Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shin wani kallo ze cigaba dayi mata daman haka kawai Ahmad da raini inaga yaga wannan lemu da idanunshi.
Shiko dariyarshi ya cigaba dayi wadda har sautinta seda ta fito fili.
"Zan fita ina son kimin tuwon shinkafa miyar kuka kafin na dawo dame dame za'a siyo zan aiko nura ya kawo ko salim?"
Taji saukar muryarshi acikin dodon kunnenta.
"Ai bani kace nayi maka ba, Inaji ai kana cewa ai maka a gidanku"
Tafa��a cikin rashin sakin fuska don yanzu kaf-kaf take dashi.
Nanata maganar yayi a ransa yanajin ta tsani mahaifiyarshi tunda gashi nan sunanta ma ta )�i fa��i wai ai maka a gidanku.
"Nan ma ai gidane malama idan zaki min kiyi in bazaki ba ki barshi kina ganin yadda muka rabu da hajiya nasan bazata yimin ba"
Yafa��i maganar da ��an fushi.
Mamakin yadda yake mata magana a gadarance ne ya kamata kamar wata sa'arshi ko matarshi.
"Kaje ka koyo yadda akema babba magana seka dawo nai maka"
Tafa��a a gajarce.
Murmushin mugunta ya saki.
Tare da��an matsota ka��an har )�afafunsu na ha��uwa.
Aikwa da sauri tajanye tata da tsananin tsoro ta yun)�ura zata tashi ya sanya hannunshi ya mayar da ita.
"To jarababbiya kullum burinki ki ribace ni don na ta�aki ki zagayo kina shan lemon tsami to zauna bani da lokacinki yanzu"
Takaicine ya kamata ta aje cup ��in a gefenta.
"Gaka nan babban jarababbe kullum burinka ka ta�a jikin daba naka ba malam ka wuce ka bani wuri bazan maka girkin ba ai ni ba baiwar u............"
"Sajeeda keda wa kike )�o)�arin zaginshi?"
Taji maganar ummah akanta wadda take fitowa daga ��aki tana tokara sandarta.
Zum�ura baki tai gaba tare da har��e hannunta a saman kirjinta tana harararshi.
Ganin ummah ta )�araso yasa ya��an matsa gabanta ka��an ya kama hannunta ya zaunar da ita cikin ladabi da biyayya yake gaisar da ita.
Fa��a��a far'arta tai tare da lalubar fuskarshi ta shafa bakinta tamkar gonar auduga.
"A,a Baban hajiya ne yau a wajan namu?"
Dayake sunan datake gaya mai kenan sabida sunan mahaifin hajiya gareshi.
Zube )�afafunshi yayi a )�asa cikin tsantsar tausayawa yace.
"Nine ummah dafatan kina lafiya?"
Cikin sakin fuska tace.
"Lafiya lau baba kwana biyu baka le)�owa mugaisa Lafiya dai ko?"
Murmushin dabai gushe a fuskarshi ba ya )�ara fa��a��awa yace.
"Kwana biyun nan ne ummah bana zama akwai sabon shagon dana ke son bu��ewa a hanyar zooroad wannan yasa bana zama sosai ina zuwa wajan masu aikin"
Yafa��a yana kallon sajeeda da wutsiyar idanunshi wadda ta ��ora cup ��in abakinta tana shan ruwan lemon tsamin.
"To Allah ya taimaka ��an albarka Allah yayi maka albarka"
Ya amsa da amin a )�asan ransa.
"Sajeedah keda wa kike fa��a ne ina tambayarki?"
Ummah ta fa��a cikin ��aga murya.
"Ummah nida wannan ��an rainin hankalinne wai tuwo zan mai sekace baiwarsa"
Tafa��a tana murgu��a mai baki tana fari da ido.
Murmushi ya saki yana ayyana abubuwa masu nauyi akanta.
Dogon salati ummah taja tare da lalubo sandarta wadda take doguwa batai )�asa a gwiwa wajan saita inda take jiyo maganar sajeeda ba, Aikwa ta ra��a mata ita a kanta.
"Dan ubanki Ahmad ��in ne zece ki masa abu kice baxaki mai ba, Koda kike ganin kin bashi shekara ��aya ai ba dubu kika bashi ba yaro ��an albarka mai sona kullum ta Allah seya zo wajena yaji damuwa ya ��auko ku��i ya bani wa kikaga yana min haka acikin gidan nan ehe?"
Tafa��a cikin fa��a.
Da sauri sajeeda ta mi)�e tana tura baki tai hanyar ��aki tana )�un)�uni.
"Ummah kiyi ha)�uri Fatimah har yanzu akwai )�uruciya akanta kinsan ita mace koda tai shekaru ��ari tofa namiji mai sheka hamsin yafita tunani babu komai karki )�ara dukanta don Allah indai akan tamin abincine tabarshi"
Yafa��a yana tashi tsaye.
"Dole tayi dan ubanta kai tafiyarka ai ba ita ta haifi kanta ba, Ai ba sajeedah ba nikaina inda inada idanu wallahi dani zanyi maka"
