Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Uwani ita ke ciyar da gidan gaba ɗaya shi dai abin da ya sa ni shi ne kawai yadda zai sama kuɗin da zai sha giya ya yi tatul ya yi ta bacci shi ne kawai a gabansa.
Duk da cewa sai taga dama take basu abincin idan kuma bata ga dama ba sai dai su kwana da yunwa ba zata basu komai ba har da Hamraz da yake ƙaramin su domin shekaru huɗu ne tsananin sa da su Umnia ɗin.


“Wannan lalataccen kallon da kikemin da waɗan nan idanun naki kamar na kyanwa, ba shi ne zai hanani abin da nayi niyyar yi ba domin gobe Goben zan ɗaura Aure tsakanin Umnia da Sama'ila Tantus babu wanda ya isa ya hana Aikin banza kawai mtsww.!”


Ta ƙari sa maganar cike da ƙarfin hali domin ta tsargu da irin kallon da Aunty ke ma ta, ta ja tsaki tare da shigewa ɗaki tana muzurai cikin ranta kuwa tana tunanin yadda zata haɗa Aunty da sabon Bokan ta da ta yi, domin ayi ma ta kurciya ta bar gidan gaba ɗaya idan hakan ma ba zai yiwu ba a saka ma ga sha'awar maza ta tambaɗe kamar uban ta domin ta gaji da ganin su a Gidan babu abin da yake tashin hankalin ta sai tsaban kyau da suke da shi kamar Balaraba wa wannan shi ne abin da yake da ɗa hura wutar tsanarsu a Zuciyarta domin ita ‘yar ta da take ɗaya tilo gare ta, ba ta da wannan kyau da suke da shi kuma suka yi gado wurin mahaifiyar su domin taji Labarin cewar shuwa Arab ce duk da cewa bata taɓa haɗuwa da ita ba sai sau ɗaya Ranar da ta kawo wa mijinta Adamu yara mata da ba za su wuce shekaru biyar ba a duniya a matsayin yaran da ta haifa bayan ya yi ma ta ciki ba tare da Aure ba, kuma ta yi tafiyarta abin ta tun daga Ranar basu sake ganinta ba har yau dake motsi haka yaran suka taso a gidan uban nasu Adamu wanda da shi gwara babu domin babu abin da ya sa ni ko kuma ya iya sai shan giya ya yi ta bacci kamar matacce. Gidan gaba ɗaya a hannun Uwani yake ita take ciyar da su shi ya sa take Rashin mutuncin da ta ga dama babu mai taka ma ta birki. Ba ƙaramar azabar wahala yaran suka kwasa a hannunta ba tun tasowar su babu nau'in wahala da basu san da zamanta ba daga hannun Uwani kuma babu mai iya kwaɓar ta a kan abin da take yi a kan su domin har da Asiri ta haɗa wurin mallake gidan da mutanen ciki.


*Present Day....*


Ƙarar da wayar Umnia ta yi shi ne abin da ya dawo da ita hayyacinta, ta sauke ajiyar zuciya bayan ta yi picking call ɗin tana sauraren Muryar ‘yar uwanta nata kuma Rayuwarta da takeji kamar tana cikin damuwa. Saboda jin muryarta da yi tana sheshsheƙar kuka.


“Aunty! Mene ne yake faruwa wai? Please ki faɗa min naji Muryar ki da alama kuka kikayi ko kike yi?.”


Umnia ta faɗa tana Miƙewa tsaye hankali a ɗan tashe.


Da kyar ta samu ta saita Muryarta tare da rage sautin kukan nata sannan ta ce.

“Betterhalf Yarana! Ina nufin ina buƙatar Yarana a tare dani ba zan iya ci gaba da jurewa ba Betterhalf har yau na kasa yarda cewa Yarana sun mutu sanadin rushewar da gidan marayun da na kaisu ya yi. Betterhalf bazan taɓa yafewa kaina ba a kan Hakan...!”


Maganar take yi cikin matsanancin dauriya da kuma sheshsheƙar kukan da yake cin ranta.


