Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita suka hadu da Hashim, yake gaya
masa yadda suka yi da Dada, ya ce, "Kaima ka yi laifi,
kana so ka jawowa Hafsa tsana a dangi ko? Ka bari kaga
iya gudun ruwansu, ai sun san komai a kai." Ya ce, "To
shikenan to!!"
Tabbas familyn Lamido auren farko yi maka za'a yi, in
kuma ka cika zakewa yanzu za'a ce maka rashin kunya,
balle Hamma da yayi fice tunda ya dauka 'yar waje
(bare).
Bayan sun gama magana da Hashim, yana kashewa sai
yaga text din, ya bude ya duba ya ja tsaki, ya mike ya
zauna bakin gadon tare da dauko wayarshi, nan take ya
ga ya dace ya bata amsa don haka ya rubuta cewa, "Ban
damu ki soni ba, asiri fa zan rufa miki, in bani ba dinma
wa zai auri 'yar gagara? Zancen aiki kuwa, kya iya
komawa, baki ji maganar Iyayenki ba ni zaki ji tawa? Kya
iyayin duk abin da kike so tunda kina da 'yanci, barikin
kenan."Lokacin da sakon ya shigo wayata kuka na saka,
Mijin da zan aura ke fadamin haka? Na kira Rahma ina
kuka wiwi na fada mata komai, ta ce, "Ki yi hakuri zan
kirashi." Na ce, "Kada ki yi masa magana, illa kawai ana
daura aure zan kama gabana." Rahma ta ce, "Ki yi hakuri
ina nan zuwa." Su da Sagir suka zo da dare, lokacin na
idar da Sallar Isha'i kenan, Shadad yana kwance kusa da
ni, ko abinci na kasa ci. Suka yi sallama na amsa, suka
zauna Rahma ta ce, "Wai mai ya faru?" Na ce, "Rahma
duba text din nan." Na mika mata wayar ta karanta, tana
gamawa sannan ta mikawa Sagir, shima ya ce, "Ki yi
hakuri, wallahi ni nasan Abubakar yana sonki, kiran kanki
Karuwa da kika yi shine silar fushinsa." Rahma ta ce,
"Kuma yaki ya saurari kowa ya ji yanda abubuwa suka
faru." Na ce, "Ni dai gudu zanyi matsawar aka ce yau
shine mijina, duk da cewa nasan ina son shi." Sagir ya
ce, "In kin gudu me Iyayenki zasu dauka? Wace rayuwa
zaki samu a gaba? Kuma zaki sake samun wanda kike so
kamar shi? Duk wadannan tambayoyin ya kamata ki yiwa
kanki su, sannan ki amsa su duka."
Na fashe da kuka, bani da zabin da ya wuce hakuri,
domin Sagir gaskiya ya fada min, Allah ka shige min
gaba. Rahma ta ce, "Ya zo ne akan batun wane irin
shagali zamu yi saboda katin da za'a bugo, na san dai
baki wuce Walima ba shiya sa na fada masa haka." Na
ce, "Wa na sani da za'a buga kati? Ni walimar ma ba
zanyi ba." Rahma ta ce, "Ka jita ko? Shiya sa nake ta
gaban kaina, na san ba zata bada hadin kai ba." Sagir ya
ce, "Yanzu dai Hafsa a shawarce ki zuba mana ido, naki
bine kawai." Na ce, "A'a, kun zo da abinda ya sabama
shari'a ba zan baku goyon baya ba." Suka yi dariya, haka
suka yita lallashina tare da kare Abubakar har dai na
danji sanyi suka tafi, bayan Rahma ta yi delete din text.
