Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Neina ta san da shigowarta, da sauri ta sha re hawayen fuskarta tana ƙaƙalo Murmushi da yafi kama dana yaƙe ta ce.

“Mai Jiddarh kece, yaushe kika shigo?.”

Ta yi ma ta tambayar ne dan kar Maiji ɗin ta riga ta magana.

“Humm Neina ke nan, yanzu na shigo saboda nasan muddun kika ware kanki tunani zakiyi a kan abin da ya riga ya faru baya, wanda hakan kuma babban matsala ne a gare ki saboda lafiya ma bata wadace ki ba a halin yanzu. Dan Allah ki kwantar da hankalin ki ina mai tabbatar miki Mienal ta kusa bayyana a jikina nakejin hakan kuma in sha Allah tana a hannu na gari, saboda haka ki dena takurar kanki da yawan tunane tunane hakan babban illa ne ga lafiyarki.!”


Neina ta yi shiru tana sauraren Maiji a zahiri yayin da baɗini kuwa ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo ma ta abin da ya faru tsakanin ta da mijinta a wancan Ranar a wasu watanni baya.



*Flash Back....*



_“Yau.! Idan nace Yau! Ina nufin a yau ɗin nan kamar yadda nayi ma Zwandun Monsters alƙawarin cewa jinin Mie da shi za'ayi sadaukarwa na yau zan yi ƙoƙarin ganin na cika, yanzu haka na bawa Mie Chocolate mai ɗauke da sinadarin saka Bacci kuma na tabbatar tasha saboda haka fita da ita daga Gidan nan ba zai yi wuya ba, domin ina da tabbacin wancan Mahaifiyarta ta, bata Gidan gaba ɗaya...” Ɗan Shiru ya yi da alama yana sauraren abin da a ke faɗa ne ta wayar, kafin ya kyalkyale da wata iriyar gigitacciyar dariya irin na cikakkun marasa imani waɗan da zasu iya aika komai a kan samun Duniya muddun Burin su zai cika. “Ban damu da halin da Neina zata shiga dan na rabata da Mienal ba domin kafin Mienal ma sauran Yaranta da basa zama duk ni ne nake bada jininsu ga ƙungiya ta 'Zwandun Monsters' domin cikar burina da ka riga kafi kowa sa ni.” Ya faɗa yana kuma kece wa da wata kalar mahaukaciyar dariya.... Tamkar saukan aradu a tsakiyar ka ba tare da tsammani ko hasashe ba, haka Neina dake tsaye bakin ƙofar ɗakin riƙe da handle na ƙofar take jiyo maganganun da mijin nata ya juya baya yake yi da alama waya yake da wani. Tabbas ta sa ni tana zargin sa bisa wasu al'amurran nasa, amma tunanin ta ko sau ɗaya bai taɓa kai ta da nisa har haka ba, ke nan shi ɗin da ya kasance miji a gare ta matsafi ne, inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali da razana Zuciyarta take, tana wani irin zillo kamar zata yo waje. Tsaban tashin hankali batasan lokacin da ta saki Tray dake hannunta mai ɗauke da Cup na Jitter juice da ta kawo ma sa ba. Tsananin tashin hankali da ruɗani ya sa ko gabanta bata iya gani da kyau tafiya kawai take cikin lalube Burin ta bai wuce ta sauka Down ba ta ƙari sa ɗakin Mienal Ɗiyarta domin kuɓutar da Rayuwarta koda nata Rayuwar zai shiga garari, bata tunanin zata bari mummunar Burin mugun mutumin da yake amsa sunan miji a gare ta ya cika a kan ‘yar nata ɗaya tilo.
A hauka ce ta tura ɗakin tare da shiga a guje ta ƙari sa wurin gadon da Mienal ke kwance a ƙudun dune tun lokacin da Daddyn nata ya shigo ya bata chocolate ta sha Bacci ya ɗauke ta a wurin.
Hankali a matuƙar tashe Neina ta fara kwala kiran Sunanta tana tashin ta, sai dai ko kwakwkwaran motsi Mie batayi ba.


