Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba komai ba, ni Allah kadai
nake tsoron na sabawa ba mutum ba, zan je kuma zaka
ji sakamako." Har ya fita Hashim ya ce, "To yaushe
zamu je wajen Fadin?" Tsaki Abubakar yayi sannan ya yi
gaba.
Lamido ya tarbe shi cikin fara'a, ya ce, "Ubana ka iya
zabe, domin ko da ni ka bari to da wuya na zaba maka
irin wannan Babban kamu, lallai kun dace." Abubakar ya
sunkuyar da kai cikin daure fuska ya ce, "Ni fa ba nine
na ce ina son Fadi ba." Ya ce, "Duk wanda ya hada ku
yayi maka gata." Abubakar ya ce, "Ni wadda na zaba
daban, bana son Fadi." Ya ce, "To kila ka gaji
takwaranka Mahaifina kenan, tarihi ya nuna mana duk
cikin zuri'ar nan shine mutun daya taba auren mata 2
lokaci daya. Fada min wadda ka zaba ita ma yau akai
mintinta, rana daya duk a sa su a lalle." Abubakar ya yi
shiru, Lamido ya ce, "Duba, taso ka matso nan, ka fada
min wadda kake so." Abubakar ya matso, ya dubi
Lamido, "Wata yarinya ce a Kano, sunanta Hafsatu, bata
daya daga cikin zuri'armu....." Wani wawan mari Lamido
ya sakar masa da bayan hannu, ya mike tsaye cikin fada
mai tsanani yana cewa, "Tir da kai, ba zaka surka mana
Zuri'a ba, tunda muka taso zumunci iyayenmu suke yi,
don haka muma ba zamu daina ba har bayanmu, don
kana takama da boko, bokon banzanka, na yi tunanin
shine yasa kake zagaye-zagaye, kana juyamu kamar
waina (masa), to kaje da Iyayenka zan yi, don ina
girmamaka saboda sunan Ubana, zan ajiye uban a gefe in
kamata inci mutuncinka, baka wuce duka ba a gurina,
FITA!!!!!
Abubakar ya tashi ya fita.
Kafin wani lokaci ya kira dukkan manyan 'ya'yanshi ta
waya ya fada musu yana nemansu gobe da safe.
Abban Abubakar yana jin kiran ya sha jinin jikinshi kan
batun Hamma ne, domin Dada ta fada masa komai
game da abin da Abubakar ya ce.
Ummi ta shigo dakin yana ta sintirin kai kawo, ta ce,
"Hamma!!!" Ya dubeta ta ce, "Ka ja surutu cikin dangi,
ko a Makaranta surutunka 'yan uwa suke yi, wai ka
canja hali yanzu baka da biyayya, ni kam ka yarda da
Fadin mana."
Abubakar ya kama hannun Ummi ya rike kam, "Tun
farko ina rokon Allah ya bani macen da nake so,
zuciyata ta san da Fadima, amma ta kama son Hafsa
ranar da na fara ganinta, nasan kema zaki so ta
Ummi." Ummi ta ce, "Hamma ina son duk abinda kaima
kake so, sai dai bana son matsalar dangi, zaka yi kallon
halin da su Dada zasu shiga, tunda kace Lamido yana
nemansu." Ya ce, "Ki taya ni addu'a, so baya barin
mutum ya ji tsoro, ni da kaina na fadawa Lamido batun
Hafsa, jikina yana bani zan yi nasara, kullum cikin
mafarkin Hafsa nake." Ummi ta ce, "Allah ya amsa."
Lamido ya mike yana kai kawo a tsakanin 'ya'yansa
wadanda suke zaune akan kafet. Dukkansu manyan
mutane ne masu fada aji, domin wannan yana wane
wannan ne a kudi. Ya dubi Mahaifin Abubakar ya ce,
"Ibrahim dauki wayarka ka kira min danka Abubakar."