Ana saura kwana 10 biki, danginsa suka nufi Kaduna da
lefe, saitin akwati mai 5 dauke da kaya masu tsadar
gaske, Goggonninsa sunyi mamaki gadin gidan da
Abubakar ya nemo aure takalawa ne lis, sai dai an
karbesu cikin karamci, da kayan abinci da nasha masu
kyau wanda Murja Matar Yaya Umar ta yo. Dakin Baba
aka share aka shimfida darduma, bayan sun ci sun sha
sukai sallah, sannan aka bude kaya. Matan gidan suka
shigo sunata yabawa saboda irin wannan kaya haka,
daya daga cikin 'yan kawo kaya ta ce, "Ina amaryar
ne?" Baaba ta ce, "Tana can Kano tana karatu a can."
Umar ya kawo dubu 10 na tukuici tare da cewa su yi
hakuri sun gode. Ko da suka dawo sun ce an karbesu
hannu bibbiyu, kuma suna da karamci Iyayenta sai dai
talakawa ne lis. Dada ta ce, "Shi dai ya sani kuma ya
jiyo." Waya Rahma ta kira Sa'adatu ta makarantarmu,
take gaya mata batun aurena yadda zasu shirya,
sannan ta ce don Allah gobe zata zo har makaranta ta
bata kati dan ta rabawa kawayenta. Sa'adatu ta ce,
"Allah ya kaimu." Rahma ta dubeni ta ce, "Kin ga illar
kin shiga jama'a, wallahi ki canja hali, dan family din da
zaki shiga suna da yawa." ......


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100



Sanadin Boko 3-05
Posted by ANaM Dorayi on 05:56 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Abubakar ya zo gurin Rahma ya kawo mata katin biki da
duk wani abu da zamu bukata, sai hotuna da yace ta
bashi dan can dangin sun matsa a kawo hotuna saboda
suna son kalanda da memo. Rahma ta kirani a wata ta
ce na shirya zan rakata gidan Matar kwamishinan ilmi, ta
ce pls na kure adaka saboda sutura itace mutum. Ban
kawo komai a raina ba, na ci kwalliya na saka after dress
akai, ita ce da kanta ta ja motar tare da yi mata tsiwar
cewar har kin kware da zaki cire (L) din? Ta ce,
"Hannuna ya fada kinsanni da karambani." Muka tsaya
wani gidan hoto mai kyau, anan ta ce min, "Hoto zamu
karba ki shigo." Naje wajen hoton muka shiga, Rahma ta
je tai magana da wani mai hoto na ga suna magana
amma ban san me suke cewa ba, na dai tsaya a ciki. Da
ta zo na ce mata, "Ina hoton?" Sai ta ce, "Wai sun kone
sai dai a sake wani." Ina zaune gefe aka yi mata wajen
kala 5, ya nuna mata ta ce yayi. Ya ce to nifa? Ta ce,
"A'a, Hafsa ai ita bata hoto." Ya ce, "To shike nan." Na
ce, "In gani Rahma." Ta ce, a'a ba zan gani ba, muka
zauna zaman jiran karba, akai editin dinshi na ce, ka
wanke mai kyau sosai fa. Muka karba muka fito. Muna
hanya na ce, "Ina gidan Kwamishinan?" Ta ce, "Daman
hoto ne, nasan idan nace miki ki raka ni ba zaki ba." Na
ja tsaki tare da cewa, "To kai ni gida."
Bayan la'asar lis ina duba wani littafin masu fasaha
wanda yake burgeni na Ikilima, Shadad na gidan Mama
na tura shi dan in nutsu ina son in samu wani abu da
zan karu da shi cikin halayen Ikilima. Duk da ciki-ciki
ya yi sallamar sai da kunnena ya dauko daddadar
muryarsa, hannunsa rike da Shadad, na dan kauda
kaina na ci gaba da duba littafin dun da na kasa
fahimtar komai a cikinsa. Shadad ya rugo yana cewa,
"Aunty ga Uncle." Na ture shi tare da cewa, "Waye
haka? Da Allah ni matsa can." Ya bata fuska, "Aunty kin
ganshi nan fa." Don kada Shadad ya fahimci wani abu
sai na ce, "Sannu da zuwa." Bai amsaba sai ya bata
fuska tare da tabe baki, "Na zo ne kawai in ganki, tunda
kina lafiya shikenan ni na tafi." Ban motsa daga inda
nake ba na ce, "A gaishe su."Ya ciro kudi ya bawa
Shadad, "Je ka zauna sai na dawo." Ya ce, "In ka dawo
zaka tafi da ni?" Ya ce, "Sai kayi hutu." Ya juya ya fita,
na bishi da kallo hatta tafiyarshi ta lafiyayyun maza ne,
komai nashi birgeni yake yi. Daidai soron ya juyo
idanunmu suka kalli juna har ciki, ya zare nashi idanun
ya kalli gabanshi, sannan ya bude kofar ya fita. Na
lumshe ido tare da shakar kamshinsa, tsam! Na mike
na nufi kofa ina leken shi, ya mike da nufin fita daga
layin ina zaton ba da mota ya zoba, na bude kofar ina
lekenshi har sai da na dena ganinshi.
