Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasan
uzurin da ya tare ta?" Manaja ya ce, "Yallabai yarinyar
nan bata da mutunci sam!" Ya ce, "Ko zan iya sanin
halayen ta marasa kyau?" Ya ce, "Na 1 bata da fara'a ga
kallon banza, kuma ta fi karfin kace zaka taimaka mata
sai ta hau bala'i, ina ce sakin fuska ma abu ne?" "Ni
kuma hakan ya birgeni." Abubakar ya katseshi, "Ban ga
laifinta ba, don ta kare mutuncin ta. Shi kenan sai ya
zama zubar da mutunci don bata saki fuska ba?" Manaja
ya yi 'yar dariya, "Yallabai yarinyar nan fa in ma sonta
kake ka hakura don ba zata baka hadin kai ba, in mata
kake so 'yan gayu isassu na debe kewa sai in kawo
maka su. A ina ka sauka?" Abubakar ya ce, "Na fada
maka ina son ta ne? Ko na fada maka ina son mata ne?
Inma matan nake so ai baka fini saninsu inda zan same
su ba, ina maka nasiha ne ka daina wulakanta na kasa
da kai, in dai suna yin abinda ya dace." Ya ce, "To zan
kula Yallabai -ya ci gaba da cewa- Ya hajiya? Ai mun yi
waya da ita jiya tace matake fada min kana Kano zaka
shigo ka duba abubuwan dake tafiya." Abubakar ya ce,
"Kwarai kuwa, bari in duba takardun. Fito min da su." Ya
jima sannan ya kammala ya fito, Manaja yana biye da
shi ya tsaya kusa da ni, "Ki yi hakuri kin ji ko?" Sannan
ya fita.Ni kam ban ko kallesu ba. Tunanina 1 ina ya kai
min yarona?
Lokacin tashina nayi na nufi Makarantar su Shadad na
dauke shi muka nufi gida. Tun akan hanya ya isheni da
labarin Uncle, Anty Uncle ya sai min ice-cream ya kai
min da muka yi break da su sweat, kuma ya tambayi
Auntynmu wai ina karatu? Ta ce mishi inayi sosai,
kuma ana lura dani wurin yin home work, yana ta jin
dadi. Na yi tsaki tare da cewa, "Yi min shiru." Da dare
ina Sallar Isha'i naji bugun gida, sai da na idar sannan
na nufi zauren nace wanene? Ba'ayi magana ba har
zan juya aka sake bugawa nace wanene wai? Yace
Abubakar ne. Na gane muryarshi amma sai nace, "Wa
kake nema?" Ya ce, "Shadad." Na yi shiru ina nazari,
hausawa sunce mai Da wawa, inna bar wannan
mutumin zaya fake da dana ya cutar da ni, gara in
masa rashin mutunci ko ya fita daga harkata. Na bude
kofar sannan na dogare bakin kofar, "Kai Malam! Ka
fita idona, ina ganin kimarka bana son ta kaimu ga
rabuwa fata-fata ni da kai, ina nufin in zabga maks
rashin mutunci, ka ja tsumman rayuwarka ka yi gaba,
ka fita harkar yarona, anzo za'a fake da yaro a cuceni."
Na ja tsaki tare da maida kofar garam na barshi tsaye
da leda shake da kaya.
Daga ranar ban kuma ganinshi ba, hakan ya min dadi
don haka na godewa Allah. Sai dai damuna da Shadad
keyi na kiran Uncle har da kuka. Kwana 8 bayan haka
ina ta kici-kicin girkin rana, yau lahadi sai da yamma
zan fita aiki. Tuwon shinkafa miyar alayyahu nake son
mana na gama kwashe tuwon cikin leda na zuba a kula
na samu Shadad yana home-work na ce, "Yauwa ka
zauna zanje kasuwa in dawo." Daman nakan barshi. Ya
ce, "To Anty." Ya tashi ya dauko kujerar da yake
takawa yasa sakata ta ciki.
Na nufi kasuwar don ba nisa sosai. Ban fi minti 30 ba
na dawo, sai dai me? Kofar gidan a bude, haka na nufin
Shadad ya cire sakata, a hanzarce na shiga. Takardun
shi suna gurin, takalminshi suna gurin. Kaf babu inda
ban dyba ba cikin gidan amma ban ganshi ba, da
hanzari na nufi makota duk da na san baya zuwa,,,,,
Me ke shirin faruwa da nine?
