Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sa kafin nan take bin Auntyn nata Umma da mijin Auntyn nata da suke kira da Bubba restaurant nasu domin tallafa musu da wani abun da ba'a rasa ba.


Ramla tana karatu ne anan wata Babbar University dake Abuja tana karantar Nazarin Ɗabi'a.... Yayin da ita kuma Maiji ta kammala karatun na Nursing yanzu haka kwana kaɗan ya rage ta fara zuwa gudanar da internship nata.

Ƙoƙari take sosai wurin ganin abin bai taso ma ta ba, tana iya kar bakin ƙoƙarin ta wurin ganin ta bijirewa umarnin da sheɗaniyar muryar dake ma ta amo a kunne take ba ta, kuma ba ƙaramin wahaltu wa da hakan take ba. Cikin Wata iriyar kiɗimammiyar ƙatuwar murya mai ban tsoro ake bata umarni da ta je ta sha jini ta yi kisa kona wanene kawai jini a ke so tasha a wannan daidai lokacin, yayin da ita kuma ta dage taƙi ta yi abin da ake umar tarta dashi.

Da ƙarfin gaske ta kuma damƙe zanin gadon da take kwance a kai yayin da gaba ɗaya jikinta ya fara Miƙewa daga kwancen da take tamkar ɗa ga ta a ke, baƙin gashin kanta ya rufe ma ta fuska gaba ɗaya, bata sare ba taƙi karɓar umarnin da alama kuma ta fara fusata su, da ƙarfin gaske suka sake ta ta koma saman gadon ta faɗa ta kwancen, kanta ya bugu da headboard na gadon, ta kurma wani gigitaccen ihu, bakinta yana fitar da wani irin baƙin jini haka ma gefan idanunta baƙin jinin yake fitarwa kamar ruwa, idanunta suka ragu daga girman da suka ƙara, jikinta ya dawo daidai daga lallan kwashewar da ya fara, gashin ta ya koma wuri guda tamkar ba shi ne yake a hargitse ba. Iyakar wahala kam ta sha shi.


Daidai lokacin kuma a ka turo ƙofar Bedroom ɗin a hauka ce Maiji da wata kyakyawar Dattijuwar mace suka shigo da alama ita ce Neina.

Da gudu Maiji ta ƙari sa tare da rungumo Lulu da ta fita a hayyacinta tana kuka sosai ta kalla Neina da ta durƙusa tana sharewa Lulu jinin da ya ɓata ma ta fuska da tissue, ta ce.

“Neina abin nan fa ya yi yawo Lulu tana cikin wani hali na tabbatar tana shan wahala sosai, gashi indai wannan abun zai motsa tana fitar da baƙin jini sosai, ya kamata muyi wani abu a kan hakan a nemo malamai na addini domin ina zargin akwai saka hannun mutanen ɓoye a wannan halin da Lulu take ciki.”


Neina ta yi shiru tana sauraren Maiji da nazarin Maganar ta, gaskiya ta faɗa. Shigowar da Ramla ta yi ne ya hana Neina faɗar abin da take shirin faɗa.

Da gudu ita ma Ramla ta ƙari sa tare da rungumo Maiji haɗe da Lulu ɗin tana kuka kuma ko basu faɗa ma ta ba, ƙarar da taji ya fahimtar da ita abin da ke faruwa. Ajiyar zuciya Neina ta sauke sannan ta ce.

“In sha Allah za'a bincika za'a nemo Malamin da ya dace wanda zai iya raba Samra da waɗan nan mutanen kuyi haƙuri ku dena kuka kunji in sha Allah zata sama lafiya.”

Jinjina kai Maiji ta yi dan batajin zata iya cewa komai a halin yanzu, sosai take masifar tausayin Lulu da halin da take ciki, ita kuwa Ramla mai arhan hawaye ban da hawayen babu abin da take yi domin ita ce mai rauni a cikin su, koda yake dole ta zama mai rauni duba da yadda Rayuwarta ta baya take. Maiji ita ce mai ɗan dama dama a cikin su kuma mai sanyin hali, Lulu kuma ita ce Jarumar cikin su.