Hankali tashe Umnia take faɗin.

“Calm Down other half just calm down your Mind gani nan zuwa gidan yanzu.”


Ta faɗa hakan tare da kashe wayar hankalinta a mugun tashe ba tare da ta tsaya jin abin da Auntyn zata faɗa ba, cikin sauri ta haɗe tarkacen ta tare da fitowa daga office ɗin sauri sauri ta shiga mahaya ta sauko ƙasa sannan ta ƙari sa motarta ta buɗe tare da shiga ciki ta bar Headquarter ɗin da gaggawa.




___
_Masu ƙorafi a kan cewa ba'a ci gaba*daga inda a ka tsaya a Page na gaba, sai da a taɓo wani wurin daban, abin da nakeso ku fahimta shi ne, labarin yanayin salon sa ne yazo a hakan saboda zaku ga ana yawan Flash Back kuma har yanzu ba'a tsaya a wuri guda ba a taɓo nan ne a kuma taɓo can, kuyi haƙuri da yadda yanayin Labarin yake zuwa haka salon yake ba dole ne sai an tashi a wurin da a ka gama a fejin baya ba_*

____
_(0708 521 2808.) 👈 Wannan lambar da nake bayarwa ga masu Buƙatar a yi musu Graphic Design ta sama matsala what'sapp sun rufe saboda hakan zaku iya samun mu ta wannan lambar a halin yanzu. (08081129487.)_

_____
*Kar a manta da danna sharing koda zuwa ga Group Biyar ne da kike ciki, sai kuma sharhi a kan abin da ya shige muku duhu, na gode Nkd's ce taku a har kullum. 😊🥳👑*

_MARUBUCIYAR...!_


1. SARAUNIYAR KYAU
2. ANEESERH (Innocent Girl.)
3. TSANTSAR SO
4. KIN CUCENI
5. RANAR BIYAN BUKATA. E.T.C. 😄


*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*
https://chat.whatsapp.com/FWlnTWWOlBb1RFtWNEwPri

*Ep-21*

*-100, Herbert Macaulay Way, Garki, Abuja, Nigeria*


*IRSHAD POV.*


Tafiya yake yi cikin nutsuwa hannunsa na dama cikin aljihun Navy Denim Trouser ɗin sa, yayin da yake sanye da riga neutral armless, daidai lokacin da ya ƙari sa bakin entrance na palon ya ciro hannun tare da buɗe ƙofar ya shiga ciki da sallama ɗauke a bakinsa yana cire longwing Shoes dake ƙafafunsa. Sai dai babu kowa a palon hatta Triples ɗin Aunty domin sun tafi School shima don yau ya makara ne shi ya sa har yanzu yake a gida bai fita ba yanzu haka Breakfast ɗin nasa ya zo ci kamar yadda ya saba.

Shiru ya yi yana nazarin ya tafi ko kuwa domin ya ga alamar babu kowa a palon. Har ya juya ke nan da nufin fita ya jiyo sheshsheƙar kuka da magana ƙasa ƙasa kuma da alama Aunty ce ke yi domin muryarta ya ji, da sauri ya juya tare da nufar ɗakin da yake jiyo sheshsheƙar, daidai lokacin da ya shiga yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin ita kuma tari ya sarƙe ta wayar dake Hannunta ta faɗi yayin da jini guda guda ya fara fitowa daga bakinta da hancinta idanunta suka fara ƙafewa tarin kuma bai barta ba.


A hanzarce ya ƙari sa wurin tare da tallafota yana kiran sunanta sai dai da alama bata jinsa domin ta riga ta suma a lokacin. Abin da zai iya tabbatar wa yaji a cikin maganar da take yi shi ne kawai Yaranta da yaji ta faɗa. Sai dai halin da take ciki bai bashi damar tunanin ko wasu yaran take nufi ba.