Shadad na samu yayi wada-wada da kudin da ya bashi,
'yan dari 2-2 ne guda goma, na kwashe su na koma
daki na zauna bakin gado ina tunani, damuwa ta ban
san zaman da zamu yi ba.
Cikin kwanakin shagali na karatowa kuma karatuna na
kara daukar zafi, don mun kusa mu fara
Jarabawa.Rahma ke shirya komai na game da walima,
ana gobe daurin aure na dawo Makaranta wujiga-
wujiga, na iske gidana dam da jama'a. Rahma ce da
makota har da dangin mijinta suna ta aiki, wasu na
wankin naman kaji, wasu na wankin kayan miya. Turus!
Na yi yayinda makota suka soma fadin ga AMARSU,
guntun murmushi nayi tare da gaishe shi sannan na
shige daki, a zuciyata na ce, "Kai su Rahma da karfin
hali." Ita kuma sai hada murhu take yi. Ta zo daki ta
sameni, "Don Allah kada ki nuna fushi ko wata alama
da za'a gane da wata matsala." Na ce, "Wai ni duk ba
wadannan ba, a ina kika samu kudin yin wannan
shagalin?" Ta ce, "Daga taskar ango." Na ce, "Shagali,
Allah ya baku sa'a."Dazu Inna ta kirani tace min tun
jiya suna Kaduna ita da danginta, tace min ya kamata
na taho." Rahma ta ce, "Mama ta ce gaskiya can ya
kamata a tafi, to sai dai mu bar walimar sai ranar
lahadi, ko me kika gani?" Na ce, "To ni dai gobe
sammako zan yi." Kafin dare an gama suyar kaji an yi
miya, duk ta ba wadanda suka tayata aiki.
Da duku-duku muka gama shiri ni da Shadad, sai ga
Rahma da direbansu, Mama ma ta shirya, Rahma ta ce,
"A dibi naman da drink a tafi da su ko?" Na ce duk
yanda ta gani, tunda kajin da yawa, sai ta debo sosai,
goma daidai muna Kaduna.Allah Sarki Baaba! Ashe har
anko suka fitar, gidan cike yake da mutane ban zaci
ganin haka ba, ashe Baaba gayya ta yo, dakin Baba nan
Inna ta sauka da danginta, na ji kunyar ganin 'yan
uwanta, amma ganin basu nuna komai ba sai na saki
jikina, suka gaisa da Mama, Baaba ta shigo muka gaisa,
ta ce, "Ga fa abincin 'yan daurin aure can nasa a dafo
shi a gidan wata mata da ke yin na kudi." Baaba ta ce,
"Ko ko za'a sayo 'yan holokon nan ne da dan cokali na
robar nan a zuzzuba a ciki?" Na ce, "Oho." Rahma ta
mike, "Baaba kin tambayi wannan ita dake jin haushi
sai kace wadda za'a yiwa auren dole? Bari inga
abincini." Suka tafi. Inna ta ce da Mama, "Baiwar Allah
nan tana kokari, Allah ya saka mata da alheri." Su
Mama suka ce Amin.