Nan take Abba ya aikata haka, shima Abubakar nan
take ya bar komai ya nufi gidan Lamido. Abubakar
gabansa ya fadi ganin daya yiwa Iyayanshi kamar masu
neman gafara. Dakin yayi tsit sai karar agogo, jiki a
sanyaye shima ya zube tare da sunkuyar da kai, sai dai
duk da haka bai ji a zuciyarshi cewa zai canja daga
batun son Hafsa ba.
Lamido ya ce, "Abubakar!!!" Cikin zafin rai ya ambaci
sunan. Abubakar ya dago da kai ya dube shi, Lamido
ya nuna su ya ce, "Su waye wadannan?" Abubakar ya
kalle su ya ce, "Iyayena ne." Ya ce, "Da kyau." Ya ce,
"To ina son ka fada musu abinda ka fada min jiya."
Abubakar ya sake dubansu gabanshi na faduwa,
musamman da suka hada ido da Baffa Magaji, Lamido
ya ce, "Ka fada musu nace." Abubakar ya kasa
magana. Ya ce, "OHO!!! ni ka raina kenan da ka zo ka
same ni kafada min saboda ba nine na haifeka ba?"
Baffa Magaji ya ce, "Ka yi magana mana, wane ne
sa'anka a nan?" Abubakar ya ce, "Dama kan batun
yarinyar da nake so ne, wadda ba 'yar cikin zuri'armu
ba." Dukkansu suka hada baki gurin tambayarshi, "Me
ka ce?" Illa Babanshi da ya sunkuyar da kai cikin
matsanancin takaici. Baffa Magaji ya ce, "Kai ko
Shaidanin yaro ne, zaka kawo mana sabon al'amari
cikin zuri'a." Lamido ya daga ma Baffa Magaji hannu,
sannan ya ce, "Ban taraku kwanakin baya ba na gaya
muku cewar kar wani daga cikin 'ya'yayenku ya kawo
mana wani sabon al'amari a cikin zuri'armu ba?" Duk
suka ce hakane. Ya ce, "To lokacin ina zargin Abubakar
zai aikata haka, gashi zatona ya zama gaskiya. Don
haka yanzu kai Ibrahim tunda ka kasa tankwasa danka
ba ka iya bashi tarbiyya ba, ina son ta bakin ka kafin
kuji ta bakina." Abba ya nisa ya ce, "Lamido Allah ya
huci zuciyarka, na jima ina fama da Abubakar akan
wannan matsalar, sam ya ki bin umurnina, don haka ina
son 'yan uwa da suke zaune ku zama shaida, daga yau
na cire shi daga cikin 'ya'yana. Ina son Lamido ya cire
shi daga cikin zuri'armu don girman Allah.
Baffa Sa'adu ya ce, "Ina rokon alfarma gurin Lamido,
da ya ba Abubakar dama muji uzurinsa kafin a yanke
masa hukunci." Lamido ya ce, "Gashi ga ku." Baffa
Sa'adu mai rike da sarauta a yanzun wato Mahaifin
Hashim ya dubi Abubakar ya ce, "Dana fada mana
dalilinka na son ka saki layin da ka same mu a kai?"
Cikin karfin hali ya ce, "Baffa duk ciki ban samu mace
mai irin halayen da kamannin da nake so ba." Abba ya
ce, "Ka ji ko? In ba rainin wayo ba ace duk zuri'armu
masu kyau da ilmi da tarbiyya amma ace ya rasa matar
aure? Sai ya je yayo mana rore-rore?" Baffa Magaji ya
ce, "Muna jin shi ai, ya fada mana irin matar da yake
so muji dame yake takama." Abubakar ya ce da su
Baffa, "Bana son macen da an kalleta za'a san
kyakykyawa ce, nafi son baka kuma zuri'armu kusan
duk kyawawa ne farare, game da batun halaye kuma,
nafi son mace da bata cika wayewa ba, sai wadda bata
cika buri ba, mai ilmi duka 2, mai tarbiyya da hankali da
natsuwa, sannan kuma 'yar talakawa wadda za taji
magana ta, ta girmama Iyayena da duk wani nawa, mai
tsoron Allah a duk inda take, mai hangen na kasa da ita
ba na sama da ita ba, wadda bata da rawar kai. Baffa
kada ku yi zaton na raina tarbiyyar 'yan matan
zuri'armu, ko ba za'a samu mai irin wannan hali a
cikinsu ba, a'a za'a samu matsalar daya ce, ina son na
auri wadda nake so kuma take so na, ba wacce take
sona ni kuma bana sonta ba, Manzon Rahama ya hana
auren dole, don yana da illoli, bana son a cikin
zuri'armu akwai dayawa wadanda zaman hakuri da
biyayya kawai suke yi, alhali babu biyayya ga abokin
zamansu, hatta dan sabawa mahalicci."
