Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko kuwa dai ta koma?.

A lissafin ta yau sati guda ke nan da Jaish mijinta yake kulle a ɗaki tun Ranar da ya sama labarin mutuwar Uncle ɗin sa commissioner ya rufe kansa a ɗaki babu irin bugu da naci da batayi masa ba a kan ya buɗe amma yaƙi. Alhininta bai wuce kar ya cutar da kansa ba kuma tana da tabbacin tsawon sati gudan bai saka komai ba a bakin sa.

Wannan shi ne abin da yafi ɗa ga ma ta hankali, duk da cewa tsawon watanni uku ke nan da Auren su amma babu wani shaƙuwa tsakaninsu, kuma ba komai ne dalilin hakan ba sai irin Auren da suka yi, Aure ne na sirri da Mahaifinta da kuma Uncle nasa da a ka kashe suka shirya, biyayya kawai ta yi wa mahaifin ta wato Mr Aabdar Dawlah sai dai tana mamakin dalilin sa na haɗa Aure tsakanin ta da wanda ba addininsu ɗaya ba, ita Christian yayin da shi kuma yake musulmi. Ta kuma sauke ajiyar zuciya a karo na Barka tai tana da tarin tambayoyi da takeso ta yi masa.
Shi ba, da yake matsayin miji a gare ta sai dai bata kai ga yi masa ba domin bata sama fuska ba, gashi kisan da a ka yi ma Uncle nasa ya biyo baya, da shi ne ya dagula komai.
Wannan karon nannauyar ajiyar zuciya ta kuma sauke wa ba tare da ko ɗar ba ta kai hannu da niyyar buga ƙofar sai taga ta buɗe ke nan a buɗe take, to yaushe ya buɗe bata sa ni ba?.


Sannu a hankali take taka wa ta shiga katafaren palon tana ƙarewa ko'ina kallo domin wannan shi ne karon ta na farko da ta hauro sama part ɗin sa. Har ta shigo. Ƙari sawa ƙofar Bedroom ɗin ta yi tare da kai hannu ta murɗa shima a buɗe yake, sa kai ta yi ciki ta shiga.

Sai dai me turus taja ta tsaya lokacin da idanunta suka yi ma ta Kyakyawan gani.


Fitowarsa daga Bathroom ke nan ƙugunsa ɗaure da towel yayin da yake goge sumar kansa da take da tsayi da wani ƙaramin towel dake hannunsa, dogo ne fari tas ƙaƙƙarfa wanda duk inda wani gwarzon saudarkin Namiji yake to Jaish ya kai ko ma a ce ta kera sa.


“Oh Gosh. Am so sorry Sir...”


Ta faɗa da sauri tana juyawa domin barin Bedroom ɗin. Ƙirjinta na wani irin bugu na tashin hankali domin zata iya cewa kaf Rayuwarta wannan shi ne karo na farko da ta ga wani ɗa Namiji a haka, Bama wannan ba babu abin da ya fi bata tsoro sai irin ƙirarsa da ta gani muraran.




Tsaye ya yi yana bin ta da kallon nazari, kamar dai ko yaushe kyakyawar fuskarsa a tamke tamau sai da yaga ta kusa ƙofa sannan ya saita Muryarsa
tare da kiran Sunanta da wata kalar da murya da ita Annabella ta kasa tantance ta.

“Annabella...!”


Dakatawa ta yi ta ɗan saita nutsuwarta tare da Juyowa tana fuskantar sa ba kuma tare da ta amsa ba sai zuba masa lumtsatsun idanunta da ta yi. Ya kawar da kai tare da ƙari sawa gaban wani makeken lafiyayyen Dressing Mirror ya ja stool tare da zama. Tsawon sakanni ba tare da ya ce ma ta komai ba. Ita ma tana tsayen ba ta ce komain ba.


“Haka ne ko sunan naki?.”


Ta ɗan kallesa jin tambayar da ya yi ma ta da tafi kama da ta rainin wayo. Sai dai ta danne tare da faɗin.

