.
“Bubba a fito min da waɗan nan ƙana nun alhakin waje domin zamufi jin daɗin yayyanka namominsu a can...”🌚

Ta faɗa tana nufar wajen. Yayin da wannan kakkauran da ta yi ma maganar ya cika aiki ta Hanyar taso ƙeyar Prof Bakori da Matarsa har zuwa katafaren palon gidan nasa da za'a iya kiransa da aljannar Duniya domin ba ƙananun kuɗaɗe a ka narkar ba wurin tsara sa. (Kuɗaɗen Talakawa ba...🌚)

Haɗe su a ka yi da yaransu mata biyu namiji daya da shi ne babba wuri guda kamar kayan wanki kafin daga bisani ita dai wannan da kallon ta kaɗai yake firgita ‘yan hanjin Mrs Bakori ta kuma bada umarni a ka matsa da Prof Bakori gefe guda domin mission ɗin nasu a kan sa ne shi kaɗai ban da iyalansa.

Palon ya yi tsit bakajin komai sai koke koken yaran Prof Bakori da na matarsa da kuma hucin fitar numfashin tsoro. Hannayensa a ƙulle suke haka ma bakinsa domin kafin Bubba ya fito da shi sai da ya kulle masa hannaye da ƙafafu.

Ta ja kujerar da Bubba ya a je ma ta a gaban Prof Bakori tare da zama idanunta a kan sa tana masa wani irin kallo yayin da zuciyarta take shawartarta a kan kawai ta ɗirkesa da bingidar dake hannunta domin idan ta yi hakan ba laifi ba ne sai ma rage mugun iri daga doron Duniya.... Amma ta daure ta cije dan a ganinta idan ya yi wannan mutuwar da zuciyarta take shawartarta ai yaci bulus kuwa, ya kamata ya ɗanɗani tsananin azaba makamancin wanda wasu mutanen suka ɗanɗana ta dalilin sa kafin ya zo ga mutuwa mara kyawu domin ta yi alƙawarin ɗai ɗai ta rayuwarsa sai ya zama abin tausayi ta yadda mabaraci ma sai ya fisa gata. Bama shi kaɗai ba har da sauran azzalumam da lokaci shi ne zai bayyana su....🩸

“Ku su waye kuma mene ne kuke nema a wurina mene dalilin ku na zuwa gidana cikin dare kuɗi kuke so ku faɗa min nawa kuke so zan baku ni dai ku kyale Ni na rayu...”

Prof Bakori ne yake wannan maganar a galaɓaice lokacin da a ka cire abin da a ka rufe masa baki da shi. Ai kuwa a matuƙar fusace ɗaya daga cikin mutanen ta buka masa wani gigitaccen naushi a haɓa bata haƙura ba ta ƙara da harbin sa a damtse. Ai kuwa ta yi ma sa ɓarna da jini kace kace. Tsananin azaba kasa koda motsi ya yi.

“Good Job Marh Ji..”

Wacca take zaune a kujerar ta faɗa tana murmushi duk da cewa fuskarta rufe take cikin face mask haka ma sauran mutanen da suke a tare. Ta miƙe tsaye tare da ƙari sawa ta ɗan durƙusa gaban sa tana taɓe baki tare da girgiza kai ta dubesa jin abin da ya kuma faɗa.
“Wace ce ke?.”
Tambayar da ya yi, ta fito da kyar. Domin sai da ta ɗan nutsu sannan ta gane abin da ya faɗa.
“Good Question. Wato kanaso kasan wace ce ni ko?, dama nan wurin nake da muradin muzo da kai a yanzu, tabbas sanin ni wacece ba zai maka wahala ba idan kayi duba da wasu shekaru huɗu baya ina tunanin ƙaramar kwakwalwarka bata manta zunubin daka aikata ba da zalunci mafi muni da ka yi ga ƙaramar yarinya wacca batasan komai ba a rayuwar ta sai tarin ƙuruciya duk da hakan kuma tana da buri a tattare da ita, amma ka tarwatsa komai saboda son zuciya, ka lalata Rayuwar yarinya ta hanyar ƙeta alfarmarta. Dabbobin mutane irin ka bai kamata da su ci gaba da Rayuwa ba. Ina tunanin ka tuna wacece nake nufi ba. _‘SAMARA’_ ‘Yar uwata ta mutu ta dalilin ka bazan taɓa yafe maka ba a kan hakan dole ne ka biya abin ka aikata ma ta dole! dole!! Dole!!!”