End of 1

Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 2-1
Posted by ANaM Dorayi on 05:26 PM, 18-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Duk gidan da na shiga kalmar iri daya ce,wato baya
shigowa. da hanxari na nufi gidan su maman rahma,ita
bata nan ma sai matar wansu tace min shadad bai xo
ba, na dawogida na sake duba ko'ina, rijiya a datse da
kwado, don haka ban kawo xaton ya fada ba. na dubi
takalman shi da takardun makarantarshi da yake hm
work, sai naji kuka ya kufce min. nayi-nayi,sannan na
mike na sake fitowa, wata daga cikin makotana ta same
ni tsaye kofar gida ina ta leke-leke,tace "kin ko gan shi?
nace,"a'a." cikin muryar kuka tace "ikon Allah, to ke ina
ki ka tafi ki ka bar shi?
nace,bakin kasuwa naje, kuma nakan bar fa. tace da
kin sani nan gidanmu ki ke turo shi in xa ki fita.kila
fakonki aka yi kina fita aka xo aka dauke shi, na tsura
mata ido. su wanene xa su dauke shi? tace, oho.mugu
yana nuna kanshi? aka dauki babba ma bare yaro, ke
dai wannan rayuwa tamu ba sai dai addu'a ba. nace,to
su wanene xa su fake ni?ban jira amsa ba na juya cikin
gidan,tamkar mai shirin daukan wani mataki.tace,kije
ofishi 'yan sanda ki kai rahoto,ban juyo ba kuma ban
tanka ba, a tsakar daki na zauna gwaraf,idanuna suna
ta kai kawo guraran yin 'yan tsalle-tsallen shi, naji na
fashe da kuka.
hakika wadanda suka daukar min yaron nan ba su min
adalci ba, don bani da wanda ya fishi duk fadin kano,
naci kukana ma ishi, bani da mai bani hakuri, na share
hawaye. abu tamkar wasa, sai gashi har anyi kiran
sallar azahar,jikina a mace nayi sallah,ina zaune ina
addu'a hawaye na bin kumatuna, sai naji sallamar
maman su rahma,na amsa ba tare da na share
hawayan ba. ta shigo tana cewa, hafsa kin ko ga
maigidan nawa? sabon kuka ya kufce min, cikin muryar
mai kuka nace wallahi har yanxun mama, tace na dawo
kawai sai suke fada min wai kun xo neman
shadad,hankakinki tashe.
na ko ro mata wajibin duk abubuwan da suka faru,
zama tayi rike da baki tana salati, tace lai finki ne in
gidan mu yayi nisa ki rike hannun abunki kije dashi
mana, angaya maki yanzu kaza batafi dan adam ba ne?
Wlh sai kaza ko rago yayi yawanshi han kali kwace
amma bil adam yana tafe ana cinikinsa, na sake
fashewa da kuka, nace mama tunfa bai kai haka ba ina
barinshi a gida, tace to yanxu me zaki fadawa dangin
uban shi da iyayenki? Na mai maita kalmar dangin
ibanshi? A cikin raina. Sallamar shi ne cikin murna ta
ka tseni, anty na yau mun sha yawo da uncle dina, ya
fado jikina, munje gurin wasa na hau doki da duniyar
sama, mun sha ice cream, harma muka dau hoto. Ban
bari ya sake cewa wani abuba na dagoshi na watsa
mai wani irin mahaukacin mari, ya yanke da wani ihu
sai ganin uncle din nashi mukayi a sukwane ya fado
cikin gidan. Na han kadar dashi ya fadi na bishi da
duka
maman rahama tana a a-a a, ban tsaya ba ina dukanshi
ina kuka. Shi kuwa uncle din nashi yana tsaye. Mama
cikin jin haushi ta wanka min mari, tace ke ma
haukaciyar ina ce? Za ki rufe dan wanan yaro da duka?