“Amma tun da na tafi basu zo leƙo ba sai yau ko?.”


Neina ta tambaya.


Jinjina kai Maiji ta yi sannan ta ce.

“E basu zo ba sai yanzu.”


_____
*- 100, Herbert Macaulay Way, Garki, Abuja, Nigeria*




*IRSHAD POV.*


Ya yi Shiru kaɗan yana ƙoƙarin biyewa zuciyarsa da take tariyo masa wasu watannin baya da suka shuɗe a rayuwarsa kuma yake fata da kar ya ƙara tunasu a cikin Rayuwarsa domin sun wuce da wani sa rai da yake da shi a Rayuwa.

*Flash Back...*


Ya kuma Murmushi yana ƙara ƙasa da kansa domin son hango kyakyawar fuskar nata gaba ɗaya. Ita ma Murmushin take ta kallesa kaɗan tana mayar da Camera ɗin ta cikin backpack Sannan ta ce.

“Suna na Ariana. Suna mai daɗi ko?.”


Ya jinjina ma ta kai, ta kuma murmusa wa. “Haka Mutane suke yawan faɗa cewa na dace da sunana, idan na tambaye su Dalili sai suce saboda ni ɗin kyakyawa ce. Kai fa mene ne Sunan ka, kai ma kana cikin team namu na lens journey da zamuyi ke nan fatan Nasara tare da addu'a kar Ubangiji ya haɗa mu da namun dawa a tafiyar da zamuyi na ƙarin ilimi cikin wannan daji mai haɗari.”

Ta yi maganar ba tare da wannan ƙayataccen murmushi ya bar saman kyakyawar fuskarta ba, tana kuma miƙa masa hannu, alama dai take da su gaisa. Bai ce komai ba, kuma bai dena Murmushin ba, ya dai ƙura ma ta ido babu ko ƙiftawa tare da kallon hannun nata da take miƙa masa._


“Pooh! Kanaji kuwa?, lafiya dai, ya ya tafiyar taku ta kasance?.”


Aunty ta kuma magana da take ta faman maimaita masa da alama ya yi nisa duniyar tunani, hakan ya sa ta ɗan bubbuga hannunta a saitin fuskarsa.


Yaja wata ajiyar zuciya tare da kallon ta, ya sauke idanunsa da suka yi ja ƙasa, har yanzu gajiya bai sake sa ba kamar yadda zuciyarsa bata gama yarda da abin da ya riga ya faru ya shuɗe ba.

“Jiya bamu samu mun yi wata fira ba. Ina fata dai komai lafiya a tafiyar taka?.”


Jinjina ma ta kai ya yi sannan ya amsa ma ta da faɗin.

“In shsha Allah.”!

Ya faɗa da ‘yar in'ina ba tare da ya damu da kallon da take bin sa da shi ba.

“Daddy ya ce jibi zaka fara zuwa Mining Company As a supervisor, zaka iya kuwa ko sai ka ƙara huta wa sosai?.”

Girgiza ma ta kai ya yi. “Zaka iya ke nan?.”

Ya jinjina ma ta kai again.

“Fatan Nasara amma naso ace ka ƙara hutawa.”

Ya yi Murmushi kaɗan yana Girgiza kai. Hutu ba dai a gidan Daddy ba, mutumin da babu abin da ke gabansa fa ce nema a nema kuɗi kota halin ƙaƙa shi dai kawai kuɗi kuɗi kuɗi...!


_
(★†★)
___

*UMNIA POV.*


Sosai aiki ya sako ta gaba ko lokacin hutu bata samu dama yanayin aikin nata ba koda yaushe take samu ta huta ba, balle kuma yanzu da ya zo da matuƙar sarƙaƙiya domin bincike suke ita da tawagar ta ba dare ba rana amma still babu wasu gamsassun hujjoji ko bayanai, sai dai duk da hakan basu karaya ba, kuma a yadda akalar binciken nata ya tafi ita da team nata sun fi zargi a kan macece ta yi kisan sakamakon wasu evidence da suka ƙara samu sai dai Wacece a'ina take kuma mene ne dalilin ta?.

