Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cika sha shidda ba amman har yazo ma a shekaru sha biyar"
Tafa��a tana lalubar fuskar sajeedah wadda idanunta sukai fam sabida kukan dataci ummah ce ta dogara ta ha��a mata ruwan ��umi takai mata bayi ta gyara jikinta da taimakon yadda umman ke gwada mata.
Wayyo ai sajeeda tafiyar �ban kaciya ta koma lokacin data sanya auduga ajikinta tana kuka tana wanke uniform ��inta, Bayan ta gama ta shanya taci abinci ta kwanta wanda ciwon mara yace salamu alaikum domin a ranar dai sajeedah taci wuya sosai dan seda aka siyo mata magani sannan ta��an samu bacci.
Washe gari innah tace ta zauna karta fita makaranta da kanta ta shirya bayan ta kammala suyan wainar ta ta)�arasa har makarantar ta tambayi ofishin mai makarantar bayan an mata iso ta shiga suka gaisa sannan ta fara bashi rahoto akan fashin sajeedah wanda ya rubuta sunan sajeedah sannan sukai sallamata ta koma bakin aikinta.
Koda ta koma gida sajeedah ta sami sauki amman datace mata gobe taje makaranta setace mata dan Allah ta bari se ranar monday sabida suna hadda a isilamiyya wadda zasuyi sauka kwanan nan haka innah tabar sajeedah agida batare data koma makarantar ba.
A satin islamiyya take fita tun safe se yamma ranar alhamis ta dawo da yamma gaf da magariba tana ta sauri taxo zata gifta ta bakin layinsu taji wasu matasa su biyu suna hira se ��ayan yace.
"Kai saddam gafa wani kaya nan yaxo wallahi waccan �bar ta ha��u"
�agowar da ��ayan zeyi seya sauke kansa a fuskar sajeedah se kawai ya kashe da dariya.
Tare da kallon abokin nasa.
"Hmm ai abokina kaine na wajan hu��u a cewa waccan yarinyar tana da kyau yes tana da kyau sedai bata da kyan asali domin mu har yau bamu san ubanta ba infact ma ana zargin shegiyace akan son abin duniyar kakarta ta tura uwarta karuwanci ta samo cikinta shiyasa muke zaune anan duk wanda ya biyota yace yana sonta muke tarar shi mu gaya mai gaskiya duk ��an mafita baze auri marar uba ba"!!!
Taji saukar maganar acikin dodon kunnenta.
*tashin hankali* !!!
6/2/22, 21:07 - Buhainat: *DAN GIRMAN ALLAH KARKI FITAR IDAN KIN GANSHI A WAJE DAN GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA NA KU�INE KI BIYA KI KARANTA DON ALLAH*


Littafin *��OYAYYAR &�AUNA* Na ku��ine akan farashin Naira #300 kacal, Idan kuma sp kike so ( ina tura maki ta private ) naira 1000 ne kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218


*30*

Tashin hankalin da sajeedah ta shiga yafi gaban kwatance,a mati)�ar ki��ime ta )�arasa gida kai tsaye zubewa tai ajikin ummah tana riskar kuka! daman innah bata nan taje kasuwar janguza siyo kayan miyar taushe wannan yasa gidan ya zama sauran ummah ka��ai se ita data shigo yanzu.
A gigice umma ke mata magana tana lalubarta, da hannunta domin jin inda take.
"Sajeedah lafiyarki maye ya sameki?"
Duk ta mata tambayar kusan a jere.
"Ummah mai yasa tun ina )�arama mutane ke cemin banda uba! yanzu harta kai ta kawo mazan anguwa na korarmin duk saurayin daya biyoni da karfar baka tani shegiya ce ummah ina mahaifina ina �ban uwanshi suke?"
Tafa��a tana kuka!
Shafo kanta ummanta tayi cikin taushin murya ha��i da lallashi tace.
"Sajeedah a kullum idan kin zomin da wannan tambayar nakan ce miki keba shegiya bace ke �bar sunnah ce kamar kowa sedai bazan nuna maki ��aya daga cikin dangin mahaifinki ba se zuwa lokacin dana ��ibama kaina inda raina Duk saurayin dake sonki toya zo wajena domin nice uwa! nice uba! agareki idan har ya yarda da hakan in bai yarda ba shikenan"
Tafa��a tana shafa kan ��iyar tata.