Na dubeta ina kuka, mama wanan yaron yana jefani
cikin damuwa, uban wanene yace yafita ba nanan
saboda ya raina ni? Uncle din shi ya sa hannu ya dauke
shi, yasa a kafada yana lalashi, shi kuwa sai tsala kuka
yake. Cikin daurewar fuska yace, nasan haka zata faru,
shi yasa ma na daukeshi ki san cewa kina kasada, ina
sone kiji halin da zaki shiga in wani yai gaba dashi saka
makon kasadar ki. Ya dubi maman rahama yace, mama
don Allah ba kasada bane tatafi ta bar yaro shi daya,
mai zai sa ba zata tafi dashi ba? Mamar rahama tace
sakarya, nima yanzu na gama yimata fada, gwara da ka
gwada mata hakan. Ni ko cikin takaici da masifa nace,
ina ruwanka da shi? Menene hadinku da zaka zo ka
dauke shi, shi shigi da kalata. Bai tankani ba, kilama
bai fahimci hausar tawa ba. Mama tace jacan sakara,
na shige daki bansani ba haushin daukar yaron nake ji
ko farin cikin dawowarshi? Mama ina ji tana cewa kayi
shuru. Kyale ta, kai kuma dana ka kyauta da kayi mata
wanan ba razanar. Shi kuwa cikin hausarsu ta filani
yola yake cewa, amma mama nikam banji dadin dukan
nan da tayi mashi ba fa, da ma ni ta buga zanfi jin
dadin hakan
don nine na buga ya bude na tafi dashi. Na motsa ranta
ne dan ta gane hakan na iya faruwa, in nace zan fada
mata da baki bazata saurareni ba. Mama tace haka ne,
ai hafsat shu‘uma ce, bayan yayi shuru, da kyar ya
mikawa mama shi. Gashi mama, don Allah ki bata
hakuri, na san cewa na taba ranta, amma fa kada ta
sake dukan shi. Mama tace kada ka damu, gulmace ta
sata dukanshi bakaga yanda ta haukace tana neman
shi tana kuka ba. Yace Allah sarki! Ban san ko nawa ya
ciro ba, naji dai yace mama ga wanan ki sai goro,
sanan na jiyo murmushi yana cewa hafsat sai anjuma
ko? Ban tamka ba mama ta shugo tana cewa, kinga
harda kudi ya bani don Allah kiyi mashi godiya. Ta
kwonto shadad a jikina, na turo baki nifa ban sanshi ba
daga bikin rahama ya liki men. Wlh na rasa yanda zan
yakice shi. Ta ce keko yarnan sai kace wace mujinta
ya mutu da kurwarki? Nifa na tambayi rahama da lilin
kin jama‘ar ki ta ke shai da mun tun rasuwar baban
wanan yaro ne gashi kunyi zaman mutunci, to banda
abinki hafsa itafa rayuwar duniya haka take kuma Allah
ya fimu sanin abinda ya dace gare mu, don haka ki
kula. Tan tahakiliki kila ya maye maki gurbin miji naki.
Nace to na fada ne ba dan na amince ba sai don kada
mama taga naki zancenta sanan ina son abar maganar
cikin tarkace kayan zakin da ya sayowa shadad ne na
ga hoton da suka dauka kala 3 sunyi kyau har wata
zuciyar tace na yaga su sai kuma wata ta gargadeni da
cewa mutumin nan bai cancaci haka a bayan idon sa
ba. In kinyi masa a gaban idonsa yanzu sai ki mutunta
hotonsa ko dan danki don haka sai na hakura na ajiye
masa. Anfi saty banji duriyar shi ba hakan yayi min dadi
shadad ne kanyi min zancen sa in na bala mashi harara
sai yayi shuru don tun da na dakeshi yake dari dari da
zancen uncle din sa. Nan na fahimci wani abu ga yaro
shi yaro dan ja a jiki ne zagi duka baya gyara yaro
janshi a jiki nuna mashi soyaya cusa mashi tsoron Allah
yi mashi nasiha tare da bashi lbr magabata. Suna tai
makawa gurin tarbiyya bana dukan shadad na fi yi
masa duk abubuwan da na lisafa amma yau daya da na
dukeshi duk ya shiga tai tayin sa. Kenan in baka yawan
dukan yaro yafi tsoron dukan
sannan ya fi jin magana. Wanan tunanin da nayi shiyaja
na sake janshi a jiki, da dadare ya gama cin abinci yayi
home work, nace ya bani lbr duk abinda ya faru a
makarantar su. Nan zan tajin wane ya iya karatu wane
ko an tada ya kasa, mun yi masa shem, nace kai fa ka
kasa ko? Yace, ina yi anty, har antyn mu tace wai nine
nafi kowa zan sake cin na 1 yanzu, nace to ka kara
kokari har a islamiyya ka dage, yace uncle yace in na
sake cin na 1 zai mun kyauta da ya so ko, uncle din shi
sai na watsar da zancen. Nayi shuru ina tunanin yanda
zanyi ga adashan da na kwasa gidan su maman
rahama dubu 20 a hannuna kudin da naci burin inyi
rigista da su, kuma ga kudin makarantar shadad, in ban
da da ba cikin satyn nan zasu koro shi, kuma ni an
kusa rufe rijista wata zuciya tace, tunda baki taba lattin
biya ba kije ki nemi alfarmar suyi maki uziri, nan gaba
sai ki basu. Don haka washegari naje naje nayi rigista
ta, har kwana 4 ba sukori shadad ba, muna home work
na ce wanan karon makarantar ku sunyi dagi amma
gobe zanje in basu hakuri kada su koreka. Yayi caraf
yace, anty an bani rasit wai na biya, ya tashi da gudu
ya nufi ja karshi yana cewa, anty yau anyi kora ma,
cikin mamaki na amshi rasit din ina dubawa, na shekara
daya aka biya nace shadad wa ya biya maka kudin
makaranta? Ya juya hannu tare da cewa ban sani ba.