Baffa Magaji ya taso ya ce, "Wato auren zumuncin ne
sabawa Mahalicci? To sarkin iya magana fada mana
inda aka ce ya haramta?" Abubakar ya gyara zama,
"Aure bautar Ubangiji ne, a duk lokacin da aka hada
Ma'aurata dan dole ba so da kauna, to ba zasu yi
wannan bautar ba yadda Ubangiji ya ce, maimakon lada
sai kaga zunubi ya samu. Mu dauki misali da gidan
Yaya Saleh, duk family ba wanda bai san tashin
hankalin da suke ciki kullum ba, banda kuma sauran
dangi da ba'a sani ba." Baffa Magaji ya ce, "Lallai
Abubakar, boko ya sa ka fitsare idanunka, kana rigima
damu saboda aurenka." Abba ya ce, "Duk wannan
zantukan naka basu isa su zama hujja ba, tunda ba
littafin da yai hani ga auren zumunci."
Lamido ya ce, "Ikon Allah!!! Ashe tun ina da rai zan
samu wani a zuri'armu da zaya kalubatanceni akan
al'adarmu? Dole ne na dauki mataki, in ko ba haka ba in
na mutu zumuncinmu rushewa zai yi." Abubakar ya ce,
"Ku yafe ni, ba zan zama sanadiyyar rushe zumuncinmu
ba, haske na zo mana da shi cikin zuri'a, ku kwatanta
dani zaku gane nufina nan gaba. Ma'ana ku barni na
auri bare." Baffa Sa'idu ya ce, "Abubakar mene ne
dalilinka na cewa ba zaka auri mace mai kyau ba?
Alhalin shine burin duk wani namiji." Ya kalli Abba, "Da
ban san yin wannan batun ba, amma yanzu ya zama
dole na fada, dalilai 2 ne suka sa nace ba zan auri
mace dan kyau ba. Na 1 Yaya Mansur in baku manta
ba lokacin da aka ce ya nemi Waslia bai ki ba, ya ce ko
ba komai ai tana da kyau, da suka yi hadari fuskarta ta
lalace, har yau ba wanda bai san irin wulakancin da
yake mata ba. Abu na 2, lokaci mai tsawo daya gabata.
(Abba ka yafe min abinda zan fada, ina dan yaro
lokacin kun dan samu hargitsi da Dada, na ji kace mata
abu 2 ne suka sa kake zaune da ita, na farko biyayya
ga Lamido, na 2 dan kyanta da take da shi. Ta yiwu ka
manta, kayi min afuwa ban so na fada ba) A lokacin in
zaka tuna ina karami amma raina yayi matukar baci
kwarai, da muka je Makaranta nake fadawa Hashim sai
ya ce Ai shi jiya ya ji Dadarsu tana fadawa Abbansu
zaman hakuri kawai take yi da Abbansu, don ita ba shi
take so ba, daga lokacin na kudurce a raina bazan taba
aure ba, sai wadda nake so take sona. Ina son iyayena
ku taimake ni, ku duba hujjojina, in kunki ni zan hakura
in yi biyayya amma har abada ba zanyi farin ciki ba.