Babu yadda zatai da ummah domin uwace gareta amman ita kam tana da bu)�atar jin ina dangin mahaifinta suke kamar yadda yawanci take jin kewarsu acikin zuciyarta, Sedai babu damar musu ga umarnin ummanta.
Zubar da abin tai daga ranta tashiga sabgar gabanta.
Har innah ta dawo nan suka cigaba da abinda ke gabansu.
Washe gari ta kama juma'a sajeeda ta kafe setabi innah wajan tuyar waina tunda se litinin zata koma skull tun safe tayi wanka taci gayu ta ��ora farin hijab akan kayanta ita ta rike bokitin miya suka nufi bakin titi napep suka hau bayan sun sauka suka bawa mai napep ��in ku��inshi, Adai-dai jecton inda zasu tsallaka su shiga rumfar innah ta tuyar wainar wata farar mota ta tawo aguje seko Ta fallatsama sajeedah ruwan daya taru a )�asa, da sauri sajeedah take duban hijabinta kafin ta daddage ta zunduma ihu bayan ta dire bokitin a kasa tabi bayan motar tana dukan glass ��in bayan motar tana Allah ya isa.
Da sauri mai motar ya dena gudu ya rage gudun motar tare da tsaida motar kana ya fito har lokacin sajeeda tana faman zuba mai Allah ya isa.
Matashine baifi shekara ashirin da biyar ba dogo ba)�i mai kyau dashi.
Cikin tattausan lafazi yake ma sajeedah magana.
"Haba )�anwata kamar baki da ��a'a seki biyoni kina zagina bayan ba'a san raina na maki ba"
Ri)�e gu)�u sajeedah tayi tana watsa mai zafafan maganganu.
"Inda bara nake ai zagina zakai amman na riko abin sana'armu shine zaka watsamin ruwan kwata to kaje Allah ya isana"
Dafe kanshi yayi yana maijin yana sara mai baya son hayaniya bare tashin hankali a rayuwarshi miskiline na ajin )�arshe.
Tsira mata idanu yay yana kallonta baice mata komai ba har sanda innah ta karaso wajan.
"Sajeedah lafiya inata kira kin min banza?"
Tura baki tayi gaba tana mai cewa.
"Innah bashi bane ya watsamin ruwa gaya nan har ya �atamin hijabin makaranta"
Tafi innah tahauyi sannan tace.
"To sa'anki ne dazaki dinga mai rashin kunya? inda wanine kinsan da tuni ya wankeki da mari"
Tafa��a batare data goyi bayan sajeeda ba.
Tsugunnawa yayi har )�asa ya gaishe da innah sannan ya bata hakuri yana yi yana duba agogon dake hannunshi.
"Tashi ��an saurayi kai xan bawa hakuri sajeedah babu kunya"
Murmushi yay sannan ya zaro rafar 1k ya mikawa sajeedah "gashi ki sai omo"
Watsa mai kudin tai saman fuskarshi kana tace.
"Kai kudi ke gabanka bani ba mtsssss"
Taja tsuka tabar wajan.
Ai mai hali bai fasawa da sauri innah ta sunkuya tana kwashe kudin tana mita.
"Kai hakuri samari miye sunanka do Allah rabu da sajeedah bata da kunya"
Murmushi yayi kana yace.
"Babu komai ai yarinya ce"
Sannan ya kuma cewa.
"Sunana ALIYU ABBA �AN CANJI, idan babu damuwa baba ina san jikar nan taki zaki bani aurenta nazo?"
Yafa��a yana dariya.
Itama dariyar tai kana ta kuma rungume ku��inta tsam a kirjinta.
"Mai ze hana Aliko ina so mana kazo gida ku gana dan bazan mata auren dole ba"
Dariya yayi ha��i da )�arowa innah wasu rafan kudin nan ta gigice tahau lafto mai kwatance tafiya yay yana dariya itama ta juya.
Tofa tunda ta koma wajan sajeedah take mita har suka tashi.
Seda suka koma gida innah ke shaidawa ummah komai ita kam ummah batai magana ba aranta taiwa �barta fatan alkairi.
A ranar Aliyu yazo wajan sajeedah a soro suka zauna tun tana mai shuru har tazo tana dariya tana basa amsa.