Wata iriyar razananniyar firgitacciyar tsawar da a ka buga ma ta da ƙarfin gaske tamkar saukar aradu haka tsawar ya sauka a tsakiyar kanta. A gigice ta ɗa go kanta tana kallon mijinta dake tsaye yana bin ta da wani mugun kallo tamkar kumurcin zaki. “Ƙoƙari kike wurin ganin kin shiga tsakanina da samun Nasara ta, bayan gwagwarmaya da matuƙar wahalar gaske da na sha kafin na kawo wannan matakin, kin makaro Neina kin ja ma kanki tun da har kikaji Sirrina hakan yana nufin rayuwarki tazo ƙarshe za'a rufe babin ki, kamar dai sauran da suka shuɗe kafin ke...” Cikin wannan firgitacciyar muryar mai cike da amo da rashin imani yake maganar, sannan ya fara takawa ya ƙari sa wurin, tare da kamo gashin kanta da ƙarfin gaske ya bugata da bango sanadin hakan goshinta ya fashe ta fara fitar da jini idanunta suka fara ƙoƙarin rufewa yayin da take ganin dishi dishi ta fara fita a hayyacinta.....

Watsar da ita gefe ya yi kamar kayan wanki, gadan gadan ya nufa Gadon da Mie take kwance har lokacin bata farka ba, ya saɓe ta a kafaɗun sa, tare da nufar hanyar fita daga Bedroom ɗin, sai dai duk yadda yaso ya yi gaba da ƙafarsa hakan bai yiwu ba, sakamakon jajircewar da Neina ta yi wurin ganin ta riƙe ƙafar da iya ƙarfin ta a kwancen da take idanunta suna ƙoƙarin lumshewa amma haka ta daure ta kama bango ta miƙe da kyar tare da dagewa iyakar ƙarfin ta, ta janyo ƙafar tasa ta dama da ta riƙe, ai kuwa gaba ɗayan sa ya yi ƙasa... Tim!!! Kakeji shi da Mie ɗin su faɗi, kan Mienal ya bugi bango da hakan ya yi sanadiyar farkawar ta a firgice. Cikin Wata kalar wahalalliyar murya Neina take faɗin. “Ki gudu Mie ki gudu domin ceton Rayuwarki idan ba haka ba wannan azzalumin sai ya ga bayan ki.”
Kuka sosai Mienal take yi Hawaye shaɓe shaɓe take girgiza kai tana faɗin. “No Neina i can't, idan na tafi ke fa wanene zai cece ki?. Bazan taɓa iya tafiya na bar ki ba.”!
Wata uwar tsawa Neina ta kuma buga ma ta tana faɗin. “Ki tafi! Ki tafi nace karki damu dani, rayuwarki ita ce mai muhimmanci a yanzu. Ya Allah.”!!
Ta ƙari she da Kiran sunan Allah da ƙarfi lokacin da mijinta ya miƙe da kyar yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin Mienal dake ja da baya cike da tsoro da tashin hankali, ita kuma Neina ta yi amfani da wannan damar ta buga masa Gilashin fure aka, ai kuwa nan da nan jini ya wanke sama fuska tamkar an buɗe famfo, amma tsaban taurin kai duk da hakan ƙoƙari yake wurin ganin ya isa ga Mienal. Da ƙarfin gaske ta kuma buga masa ɗayan vase ɗin a tsakiyar kai tana ci gaba da faɗin Mienal ta gudu. A fusace ya juyo tare da kifa ma ta wani bahagon mari, da sai da wasu taurari suka gifta ta idanunta kafin jin ta da ganinta ya ɗauke gaba ɗaya sai dai kafin idanunta su gama rufewa tana ganin lokacin da Mienal ta kurma ihu tare da ficewa daga Bedroom ɗin da gudun tsiya shima kuma ya bita yana dafe bango domin ba ƙaramin rauni Neina ta yi masa ba.....



