Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai dai ki
yafe mana, Allah ya baki hakuri."
Ni dai nayi daki.
Na koma Kano naci gaba da zuwa Makaranta, wata uku
jal ya rage min in kammala HND dina, tun tafiyar
abubakar bamuyi waya ba sai dai text yake turo min.
Cewar inyi hakuri wai abubuwa sunyi masa yawa shi
yasa, amma zai kira ni ina ranshi.
Cikin bacci naji karar wayata da faduwar gaba na tashi,
sai da na kalli agogo karfe 2 da minti 40 sannan na
dauki wayar na duba sadeek dina na furta a hankali
sannan na daga wayar a hankali na furta "Amincin Allah
a gareka" ya amsa da cewa " Ameen kema amincin a
tare dake, na tashe ki a bacci ko?
Nayi rigingine tare da matse filon a kirjina, nace ka isa
kayi fiye da hakan"
Ina jiyo sautin mumurshinsa ya ce tunaninki ya hana ni
bacci,kewar muryarki ta dame ni shi yasa na yanke
shawarar kiranki. Na ce Nima kewar ganinka nake yi
yaushe za ka dawo? ya ce, da gaske kin kosa ki ganni?
na ce um, ai ganinka ya fiye min komai a rayuwa
Sadeek dina. Ya numfasa"Me ki ka tanadar min kafin
nazo? Me ka ke so mijina? Ya ce, ke kadai nake so. Na
sake tausasa murya,Ni taka ce mijina,zan zama mai
binka a kowane lkc. Ya ce Na gode Hafsat,zan nuna
miki kalar soyayyata,za ki sha mamakina. Na katse
shi,"Wace iri ce ka fada min. ya ce a"a sai in nazo za
ki ga zahiri,yanzun zan sunbace ki in kin amince. Na ce
Bismillah. Sai kawai naji sumbarshi a cikin dodon
kunnena har cikin karamin yatsana, ya ce kiyi bacci da
mafarkina mai dadi. Na ce ba zan iya ci gaba da bacci
ba, zan tashe ne in nuna murnata ga Allah,tare da yin
addu'a ya tsare min kai, ya baka duk abn da kaje
nema,ya kuma dawo min da kai lfy. Da sauri ya ce,
Amin-amn sweet heart . Na ce Wannan Sunan Fadima
ne, zan fi so nima kasa min nawa. Ya ce, To shi kenan.
Kusan sakon hudu sannan ya ce, ki kashe wayar,na ce
kai ne babba kai ya kamata ka kashe,ya ce na gode.
Abin tamkar cikin mafarki, wai ni ce matsalolina ke ta
kwakkwancewa a hankali. Na tashi cikin farin ciki nayo
alwala nazo na zube gabn Ubangijina, addu'o'i nake
tare da nuna godiyata ga Allah. Na kuma yi wa mijina
shima, Allah ya dawo da shi lfy,ya biya mishi dukkan
bukatarshi na alkhairi,tare da dukkan Musulmi baki
daya. Ta gidan Rahma na biya na ce Lissafo min
abubuwan nan da ki ka ce ya dace in yi amfani dasu.
Ta dubi ne, Wane abu kenan? na ce, Na Amare..
-Ta sheke da dariya, sannan ta ce, "Dadina da gobe
saurin zuwa, yau ke ce kika zo neman abin da nayi ta
binki da shi kina gwasale ni?" Nima 'yar dariya nayi
sannan na ce, "Fada min." Na fito da memo da kuma
biro daga jakata. Ta ce, "Da gaske ki ke yi? To ai gara
kam ki rubuta don ba zan baki hadadde ba, zan fada
miki abubuwan da ya kamata ki dinga ci." Na ce to.