Kwanci tashi soyayya mai )�arfi ta )�ullu tsakanin Aliyu da Sajeedah duk da irin sukar da ake kai mai inya fita amman bai ta�a juya mata baya ba ta �angaren karatunta yanzu tana jss2 zata shiga 3 shekara guda kenan suna soyayya da Aliyu tuni ya kashe innah da ku��i domin yama hanata fita suyar waina shiya ��auki nauyin cida shansu harma da ku��in makarantar sajeedah wanda tuni zance ya cika unguwa na jikar habiba ta samo mai kudi yana kashe masu ku��i.
Sajeedah ta shiga jss3 lokacin dasuke )�o)�arin shiga ss Aliyu yacewa innah ze aiko a tambayar aurenta.
Babu wata damuwa innah ta amsa mai da zancen sabida haka wajan mijin hansatu malam bala, mahaifan Aliyu sukaje bayan gaishe-gaishe akai maganar aure harma da saka ranar da zasu kawo ku��in aure wanda innah taje takanas har rano ta shaidawa �ban uwanta akan sesu zo nan su amshi ku��in auren sajeedah da Aliyu.
Waye Aliyu?
�ane wajan Alhaji abba ��an canji wanda iyayensu suka haifa su' biyu dagashi se )�anwarshi wadda batafi shekara biyar ba a wannan lokaci ya kammala karatunshi inda shima ya fa��a harkan canji irin na mahaifinshi,wanda yana tafiya nema akan hanyarshi ta zuwa kasuwar wafa suka hadu da sajeeda inda soyayya ta kullu atsakaninsu gidan mahaifanshi na nan gwauron dutse, lokacin dayaje ma iyayenshi da maganar aure sunyi farin ciki matika domun daman burinsu yay auren shi da wuri su sami jikoki tun wuri ga ��an nasu tilo namiji wannan yasa suka soma shirin aure cikin sauri.
Wannan kenan!
Ranar juma'a da yamma su baffa usman da wani )�ani awajan marigayi har��o suka sauka agidan innah inda tacika su da abin arzi)�i naci da sha zama sukai a tsakar gida suna cin abincin kafin su ��unguma zuwa gidan malam bala domin amsar ku��in auren sajeedah da Aliyu........
6/3/22, 11:39 - Buhainat: *DAN GIRMAN ALLAH KARKI FITAR IDAN KIN GANSHI A WAJE DAN GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA NA KU�INE KI BIYA KI KARANTA DON ALLAH*


Littafin *��OYAYYAR &�AUNA* Na ku��ine akan farashin Naira #300 kacal, Idan kuma sp kike so ( ina tura maki ta private ) naira 1000 ne kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218


*31*

Su baffa usman zama sukai suka baje suna cin abincinsu sosai innah na kwasar su da hira, cikin farin cikin dake ranta na samun mijin jika na kere sa'a datayi.
Babu abin da innah ke gaya ma su baffa usman se abin arzi)�i na romon da suke lasa wajan Aliyu, yadda yake ��awainiya dasu kamar mahaifansa.
Sosai baffa usman yaji da��i har yana ce mata.
"Kingani ko habiba ai zafin nema baya kawo samu, Lokacin da kika ��aga hankali akan sekin auri mai kudi baki samu ba kikazo kikaci buri kan �barki itama bata samu ba se akaron banza jikarki ta samu kinga lamarin Allah ko?"
��ata rai tayi tana ��an kallon gefe sa'annan tace.
"Do Allah baffa kabar tuna baya kana tunamin da marigayi ado bawan Allah"
Seta hau kuka! tana share hawayenta.
Baffa yace.
"Bara mu tashi mu)�arasa kar ba)�in suzo habiba bazamu biye taki kita mana kuka ba"
Yana )�o)�arin tashi sukaji bugun )�ofa tare da sallama.
Da sauri innah ta kira Sajeeda dake ��aki ita da umma bayan tazo tace mata ta le)�a waje ana sallama taga ko suwaye.
Hijab ta sanya kana ta fita.
Dattijan maza ne guda biyu ��aya farine tass mai far'a dan gashi nan yanata sakin murmushi se ��ayan ba)�i gajere marar sakin fuska sosai kamar ma ransa a �ace yake.
Tsugunnawa tai har )�asa tana gaishesu sannan tace.
