Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙari sa wurin idanunta suka sauka saman fuskarsa dake a kwaɓe sai ta kasa ƙari sa abin da ta yi niyya ta zuba masa ido.


Hannunta dake a baki tana tsotsa Samara ta fito da shi, idanunta a kan ‘yar uwan nata zata yi magana ke nan taji cikin wata kalar sassanya kuma nutsatsitsyar murya an furta wata gajeruwar kalma da turanci.


“Selfsame.!”


Ya faɗa yana dubansu gaba ɗaya ganin tsananin kamanni da juna da suke yi tamkar an tsaga kara domin idan baka san su ba, kuma ka gan su a mabanbantan wurare zaka yi tunanin duk mutum ɗaya ne.


“Lah ashe Mutum ne wallahi mutum ne shi..”


Samara ta faɗa tana washe baki. 😂


Yayin da Samra da shi suka zuba ma ta ido. Ya ɗan yi Murmushi da turanci ya kuma faɗin.


“Kin yimin rauni fa.”


Wannan karon gaba ɗaya sun fahimce abin da ya faɗa domin ba baya ba suna jin turanci.


Toshe baki Samara ta yi yayin da Samra ta kuma dubansa a karo na biyu ta ce.


“Kayi haƙuri Ɗan Uwa Samara bataji gashi kuma ta fitar maka da jini bari na taimaka maka.”


Ta faɗa tana duban yadda jini yake fita a yatsar nasa tare da ƙoƙarin cire kallabin kanta dogon gashin kanta mai santsi da yake a kwance babu kitso ya bayyana gaba ɗaya ya zubo a bayanta sakamakon garin cire kallabin ta haɗa da ribbon da a ka tufke gashin da shi, da ƙaifaffen haƙorinta ta yi amfani wurin ya gar kallabin sannan ta kamo hannun nasa ta fara kici kicin ɗaurewa wai a nufinta domin jinin ya tsaya. Yayin da ita kuma Samara jikinta ya yi san yi domin bata cijesa da nufin fitar masa da jini ba, duk da cewa zuwa lokacin an shaide su da muddun faɗa ya haɗa su da wani har haƙoransu ya taɓe su tofa sai sun fitar musu da jini koda bada niyya suka yi ba Sanadin hakan ne ma ya sa yara suka yi baya baya dasu a ka ware su daban ana yi musu kallon Monsters.

“Ai kinga abin da kika yi ko?. Kin fitar masa da jini kuma na hanaki cizon kowa.”


Samra ta faɗa tana galla ma ta harara. Kamar ba Samara ɗin ce babba ba. Shi kuwa da bakinsa ya yi nauyi yana kallon abin almara sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya ganin yadda wacca ta zo daga bayan ta ja hannun ta farkon zasu bar wurin.


“Wait..”


Ya faɗa tare da ƙari sawa garesu ya kuma faɗin.


“Ku ‘yan biyu ne? Kuma anan gidan kuke zaune ina Iyayen ku?.”


Ya tsinci kansa da yi musu wannan tambayar cikin harshen turanci domin tafi masa sauƙi wurin magana ba tare da ya sha wahalar fitar maganar ba.



Lokaci guda yanayin dake fuskokinsu ya sauya zuwa wani yanayi daban da ya kasa ganewa.

“Bamu da kowa mu kaɗai muke rayuwa kowa ya tsanemu bamu da iyaye kuma haka wasu suke ce mana wai monsters.”


Duk wannan maganar Samara ce take yi domin ita ce mai sauƙin hali Samra kam akwai zuciya shi ya sa ko yanzu da ya yi musu tambayar. Auntyn su ta tuno kuma ranta ya yi matuƙar sosuwa domin a ganinta Auntyn su ta tsanesu ne shi ya sa ta tafi ta barsu.



Cike da al'ajabi da kuma tausayi yake Kallon su yana jinjina kai sai kuma ya ɗan yage tsawon sa zuwa daidai nasu ya zuba musu ido tsawon sakanni sannan ya buɗe baki ya ce.