(Fruits ne ta yi mata listing including Nono, zuma,
madarar shanu, nonon rakum, kokumba da gurji) Ta ce,
"Kin rubuta?" Na ce, "Eh! Amma zan ta cin su ne haka
ko yaya abin ya ke?" Rahma ta ce, "Kina iya cin su ko
ki hada wannan da wancan. Na barki kije ki gwada
basirarki." Na natsu ina kara kallon abubuwan, sannan
na mike tare da cewa, "Bari in tafi kada Shadad ya
dawo ya same ni, amma zan baki mamaki. Sai kin zo
gurina rokon in fada miki irin nawa sirrin." Ta ce, "Zamu
gani." Na tafi ina dariya. Na cema dan adaidaita don
Allah ya kaini kasuwa. Ya ce, Ba komai." Duk abin da
na rubuta sai da na siyo su. Ta kan kankana na fara na
fere bayan na markade ta har 'ya'yanta cikin blender,
na dauko kwakwar da na yanka kanana itama na nika,
na daka raken da na yanka kanana. Na fidda ruwan shi
na hada su guri daya ban ko tace ba na fasa madara
peak na zuba zuma na fasa kankara na jefa, ranar shi
ne abincin dare na. Da safe kuma ina da garin alkama,
na dama shi da madara na zuba zuma, bayan na dama
shi ya zama kunu na sha. Da na dawo makaranta na
dafa zogale na yanka gurji a ciki kanana, na kwada da
kuli na zuba tumatir. Nan na zauna na ci na koshi,
sannan na kora da kunun aya da dabino da kwakwa da
madara da zuma yayi kauri na sha na yi kat. Da daren
ranar kuma farfesun kaza na yi ruwa-ruwa na
lankwashe na sha romon sosai. na yi kat, na zauna ina
cin apple (Hhhhhh, lallai Hafsa da gaske take yi 'yan
uwa, shan romo har da lankwashe kafa?
Washegari hadin kazar amare na yi ta tamkar yanda na
taba ji. Tun daga ranar ruwan 'ya'yan itace shi ne
ruwan sha na, dukkan abubuwan da Rahma ta lissafo
min na maidasu abincina, abin sha na. Kafin sati daya
ni da kaina na yarda cewa na hadu, kai ina mamakin
kaina idan na tuno irin kalaman da nayi ma Abubakar
idan ya kira ni. Shi kan shi Abubakar din baya iya
daukar awa 3 ba tare da ya kira ni ba, lallai na amince
iya yin lafazi mai kyau ga miji yana sa mace ta mallake
mijinta, nuna damuwa ga damuwar miji tana sa miji ya
kara son ki.
Ana gobe za su dawo na shiga kasuwa na yo cefane,
duk da bani da tabbacin cewa Kano zai sauka, Na
damu ya zo don shirina da nayi ya soma damuna. Ina
kwance bayan la'asar na kira layinshi ya daga, cikin
sauri ya ce, "D only! Yaya ne?" Na ce, "Hayate don
Allah ta nan zaka biyo?" Na yi maganar cikin sigar
shagwaba. Ya ce, "Muna tare da Abba yanzun, zan kira
ki in mun rabu dashi kin ji?" Na ce, "Toh." Ba'a fi koh
minti 10 ba ya sake kirana. "D only kina jina?" Na ce,
"Eh!" Ya ce, "Muna tare da Abba ne kin ga ba dama mu
rabu ko? Kuma Fadina tana sa ran zuwana." Na ce,
"Kai Hayate (cikin shagwaba nake maganar) Ba fa nan
ka tashi ba, don Allah ka min adalci in ganka kawai ka
wuce, ko ba ka zauna ba." Zai yi magana na ce,
"Please Mr Cool, bana jin zan iya kwana 2 ban ganka
ba, sorry pls." Sai naji yayi ajiyar zuciya tare da cewa,
"To yanzu yaya zan yi da Abba?" Na ce, "Ya san kana
da ni fa a Kano, in kace zaka zo ai bana zaton cewa
zai yi fada." Ya ce, "Bana son ayi zargin cewa nafi
sonki amma zan dan yi dabara in zo din ko ban kwana
ba, muka ga juna sai na wuce." Na ce, "To na gode Mr
cool. Sai na ganka."
Hmm! Ranar da zai dawo ko Makaranta ban je ba, tun
safe na ke hada mishi sinasir da miyar alayyahu,
simmer fish, meat bolls, meat into potatoe da peppered
chicken. Na yi fruit salad na yi coslow, jus din
cocumber, sai kuma na yi masa coconut drink.
Nan na shiga jera masa duk abubuwan da na tanadar
masa. Jus din na soma zuba masa ya sha sannan na
bude masa dukkan abubuwan da na girka na ce,
"Wanne zan soma zubawa?" Sai da ya hadiyi miyau
sannan ya ce, "Kowanne kadan." Tun da ya soma yake
fadin, "Alhamdulillah Masha Allah, na yi dace kam."