"Ance naga ko su waye?"
Cikin ��aga murya bakin yace.
"Kije kicewa kakarki baban Aliyu ne yazo da kansa ba aike ba"
Da sauri ta ��ago gabanta na fa��uwa tana dubansa.
"Kalleni da kyau koma kece shegiyar yarinyar data asirce min yaro yake faman zuba muku ku��i batare daya san asalinki ba"!!!
Da sauri wannan farin mutumin yace.
"Haba Alhaji abba wannan ba kimarka bane inda nasan wannan abu zakai da ban rakoka ba"
Yafa��a cikin rashin jin da��i.
"Dakata Alhaji Habibu! kokai ma nasan bazaka bama ��anka wannan shegiyar...........!
"Datakata malam!!!
Ummah dake dogaro sandarta ta katse shi, wadda ta lalla�o ta biyo bayan �barta jin shurun yayi yawa.
"Kada ka kuskura ka )�ara cewa �bata shegiya domin duk munafukin dayama ce maka ita shegiya ce seya nemi ragon daze yanka mata tazama �bar sunnah na fa��i da babbar murya sajeedah �bace �bar halak kamar sauran �ba�ba sedai )�addara tasa na rabu da mahaifinta )�addarar dakai zakaje wajanta nima zanje wajanta wato mutuwa! nagaji da jifan da ake binmu dashi ni ba'a barni na huta ba itama datazo duniyar yanzu ba'a barta ta huta ba habahaba!!!
Tafa��a da )�arfi.
Wanda ya janyo hankalin su innah suka fito wajen suma.
Shima Alhaji mahaifin Aliyu ransa ne ya �aci na yadda ummah ke gaya mai maganganu nan da nan yahau mata cin zarafi ha��i da tijara wadda tajanyo idanun mutane kansu.
Sajeedah kuka! take gaba ��aya komai na rayuwa ya fitar mata akanta.
Basu tsinke da lamarin ba seda sukaga Aliyu ya janyo mota yazo shima cikin fushi yake nuna sajeeda da hannunshi.
"Fatimah kin cuceni mai yasa kika rufemin cewar baki da uba! duk maganganun da jama'a ke gayamin nake )�aryatawa sabida banji daga bakinki ba se jiya zuwa yau mukaji daga bakin da baze )�arya ba bakin mutumin da kakarki mai son abin duniya ta turamu wajansa mu nemi izinin aurenki ashe babu abin da kuka ha��a dashi mijin )�awarta ne shike gayan ke shegiy...........!
"ALIYU"!!!
Sajeedah ta mi)�e tsaye bayan ta kira sunanshi.
"Naji ni shegiya ce amman kamanta da ana ��auko �ba agidan marayu araina a aura kuma a zauna da ita? ka manta da ana auro karuwa a bariki a zauna da ita ka manta da ana tsintar �ba a ri)�e a aura batare da ansan asalinta ba? bare ni danake zaune da kakata da uwata cikin darajata ba ta zubar na fita ka ganni ba? tabbas Aliyu kaine shege! bani ba domin kai inda ��an halak ne da ayau ka nunan halaccin so baka gujeni ba! to Aliyu kaje dan kafasa aurena ai ba kai ��aya bane namiji kuma sha Allahu sena auri namijin dayafi ka kyau ku��i )�uruciya tare da ilimi da asali insha Allah yadda ka tozartani a bayyanan nasi seka nemoni a bainan nasi lokacin da tafiya tai maka nisa"
Tana fa��in haka taja hannun ummanta suka bar wajan.
Maganganu suka ��anyi dasu baffa usman sannan suka tafi nan kowa ya watse.
Babu da��i innah ta koma gida inda anan ta tarar da tashin hankalin dayafi gaban kwatance!
Ummah ce ta birkice mata tana ta kuka tana fa��in maganganu.
"Innah duk kece silar jefamu wannan hali ni gashi ban wuce aure ba amman silarki naki samun miji sabida son duniyarki da kwa��ayi gashinan jikarki tun da ranki itama taki samun mij........!
Tas! tas!!tass!!!
Baffa usman ya wanke ummah da mari yana huci yace
"Aisha kinci ubanki uwar taki kike gayawa haka maza bata hakuri dan ubanki to ba ita ta hana yarki samun miji ba rashin yi mata biyayyar da kikai ne yasaka �barki ta kasa samun miji"
ta inda ya shiga bata nan yake fita ba seda yay mata tas sannan ya rabu da ita.