“Kuna da kowa mana.!”



“Wanene?.”


Samara ta kuma tambaya domin tana mafarkin a wayi gari suma ace suna da Dangi kamar kowa su fita a wannan Rayuwar ta maraici.


“Allah mana! Allah yana tare daku kuma sannan nima ina tare daku kuma sannan nayi alƙawarin baku kariya da riƙon ku da Amana da kuma kulawa daku da duk ƙarfina da dukiya har zuwa ƙarshen rayuwata..!”


Shiru suka yi suna dubansa da alama suna tantama ne a kan maganar sa.


“Amma me ya sa za kayi hakan bayan kasan cewa muɗin ba kowa bane?.”


Ya yi ɗan murmusa jin tambayar da Samra ta yi masa a wanann karon.


“Saboda me kika tambaya?.”


“Saboda rashin imani da son zuciya ya yi yawa a yanzu kowa kansa ya sa ni babu mai taimakon wani koda ma ya yi taimakon domin son cimma wani muradi na son zuciya ya yi...”


Da tsananin mamaki yake dubanta da bazata haura shekaru goma sha ɗaya zuwa sha biyu ba a duniya amma take da wannan kaifin tunanin.


“Kai ma baka da kowa ne kamar dai mu?, baka da da Mama da Baba da duk ‘yan uwa?.”


Samara ta tambaye sa. Ya ɗan yi shiru yana dubanta tare da nazari a kan amsar da zai bata.

“Ina da Mama sai dai ta tafi ta barni tun bansan kaina ba.”


Ya tsinci kansa da faɗin hakan yayin da can ƙasar Zuciyarsa yake jin babu daɗi kuma Kamar Kullum tambayar dake ransa game da mahaifiyar tasa ta kuma tsaya masa arai. _Shin mene ne dalilin ta na tafiya ta barsa tun bai san kowa ba, bai san kansa ba, bai san komai ba kuma bata ƙara waiwayarsa ba har yau dake motsi?_


“Ayya ka dena kuka na fama maka abin dake damun zuciyarka ne? Kayi haƙuri ka dena domin Samra ta ce jarumi baya kuka ragwaye ne suke kuka, domin babu maraya sai rago, shi ya sa nima na de nayi bakaga ina da kwanji ba ma ai saboda bana kuka ne.”



Ta yi maganar iya gaskiyar ta tana masa nuni da hannunta alamar dai yaga kwanjin ta.

Maganar ta basa dariya kuma ta basa tausayi kuma sannan yaji tausayin su da shi kansa.


“Shi ne kuma naga kike kuka ɗazu?.”


Ya tambaya. Kama baki ta yi. “Lah ai na manta jarumai basa kuka.”🤓


Murmushi kawai ya yi yana Miƙewa tsaye ya ce.


“Wacece Samra?.”


Kallon juna suka yi sannan suka kallesa a tare suka ce. “Gata.!” Samara ta faɗa hakan, yayin da Samra ta ce. “Gani!.”
Sosai wannan karon suka basa dariya da ya kasa riƙewa har sai da ta fito fili suka sake baki suna kallon sa.


“To kana da Baba? Mu dai bamu da shi.”


Ya kalla Samara da ta faɗa.


“Yes i have a father..!”


“Kai kam kaji daɗi.”


Suka faɗa a tare with pity face.


“Kuma kunji daɗi mana.”


“Ta ina?.”

Suka tambaya.


“Saboda kuna da ni mana ko kun manta Alƙawarin da nayi muku ne yanzu?.”


Gaba ɗaya suka Girgiza kai sannan suka ce. “A'a.”

“Zan yi matuƙar ƙoƙari wurin ganin na cika alƙawarin dana ɗauka a kanku, muddun ina numfashi babu abin da zai cutar daku. Daga yau selfsame sunan ku ke nan a wurina.”


Gaba ɗaya suka yi dariya da alama sun amince da shi har zuciyar su domin ba'a taɓa musu daddaɗan Lafazi irin wanda ya yi musu ba a yanzu.