Ta ƙari she maganar a matuƙar zafafe tana miƙe wa tsaye ta juya baya tare da sakar masa alburushi a ƙafa.

Gigitacciyar ƙarar da ya saki ta amsa a gaba ɗaya gidan. Yaransa da Matarsa suka saki ihun suma tare cikin tsananin tashin hankali na ganin abin ke faruwa da ubansu.

“Shiru! Kuyimin shiru a nan idan ba so kuke na kashe sa ba yanzu.”

Ta faɗa cikin tsawa tana zare musu kaifafan idanunta. Ai kuwa shirun kakeji kamar ruwa ya cinye su. Ba ƙaramin firgita da lamarin suka yi.

“Zan iya na saka yanzu a kekketa waɗan nan yaran naka mata su biyu, domin na ɗauki fansa na abin da ka yi ma ‘yar uwata da sauran matan da basuji ba basu gani ba, amma ba zan yi hakan ba, kasan saboda me?. Saboda idan nayi hakan bana da banbanci da kai da kuma sauran azzaluman.”

Ta ɗan yi shiru, da alama batason tuna abin da ya riga ya faru a baya, sai dai ya ta iya?, hakan ya zama dole a gare ta. Ta ɗan dubi yaran nasa sannan ta dubesa.

“Kaji kunya Wallahi Tsohon banza ina tunanin yanzu ka tuna wacece ni da kuma wacca kayi ma rashin adalci ka lalata ma ta Rayuwa har ta mutu sanadin ka. Lokaci ya yi da zaka girba abin da ka shuka bana buƙatar jayayya. Ku kunna Camera ku sai ta ta kansa ya yi bayanin dukkanin mugayan halayensa yanzu.”

Ta ƙari she maganar tana duban mutanen da suke tare. Da sauri kuwa Namijin Kakkauran ya ciro wata Camera tare da sai ta saitin fuskar Bakori sannan ya kunna.

“Ka shirya faɗar gaskiya ko kuwa sai na harbe ta?.”

Ta faɗa a zafafe tana ɗa na bingidar ta saitin kan matar sa.

Prof Bakori da tun da ta fara maganar har ta zo wurin da ta ambaci Samara ya tuna komai, kuma ya fahimci komai saboda haka mai maimakon ya razana ko kuma nuna nadama na abin da ya aikata da kuma tsoro na abin da zai faru da shi gaba. Sam bai yi hakan ba sai ma wata shegiyar dariya da ya yi yana goge jinin dake bakinsa wanda sanadin naushin da a ka masa ne bakin ya fashe. Ya sa ni komai ya yazo ƙarshe kuma yanzu tun da har ta faɗa abin da ya kawo su garesa hakan yana nufin Z.M sun ji komai ta na'urar su dake a ƙirjinsa, da hakan yake nufin rayuwarsa ce tazo ƙarshe domin sirrin ya fita har Matarsa da yaransa sun sa ni, ko ya faɗa ko kar ya faɗa mutuwa ta zama dole a garesa a wannan daren sai dai bai san zuwa wani lokaci ba.

”Zaka yi bayani ne ko sai na harbe ta?.”

Ta kuma faɗa a matuƙar fusace ganin yana dariya ke nan ko'a jikinsa?.

“Kwantar da hankali ki ‘yan mata ai ko da nayi bayani ko ban yi ba wata rana zaki san gaskiya kuma ni ɗin nan ba zan rayu ba, saboda haka ki kwantar da hankalin ki zan miki bayani, sai dai ina fata zuciyar ki tattaura ce domin zata iya bugawa idan taji labarin da zan faɗa yanzu mai tsananin firgitarwa da gigita tunanin duk wani mahaluki.”


Gaba ɗaya su biyar ɗin suka dubesa dama su Biyar ne cir. Da tsananin mamaki haka ma iyalansa. Sai dai bai damu ba domin Ranar wanka ba'a ɓoyen cibi kuma idan basu san gaskiya ba yanzu zasu sa ni bayan mutuwarsa domin ya yi imani ba zai rayu ba.