“E.”
A taƙaice.


“Mene ne ya kawo ki nan?.”


Sai da a ka kuma ɗaukar tsawon sakanni ashirin kafin ya jefo ma ta wannan tambayar.

“Am'um just dama kawai na zo ne domin dubaka and Ina so na faɗa maka ina son zuwa Gidan mu in anjima.”


Yanzun ma still sai da a ka kuma kwashe kusan minti ɗaya da ‘yan sakanni da alama tattaro kalaman da zai faɗa yake sannan ya ce.

“Kada ki sake. I mean karki sake shigowa nan ko kuma tunkarar wurin da nake and already na faɗa Miki koma ina ne kike da buƙata zaki iya zuwa ba sai kin tambaye ni ba coz i don't care...”


Wannan karon Annabella ta kawo ita wuya, zuciyarta tafarfasa take. Kamar ko yaushe tunani take a kan mene ne dalilin mahaifin ta na ha ɗa ta Aure da wannan mutumin, ba ta ce masa komai ba domin batajin zata iya wata magana a halin da take ciki yanzu. Da gaggawa ta kai hannu kan handle na ƙofar domin fita, sai dai cak ta dakata da buɗewar da take ƙoƙarin yi sakamakon maganar da taji ya kuma.


Duk da bai so ƙara magana ba, amma hakan ya daure ya ce. “Kar ki ƙara saka kalan waɗan nan kayan dake jikin ki, na tsani jar kala da jan kaya, har wannan kwalliyar mai kama da ta aljanu bana buƙatar ki sake yi muddun kinsan zamu haɗu idan kuma ba haka ba....!”


Ya ɗan cije bakinsa ba tare da ya ƙari sa ba, yana ɗan Girgiza kai tare da lumshe ido kaɗan. Ya jingine bayan sa jikin stool ɗin da yake zaune.



Annabella da maganganun sa suka shigeta kwarai tare da bata mamaki kuma kanta ya ɗaure matuƙa, ta kai duba i zuwa kayan dake jikinta it her favorite color, ja ba shi ne best color nata. Sanye take cikin wata ɗamammiyar English Gown Red color, ƙafafun ta da wasu High hills takalma masu tsini, fuskarta kuwa tasha ɗanɗa sheshan make-up da wani red jan baki da ta sha, dama gata fara ta yi kyau sosai ta fito kamar wacca zata fita Gasar SARAUNIYAR KYAU ta Duniya. 👑😍

Dama hakan take Annabella mace ce mai son gayu da tsafta sosai ga iya kwalliya.

Buɗe ƙofar ta yi tare da fita ba tare da iya ce masa komai ba tsaban takaici.


Dafe kansa da ya fara sara masa ya yi yayin da mummunar tunaninsa yake basa dama na aikata abin da ƙwaƙwalwarsa take hasaso masa yayin da zuciyarsa take kuma tursasa masa hakan. Da ƙarfin gaske yakai hannun sa duka biyun tare da dafe kan nasa yana sakin wata ƙara yayin da yake ƙoƙarin ganin muryar da take masa amsa kuwa a koda yaushe cikin kunnen sa bata sama Nasara a kan sa ba, sai dai hakan ya cutura babu abin da ke amsa kowa a kunnen sa fa ce wannan zazzaƙar muryar nata da ba zai taɓa mantawa da ita ba duk da idanunsa a rumtse suke amma hasaso masa wannan kyakyawar fuskar nata yake tana tsaye gaban sa ta ɗan durƙusa kaɗan, kamar ko yaushe sanye cikin jar Doguwar riga fuskarta wadace da make-up hannunta riƙe da kaifaffiyar wuƙar da take yawo da ita saman wuyansa, jajayen laɓɓanta suna furta... “Burina ka kirani da Mommy hakan kaɗai ya wadatar kuma zan kyale kayi Rayuwar ka kamar sauran ‘ya‘ya... If not kuma...” Ta yi Shiru ba tare da ta ƙari sa ba tana cizon laɓɓanta tare da ɗan luma wuƙar a wuyansa har sai da jini ya ɗan ɓullo daidai lokacin shi kuma ya saki ƙarar azaba tare da faɗi ƙasa sunamme.....