A hanzarce hankali tashe ya saɓe ta a ƙafa ya fito da ita compound na gidan yana kwalawa Driver kira. Da sauri ya saka ta a mota bayan Driver ya buɗe, a hanzarce shima Drivern ya shiga tare da jan motar Irshad yana saba umarnin su tafi hospital dake kusa domin tana jin jiki sai a hanya Irshad ya samu ya kira Daddynsu Alhaji Khalil I Khalil sannan ya faɗa masa abin da ke faruwa ai kuwa hankali tashe shima Alhaji Khalil I.K ya baro abin da yake yi ya nufa asibitin.




*UMNIA POV.*


Tuƙin take yi amma tsaban yadda hankalinta yake a tashe sai taji kamar ma motar bata sauri duk da gudun da take yi a titi. Cikin nufar Ubangiji ta ƙari sa Gidan lafiya.
Ajiyar zuciya kawai take saukewa lokacin da ta fito daga motar ta da ta paka a tsakiyar compound na gidan, zata shiga ciki amma sai wasu daga cikin securities na gidan da suka san ta suka tsayar da ita, ɗaya daga cikinsu ne ya ce.

“Madam bata nan ba'a daɗe ba ƙaramin Oga (Irshad ke nan) ya tafi da ita zuwa asibiti bata cikin hayyacinta ina ga ma suma ta yi.”


Dafe goshi Umnia ta yi hankalinta yana da ɗa ɗugunzuma wurin tashi da kyar ta samu ta saita nutsuwarta tare da tambayar sa address na hospital ɗin.

Ya ce bai sa ni ba sai dai ya kira ƙaramin Oga ya tambaye sa.

“No need bar shi kawai zan kira sa da kaina buɗemin gate na tafi.”


Ta faɗa tana ciro Wayarta tare da nufar motarta ta shiga ciki bayan ta dannawa Irshad kira, wurin kira uku ta yi bai ɗa ga ba, sai a na huɗun ta samo ya ɗa ga nan yake faɗa ma ta asibitin da suke. Ajiyar zuciya ta kuma saukewa sannan ta tayar da motar ta ta bar gidan direct zuwa address na asibitin da ya bata.


*ICPC STAFF CLINIC ABUJA, NIGERIA.*



Bata gama paka motar yadda ya kamata ba, ta fito a hanzarce ta ƙari sa shiga ciki sauri sauri kunnen ta maƙale da wayarta tana sauraren Irshad da yake ma ta bayanin ta ɓangaren da suke har ta ƙari sa wurin.


“Ki kwantar da hankalin ki tana ciki likita ya ce babu damuwa sosai akwai abin da ta tuno ne ya jefata a wannan halin da take ciki.”


Cewar Alhaji Khalil I.K yana duban Umnia da ta ƙari so wurin tana tambayar halin da ‘yar uwan nata take ciki.


Jinjina kai kawai ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba domin ji take kamar zatayi kuka tsoro take yi kar ‘yar uwan nata ɗaya tilo da take da, ta tafi ta barta. A halin yanzu hankalinta ba'a kwance yake ba sai Aunty ta dawo daidai. Wuri ta samu ta zauna saman resting chair dake gefe ta dafe kanta cikin rashin abin yi tana tunanin Rayuwarta ta baya.