Duk jikinsu yayi sanyi, kuma sun tabbata kowannensu
yanada shigen wanan matsalar ko shi bai son matar ko
ita bata son shi, amma wanda suka hada kansu su
suna zaune lfy. Baffa sa‘adu yace, ina rokon lamido
yayi mashi izini yatafi, mukuma munyi shawara. Lamido
yace, ya iya tafiya. Abubakar ya mike cike da kwarin
guiwa ya fita. yasan adu‘a bata faduwa, don tashi yake
tun 2 dare ko 3 yana fadawa Allah matsalar shi.
Lamido ya dubesu daya-bayan-daya, kuna nufin kun
amince da batun sa? Baffa jume yace, a a sai yanda
kace. Baffa sa‘adu yace, da zai yuwu hujjojinsa sun isa
a duba lamarin, koda a gaban kotu ne. Amma in
zancena ya bata ran lamodo aimun afuwa.
Lamido yace ban gamsu ba har yanzun, biyayya muke
bukata kuma kuje kuci gaba da shirin biki duk suka
watse, kowa zuciya cike da nazari.
Da dare ya sake zuwa gidan Baffa sa'adu don ya lura
shi mai saukin kaine, kuma zai iya taimaka masa har
yaga ya ci nasaram ya ce Baba na zo ne naji ko kun
gamsu da bayanin bayan tafiyata? Baffa ya ce, Lamido
bazai taba amincewa ba, ni kaina na cutu da wannan
hadin da ake yi tsahon lokaci, sai da na sake Aure
sannan na sami nutsuwa.
Dalilin musgunawar da mai dakina take min duk dan
ranta baya son auren mu. Aure na da Bilki ita ma 'yar
dangi ce amma ni na ganta na ce ina sonta, ta yarda.
Daga kanta ne na gane aure kina so ina so shine aure,
in mace tana sonka tana kaunarka da ka sami matsala
zata fara tausayinka, zata yi komai don ta faranta
ranka.
Amma in mace bata kaunarka, Abubakar akwai matsala
babba. Ni yanzun shawara daya zan baka, ka gwada.
Kaje ka sami Limamin Masallacin Juma'a kasan aminin
Lamido ne ko?" Abubakar ya ce eh, ya ce to kaje ka
same shi kayi masa bayani da neman tainakonsa, kila a
dace. Kasan mu 'ya'yansa ne bamu da wani karfin
tankwara shi, ga rikicin tsufa. Muna son mu lallaba shi
ne har mu rabu lafiya.
Abubakar ya ce za shi.
Sai da kafa ta dauke sannan ya shiga gida. Don yana
tsoron haduwar shi da mahaifinshi. Yana maida kofa
ana turowa, sai da gaban shi ya fadi, zaton shi Dada
ce, amma ai yaga Ummi ranta a bace. Ya matsa ta
shiga, ya dubi agogo sha biyu ta gota, ya ce Ummi kina
menene baki bacci ba?
Ta zauna "Hamma ka janye auren kan nan mana, Dada
ta yini kuka, hawayenta ba sauki bane a wajenka." Ta
zamo ta durkusa, "ka dubi Allah kayi hakuri ka yarda
cewa haka Allah ya so ganin zuri'armu.
Ya kama ta, "Tashi Ummi Dada da Abba zasu fahimce
ni da zarar komai ya daidaita, kije ki kwanta, fata na
daya ki taya ni fada ma Allah shine kadai mai maganin
matsalata. Baffa Sa'adu ya bani dama ta karshe, idan
har na gwada bata yi ba, na dauki alkawarin cewa na
hakura."
Ta ce "zanci gaba da yi maka addu'a," Ta fita.
daga sallah asubahi bai dawo ba saboda tsoron haduwa
da mahaifansa, gidan Hashim ya karya duk da ruwan
tea ne ya sha. Yayi wa hashim bayani, hashim yace,
sannu namiji. Kayi kokari, zan rakaka gurin liman.