“Wasu kalan mutane ne masu baƙar zuciya mai cike da buri na tara abin Duniya da kuma samun ita Duniyar a tafin hannunsu. Zasu iya komai a kan hakan idan nace komai ina nufin komai domin dama ai *RANAR BIYAN BUƘATA* _Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba_ sunan ƙungiyar *Zwandun Monster's* Ƙungiya ce da mutanen da zuciyoyin su da imaninsu suka daɗe da ɓurɓurshewa suke domin ƙungiyar ta haɗa mutane da dama daga sassa daban daban na Duniya kuma abu ɗaya shi ne ya haɗa su wato NEMAN DUNIYA da kuma samun ta a tafin hannunsu, tabbas sun samu sai dai kafin nan imanin su ya daɗe da barin zuciyoyin su. Domin kuwa abubuwan da zasu aikata kafin shiga ƙungiyar da kuma bayan shiga, babu Mutum mai ɗigon imani da zai yi. Ƙungiya ce ba kalar ko wacce gama garin ƙungiya ta neman Duniya ba, wannan ta sha banban da kowanne haka zalika mutanen dake cikinta Duniyar kawai suka saka a gaba, ba iya ka tsafi shi ne abin da ƙungiyar ta do Gara da shi ba, kasancewar akwai manyan mutane masu tarin ilimin boko a cikinta hakan ya sa ta Kasance daban da sauran ƙungiyoyin matsafa, ita wannan har da ma'aikata gareta da suke aiki ake biyan su albashi a wata kamar dai masu aikin gwamnati, kuma sannan Ƙungiyar ta kasu kashi biyu ne, duk shekara members na cikinta suke bada jini na budurwar da a ka yi ma fyaɗe to wannan jinin da shi a ke musu tsafi. Ni ma ina daga cikin mambobin ƙungiyar kuma ni ƙarami ne a ciki kuma aikina shi ne nemo musu ‘yan mata na kai musu sai a sama wasu daga cikin members ɗin su ne zasu keta alfarmarta waɗan nan ‘yan matan sannan wannan jini da ya zuba da shi ne a ke musu baƙin tsafi domin cikar Burin su, shi ya sa na kasance professor a jami'a domin a nan ne kawai za'a sama matan da ake so ni kuma nake musu barazana da jarabawa ko wani abun har na sama Nasara a kan su na kai su wurin da ya dace sannan na barsu anan, ni bana musu komai domin kamar yadda na faɗa ne akwai members daban masu raping ɗin sannan a yi amfani da jinin. Wannan kaɗan ne ko nace kaso kaɗan kuma gutsire daga cikin abubuwan da a ke yi a wannan ƙungiyar domin ni ɓangaren da nake aiki kawai na faɗa kuma nima member ne a cikin su sannan ma'aikaci su, manyan shugabannin ba kowa muka sa ni ba, zan iya ce muku ma har yau ban san wanene ainihin wanda ya kafa ƙungiyar ba, abin da na sa ni dai shi ɗin Namiji ne, sai dai a'ina, yake waye shi?. Duka ban sa ni ba, abin da na sa ni shi ne koma wanene shi ba ƙaramin mai basira ba ne sannan naji Labarin cewa matashi ne domin ko shekaru arba'in bai cika ba. Commissioner of police na ƙasar nan da aka kashe kwanan nan shi ne shugaba na biyu a ƙungiyar gashi yanzu an sama wani ya kashe shi. Yanzu haka ma ƙungiyar Zwandun Monster's suna nasu Binciken daban a kan makamashin commissioner domin ko wanene tabbas yasan wani abun saboda haka ci gaba da kasancewar sa a raye Babbar barazana ce ga ƙungiyar, sannan kuma hankula ba'a kwance suke ba ana cikin hatsaniya sosai da neman wanene zai maye gurbin commissioner matsayin shugaba na biyu wanda shi ne kawai members suke iya gani basa iya ganin ainihin shugaba sai mutum ya kai wani matsayi.... Duk wannan abin fa dana faɗa kaɗan ne daga cikin bayani a kan ƙungiyar domin ko nima da nake matsayin member kuma ma'aikaci a ƙungiyar ba komai na sa ni ba, abin da na sa ni bai fi kaso 10% cikin 100% ba ....”


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...”


Shi ne kawai abin da ta iya faɗa da kyar ƙwaƙwalwarta ta gaji daji wannan baƙin labarin. Da ƙarfin gaske ta ce.

“Ya isa ka dakata!.”

Ta faɗa da ƙarfi tare da harbin sama da ƙarfin gaske tana rumtse ido. Da sauri ɗaya daga cikin mutanen mace wacce ta naushi Prof Bakori a ɗazu ta ƙari sa tare da kamota tana faɗin.

“Cool down mana bayanai fa yake bamu na abin da muke nema ki nutsu ki kwantar da hankalin ki.”