Tafa��a cikin sakin fuska.
Murmushi yay can )�asan ranshi.
"Ummah nagode se anjima"
Yafa��a yana juyawa ya fita.
Harya bar falon tana faman saka mai albarka.
Mita ummah ta cigaba dayi har sajeedah ta fito falon bayan ta idar da sallah.
Samun waje tai ta zauna yau bata da girkin gidan mama ce zata amsa.
Gobe kuma Anty ita da girki se jibi wanda zatai kwana uku da wuni guda tana yinshi wato girkin hajiya.
"Ummah yanzu idan uwarsa taga nai masa girki )�ilan ta kasheni wannan tasa na)�i amincewa amman kiyi ha)�uri zanyi masa"
Tafa��i hakan domin kwantar da hankalin ummah sabida bata son ummah tasan mai Ahmad yake mata.
"To amman ke yarinya ce? dazakina gaya mai dik maganar data zo bakinki, Kullum kika fita aiki yaron nan seya zo gaidani ya ��auki dubu biyar dubu goma ya bani yace na ri)�e Banda kuma halarcin dayay mana a baya shin mai Ahmad ze nema ya rasa na alfarma mu kasa yi masa?"
Ummah ta fa��a cikin fa��an da bata daina ba har yanzu.
"Kiyi ha)�uri ummah kuskure nayi"
Tafa��a cikin biyayya sajeeda badai biyayyar mahaifiya ba.
"To la'asar nayi ki ��ora mai a )�aramin kicin ki ha��a mai komai kafin ya dawo"
Tafa��a tana kishingi��a da kujera.
"To ummah"
Itama sajeedar ta fa��i ranta na mata suya.
Baccine ya ��ebe ta wanda bata farka ba se wajan )�arfe ukun yamma, Alwala tayo tazo ta tashi ummah, shinfi��a abin sallah tayi )�arfe uku da rabi ta tayar da sallar la'asar tana idarwa ta fa��a kicin indomie ta dafo masu guda Uku manya ta zubo a faranti ta kawo falon sannan ta koma ta ��auko pure water a frij ta dawo ummah na idarwa suka fara ci sabida yau bata son fita �angaren matan gidan bare taje ta ��ebo masu abincin.
Bayan sun kammala ta ��auke farantin takai kicin ta ��auraye.
Bata bar kicin ��in ba seda ta kammala ha��a ruwan miyar sannan ta fito tai zaman azkar tana idarwa ta koma ta ka��a miyar kukan sannan ta ��ora sanwar tuwo.
&�arfe biyar ta kammala tuwon da miyar ta zuba a sabon fulas suma ta kwashe musu nasu.����������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������
Wanka tayo ta tube kayan jikinta ta shirya cikin marun les doguwar riga bubu tana kammala shirin wayarta tahau ringing!
Ta nufi inda take ta ��auka.
Yalla�ai
Tagani rubuce.
Murmushi ta sauke tare da ��aga wayar cikin girmamawa suka gaisa da ogan wajan aikin nata yana mata yaya jiki tare da cewa in bazata damu ba gasunan tare da Rabi'a zasu zo dubata murmushi ta sauke tana mai godiya tare da katse wayar tana yaba karamcin mutumin wanda yake kamar uba agaresu sabida babbane sosai shiyasa kowa yake girmama shi acikin asibitin.
Bayan ta kammala,wayar )�arasa shirinta tayi cikin nutsuwa ta fito falo take sanar da ummah.
Murmushi ummah tayi tana fatan Allah ya kawosu lafiya.
Zamanta da kamar mintuna goma suka )�araso waya yay mata akan suna bakin gate.
Gyarawa tai tare da ��aukar mayafinta ta fita bakin gate suka gaisa da mai gadi ta bu��e )�ofa ta fita Fitowa sukai shida Rabi'a ta taresu da farin ciki �war hira suka ta�a sukai mata yaya jiki sannan yace zasu koma.
Babu yadda batai dasu ba akan suzo suje su gaisa da ummah amman Rabi'a ta)�i tunda daman shi Yalla�ai baze shiga ba,
Sam bataji da��in hakan ba don haka seta kama murfin motar tare da le)�awa ciki tana ma rabi'a mita kafin ta ��ago tana hararrata.
Yalla�ai na )�o)�arin jan motarshi subar wajan Motar Ahmad ta shigo layin a guje wanda yayi kan motar yalla�ai ganga ganga wanda da sauri yalla�ai ya saita sitiyarin sa cikin tashin hankali yayi gefe.
Itama da sauri tai baya aguje tare da bu��e )�aramar )�ofa ta shige hankalinta a mati)�ar tashe sabida yadda ta hango mutuwa, Sabida yadda ya saita kan motarshi tabbas bada ban ta kauce ba wallahi seya bi takanta.........
*TOFA*

