Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana tunda shi ba mai
haya niya ba ne, Mun je naga dakin, karami ne ta ce
dubu shida shekara, dari biyar kenan dk wata, na ce ba
komai, zan biya. Naje banki na ciro dubu ashirin cikin
kudina nazo na bata shida, naje kasuwa na siyo kayan
abnci da yar tukunuya da dan risho na dawo.
Zaman mu da Hjy Iya ba matsala, don ina bn ta sau da
kafa,daga ni sai ita a gidan tun Asubahi in na tashi zan
wanke mana bandaki, in share tsakar gidan, komai na
dafa zan bata. In ko zan yi wanki na kan ce kawo naki
Hjy, kullum sai dai ka ji tana shi min albarka, Shadad
kuwa dama tuni ta ce in dinga bar mata shi tunda in
bana nan ba shi da matsala, musamman in ya gane cewa
gidan muke kwana. In ko unguwa na fita dashi kiwa ce
dashi, sannan ya yi ta 'yan rigime-rigime. Mun zauna
yanzu albashina da kyar nike kai dubu biyar banki a
wata, saboda hidimomin gida wanda a da ban san suba,
kai ko kan wannan ba zan manta da Doctor ba, domin ita
ce ke yi min komai. Burina na gaba shi ne, in koma
makaranta, amma yaya zan yi da aikina wanda shi na
dogara da shi? Wata rana da dare na shiga gurin Rahma
muna hira, na ce mata ina son na koma makaranta, ta ce
aikin fa? Na ce shi ne matsala, amma ina son in samu ko
'yar Diploma ba sai nayi jami'a ba, ta ce hakan ma yana
da kyau. Aikina daga karfe takwas din safe ne zuwa
hudu na yamma, sannan wasu su zo masu kaiwa dare,
na ce Rahma ko in koma aikin dare ne. Ta ce albashinsu
fa bai kai namu ba kuma yawan cinsu duk maza ne, na
ce to ya zanyi? Haka nan zan hakura in dai manaja zai
yarda ta ce matsayaci ba, sai shegen iko sai ka ce gurin
shi. Na ce ai dama ba shi ne da gurin ba? Ta ce ba shi
ba ne, na wata Hjy ce mai kudi, ina zaton ma ba a kano
din nan ta ke ba. Na ce to Allah dai yasa in dace zan
tare shi in masa mgn, Rahma ta ce to in ya ki fa? Na ce
ki taya ni addu'a ya yarda, Rahma ta ce to Allah yasa a
dace, in za ki masa magana sai muje tare .Haka ce kuwa
ta faru, domin washegari muna tashi daga aiki sai muka
nufi ofishin manaja, yana zaune gabn shi laptop ce.
Muka gaishe shi, cikin daurewa ya amsa, na ce "Yalla6ai
nazo neman uziri ne. Ya harare ni,wannan karon ko me
kika zo nema kuma kowa ya mutu ba zan ba ki wasu
kwanaki ba, sai dai in ki nemo wadda zata zauna
madadinki. Rahma ta ce, Sir, ba mutuwa akayi ba, tana
son koma mkrnt ne. ya ce, to sai ta bar aikin. " Ya ci
gaba da abn da yake yi. Muka kalli juna ni da Rahma, na
ce ko zan iya komwa akin dare? ko kuma in zo duk lkcn
d nike free hr dare? Ya ce wace makaranta? Na ce poly
zan shiga, ya kalle ni dama ba ki riga kin shiga ba? Na
ce eh, ya ce to in kin shiga sai muyi magana. Ni da
Rahma muka yi godiya, bai amsa mu ba, mu dai muka
fita muna mamakin yanda ya saurare mu. Ina jin an fara
saida form na garzaya na sayo. Rahma tana ta min
dariya wai na cika zumudi, Allah shi ne mai shirya ma ba
wa al'amuran shi. Yau gani na samu gurbin karatu a poly,
daga karfe daya zuwa biyu nake tashi, uku in zo shago,
bn damu da rage min dubu biyun da aka yi cikin
Albashina ba, saboda na samu shiga makaranta. Kuma
na samu irin course din da nake so, wato (Mass comm)
Rahma da murnarta take shaida min saurayinta Sagir zai
turo magabatan shi, na ta6a baki tare da cew. "Yau an
yo odar kaya a shop din nan, kin lura? Tace eh na lura
mana. Amma me yasa kullum na dauko batun Sagir sai
ki daure fuska? Haka nan ranar da na ce kuje ku gaisa
kikaki.Shi ko kullum sai ya ce in gaishe ki. Na ce, um, ki
dai yi hattara da samarin yanzun. Ta ce, Sagir yana da
kirki kuma aurena zaiyi, na kafa mata ido, kada ki ba wa
namiji amana fa, in kin yarda kenan. "Ta ce, to zan kula.
