Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mukayi,
kunun gyadane da lafiyayyen kosai, da kuma kayan tea
gamai muradi.natashi nashiga wanka bayan mungama,
kayan rahma nasaka cikin sabbabin kayanta, rahma tace
bari tadan fita cikin gdan tagani, jim kadan tadawo tace,
wai gaskia babban gdane, gasu da tarin zuri'a, nace
hum! Allah yasa mudace, rahma tace amin, can saiga
wasu yanmata 3, 2 manya, 1 karama, ina zaune bakin
gado suka shigo har ciki, biyun sunyi kama da abkr, duk
yanda akayi kannensane, duk suka tsuramin ido, bayan
mun gaisa, su kuma sai mgn suke cikin fillanci harda
daria, (nidai nagane gulma suke) karamar cikinsu ta
matso kusa dani tana cewa cikin harshen turanci, aunty
sunana ummi, wannan kuma sunanta rukayya, yayatace,
wannan kuma sunanta husna, abokiyar wasanmuce,
dukkanmu kannen hamma ne, nace to sannunku da
zuwa, ta dubi sauran tana sauraron abinda suke cewa,
sai naga tahade rai, sanna itama taci gaba dayi musu
mgn cikin fillancin, abinda nake zargi ni suke kushewa
ita kuma bahaka tasoba, saina samu kaina da tsarguwa,
su 2 suka tashi suka fita suna daria, nace musu sai
anjimanku, sukace to, ita kuma ummy tadawo kusa dani
tazauna, tacemin hammansu yana sona da yawa, dan
Allah na kula dashi, nayi yar daria nace to ngd ummy,
kuma zanbi shawararki, sai naji yarinyar tashiga raina
mai hankalin manya, tace kinyi kyaufa, anjima za'ayi
budan kai nace, ya akeyi? Tace kubakwayine? Nace a'a,
tace yanada kyau, zaku zaunane sai a bude fuskanki
inkin rufe, anayi ana gada, daga nan sai dangi suyi fansa,
nace mekenan? Tace kudine za'ayi ta zuba muku, sai
kuma a kawo faute daga gidan amare, nace shikuma
mene faute? Tace ba ankai muku suddajeba? Na tsura
mata ido, mene suddaje? Tace kayan dangi mana, ba
ankai mukuba? Nace eh, tace toshine suddaje din ai,
nace to menene faute? Ina nufin me akeyi dashi? Tace
kayane su kuloli dasu. Kaya dangin amarya suke badawa
wasuma harda gado sukeyi, nace to, rahma tace in kuma
mutum bai sanibafa? Tace ai duk zuri'armu sun sani,
rahma nace abinda mukeyi acan zamuyi sai mubasu hkr
muce bamusan sunayin hakaba, tace, ai baza'a damuba,
tunda an sani cewa baku saniba, karfe 4 daidai lkcn gdan
yacika dam kidan sarauta ke tashi, kai zuri'ar abkr akwai
kyau, sunata shigowa kallona, ummi taje kiran da abkr
yamata, don tuni sunyi waya yasan cewa tana gdan, ta
shigo dauke da katuwar leda, tace anty canza kaya
donga adda fadi nan sun iso, kuma nasan hamma da
abokanshi ma sunata shiri, shine yace in baki kayan nan,
muka bude nida rahma nace, kila dai a dinken yasiyo,
rahma tace, daga gani don gasunan a ledarsu, nace Allah
yasama to sumin daidai, daya leshine da aka hada da
swis, dayan kuma leshine zalla, sai shadda doguwar riga
taji aiki, sai atamfa, nace toni wanne zan saka? Rahma
tace kisa leshin nan, ummi tace aunty kisa shaddar nan
mana gata ja tunda keba fara bace, zakiyi kyau, nace
rahma duba akwatii akwai takalmi ja cikin kayan can?