A gigice ya watsar da kayan dake saman Dressing Mirror ɗin yana kuma sakin wata gigitacciyar ƙara tare da zubewa a ƙasa yana fitar da wani gigitaccen numfashi.... *_Ya tsani jar kala, ya tsana ganin mace da make-up, ya tsani ganin kyakyawar mace Finally ya tsani kyawawan mata fiye da komai a Rayuwarsa_*🥺😳




___
*_DSS Headquarter Maitama Evenue Abuja._*


*UMNIA POV.*

A fusace D.G Bilal Yusuf Bilal ya watsar da files ɗin dake hannunsa a saman desk dake gabansa tare da Miƙewa tsaye ya daki desk ɗin da ƙarfi, yana watsa gigitattun idanunsa a kan ta yake faɗi cikin wata kalar kakkaurar murya a tsawace.


“Mene ne wannan Officer bafa wasa kikazo yi nan ba, ace wannan ƙaramin binciken ya gagare ki gamawa kinsan irin matuƙar takuramin da a ke ne ta sama wai ma mene ne kika bincike tsawon kwanaki goman nan?.”


Ya ƙari sa a zafafe yana kallon ta.


Ƙara cije laɓɓanta ta yi tana ƙoƙarin controlling kanta tare da saita nutsuwarta ta buɗe Murya da kyar kai da ji kasan ta kawo iya wuya ta ce.


“Mun yi bincike a kan gashin da a ka samu kuma mun tabbatar da gashin na mace ce kuma mun gano ko wacece sannan mun isa gareta, sunanta Clara aikin ta ne kai saƙo daga restaurant da take aiki zuwa Wurin da a ke buƙata a wancan Ranar ma ta kai ma commissioner pizza ne da kuma shawarma kamar yadda ya buƙata, a yadda muka bincika shi ne a wancan Ranar ƙoƙarin raping nata ya yi ita kuma ta yi yadda ta yi iya ƙarfin ta ta buga masa kwalba a kai sannan ta gudu iya abin da muka Gano ke nan bayan mun bincike ta.”


Ta ɗan yi Shiru tana sauke ajiyar zuciya tare da ci gaba da cewa.


“Sorry Sir ina mai tabbatar maka da cewa koma wanene makashin yana dab da shiga hannun mu am very sure?.”


Ya ƙura ma ta idanu kamar mai son tabbatar da kalaman ta, ita ma ta zuba masa nata kaifaffun idanun Zuciyarta a jagule da ɓacin rai lissafa yadda zata wanke fuskarsa da tafi na shouting da ya yi ma ta take. Ta ɗan Girgiza kai tare da cije laɓɓanta tana damƙe Hannunta na dama ta kawar da kai.....


________
_Zakuga Page ɗin is very short. E ku kukaja coz of bakwa comment bakwa like ko reacted balle uwa uba share a gaskiya banajin daɗin hakan sam, ku daure kuna Comment in sha Allah Ni kuma nayi alƙawarin zaku dinga samun Long page wata Rana ma two page's a rana._

*_If not kuma a gaskiya indai banga canji daga gare ku ba next page will be delayed ❌🪄_*

______
*_Don't Forget to Like, Comment, and share Fisabilillah, domin waɗan nan sune supporting nawa da zakuyi ku ƙaramin gwarin gwiwa Nkd's ce taku a har kullum ✍️✊🪄_*
_______
________
_______
___
*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*




*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Arewabooks: @Khadeejarth Sabi'u Yahyah.*


_Dedicated To Oum Yasmeen.❤️_

𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫

*Ep_17-20*


https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20




*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*


Ɗaki ne madaidaici wanda ya fi kama da ɗakin taro ko bincike na kwararrun jami'ai duba da yadda gefe guda na bangon ya kasance ɗauke da Black detective board an yi Linking pictures na mutane da red thread, wuri guda jikin board ɗin ɗauke da wasu rubuce rubuce wasu kuma alamar tambaya ne haɗe da sunaye a jikin wasu pictures ɗin, pictures na mabanbantan mutane da wurare ne a jikin detective board ɗin.