Rahma ta dawo tana cewa, "Abinci yayi kyau, ta zuba
wadatattun kayan lambu, yanzu bari a dauko naman
nan a zuba a kai, na bada kudin take away din." Nan
suka zuba abincin da naman kaji, ga drinks, Innarmu ta
ce, "To shi Babanku kinje kun gaisa?" Na ce, "A'a." Ta
ce, "Yana dakin Malam Garba ki je." Nan na fita,
Shadad ya biyoni na rike masa hannu, ina jin lokacin da
wasu ke cewa, "Hala wannan shine dan nata?" Ban
damu da in juya inga ko su waye ba, na fita.
Mun gaida da Baba, ya dauki Shadad tare da cewa,
"Muhammadun ne wannan?" Na ce, "Shine." Ya ce, "To
Allah ya yi masa albarka." 'Yan daurin aure sun zo
ance nan suka kwana gidan aminin waliyyinsa ko?" Na
ce, "Eh." Duk da ban sani ba, ya ce, "To Hafsatu, ke
dai ba kankanuwar yarinya ba ce, Allah ya kawomu
lokacin auranki, don Allah kiyi hakuri ki zauna da Mijinki
lafiya tare da ladabi da biyayya, ni dai in kin min haka
kin gama min komai." Yayi mata nasiha sosai, ya ce,
"To Alhamdulillah, Yayanki Umar shine ya sai miki gado
da kujeru daidai karfinsa, Baabarku kuma ita ce ta sayi
duk abinda aka dafa, sadakinshi da shi aka sai miki
katifa da fuloli. Sai dai Innarki da tace ta zo da kudi sai
kin zo za'a shawarceki, nima ta gefena dangi sun zo
daga Maiduguri sun bani gudummawa dubu goma ce na
ba Umar." Na ce, "Oh Allah! Mai rufawa bawa asiri,
Allah ya saka da alheri." Ya ce, "Amin, Allah ya baku
zaman lafiya." Na dawo gida na bar Shadad gurin Baba,
Innarmu ta ce, "Ya miki bayanin komai ko?" Na ce,
"Eh." Ta ce, "To ni nan gurina kawunanki da sauran
dangi sun hada dubu hamsin, ni kuma nayi adashi na
dauki na dubu sittin, sai na bada hamsin, goma kuwa
na basu Ummi saboda anko da suka ce tunda Yayanki
hidima ta masa yawa.Sannan ta ce, "Shi kuma Babansu
Rabi'u (mijinta kenan) ya bada dubu hamsin, nan dubu
dari da hamsin kenan gaba daya sai asan yadda za'a yi
da su." Na ce, "Ni dai Inna duk yanda kuka yi daidai
ne." Muryata ta soma rawa zanyi kuka, "Ban zaci zaku
kula ni kumin wannan gatan ba, dan na riga na watsa
muku kasa a ido." Kanwar Innarmu ta ce, "To komai ya
wuce Hafsat." Innarmu ta ce, "Kayan kicin zaku je ke
da Rahma kasuwa ku sayo yanzu tunda an ce ana
gama daurin aure zaku wuce da kayanki." Na ce, "Da
an sani ba'a sai kayan anan ba, don tafiya yola da kaya
aiki ne, in naje can a siya." Inna ta ce suma sai da aka
siya sannan suka zo, amma an ce su zo da motar dibar
kaya, dan Umar ya fada ma angon cewa su zo da ita.
Na ce, "To yanzun me za'a siyo?" Ta ce, "Ke kika san
abinda ya kamata." Na ce, "Tab, to ni ai bani ma da
komai tunda Karatu nake yi banyi tunanin auren nan
kusa ba." Ta miko min kudin nace Rahma ta karba.
Mun fito zamu tafi muka ga Sakina kanwata 'yar wajen
Baaba nace ta zo mu tafi. Muka je a motar Rahma nan
kasuwar bacci, na sai kayayyaki su TV da kayan
kitchen duk na amfanina da su blender da sauransu.
Mun kashe dubu chasa'in, ragowar kudn na sai kayan
gara dan ma Inna ta yi cincin, dubulan da alkaki.