Saiga ja takalmi gami da mayafi, ummi tace kiyi amfani
da bakake, kuma hamma yanason jan abu ga mata, don
in zai saya mana zani dole saikaga ja aciki, na sake yo
wanka na zauna gaban madubi nadauki kwalliya, harsu
ummi suna cewa gaskia nai kyau, na saka sarka da
sauran tarkacen karau, suk su rahma da sakina kowa
yayi kwalliya, zuwacan abokan wasansa suka shigo
sunamin tsiya wai in fito, yan'uwana suka takamin baya
muka nufi gurin. Katuwar darduma ce shimfide, tun kafin
mu karaso na hangi hamma sanye da shadda blue mai
kyau da tsada sai sheki take, gefenshi fadima ce wato
kishiyata, tana sanye cikin wani yadi, tsananin kyan
yadin ne yake bayyana tsadarsa, taci gwargwaro, ga
gwala gwalai, gabana ya fadi don kyawunta ya wuce
misali, ina isowa kanshinsu yadaki hancina, duk sai na
jini na zama wata ga daini nan, donko nasan ko a kyau
baxan kama kafa da itaba, muka kalli juna nida ita ido
cikin ido sannan na dauke kaina na zauna, guda ta soma
tashi, sai aka umarcemu da mu rufe fuskokinmu da kyau,
duk muka rufe sai aka kira kannenshi wai su fara bude
uwargda, rukayya ta bude fadi, mai guda tafarayi sannan
danginta suka shiga zuba kudi, daganan saini, ummi ce
ta bude fuskata nima, nima dai dangina sukadan
watsamin abinda ke garesu, bandamu da kudin da aketa
zuba musuba, musamman abkr don al'adace da addiniba,
(inama ni suka bawa kudin nan) can kuma saiga iyayen
fadi sun kawo faute wajen dangin abkr, kayan gado dan
italy na kwali, da kuloli da sauransu, aka shiga sanarwa,
rahma ta duko kusa dani tace ya za'ayi? Nafito musu da
garar nace suma abasu, buhunan shinkafa talia, dasu
dubulan da alkaki da yan samirun damukazo dasu, haka
kuwa sukayi, basuce komaiba da aka basu, rahma tace
suyi hkr bamusan yadda suke abubuwansuba shiyasa,
nan naga anata raba kalandu zuwa jakunkuna da memo
da jota, dadi sauransu, hotuna nake mamakin inda
akasamu nawa, kamar tare muka dauka? To suna nufin
tare muka dauka? Yana tsakiyarmu ya kwanta bayan
fadima, nikuma na kwanta a bayanshi, dukkanmu muna
daria.
ina sanye da jallabiya, al'ajabi ya cikani, sai daf da
magrib aka tashi, muka koma dakina, dama na kosa mu
koma, na janyo daya daga ciki jakunkunan da akaba
dangina nace, yaushe ne har mukai wannan hotunan ni
hafsa? Rahma tai daria tace lkcn daxamuje gdan
kwamishina, idan nace kizo muje baxuwa zakiyiba,
shiyasa nahada baki da mai hotan yamiki baki saniba,
computer kuma tatsara abubuwa, daman fuskarki kawai
muke bukata kuma gashi munsamu, rahma tabude
jakarta tace ga hotunan yanzu kigani, tabani na kalla,
amma nace Allah ya isana amma, nace dubi yanda nayi
acikinsu kamar wata yar aikinsu, badai shine yaji kuma
ya ganiba inji rahma? Nace ga yanmatan nan kannenshi
zasuyi rainin wayo, rahma tace, kedai tsakaninki da kowa
mutunci, nace shima sai wani shareni yake, shiyasama
da ana hotunan nan da danginsu ban cusa kainaba ciki,
nayi zugum ina kallon fadima, kishinta nacin raina, nace
rahma, fadima tana da kyau, ina zaton abkr yafi sonta,
me kamar wannan mezai damu kansa dani kila ya
aurenine don wata manufa, rahma ta mike cewa, saikiyi
kuma, nikinga tafiyata zan sallah, gara ke hutu kike, saiki
zauna kiyi tayi ke kadai, bayan sallar isha'ine aka kawo
mana abinci cikin kuloli, nan aka shiga ci tare da lbrn
karamcin mutanen yola, dan bikin nasu ya burge dangina,
tabbas yola nima zance sunada karamci, ina kwance
tunanin yanzu abkr yanacan tare da matarsa, sai mukaji
sallama, rahma ta amsa, tace rufe fuskarki ga angonki
nan, nace mezaizo yayimin? Rahma tace inya shigo saiki
tambayeshi magulmaciya, koda baki fadaba nasan
tunaninshi kikeyi, nace kada kimin sharri, tunanin me zan