Wata rana ta ce min za su je gidan Yayar Sagir, zata
gaishe ta, wai tayi 6ari, na shirya muje na kalle ta
dabadan Rahma ba ce dana zabga mata ashar. Amma
Rahma ta wuce in zage ta, kema da zan fada miki ki ji
da sai na ce miki kada kije, ta ce ko zan san dalili? na ce
yaudarar mazanzamani.Tayi 'yar dariya, "Hafsat me yasa
kin matukar tsanar maza ne? Me suka miki har haka?"
Murmushin takaici ya subuce min na ce, "Sun min da
yawa." Ta ce, "Kada ki manta shekararmu 1 da Sagir
kuma kudin gaisuwarshi na gidanmu." Sam ban san
lokacin da maganar ta subuce min ba sai ji nayi ina
cewa, "Shekaru 3 da watanni muka yi ni da Munnir,
amma hakan bai hana shi yaudarata ba."Hawaye suka
soma zuba daga idona. "Rahama zan fada miki amanar
sirrina, in kin boye min kin kyauta, in kin tona min don
kanki ke da Allahn ki." Nan na kwashe komai na labarta
mata, ni kuka Rahma kuka, ta rungumeni babu mai ba
wani hakuri sai da muka gaji da kanmu. Na ce, "Rahma
zan koma boko ne kawai don faranta Ran Mahaifiyata,
Insha Allahu zan kawo haske cikin zukatan Iyayena
SANADIN BOKON nan." Rahma ta ce, "Ina bayanki, Allah
ya shige mana gaba. Lallai zan ja baya da Sagir kuma ba
zanje gidan Yar tasa ba." Na ce, "Na kula Sagir dinki
kamar bashi da matsala, duk daba anan take ba. Ki ci
gaba da mishi yadda kika saba amma ko da wasa kada ki
bishi wani guri. Amma ni a kan kaina na gama soyayya,
na kuma sha alwashin duk namijin da yayi gangancin
cewa yana sona zan ci zarafinsa matuka. Rahma ko
kinga laifina?" Ta ce, "A'a."Rahma 'yar amana ce, ko
Mahaifiyarta bata fadawa labari na ba, haka na ci gaba
da Karatuna tare da aikina, na tsare mutuncina ko a
makaranta nasha jin ana zagina wai na cika girman kai,
daga ganina ni ba 'yar kowa bace sai shegen Iyayi, ga
daure fuska. Sam ban damu ba, sai dai mutum in ya isa
ya zo gabana ya fada.
Kwanci tashi har na hada Diploma, kuma ina da burin ci
gaba da HND,shekara 2 kenan. Cikin shekara 2 har
Shadad ya isa shiga Makaranta, kuma na lura zaya dauki
Karatu sosai, shekarunshi 4 kenan da 'yan watanni. A
hanyar zuwa gurin aikina naga wata Makaranta Al-Iman,
boko ce da Islamiyya don haka na je Makarantar na
karbar masa form, sun ce yaro ya zo tun 8 na safe sai 6
na yamma. Duk da Islamiya da hadda, sati da lahadi sai
karfe 2 zai je. Alhamis da Juma'a karfe 2 zasu tashi.
Tsarin makarantar ya min daidai domin zan samu lokacin
daukan shi, sati na zagayowa ya soma zuwa, da dare
kuma inai masa bita.