Dadi nake ji tamkar in yi tsalle sai sake zuba mishi na
ke, ya ce, "Bar shi kada in kasa bacci." Na sirka mashi
ruwan wanka, ya ce da na sanyi zai yi na ce, "A gajiye
ka ke zaka fi jin dadin wanka da na dumi." Ya ce, "To."
Daki ya shiga ina daga waje ya bude jakarshi ya canza
kaya, sannan ya ce, "Zo ki raka ni in kama masauki."
Na ce, "Nan gidan ba za'a iya bacci ba?" Ya yi dan
murmushi, "Zo dai mu je mu dawo."
Shahararren masaukin bakin nan muka je ya kama daki,
na bata rai. Bayan mun zauna bakin gado ya ce, "Yi
min dan murmushin nan mana." Na dan harare shi da
wasa, "Ba ka 'ki kwana gidana ba." Ya ce, "To ni nan
zaki taya ni kwana." Na zaro ido, "In taya ka me? Tab!
Tunda dai na rako ka maidani gidana." Ya ce, "Tsoro
nike ji, dakin yayi min girma." Na harare shi tare da
cewa, "Da can ba kai daya kake kwana ba?" Ya ce, "To
ai yau na soma jin tsoron, ba kin ce kin min tanadi ba?"
Na ce, "To ba na baka ka ci ba?"
Ya ce, "Daman wai tanadin abinci ne?" Na ce, "Eh
mana." Ya ce, "Ammafa ba haka muka yi da ke ba." Na
ce, "To yaya muka yi?" Ya mike ya dauko jakarshi, "Zo
ki gani." Ya fitar da duk kayan jakar, can kasa ya fito
da wasu kaya, kayan baccine 'yan India masu shegen
kyau, baki da pink ne. Ya fito da pink din ya ce,
"Gwada wannan in gani." Na amsa na daga ina kallo,
akwai kyau amma zai fi dacewa da sunan Fandarinki
tsirara. Na yi tsaye ina kallonshi yana mai da kayan, ya
mike, "Kawo in gwada miki." Na ce, "Zan iya." Na fada
toilet na saka, na dubi kai na, zan iya fita kuwa? Na yi
ta maza na kama kofa zan bude, sai kurum na ga ya
bude ya shigo. Na runtse idona shi kuma ya ce, "Kai
cancadi! Zo mu je in miki hoto." Ya rikeni muka fito.
Ya zauna bakin gado tare da dorani kan cinyarshi, Kai
Subhanallah!!! Abubakar ya fara shafani tun daga
wuyana har ya sauko kirjina wanda ba kace na shayar
da Shadad ba, ya rude ya shiga kissing dina, anan dai
ya dinga yaba min irin goyon bayan da na bashi tare da
tanadin da nayi masa, ya dinga min surutai wanda bana
gane mai yake cewa, sai dai numfashinsa kawai nake ji,
kai ba zan manta da wannan rana ba, son Abubakar da
kaunarshi gami da kishinsa sun karu gareni, kai na so in
cuci kaina, kuma na yarda cewar soyayyarshi mai tsada
ce, amma na kula shima ya yaba da ni matuka. Nan
muka yi Magriba da Isha'i munata tarairayar juna, ian
kallonshi ya kashe dukkan wayoyinshi, a takaice dai
nan muka kwana muna faranta ran juna cikin farin ciki,
ko kuda baya son yaji a jikina.
Misalin Goma na safe muka dawo don 12 zai nufi Yola,
amma sai muka bude sabon shafin soyayya anan gida
na, ya dinga lugwiguita ni yana zantuka iri-iri masu
wuyar ambato, Abubakar ya dinga santi tare da yabon
Hafsa cikin kalamai masu dadi, nan muka kwashe
lokuta da dama dan bamu san lokaci ya tafi ba, har ya
so ya makara. Ni kam da zai tafi har da kukana, ya
lallashe ni da cewa jibi zai zo mu wuce Kaduna don
karkare shari'ar nan, da kyar ya lallasheni sannan ya
tafi. Kwana daya jal da muka yi ya sani na manta duk
wata damuwa da ke raina, lallai Abubakar shine irin
mijin da mata ke so, wanda zai shagwabaka, ya so ka
kuma ya riritaka, har ka mance a duniyar da kake.