Sannan ya juyo kan innah.
"Kekuma Habiba kinga ni ko son abin duniya da kwa��ayi ya kaiki halaka! bare da kika fifita fiye damu ya ha��a maki tarko! mijin kawarki da kika nuna a matsayin naki sabida yana birni karki kai surukanku kauye shiya soke auran jikarki habiba tabbas wannan in bai sakaki darasin duniya ba bazaki taba yin hankali ba"
Kuka innah take tana taga sharrin mutum kafin ta lalla�a su baffa da )�yar akan su kwana da safe sa tafi adaran ranar babu wanda ya rintsa agidan domin kwana sajeedah tai tana kuka ummah na kuka! babban tashin hankalin ummah a yanzu shine taga dawowar usman aboki Aminu baban sajeedah wanda taji labarin ya sami aiki acan indiya wanda take so yay mata jagora zuwa gombe domin ita a yanzu da bata da idanu tayaya zata iya zuwa, Tana son taje can kodan sajeedah ta wanke zargin dake ranta sedai kash usman har zuwa wannan lokacin babu shi a nigeria babu labarinshi yana can kasar tare da iyalinshi ahaka bacci ya sace ummah.
6/3/22, 11:39 - Buhainat: *DAN GIRMAN ALLAH KARKI FITAR IDAN KIN GANSHI A WAJE DAN GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA NA KU�INE KI BIYA KI KARANTA DON ALLAH*

Littafin *��OYAYYAR &�AUNA* Na ku��ine akan farashin Naira #300 kacal, Idan kuma sp kike so ( ina tura maki ta private ) naira 1000 ne kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218

}� }� }� }� }� }� }� }� }� }� }� }� }� *32*

Tunda ya kwanta bacci yake hango kyakykyawar fuskarta acikin idanunshi tana kuka! �barta na kuka! mahaifiyarta na kuka!
Tabbas wa��an nan bayin Allah sunyi mati)�ar bashi tausayi mai yasa mutane suke da hassada da bakin ciki, a yadda take furucinta ka��ai kasan an sakasu agaba ita da �barta an takura musu.
Bacci gagarar idanunshi yayi a wannan dare seya mi)�e ya shiga ban��aki ya ��auro alwala, ya tada sallah ta nafila ya jima yana mi)�awa Allah lamuranshi, Kafin ya tashi ya koma gado yaja abin rufa da asubahi da )�udirin abin da ya kwana ya tashi bayan sun fito daga masallaci, Bai koma gida cikin iyalanshi ba, kamar yadda ya saba, seya saka ��anshi ya goyashi a bayan babur kai tsaye kurawa suka nufa da wannan asubahi, Lokacin da suka sauka a bakin babban gida, Duk mazan dake )�ofar gidan mamaki sukai kafin su taso suna mai sannu da zuwa da far'arshi da komai yake gaisawa da mazan wa��anda yawanci )�anenshi ne da kuma �ba�bansu da �ba�ban yayansu, Bayan sun kammala ya dakatar da ��an nashi shiya shiga babban gidan �angaren farko ya shiga cikin babban falo.
Farin dattijo ne wanda ze kai shekaru Hamsin da biyar zaune yana shan shayi ba)�i ga carbi a hannun shi, Jin sallamar ��an uwanshi da farar asubahi yasa ya dakata dashan shayin kana ya aje kofin yana kallon )�anin nashi harya zauna kusa dashi.
"A,a Habibu lafiya dai? ko legos ��in za,a koma?"
Murmushi yayi kana yace.
"A,a yaya shu'aibu ba haka bane mudai soma gaisawa"
Sesuka gaisa da junansu cikin mutuntawa sannan yace masa.
"Yaya daman akwai maganar dake tafe dani.............wato jiya na raka abokina Alle abba! gidan surukansa.......tiryan-tiryan ya zayyane wa yayansa dukkan abin da yagani da komai harma da )�udirinsa wanda ya kwana dashi kana ya sunkuyar da kansa )�asa ya cigaba da cewa.
"Yaya wannan jahadin nake son ka shigemin gaba nayi a matsayinka na yaya kuma uba agaremu Idan hakan bai sa�a shari'a ba"
Murmushi Alhaji shu'aibu ya saka kana yace.