*FLASH BACK...*



Kamar yadda Uwani ta faɗa washe gari ta tara mutane a ka ɗaura Aure tsakanin Umnia da Sama'ila Tantus bisa sadaki dubu hamsin da ta riga ta gama da babin su. Ba ƙaramin tashin hankali Umnia ta shiga ba lokacin da ta sama wannan mummanar labari na aurenta ta suma yafi sau goma ana watsa ma ta ruwa ta tashi, tun tana ganin abin kamar ƙarya har yamma ta yi wasu mata su uku suka zo wai tafiya da amarya. Sosai hankalinta ya ƙara ɗugunzuma wurin tashi a lokacin musamman da ta nema ‘yar uwanta Aunty sama ko ƙasa ta rasa haka nan tanaji tana gani waɗan nan mata suka tafi da ita wai zuwa Gidan Mijinta. Abu kamar wasa tun ana ɗaukar sa ba'a har ya fito fili cewar Safiyya ta tafi Duniya yawon ta zubar domin har da wanda yake cewa ma ya ganta a Lagos maganganu dai gasu nan kala kala babu irin wanda ba'a yi. Ita kuwa Umnia tsananin azabar da take kwasa wurin ƙazamin tsohon da a ka ɗaura ma ta aure da shi a matsayin Mijinta tun a Ranar ta ta farko a gidansa da kuma tashin hankalin da take ciki na rasa ‘yar uwanta ga kuma duka yau da gobe da azabtar wa da take kwasa wurin Sama'ila Tantus a cewarsa ita baiwarsa ce tun da kuɗi ya biya Uwani ta siyar masa da ita shi ba'a son ransa ma a ka ɗaura Aure ba. Tsawon shekara da shekaru Umnia take azabtuwa cikin wahalar wannan baƙin Aure da sai daga baya ta gane dalilin da ya sa Sama'ila Tantus ya aure ta wai domin ɗaukar fansa a kan mahaifin su shi ne ya aure ta yake Azabtar da ita tsawon shekaru kuma still har zuwa lokacin bata ga ‘yar uwanta ba zuwa lokacin kowa ma ya cire rai da Dawowar Aunty domin an ɗan kwashe shekaru masu ɗan dama. Zuwa lokacin tsananin azaba ya saka zuciyar Umnia ta ƙeƙashe babu tsoro ko fargaban kowa a tare da ita a lokacin tun bayan kwantawa ciwon da ya yi ajalinta da Uwani ta yi.

Akwai wata rana da ta kasance mai ɗumbin tarihi wurin Umnia Ranar da Sama'ila Tantus yazo yana dukanta da belt wai ya sakata wanki da guga ta ƙona masa kaya a lokacin a tsakar gida ne ita kuma ta yi amfani da wannan damar ta taɗiyo ƙafarsa ya faɗi nan take kansa da ya bugu da bango ya fashe jini ya fara tsatata kamar an buɗe famfo. Umnia ta yi matuƙar Girgiza lokacin da ta gane Sama'ila Tantus ya mutu ma'ana dai ta kashe sa bisa tsautsayi, sai dai ko kaɗan bata ɗa ga hankalinta ba domin kuwa a ganinta daidai ta yi domin mugayen ayyukan Sama'ila Tantus ya cancanci ya sama mutuwa ƙasƙantacciya sama da wacca ya yi. A lokacin koda ‘yan sanda suka kamata bayan binciken ainihin abin da ya faru na tsawon watanni uku ta zauna a Gidan gyaran hali kafin daga bisani wata mai kuɗi ta fitar da ita koda ta nema sanin wacece sai da kyar ta gane cewa Aunty ce ‘yar uwanta ta zama hakan bayan gwagwarmayar rayuwa da ta sha daga lokacin ne kuma Rayuwar Umnia ta canza gaba ɗaya bayan ɗan wani lokaci ta koma makaranta ta ci gaba da karatu bayan kammala diploma da ta yi ne da kuma makarantar bada hoto ta musamman da ta shiga ne ta sama aiki a DSS kuma ita ta nema hakan, nan ta fara aikinta cikin Nasara da kwarewa tsawon shekaru uku ke nan da fara aikin ta da DSS.

*_PRESENT DAY...*

*_Wannan shi ne labarin UMNIA, shin Mene ne labarin Safiyya (Aunty), Ga kuma Hamraz shima wani irin gwagwarmaya ya sha bayan rabuwar sa da su UMNIA?._*