(Ohh! Su Hafsah sai sambatu ake) Ya san so yasan
sirrin so, ya san yanda ake zama da mace. Haka ya tafi
ya barni da kewarsa duk na rikice.
Da dare ina kwance tamkar in kirashi amma sai na tuno
can mafa yana tare da matarshi, kishi ya isheni, yanzun
duk irin kulawar nan da ya bani haka zai bata? Sai
hawaye masu dumi suka soma sakko min, can dai na
dauko wayata ina kallon hotunan da muka dauka ni da
shi cikin soyayya da kauna irinta masoya, lokacin muna
cin abinci cikin soyayya da tsokanar juna a masaukinsa,
kawai sai na samu kaina da rubuta masa I LOVE U na
tura masa. Can har na fara rubuta dogon text na
soyayya, sai kuma na fasa na ce abinda baka so a
maka kai ma kada kayi ma wani, don haka sai na
danne.
Kusan 12 sai ga kiranshi, da sauri na daga, a hankali
yake magana ina zaton ko Matarshi ta yi bacci ko
kuma ta dan fita oho, ya ce, "The only kina jina?" Na
ce, "Eh." Ya ce, "Na ga sakonki, ina sonki sosai, ba zan
manta irin kaunar da na sha a gareki ba, kin jiyar da ni
dadi matuka, inata tunanin kasancewa tare da ke, kiyi
bacci kinji?" Cikin Marairaita na ce, "Ba zan iya ba Cool,
yaushe zaka zo?" Ya ce, "Zan kira ki anjima kin ji?" Na
ce to. Ya ce, "To in kin kasa bacci tashi kiyi mana
addu'a Allah yasa mun samu Baby." Na ce, "To Cool,
miss U." (Hhhhhh, Su Hafsah an hau duniyar sama an
gaza saukowa)
Hakan kuwa na yi, da nayi alwala na dauki Al-kur'ani na
soma karatu, sai na samu nutsuwa. Kusan 2 na dare ya
kirani, "Me ya hana ki bacci d only?" Na ce, "Tunaninka
mana." Ya ce, "Nima kina raina Hafsah, da ban same ki
ba da nayi asara." Na ce, "Wai! Ni ce zan ce da nayi
asara don irinka akwai wuyar samu." Ya ce, "Maza da
yawa ba zasu gane ba sun fi kallon kyan fuska, Hakika
suna zaban tumun dare." Na yi dariya sannan na ce,
"Ka kwanta don Aunty Fadima ma baza ta so muna yin
doguwar hira lokutan kwanan ta ba. Sai da safe." Ya
ce, "To." Na sake alwala na zo ina Nafila dan wannan
sallar tana da Muhimmanci gurinmu, in har zaki yarfe
bacci ki tashi daidai wannan lokacin ki fadama Allah, to
kuwa duk wata matsala taki zata yaye. Ubangiji da
kanshi yake cewa da mai bukata ya tambaye shi Shi
kuma ya biya mana, wannan kadai na tsare, ba boka ba
mallam ga matsalolina a hankali duk sun warware.
Allah ka yaye mana dukkan matsalolinmu Ameen.
Ranar Lahadi kuwa ranar da zai zo cewa yayi in masa
tuwon semo, sai kuma in masa jus din Shinkafa din
nan. Miyar danyar kubewa na yi masa, ta ji
bushashshen kifi da nama, na masa jus din shinkafa,
sai irin kunun ayan da nike sha mai dabino da kwakwa
da zuma. Wando da riga na ci sabbi ne na siyo su, da
ina zaton ba zan iya saka wando ba amma daga baya
sai na ce kiji kana cewa baka iya kukan mutuwa ba
Uwarka ce mata mutu ba. Da kadan ya wuce gwiwata,
rigar ma ta dame ni. Kallona yayi ta yi tunda ya shigo
na masa oyoyo, da kyar na bambare daga jikinsa don yi
masa shimfida, ya ce, "Ya ya aka yi kika san ina son
shigar English wears?"