Muka sai shinkafa buhu 2, taliya 3, semi 4 manyan
galan na manja da na man gyada 2-2. Nan dai muka
kashe kudi, sannan muka nufi gida. Mun samu ana loda
kaya wai motar kaya zata yi gaba, don haka Rahma
tace ma Yaya Umar ga wasu a saka a tafi da su. Ya ji
dadin ganin garar da nayi ya ce, "Dama ita yake ta
tunani ina zaya samu kudi ya saya?" Ni kam na shige
gida guri tunda ya soma cika.Misalin karfe biyu aka
daura aurenmu da Abubakar, lokacin da wata marokiya
ta shigo tana rangada guda, jikina yayi sanyi lakwas,
yau na zama matar aure, sai dai nayi missing din
al'adunmu, kamar sa lalle, kamu, ko fulawa ba'a zana
min ba bare gyaran kai. Na watsa ruwa na zo na zira
Jallabiyyar cikin akwatin da mayafinta. Rahma ta zo ta
sani sai da nayi kwalliya na shafa turare, sannan ta
taya ni na zabi sarka da 'yan kunne da abin hannu
zuwa zobuna, nan take na yi kyau. Jallabiyyar ta sha
ado. Ta ce, "Ki zo ku gaisa da su Hashim da Sagir za
suyi Yola, mu sai gobe da Asubahi. Kinge kenan muna
da lokaci yau da yamma sai muje muyi gyaran kai tare
da yin fulawa.Na ce, "Ke nifa in dai da Abubakar ba zan
fita ba don kada ya yarfani a cikin mutane." Ta ce,
"Suna wani shago can da Umar ya kaisu, suna cin
abinci." Muka nufi shagon gurin su Hashim, Abubakar
bai zo ba Sagir ya soma min tsiya, "Gata ango, gata
Ango, cancadin shagali." Hashim ya ce, "Yi ma Umar
waya ya turo mana mai hoton nan dole Ango ya ga
hoton wannan shiga, sai kace Balarabiyar Sudan Masha
Allah!" Na ce, "Kuna dai zagi na ne, kuma na gode."
Muka gaisa Hashim ya ce, "Baffanmu sun tafi don Jirgi
zasu bi mu kuma da ku Asubanci zamu yi." Na ce,
"Gaskiya mun fa shirya Walima a Kano." Rahma ta ce,
"To sai dai randa kika dawo kuyi." Na dubi Rahma,
"Gobe zamu bar Yola ko? Don ina son yin karatu nan da
kwana goma zamu fara zana Jarabawa." Hashim ya ce,
"Ture batun komawa Kano gobe don Yola goben ne
zamu soma namu biki." Sagir ya ce, "Mu ma sai an
gama biki zamu wuce, na fada gurin aikina." Na ce,
"Um!" Tunani na daya ban dinka komai ba, waton bani
da sabon kaya, Rahma ma tayi wannan tunanin, amma
bata ce komai ba lokacin wayar Hashim ta yi ruri ya
daga kawai sai na ji ya ce, "Yawwa Munnir, ka shigo
layin? In ka shigo layi na 3 din muna nan a wani shago
jikin masallaci." Tsigar jikina ta soma tashi, kafafuwana
suka yi rauni har na kasa rike kaina, na jingina da
bango. Duk sakamakon sunan da naji an kira "Munir."
Duk da bani da tabbacin akan cewa wanda na sani din
ne.
Ban ankara ba na ji muryarshi a kofar shagon yana
sallama, numfashina ya yi sama da kyar na kwato shi,
yana shigowa gurinmu ya soma jeho idanu shima
mutuwar tsaye ya yi yayin da muka kalli juna ido cikin
ido.Hashim da bai kula ba fadi yake, "Abinda ka
makara, tuni an daura auren." Sam Munnir ya kasa
kauda kanshi daga dubana, ban san nufin kallonshi
gareni ba, amma ni kallon tsana ce da kiyayya mai
tsanani nake masa, zuciyata ta shiga fadi min cewa,
"Tashi ki shake shi, wanke shi da mari." Tsam na mike
na fice a fusace, Hashim ya ce, "Zo mana Hafsat
lafiya?" Rahma ta mike ta kwala min kira, "Hafsat!