*IRSHAD POV.*


Bai bar asibitin ba har sai da ya tabbatar da farfaɗo War Aunty sannan ya tafi domin sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa kuma kalaman Aunty da ta ce Yaranta su ne suka dawo kansa. Kannasa ya yi wani irin juyawa tunanin baya yana zuwa masa a ka tamkar a mafarki ko a ce wanda ya farfaɗo daga cuta haka fuskokinsu suke dawo masa a ƙwaƙwalwarsa duk tsawon waɗan nan shekarun ya manta da su bai tuna da su ba sai yanzu da kalaman Aunty suka yi sanadin. Duk da cewa bai san wasu Yaran take nufi ba amma zai bincika ya gani.
A matuƙar gigice ya ja motarsa ya bar asibitin gaba ɗaya kuma hankalinsa da tunanin sa ya koma kan su, su ba selfsame ɗin sa ko wani hali suke ciki a yanzun?. Ya gama yanke wa zuwa gobe tafiya Katsina ta zama Dole a garesa domin bincikar halin da selfsame ɗin sa suke ciki su ɗin amanarsa ne kuma rayuwarsa ji yake ya tsani kansa da har ya iya mantawa da su tsawon shekaru har huɗu fatan sa bai wuce suna lafiya ba kuma bayajin zai iya yafewa kansa muddun wani abun mummana ya samesu, da wannan tunanin ya koma gida kuma a Ranar ya fara shirya shiryen zuwa Katsina da zai yi gobe...


_Turƙashi.! Da wata a ƙasa fa, ko su waye waɗan nan selfsame haka da Irshad zai je Katsina nema?._



★★★


*LULU POV.*

*09: 25, Na dare.*

A karo na biyu ta kuma ɗa gowa tana duban Maiji dake zaune gefanta ta ɗan yi tagumi da alama ta yi nisa a Duniyar tunani.


Ajiyar zuciya ta sauke tana a je English Book dake hannunta tana karantawa sannan ta ɗan tafa hannayenta saman fuskar Maiji ɗin tana faɗin.


“Lafiya kuwa akwai matsala ne?.”


Ɗan firgita Maiji ta yi tana ɗan dafe kanta dake sarawa ta ce.


“Ba wani abu ba ne fa, kinsan yau na fara zuwa asibiti to a hanyata ta zuba a ka sama wani ɗan Hatsari Allah ya sa ina wurin na taimaka wa waɗan da suka ji rauni, ashe wasu sun ɗauki video kuma har ya kai ga shugaban mu kuma ya yaba da kwarewa ta, shi ne a ka zaɓe ni cikin waɗan da za su tafi Mining Company na wani shahararren mutum ne dai haka matsayin masu jinya.”


Tun da Maiji ta fara magana Lulu ta zuba ma ta ido tana dubanta bata ce ma ta komai ba har sai da ta kai aya, sannan Lulu ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin.



“Thank God na tayaki farin ciki ina ga ai a can ɗin zakufi samun experience ko?.”


Ɗan ya mutsa fuska Maiji ta yi tana faɗin. “Not really dai kam domin ni haka kawai naji gabana yana faɗi kuma ban san dalilin ba.”


Ta faɗa damuwa tana ɗan bayyana saman farar kyakyawar fuskarta da yanayin fatarta tafi kama da na shuwa Arab.


“Ki kwantar da hankalin ki in sha Allah babu komai sai Alkhairi kinji, and yaushe ne zaku fara zuwa Mining Company ɗin?.”

Lulu ta tambaya domin kawar ma ta da maganar ta na faɗuwar gaban da ta ce tanaji.

“Wai jibi suka ce.”


Maiji ta bata amsa tana Miƙewa tsaye tana hamma.

“Bari ki gani in gudu sai da safe Lulu sweet dreams.”


Maiji ta faɗa tana sumbatar goshin Lulun sannan ta ma ta sallama ta fita, yayin da Lulu ta bita ta da kallo har ta fita. Maimakon Lulu ta ci gaba da karanta littafin da take yi sai ta a je a gefe tare da Miƙewa tsaye ta ƙari sa gaban window na Bedroom ta ya ye curtain ɗin domin shaƙar fresh air ta kan yi hakan a duk lokacin da ta kasance ita ɗaya kuma daga hakan ne zuciyarta take samun damar tariyo ma ta mummanar rayuwarta ta baya mai cike da ƙalubale duk da batason hakan domin batason tuna dalilin mutuwar twin's Sister nata bisa son zuciya na wasu mutanen masu son kansu da yawa a Rayuwa da kuma neman Duniya domin ita ɗaya suka saka a gaba.