Daga sama sosai D.G ya matsa ma ta a kan lamarin, shi ya sa ko sukuni bata wani samu balle lokacin tunani always Busy take.


_____

*🌹 Perfectly Pen's ✍️✊*


*Our Ongoing Book's...✍️*


*1_ƘADDARA CE!.*

*BY: C Candy.*

*2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*

*BY: Queen Kainaat.*


*3_RANAR BIYAN BUƘATA.*

*BY: Nainarh KD Nkd's.*


*4_DESTINY LOVE.*

*BY: Oum Yasmeen.*



*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝*



*🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥*.



_____

*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*


𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫


*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Arewabooks:@KhadeejarthSabi'uYahyah.*


_Dedicated To Oum Yasmeen.🔥_

https://arewabooks.com/chapter?id=667e4d52fa05d6121a41e085
_
*DANNA LINK NA SAMA DOMIN KARANTA COMPLETE PAGE*👆

*Ep_9-10*


*Ctystal Hospital: plot 501 Bangui Street, Aminu Kano Crescent, wuse, Abuja, Nigeria.*


Dr Abdallah ya ci gaba da faɗin.

“Ciwon nata yana kamanni da hysteria sai dai duba da bayanan da kika bada da kuma binciken da aka yi, ba hysteria ba ne, da ace lokacin da abin yake taso ma ta tana ‘yan bige bige dai ko surutai tohm za'a iya kiran hakan cutar hauka ke damunta, amma yanzu bamu tabbatar ba har sai mun ƙara zurfafa bincike akai.”


Shiru Maiji ta yi tana sauraren abin da Dr ɗin yake faɗa, bai bata haushi ba sai ji da ta yi ya ce wai ciwon hauka, ke nan mahaukaciya ya mayar da Lulu ɗin, ranta ya ɗan ɓaci na rashin dalili bayan kuma ita ta gallaza sai an zo Hospital an fara bincika kafin a kira wani malamin haka Lulu ta biye ma ta suka zo badan tanaso ba.

“Shikenan mun ji mun gode, Lulu zo mu tafi.”

Ta faɗa hakan lokacin da ta miƙe tare da kamo hannunta Lulu da ke zaune tana jinta tai banza da ita.


★.…..

“Wai da gaske Murmushi nake gani a saman fuskar ki?.”

Maiji ta tambaya a lokacin da ta tashi motar ta karya kwanar fita daga hospital ɗin bayan sun fito sun shiga Motar.


Taɓe baki Lulu ta yi idanunta na kallon hanya ta ce.

“Ba dole nayi Murmushi ba idan ta kama ma harda dariya zan yi ehee.”


Maiji ta ɗan kalleta kaɗan jin abin da ta ce.
“Wato dai ni kike ma Dariyar ba komai zan rama ne, saboda na kawo ki wurin Dr ya duba lafiyar ki, kikemin dariya ko dan raina ya ɓaci lokacin da ya kira ki da mai ciwon hauka shikenan ai.”


Maiji ta faɗa tana ɓata rai kamar da gaske ta yi fushin. Taɓe baki Lulu ta yi idanunta na kallon wuri daban kamar ba zatayi magana ba sai kuma can ta ce.

“Sorry nasan saboda an kirani da mai ciwon hauka shi ya sa ranki ya ɓaci. Sai dai ban ga laifin sa ba dan ya yi tunanin hakan domin da hakan na dace ko kin manta.”


Shiru Maiji ta yi taƙi kulata don ta lura yau dai kamar ba Lulu Mace mai zafin rai da saurin fushi take tare ba, wata ƙila wannan wata ce daban.


“Shikenan nayi shiru tun da ba zaki kulani ba, bari ki gani ma bacci zan yi.”