Tambaya daya ya min wadda ta sa ni kwana kuka, tare
da tunanin me zai faru nan gaba? Ko ba komai nasan
nan gaba akwai kura, abin da ya faru ranar da ya fara
zuwa Makaranta ya dawo muna yin home work ya ce,
"Anty." Na dube shi, "Menene?" "Me yasa da kika kaina
Makaranta baki sa min sunan Babana ba? Duk 'yan
ajinmu ana kiransu da sunan Babansu, ni kuma ana
kirana da Shadad H." Gabana ya fadi, amma da yake shi
karami ne yanzun ba zai fahimta ba sai na ce, "H din nan
farkon sunana ne Hafsat na sa maka ko baka so?" Ya ce,
"Anty kowa sunan Babanshi yake sawa, wani yaro yace
min wai menene H? Wai Hamza sunan Babana?" Na ce
masa, "Ban sani ba, nace ba sunan Babanka ba ne,
sunana ne kaji ko?" Ya ce, "To." Can kuma sai naji ya ce,
"To shi Babana ya sunan shi?" Gabana ya sake faduwa
na daure na ce, "Na manta, amma in na tuna zan fada
maka." Na mike don kar ya sake yi min wata tambayar.
Shadad karamin yaro ne amma in ya maka magana sai
kayi zaton Babbane. Ina tsoron nan gaba kadan ya
tsareni don in fito masa da Ubansa, abu 1 na sa a raina,
shine zan zama uwarsa kuma ubansa, zan yi masa komai
da uba zai ma dansa.
Tun da na bar gida har yau ban daina kuka ba, ban daina
tunanin iyaye da 'yan uwana ba, kullum sai na zubar da
hawayena tare da yin Allah ya isa kwando dubu ga
Munnir, ba zan zagi Boko ba sai dai ba zan gaji da cewa
itace sanadin shigata matsala ba.
Haka kwanaki suka yi ta shurawa Allah ya taimake ni na
koma don samun HND sai dai manejin rayuwa nike,
albashina yayi karanci ya dauki nauyin karatuna da na
Shadad, don ma na tara kudi da farko lokacin Dr. tana
nan. Sai dai na dauki alkawarin ko zamu kwana ba mu ci
ba bazan taba neman taimakon abokin halitta ba, sai dai
in nema a gurin Mahalicci.
Cikin wannan halin yarinyar Hajiya Iya wadda ke zaune a
Saudi ta zo ta dauke ta tare da barin amanar gidan a
hannun Babban Yayan Rahma. Amma ni Hajiya Iya ta ce
in yi zamana kyauta har sai lokacin da Allah ya daga,
don ta ce ina lura da ita, kuma duk abinda na ci sai na
bata koda bata san da shi ba. Na ji dadin samun wannan
rangwame duk da cewa kudin ba wasu yawa bane dama,
amma sauki yana da dadi. Na dawo ni 1 a cikin gidan, in
zan fita na kulle, in sati ne ko lahadi ko dai wane lokacin
ne Shadad ba zai je Makaranta ba sai na kai shi gidan su
Rahma gurin mama, in ko ba nisa zanyi ba nakan yi
kasadar kulle shi ya taka kujera ta ciki ya sa sakata, in
na dawo sai na kwankwasa ya bude.
****** ******** *******
A garin Kaduna tun da aka wayi gari Hafsat ta gudu,
bakin ciki ya karu ga zuciyar Innarta, don haka ta tattara
yanata-yanata ta fice ta bar su Ummi suna ta kuka,
Baba tana lallashinsu. Har ta isa Malimfashi idanunta
basu kafe da hawaye ba, bata boyewa 'yan uwanta
komai ba,sunji bakin ciki suma saidai sun bata shawarar
tayi mata addu'a kada ta mata baki.Haka ta ci gaba da
zama har zuwa lokaci mai tsawo. Wani abokin wansu
Babba ya zo ziyara daga Huntuwa ya ganta ya ce yana
sonta, bata da zabi tunda duk yayyinta sunnuna sun
amince, kuma aurenta da uban 'ya'yanta ba kome.
Alhaji Danlami Matarshi ta rasu wurin haihuwa, amma
yana da yara kuma yana zaune tare da su ne,
shekarunsa 3 kenan rabonsa da aure, ta tare a gidansa
dake Nasarasa Funtuwa, dole ta koyi hakuri domin zama
da yara sai hakuri, in ta kalle su sai ta tuna da nata da
ke can wani gida. Sai ta kyautata musu ko don a
kyautata ma nata, yadda take kula da Yaran sai suma
suke son ta.