*_Present Day...._*


Maiji bata bar bedroom ɗin ba har sai da taga Neina ta kwantar da hankalin ta, ba kuma wai don tunanin ya kyaleta ba. Kawai don ita Maiji ɗin nata hankalin ya kwanta shi ya sa ita ta kwantar da nata hankalin...


_____
*LULU POV.*


A waɗan nan ‘yan kwanakin sam bata sama sukuni ba gashi tunani yaƙi barin ta tun lokacin da ta sama labarin mutuwar commissioner lissafin ta ya rushe gaba ɗaya. Yanzu haka ma kwance take saman Bed nata ƙudun dune bawai kuma don tana jin sanyi ba, a'a Shiru ta yi tana nazarin Rayuwa da kalan Mutanen dake Cikin ta na kirki dana banza sai dai a wanann zamanin da muke yanzu da son zuciya ta yi yawa a cikin ta, na banzan son fi na kirkin yawa hasalima na kirkin suke mutuwa suna barin na banzan....


*Flash Back...*


Hawaye take fitarwa, Hawaye na baƙin ciki tsantsa da damuwa amma hakan take daurewa tana jajircewa kanta tana bawa kanta da kanta gwarin gwiwa sannan tana kuma tabbatar wa kanta cewa hakan da take ƙoƙarin yi shi ne daidai kuma hanya mafi dacewa da ta ɗauka domin inganta Rayuwar ‘ya‘yan ta da saka ran su taso cikin Rayuwa mai inganci duk da hakan zai yi matuƙar wahalar gaske duba da da irin wurin ta kawo su, amma kuma bata da wani zaɓi fa ce hakan....


Kamo hannun su ta yi ta haɗe wuri guda tana Hawaye suna Hawaye a durƙushen da take gabansu daidai tsayin su ta fara magana cikin sanyin murya.

“Samara kece Babba ki kula da Ƙanwar ki Samra kinji nan wuri ne da baku san kowa ba Hakazalika babu wanda ya sanku zaku haɗu da mutane iri iri ku dage ku tsare mutuncin ku kada ku taɓa bari mutuncin ku ya zube a titi kunji?.”


Basu iya bata amsa ba sakamakon kukan da suke yi da iya kar gaskiyar su domin duk da ƙarancin shekarun su sun gane ina ne wurin da Auntyn tasu ta kawo su, orphanage ne, ke nan anan za su ci gaba da Rayuwa su kaɗai ita kuma fa?.

“Aunty! Bama son nan ki koma damu Gidan mu.”


Kallon Samra da ta yi maganar Auntyn ta yi Zuciyarta tana kuma rauni amma banajin zata iya komawa dasu inda take domin a halin yanzu Rayuwarsu a cikin Hatsari take nan ɗin wato gidan marayun shi ne wuri mafi safe a gare su.


Girgiza kai tahau yi sannan ta ce.

“Hakan ne ba zai yiwu ba, zaman ku anan shi ne mafi aminci a gare ku. Ni zan tafi idan da rabon zamu sake haɗuwa ina fata hakan ta kasance koda sau ɗaya ne a rayuwata.”

Ta ƙari she maganar tana Miƙewa tsaye sannan ta yi ma matar dake tsaye gefansu cike da tausayawa a gare su alama da ta tafi da su.

Tabbas akwai matuƙar ciwo da raɗaɗi rabuwa tsakanin ‘ya‘ya da mahaifiyarsu, ba ko wace uwa ba ce zata iya sadaukarwar da Aunty ta yi, sai dai tanajin hakan da ta yi shi ɗin ne daidai domin a ganinta a gidan marayu ne kawai Rayuwar yaran nata zai inganta kuma wancan mugun mutumin idanunsa ba zai kai kan su ba.