Su biyar ne a ɗakin huɗu suna zazzaune saman wasu kujeru yayin da ɗaya take tsaye tana magana.


Lulu ta saita Muryarta dake ɗauke da ɗan ɓacin rai sannan ta ce.


“A halin yanzu muna da buƙatar sake wani plan about our mission saboda gaba ɗaya plan ɗin mu ya rushe sakamakon mutuwar commissioner da bamu san wanene ya aikata ba da kuma dalilan sa sai dai yanzu ba wannan ne a gaban mu ba, i think we should go to our next target and handle it.”


Ta faɗa tana jinjina kai tare da zura Hannu a aljihun baƙin Wandon jeans dake jikinta tare da mayar da dubanta zuwa gare su.


“Yanzu ta ina ya kamata mu fara ke nan sannan ina ga bai kamata muce zamu bar case ɗin mutuwar commissioner ya tafi a haka ba ya kamata mu binciki lamarin ko nace makashin....”


“Yeah, go on, i am listening to you.”


Cewar Lulu tana kallon Maiji ta yi maganar.


“E shikenan ai ina nufin Mu fahimta cewa ko wanene ya kashe commissioner ya yi ne domin abubuwa biyu zuwa uku, na farko ko dai domin ɗaukar fansa na wani abu da ya taɓa masa a baya, na biyu kuma zai iya kasancewa biyan sa aka yi domin ya kashe sa saboda haka yana da kyau mu bincike ko wanene Makashin kafin muje ga next target namu ko ba haka ba.”

Ta ƙari she tana ɗa ge Hannu tare da kallon mutanen palon.


Ramla ta ce. “Of course not a tunanina ɓata lokaci ne Kawai tsayawa bincikar asalin dalilin mutuwar commissioner ina ga kawai tun da shi ya mutu muje ga Next target ɗin mu.”


Ɗan gyaran Murya Bubba ya yi kaɗan gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu gare sa yayin da shi kuma ya ce.


“Duka kuna da gaskiya yana da kyau mu bincika a kan ainihin dalilin mutuwar commissioner but not now abin da zamuyi yanzu kawai shi ne mu bi mutumin da muka tsara shi ne gaban Commissioner a mission ɗin.”


Neina da ta har ɗe hannu a ƙirji tana sauraren su gaba ɗaya ba tare da ta ce komai ba, har sai da ta gama jin ra'ayoyin su a kan lamarin dama can haka suke sai kowa ya faɗi shawarar da yake gani ta dace wacca ta yi sai a ɗauka, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin.


“A cikin la'anannun wanene next target ɗin?.”



Kai tsaye Lulu ta bata amsa da faɗin.


“Prof Bakori! He is our next target, right?.”

Ta faɗa tana cije laɓɓanta da ɗan ƙarfi Prof Bakori wani suna mai amsa amo a kunnen ta duk lokacin da a ka ambata balle kuma ita da kanta ta furta, Prof Bakori wani azzalumin mutum ne da ya tarwatsa ‘yar ragowar farin ciki dake Rayuwar ta, bata tunanin zata taɓa yafe masa forever sanadin sa da son zuciyarsa ‘yar uwanta kuma Rayuwarta ta rasa Rayuwarta.


“Samra kina lafiya kuwa?.”


Neina ta tambaya cike da kulawa tana dubanta.

Ɗan kawar da kai ta yi tana mayar da hawayen da suka taru ma ta kamar dai ko yaushe ta daure ta jajirce ta mayar da komai ba komai ba cikin dakiya ta ce.