Littafin *��OYAYYAR &�AUNA* Na ku��ine akan farashin Naira #300 kacal, Idan kuma sp kike so ( ina tura maki ta private ) naira 1000 ne kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218
5/27/22, 07:27 - Buhainat: *_��OYAYYAR &�AUNA_*��.\
{ _Eternity Love_ }

NA
*AUTAR MANYA*


HOME OF QUALITIES WRT ASS....

14


Gabanta na tsananin fa��uwa jikinta yana rawa take jefa )�afafunta a hanyar sashen su, Gaba ��aya hankalinta yayi cikin gida sam taji ma sallamar da suke dasu Rabi'a ta fita aranta sabida ita a duniya tana da tsananin tsoron lafiyarta wannan ganganci da Ahmad yaso yayi akanta ba )�aramin tsurar da ita yayi ba cikinta har juyawa yake wata irin guduwa ce keson tsirga mata sabida tsananin tsoron dake cinta.

Tana kai hannu zata bu��e )�ofar sashensu taji an fisgo mayafinta cikin masifa da bala'i yake tsareta da manyan idanunshi wa��anda suka jirkice suka sauya kala zuwa jajir suna aman wutar bala'i hannunshi shikanshi rawa ike sabida �acin rai baisan maganar ta fito fili ba sedai tsintar muryarshi yayi yana tuhumar ta kamar haka.
"Keda ubanwa kike tsaye dan rashin tarbiya da ��a'a zaki kawo gardi )�ofar gidan mutane?"
Tsaki taja mai )�arfi itama cikin masifa ta buge hannunshi tare dajan dogon tsaki.
"Kaci darajar wani abu da nima sena zageka mai ya ruwanka da tsaiwata"
Tafa��a tana )�o)�arin bu��e )�ofar.
Ya )�ara buge hannunta da )�arfi ya fincikota ya wurgata gefe.
"Nace ki gayamin da ubanwa kike tsaye dan kutumar ubansa kowani shegene?"!!!
Ya buga mata tsawar daya sa ta dur)�ushe tai )�asa tare da aza hannunta a kunnenta ta toshe sabida hargowarsa.
"Dan baki da wayo baki da tunani shine zaki kawo )�ato gidan nan in banda rashin tarbiya da rashin ��a'a miye zaki aje mana gardi a )�ofar gidan ubanmu, Dama abinda kike kenan idan kin fita aikin, To wallahi kin kusa daina fita shegen aikin private wanda albashin naki baifi dubu talatin ba har kike gadara dasu"