_
_To kamar dai yadda na faɗa muku ne akwai sarƙaƙiya sosai dole sai ana yawan Flash Back sannan za'a gane ainihin abin da ya faru a baya, ina fata kuna fahimta._
___






_(0708 521 2808.) 👈 Wannan lambar da nake bayarwa ga masu Buƙatar a yi musu Graphic Design ta sama matsala what'sapp sun rufe saboda hakan zaku iya samun mu ta wannan lambar a halin yanzu. (08081129487.)_

_____
*Kar a manta da danna sharing koda zuwa ga Group Biyar ne da kike ciki, sai kuma sharhi a kan abin da ya shige muku duhu, na gode Nkd's ce taku a har kullum. 😊🥳👑*

_MARUBUCIYAR...!_


1. SARAUNIYAR KYAU
2. ANEESERH (Innocent Girl.)
3. TSANTSAR SO
4. KIN CUCENI
5. RANAR BIYAN BUKATA. E.T.C. 😄



*_Naga Masoyan Aneeserh Innocent Girl book nawa suna da yawa kam 🤩 duk mai bukatar complete na Aneeserh ya yi min magana (08081129487)_*






*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

# Human Trafficking
# Terrorism
# Son Zuciya
# Cruelty And Revenge
# Needs Justice 🩸🔥💔




*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Ep-22*


*_FLASH BACK_*


*Orphanage Home, Katsina.*


Haka Rayuwar Samra da Samara ta ci gaba da gudana a gidan marayu tun bayan kaisu da mahaifiyarsu ta yi kuma ta tafi ta barsu bata sake waiwayarsu ba.

Rayuwa suke mai cike da kaɗaici su biyu sun ƙi yarda da kowa sun ƙi aminta da kowa. Sudai burin su kawai shi ne Mahaifiyarsu ta dawo ta ɗauke su daga Gidan su koma gidansu su ci gaba da Rayuwarsu abin su. Har kullum tunanin su bai wuce a kan dawowar Auntyn su ba tun suna saka rai da ƙirga kwanaki har abu ya yi nisa kwanakin suka wuce satikai suka biyo baya haka shekaru suka shuɗe. Auntyn su bata dawo gare su ba kuma har zuwa lokacin basu cire rai da dawowarta gare sun ba, kullum cikin saka ido suke da fatan ganin ta wata rana. Tun basa kula kowa dai har sauyin yanayi na yau da kullum ya sa suka ɗan fara sakewa kaɗan da sauran yaran dake Gidan marayun, sai dai basu sake jiki sosai ba kuma sun ci gaba da karatunsu a gidan domin akwai ɓangaren boko daban haka zalika na Arabi. Ta wannan ɓangaren dai sun mayar da hankali sosai domin basu manta da maganar Auntyn su ba na cewa ilimi shi ne Rayuwa.


★★★
****



Tsugunne take cikin lambun gefan wata doguwar kujera ta zama, duka fuskarta duƙunƙune cikin hijabin jikinta ta cuta ba'a hango fuskar nata, sosai take kuka irin mai cin rai ɗin nan da taɓa zuciya daga yadda sheshsheƙar kukan nata yake fita zata fahimci ba ƙaramar damuwa ne ke damunta ba, take ƙoƙarin gusar da ita ta hanyar yin kukan. Kukan ta take bil haƙi da gaskiya bata damu da ƙarar takun da a ke ba alamun ana tahowa wurin idan ma ta san a na yi ke nan.


A firgice ta ɗa go fuskarta sakamakon taɓa kafaɗunta da a ka yi, kuma ba tayi tsammani ba wannan dalilin ne yasa ta ɗa go a firgice tana watsa ma kyakyawan matashin Saurayin mai kama da Laraba da yake tsaye gabanta jajayen idanunta, laɓɓanta rawa suke yayin da ta fara ƙif-ƙifta idanu jikinta ya fara rawa da alamu na tsoron ganin sa ne, ta iya yiwuwa tsantsar kyansa shi ne ya ruɗata har bata san lokacin da ta buɗe Bakinta dake rawa ba cikin zazzaƙar Muryarta mai daɗin saurare ta kwala ihu mai matuƙar ƙarfi tana toshe kunnen ta da hannayenta tare da ci gaba da faɗin.