“It's Nothing, Forget it.”


Shiru kawai Neina ta yi domin ta gane halin da ta shiga sai dai ta sha re tare da faɗin.


“Sai mu tsara wurin da ya kamata da kuma rana da lokaci.”


Ramla ta ce. “Mai zai hana mu shirya a gidan sa zamu tare sa, saboda ina tunanin it too risky muje a makaranta saboda akwai tsaro sosai.”


Ta faɗa sakamakon sanin jami'ar da yake Koyarwa kuma ita ma nan ne take karatu akwai matuƙar tsaro sosai idan suka ce a can zasu aiwatar da misson ɗin zasu iya samun matsala.


“Ya kuke gani?.”


“E Neina gaskiya Ramla ta faɗa a Gidan nasa dai zai fi.”


Cewar Maiji a yanzu. Shi ma Bubba ya jinjina kai cike da gamsuwa.

Amsawa Neina ta yi nan dai suka ci gaba da tsara plan nasu yadda komai zai tafi musu a daidai tsawon awanni sannan daga bisani suka sama matsaya kuma suka ware rana da lokacin da zasu aiwatar da misson ɗin nasu.

“Kamar kullum dai ina ƙara tuna muku cewar Badan komai muke wannan gwagwarmayar ba sai dai dan samun ADALCI not for revenge na abin da azzaluman suka mana. It just for Justice haka ne?.!”


Gaba ɗaya suka jinjina ma ta kai cike da gamsuwa. “Oakay ohya let go a yi abin da a ka saba.”


Ta faɗa tana buɗe musu hannayen ta daga tsayen da take gaba ɗaya suka ƙari sa tare da rungumota suna ɗan Murmushi dama sun saba tun bayan haɗuwar su da zamanto War su family guda kuma team ɗaya da suka kafa domin samarwa kansu dama al'umma musamman marasa galihu da a ke zalunta adalci duk lokacin da zasu shirya wani plan ƙa'ida ne idan suka kammala sai sun rungumeta tare da fatan Nasara ita kuma a koda yaushe cikin tuna musu cewar ba don ɗaukar fansa suke abin da suke ba, sai dan samun adalci da ya yi ƙaranci a ƙasar take yi kuma sun ji sun aminta sannan sun gamsu da hakan.


Harɗe hannayensa gaba ɗaya ya yi a ƙirji tare da zuba musu ido yana Murmushi. Murmushi ita ma Neina ta yi tana kallon sa ɗan uwanta mai ƙaunar ta da fahimtar ta a ko wani hali Bubba nata.


*WANNAN KE NAN*



*UMNIA POV.*


Zaune take a office ɗin ta kamar ko yaushe sanye cikin uniform nata na aiki hannunta riƙe da files tana dubawa tare da Nazarin su.
A hankali ta ɗan ɗa go kanta kaɗan tana duban Amelia da ta shigo office ɗin ba tare da neman izni ba kamar dai yadda ta saba. Ɗan Murmushi ta yi domin tasan abin da ya kawo ta. Bata ɗauke idanunta a kan Amelia ɗin ba ta ce.

“Amelia! Ke ce a wannan lokacin ya kike kwana biyu?.”


Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta ƙari sa gaban madaidaicin fridge dake gefe, ta buɗe tare da ɗauko Bottle na ruwa sannan ta dawo ta miƙa ma Amelia da ta zauna tana amsa ma ta da faɗin.


“Ni ce Officer ke har kya tambaya ya ya nake bayan sanin yanayin aikin nawa ko hutu bana samu balle lokacin kaina koda yake ya muka iya gaba ɗaya duk a cikin aikin al'umma ne kuma munji mun gani.”


Ta ƙari she maganar tana dariya tare da karɓar bottle na ruwan da Umnia take miƙa ma ta tana faɗin. “Thanks Dear.”

“Never Mind.”