Yafa��a tamkar ze kawo mata duka.
Itama cikin masifa ta mi)�e tare da ri)�e )�ugunta.
"Dakata bafa tsoronka nakeji ba waishin mai ya ruwan ka dani ne in gadarar ka gidan uba nima ina dashi kuma wallahi ina gab da barin gidan nan kaji da kyau maganar aikina kuma Alhamdulillahi ko dubu goma ake bani ni ban raina ba domin tafimin naje nai maula konai ro)�o, Haka nan albashina yana rufamin asiri tunda ban ta�a zuwa nace ka bani kwabonka ba idan kuma kaika biyamin ku��in makarantar ka kaini seka cireni daga cikinta, aikin banza aikin wofi zance kuma yanzu na fara kazama kububuwa )�arewar fushi"

Tana gaya mai haka ta kuma yun)�ura zata shige ciki.

Da wani zafin nama ya janyota ya matseta da jikin bangon wajen hannunshi yasa ya mur��e bakinta ya sha)�o mata wuyanta.
Seda yaga ta fara kakarin mutuwa tana tari sannan ya sassauta ri)�on nata ha��i da tanka��ata gefe.
Wuyanta ta ri)�e tana numfashin azaba.
Akanta ya tsaya yana ka��a )�afa kamar wani soja.
"Tabbas inna )�ara ganinki da wani ��a namiji zan maki illah na, nakasa ki yadda ko kallo bazaki ishi kowani namiji ba,wallahi senai maki abin da zaki ji )�yamar kanki"
Yafa��a tare da wucewa fuwww.
Cikin fushi yabar mata wajan.

Zubewa tai a wajan tana kuka wiwi.
To mai Ahmad yake nufi da ita?
Kullum yasata agaba yana mata gorin ta)�i aure amman kuma tayaya ze jefeta ta da wa��annan mugayen lafuzan wanda tasan tabbas ze iya aikatawa sabida yadda yake da tattaurar zuciya.
Tajima a wajan tana kukan takaici kafin ta mi)�e ta shiga ciki.
�aki ta wuce ta tarar da ummah muryarta sha)�e take shaidawa ummah su rabi'a sun wuce sunce sauri suke.
"Sajeedah yaya naji Muryarki kamar kinyi kuka?"
Ummah ta jefa mata tambayar.
Hannunta nakan handle ��in )�ofar bayi tace.
"Mura ke damuna"
Tana fa��in hakan taja kofar ta shige bayin.
Alwala ta ��auro ta magrib.
Sannan ta fito gaban madubi ta tsaya ta dubi wuyanta duk shatin hannunshi wajan yayi jawur abinka da farar fata.
Hawayene masu zafi suka zubo mata ta share tare da daukar hijabi ta fita falo.
Tana fita ana kawo nepa fanka ta kunna ha��i da jona wayarta a chaging sannan ta shinfi��a sallaya ta soma gabatar da sallar magarib jin anata kira a masallatai.
Ta jima tana addu'a musamman akan Allah yayi mata tsari da Ahmad domin ita yanzu tsoro yake bata a iya lokacin sabida tsabar tashin hankali har rama tayi idanunta sunka ciko suka kumbura tamkar mai ciwon idanu.
Bata mi)�e ba seda tayi sallan isha'i sannan ta ninke abin sallar tare da komawa ��aki ta sauya kaya zuwa riga da wando na cotten masu laushi milk colour ta mutstsika humra a jikinta, Hula ta ��ora a saman kaya ha��i da ��ora hijab kicin ta fita tare da zubowa ummah tuwon datayi tare da ruwan pure water ita kam batajin zata iya kai komai bakinta.
Bacci ma zatayi sabida gobe tana son fita da wuri.
Ta dire plate ��in abincin gaban ummah tare da ruwan tana )�o)�arin ta mi)�e ummah tace.
"Sajeeda takwas tayi?"
"A,a ummah bakwai da arba'in"
Ta bata amsa tana )�o)�arin kwanciya saman kujera.
"To lafiya Baban hajiya bai zo ya ��auki tuwonsa ba �auki ki kai masa can wajan nasu kinga ba lallai ya zata kinyi ba"
Gabanta ne ya fa��i jikinta yahau rawa sabida ita yanzu ambatar Ahmad ka��ai akai tana tsintar fa��uwar gabane sabida tsananin tsoronsa datake ji a yanzu ya zame mata ��an hakin daka raina.
"Sajidah ba magana nake maki ba"
Cewar ummah