“Kayi alƙawari?.”


Cewar su gaba ɗaya a tare. “In sha Allah..”


Ya basu amsa. “To ni kuma da wani suna zaku dinga kirana?.”


Da sauri Samara ta ce. “Best Daddy...”


Ai da sauri tun kafin ta ƙari sa ya hau girgiza kai yana faɗin. “No ku canza dai.”


Samra ce yanzu ta ce. “Dimple Perfect.”


“Kaji wani suna kuma...”😅


Ya faɗa a Zuciyarsa yana murmusa wa.


“Nice name and nice you, daga yau da Dimple perfect zakuke kirana, ohya come and give me a nice hug my selfsame.”


Da gudu suka ƙari sa ya yi musu side hug a tare gaba ɗaya suna Murmushi cike da farin ciki yayin da shima yaji Zuciyarsa ta yi ƙal....


Tun daga wannan Ranar a daidai wannan lokaci a wannan taƙin Rayuwar su ta sauya daga yawan baƙin ciki da ƙunshi na rashin iyaye ta karkace ta koma zuwa wata kalar Rayuwa mai daɗi mai tsayawa a rai cike da farin ciki, kamar yadda ya yi alƙawari a gare su bai manta ba duk da cewa sun ci gaba da zama a gidan amma duk wata hidimarsu tana kansa a Sanadin su yasa a ka rushe ginin makarantar dake gidan marayun zuwa katafaren ƙerarren ginin makaranta na zamani a sanadin su ya sa abinci ya wadata a gidan abubuwa na Alkhairi da dama sun faru a gidan a sanadin su. Duk da cewa baya zuwa wurin su sosai domin da daɗewa ya koma ƙasar da yake karatu dama hutu yazo shi da Familyn sa suka zo Katsina Dangin Mahaifin nasa shi ne fa ya biyo Uncle ɗin sa gidan marayun kawo ziyara abin da ya faru ya biyo baya. Sosai yake ƙoƙarin ganin sun manta da wani baƙin ciki dake Rayuwarsu ta baya ya mayar da hankali wurin gina musu ingantacciyar sabuwar rayuwa da zarar ya sama hutu yake zuwa gare su wani lokacin ma sai dai kawai su ganshi ba tare da ya sanar da su zai zo ba, a hakan kuma Rayuwar tana gangarawa sabo mai tsanani ya shiga tsakanin su da shi, kuma shekaru sun ɗan ja, sun kuma zama ‘yan mata domin tuni maƙerin budurci ya gama ƙera sa a tare da su. Domin Akwai lokacin da ya kawo musu ziyara ya kasa gane su, su ma sun kasa ganesa domin an ɗan kwana biyu rabon da ya zo da kansa saboda karatu da ya yi zafi sai dai ya aiko, shi ne fa ya yi musu zuwar bazata... Ya cika da mamaki ganin yadda selfsame ɗin nasa suka koma haka.

Suma hakan ganin yadda ya koma Kyakykywan Balaraben saurayi mai ji da dukiya da tsantsar kyau da kwarjini. A lokacin ba zasu haura 16 year's ba kuma a lokacin ne suka kammala Secondary school nasu har sun fara zuwa jami'a suna matakin level one first semester suna dab da fara jarabawa.

A lokacin tsoro ya kama shi musamman ganin irin Tsantsar kyau da yaran suke da shi kamar jinin larabawa ya fara tunanin zaman su a wurin akwai hatsari duk da cewa ana basu kulawa da tarbiyya mai kyau a gidan. Sai dai shi hakan bai wadace shi ba. Ya gama yanke wa kawai Next time idan ya dawo hutu tare zasu koma, sai dai shi ya ci gaba da kula da su, zaman su a gidan marayu ya ƙare, musamman da ya fahimci mene ne feelings nasa a kan ɗaya daga cikinsu. 🤯
Haka kawai ya yanke a ransa ba tare da sa ni a kan mene ne ƘADDARAR dake gaba ta tanazar ba...!💔