Da mamaki na kwana, da safe kuwa makarantarsu
muka nufa kai tsaye bayan ya shiga aji ofishin mai
karbar kudin makarantar, muka gaisa ta ganeni, nace
shadad yazo da rasit wai an biya mashi kudin
makaranta, wanda nasan ban kawo ba
tace uncle dinshi bai fada maki zai biya ba? Na kasa
magana, tace to shine ya zo ya biya na shekara 1. Sai
sabuwar shekara zaki soma biya kudi. Da kyar na ce to
shi kenan, na fita na nufi makaranta rai na a bace. Shi
wanan habubakar din ba za ya fita hanyata ba kenan?
Shi ma yana son dole sai ya cika burinsa a kai na.
Tabdijan! Duk ranar da yasake gigin hada ido danine
zan rufe idona ne in zage shi tas, yanda zai bar
rayuwata ta huta. Abubakar lamido kyakyawan saurayi
bafulatanin jahar adamawa dan yola, tuki yake cikin na
tsuwa har ya isa gidansu tamgameme da ke bayan PZ,
ya ajiye motar a mazaunin ta, sannan ya fito cikin
takun na tsuwa ya nufi cikin gidan. Yan mata ne 2 a
wadatacen palon duk kansu 1, sai dai in ka kali
fuskarsu zaka gane daya tayi tsawon kafa ne, ta taras
da yar uwarta. Suka amsa sallamarsa, karamar ta taso
da sauri tana cewa (cikin harshen fillanci) sannu da
dawowa hamma. Ya rumgumota gefen shi cikin
harshen turanci ya ce mata. Yaya makaranta? Ta amsa
da lafiya. Babar ta dubeshi da murmushi tare da
mikewa tsaye dan girmama shi. Hamma sannu. Yace
rukayya sannu da gida, ina dada tana ciki? Suka ce eh,
tana ciki tare da baki. Ya nufi dakin shi, ummi tana rike
da hahhun shi. Ya zauna bakin gado ya dubeta. Me
kuka dafa? Tace tuwon semo da miyar kubewa danye.
Je ki kawo mun shi kuma ya tube ya dan watsa ruwa
ya tasa tuwon agabanshi amma ya kasa ci, tun lokacin
da yaga hafsat ya ganeta daga muryarta duk da girman
da tayi, bai sa ya kasa ganeta ba. Yana son sanin mai
ya faru bayan da ya barta. Ina su innarta? Ina babanta?
Me yasa ta canja daga mai tsananin wasa zuwa ma
fadaciya? Me yasa ta canja daga mai son mutane zuwa
me kin mutane? Mai yasa ta canja daga mai son tai
mako zuwa mai kin tai mako?
wata zuciyar tace ita kadaice zata baka wanan amsar.
Tunanin ya katse lokacin lokacin da yaji hannun ummi a
bayan shi, yasani ita ce dan suna mayukar shiri da ita.
A hankali ya dago kai ya dubeta, ta tsura wa fiskarshi
ido, tana da kishin yaransu kamar yanda aka san fulanin
adamawa da yola nayi, da wuya kaji sunayin wani yare
in ba nasu ba. Shi kuma abubakar ya fi mai da musu da
turanci, haka ma abban su. Tace hamma me ya faru
ne?Baka ci tuwonba kuma gashi kana ta tunani. Yayi
dan murmushi tare da cewa ummi, me kika gani ne?