Hafsat!" Sam ban saurara ba ko ganin gabana bana yi,
da ganin Munir gara ganin mai daukar raina. Na share
zufa bayan na zauna, sam ban ji me su Innu suka cewa
ba, ashe wai ina ta tsallake mutane ina wucewa.Rahma
ta zauna tana tmbyata "menene? sai alkcn hawaye
suka soma sin tiri akan fuskata. ckin kunnena tasa tana
cewa shine baban shadad ko? naji sunansa munir tunda
hashim ya ambata" Ban tanka taba, sai da nayi kukana
ma'ishi, tun mutan dakin suna tmbyata har suka hkra.
Rahma tace, fada min idan shine' nace shine me zaki
masa? ta mike nace koma ki zauna" tare da riko ta. Na
sauke numfashi Rahma barshi, abu daya nake son san
menene dangantakarsu da abbkr? indai yan uwane to fa
in sama da kasa zasu hadu ba zan zauna da shi ba,
Rahma tace daina msalin nan babu kyau yanzun ki bari
zan kirasu gashim anjima Na ce ki barsu kawai zan
bncika a sannu, sukam su sagr mamakin hafsa ne ya
cika su,sai dai shi hashim ya zargi wani abu.Lallai
shadad yana matukar kama da munir ya dubi munir
wanda ya kasa zaunawa yace zauna mana ranka ya
dade, ga abnci, munir ya zauna bayan ya ciro hankici
yana share zufa,sagr ya mika masa hannu suka gaisa,
haka ma hshm. Nan dai suka juya hira,ya nuna sagr
"wannan ne angon? Hashim yace a'a yana yola, kasan
na fada maka mata 2 zaya aura. shadad na rike a
hannun yaya umar, dawowarsu kenan daga gdan yaya
umar din. yace kawu bari in je gurin antyna, tana can
dakin? umar yace "Ehh don shigarsu dakin ne yAya
umar ya fita shi da shadad sai yanzu suka dawo. ya
shiga da sallama jikin sagr ya nufa yana me fadin Uncle
ina antyna? sagr yace tana gda. munir ya tsurama
yaron ido,gabanshi yana wata irn faduwa ya bi yaron da
ido lkcn da yaron ya fita a guje. tamkar ya cafko yaron
yakeji don ya sake kallonshi da kyau,ko kuma duk cikn
firgicin ganin hafsa din ne? ya mike cikin tashin
hnkali,yace to Hashim Allah yasanya alkhairi, nizan tafi.
Hashim yace da sauri? munir yace em inada dan wani
uzurine, suna fita yi masa rakiya sai waiwaye2 yake,ya
shiga motarsa ya tada tafe yake yana zantuka shi
kadai, tmbayr kansa yake" shon wannan yaron mai
matukar kama da shi dan hafsa ne? cikin sane kenan
ta haifa?a fili yace lallai zan amshi dana dubi yanda
kaunarsa ta zirga ckin jinina,amma kuma.... ya doki kan
styarin motar tare da cwa tab nasan za'ayi
rigima,yanxun wama zan tunkara da wannan magnar?
tunda iyayena ba wanda yasan zancen? ko gdansa
yakasa zaune da tsaye,duk ya damu gashi badama ya
fadawa matarsa. sai dai ya yanke shawarar dadynsu da
zancen, Nikam ban da tursasawar Rahma bazan yi wani
lalle ba,amma haka tasa sakinarmu da ummi suka
nemo mai zanen fulawa ta yarfa min a hannuwa. tasiyo
man shamfo sbd anwuce da akwatunana (lefa) dama
kayan dangi daban suka kawo wai suddaje. don haka
ba'a taba nawa ba,tayi min don tayi tayi nace bazani
saloon ba, na manta da wani abn takaicin da rahma
tamini tarkacen mata ne wai sai nasha.