Na ce, "Duk abinda ka ke so a kwayar idonka nake
karanta, ai ba kallon kawai nake maka ba." Ranar dai
mun ciyar da juna abinci, sannan muka shiga wani
shafin, daga baya muka yi wanka muka dunguma gidan
su Rahma. Shadad kuwa sai tsalle da ya ganmu, da
zamu tafi ya so binmu, har zan ce mu tafi da shi sai
Abubakar ya ce, "Shadad unguwa zamu, amma gobe
zaku taho da Uncle dinka na nan gidan." Ya ce, "To."
Muka dawo nan gidan muka kwana.
Gaskiya duk macen da ta samu miji kwatankwacin
Abubakar, to ta gode ma Allah, mamaki na daya, yanda
ya iya kula da mace ta kowanne fanni......


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 4-05
Posted by ANaM Dorayi on 05:17 AM, 29-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Asubanci muka yi tare da su Sagir, Sagir ke tuki shi da
Abubakar, ni da Rahma da Shadad muna baya. Sagir na
zuba mana hira don shi Abubakar mutum ne bame
yawan surutu ba, sai dai mun ta hada ido da shi ta
madubi sai ya kashe min ido daya mu yi murmushi, har
Rahma ta gane mu ta ce, "Kai ku dai wanna soyayya ko
ina sai kun nuna ta?" Na ce, "Kuma ku nuna mana."
Kotu ta cika lokacin hankalina na tashe, gani nake shi
kenan za'a kwace min da. Bayan gabatarwa Alkali ya
bukace mu muka fito ya ce, "Ina yaro?" Aka fito da shi
ya ce, "To a musulunce za'a yanke hukunci tunda mu
Musulmi ne." Duk muka amince. Alkali ya yanke cewa,
"Duk da cewa fyade aka yi mata ta samu ciki, to dan ba
dan Sunna ba ne, ma'ana ba ta hanyar aure aka haife shi
ba. Don haka in ma ace tayi cikin shege dan nata ne ba
a danganta shi da namijin saboda sai da yardarta, don
haka wannan ma nata ne, sai dai shawarar da zamu iya
bata ita ce ta bawa wannan mutum dan saboda zata fi
mutunci, haka nan shi dan ko kuma a ba yaron zabi zai
bi Uban nasa shikenan. Sannan hukuncin fyade tunda an
ce bai taba aure ba, to za a yi masa bulala dari." Nan fa
suka soma kuka, Mom ta zo tana kuka tana rokona wai
in basu shi, na ce "Gaskiya ba zan iya bada dana ba."
Shi kuma Dad dinsu ya samu alkalin suka kiramu suna ta
rokonmu wai tunda gashi shi za'a dake shi, gashi bashi
da koshin lafiya. Abubakar ya ce, "In dai yayi hutu za'a
ringa kawo shi saboda ya san Ubanshi da danginshi."
Suka yi ta godiya muka kame kanmu. Kano muka wuce
bayan mun je gidanmu kowa na taya ni murnar cin
nasara, daga nan muka koma Kano. Na gama jarabawata
ta fita, murna ba a magana yanzun saura service
Washegari da gaggawa Abubakar ya zo ya tafi dani Yola.
Shadad kuma dama Sagir ya kai shi Kaduna gidan
Babanshi suna ta murna. Shi kam da kyar ya lallasu daga
kukan da yake sai da Sagir din ya kira ni ya ce in mishi
magana. Na ce, "Shadad." Ya ce, "An'am Aunty, ni zan
dawo ne ki fada ma Uncle ya dawo da ni." Tausayinshi
ya kama ni na ce, "Gidanku ne ai, gidan Babanka da kake
ta damuna da zancenshi." Ya ce, "Aunty ban san su ba."
Na ce, "Zaka san su kayi hakuri kaji ko?" Ya ce, "To."
Munir ya ce ma Mom ta amshi lambata in ya so sai su
dinga kira mishi ni. Sagir ya bada lambar sannan ya tafi.
Ikon Allah Shadad na ganin gata, tamkar a cinye shi don
tarairaya, har an sai mishi waya don ya dinga kirana, ni
kam cewa na yi kada su bata min tarbiyyar yaro, saboda
su ba su da tarbiyya. Mahaifin Munir ya yiwa Shadad
kyautar gidanshi da ke Kabalar road, tunda wai an ce
bashi da gadon Ubanshi. Suka bude mishi account ni kam
ina can Yola gidan mijina mai sona da gaske.