Cikin haka ta samu ciki ba don san ranta ba, amma ba
zata butulcewa kyautar Allah ba. Ta haifi danta namiji ya
ci sunan Rabi'u. Umar ya kan kawo mata ziyara da 'yan
kannanshi, mijinta yanada kara don in zasu tafi yanai
musu shatara ta arziki. Shi kuwa Babansu Hafsa har yau
yana bakin cikin tafiyar ta duk da shine ya koreta, yana
kuma addu'a Allah kada ya bashi mai irin halin Hafsa
cikin 'ya'yansa, ganin halinta ne da na Uwarta, ko wani
buri suka ci na son abin duniya shiyasa suka dage da
boko, boko har taje ta yi abinda taga dama.Ni kuma
lokacin rayuwa ta min tsanani, zuwa wannan lokacin
kudin da ke cikin account dina sun kare, albashina ya
min karanci, karatuna ga na Shadad, ga abinda za mu ci,
omon wanki, sabulun wanka har da suturar sawa, duk a
dubu 8. Don ma bana biyan haya. Yau na wayi gari ko na
karyawa bani da shi, ga shi wannan watan shine zan
bada kudin term na Shadad dubu 4, gashi zan yi
registration, gashi bamu da komai na abinca ga kudin
dan adaidaita sahu. Hakika komai ya tsananta gare ni,
kukana ya karu, nadamar barin gidan Iyayena ta sake
shigata sai dai ba zan iya komawa gidan yanzu ba, duk
da kuncin rayuwar da nake fuskanta. Lallai babu komai
cikin barin gida in ba takaici ba, danabi Mahaifiyata na
san danginta za su saurareni za kuma su fahimceni, zan
samu gata ni da dana kafin Allah ya min sakayya akan
Munnir. Bana ba duk wata 'ya mace shawarar barin
gaban iyayenta don gudun zubewar mutuncinta. Hawaye
na bin kumatuna ban damu da na share su ba, domin da
hawaye na karewa da yanzun nawa sun kare. Muryar
Shadad ce ta katseni, "Antyna menene yake damunki
kullum kike kuka?" Na share hawaye tare da kakaro
murmushi, "Babu komai." Ya dafa cinyata, "Kina tunanin
Iya ne?" Na ce, "Eh." Ya tambayeni ni don ya san kalmar
da zan fada mishi kenan, a duk lokacin da ya tambayeni
haka nake ce masa. Ya bata rai, "Anty to muje gurin Iya
din, ni bana so kina kuka." Na ce, "Da nisa jirgi ake hawa
kuma bani da kudi." Ya ce, "To ina girma zan saya mana
jirgi muje ko?" Na ce, "Allah ya sa." Kicin na shiga ina
dubawa, ko zan ga dan wani abin na baiwa Shadad, duk
da nasan cewa bani da komai. Shiru na yi tare da tunanin
abinda zan bashi. Rahma ta yi sallama, na amsa, ta
shigo kicin din tana cewa, "Ina Hajiyar gidan nan?" Na yi
guntun murmushi tare da cewa, "Rahma kenan, duk
tsokana kin santa." Ta ce, "Na zo shan tea din kin nan
mai kayan kamshi." Na ce, "Sai dai na baki kayan
kamshin ki je ki dafa." Ta zuba min ido cikin sanyin jiki,
sannan ta ce, "Hafsa kin 'ki daina kukanki ko?" Na ce,
"Ina kika ga ina kuka?" Ta ce, "Haba Malama, ga idonki
nan?" Ta shiga bude-bude, bata ce min kala ba ta fita.
Ina cewa, "Rahma zo ki ji." Bata juya ba ta wuce. A
zuciyata na ce Rahma kenan, ita dai ta tsani ta ganni
cikin damuwa, ina son zama da ita don ita kadai ce kan
sani murmushi. Jim kadan sai gata da kunshin kosai da
jug dauke da koko, bata min magana ba ta zuba ma
Shadad. Na ce, "Rahma koko kuka dama?" Ta zabga min
harara sannan ta ce, "Ai wallahi Hafsat kina bani haushi,
ina lura da ke duk matse-matsen da kike yi cikin satin
nan, har ta kai baki da abinda za ki ci amma ba zaki iya
tambaya ba? Ni kam ko yaushe gidan ki nake cin abinci,
saboda ina daukarki 'yar uwa ta jini." Na ce, "Rahma
dama ni dake ai babu wani bambanci duk daya ne." Tsaki
Rahma taja, sannan ta dora min dari 5 kan cinya, zan yi
magana ta ce, "In kin ce tak Allah ya isa." Da kallo na
bita har ta fita sannan na saka dariya, Rahma kenan.