"Haba habibu wani irin sa�a shari'a ni ai farin ciki ma nayi daka nunan girmana inda wanine gaban kansa zeyi kai masha Allah, Allah ya ji)�an hajiya da malam Allah ya )�ara ha��a kammu amin"
Alhaji shu'aibu ya fa��a yana mai yalwata far'ar dake fuskarsa.
"Yanzu waye ya kawoka nan ��in?"
Cewar Alhaji shu'aibu.
Murmshi yayi kana yace.
"Yaya kaima kasan duk yaran nan babu wanda ze kawoni kamar wancan rigimamman Amadu,Shiya kawoni yana waje"
Dariya Alhaji shu'aibu yayi kana yace.
"Oh Amman baka da tsoro ni ai baxan yarda amadu ya kawoni ba yayi )�an)�anta koda yake girman jikin Amadu ai se ace ya girmewa anas"
Dariya sosai Alhaji habibu yayi tare da cewa.
"&�warai kuwa yaya Ai Amadu masha Allah, wato a yarana shika��ai zan sarrafa yabini son raina amman wallahi yaya sauran bazasu yiba yanzu zasu hau bani uziri, Damma kwanan nan shi Amadun ya)�i makaranta kullum sebin yaran layi suna shaye-shayen banza duk da ance shi baya sha amman )�anwarsa tace taga yana shan taba"
Salati Alhaji shu'aibu yahau yi yana tafa hannu.
"Yanxu Amadun da baifi shekara sha biyar ba ya soma bin yan shaye shaye to kai wani mataki ka ��auka?"
Murmushi Alhaji habibu yayi kana yace.
"Kasan yaya tunda na baro legos yau shekaru uku kenan komai fa baya tafiya kamar da kasan harkan canji daman hawa da sauka ce, Shagona na wafa kuma ba wani babban jari ciki daman da nufina na kwashesu muyi wafa, To shi Amadu ya)�i yace shi baze dogara da sana'ar mahaifi ba yafison ya nema da guminsa, To shine yake jan adaidaita sahun wani yaro anan bayanmu amman nikam tunda yanzu yana ss2 kasan yana da haza)�a duk yafi su anas aji a makaranta, yana candy xan kaishi umaru musa nan katsina"
yafa��a yana mai sada kanshi a )�asa.
"Amman habibu kayi ganganci tayaya yaro kamar amadu zaka bari yana jan adaidaita tun yanzu duk da girman jikinsa kana ganinsa kamar ya shekara ashirin amman rayuwar zaka duba ai"
Murmushin dake fuskarshi ya��an gushe cikin damuwa yace.
"Yaya baxaka gane ba mahaifiyar Amadu tana da wani irin hali yanzu idan na hanashi bala'i zamuyi da ita, kuma sannan tana da bu)�atar yayin domin yana taimaka mata sosai kasan matsalar gidan yanzu da Allah ya��an jarabcen ba kamar daba kaga shi muneer ya samu aiki anas ma yana fita wani shago anan makotanmu suma sauran duk suna da abinyi, To wallahi yaya daidai da )�wandala su' su anas ��in bazasu taimaki Amina da ita ba kaga tana da )�ananun �ba�ba agabanta amman wani bin inba Amadun ne ya nemo ya bata ba to wallahi seka ganta abin tausayi, bamai taimakonta agidan dagani se ��anta duk sauran suka samu yana gindin mahaifansu, Baxasu taimaketa ba sabida idon tsiya kaga fa yaya wani bin ana ganin tashin hankalin amina wallahi duk tafisu kyan hali, wannan yasa bazan hanashi ba domin dayaje yay sata gwara ya nema sukuma abokansa da suke shaye shayen tare muna musu addu'a Allah ya shiryasu amin"
Yakai maganar cikin jin takaicin rashin ha��in kan matansa.
"To maganarka haka take habibu domin kaine agidan amman ni kam nafi ganin laifin amina sabida shegen kishinta na tsiya ta)�i barin kowa ya zauna lafiya yanzu hakafa rabon data zo gidanan nan har an manta sabida kawai mun aura maka shafa'atu to yaya xa'ai da rabo, Saboda haka kaita addu'a Allah ya ha��a maka kan zuri'arka sannan ka tashi muje can ��in shi amadun ya koma gida se sabi'u ya kaimu a motarsa"
Tashi tsaye sukai Alhaji habibun yana cewa.