Yau gidan Fadima yake, amma ya kira ni wai zaya zo
cin abinci da rana. Na ce, "A'a, sai dai na yarda ka aiko
a karba maka, don kada mu shiga hakkinta, Don nima
ba zan so amin ba." Ya ce, "To naji." Na yi masa
french dish rice serve with grill chicken, sai kuma na
masa dan waken rogo da dawa, dama ina da garin,
sannan na masa jus din karas, duk san da zanyi girki na
kan yi da dan dama saboda mutan gidanmu suna son
abinci na.
Hakan nan na kan kirkira girki inyi ma Abba da Lamido
da kalokin Jus na kan zauna ina kallon tashar girke-
girke ina rubutawa na Chanis ko Italia ko Senegal da
dai sauransu. Saboda kawai in samo girki wanda ba a
saba da shi ba.
Fadima ta dube shi, "Ban gane nufinka da amsa abinci
gidan Hafsa ba?" Ya dube ta bayan ya dire kofin
hannunsa ya cea, "Ta iya girki ga kokarin yi, bata da
kuiyar dafa abincin ko kala nawa ne." Ta hade rai, "Ni
ban iya ba kenan?" Ya ce, "To ke ko kin iya din ma
yaushe kyuya zata bar ki? Ballantana kure girkinki shi
ne shinkafa da miya ko taliya. Da zaki daure da kin je
kin koyo kafin ta tafi CAMP." Ta harare shi sannan ta
ce, "God Forbid in je gurinta koyon girki ka cuce ni,
kuma wallahi ba zan yarda ba. A ranar girkina ace
abincin ta zaka ci? In an sake kawo min nan zan zubar
dashi." Ya ce, "To shi kenan, zan so ki zubar din." Cikin
fushi ta shige daki. Duk ranar da yake gidana akwai
wasu jus na kankana, Apple, ayaba, madarar ruwa,
zuma da kuma garin ridi, in sa kayan itacen a blender
in nika in zuba madarar da zumar da kuma garin ridin in
sha, in kuma zuba masa ya sha, har dai wata rana ya
tambayeni me nake sawa cikin wannan jus din? Don shi
kan shi yana jin shi kullum yana kara lafiya da kuzari,
yakan kuma ji yanayi daban da in bai sha ba. Na ce
'ya'yan itace ne. Har ma watarana a gabanshi nake
hadawa. Wataran kuma in hada rake, zuma, madara
peak, garin ridi. Kafin wani lokaci sai gashi na zama
Malama ta hada kayan gyaran jiki, in mun yi waya da
Rahma in na fada mata wasu sai tayi ta mamaki, na ce,
"Dama na fada miki."
Abin da yafi bani mamaki, da zan tafi CAMP a Kaduna
aka tura ni har da kukan shi da hawaye don damuwa.
Shi ya kai ni sannan ya biya ya taho da Shadad ya kai
shi gidan Rahma a Kano. zaman sati 2 a camp ko ni na
san na yi missing din gwarzon masoya, Abubakar
Sadiq.
Fadima ta dubi Rukayya, "Kin san Allah ni zan kai karar
Hamma gurin Abba, sam baya cin abincina sai na
Hafsa. Don gulma har nan zaki ga ta yo ta aiko mishi
da shi, kenan ya fada mata cewa ban iya girki ba."
Rukayya ta ce, "Ai Hamma ta riga ta gama da shi, ke
har su Daada ma in kinji yanda suke yabonta? In ta yo
abinci ta kawo ma Abba kiga su Ummi har ma Daada
din sai suyi ta yabonta." Ta ce, "To gurin Lamido
zanje." Rukayya ta ce, "Kin ji ma inda zaki fi jin dadin
kai karanki, kuma zaya ci musu daga shi har ita. Dama
ai ba son auren yake ba, kila ma yana kushe auren."
Cikin zumudi Fadima ta ce, "Anjuma zan je."
Ta shigo gidan da sallamarta suka gaisa da mutan
gidan, tsoffin suna mata tsiyar cewa sun kwace miji. Ta
shiga gurin Lamido, bayan sun gaisa ta ce dama ta
kawo karan Hamma ne. Lamido ya gyara zama ya ce,
"Tun kafin aje ko'ina har an soma matsala? To me ya
faru?" Ta ce, "Baya cin abincina, ranar da yake gidana
sai ya aika nan a karba mishi abinci fa, kuma in nayi
magana sai ya ce ta fini iya girki. Shi ne ni na gaji da
wannan maganar." Can ya ce, "Shikenan?" Ta ce, "Eh."