Girgiza kai kawai Maiji ta kuma yi sannan ta ɗan saci kallon Lulu da ta rufe ido bacci yana ƙoƙarin ɗaukar ta.


_“Aunty Wai da gaske Samra tana da aljanu?.”_



Ya mutsa fuska Lulu ta yi ƙwaƙwalwarta tana tuna ma ta a wasu shekaru can abin da ya faru.


*Flash Back...*


Samara bata jira amsa daga wurin Mahaifiyar tasu ba da suke kira da Aunty, ta kuma cewa.

_“Kuma da gaske ne wannan mutumin da ya zo Gidan mu har ya mareki a gaban mu sannan ya ce sai kwace mu daga hannun ki shi ne Baban mu?.”_


A tsorace Aunty take Kallon Ɗiyar nata tana Girgiza kai cike da tashin hankali jin abin da take faɗa. Shikenan kuma Komai ya rushe daga yadda yake bayan cutar ta da ya yi, ya kuma dawowa cikin Rayuwarta ita da ‘ya‘yan ta domin ya raba su, ya tarwatsa musu Rayuwa. Sai dai tanaji muddun tana raye ba za ta taɓa bari hakan ta faru ba koda mene ne kuwa zatayi domin ganin ta kuɓutar da ‘ya‘yan daga sharrin wannan baƙin mugu da ya yi sanadin rabata da duk wani farin ciki na Rayuwarta ya tarwatsa komai ya raba ‘yar uwa da ‘yan uwanta ya yi sanadiyar tsintar kanta a halin da take yanzu, an ya kuwa zata iya yafewa wannan mutumin kuma don mugunta yanzu neman rabata da yaran nata yake a bisa son Zuciyarsa da neman Duniya zai rabata da su da ta mallaka a rayuwa bayan kowa ya gujeta.


_“Dama kullum ‘yan class ɗin mu suna cewa bamu da Baba mu shegu ne saboda ke kike kaimu makaranta, yanzu zance musu su daina zagin mu, muma muna da Baba sai dai mugu ne tun da ya mareki kuma ya yi ƙoƙarin yima Samra fyaɗ.....”_


Bata ƙari sa faɗar abin da ta yi niyya ba, sakamakon buge ma ta baki da Aunty ta yi, nan da nan kuwa wurin ya fashe jini ya fita.
Samra dake kwance saman laps ɗin Auntyn tana sauraren su kamar mai bacci ta yi saurin tashi tare da rungumo ‘yar uwanta suna kukan a tare suna kallon yadda lokaci guda Auntyn tasu mai kaunar su ta rikiɗe ta koma wata abar firgitar wa a gare su, saboda ɓacin rai.

_“Shi ba uban ku ba ne shi mugu ne mugun da ya raba tsakanin ‘yar uwa da ‘yar uwarta ya raba ‘ya da Mahaifin ta mai ƙaunarta ya yi ma Yarinyar da batasan komai ba a rayuwarta fa ce kare kanta da mutuncinta daga maza ɓata gari, shi kuma ya yi amfani da wannan damar ya raba ta da mutuncinta domin biyan buƙatar sa na neman Duniya, kuma shi ne yanzu ya dawo domin raba mahaifiyar da ta yi matuƙar gwagwarmaya wuya ko daɗi wurin ganin yaran ta biyu sun taso cikin rayuwa mai inganci, a kan su ta rabu da kowa nata ta zaɓa ta yi nesa da Danginta domin ta basu Rayuwa mai inganci a wurin da bata san kowa ba kuma kowa bai santa ba, duk dan Yaran da ta samu ta hanyar keta alfarmarta da wani can ya yi saboda Burin Duniya, duk dan su taso cikin mutunci da kima kamar sauran ‘ya‘ya...”_


Ta yi Shiru sakamakon wani malolo da ya tokare a maƙoshin ta yaƙi gaba bare baya... Ta kai Hannu tare da dafe sai tin Zuciyarta tana tari da kyar... Da gudu yaran suka ƙari sa wurin tare da rungumota suna kuka sosai... Samra kuwa babu fuskar da take ma ta yawo a allon Zuciyarta fa ce fuskar wannan baƙin mutumin da ya zo Gidan su a rannan ya mare Antyn su a gaban su sannan ya yi ƙoƙarin raping nata matsayinta na Yarinya ƙarama da bata haura shekaru goma ba a duniya bai duba wannan ba.