“Wayyo.! Taimako.!! A taimake ni aljani ne ya taɓe ni wayyo ni Samara Aunty ki taimake ni.!”


Idanunta rufe gam kuma jikinta na rawa take wannan sumbatun.


Da sauri matashin Kyakyawan saurayin dake tsayen yakai hannu ya toshe kunnen sa duka biyu yana rumtse ido domin zaƙin Muryarta da ya cika wurin dake barazanar lalata majiyar sautin sa.

A tare suka buɗe ido kamar almara. Kamar yadda ya zuba ma ta Frisco eye nasa yana kallon ta ba tare da ya ce komai ba, haka nan ita ma ta zuba masa nata cool eyes ɗin tana dubansa daga sama har ƙasa. A hankali ɗan ƙaramin bakinta ya motsa ba kuma tare da ta ce wani abu ba, sai kuma ta miƙe tsaye, ta fara takawa tana isa gare sa har sai da takai wurin da yake tsaye sannan ta tsaya tana dubansa, so take takai hannu ta taɓe sa domin ta tabbatar wa da kanta cewa mutum ne ko aljan, amma ta kasa, wannan dalilin ya sa ta tsaya tunanin abin yi. Tunawa ta yi ai an ce ƙafafun aljanu kofato ne ba irin ƙafar mutane ba, wannan tunanin da ta yi yasa da sauri ta kai dubanta zuwa ga ƙafafunsa. Sai dai rashin Sa'a bata iya gane komai ba, domin kuwa ƙafafun nasa suna rufe ne da Oxford Shoes coffee color, ɓata fuska ta yi domin ta rasa wani dabara zata kuma yi domin tantance mutum ne a gaban ta ko aljan.


Zuwa yanzu ya gane abin da take nufi wanann dalilin ya sa shi sakin ɗan Murmushi irin na gefen fuska da ya bayyana lutsatstsen dimple ɗin sa kuma daidai lokacin da Samara ta ɗa go da dubanta zuwa gare sa, Ai kuwa ta kuma ruɗewa ganin dimple ɗin, ta wangame baki domin ihu ya yi saurin toshe ma ta baki yana ƙara girman idanunsa a kan domin ba zai so wannan karon tsautsayi ya saka wannan zazzaƙar kaifaffar muryar nata ya kashe ma sa kunne ba.😅


Cizo ta ganna masa a yatsar sa dake saman bakin nata, ai kuwa da sauri ya janye hannunsa yana yarfewa ya zuba ma ta ido kuma har lokacin bai ce komai ba, domin ɗabi'ar sa ce a hakan rashin magana, dan kuwa ba zai taɓa damunsa ba don ya kwana bai furta komai ba, jinsa yake kamar JININ SARAUTA (BY Maryam Lumu) sai dai ana yawan masa uzuri idan a ka yi duba da abin da ya faru da shi da har ya yi silar kawo masa in'inar da ta saka ya rage 85% na magana da kowa dama kuma maganar can Asali bata damesa ba.



Dariya ta yi ganin yadda yake yarfe hannu da alama kaifafan haƙoranta sun yi masa lahani ma.


“Samara me kike anan, wanene wannan, ina ne kika shiga nake ta neman ki kizo mu tafi class idan ba haka ba kinsan wannan mugun teacher Lahab ɗin ba kyaleki zai ba Kum....”


Matashiyar yarinyar da ta shigo lambun tana maganar wa ‘yar uwan nata kuma idanunta a kan mutumin dake tsaye gaban Samara ɗin ya juya baya bata iya hango fuskarsa sannan bata dena faɗar abin da take faɗa ba, har sai da ta

Please Login or Register in order to submit comment