Tace baka ci towon ba kuma gashi kana ta tunani. Yayi
murmushi tare da cewa ummi kenan! Gajiya nayi yau,
shiyasa kika ganni haka ya janyo tire ga banshi tare da
cewa, zauna muci. Tace nikam na koshi, kaci sai in
fitar da kayan, kuma bakin dada suntafi ta fito. Yace
to. Ya dan tsa tsakala ya ture, ummi tace hmma ni sai
nake kallon kamar ba gajiya bace, in mutun ya gaji in
yayi wanka yana cin abin ci sosai, kafin yayi bacci
gajiyar ta tafi. Ya dubeta ko? Tace, eh, yayi murmushi.
To me ke damuna? Tace, ina kallon kamar tunani
kakeyi ko? Yayi murmushi har dan sauti yafita, san nan
yace to tunanin me? Ta juya hannunta tare da cewa
oho. Ya lumshe ido. Ummi tana burgeshi yarinyar tana
saurin fahimta shi yasa suke shiri yarinyar tana sonshi
fiye da sauran yan uwanta
shi ma yana yana son yarinyar, ta katse shi gashi kana
sake yin wani tunanin? Yace tunaninki nake ummi, tace
tunanina? To me nayi? Yace saurin fahimtar ki, tayi
murmushi, to na gane cewa kana tunani kenan? Yace
eh tace to tunanin me kakeyi? Ya mike zan fada maki
amma yanzu muje wajen dada. Mahaifiyar tasu tana
kokarin kashe TV din da rukayya ke kallo tare da yin
fada cikin harshen fillanci. Na fada maki bana son
yawan kallon nan, in kin gama rubutun to kije kicin kiyi
min wanke-wanke. Zatayi magana sai ta fasa, saboda
ganin hamma. Ta mike ta nufi kicin din. Da girmamawa
ya gaida dadar su, ummi tace su ya findo sun tafi?
Yace dama sune kuka ce min baki? Da na shiga mun
gaisa ai, tace sune kuma saboda kaine suka zo. Anjuma
zamu zauna da kai in babanku ya dawo. Ya dan ware
ido, gurina? Ta nufi daki tana cewa in mun zauna
zakaji, nima na gaji. Ummi ta dube shi, hamma ka zabi
mata? Yace in na zaba kece zaki fara sani, ta ce zaku
fara fada da dada kamar yanda kukeyi da abba. Nasani
dada zatayi maka zancen aure ne, don lamido ya tarasu
da baka nan kaje kano bikin abokin ka ya mai da
hankali sosai gurin ta, suwa ya tara? Tace su faffa
dukansu, harda fafa na abuja da abba da su gogo
dukansu. Ya danyi di, tabbas ya kure kakan nasu, yau
kwana 3 da dawowar shi amma ba wanda yace mashi
komai? Yayi a jiyar xuciya me suka ce? Tace abba ya
fada dada amma bata fada mana komai va, amma dai
lalai saboda kai lamido ya hada taron, yace shi yasa
tun da na dawo abba da dada suke daure min fuska har
nayi zaton da na dade a kano ne
musalin 9 wayar shi tayi kuka, yadaga ya duba afili
yace abba. Tare da kalon hashim. Nawa zan tafi, abba
na kira na. Ya dauki wayar cikin fillanci abba ke fada
mashi yana jiransa, yace to gani nan. Yace nikam na
boni hashim gara ka bonin, in kuma baka da lfy ne ka
fada mana. Abubakar yayi dariya, kaima ka daina goyon
baya na? Yace eh, na daina tunda har da iskanci, ace
kaf dangi baka ga matar aure ba? Kowacce kace baka
so mugashi har munyi yara. Abubakar yace, in nayi
aure yan bibiyu zan haifa kaga sai in kamo ku. Ya daga
murya yana cewa, shatu na tafi. Yace to ka gaida gida.