Bayan la‘asar suka sami liman agida, sun gaisheshi
sannan suka gabatar da kansu, yayi murna da jin
jikokin amininshi ne, daga nan suka kora mashi jawabin
komai. Liman yace, to zan ganshi in Allah yaso zamu
tautauna batun, in kuma ya sausauta ra‘ayinsa to akan
nada kyau, don nasha yunkurin in fada mashi wanan
al‘adar tayi tsuri, musanman in yana bani lbr matsalar
gidan yayansa ko wasu daga jikoki wadanda basa
zaune lfy. Amma nakan fasa in na tuna yanda ya dauki
lamarin. To yanzu tunda dama tasamu zanyi kokari in
nusar dashi. Sukayi godiya sannan suka tafi. Duk
aranarce dai liman yayi tattaki zuwa gurin lamido, sunyi
murna da ganin juna, duk da cewa ko yaushe suna
haduwa. Sun gaisa sannan liman ya soma da cewa,
aminina gurinka nazo da batu mai matukar muhinmanci,
duk dacewa batun nawa ba zaiyi maka dadi ba. Amma
inaso kakali lamarin ta fiska 2, addini da kuma zamani.
Ni da kai dukanmu musulmai ne, muna koyi ne da
manzon tsira (s a w) addini ya amince muzabawa
yayanmu maza na kwarai amma bai yarda muyi musu
auran dole ba. Idan muka dubi fiskar zamani zamuga
cewa, mubar yayanmu suyi auren so da kauna, zaifi
bamu kwanciyar hankali. Lamido yace, oho! Abubakar
ya kawo maka karata kenan? Liman yace a a yazone
yanemi da in rokyaka ka amince, yayi aure da wada
yake so, wai shin ma wane dalili yasa ku rike wanan
al‘adar sai kace bauta?
Lamido ya ce iyaye da kakaninmu suna gudun hada iri
da wani ne saboda kada mu gauraya da mugun iri.
Liman yayi dariya sannan ya ce, da kai dani da bature
da balarabe da igbo da hausa da duk wani yare daga
mutum daya muke shine Annabi Adamu Alaihissalan.
Sannan Manzon Rahma ya fada mana Musulmi 'yan
uwan Musulmi ne.
Lamido ya ce, amma nasha ji daga bakin ka kana cewa
mai yanke zumunci ba zaya shiga Aljanna ba, wata
rana kace ba mai shiga Aljanna sai mai sada Zumunta.
Liman ya ce to ai ba ana nufin ka kamo wannan ka ce
sai sunyi aure ne zumunta ba.
Abinda ake nufi shine Ziyara, kwana biyu ka dade baka
ga dan uwanka ba, shirya kaje ku gaisa kuyi zumunci,
wannan shine sada zumunta. Yanke zumunta kuwa
shine kace wane baya zuwa, don haka nima na gaji da
binshi bazan je ba, kowa ya zauna a inda yake. Shine
yanke zumunta, don haka ka sassauta ra'ayinka ka tafi
dashi daidai da zamani.
Sannan daidai da turbar addinin Musulunci, cewa aka yi
in zaku yi aure ku nema wa 'ya'yanku Uwa ta gari.
Sannan ana auren mace saboda abubuwa guda hudu,
asalinta, kyawunta, kudinta da Addininta, Manzo SAW
ya ce na hore ku da ma'abociayar Addini, don haka
shawara anan sai ku duba, suwaye iyayenta? Kuma
wanne irin hali gareta? In mai Addini ce shike nan.
Ku hakure ku cebakomai saikuga ci gaba, ku cire 'yar
wani dangin kusa ta cikin naku shine karuwa, shine
zumunci dangin ku sun zama 'yan uwa da danginta,
kuma ko bayan ranta zaku yi ta zumunci da danginta.
Liman ya dinga bashi misalai tare da Hadisai zuwa
Ayoyi, har jiki Lamido yayi sanyi, ya ce to zai gana da
'ya'yanshi, in yaso za a bincika aji asallinta. Amma fa
sai dai in ya yarda ya hada mata biyu, domin baza a
fasa Fadi ba.