Haka ya gama abin da ya kawo sa gare su zuwa yamma ya yi musu sallama domin a ranar zai koma, ai kuwa kamar ƙananun yara sun sha kuka sosai domin haka kawai suke ji kamar haɗuwar su ta ƙarshe ke nan da shi gani suke kamar zai manta da su ba zai dawo gare su ba. Sai dai yadda ya yi musu alƙawari kuma yake ƙoƙarin ganin ya cika hakan ya ɗan basu gwarin gwiwa na cewa Dimple Perfect nasu ba zai manta da su ba duk runtsi duk wuya, basu ƙara tabbatar da hakan Bama sai lokacin da zai tafi yadda yake hawaye kamar yaro ganin suma suna yi haka suka kuma ɓata lokaci suna kuka tare duk da zuwa lokacin ya dena koda side hug da yake musu, badan zuciyoyin su sun so ba haka suka rabu cike da kewar juna suna yi ma kuma juna fatan Alkhairi. Haka Rayuwar su ta ci gaba da gangarawa har lokacin wani ɗan taƙi da Samra ta yi masa take da TAƘIN ƘADDARA domin a taƙin abubuwa da dama suka faru dasu abubuwa masu tsayawa a rai mummanar ƙaddara ta afko musu a silar son zuciya na wasu mutanen da kuma neman Duniya da ya saka wasu mutanen suke aikata komai ba tare da tunanin mai zai je ya dawo ba, su dai kawai su sama biyan buƙatar su basu damu a za'a rasa rai sanadin hakan ba domin a ganin su _RANAR BAYAN BUƘATA_ Ai rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba.....


*🩸(_Mafarin Ƙaddarar su..!_)🩸*

😭😭

*2020*
*SHEKARA TA DUBU BIYU DA ASHIRIN*
*BAKORI LOCAL GOVT, KATSINA STATE...*


_Dagelawai Street_





Tafiya take yi a gefen titin daga yadda take tafiyar cikin tsananin dauriya hawaye na ma ta zuba kuma ba ta damu da ta sha re ba zaka san ba ƙaramar damuwa da baƙin cikin rayuwa take ba ji take ta tsani rayuwarta ta tsani kanta komai ya fi ce ma ta a kai, tunanin Rayuwa take yi idan ta ce Rayuwa tana nufin komai dake Cikin ita Rayuwar son zuciya shi ne silar komai cikin kunnuwanta kuwa wannan muryar tasa ce take ma ta amo yayin da ya tsareta yaƙi bata hanya kuma yake faɗa ma ta ɗayan biyu ne kodai ta amince da shi ta ko kuma jarabawar ta ba zata yi kyau ba, ya daɗe yana neman ta amince da shi ta basa kanta tun ranar da ya fara ganin ta a school ɗin amma taƙi aminta babu irin naci da bai yi ba, amma taƙi shi ne yanzu da suka yi jarabawa na kammala level one ya tsareta yake faɗin muddun bata amince da shi ba to kuwa jarrabarwar ta ba zata yi kyau ba kuma yake fata ma ta sai ya yi ajalin rayuwarta sai ya dusashar da duk wani farin ciki dake ciki muddun bata amince ta saba kanta ba.

Wai me yasa a rayuwa wasu mutanen basu da imani ne, kan su Kawai suka sa ni?.
Wai me yasa wasu mutanen suke zama sheɗanu saboda son duniya?.
Wai mene ne yake damun mutanen mune na yanzu?. Jahilci ko son zuciya da neman Duniya?....
Waɗan nan su ne kawai tambayoyin da suke ma ta yawo a ƙwaƙwalwarta. _A wancan lokacin_
Ta ɗa go da idanunta dake zubar hawaye Muryarta a shaƙe ta kira sunansa. “Prof Murtala Bakori..!”. Sannan ta ci gaba da faɗin.
“Na rantse da Allah mai girma idan kaga kayi Nasara a kai na ka rabani da mutuncina to ka tabbata sai dai idan bana hayyacina ko kuma bana Duniyar ma gaba ɗaya kuma duka maganganun ka na yanzu nayi recording a wannan wayar ta hannuna da kake gani kuma kai tsaye yanzu wurin Director's na jami'ar nan zan kai, ba tarwatsa Rayuwata ba, idan kaso karka barni da rai, ba alfaharin ka shi ne riƙe min sakamakon jarabawa ba, ka je na Barka da Allah shi ne zai mana hisabi muddun ka cutar dani....”