tsayayi? Kafin tace wani abun sun shigo, hashim yace sai
mun sayi bake kenan? Naga amaryar tasha lullubi, rahma
tace dame kake zato? Nan dai sukayi addu'oi tare dayi
mana nasiha, sannan suka mikawa rahma kudi da ledar
kaza, daya daga cikin wadanda bansaniba yace, to tunda
anbiya saiki bude mana fuskarki mugani, nayi musu
shiru, haka nan naki bude fuskar sugani, nayi shiru
sannan suka mike dukkansu, abkr ya dubi rahma, saiku
zama cikin shiri, kunayin sallar asubahi in Allah
yatashemu zaku dauki hanya, tace to, abokan suka fita,
rahma ma tafice, saini saishi, duk mukayi shiru, yana dai
tsaye, yace, inbaki da mgn nizan tafi gurin amaryata,
uwargidanki kenan saida safe, da sauri na dubeshi bayan
na janye mayafin kaina, shima ni yake duba, bansan me
yake zuciyarshiba, nidai tawa zuciyar kishine fal, na
kauda kai cikin takaici nace, to dama akwai wanda yace
ba amaryarka bace? Allah yabamu alheri, na mike tare
da tura kofar toilet na shige, banjin fitsari amma dole
nayishi, don banason tsayawa kusa dashi, dana fito
yatafi, ina jiyosu sunayiwa sauran yan'uwana sallama
afalo, Rahma tashigo, har kunyi sallamar? Nace na lura
bazaki rike mijinki da kyauba, kada dai kimanta cewa ku
2 ne, nace um! Niba shine agabanaba, kuma bazan
wulakanta kainaba, don na lura bana cikin yan kayanshi,
abinda nasani shine, duk zaman daya zaba shi zamuyi,
rahma tace shikenan, in kinyi tunanin yanda zaki kama
mijinki a hannu kya kirani a wayata, tajawo ledar
gabanta, bari mu tayaki cin kajin tunda ba ango, nace ke
ango ya dama, niko ajikina, tace, abakiba, nan tafito da
kaza daya, nace su dauka suka tace a'a, bansan meya
hanani bacci ba wannan dare, alwala na dauro nazo na
duka inata nafila, sai naji raina yayi sanyi harma bacci
yana dibana, kacaniyarsu rahmace ta farkar dani, sunata
shirin tafia, nima na tashi nahau shiri, rahma tace, waike
inazaki naga kina diban kaya cikin karamin akwati? Nace
kano mana, karatuna zanyi wasa dashine? Tace kun
shirya hakan keda mijinki? Nace um! Zancen kikeso.Sai
gasu sun shigo, waisu fito yan kd, nace ni yan kn zanbi,
damasu mama sun tafi da shadad sbd makarntashi, na
zura hijabina, yan gdan sun shigo sunata godia ga yan
kd, tare dayi musu alheri wai inji lamido, turaman
zannuwa ne da kudi na shan ruwa a hanya, har sun shiga
motoci saiga abkr akan mashin ya tuko, yana sanye da
farar jallabiy mai gajeran hannu, dama ina cikin tunanin
watonba zayazo yayi sallama da yan'uwanama, kallo
daya nayi mishi nakau dakai, duk sai naji haushi yake
bani, musamman da zuciyata take rayamin cewa daga
ganinshi yasha amarci, ina kallo shima yaciro kudi ya
mika musu, motarsu tatashi ta nufi gate, na juya nabarsu
nan tsaye dasu rahma, ko karyawa na kasa, duk tsananin
son masa (waina) danakeyi, sagir yana kiran rahma waita
shirya, nima na hau kintsi, rahma sai daria takemin. Can
suka shigo dasu abkr, sai kamshi tare da kyallin goshi
yake, daga ka ganshi ango dai sosai, yasha boyil mai
ruwan kasa, hula minista baka, takami ma haka, suna
gaisawa rahma tace, waida hafsa zamu wuce kn? Na
zabga mata harara, wai nema? Ya dubeni da mamaki,
mexakije yi kn? Nayi farin rashin kunya tare da murguda
baki, menakeyi da jarabawa na tahowa zaman me zanyi
anan? Rahma tace zaman aure, nace hum! Sai naga yayi
murmushi, sagir yace, kibari ai angon zai kawoki ida lkcn
zana jarabawar yayi, nace nidai gaskia tafia zanyi,
idanuna suka kawo kwalla, sagir yace to abkr amaryar
nan shagwaba takeji, abkr yace, tayi son ranta, amma
tafia sai nai niyya, rahma tace ni tunaninama Allah yasa
miyar nan bata lalaceba, sannan walimarmu tasha ruwa.