Tura baki tayi gaba tare da mi)�ewa ta gyara hijab ��inta ha��i da shiga kicin ��in ta ��auko fulasan guda biyun duk a hannayenta.
Takalmi ta zira a )�afafunta tare da nufar )�ofa ta bu��e ta fita.
Tajima a bakin sashensu sabida ��akinsa shine a farko duk hasken farin )�wai ya game wajan tana ta son taga wani a mazan gidan ya gifta ta bashi ya mi)�a mai tana kuma tsoron munafurcinsu kar aje a gayawa hajiya tasan ta shiga uku!
Ganin tana cin lokacinta yasa tai shahadar nufar bakin )�ofar jikinta dik yayi sanyi.
Hannu tasa zata )�wan)�wasa mai amamakinta setaji )�ofar a bu��e.
Turawa tayi cikin nutsuwa tayi sallama a hankali tare da kutsa kai ��akin.
Hasken farin )�wai ne ya haske ��akin ga sanyin Ac da )�amshin turare mai sanyi.
Kai tsaye gaban ��an )�aramin teburin cin abincinsa takai fulasan ta aje hamdala tayi ga Allah tana jin da��in rashin ganinsa da batayi ba.

Sedai me juyawar da zatayi taji kamar nishi a bayanta da sauri takai dubanta inda takejin nishin.

Kwance tagansa sam�al a saman gado yayi rufda ciki jikinshi babu riga se farin wando dogo dake jikinshi.
Hannunshi dafe da kirjinshi yana janyo numfashinsa da )�yar.

Daga tsayen da take ta fahimci baya jin da��i kamar yana fama da ciwon )�irji ko )�arancin fitar numfashi.

Duk yadda takejin haushinsa batajin zata iya tsallake shi yana cikin wannan hali musamman yadda taji ummanta na nuna yadda yake kula da ita tabbas duk wanda yake girmama mahaifanka yake sonsu baka da kamarshi.
Azuciyarta ta ��auki al)�awarin ba ita ba shi amman zuciyarta a yanzu dataga halin da ike ciki ta kasa daurewa.
Jin numfashin nasa na )�ara sama yasa ta )�arasa gaban gadon da sauri har tana cin tuntu�e.