Umnia ta faɗa tare da komawa ta zauna tana mayar da hankalinta ga Amelia ɗin da ta a je bottle na ruwan a saman desk dake gabanta bayan tasha kaɗan, tana faɗin.


“Kwana biyu bamu haɗu da shi ba, ina fata dai yana lafiya ya ya Bito fa?.”


Umnia ta ɗan rage girman idanunta tana dubanta cike da sheƙiyanci ta ce.

“Wa ke nan kike nufi?.”


Ta tambaya tana dariya. Amelia ta galla ma ta harara.

“Bana son Rashin M fa Umnia ai kin fi kowa sanin wa nake nufi Hamraz nawa mana.”


Umnia ta ɗan taɓe baki tana gimtse dariya ta ce.

“Af sorry fa na ɗan manta ne.”


“Ke kika sa ni dai, ni dai bani amsa ta yana lafiya?.”


Baya ta yi tare da jingina bayanta jikin kujerar tana faɗin. “Nima dai ban sa ni ba kam amma zaki iya zuwa ki duba, kuma ba Bito a ke cewa ba Bittu ne. Amelia har yanzu Hausar ki da sauran ta bata gama nuna ba.”



Amelia bata dena hararar Umnia ba ta lura yau tsiya takeji, ta daure ta amsa ma ta da faɗin.


“Na lura yau magana kike nema, ni kuma ba biye miki zan yi ba domin kina daf ne da zama surukata saboda haka ki ci gaba da min rashin m yadda kika ga dama zaki sa ni ne very soon.”


Ta faɗa tana Miƙewa tsaye domin ta lura ja ma ta rai kawai Umnia zata yi ba zata bata amsar da take nema ba na jin lafiyar Abin ƙaunarta, gwara kawai gobe idan zatazo aiki sai ta biya ai ba nisa ne a tsakani ba.


“Oh sorry masoyiya indai Hamraz ne kun fi kusa saboda haka yana lafiya Qlau Qlau ma, ki zauna mu ci gaba fira dama babu abin da nake yi a yanzun.”


Murmushi Kawai Amelia ta yi halin Umnia sai ita, bata tunanin banda ita da kuma Safiyya (wato twin's sister ɗin Umnia ɗin) sai Hamraz banda su da wuya a sama mai iya jure zama da Umnia domin murɗaɗɗen halin ta. Ita ma ɗin har yanzu bata gama sabawa da wasu halin na Umnia ba, duk da cewa tsawon shekaru suna tare a jami'a suka haɗu har ta kai su ga yanzu da suke aiki da Dss ita Amelia fannin na'ura ta karanta, kuma sanadin haɗuwarta da Umnia ta san Hamraz sannan har ta fara son sa tun kafin Matarsa ta rasu gashi har yanzu da ta rasu ko kyakyawan kallo bata samu daga gare sa ita kuma taƙi ta haƙura da shi, duk da cewa ba wasu shekaru ne mai yawa tsakanin ta da shi ba, she's just thirty something domin Umnia ta girme ta.



“No thanks bar shi gobe zan biya da kaina na dubasa, ki ci gaba da aikin ki da kika ga zaki iya kam, na zaƙulo makashin commissioner domin na lura D.G a zafafe yake a kan lamarin, nima komawa zan yi wurin nawa aikin ɓangaren da na fi kwarewa.”

Amelia ta faɗa tana ya mutsa Black Beauty fuskarta.


Shafa goshinta Umnia ta yi tare da mirza hannunta da hakan ya zama ma ta ɗabi'a, ta dubi Amelia da idanunta da suka yi ja tsaban rashin samun wadataccen bacci da zafafa ga aiki, ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin.


“Tohm shikenan a gai computer uwar na'ura.”


Murmushi Amelia ta yi tana girgiza kai tare da fita daga office ɗin.


Yayin da Umnia ta yi shiru tana kallon gefe guda ba tare da ta ci gaba da abin da take yi ba ƙwaƙwalwarta da bata gajiya a kan komai ta fara tariyo ma ta wasu shekaru baya wani abu da ya taɓa faruwa, lumshe ido ta yi tare da tattare gaba ɗaya nutsuwarta tana tariyo abin da ya faru.