"To Amin yaya sukam mazan se son barka suna da son junansu musamman shi amadu uwarsa bata son yana shiga cikinsu wai acewarta basa kaunarshi amman babu ruwanshi haka yake binsu ita amina tata ce ta fito fili yaya amman da shafa da Hadiza suma ba baya ba"
Yafa��a yana mai fita daga falon.
Waje ya nufa wajan wannan farin matashin yaron wanda a kallo zaka kaishi kusan shekaru ashirin saboda girman halittar da Allah ya bashi amman a zahiri baifi shekaru goma sha biyar ba.
Farine sosai irin mai jan nan yana da dogon hanci mai ��an fa��i yana da manyan idanu bakinsa ba)�ine sabida busa haya)�i gashin kansa na fulani ne haka nan yana da cikar gira kallo guda zaka mai kasaka shi acikin jerin kyawawan mutane kyau bana wasa ba.
Yana ganin uban ya tawo ya sauko daga saman babur ��in tare da cewa.
"Dady mu tafi ne?"
Ko a tsayi ma yakusan kamo mahaifinshi domin shima uban yana da tsayi sosai sedai bai kai uban )�iba ba.
"A,a amadu tafi gida kai shirin makaranta zamu fita da yaya ne"
Shafa kanshi yayi ka��an yana murmushi.
"Dady wace makaranta kuma tab wallahi babur zan karbo na fita ban ha��awa oga balance ��in jiya ba"
Yafa��a batare dayay munafurci ba.
"To Amadu Allah ya kiyaye akula da manyan motoci yanzu makarantar bazaka je ba kenan?"
Yafa��a a tausashe sabida yadda yaga ��an nashi se ana binsa a hankali, duk ��an dakaga yana da ��an zafin kai ka��an baka mai fa��a da nasiha da ban baki kake mai magana sekaga yabi ka yadda kake so.
"Dady zanje ko da ankusan tashi ne sona ke na ha��awa hajiya ku��in gudumawar bikin )�anwarta yanzu haka nai rabi dady shiyasa ko gani bana yi sosai sabida baccin dana ��auka"
Yafa��a yana mai kokarin tada babur ��in dayake kai wanda nasa ne daya saya da kudin����������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������sa sabida makaranta.
"Amadu kai hakuri zuwa karshen wata ni zan bawa amina kudin kai kaje makaranta"
Dariya Ahmad yayi irin ta basawa kana yace.
"Dady tun ina karami kake ��awainiya damu dady wani irin kudine bamu kashe ba wani irin kayane bamu saba hajiya wani irin ku��ine bata ri)�e ba tai sana'a muna legos kamar me to yanzu kuma dan Allah ya jarabce ku semuyi kuka!to dady dan Allah kaji da )�annemu mukam kabarmu mu nema da zufarmu Allah ya taimake mu"
Yafa��a yana mai jan babur ��insa yabar wajan.
Alhaji shu'aibu ya shirya cikin manyan kaya sabi'u )�aninsu shiya ��auko mota yajasu tiryan tiryan dady ya kai �ban uwanshi har kofar gidan innah lokacin wajan shidan safiya.
Dan haka se Alhaji shu'aibu yacewa sabi'u ya buga masu gidan sedai me kafin ma sabi'u ya buga su baffa usman sun bu��e hannunsu rike da leda alamun tafiya zasuyi innah ta rakosu.
Da sauri dady ya karasa wajansu suka gaisa a mutunce sannan Alhaji shu'aibu yace inba damuwa suna son ganinsu.
Innah da sauri ta koma gida tai masu shinfi��a a soro.
Zama sukai aka gaggaisa sannan Alhaji shu'aibu ya soma bayani kamar haka.
"Ni sunana Alhaji shu'aibu se )�anina Alhaji babibu ��an canji, wanda jiya shiya rako abokinshi nan kofar gidan wajan wannan yarinya da akai babu da��i abin bai mana da��i ba sam, Sabida haka in babu damuwa muna so dan Allah abamu auren ita mahaifiyar yarinyar domin ajiya )�anina habibu ya ganta kuma yaji yana sonta

Please Login or Register in order to submit comment