"Me ya same ka? me ya same ka? me ya same ka?"
Ta nanata sau uku!!!
Jin bai bata amsa ba yasa ta zauna a gefen gadon a matsayinta na nursing yasa ta tausasa lafuzanta gareshi.
"Ka daure ka tashi sena duba ka naga maike damunka idan yaso na baka magani"
Yana jinta sarai amman zuciyarshi bata )�aunar kallonta duk da tsananin son ganinta da )�wayar idanunshi keson yi,Yanajin dama ya mutu ya huta da irin zafin da zuciyarsa ke mai wadda take barazanar tayar mai da ciwon sa dayay shekara da shekaru bai tashi ba. wato Ciwon zuciya!
Ganin time naja yasa takai hannunta gadon bayansa saman farar fatarsa ta saka hannu ta janyoshi.
Dayake )�arfin ba ��aya ba yasa ta soma kici kicin yadda zatai ta juyo dashi ya kalleta se faman dambe take da numfashinta itama.
Da )�yar ta mirginoshi gabanta wanda kansa bai dire a ko'ina ba se a saman cinyarta.
&�ura mata jajayen idanunshi yayi wa��anda har yanzu basu surka ba yana kallonta dasu batare daya tanka mata ba.
"Sannu kadaina nishin bara na ��auko maka magani, Badai ciwon ka keson tashi ba kaine Ahmad kana wasa da magani"
Dayake kowa yasan yana da matsalar ciwon zuciya tun rasuwar mahaifinsu ya samu lalurar.

Nishin dai ya cigaba dayi wanda ya bata tabbacin numfashinsa is very low, dole se an masa dubara ya samu dai dai to.
"Amman please kadaina ��orama kanka damuwa sabida baka da cikakkiyar lafiya inma maganar hajiya ce ta ��azu kai addu'a"
&�ureta yayi da idanu yana nanata maganarta mai cike da rainin wayo wato bata masan meye matsalar shi ba.
Sunkuyo da kanta tayi dai-dai saitin hancinsa numfashinsu ya ha��u waje ��aya )�amshin humrarta ya bugi hancinsa lumshe idanu yayi yana mamakinta.
Bakinta ta bu��e ta ��ora akan bakinsa batai wasa ba ta fara hura mai iskar cikin bakinta zuwa cikin bakinsa ( tofa )
Tsintar kanshi yayi da jin da��in hakan ya ��ora hannunshi a saman kanta yana shafawa seda ta tabbatar da numfashinsa yayi dai dai.
Sannan ta zare bakinta a nasa tare da ture kanshi tana )�o)�arin tashi tabar wajan.
Ri)�o hannunta yayi tare da lumshe mata idanu ya��an tura bakinsa gaba kamar yadda yake ma hajiya in shagwa�arsa ta, tashi.
Janye hannunta tayi tare da girgiza mai kai tabar mai ��akin tana tafe tana mamakin abinda tayi.
Ahmad rigima Ahmad shagwa�a Ahmad daru!! caiiiii!
Tana isa sashensu ta iske kira daga hajiya gabanta na fa��uwa tabi bayan rukayya duk zatonta wani yaga gilmawarta a �angaren su Ahmad.
Da addu'a ta )�arasa sashen.

Zubewa tayi a gaban hajiya tana gaisheta bata amsa ba se maganar data soma yi mata.

"Gobe kizo da wuri zamu shiga kicin zaki mana abinci akwai babban ba)�on dazezo waje na,yaron )�awata hajiya Aisha, ya dawo daga london zamu ha��a mai abinci mai kyau ki tabbatar bakwai kin halarci kicin"

Idan bata manta ba hajiya Aisha kamar matar data ta�a zuwa wajan hajiya kwanakin baya mace mai tausasan kalamai.
"Hajiya yau banje aiki ba gobe xan fita morning duty da wuri"
Tafa��a kanta a sunkuye.
"Uban morning dutyn nace ubansa shi dutyn! har kina da dutyn dayafi ki dafa ki ��ora to dan uwarki bazaki je ba na soke na goben dole kixo ki mana girki inba haka ba sena sa�a maki"
Tafa��a tare da mi)�ewa tabar falon.
Dariya su zuby suka saka suna daga saman kujera suna chart.
Takaici yasa ta mi)�e ta fita daga part ��in harta koma part ��insu bata da walwala.
Ummah ce ta tsareta da tambayar yaya sukai da hajiyar bayani tayi mata ranta a cunkushe.
Kana ta mi)�e ta nufi gado ta kwanta da tunani kala kala acikin zuciyarta..........