Ta gama maganar tana juyawa ta nufa ƙofa domin fita da office ɗin nasa kuma kamar yadda ta faɗa masa ne zuwa wurin Director's na makarantar zata yi ta kai recording na muryar nasa kowa yaji abin da yake yi.


Tsaban tashin hankali na kalaman ta da ɓacin rai na abin da ta ce zata yi a kansa ya sa Prof Bakori bai san lokacin da ya miƙe ba, a zafafe ya ɗauki wata kwalbar dake saman Desk dake gaban sa ya nufeta gadan gadan daidai lokacin da ta kai bakin ƙofar tasa Hannu zata buɗe shi kuma ya ƙari sa wurin ba tare da jiran komai ba, iya ƙarfin da Ubangiji ya masa ya buga ma ta wannan kwalbar a ka, ai kuwa take a wurin ta zube sumammiya goshinta yana zubar da jini ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba sai dai ba za ta manta ba kafin idanunta su gama rufewa ta lura da Dariyar da yake yi da wasu maganganu da bata ganewa sannan kuma tana gani dishi dishi ya fara janta ya saka a wani abu da yafi kama da buhu ya kaita zuwa motar sa ya saka a Boot sai a lokacin ne ta ƙari sa suma sakamakon kanta da ya bugu da wani ƙarfe na motar...😭




A hankali take buɗe wa manyan idanunta tana mamakin ganinta kwance gadon asibiti ga Samra a gefanta tana kuka tare da wata Malama Zakiyya ɗaya daga cikin masu kula da su a gidan marayun. Sai a lokacin ƙwaƙwalwarta take tariyo ma ta ainihin abin da ya faru da ita. “Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un...” Kawai ta iya furta wa da kyar tana kici kicin tashi zaune sai dai ta kasa sakamakon ƙafafun ta da suke ma ta raɗaɗi na zafi, da ƙarfi ta cizge drip dake Hannunta.
Da iya ƙarfin ta ta yi amfani wurin ganin ta sauko daga gadon amma ta kasa koda motsi, kuka take sosai zuwa yanzu ta gama tuna Komai da ya faru tabbas Prof Bakori ya yi Nasara a kan ta ya gama da komai nata mutuncin ta tabbas a wancan Ranar ta iya sanin abin da ya faru domin tsananin Azaba shi ne ya farkar da ita daga suman da ta yi, sai dai iya roƙo, cizo, ya ƙushi, ihu duka basuyi amfani ba har sai da wannan baƙin mugun ya yi Nasara a kan ta ba tare da ta iya kwartar kanta ba sakamakon abin gusar da hankali da ya fesa ma ta, sai dai duk da hakan hankalin nata bai gushe yadda ya kamata ba.



“Samara ki dakata Dan Allah ki bari kina famawa kanki rauni ne yau satin ki biyu anan baki san inda kanki yake ba bayan shafe awanni arba'in da huɗu da muka yi ana Neman ki, sai da kyar a ka sameki cikin wani kango da babu kowa, Samara FYAƊE! a kayi Miki abin da muke jin Labarin sa yana faruwa a kan wasu mutane ga shi yanzu a kan ki ya sauka...!”