Nace matama gwara takwashe tarkacenta inba hakaba
zatayi asarar kudinta, don zubarwa zayi, tace gashinan
cikin jakata in naso naje nazubar, inkuma na shirya sha
to inkirata taimin bayani yadda ake amfani dasu, nace
kanki akeji, gdan yaya umar mukaje kwana, sam na
kasa bacci, gaskia bansoba naga munnir sai naji nakara
tsanar maza, Allah ya sani indai dan'uwan abkr ne toba
zan zauna cikin zuri'arsuba, ke amarya tashin manta
doguwar tafia ke garemu? Wanka kawai nayi don ina
fashin sallah, na kintsa jikina sosai muka fita tare dasu
ya umar, ummi da matar ya umar duk tare zamu tafi
dasu, dangin inna duk tare muka tafi dasu, nida
sakeena da rahma a motar hashim da sagir, harda
shadad aka tafi, lallai yola akwai nisa, tun muna tafia
ina hira har nai bacci dan bantaba doguwar tafia irin
hakaba, bamu isaba sai gaf da magrib, tunda karfe 6 na
safe, kuma wai haka dinma sai naji ana cewa munyi
sauri, dankareren gate ne muka dosa, sai kace na gdan
yari, muna shiga gdan dam da mutane haske ko'ina,
mayafi naja na rufe fuskata, lkcn naji gdan yadauki
guda anata fadin gasu nan sun iso, rahma ce take
rungume dani, har zuwa kofar shiga tace, kishiga da
kafar dama kiyi addu'a, hakan nayi, sannan aka zarce
dani can dakin, nan da nan zugar dangin suka cika
falon, har dakin da nake, sai fillanci ke tashi,
daidaikune suke mgn da hausa irin wadda bata goge
din nanba. wata ta duko kaina, amarya bude fuskarki
muganki, ke kam wane irin kyaune dake har hamma
yafita hayyacinsa danke? Na sake sunne kaina cikin
cinyoyina, wata tace, nana ke kam baki ganta acikin
hotunan kalanda ba? Tace nagani, sonake inganta afili,
rahma tace, sai kingaji da ganinta, tunda nan zamu bar
muku ita, ankawo kulolin abinci, shinkafa da miya da
nama, sai kunun gyada da sauran drinks, suka dan rage
nan muka shiga cin abinci, nikam wanka na mike zanyi,
bayina acikin dakina yamin kyau, nafito na zura kayan
bacci, sukuma suka shiga sallah, rahma tace, shine
zakisa kayan bacci? Nace ina naga sabon dinki,
tsofaffinma banzo dasuba, na saka katon hijabi, sukuma
cikin daren nan suka hau yin jeren dakina, sun saka
kujeru a falo ina juyosu suna tababa, anan za'asa, anan
zaifi kyau, suka dawo daki suka hada gado, suka dibi
na kicin sukaje suka jera wanda shima kenan falon,
matsayina na yar talaka amma iyayena sunyi kokaro,
suka hau gado suka kwanta nikuma nakwanta kan kafet
dan nasaba da kwanan kasa, rahma tazo kusa dani
takwanta, sai wayarta tashiga ruri, nace to masoya ga
angonki nan, ta fito da wayar tana cewa, yanzun nanfa
muka gama dashi, kurum sai naji tana cewa,
ango_ango, munyi fushima, baka kira ba muna hanya,
mun iso tuni ka sharemu, ina jiyo muryarshi .......