Littafin *��OYAYYAR &�AUNA* Na ku��ine akan farashin Naira #300 kacal, Idan kuma sp kike so ( ina tura maki ta private ) naira 1000 ne kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218
5/27/22, 07:27 - Buhainat: *_��OYAYYAR &�AUNA_*��.\
}� }�}� {}� _Eternity Love_}� }}�}�
}� }� }� }� }�}�
}� }� }� }� }� }�}� NA
*AUTAR MANYA*

_Writter Of_
*Auren Bare*
*Zuma a baki*
*Ba)�ar fata*
*�an majalissa*
*Rabon wani*
*Koba so*
*H a s k e*
*Da izzata*
*E.t.c........*

}� }� }� }� }� }� }� }� }� }� }� }� 15

Koda asubahi da )�yar ta mi)�e daga saman gado duk jikinta tsami yake mata na gajiya, Bayi ta fa��a ta ��auro alwala tazo ta fara yin raka'atul fijir sannan ta soma gabatar da sallah ta jima tana kaiwa Allah kukanta acikin sujjadarta ta )�arshe kafin ta ��ago tai sallamata azkar ta karanto ta shafe ajikinta sannan ta ninke abin sallar ta fita falo wajan ummah dake zaune itama saman sallaya tana lazumi gaishe da ita tayi sannan ta mi)�e, Ta koma ��aki gyaran gado tayi ta share ��akin ta goge shi tass sannan ta fito falo nan ma ta gyara aranta ta )�udiri niyyar babu inda zataje koda zata kasheta.
Bakwai dai dai ta kammala komanta hatta wanka ta shirya kanta cikin white uniform riga da wando seta ��ora ��an hijabi a saman kayan gaban madubi ta )�arasa ta dubi kanta ba )�aramin kyau kayan suka yi mata ba turare ta fesa sannan ta ��auki black shoe ta saka tare da ��aukar jakarta ta fita.
Koda yaushe tana )�o)�arin ��ora after dress akan uniform ��inta amman yau rashin wanki yasa bata ��ora ba haka ta fita falo tana zuba )�amshi.
"Ummah zan tafi nasan yau kina azumin alhamis shiyasa ban ha��a maki break fast ba sena dawo insha Allah da wuri zan dawo sabida na ha��a maki abin da zaki bu��a baki"
Tafa��a tana mai kama hanyar fita.
"Sajeedah Zonan"!
Taji saukar muryar ummah a cikin dodon kunnenta.
Dawowa tayi da baya ta zauna a gabanta.
"Ummah gani"
Tana yi tana duba ba)�in rolex na mata dake ��aure bisa tsintsiyar hannunta.
"Ba hajiya Amina tace kije da wuri kuyi girkin ba)�o ba?"
Ummah ta jefa mata tambayar.
"Eh ummah ta gayamin amman gaskiya banajin zuwa sabida kinga asibitin mu private ne jiya banje ba sannan yau ma ace banje ba duk,da yalla�ai ya sani amman ai kamanci kamata"
Tafa��a tana )�wa�e fuska zatayi kuka!
Ajiyar zuciya ummah ta saki tana maijin tausayin ��iyarta'ta a )�asan zuciyarta kuma tabbas! maganganunta suna bisa layin gaskiya.
"Jeki Allah ya tsare hanya amman ki daure ki dawo da wuri seki le)�a ki taimaka masu"
Murmushi ta sauke tana mai jin da��in yadda ummah ta fahimceta cikin sau)�i kafin tace.
"Nagode ummah na sena dawo"
Tafa��a tare da kama hanyar fita daga falon.
Tana tafe tana kare bayanta da hannunta sabida yadda take da )�irar baya yasa take )�o)�arin �oye surarta, Harta )�arasa harabar gidan babu kowa sabida safiya ce don haka ta kama hanyar gate tana tafe tana sauri ganin takwas ta kusa.
Gaisawa sukai da maigadi ta tura kofar ta fice.