Da kyar ta samu tarin ya sassauta ma ta, ta kamo hannun yaran nata ta haɗe wuri guda sannan ta fara magana da kyar kai dagaji kasan ba ƙaramin Azabar wahala take sha ba.

_“Ni ce uwarku kuma ni ce uba a gare ku ni ce komai naku, naso ace ƙaddara ta bar mu wuri guda a tare, sai dai hakan ba zai yiwu ba, dole zan nema muku wurin da ya dace daku ci gaba da rayuwa domin ku tsira da mutuncin ku sannan ku kuɓuta daga hannun wannan azzalumin mutumin kuma sannan ku riƙe wannan cewa shi ɗin azzalumi ne kuma mugu mai son kansa da neman duniya.”_

Kuka sosai yaran suke gunin ban tausayi ita Samara ma da take da asthma har ta fara fita hayyacinta, Samra kuwa tsaf duk gaba ɗaya maganganun Mahaifiyar tasu sun shiga kanta kuma sun sama wuri sun zauna. Yarinya mai matuƙar kaifin basira da tunani saboda haka taso ta fahimci wani abu daga cikin maganganun Mahaifiyar tasu sai dai shekarunta bai kai nan ba, domin lamari ne da ko da ɗan shekaru hamsin yaji tamkar sauka irin ta aradu da kuma tsananin sarƙaƙiya da ruɗani da kuma firgitarwa zai kasance a gare sa, balle a gare su da bazasu haura shekaru goma a duniya ba a wancan lokacin.


*_Present Dqay.!_*
_

“Lulu! Lulu, Lulu, ta Lulu tawa kwana biyu bamu haɗu ba daga ina haka naga har kyau kika ƙaramin wato Bama kiyi kewata ba ke nan?.”


Kallon wurin da suka shigo ta yi sannan ta kalla mai maganar tana dafe kai, wai ashe har sun ƙari so gida sun ma fito daga mota sun shiga palo bata sa ni ba, har sai da taji maganar wannan mara aikin yi ɗin a wurin ta, e mana mara aikin, tun da a haukarsa son ta yake ba, hakan rashin aikin yi ne Babba a wurin ta. Soyayya ma bata taɓa yi ko tunanin yi ba balle kuma a je ga maganar saurayi. A da kam da ƙuruciya ke ɗawainiya da ita, taso ta shiga cikin sahun jerin masoya tare da mutumin da take Ganin shi ne daidai da zaɓin ta, sai dai kuma idan aka ce ƙaddara! Tofa la shakka ɗan Adam baya wuce tasa ƙaddarar....


“Ka rabu da ita bata jin daɗi sosai, to ya kake two days ka ɓuya ko duk karatun ne?.”


Maiji ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi tana zama saman 1sieter, domin ita ɗin mace ce mai sauƙin kai da kuma fara'a shi ya sa kowa nata ne babu ruwan ta. Ita kam Lulu ko ci kanka bata ce masa ba, ta nufa Up abin ta.



“Ayya mene ne yake damunta hakan?.”


Ya tambaya fuskarsa tana nuna damuwa domin shi da gaske yake son Lulu yake.

“Ciwon kai ne kawai fa kuma tasha magani.”

Maiji ta basa amsa da faɗin hakan a gajarce kana ta canza firan da faɗin.


“Yaushe kazo ne, babu kowa ne a Gidan Neina fa?.”


Sai da ya sauke ajiyar zuciya jin ba wani Babban abu ba ne sannan ya ce.


“Ina ga ta shiga can part ɗin ne wurin abokan hiran nata.”