Cikin tsananin matsanancin kuka da fitar hayyaci Samra take wannan sumbatun yayin da ta kamo ‘yar uwan nata ƙam gaba ɗaya suna wani irin gamjin kuka gunin ban tausayi, Samara ta yi tsitt tana sauraren Samra yayin da ɗif kukan da take yi ya dakata jikinta ya saki alamar dai ta suma, daidai lokacin kuma likitan da Malama Zakiyya taje ta kira ya shigo haka ya yi abin da zai iya a kan ta, ita ma dai Samra sai allurar bacci suka yi ma ta saboda yadda take kuka kamar ranta zai fito.

Bayan wasu kwanaki a ka sallame Samara daga Asibitin suka koma Gidan marayun tare da kai ƙarar abin da ya faru a ofishin ‘yan sanda sai dai abin takaici shi ne sam ‘yan sanda sun ƙi suyi bincike a kan abin sai wasu irin tambayoyi nacin mutuncin da suke ma ya wai ta yi musu bayani yadda ya yi lokacin da zai ma ta fyaɗen wai domin ta haka ne za su san yadda zasu yi bincike a kan lamarin. Tsananin ɓacin rai shi ne ya saka ta baro ofishin ‘yan sandan ba tare da ta ce musu komai ba ta biyo titi tana kuka mai cin rai da tsanar Rayuwa. Yayin da Samra take bin ta a baya tana Faman kwala ma ta kira tare da sauri domin ganin ta ƙari sa gare ta, tunanin da ta ke yi da kuma kuka da ya saka take gani dishi dishi har Batasan inda take jefa ƙafafunta ba, daidai lokacin da ta dakata da tafiyar da take yi ta juya domin kallon Samra a daidai lokacin kuma wata ɓakar mota Highlander ta hawo titin da wani irin matsanancin gudu na tashin hankali gadan gadan saitin wurin da Samara take tsaye tsakiyar titin ba tare da ta ankara ba wannan motar da ta ƙari so ta yi wani irin ɗibar karen mahaukaciya da ta ita kuma ba tare da ta tsaya ba ta yi gaba abin ta yayin da Samara ta zube gefe tana fitar da jini ta hanci da baki kuma kanta ya fashe.

A lokacin mutane suka taru a wurin ana kallon yadda take fitar da numfashi da kyar idanunta a kakkafe nishi tana fita da sauri sauri. Ita kuwa Samra cak taja ta tsaya daga kiran sunan Samara ɗin da take yi tun lokacin da ta hango motar take ma Samara alama da ta matsa ganin bata gane ba shi ne ta buɗe baki domin ma ta magana, sai dai irin bugun rashin imani da mai motar da fuskarsa ta haddatu a ƙwaƙwalwar Samra ya yi ma Samara ɗin shi ne abin da ya sa ta tsaya cak kamar wacca wutar lantarki taja. Wani irin wahalallen numfashi da Samara taja tare da kiran sunan Samra shi ne abin da ya dawo da ita hayyacinta ta ja wani irin wahalallen numfashi da haɗiye wani irin mugun yawu ta watsar da abin dake Hannunta da gudu ta ƙari sa tana ture mutanen da suke taru ana kallon abin da ke faruwa ta ƙari sa wurin tare da kamo ‘yar uwan nata da fuskarta da jikinta gaba ɗaya jini ya gane wanke wa ta ɗaurata a saman cinyarta tana neman a gaji sai da kyar a ka samu ta bari a ka saka Samara a Napep domin kaita Asibiti ita ma ta shiga sannan Matuƙin Napep ɗin yaja.


_Tsugunno bata ƙare ba...😭_




Domin koda suka ƙari sa asibitin ƙiri ƙiri babu irin roƙo da batayi ma Likitocin ba a kan su taimaka su duba ‘yar uwanta karta mutu amma sun yi kunnen uwar shegu domin kuwa Hospital Drivern Napep ɗin ya kai su sun ƙi karɓar Samara su bata agajin gaggawa wai haka tsarin asibitin yake wai har sai an biya tukunna kuma wai aiki za'a ma ta, suka ambaci kuɗaɗen da yawansu suka shallake tunanin Samra.