Liman ya ce, "Wannan ba laifi ba ne." Lamido ya kuma
tara 'ya'yansa ya gaya musu cewa, sakamakon zuwan
da Liman ya yi yayi masa bayanai da dama akan
wannan lamari, dan haka ya nada Baffa sa'adu da su
binciko masa 'yar wane ne? Sannan ya ce da Abba in
yaje gida ya turo masa Abubakar.
Ko da Abba ya dawo gida bai samu Abubakar ba,
sannan duk wayoyinsa a kashe suke, ya kira Hashim
yake gaya masa in ya ga Abubakar ya fada masa
Lamido yana neman sa. Tare suka je gurin Lamido ya
ce, "Hakika kana da sa'a, zan amince da auren in naji
cewa Iyayenta masu mutunci ne, itama 'yar mutunci
ce. Sannan kuma in ka yarda ka hadasu 2 ka auri Fadi
itama. Sannan ita yarinyar tunda bakuwa ce anan gida
na zaka kawota mu zauna da ita muga irin nata
dabi'un." Har zai ce wani abu sai Hashim ya zungure
shi, sannan ya ce ya amince. Lamido ya ce, "Shi bashi
da baki ne sai kai?" Sannan Abubakar ya ce, "Na
amince." Lamido ya ce, "To sai kuje, in mun shawarta
lokacin da za'a je zaka ji."Farin ciki gurin Abubakar
baya misaltuwa, ya isa gidansu da karfin gwiwa. Dada
tana zaune suna hirarsu da Rukayya, ya zube gabanta
yana neman gafararta, sun ji komai daga bakin Abba,
sai dai ta ce, "Shawara daya zan baka, kada ka yi rawar
jiki akan bakuwar da zaka kawo cikinmu, ka nuna
kamar kafi son 'yar uwarka a kanta, ka tashi mun yafe
maka. Ka samu Abba ka bashi hakuri, sannan ka samu
Hashim ku je gurin Fadi." Ya ce, "To." Ummi cikin
murna ta ce, "Ni kam in zaka Kano zan bika muje na ga
Hafsat." Ya ce, "To, Amma sai na fara zuwa in na dawo
sai muje tare."shi da Hashim suka nufi gidan Goggo
Jami, sun jero ita da Fadi zasu fita, hannun Fadi rike
da makullin mota, sai ga Abubakar. Suka tsaya Goggo
da fara'a ta ce su shiga. Fadi ta musu sannu da zuwa,
suka gaisa sannan Goggo ta koma ciki tasa a kawo
musu abin sha duk da cewa da safe ne. Fadi ta gaishe
su, Hashim ne ya ce, "To Fadima, kin san dai dalilin
zuwanmu tunda magana ta yi nisa, yanzun ma yana kan
hanyar tafiya ne muka biyo. In ya dawo zamu zo zuwa
na musamman." Ta ce, "OH, zashi gurin KISHIYATA
ko? In kaje ka gaidata." Ta mike, "Nima zan je office
ne." Suka mike suma, Abubakar bai yi magana ba,
Hashim ne ma ya mata sallama. Suna hanya inda
Hashim zaya kai shi filin jirgi don zuwa Kano. Ya ce,
"Kuna ta fadin Fadi nada mutunci, dubi irin tarbar da
tayi mana." Hashim ya ce, "Kishi ne, taga kowa a
family ita daya ake aure, amma ita su 2, dole ta damu."
Abubakar ya ce, ....




zaharaddeen Shomar
what's app 08168575100





Sanadin Boko 2-6
Posted by ANaM Dorayi on 11:25 PM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
"Ummi fa dole ta tsani auren Fadi, saboda ita bata da
kirki, da ace ina da yanda zan yi to ba zan auri Fadin
ba." Hashim ya ce, "Na kula ai da zaka yiwa Lamido
musu ne, shiya sa nayi saurin amsawa." Haka suka yita
hira har ya kaishi filin jirgi, yau dai da farin ciki ya nufi
Kano, kuma baya jin zai samu matsala da Hafsat.