Karatuna ya shiga wani hali, har ina ganin in ba wani
ikon Allah ba tsayawa zaiyi. Cikin wannan matsatsi aka
sa ranar auren Rahma da Sagir, kullum tunani na me
zanyi ma Rahma lokacin bikinta? Da dare Rahma tana
min kitso muna hira na ce, "Rahma kin san me nake
tunani?" Ta ce, "Kudin Registration?" Na ce, "A'a, so nake
ki fadi abin da zan miki lokacin biki." Cikin tsokana ta ce,
"Italian bed da leader sit." Muka sa dariya, na ce "Allah
ya hore, har kayan kicin sai na miki." Ta ce, "Ni dai
Hafsat nafi son ki bada hadin kai lokacin bikina kin ga
dai bani da wata aminiya sai ke, sauran duk kawaye ne."
Na ce, "Tabdijan! Rahma kada ki sani yin abinda ba zan
iya ba." Ta saki kaina, "Kin san Allah?" Ta nuna ni da
kibiya, "In bikina ya yi kyau ke ce in ya baci ke ce, kuma
yanzune zan san matsayina a gurinki." Na ce


Zaharaddeen Shomar
what's app 08168575100


Sanadin Boko 1-8
Posted by ANaM Dorayi on 12:13 PM, 18-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
, "Maida wukar, Allah ya kaimu. Yauwa dama ina son in
miki batun da ke raina. Ina son in samu manaja ya bani
koda rabin albashina ne in sai ma Shadad takardu." Ta
ce, "Kin san rashin mutuncin sa, abinda zai fi dai in
tambayar miki rance gurin matar Yayana." Na ce, "A'a ki
bari zan same shi in yaga dama zai yarda." Rahma ta ce,
"Hafsa kenan, ke bakya son bashi sam! Kuma ai naga
bashi hanji ne yana cikin kowa." Na yi 'yar dariya. Haka
kuwa na yi, na samu manaja da bukata sai ya ce, "Kin
cika daure fuska, da ace kina da fara'a har karin albashi
zan miki. Banda kyautukan da zaki yi ta samu a kai-a
kai." Na sake hade fuska, "Bana bukatar karin ko wata
kyauta. Hakkina kawai nake so." Ya ja tsaki, "To sai ki
jira lokacin baki hakkin ya yi, ke bazaki taba ganewa ba.
Wai me ma zakiyi da kudin?" Ban amsa shi ba har sai da
ya sake maimaita tambayar, Na ce, "Zan biya kudin
littafan makaranta ne na yaro."Ya yi tsaki, "To sai ki jira
lokacin don in kin ga na yiwa mace mutunci itama ta yi
min ne." Na mike ba tare da na sake magana, don
Manzon Allah ya ce ka fadi alkhairi ko kuma ka yi shiru,
amma na so in zabga masa ashar in ya so ya kore ni
gaba 1 daga aikin. Cikin kwanakin sai manaja ya soma
shige min, duk da dinke fuskar da nayi masa, ya zo ya
kawo min albashina wai gashi nayi bukatar da zan yi, na
ce ya barsu ai ni na ma hakura. Kwatsam! Rannan sai
naji ana buga min gida, lokacin 9 ta gota na dare, don
har na soma bacci. Na zo na bude, nayi mamakin ganin
manaja a gidanmu na ce, "Lafiya?" Ya ce, "Kalau, na zo
ne mu gaisa." Na ce, "Na gode da gaisuwa. Sai da safe."