A wancan Ranar a wancan lokacin haka suna ji suna gani Auntyn ta tafi ta barsu a wurin da basu san kowa ba haka ma kowa bai sansu ba, banda ƘADDARA! bana jin akwai wani Abu da zai raba uwa da ‘ya‘yanta like this......
_____

*_Zaku ga ana yawan Flash Back a labarin, a haka salon yazo sai Haƙuri 🔥🔥🔥_*

*_Don't Forget to Like, Comment, and share Fisabilillah, domin waɗan nan sune supporting nawa da zakuyi ku ƙaramin gwarin gwiwa Nkd's ce taku a har kullum ✍️✊🪄_*
_______
________
_______
___
*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*




𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫


*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Arewabooks:@KhadeejarthSabi'uYahyah.*


_Dedicated To Oum Yasmeen.🥳_


https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20


*Ep_13-14*


*-25, Yakubu Gowon Crescent, Asokoro, Abuja, Nigeria.*




“Mommy ki duba so nake ki tayani zaɓen kalan kayan da zan saka Ranar Birthday na.”

Mulaika ta faɗa tana nuna ma Mommyn nasu tulin kayan da ta jide saman Bed ɗin, sarƙoƙi ne ‘yan uban su expensive sai kuma dogayen riguna English Gown wurin kala Biyar. Mommy ta dubeta sannan ta dube saman Bed ɗin tana kallon kayan ta buɗe baki domin magana sai dai kafin takai ga furta wani abu Tamannah da ta shigo Bedroom ɗin wurin Mommyn nasu domin su yi magana, ta tsinkayi abin da Mulaika ɗin take faɗa, a fusace ta ƙari sa shigowa cike da Bala'i ta dubi ƙanwar nata tana faɗin.

“Wani Birthday kuma zakiyi kin manta halin alhini da muke ciki ne kike magana a kan Birthday are you out of your Mind?.”

Ta ƙari sa maganar a fusace tana daka ma ta tsawa. Sai dai abin da zai baka mamaki, shi ne ko a jikin Mulaika. Taɓe baki ta yi tana tattare kayanta ba tare da ta ce komai ba.

“Mulaika.”!

Tamannah ta kira Sunanta a kufule, bata bari ta amsa ba ta ci gaba da faɗin.

“Karki kuskura kiyi wannan Birthday ɗin kinji na faɗa miki don na lura baki da hankali an kashe mahaifin mu ko sati ba'a rufa ba shi ne kike maganar Birthday...”


Sai a lokacin Mulaika ta juyo ta kalleta sannan ta ce.
“To shi Mahaifin namu da a ka kashe wani waliyi ne da ba zan yi Birthday party ba dan ya mutu, ina ce dai hakan ya koya mana, ko kin manta a washe garin Ranar da Amma (wato kakar su ta wurin uwa.) ta mutu ya haɗa Miki Birthday party a wancan shekaran, waye ya yi Miki magana. Sai ni yanzu za'a ce kar nayi. Aikuwa Mutum ya yi ƙarya wallahi domin RANAR BIYAN BUKATA _Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba_ Shi ya tafi muma kuma lokaci muke jira.”


Ta kai ƙarshen zancen nata tare da ƙoƙarin bi ta gefanta domin ta fi ce daga Bedroom ɗin. A fusace Tamannah ta janyo ta baya tare da ɗa ga hannu da niyyar sharara ma ta lafiyayyen mari.

“Ke Tamannah mene ne hakan baki da hankali ne, a kan me zaki mareta?. Kadaki kuskura kinji na faɗa miki.”

Cewar Mommyn cikin tsawa tana kallon su gaba ɗaya domin ranta ya yi mugun ɓaci. Dakatawa Tamannah ta yi tare da sauke hannunta tana furzar da huci mai zafi daga bakinta.

“Ai wallahi da kin sa ni ki kyaleta Mommy ta gani idan tsayawa zan yi ta marenin. Kuma Birthday party sai nayi a cikin Gidan nan ma naga mai hanani, shi Daddyn ai ba abin Alkhairi ya shuka da yana yare ba. Kije ki bincika mutane da dama farin ciki da mutuwarsa suka yi, har da masu fatan da zasu haɗu da wanda ya kashe sa godiya zasu yi ma sa Kum.....”