Ta ɗa go rinannun idanunta tana duban ta ta ce. “Na nutsu fa kikace bayan gama jin abin da ya faɗa kike faɗa min na nutsu ke nan ita ma Samara abin da suka yi ma ta ke nan da jinin ta, tsafi!”

Ta yi shiru tana cire leɓe.

Ɗayar budurwar dake gefe wato Ramla, ta ƙari sa garesa tare da ɗan rangwafawa tana dubansa da idanunta da suka yi jajur matuƙar ɓacin rai kwance a cikin su. Rayuwar ta ta baya ta tuna, kalmar fyaɗe da ya faɗa ta tuna ma ta da Rayuwar ta baya. Da kyar ta daure da jure ta cije ta ce.

“Ke nan ita ma Samara abin da kukayi da jinin ta ke nan?
Tsafi!.”

Ta tambaya da kyar. Yayin da duk suka yi shiru suna sauraren sa, har da yaransa da matarsa da tuni suka yi tsit jin wannan tashin hankali yafi gaban kuka domin ƙaramin abu a ke ma kuka.

“Ka bamu amsa mana!.”

Maiji ta faɗa a tsawa ce tana sakin Lulu da ta ɗan nutsu domin sauraren amsar da zai bada yayin da ƙirjinta yake mugun bugu.

“Ina ga bai da baki sai na basa kyakkyawar naushi tukunna.”

Bubba ya faɗa yana damƙe hannu tare da yunƙurin ƙari sawa Wurin.

“A'a bawan Allah ai ba ma sai ka wahalar da kanka ba wurin naushi na. Ni da zan mutu, ba ƙaramar Sa'a na naci ba da na kai har i yanzu da nake tona asirin ƙungiyata nake faɗa muku, duk da cewa nasan hukuncin hakan shi ne kisa amma na zaɓi na mutu ko na samu muna nan zunubaina su ragu.

“Samara yarinya ce nutsatsiya mai shiga rai, kuma kyakkyawa wacca kyan ta da dirinta yake rikita duk wani ɗa Namiji mai cikakkiyar lafiya. Na so ta sosai duk da cewa kaso 80 na sha'awa ne, babu yadda ban yi ba a kan ta amince min, amma taƙi, nayi naci magiya duka taƙi yarda, sai Ranar da na sama dama a kan ta lokacin da ta ɗauki record na muryata ta ce zata kai ga director's na makaranta, ni kuma tsoron kar asirina ya tonu shi ne ya sa ka cikin tsananin ɓacin rai na aikata ma ta abin da nayi har na rabata da mutuncinta sannan na yar da ita a gefen bola, sai dai na rantse da Allah ita ba'ayi komai da jinin ta ba, domin sanadin abin da nayi kuma na hana jinin ta ba ƙaramar hukunci na samu ba daga ƙungiya sss....”


Kasa ƙari sa abin da ya yi niyyar faɗa ya yi sakamakon wani wawan naushi da Lulu ta buga masa a baki da bindigar dake hannunta. Da sauri Maiji ta janye ta gefe yayin da duka suke bin sa da wani mugun kallo cike da tsana.

“Ki bar ni na kashe sa kawai sanadin sa ‘yan mata da yawa sun rasa rayukansu cikin su kuma har da ‘yar uwata yayin da wasu kuma Rayuwar su ta tarwatse. Wannan mutumin ya cancanci ya mutu nace ki barnnnnnnnnnn ah..!!!”


Bata iya ta ƙari sa maganar ba sakamakon wani abun mai kama da bomp da ya fashe saitin ƙirjin Prof Bakori. Ai kuwa take ya zube yana fitar da wani irin wahalallen nishi, yayin da yake buɗe bakinsa domin so yake ya yi magana.

Da sauri Lulu ta kwace daga riƙon da Maiji ta ma ta tare da ƙari sawa wurin ta ɗa gosa ganin yana so ya yi magana. Da kyar ta iya jin maganar nasa da ta fito a rarrabe kuma ta zama maganar sa ta ƙarshe a Duniya.
“Yyyyyi ‘yar uwarrr kikki tana raye bata mummutu bbb...”


Sauran maganar ta maƙale sakamakon rai da ya yi halin sa, daidai lokacin kuma ƙarar jiniyar motocin ‘yan sanda suka cike gaba ɗaya unguwar.


Za'a iya cewa kamar Statue (mutum mutumi) haka Lulu ta koma saboda tsananin shock da ya ziyarce ta na jin abin da ya ce, tabbas ita ba kurma ba ce ta ji da kyau, ke nan yana nufin Samara ɗin ta bata mutu ba tana raye garin ya ya ? Waɗan nan sune kawai tambayoyin dake cin ta Gashi babu damar ya amsa ma ya ya riga ya mutu.