Nace in kinje kirabawa makota, rahma tace to, narigasu
isa wajen motar, nakama murfin zan bude, abkr ya
dallamin harara, na matsa ya bude musu suka
shiga.bayan tafiyarsu rahma, ina tsaye na cije lebe ina
kallonsu, zuciyata tana tukuki, da sauri na juya daki,
nafada gado ina kuka tamkar yarinya, tausayin kaina
nakeyi, bansan irin rayuwar dazanyiba, kamshin
turarensane ya cikamin hanci, don haka saina zaci yana
tsaye, da sauri na dago kaina tare da waiwayowa, shine
kuwa, yace sbd kina zaton za'a cinyeki shiyasa kikeson
tafia ko? Na zuba mishi ido ban tabkaba, shima ni yake
kallo, ya dauke kanshi daga kallona, koda yake dama
bani kike soba, na sunkuyar dakai, yace gaba, ance so
dayane tak! Kuma tuni kin dorashi kan wani, na dago da
sauri muka hada ido, na juya mishi baya cike da suyan
rai, kana nufin bana sonka? Yace basaina maimaitaba, in
kuma ba hakaba, menene dalilin kukanki? Nadubeshi, duk
wata amarya tanayin irin wanan kukan a wannan ranar,
dole nayi kewar yan'uwa, yace ko? Amma dana zaci ba
yauce rana ta farko dakika soma rabuwa dasuba?
Gabana yafadi don na fahimci mgn yajefamin, ka iya
fadin duk abinda ranka yaso game dani, don naga kamar
don hakan ka aureni, na zauna bakin gado cikin bakin ciki
tare da tausayama kaina, yatako ya matso kusa dani, don
haka na aureki, kuma zanci gaba da fada miki duk mgnr
da tazo bakina, sbd baki iya tauna mgn ba kafin ta fito
daga bakinki, duk sanda na kalleki saina tuna cewa ke
karuwa ce ada, na mike a fusace, zamanmu bazai yiwuba
matsawar zaka dinga kallona wa wannan fentin, ya
zauna kan madubi yace, waya shafa miki fentin? Inace
kece da bakinki kika shafama kanki? So yajaki kika zubar
da kimarki, kuka ya kufcemin, cikin kukan nake cewa,
nikam tafiya zanyi, kasakeni.Yayi yar dariya ' ina sonki
tsakanina dake babu batun saki. Tafia ce dai in kince
zakiyi ta bazan sha mamaki ba tunda mahaifanki ma kin
tafi kin barsu bare ni. Yanzun ma kya iya tafia in kinso
ya juya ya fita, nace 'subhanallah' wannan wace irin
rayuwa ce? Nayi kukana na qoshi sannan na share
hawayena babu me bani haquri. Na kira Rahma suna
hanya cikin dusasshiyar murya nace Rahma Abubakar
yazo yaci mun mutunci ni gsky bazan iya zama dashi ba.
Rahma tace meya fada miki? na sanar da ita komai tayi
shiru na dan lkc can tace kiyi haquri duk laifin kine da
kika sanar dashi ta bai baishi kuma mutun ne mai mita
tare daqin saurare. Munyi munyi ni da sagir kan cewa ya
sauraremu dan muyi masa bayanin gsky lamarin sai
yace"Ai kin gama magana shi ba zaya iya jin wata
kwaskwarima ba sannan yayanki umar yace masa da
soyayya ya yaudareki kika bada kanki don haka yanzun
shawarata itace kiyi shiru da duk abinda zai ce kada ki
tanka shi. Na kula yanada mugun kishi ne nace ko gidan
karuwai ya ganni yace yana so bai dace yazo kuma ya
dinga ca6a min magana ba. Rahma tace kada ki damu
zai zo ya yi nadama nace kinga dai ga jarabawar mu
tazo bana zaton zan zana ta. Na sake rushewa da kuka
shekara ta ta qarshe Rahama tace ki daina damuwa
addu'a itace kadai mafita Allah zai kawo sanadiyyar da
zaya fahinci gsky nace shi kenan. Ranar har magriba
ban kuma ganinshi ba abinci daga cikin gida ake
kawominsanda saudatu ta kawomin na dare na rana ko
bude shi banyi ba. Tace ke kam baki san cin abinci gashi
kina ta kuka kiyi haquri aure kenan zaki saba damu in kin
saki jiki. Mu kam bamu da wata matsala nace to nagode
nayo wanka don na fara sallah.