“Mulaika! Ya isa nace fita daga ɗakin nan yanzu kafin ranki ya ɓaci.”


Mommy ta faɗa domin Zuciyarta ba za ta iya ci gaba jure kalaman Ɗiyar nata ga Marigayin mijin nata commissioner of police Aashir Aasaal ba, duk da cewa yes ta sa ni gaskiya Mulaikan take faɗa.


Mulaika a ka ce ta fita amma tsaban taurin rai ko motsi taƙi yi. Sai ma Tamannah da kalaman Mulaikan suka yi matuƙar shigarta kuma suka da sa ayar tambaya a Zuciyarta, fita ta yi daga ɗakin a zuciye.... Bata ƙasar lokacin da a ka kashe sa, sai labari ta samu ta waya haka ta tattara ta dawo ta baro U.k da take zaune can tana aiki da wani Babban Company na ƙasar. Dama tun ba yanzu ba take da Burin dawowa domin tayima mahaifinta tambayoyin da suke cin ran ta a kan dalilin sa na zaɓa ma ta karatu ɓangare mafi hatsari, a ganinta, da ya yi, Chemical Engineer, ta karanta, sannan kuma bayan ta kammala karatun ya nema ma ta aiki a Babban Company a ƙasar U.k. burinta ta zama Likita amma saboda farin cikin mahaifin nata da yake nuna ma ta fiye da sauran ‘ya‘yan sa ya sa ta haƙura ta karanci abin da yake buƙata. Yanzu kuma lokaci ya yi da ya yi ma ta Alƙawarin faɗa ma ta Dalilin sa, sai dai an sama wani ya kashe sa, tambayar ta a har kullum shi ne mene ne dalilin makashin kuma me yasa ya kashe sa. Ga maganganun Mulaika na yanzu da suka tsaya a ƙwaƙwalwar ta ta haddacesu. _“Shi Daddyn ai ba abin Alkhairi ya shuka da yana yare ba. Kije ki bincika mutane da dama farin ciki da mutuwarsa suka yi, har da masu fatan da zasu haɗu da wanda ya kashe sa godiya zasu yi ma sa..”_ Waɗan nan maganganun na Mulaika su ne yanzu abin da suka tsaya a tunaninta, sai dai ta yi ɗamara a kan gano makashin Mahaifin nata kuma sannan ta san dalilin sa na kashe ma ta uba, yanzun ma, ta shiga Bedroom ɗin ne domin ta faɗawa Mommyn zata tafi wurin Jami'an da aka bawa bincike a kan mutuwar mahaifin nata, gashi Mulaika ta ɓata ma ta rai, bata faɗa ma ta ba, ta fito. Tsaki taja tana shiga Bedroom ɗin ta domin shiryawa ta tafi Dss Headquarter ɗin....



____

*-100, Herbert Macaulay Way, Garki, Abuja, Nigeria*

*_8:20, Na Dare_*

*IRSHAD POV.*



_P_B_
_“Har yanzu fa ban san sunan ka ba, wancan Ranar mun rabu baka faɗa min ba. Now tell me what is your name?.”

Ta faɗa tana dubansa.

Ya yi matuƙar ƙoƙari wurin haɗo kalmomin da kyar ba tare da in'ina ba ya faɗa lokaci guda ya ce.

_“Irshad!..”_

Ta yi Murmushi. _“Nice Name.”_


_P_D_

_____

“Pooh! Lafiya kuwa are you hearing me, wai mene ne yake faruwa ne kwana biyu kamar kana yawan tunani fiye da kima?.”


A hankali ya ɗa go Frisco eye nasa kamar ko yaushe cike suke da gajiya. Ɗan girgiza kansa ya yi. “Nope.”
Ya faɗa a gajarce.

“Ka tabbatar?.”