“Ki taso mu tafi zaman mu ana akwai hatsari ‘yan sanda sun zo.”


Maiji ta faɗa a zafafe tana ɗa go ta domin su tafi kar police su shigo su samesu. Bubba da ya naɗe Camera ɗin da ya gama recording komai from A to z ya ce. “Taso mana Lulu akwai hatsari police sun riga sun zagaye anguwar ci gaba da tsayawar mu akwai matuƙar hatsari.

Da ƙarfi Lulu ta janye jikinta daga riƙo ta da Maiji ta yi, Maiji bata haƙura ba ta ƙara riƙo da gudu suka nufa hanyar ƙofar da suka shigo ta ciki, sai dai kafin su ƙari sa Lulu ta kuma kwace hannunta tare da nufar wurin da ta tsugunna gaban gawar Prof ta ɗauki sarƙarta da ta faɗi. Ta juyo ke nan zata tafi shi kuma yaron Prof da Allah ya ba shi Sa'a ya kwance daga ɗaurin da suka masa ya ƙari sa da sauri tare da kai hannu a zafafe ya cizgi face mask dake fuskarta ai kuwa take kyakkyawar fuskarta ta ta ta bayyana.

Ban san mene ne ba, tsananin kyawunta da ya gani ne ya hana shi motsi, ko kuwa shock ne ya ɗibesa sakamakon idanunsa da suka shiga cikin nata. Shi dai bayan ganin fuskarta ya tsaya ne kamar mutum mutumi yana dubanta baki wagame.😅

Ita kuma ta yi amfani da wannan damar ta hanyar turasa baya, sannan ta kwasa da gudu tabi ƙofar da su Bubba da Ramla da Maiji suka bi sannan ta fita gaba ɗaya suka fita ta inda suka shiga gidan ba tare da ‘yan sanda sun yi nasarar kamasu ba haka zalika Camera ɗin tana tare da su. Jiki a sanyaye suka koma gida kowa da tunanin da yake yi, sai dai fa maganar cewa Samara bata mutu ba tana raye maganar ta taɓe su, especially ma Lulu. Neina dake can Gida hankali tashe suka tarar nan suka bata Labarin abin da ya faru basu ja zancen ba ganin dare ya ja suka yi sallama daga meeting room ɗin sannan ko wacce ta nufa bedroom ɗin ta tunani fal ranta, especially ma Ramla da maganar fyaɗe ya tuno ma ta da nata rayuwar a baya shekaru huɗu ba ke nan...


_Ba Zan Lamunci A Canzan Labari Kota Wata Siga Ba¡!¡❗_
____

*_Ya ilahi! Ke Duniya ina ne zaki Damu?🤔🤔_*
_Allah dai ya sa mu dace, in mun dace mu dafe 👍❤️😍_

*_Oh wannan ne abin da yake ainihin.🤨*
*Shin wane ne wannan creator na _Zwandun Monster's?_*

*😳😳 Wai da gaske ne Samara tana raye?? Turƙashi!!!!!*

*Wai shin ma mene ne ainihin labarin Ramla?, Ni kam zan so sani fa. Kuma masu karatu haka ne ko ta wurin ku, nasan kuma zaku so sanin ainihin labarin Ramla 🩸 to shikenan babu damuwa mu haɗu kawai a next page, zamu tashi ne da labarin Ramla, domin sai idan mun ji labarin ta ne zamu fi gane abin da zai faru a gaba🔥*


*A yi like Dan Allah 🙏 share fisabilillah ❤️ and comment domin shi ne gwarin gwiwar tawa 👏🙌*


*Nkd's ce 💋*

# RANAR BIYAN BUƘATA
# NAINARH KD



. . . Perfectly Pen's📚. . .

*🔥 RANAR ßIYAN BUƘATA 🔥*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

. . Nainarh KD Nkd's ce . . . ✍️
07067953066.


_Salma Ahmad Isah (Candy) Da Khadijah M Abdulwahab (Queen Kainaat) wannan feji naku ne mutanen amana, Allah ya bar ƙauna 👏❤️_

_
E . 26.


KADUNA STATE!


‘Yan mata ne su wurin shida a cikin madaidaicin ɗakin. Suna zazzau ne kowaccensu taci ado an ƙure a daka, kai da gani kasan cewa

Please Login or Register in order to submit comment