Na juya ya ce, "Kina nufin har mun gaisa? Bai dace ki yi
min haka ba." Na ce, "Za a min fada an hanani fita." Na
fadi haka da nufin karema kaina mutunci. Ga mamakina
sai naji ya ce, "Haba yarinya, ni zaki yi wa karya? An ce
miki bansan cewa zaman kanki ki ke yi ba? Ni zaki saki
jiki ki ci arziki ki saki, in ba zaki saki ba talauci sai ya yi
ajalinki." Jikina ya yi sanyi lakwas, na maimaita kalmar
zaman kaina! Na ce, "Ni ce mai zaman kaina?" Ya ce,
"Sharri na miki? Kowa ya san ke kadai ce ba kuma a san
iyayenki ba." Ya ja tsaki tare da cewa, "Banza mara
rabo." Ya tafi.
Ranar na yi kukan da ya isheni, wato kowa ya san
zaman kaina nake? Wata zuciya ta ce, "To yanzun ai an
daina kiwon dabba mutum ake kiwo." Sai dai da mutane
zasu min adalci ya kamata su san cewa bana hulda da
maza, da ace ina da wani aikin lallai zan bar super
market din nan, sai dai bani da zabi.
Da safe duk da kirkiro fara'ar da nike yi sai da Rahma ta
gane cijewa nake yi saboda damuwar da ke raina. Ta
kafa min tambayar me ke damuna? Nanfa na fada mata,
na kara da cewa, "Dama duk mutanen unguwar nan
kallon da suke min kenan? Ina zaman kaina?" Rahma
cikin muryar lallashi ta ce, "Sam, shi dai yabi diddigi ya ji
cewa ke 1 ce anan. Amma ba maza kike tarawa ba,
kowa yana yabonki a unguwar nan don kin tsare kanki,
kuma shi ya fada hakane don takaicin bai samu abinda
yake so ba. Ki barshi da Allah." Nace, "To in ban barshi
da Allah ba yaya zan masa? Ai bani da yanda zan yi
dashi. Da ace ma ina da wani aikin barin musu wurinsu
zan yi." Rahma ta ce, "To ai ba gurinshi ba ne shima cin
arziki yake yi, don haka ba inda za ki je." Daga wannan
lokaci muka sa 'yar tsama da shi, ya bi duk ya tsane ni,
nima kuwa ya kara dasa min tsanar maza, yana son ya
ga nayi wani dan kuskure ya tozarta ni, niko duk wata
hanya da zata ja min cin mutuncin shi na 'ki sakaci da
ita, lokacin zuwa aikina baya cika nake isowa,
musamman in zuwan safe zan yi.
******** ******** *****
Munnir an kammala karatu an kuma dawo gida. Tuni ya
manta da wata Hafsa da labarinta. Ya iso gida cike da
soyayyar Mina, yarinyar wani kusa ce a gwamnati, sun
kulle ne tun a yanar gizo ta (Facebook), sun jima suna
soyayya kafin suga juna, bayan ya zo hutu itama ta dawo
daga inda take karatu, suka hadu. Sun yaba da juna, sai
dai sanin cewa ba za ayi musu aure da wuri ba suka
kazanta soyayyar su ta hanyar biyan bukatar zukatansu.
Sam! basu dauki hakan laifi ba, nasu ganin duk cikin
soyayya ne a nasarance suke koman su don boko suka
sani, shi suka iya, kuma shi suke yi. Sun dai kulla
alkawari ga junansu cewa za suyi aure in lokacin yinsa
ya zo, Allah ka shirye su shirin Addinin musulunci.
(Ameen).
¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Bikin Rahma ya gabato don haka na ciro dubu goman da
na makale na ce mata na ba da rabin kudin Registration
naje nasai mata sestin kula da jug. Dubu bakwai na
kashe, nazo na kai mata gida, batan hakan ya min dadi.
Su Mama suna ta gdy, ta ce yanda garin nan babu kudi
shi ne zaki ta wannan dawainiya har haka? Na ce Mama
ta kama ne. Da dare ina krtn Alkqur'ani,sai gata ta ce,
Yayi kyau Hafsa, ina kika samu kudin sayan kayan ban
masu tsada?Na ce Daga Sarki Allah. Ta ce, ba dai kudin
Registration din ba ne? Na ce in sune fa? Don Allah zo ki
zauna muyi batun anko. Ta ce ba zama nazo ba ki zo in
ji Sagir da wani abokinshi, ki fada musu kudin abubuwan
da zamu yi. Da karfi na ce " What? hum........ hum.....