Nayi shafa'i da wuturi sannan nayi shirin bacci sam bana
kojin yunwa na hau gadona kwanta. Text ya shigo cikin
wayata na duba shine angon nawa. Yace bazan samu
shigowa ba don fadi bata san in fitavqila sai gobe. Duk
suyan da raina ke yi sai na rubuta cewa Allah ya kaimu
ka gaisheta. Na share hawayen da ya zubomin sannan
naje na rufe qafata. Abubakar dake kwance kan gadon
shi tsararre tun da ya shigo daha salkar isha'i yake kai
kwance. Gaban mudubin dakin fadi ce tana fesa turaruka
shi masu qamshi sanye take da rigar bacci me shegen
kyau tare da ma'ana. Daga inda yake kwance yana
kallan ta zuciyarshi fadi take ina ma ace hafsat ce haka
a gabanshi. Me yasa ta fadi mishi cewa ita karuwa ce?
Me yasa ta kasa adana masa kantahar zuwa lkcn da zai
aureta?.Shin maza nawane suka kwanta da ita? Abinda
ke sashi ganin ba zaya kusanta kanshi da ita ba kenan.
Dalilai 2 suka sa shi auranta na 1 tsabar santa da
qaunarta na 2 kuma.....

Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100



Sanadin Boko 3-07
Posted by ANaM Dorayi on 06:01 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Na biyu kuma yanda yayi yaqi da danginsa don ya samu
ya aureta. To sai da damar ta samu sannan yaji wannan
muguwar maganar ba abin yace ya fasaba lamido ya ce
don me? In kuma ya fadi dalilin shi zasu qara qarfafa
al'adarsu tare da kafa misali dashi. A duk lokacin da
wani yayi yunqurin auro yar waje a cikin family kai yasan
sai lamido yasa an rubuta shi cikin kundin tarihin family
dinsu. Gsky bai so hafsat ta furta zancan nan ba gaba
daya haushinta yakeji shine mafarin daya tura mata
wannan saqon don ya qara bata haushi. Zaman Fadi a
bakin gadon yayi daidai da shigowar amsar dana bashi
koda ya karanta sai kuma tausayi ya kama shi tamkar ya
rubuta ban baki amma sai ya fasa. Ni kuwa sallah ke
nutsar dani a duk lkcn dana samu kaina cikin damuwa
don haka ita na duqa yi har nisan dare sannan na kwanta
zucita wasai. Gsky ko yaushe ina alfahari kasantuwa ta
musulma kuma ina roqan Allah ya kashe ni cikin
musulunci. Da safe bayan nayi wanka na rufe jikina da
hijabi na nufi 6angaren mutanan gidan daki daki na gaida
su. Tsohuwa gwagwal itace tace min lamido yana
gefanshi inje mu gaisa.Kan kujera na sameshi da carbi a
hannunshi na zauna gefe sannan na gaida shi cike da
ladabi yace yarinya hafsat ko? Nace eh yace to kina jin
dadin zama damu? Nace eh yace to madalla kiyi ta
haquri har zuwa lkcn da zaki saba damu. Sannan in kinga
wani abu baki gane ba ki samu gwagwal zata yi miki
bayanin komai. Nace to nagode ya ce babu komai na
tashi na nufi sashe na na samu abin karina Kunun
tsamiya da qosai nakai kicin na aje da yake ya kawo
kayan tea sai na hada ruwan lipton na sha. Ai kuwa
tamkar na tsokano yunwar don haka sai na tsiyayi kunun
na sha da qosai
Na shiga gyaran dakina na tsaftace ko ina sannan na
saka turaren wuta na koma gado na kishingida. Can
wayata ta soma ruri na duba Rahma ce na dauka muka
gaisa tare dayi mata bangajiya. Ta sake bani haquri tare
da shawarwari sannan tace min miyar nan da kaji duk
tabai maqota sannan ta basu haquri game da batun
walima kan cewa bamu zaci zaa wuce yola ba. Nace
shikenan muka dan zanta sannan mukayi sallama.Ummi
ta shigo da sallama cikin fara'a na tareta. Ta gaida ni
cikin girmamawa sannan tace Dada da Abba suna gaishe
ni nace ina amsawa na ce ga kunu da qosai a kicin tace
ta qoshi don yanzunnan ta karya muka zauna muna hira.