Zaharaddeen shomar
whatsapp 08168575100



Sanadin Boko 3-06
Posted by ANaM Dorayi on 05:57 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
yana cewa, ai munata yin waya dasu sagir, sun tabbar
min kuna lfy, na tabe baki yace, to yaya kuke? Tace lfy,
mungama shirya muku komai, gobe asubanci zamuyi gda,
yace au, kuna nufin baxaku tsaya ayi budan kaiba? Tace
ai mun gama budan kai tunda munkawoma ita.
yace to nawa zan fansheta? Rahma tace mekenan? Nima
na tashi zaune tare da kara matsowa, sannan na kara
kanga kunnena, yace, toni kam bansan yadda zan muku
bayaniba, amma zaifi kyau ku tsaya dan kar kubar mata
abin gori, kunsan halinku dai mata, rahma tace, to zamu
tsaya, sai daifa mu bamusan yanda kuke gabatar da
al'adunkuba, sannan amarya bata da dinkakken kaya,
yace meya hanata dinkawa? Kodai bata shirya aurenaba?
Tunda tun asali bani takesoba? Rahma tace, wannan
batun aiya wuce, don dama bata da wanda takeso,
zuwankane kakoya mata soyyaya, yace rahma kenan! Ai
ina zaton soyyayar da kawarki ta iya niban kai gurinba,
amma dai ya wuce ta bakin naki, sannan kuma za'a
kawo mata kayan sawa, mu nan garin dama haka ake kai
kaya, don amare basa amfani da kayan akwatin sai dai
ayi musu a gidajensu, rahma tace, hali keyin haka,
mukam talakawa irinmu kuwa lefen muke amfani dashi,
ta canza batun da cewa, ina angona? Yace mun saidashi,
tace tabdi! Ba'a kake, da kunga gayyar kanawa, don
Allah yana kusa banishi inji muryarsa kona samu nai
bacci, ya saki daria, na lura kin shagwaba sagir dayawa,
shiyasa yadamemu da tadinki, na sulale a hankali na
kwanta, da alama bata fahimci abinda yake nufiba, suka
gama surutunsu da mijinta sannan sukai sallama da hirar
soyyayarsu, dare ya tsala, kowa na kwasar baccin gajia,
amma niban dani sbd hakikanin gaskia kalaman abkr sun
soki zuciyata, mutsu mutsu nane yatashi rahma, tace a
hankali lfy? Nace rahma mekika fahimta da mgnr abkr?
tace namefa? Na juyo da cewa, yace damacan bashi
nake soba, sannan yace soyayyar dana sani shi baikai
gurinba? Lkcn dakikace zuwanshine ya koyamin soyy,
rahma tace, kinsan nifa bakoda yaushe nake zama
nazarin mgn irin hakaba, amma ke mekika fahimta? Tace
wlh rahma koyaya mutum yai zance nasan meyake nufi,
inada wata baiwa tadaban akan karantar mutum, ko
zolaya yayi ina gane manufarsa, nufin abkr damacan
munnir nakeso bashiba, sannan na iya soyyayar da baikai
gurinba, to sbd soyyaya nasakarwa munnir kaina har na
samu ciki shiko bai taba hakanba, rahma tayi shiru itama
ta fahimta, amma don kada na tashi hankalina agane
inada damuwa sai tace, kada kiyi masa wani zato, ta
yiwu ba nufinsa kenanba, (kai abkr na gasawa hafsa
mgn gaskia, yan'uwa kuja mai kunne mana) nace hum!
Rahma tuni na hararo irin zaman da zamuyi da abkr
shiyasa nake gudun aurena, yanda na fahimci halinsa, shi
mutum ne mai tausayi dason kyauta, sannan mai
jajircewa ne akan abinda yakeso, wanda bai kaucema
addini, sai dai kash! Yanada naci tare da mita idan an
masa laifi, sannan baya bincike bare saurare, kinga
kozansha wuyar zama dashi in nayi la'akari da irin
halayen nan, sannan zai dinga jefamin mgn, hwy suka
soma zubomin tare da sintiri afuskata, Rahma tace, duk
wannan hasashen nakine, don haka kibar mummunan
zato a kanku, kiyi fatan alheri, nace to Allah yaxaba
mana mafi alheri, sai kusan assalatu sannan nasamu
bacci ya daukeni, da safe karin kumallo mai kyau

Please Login or Register in order to submit comment