Aunty ta kuma tambaya tana kallon sa ba tare da ta yarda da babu komai da ya ce ba dole dai akwai wani abun da yake damunsa.

“Sure.”

Ya bata amsa. Ta ɗan shiru kaɗan tare ɗan Murmushi, abin yana bata mamaki bai cika yin in'ina ba idan turanci yake amma muddun ya ce zai yi Hausa anan kwaɓar take.


“To ya aikin naka ya kasance a yau Ranar ka ta farko As supervisor in mining company?.”


Ta tambaya tana ƙara zuba masa abinci a plate dake gabansa. A kullum tana ƙoƙarin tana jansa da fira saboda ya dinga magana, ko ya ya ne, duk da tasan yana matuƙar ƙoƙarin sa wurin yin hakan.


“Alhamdulillah.”


Ya faɗa yana Miƙewa tsaye.


“Ma sha Allah, ina kuma zaka badai ka ƙoshi ba?.”


Ta tambaya da mamaki. Sai da ya ƙari sa gaban sink tare da wanke hannunsa badan ya ɓaci ba, sannan ya juyo yana ma ta murmushi ya ce. “Momma Aunty.” Ya yi ma ta alama da hannu alamun Bacci saboda a gajiye yake.


Ta yi shiru ba tare da ta iya cewa komai ba. Ta bisa da ido ya yi ma ta sallama sannan ya fita daga part ɗin nata dama domin ya cika tumbin sa da daddaɗan girkinta ya zo.

Girgiza kai kawai ta yi. Matar uba ta cuci Irshad gashin nan dai Mutum har Mutum. Sadaukin Namiji ɗan kwalisa ga kyau da dukiya ya tara duk wani quality da mace ke buƙata wurin da namiji, sai abu guda da ya rasa shi ne magana, duk da dama can haka yanayin halittar sa take ba Mutum ne shi mai yawan surutu ba, sai kuma ya haɗu da wannan iftila'i daga Allah Sanadin azabtar War matar ubansa a gare sa, ya dena maganar da a ke fahimta sai dai tazo a rarrabe ƙarfi da yaji ta mayar da shi mai in'ina bisa son zuciya irin nata... Mahaifiyarsa Balarabiyar Ethiopia ce nufin Allah shi ne ya haɗa ta da Alhaji Haashir har ya kai su ga aure, sai dai auren bai je ko'ina ba suka rabu, ba komai ne sanadi ba sai tun lokacin da ta sama ciki ta nuna bataso shi kuma Alhaji Haashir ya ce yana son abin sa, an yi tashin hankali da ita sosai a wancan lokacin sai da kyar a ka samu ta haƙura bata fitar da cikin ba ai kuwa tana haihuwa a asibitin ta bar masa jaririnsa wai kafin yaje gida faɗawa dangi sai dawowa ya yi ya tarar da jariri ita kuma Aabirah ta yi tafiyarta, ransa ya ɓaci sosai da hakan shi ne ya zama sanadin rabuwarsu, har yau dake motsi. Haka Badan yanaso ba ya mayar da jaririn hannun Mahaifiyarsa kafin daga bisani ya ƙara Aure zuwa lokacin yaron da ya ci suna Irshad ya kai shekara ɗaya da rabi a duniya, shi ne ya ɗauke sa daga hannun Mahaifiyarsa ya mayar da shi Wurin matarsa Abida. Da zuciya ɗaya ya yi hakan kuma ta tabbatar masa zata kula masa da ɗan sa tamkar nata kuma ya yarda da ita har ya kai ga bata yaronsa. Ai kuwa nan ta tasa yaro ƙaramin sa da shi da azaba nau'i nau'i ba tare da wani dalili ba haka yaron ya taso cikin karɓar azaba daga hannunta kuma Alhaji Haashir bai taɓa lura da hakan ba sakamakon kasancewar sa mutum ne ɗan kasuwa ko lokacin kansa baya samu bare kuma na Iyalansa....
Bai ankara da azabtar da yaron da take ba sai Ranar da dubunta ya cika ta saka ma Irshad yaron da ba zai wuce shekaru goma a duniya ba a wancan lokacin garwashin wuta a baki wai dan kawai ta kira Sunansa yaƙi ya amsa. Sanadin hakan yaron ya zama kamar kurma babu um bare um'um. Ran Alhaji Haashir idan ya yi dubu to ya ɓaci da abin da ta yi ai kuwa a wurin ya rattaɓa ma ta saki har biyu lokaci guda. Irshad ya daɗe yana jinya a Babban Asibiti dake Malaysia da taimakon Allah tare da jajircewar likitoci maganar sa ta ɗan dawo sai dai ba ta fitowa daga bayama ya koma in'ina.... A can ƙasar Malaysia Alhaji Haashir ya bar sa ya ci gaba da karatu bai dawo da shi Nigeria ba har sai bayan da ya ƙara Aure ya Aura Safiyya da suke kira da Aunty Amarya zuwa lokacin kuma matsawar da Danginsa da ita kanta Abida ke masa ya sa ya dawo da ita bawai dan ransa yaso ba... Kuma haka Rayuwar Irshad ta ci gaba da gudana a Malaysia iyakar sa da su sai dai yazo musu hutu, a hakan ne har ‘yar shaƙuwa ta shiga tsakanin sa da matar baban nasa, burin Irshad tun yana yaro bai wuce zama wani a ɓangaren ɗaukar hoto ba, sai dai shi kuma Mahaifinsa kasuwanci yakeson ya karanta, hakan ya haƙura ya yi biyayya ya karanci kasuwanci sai dai gefe guda yana ɗaukar course ta ɓangaren karatu a kan ɗaukar hoton. Bayan wasu shekaru ne kuma bayan ya kammala karatun sa ya dawo Nigeria ba tare da ya fara aiki ba Alhaji Haashir Mahaifinsa ya yi masa wata Babbar bazata ta hanyar basa damar zuwa wani tafiya na ƙaro ilmi ta ɓangaren ɗaukar hoto a sri Lanka na ƙasar Indiya, ya yi farin ciki sosai da hakan kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya shirya kuma ya tafi tsawon watanni Biyar, a can ne kuma wani babi na daga ƙaddararsa amma ya fannin Soyayya ya faru Tsakanin sa da Ariana kyakyawar budurwa mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen namiji da ya san kansa.....