Tunda bawan Allah nan ya tafi na kasa sukuni, ga
rigimar Shadad yana Aunty Uncle fa? Tun ina cijewa
har ta ni da kiran layin wayarsa, amma abin takaici ana
fada min yana kashe.
Daga bisani nayiwa kaina fada na watsar da lamarinsa.
Shadad ya murmure ya koma makaranta nima na koma
bakin aiki na. Na yi mamakin Manaja da bai ce min
kala ba, su Ishak ma sai mamaki suke yi, na kuma ci
gaba da zuwa makarantata.
Tun mun horu da shan garin rogo, yanzun ma shi na
jika ma a matsayin abincin dare. Na shimfida mana
tabarma a tsakar gidan kasancewar lokacin zafi ne ga
Kano akwai zafi. Muna cikin sha naji bugun gida, na
tashi naje na tambaya wanene?
Muryar da ban tsammace ta a lokacin ba ce. Ya ce ni
ne Sadeek, jiki yana bari na bude, ta re da haska
wayata, na ce "Sannu da zuwa, shigo." Ya shigo Shadad
har yana faduwa garin gudu yana fadin "Uncle." Uncle
ya daga shi sama, na kakkabe masa tabarma ya
zauna.nakawo masa ruwa, nazauna ina cewa ina yini?
Yace lfy, ya jikin shadad? Nace ya sami sauki. Don ya
latsani yaji ko na damu dashi yace, shine tun da natafi
ko flashig nace ai bakamin sallama ba,kuma wayar taka
ai akashe take. Yayi murmushi, yau naga canji anty.
Kina ta min fara‘a yau ba daure fuska ba harara, why?
Nace ina sa ran zan sami lbr mutumin kirki a gurinka,
wanda ya taimakeni tsawon lokaci da ya wuce,
mutumin da ya fara gina karatuna, yace meyasa kike
tsamanin samun lbr sa gurina? Nace, kun dibi kama,
sannan kayi mun batun da yayi min a lokacin baya,
wato na buga kudi, yace, fada mun yanda kukayi dashi,
na kalmashe kafa. Na zaiyana mushi yanda mukayi da
shi, yayi dariya. Banyi mamaki ba lokacin da yace, wai
hafsat me na kara ne kika kasa ganeni. Alhalin ni kuwa
tun lokacin da muka daukeki zuwa wajen buki rahama
da sagir na ganeki, duk da da yarinyace kwarai kuma
siririya, in kina yar gala-gala takar yar siririyar kafar ta
karye. Nace dama kaine? Sunanka abubakar sadeek?
Nce wallahi ban ganeka ba, idanunka dai in nakala sai
inga kamar na taba ganinka, kai gaskiya fa tunda muka
hadu kake taimako na, na gode Allah ya saka maka da
mafificin Alkairi. Sannan ina so ka yafemun rashin
kunya da rainin da nayi ta maka bisa rashin sani. Yace,
nifa bakiyi min komai ba, asalima burgeni kikayi, ya kali
kofin gari bance ki daina shan gari ba? Nace shi muke
dashi, yace ina indomie da na sai muku? Ace ba ajiya
ka bani ba? In zan kwana ban ci ba ba zan taba abin
wani ba, yace naku ne fa, banaso muyi jayaya yasa
nace maki nawa ne.
shadad yace uncle bakace ka daina guduwa ka barni
ba? Yace, tafiyar gaugawa ce ta sameni. Ya dube ni
yace wannan zuwan na musan man dan ke, duk da
zuwan da na dun gayi abaya suma dan kene, ki shirya
gobe zamu tauna muhimmin zantuka zan shigo, nace
to. Ya mike ki dafa ma shadad indomie, zakaci ko?
Shadad yace eh, yace to ni zan tafi kada kayi rigima,
zan zo da safe in kaika school. Yace, to uncle, suka
rakashi bakin kofa sannan suka rufe gidan suka dawo.