Abubakar lamido shi ne da na farko a gurin ma haifiyar
shi, hajiya fatima wada suke kira da (dada) da alhaji
ibirahim lamido wanda suke kira abba. Duk wanda yake
garin yola yasan lamido abubakar (family) saboda
dukiyarsu da kuma akidarsu ta kin auran bare. Suna da
yawa matuka, sam basa son su bada yayan su waje
kokuma dan su ya auro, basu taba ba tun kaka da
kakanni, haka suke har yau. Lamido yana da yaya
kusan 30 da yankai, maza da mata. Matan sa 4 ne,
kuma dukansu dangin shi ne alhaji ibrahim shi ne da na
3 gurin mahaifiyar su gogwal, wace itace matar farko,
haka shine wanda ya fara yin kudi fiye da mahaifin su
kafin kanansa su biyo baya. Lamido abubakar sarkine a
wancan lokacin, mai fada aji, kafin ya sauka ya ba
baban danshi sa‘a du maifin hashim. Lamido yanada
tsutsuran ra‘ayi a kan auren waje, duk yayanshi maza
saidai yace shirya kaje wajen wance yar baffanka ko
yar gogonka, inko macece sai dai yace wane zai zo ki
shirya
ko jikokinsa haka ne abbukar su 7 ne gurin
mahaifinsu,usman ke bin sa, sai umar, sai aiyu sai
kasim, sanna rukayya sai auta hauwa'u, sunan gogwal
ta ci suna ce mata ummi. shi ko abbukar sunan
mahaifin lamido yaci, kakan babanshi kenan, shi yasa
lamido ke san shi duk cikin jikokinsa yafi son baban shi
abbukar kaf family hammam suke kiran abbukar don
girmamawa. yana da wani irin kwarjini mai ban mamaki
ga farin jini kowa na son shi, bugu da kari ya taso
hannun shi sake, ma'ana yana da yawan kyauta. ya
sanka bai sanka ba in yana da shi xa ya baka, shi yasa
kawunan shi da goggonin sa su yafendon sa har su
baffan shi kowa na son hama ya auri yarsa. su kan su
yanmatan cikin family suna son sa, wasu har sun yi
masa maganar, wasu sun aiko amma baice ma kowa
kala ba. abbukar mutum ne da yake tsayiwa kan
ra'ayinsa, a tsarinsa baya sha'awar macen da xata ce
tana son shi, yafi son yaga mace da kansa yace yana
sonta, matsalar shi duk cikar family bai ga wadda ta
mishi ba, duk kuwa da kyawun yanmatan
yana cikin maxan da kyau baya tsarin shi. a yanxu haka
yana da (mastets digree) a fannin kasuwanci, yana jan
kamfanonin abban su ne yayin da abban ke hutawa,
tun kusan shekaru 7 bay, lamido ke zaba mishi
yanmata yana cewa sai yayi master xaya yi aure. a
tarihin gidan su shi ne da na farko wanda ya karya
dokar lamido, ya ki yi aure a lokacin da ya bukata,
bayan ya kammala karatu ya soma aiki.lamido ya kira
shi yace mishi abbana, ina son ka shiga da kanka gidan
baffanninka da ggonninka ka duba mata, in ma da xan
zaba maka da kaina sai in ce kaje gidan baffanka na
abj yaransa suna da kyau.
Abubakar ya dubi kakansa, lamido nifa ba mai kyau
nake so ba, kaikam sakarai ne saikace ba dan boko ba?
Kowa yana son mace mai kyau, yace ban da ni, akwai
wasu halaye danake son matata ta kasance dasu, a dan
bani dama in tantance. Lamido yace to ubana, na baka
wata 2 lokaci ishashe ya isheka kayi duk bin cikenka,
abubakar yace na gode. Wata 2 har da saty 2 lanido
yaji abubakar shuru, dan haka sai yasake aikowa ayi
mashi kinran abubakar, wanda ya kasance cikin wanan
kiran a kowanne lokacin. Abin da ya kudirta shine ba za
ta taba kai kanshi gurin lamido ba, har sai lokacin da
ya kirashi. Ba yan salan isha‘i ne ya sami lamido a
gidan shi, cikin falonshi mai tsari irin na masu kudin da,
duk da haryanzu a kwai kudin bai damu da canja tsarin
falon ba, don ya masa. Ya zauna tare da gaida lamido,
sannan ya sunkuyar da kai, lamido yace cikin yar
tsokana, abba na nasan kana da kara ko da ka zaba
mace ba zaka iya zuwa gabana ka fada ba. To dan
matso ka fada mun gidan wa kaga matarka? Wacece
tayi sa‘ar samun namijin duniya kamarka? Abubakar ya
lumshe ido sanan ya sunkuyar da kai yace, gaskiya
lamido saboda aiyuka bansamu zuwa ko ina ba. Fuskar
lamido ya canja daga fara‘a zuwa daurewa. Sannan
yace duk tsawon lokacin nan bakaje ka aiwatar da
abinda muka zanta da kai ba, don baka dauki abun da
muhim manci ba? Yace, a a yanayin aiki ne. Lamido
yace yayi kyau yau wace rana? Abubakar yace alhamis,
yace to gobe in an taso sallar juma‘a ka kira hashimu
kuzo ina nemanku.

Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 2-2
Posted by ANaM Dorayi on 05:46 AM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Abubakar yace to. Lamido yace tashi kaje, bai amsa sai
anjuman da abubakar yace masa ba. Duk da abubakar na
sane yaku ma dawo gida daga ofis, bayan salar juma‘a
sai ya kishin gida har dan bacci ya soma daukar shi,
sannan yaki kiran hashim ya fada mashi kamar daga
sama sai yaji an doki kafadar sa,
ya bude ido yaga hashim tsaye, yace har ka iso?
Hashim yace na iso ina? Ka fada min ne? Yanzu lamido
ya kira wayata yace ya yajimu shuru. Nace me yafaru?
Yace baka famun yana neman mu ba. Na kareka nace
ka fada min, nace na mantal yace ya bamu minti 20.
Abubakar yace kanme zakayi karya? Kawai kace masa
ban fada maka ba. Hashim yace tashi dai muje, amma
bari ka canja kaya, ya bude duriwar manyan kaya ya
ciro masa shadda waganbari bowa mai kalan sararin
samaniya. Hula baka minister, ta kalmi baki, yace tashi
dan Allah fadan lamido bashi da kyau, tunda in ya tashi
sai ya fara cin uban iyayen mu kafin ya dawo kan mu.
Abubakar ya soma sa kaya yana cewa, ni nifa kasan
Allah? Eh inji hashim, babu mai min auren dole. Sai irin
matar da tai min, mace 1 nakeso a rayuwata, kuma sai
na zabi duk wadda ta hada duk irin halayen da nake
son don bana son inyi mata 2 ko 3, 1 nan ta isheni.
Hashim yayi dariya, sanan yace niko har na hango
wace zan kara da ita fatana Allah karyasa lamido yace
wajenta zamuje. Abubakar ya dube shi kana nufin wai
lamido zai ce min in je gurin wata ne? Hashin yace
kaima ka sani, domin in baka manta ba juma‘a kamar
haka yace kasameni muje gunsa, mukaje yace muwuce
wirin shatu. Kana nufin munfika biyaya ne? Kada ka
manta mahaifiyar ka da a haifin ka yar mace da dan
namiji suke, kuma suma hadin ne. Abubakar yace duk
ina sane, hasim kanayi kamar baka san ABUBAAR
SADDIK ba, zaku sha mamakin zuri‘ata tashi muje
Hashim ya mike tare da ajiye kwalbar turaren da ya
kara fesawa a mazauninta.
Duk suna zaune gaban Lamido, wanda fuskarsa ke
take, yace Hashimu kuje gidan Baffanku Adamu, 'yan
matan gidan guda biyu ne, ka zabi daya da kanka ina
jiranku bayan sallar isha'I".
Hashim yace to, mun gode. Sai mun dawo. Suna mota
Hashim na tuki, Abubakar yana ta son tuna 'yan matan
gidan Baffa Adamu. Anya ya san su ma?
Hashim ya katse masa tunani da cewa, "Kai duk ruwan
idonka saika zabi daya daga cikin yaran gidan Baffa
Adamu." Abubakar yace ba dole bane su min. Hashim
yace Allah yasa kada ka canki wadda nake hari."
Tsaki Abubakar yaja, sannan yace tun kana yaro zaka
tara ma kanka gajiya, ka hada mata suyi ta maka
rigima kullum kuna fada Lamido, gashi kai ba dama ka
saki wata duk danginka irin gidan Yaya Sule gida sai
kace sansanin yaki."
Hashim yayi dariya harda dukan sitiyari, sannan ya ce
ni nan sai na gaji Lamido hudu nan sai na hada, Allah
ya taimaka inji Abubakar.
A

Please Login or Register in order to submit comment