Haka nan tanaji tana gani tana rungume da ‘yar uwanta a tsakiyar asibitin Mutane da yawa sun taru suna Kallon su amma babu wanda ya iya taimaka musu da komai. Samara tana kwance saman cinyar Samra cikin hali na rai ko Rayuwa numfashin ma da kyar yake fita wai dan ma wasu daga cikin ma'aikatan asibitin sun ji tausayin su an samu wanda ya bada oxygen aka saka ma ta, idanunta a kakkafe tana kallon sama numfashin ma ya dena fita.
Haka Samra tanaji tana gani ‘yar uwanta ɗaya Danginta farin cikin ta rayuwarta ta mutu cikin wannan halin babu wanda ya iya taimaka musu a gaban ta numfashin Samara ya dena fita yayin da ta dakata da ko wani motsi alamu dai rai ya yi halinsa, a take a wurin Samra ta faɗi sumammiya bata ƙara sanin inda kanta yake ba.


Sai bayan wasu kwanaki da ta farka ta ganta a wani irin baƙin gida mai cike da ababen tsoro da mutane kala kala sai daga baya take samun labarin wai suna a Lagos ana ƙoƙarin fita da su daga ƙasar domin a siyar dasu. A firgice ta farka kuma ta sama kanta a wannan halin da ya yi matuƙar Girgiza duniyar ta, tunaninta bai wuce a kan shin ina gawar ‘yar uwanta yake ba, kuma garin ya ya tazo Lagos sai dai babu mai bata amsar tambayoyin..... Haka ta ci gaba da Rayuwa tsawon kwanaki a wanann baƙin gidan kafin a wani dare ta yi ƙoƙarin gudu daga gidan su biyu tare da wata budurwa da ta kasance ‘yar asalin mai duguri ce sunanta Hauwa'u ana kiranta da Maiji. ƘADDARA CE! Ta yi silar haɗuwar su a nan gidan kuma a wancan Daren Allah ya basu damar guduwa daga Gidan bayan shafe kwanaki suna gudu a daji sun samu sun fito cikin gari da kyar daga bisani suka samu wurin ɓuya makafa tsawon kwanaki suna garari da gararanba a garin Lagos domin nemawa kansu mafita da abin da za su ci, domin babu mai basu, silar hakan suka haɗu da Ramla cikin wani mummanar hali kuma suka taimaka ma ta suka ci gaba da Rayuwarsu su uku abin su kafin wani lokaci suka koma Abuja sanadiyyar hakan kuma a ranar da suka sauka Abuja BUBBA da Matarsa Umma suka shigo Rayuwarsu kafin Neina da take matsayin Yaya a wurin Bubba ita ma ta shigo Rayuwarsu sannan munanan abubuwa da dama suka biyo baya da suka ƙari sa tarwatsa farin cikin dake Rayuwar kowannen su kuma zuciyoyin su suka bushe babu abin da suke buƙatar samu sai ADALCI kuma kafin samun wannan sai ka zama Very Strong ka mayar da komai ba komai ba, sai kayi juriya matuƙa, a taƙaice wannan ke nan abin da ya faru da Samra (Lulu) har take matakin da take a yanzu....


_Wannan shi ne labarin Samra ita da ‘yar uwanta Samara da irin gwagwarmayar da suka sha a Rayuwar har ya yi silar rasa Rayuwar Samara.🩸😭💔_



1. Shin mene ne ainihin abin da ya faru har Samra ta tsinci kanta a Lagos?.
2. Wane ne Prof Bakori shi ne mutumin da yake matsayin next target nasu Samra, mene ne zasu yi masa?.
3. Ramla, Maiji Dukkanin su mabanbantan mutane ne kuma ko wacce tana da Labarin ta, shin ya ya Labarin su yake wani irin ƙalubale suka fuskanta a nasu Labarin?
4. Mene ne ainihin abin da ya faru da Mienal Ɗiyar Neina kuma tana a wani hali a halin yanzu shin tana

Please Login or Register in order to submit comment