*Flash Back...*


Tana zaune ne saman tabarma ita da Hamraz da ya kasance ɗan ƙanwar mahaifinsu da ta rasu tun a wurin haihuwarsa, da ga nan matar baban nasu Uwani ita ta ci gaba da kula da shi tare da ‘yar ta da take goyo a wancan lokacin.


Duk da cewa fira suke amma hakan bai hanata jiyo ƙarar takun Uwani ba mai kama da na samu dawan farko, tsaban ƙibanta da girman jiki. Wani irin zillon bugu tamkar zata fito waje haka Zuciyarta ke ma ta, ta miƙe da sauri tana ƙoƙarin amsar ledojin dake hannun Uwanin. Ai kuwa ta daka ma ta wani uban tsawa da gardiyan Muryarta a ɗa ge take dubanta tana faɗin. “Umnia!! Yau ni ce zan shigo tsaban gulma kike neman kwatarmin ledar hannuna saboda maita irin na uwarku da ta manne wa ubanku har ya ma ta cikin da ta haifeku ba tare da Aure ba, kuma ta tafi ta bar ku da halinta na kwaɗayi da son abin Duniya. To aradun Allah ba zata saɓu ba. Aure zan Miki na huta kuma ban ga uban da zai hanani ba domin ni ke ciyar daku ba wancan mashayin uban naku ba. Sama'ila Tantus shi zan aura Miki Gobe Goben nan zaki bar min gida ki koma can gidansa domin a Goben za'a ɗaura.”


Ta ƙari sa maganar tare da kifa ma ta lafiyayyun maruka dama da hagu tare da jifa da ita gefe tamkar kayan wanki.


Wani irin wahalallen kuka Umnia ke yi kukan da yake fitowa tun da ƙasan zuciyarta wannan wacca kalar Rayuwa ce Aure kuma nawa take kwata kwatan ta da za'a ce aure za'a ma ta kuma bada kowa ba sai Sama'ila Tantus Mutumin da kowa ya shedesa da shan giya da neman mata.

Da kyar ta samu ta tashi daga jifan da Uwani ta yi da ita, da gudu tana ɗingisawa ta ƙari sa wurin Uwani dake ƙoƙarin shiga ƙazamammen ɗakin da yake daf da rushewa. Da dukkan hannayenta ta kamo ƙafafun Uwani cikin zubar hawaye take bata haƙuri a kan ta janye maganar Auren da ta yi.

A fusace kuma cike da zalunci da mugunta Uwani ta watsar da ita gefe tare da kai ƙafa zata hamɓareta sai dai gam, taji an riƙe ƙafar da mugun ƙarfi, da sauri ta ɗa go tana duban wacca ta yi hakan.

“Safiyya!.”

Ta faɗa tana duban matashiyar budurwar dake gabanta tana fitar da huci.

A fusace Safiyya tayi wurgi da ƙafar Uwanin da har sai da ta kusa faɗi domin ƙibanta rinjayrta yake yi.

Wurgi da bokitin fenti dake hannunta ta kuma yi ba tare da damu da ragowan kunun dake ciki da ya zube a ƙasa ba sakamakon fashewar da robar ta yi. Dawowarta ke nan daga tallen kunun da take ma Uwanin a kullum takai bakin tasha.

Da gudu ta ƙari sa wurin ‘yar uwan nata tare da ɗa ga ta tsaye, tana duban Uwani da ta miƙe tana muzurai domin kuwa duk iya shegenta da muguntar ta baya aiki a kan Aunty wato Safiyya saboda zafin kai da Yarinyar take da babu mai iya tankwarata ta tankwaru har ita kanta Uwanin balle kuma mahaifin su da babu abin da yake taɓuka wa a gidan domin

Please Login or Register in order to submit comment