Tun da na kwanta bayan nayi shafa‘i da wuturi na kasa
bacci. Tunanina wacce irin magana zamuyi? Nasani ba
zaya wuce zai yi mun batun bayan rabuwa ba, domin
nasan zaya iya cewa zai mai dani gida. Niko anawa
ganin lokacin komawata gida baiyi ba, duk da ina ceke
da son kannena, da yaya umar, harma da shi babanmu.
Inna kuwa ita nafi son gani, ina so kafin na hadu da ita
sai na zama wani abu a SANADIN BOKO. Zan wanke
laifina zanyi abun da na kasa a baya, a fili nace
banyiwa inna adalci ba, Allah kada ka dauki raina sai
ka hadani da ita na roke ta gafara. Kuka ya kwace min,
da dakina zaiyi magana da zaice yasani lokacin kuka na
kenan.ringin din wayata ne ya ka tseni, na dauka ina
kalon numbobin, nayi mamakin yanda na hadace
numbobin shi aranar da na fara ganin shi. Nayi salama
muryarsa kasa-kasa bani son ya fahimci nayi kuka, ya
amsa kin soma baci ko? Nace a a yanzunan na gama
shafa‘i da wutiri, yace shadad fa? Nace yayi bacci shi
tuni.
duk mukayi shiru har saida na duba naga wayar na
kunne, nace kana jina? Yace ina jin ki, muryarki nake
son ji ki min hira. Nace wace irin hira? Yace ko wace,
ina jinki. Me kakeso mu tautana gobe? Yace wannan
sai gani gaki, nace to Allah ya kaimu, yace amin.
Yauwa, ummi tace in gaisheki, bansam me yasa naji
faduwar gaba ba, nace wacece haka? Yace kanwata,
itace autarmu. Nace to ina amsawa. Ya akayi ta sanni?
Yace, duk dangina sun sanki, labarina ka basu? Yace,
eh, to me kace masu? Yace, zan fada maki shi gobe.
Nace, to wai meyasa ka damu da ni tun farkon ganina
ina yariya kake ta taimako na? Yace kila Allah yayi nine
kawai don in taimakonki, kila watarana kayi min gori,
shiyasa bana karbar taimakon maza, ko kasa in saka
maka da wani abu wanda bani da izini a kansa. Yace,
me kike nufi? Yaci gaba, kada ki damu kanki, ni bakince
rance nake baki ba, zaki biya ni, nace dame zan
biyaka? Naci gaba da cewa, kai baka cikin wadanda
zasu cuceni, kai na daukeka yayana ciki 1. Yace a a
kada ki dora min dutsin da zai shiga tsakanin halas da
halas, nace kamar yaya? Yace sai dai nazo gobe, yace
kiyi bacci dani a ranki zakiyi mafarki innazo kifada min,
goog night. Ya kashe wayar. Nayi shuru ina so in tono
abubuwan da mika tau tauna, amma na kasa, illa
kalmarshi ta karshe da yace kada nashiga tsakanin
halas da halas, dan kawai nace shi yaya nane na
daukeshi uwa daya uba daya? Kamar yanda na saba
duk bayan sallah asubahi sainayi azakar, haka da
magariba. Yanzuma na gama namike na cika bokiti
daruwa na nufi wanka. Da nafito nazo na tashi shadad,
yana bude ido nace mashi adu‘ar tashi daga bacci kada
ka manta. Nan take ya karanta. Na sunkuce shi sai
bayi, nai masa wanka nasashi yayi alwala, na zura
mashi jallabiyar sa mai gajran hannu wanda na sai
masadon yin sallah. Nace to maza yi sallah kuma kayi
adu‘a yace to. Na koma na dauko sabulun da mukayi
wanka dama na wankine nazo na wanke muna
kayanmu, cikin raina ina mitar kayan shadad duk sun
kode inna sami kudi zan sai mai wasu. Tsaf na
shiryashi cikin kayan makaranta na dafa mashi indomie,
na share ko ina gyara. 7 da rabi na gama komai, sai
kurum naji bugun gida, nazaci dan a daidaitana ne sai
da na bude naga Abubakar tsaf cikin

Please Login or Register in order to submit comment