Ya ƙari sa faɗa yana dariya. Ita ma Maiji Murmushi ta yi dan ta fahimta wurin da yake nufi. Ɓangare daban daga cikin gidan Foundation ne guda da aka ware shi ya zama wurin kula da gajiyayyu da kuma ƙana nan yara waɗan da ƙaddara ta raba su da iyayensu, kamar waɗan da suka ɓata a wani wurin kuma ba'a ga Iyayen su ba, ko kuma waɗan da aika haifa aka ‘yar a wani wurin ko kuma marayu sai kuma tsafaffi waɗan da iyalansu basu basu kula da ta dace ko kuma basu damu dasu Bama gaba ɗaya, duk yawancin su ne a wurin Neina ita ce ta kafa Foundation ɗin kuma take tallafa musu da Dukiyarta da lafiyarta da ƙarfin ta, da kuma iliminta, domin ganin Rayuwar ko wannensu ta inganta.


Ganin yadda yake ‘yan waige waige ne ya sa ta ɗa go kanta daga danna wayar da take ta kalle sa tare da faɗin.

“Lafiya dai ko?.”


Ya yi Murmushi.

“Ban ga abokiyar faɗar tawa ba ne.”


Ita ma Murmushin ta yi don ta fahimci Fatiyya yake nufi.


“Abrad ke nan ka manta tana restaurant ai Fatiyya yanzu ba zama kuma.”


Buɗe bakinsa da ya yi domin magana hakan ya yi daidai da shigowar Neina Palon ita da Ramla bakinsu ɗauke da sallama.

Amsa musu shi da Maiji suka yi sannan suka ƙari sa shigowa Ramla sai faman galla masa harara take yi, shi kuwa ya yi dariya domin yasan dalili, saboda haka tun kafin ta ce wani abu ya riga ta da faɗin.


“Sorry fa Allah da gaske tun jiya naso kawo Miki sai dai Dawowar Pooh ita ce ta hanani ƙari sowa kuma fa har na kamo hanya sai juyawa nayi.”


Ya faɗa yana miƙa ma ta wasu folders. Sai da ta karɓa sannan ta dakata da galla masa uwar harara da take kana ta ce.
“Ni ba tambayar ka nayi ba, na goda Allah ma daka kawomin yanzu domin na san ka da shiririta wata ƙila ma mantawa kayi.”

Ta yi maganar tana mayar da kallon ta ga Maiji sannan ta ce.

“Maiji kun dawo lafiya. Ya ya Lulu ɗin tana ina ne?.”


“Alhamdulillah kam. Tana sama.”

Maiji ta bata amsa.


Ramla ta nufa stairs hannunta riƙe da folders tana jin sa yana faɗin.


“Da gaske nake jiya naso zuwa ko dan ganinta ita ba sanyin ruhina sai dai Dawowar Dodo shi ne ya hana ni.”

“Kai ka sani kuma Ni kam tun da folders sun ƙari so gareni komai ta fanjama sannan ka shirya ma haɗuwa da Discipline mugu a gobe.”


Ta faɗa tana haye wa sama abin ta. Shi kuwa ya yi Dariya sanin wa take nufi, wani lecturer nasu ne a jami'a saboda tsananin zafin sa da kuma mugunta a cikinsa shi ya sa suke ce masa Discipline mugu.


“Da alama koma wanene wannan wanda ka kira da Pooh Dodo ɗin ba ƙaramin shakkan sa kake ba tun da har ka fasa zuwa nan. Kawai saboda jin labarin ya dawo.”