Rahma kada ki sani cikin hulda da maza. kije kawai ki
amsa, na yarda zamu je kasuwa siyayyar tare. Zata yi
mgn na rantse mata da girman Allah cewa ba zani ba, ta
juya ba tare da ta ce kala ba. Nasan tayi fushi, amma
sam fushinta bai dame ni ba, in dai akan abin da zai sa
nayi hulda da maza ne har nai musu dry. Don ni nasha
alwashin namiji ya gama ganin hakorina. Mun je kasuwa,
duk abn da zamu bukata gurin walima mun sayi, don
Walima kadai zamu yi kayatacciya, sai dai ta ce, Sagir za
suyi (Dinner) kuma za su yi (Pink & blue day). Kullum
rokona take in je har dai na amsa mata zani. hakan ya
tilasta min siyan shadda kamfala (pink) mai ratsin
bulu,yayin da Shadad na dinka masa(blue) din shadda,
atamfar walima kuwa Rahma da kanta ta sai min.,
Bikinmu yayi kyau, komai a gidana aka yi duk da cewa
ina zuwa gurin aiki da mkrnt, kin yi wa Manaja mgn nayi
don ba zan sake yi mishi wani zance ba, ko neman wani
abu. Ranar daurin aure kam ban je makarantaba, kuma
banje aikin ba, saboda aubuwan sun kwa6e min.
Malamai sun halarci walima, sun kuma yi nasiha akan
mahimmancin yin aure tare da falalar da ke tare dashi.
Sun ja hanklin iyayen yara masu cewa su dole sai
'ya'yansu sunyi boko mai zurfi, ko sai sun kama aikin
kafin suyi aure. da cewa wannan ba koyarwa addinin
Musulunci ba ce. Suka ce, ita mace babu abinda yafi
daraja da mutunci a gare ta irin aure. Sun ce boko ba ya
hana aure, kamar yanda aure baya hana boko. In
'ya'yanku suka lalace saboda kun hana su aure sai boko,
hakika laifin zai fi ta'allaqa a kanku iyaye., Nasihar da
suke yi ta sani shiga dogon tunanin, ni kaina misalice
SANADIN BOKO gani yau na zama 'yar kaina, domin da
ace ban ce bokoba nabi zancan mahaifina nayi auran da
yaso, da yanzun ina tare da dangina da ban kashe auran
iyayena ba, da ban haifi shege ba, da maxa ba su dinga
latsa ni suna son mu lalace ba. Ban san hawaye na
sauka daga idanuna ba, sai dai hannun Rahma naji a
kumatuna tana share min tare da yi min rada a kunne.
Haba Hafsa cikin fa taro ki ke, ya ya za ki ba mutane
damar yin tunanin ke wacece? Please ki share don Allah.
Walima ta tashi lfy, na ce da Rahma bari na leka shop,
kin san ban dauki uxiri ba, ta ce min ba damuwa. Naje na
samu su Ishak, ya ce nasan kuna biki shi yasa ban tashi
ba, na fada mawa manaja cewa zan zauna madadin ki
har ku gama biki, ya kuma san auran Rahma ne shi yasa
bai ce komai ba.Ya kara da cewa, ki koma har sai kun
gama ki mata fatan alheri, mun so muzo daurin aure
amma kin san Manaja. Na ce na gode, ya ce a'a ba
komai, wata rana irin haka zata iya faruwa da mu, na
dawo nake fada ma Rahma ta ce, Ishak da Musa suna da
kirki sosai, dn dai kin kasa Fahimtarsu ne. Na ce, Ba zai
sa don sun kar6ar min aiki in sakar musu fuska ba,
gaisuwa kawai ke hada mu ko da, kuma ita zan ci gaba
da yi kadai. Anje anyo ma Rahma danki(jere) an zo ana
ta lbrn kyan gidan an ce ango ma ya zuba labulaye da
kayan wuta, Sai an kai Amarya sannnan za'ayi sauran
shagalgulan da ango suka shirya, wai ba a son mutane
suyi yawa, sai ka nuna pass sannan zaka shiga. Da muka
kai amarya unguwar Sharada, gidan kam ko ni ya min
sosai, taso in kwana na ce mata ta min hakur sai gobe in
mun hadu gurin (pink & blue day' . Ta ce don
girman Allah

Please Login or Register in order to submit comment