Ya ce, "To yanzun ina Baban nawa?" Ta ce, "Yana cikin
gari." Lamido ya kira shi a waya ya ce ya zo yana
nemanshi. Kusan minti 30 sannan ya iso Lamido ya ce
masa, "Daga ina?" Bai ji mamakin ganin Fadi ba.
Lamido ya karanta mishi laifukan da ta fada, sannan ya
tambaye shi ko haka ne? Abubakar ya ce, "Haka ne."
Lamido ya ce, "Don me to baka son cin abincin nata?"
Abubakar ya ce, "Don bata iya ba, kuma don na amso a
gurin Hafsat wadda ta iya bana zaton na yi laifi.
Saboda Manzon Rahma (S.A.W) yana amso abinci a
gurin Nana Safiyya ya ci in yana dakin kowacce daga
cikin matanshi. Don haka ni Sunna na yi." Ta ce,
"Amma shi bai yi wulakanci ba." Lamido ya ce, "To naji
yanzun dai sai kiyi kokari ki gyara." Abubakar ya ce,
"Abin da in riga ta dawo wa kullum sai na fa jira ta ta
dawo sannan ta min abincin. Ita kuma Hafsah ko ina
zata sai tayi min abincin ta bari in dai tana gari, amma
ita wannan sai son jiki." Lamido ya ce, "Ka yi hakuri
tashi ka je abinka.Bayan fitar Abubakar Lamido ya ce,
"Ke Fadima abin da zan fada miki, kin ga bakuwar
yarinyar nan? To ta fiki hankali. Tun yaushe rabonki da
gidan nan da sunan ki zo gaishe mu? Ita kuwa ko bata
garin nan ta kira mu ta gaishe mu a waya. Girkinmu
daban ga girmama mutane, don haka ki nutsu ki zauna
lafiya. Ba zan 'kita ba don tana bare, dama ai mugun iri
ake tsoro." Fadima dai ta tashi jiki babu kwari ta tafi
gida, zuciyarta cike da haushin Hafsah, wato ta zo zata
siye dangi? Ta ja wani Uban tsaki.
Allah cikin ikonsa mun gama CAMP sai dai Abubakar
ya ce zai yi duk yanda zai yi a barni a Yola, ba zan
kara nisa da shi ba. Daga baya ma ya ce in na gama
bazan yi aiki ba, ni dai ina jin shi ban ce komai ba.
Allah ya taimaka da ya shiga ya fita sai ko aka barni a
Yola, ni kaina nayi murna don bana son inyi nisa da
mijina, Shadad ya dawo Yola shima Abubakar ya canza
masa Makaranta mai kyau, duk da cewa Iyayenshi suna
ta turo kudi wai na karatunshi. Dad har Yola ya zo
kuma ya sanar da abokinshi Mai Martaba Baban su
Hashim cewa Shadad jikan shi ne, don haka yaron bai
da matsala ko cikin gida, gashi da farin jini.
Cikin haka ne FADIMA TA SOMA LAULAYIN NAN, naga
rawar kai wurin Abubakar da 'yan uwansa, ganin haka
nima na soma zuwa kullum ina dubata, sai ta tsiri cewa
wai turarena na sata amai, in daina zuwa. Abubakar ya
ce, "Fadima ta ce bata son turarenki ki daina zuwa
kawai." Allah yasan na ji haushi, amma sai na share
saboda sanin halin Abubakar shi mutum ne sak babu
kwane-kwane a tsarin shi, baya rufa-rufa ko kara
zance, yanda aka fade ta haka yake daukenta, shi yasa
na sha wahala lokacin da na ce mishi ni karuwa ce, har
sai da ya zo ya ji komai da kunnanshi na samu sukuni.
To yanda Fadima ta ce haka zai fada gaskiya
tsagwaronta yake yi ba ruwanshi, don haka na ce, "Shi
kenan, na ringa kiranta a waya muna gaisawa." Ya ce,
"Hakan zai fi." Daga baya sai ta tsiro cewa ita ba zata
iya bacci ba sai in yana gurinta, Ya ce to bari ya same
ni. Ina

Please Login or Register in order to submit comment