*WANNAN KE NAN...*


____
_Jan Hankali_

*_Dan Allah Iyayen mu mata a dinga haƙuri da Rayuwa musamman a kan riƙon ‘ya‘yan Miji, wani abun sai an daure amma duk da hakan a dinga haƙuri ana kawar da kai bawai dan mijin ki ya baki yaronsa da K'addda ta fitar da Mahaifiyarsa daga Gidan ba, ke kuma shikenan kin sama hanyar Azabtar da wannan yaron ba kuma tare da ya yi Miki komai ba. Ko kuma wai dan ke kina da wani kwakwkwaran hujja ko dalili ba. A daure a riƙe yaran da basa tare da Mahaifiyarsu tsakani da Allah domin ba'a san yadda Rayuwa zata kasance ba a gaba._*

*Mu tara a next page domin jin yadda zata kaya.*


*_Don't Forget to Like, Comment, and share Fisabilillah, domin waɗan nan sune supporting nawa da zakuyi ku ƙaramin gwarin gwiwa Nkd's ce taku a har kullum ✍️✊🪄_*
_______
________
_______
___
*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*

𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫


*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Arewabooks: @Khadeejarth Sabi'u Yahyah.*


_Dedicated To Oum Yasmeen.❤️_

https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20


*Ep_15-16*


*-100, Obafemi Awolowo Way, Jabi, Abuja, Nigeria.*


*ANNABELLA POV.*


Ta yi tsaye bakin ƙofar hannunta riƙe da handle na ƙofar, tunani take a kan ta shiga ne

Please Login or Register in order to submit comment