Cewar Maiji tana Dariya bayan ta yi ma Neina da ta zauna sannu da zuwa dama tun ɗazu Neina sun gaisa da Abrad ɗin da ya zama ɗan gida domin ya saba da kowa Jami'a ɗaya suke da Ramla Department ɗaya haka ma course ɗaya suke karanta Sanadin hakan suka haɗu daga nan abota ta shiga tsakanin su Sanadin hakan kuma har gidan yake zuwa anan ne ya saba da kowa na gidan kasancewar sa mutum ne mai yawan barkwanci ya zama abokin faɗa tare da Fatiyya, ita kuwa Maiji cikin mutumtaka suke gaisawa haka ma da Neina yayin da ita kuwa uwar gayyan da tun Ranar da ya fara ganin ta ya fara son ta kuma yake nuna ma ta alama, sai dai ko kallon arziƙi bai taɓa samu daga gare ta ba, domin ta riga ta faɗa masa ita babu soyayya ko Aure a gaban ta sai dai da alama bai ji ba domin ya ci gaba da nace ma ta, za'a iya cewa ma kusan saboda ita yake zuwa Gidan.



“Ke kam ba za ki gane ba ne kawai domin ban ma san ta yadda zan miki bayanin Pooh ba ya wuce duk yadda kike tsammani mugun shakkan sa muke Especially ma Abdallah da har wani rawan jiki yake a gaban sa.”


Abrad ya yi maganar yana dariya. Ita ma Maiji dariyan take domin burgeta Abrad yake sam bata gajiya da fira da shi.

“Ai kam naga alama.”


Ta faɗa nan suka ci gaba da fira wani lokacin su sako Neina ciki daga bisani ma ta tashi ta shige ɗaki ta bar su nan bata daɗe da shiga ba shima Abrad ya yi ma Maiji sallama ya tafi yana faɗa ma ta zai biya ta restaurant ma domin kawai ya tsokana abokiyar faɗar tasa wato Fatiyya. Dariya kawai ta yi sai bayan tafiyar nasa sannan ita ma ta tashi ta shiga Ɗakin da Neina ta shiga a ɗazu.

_____
*_Don't Forget to Like, Comment, and share Fisabilillah, domin waɗan nan sune supporting nawa sa zakuyi ku ƙaramin gwarin gwiwa Nkd's ce taku a har kullum ✍️✊🪄_*
_______
________
_______



_____

*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*


𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫


*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Arewabooks: @Khadeejarth Sabi'u Yahyah.*


_Dedicated To Oum Yasmeen.❤️_



*Ep_11-12*


*MAIJI POV.*


Kamar yadda ta yi tsammani kuma ta riga ta sa ni, zaune ta hango Neina gefan Bed ta zuba tagumi hannu bibbiyu da alama dai ta tafi sana'ar, wato tunani da babu Ranar denawa a gare ta, har sai Ranar da abin da take tunanin domin sa ya dawo gare ta, sai dai hakan abu ne mai matuƙar wahalar gaske.

A hankali ta fara takawa har ta ƙari sa wurin ta sannan ta zauna a ƙasan carpet dake wurin ta zuba wa Neina wacca da alama ma batasan ta shigo ɗakin har ta ƙari so wurin ba ma, ido tana kallon ta cike da tausayawa, tabbas Neina Abar tausayawa ce, tasha gwagwarmaya sosai taci matuƙar wahala a hannun mijinta a da, kuma mahaifi ga Ɗiyarta da ta ɓata tsawon watanni duk a dalilin son zuciya da neman Duniya ido buɗe irin nasa.... Ɓatar ‘yar nata shi ne dalilin damuwarta, a kullum burinta bai wuce ina ne za'a ga Mienal ba, babu inda ba'a bincika ba, faɗin ƙasar Nigeria, an yi binciken amma shiru kakeji babu alamar Mienal ko labari a kanta. Tun ana binciken har an gaji an fawwalawa Allah komai...


“Shin tana ina ne, wani hali take ciki, tana raye ma, idan tana rayen a'ina kuma a hannun su wa??.”


Wannan shi ne tambayar da Neina take ma kanta a kullum, yanzun ma hakan take furta wa a fili ba tare da ita kanta ta san tanayi ba.

Girgiza kai kawai Maiji ta yi Hawaye na zubo ma ta, ta sha re, sannan ta kamo hannun Neina ta riƙe ƙam ba tare da ta iya furta komai ba. Sai a lokacin

Please Login or Register in order to submit comment