Ahmad dake fitowa daga cikin masallacin dake kallon gidan su yanzu shiya dakata a )�ofar masallacin yana kallon sajeedah tana bu��e )�ofa zata fita.
Dama wannan shine al'adar Ahmad yawanci idan baze fita da wuri ba yana )�o)�arin yaga idan yayi sallar asubahi bai koma bacci ba zamansa yake a masallaci har gari yayi haske sannan ya fito daga bisani yaje yay wanka ya fita filin motsa jiki dake bayan layinsu.
To yauma baze fita da wuri ba sabida kwana biyu baya zuwa shago komai yana wajan Mj abokinsa wanda shima a shagon Ahmad ��in yake ��inki.
Shi abinda yasa baya fita yana zuwa wajan ginin sabbin shagunan sa daze )�ara bu��ewa anan titin zooroad, sannan idan ya gama da nan yayo gida wajan ginin gidansa da ake )�arasa mai anan kusa da gidansu inda duk maxan gidansu anan mahaifinsu ya basu filaye kafin ya rasu.

&�amshin turaren tane ya sanar masa da )�arasowarta gabanshi, Da sauri ta kawar da kanta daga kallonshi sabida kunya guda biyu data tarar mata ta farko shan lemun tsami dayaga tana yi ta biyu kuma Abinda tai masa jiya da daddare shima ya tsaya mata acikin ranta.
Da sauri take tafiya har tana ha��awa da gudu-gudu wanda ya bawa dukkan ilahirin jikinta damar ka��awa kamar da gayya musamman mazaunanta wa��anda bata sani ba har shatin pant ��inta ana hangowa.
Rintse idanunshi yayi yana binta da kallo gaba ��aya hankalinshi ya tashi idanunshi sun koma red colour jijiyar kanshi ta mi)�e tana harbawa ransa idan yayi dubu ya �aci,tsananin kishinta ya addabi zuciyarsa wanda bai san yana takawa da )�arfi yana binta a baya ba.
Sam yakasa magana sakamakon )�una da suyar da zuciyarsa take mai wanda ya bawa ma)�ogoranshi damar bushewa yay )�amas.
Binta yake a baya harta kai babban titin gadon )�aya.
Cikin hukuncin Allah yana gab da ze cimmata ta sami mai napep da sauri ta haye tana cemai "tal'udu Sameerah clinic muje malam".Ta fa��a da sauri tare da gyara zamanta.
Seda taga sun hau kwalta sannan taja numfashi tana hango shi ta glass yana kaiwa da komowa alamun shima abun hawan yake nema.
Har takai bakin gate na asibitin hankalinta bai kwanta ba Fargaba ce fal zuciyarta na wannan hatsabibin yaron karya biyota domin yanzu Ahmad lamarinsa ya fara firgitata.
Ku��in ta mi)�awa mai napep ta sauka ta shiga ciki.
A reception ward suka ha��u da rabi'a zata shiga office dan haka da sakin fuska suka gaisa kana suka shige office domin fara gudanar da ayyukan dake gabansu.

Iska ya kaima naushi.
"Kin raina min hankali kin mayar dani mahaukaci tabbas yau zakiga hauka"
Yafa��a a fili yana taune )�asan la��ansa.
Da )�afa ya )�arasa har babban titin gadon )�aya.
A wannan titin saman ya sami napep kai tsaye asibitin ya bita domin ai ba, ba)�onsa bane dole ta dawo gida wallahi mati)�ar yana raye bazata fita da wannan shigar ba...........

Littafin *��OYAYYAR &�AUNA* Na ku��ine akan farashin Naira #300 kacal, Idan kuma sp kike so ( ina tura maki ta private ) naira 1000 ne kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218
5/30/22, 07:46 - Buhainat: *_��OYAYYAR &�AUNA_*��.\
{ _Eternity Love_ }

Please Login or Register in order to submit comment