Tace aunty hammana yana sanki da yawa kiyi kallan
yanda yayi rigima a cikin family dinmu dan ya aure ki?
Nace haba wace rigima yayi? Nan ta shiga bani lbrn na
jima ina mamakin wannan irin al'ada Nace kenan ba kwa
sona? Tace muna sanki mana sai dai yanzu aikin kine ki
koyama danginmu sonki da son duk wani bare dazai
shigo cikin mu bayanki,nakalli yarinyar qarama da
hangen irin na manya nace ta yaya zan koya musu haka?
Tace aunty ke zaki fini sanin hanyoyin da zaki bi don su
soki kadan din dana sani shine halayen kirki yin kyauta
tare da sakin jiki damu Saura kin fini sanin halayen da
zaki nuna a gaba in mun kawo bare in munce zamu aura
baza a hana mu ba tunda basuga wani mugun abu daga
gareki ba Nayi dan murmushi ummi kenan insha Allah
danginku ba zasuyi takaicin da kasantuwata cikin ku ba.
Kusan qarfe biyu ya shigo lkcn ummi ta tafi ni kuma na
soma bacci A jikina naji cikin bacci ana kallona ko nace
ana tsaye a kaina a hkl na bude idona Qamshi turaren sa
ya daki hancina sanye da qananan kaya yayi kyau
matuqa, bai san cewa na farka ba Ni kawai yake kallo ba
wai fuskata yake kallo ba amma a hkk na yunqura na
tashi ya dubi fuskata kin dai yi sallah ko kike bacci?
Nace nayi sannu da zuwa yaya Fadima? Ga mamaki na
sai naga yayi murmushi tare da cewa lafiarta kalau
kenan yafi santa? Wayata tayi ruri ko ban sani ba Rahma
ce wayar tafi kusa dashi don tana kan mudubi ya daga
ya duba sannan ya ajiye nazo na daga muka gaisa tace
na jiki sanyi dayawa har yanxu dai? Nace Rahma me zqi
canja ni dai ki tayani addu'a Tace insha Allah taci gaba
dama na kiranki ne in fada miki cewa na rabar da duj
niyar nan da naman kada ya lalace. Sai dqi na rage miki
kadan a gidana in kinzo sai kiyi amfani da shi Nace ki
barshi kawai Rahma ta yiwu nazo kenan sa'adatu
sulaiman ma dazu ta kirani ta fadamin cewa wai tamin
test dina da suka rage nace mata to nagode Sai dai bani
da tabbacin zanyi jarabawar Rahma tace insha Allah
zakiyi nace Allah yasa nagode ki gaida mama da shadad
baya rigima? Tace ai yaqi zama tunda ya ganni yaqi
mama nace Allah sarki to sai anjima mukayi sallama Na
dubeshi bazaka xauna ba emm......akwai abinci ya tabe
baki am okay ba zama zanyi ba ki shirya inkaiki kuga
juna da fadimana,na maimaita fadimarshi? Amma sai na
danne na miqe na fada bandaki wanka na soma shi kam
dakin yayi ta bi da kallo tare da shaqar qamshin turaren
dana turare dakin dashi tun safe idanunshi suka sauka
kan rigar baccina wadda na ninke ta kan gadona Ya
dagata ya warwareta ruwan hanta ce mai santsi kalar ta
mishi kyau zaya so ya ganta sanye a jikin hafsat Ya kai
rigar ya dorata a fuskar sa a hankali yake shaqar
qamshin ta irin wanda yasoma ji tun ranar da suka rage
mata hanya motsin qofa ne yasa shi jefar da rigar ya
kuma juya ma gadan bayatare kuma da sake hade rai.
Na zauna gaban mudubi duk da cewar kayan ne a jikina
wato da nayi wankan ban fito ba sai da na saka rigata.
Na janyo mai na soma shafawa yace wai wanka kikayi?
Ni fa ba nazo dogon zama bane Na dubeshi ya wani
tsare gida bance komai ba naci gaba da murza mai a
qafata ina yan shafe shafen su eye pend ya kuma
katseni Kada ki 6ata lkcn gurin yin wani shafe shafe don
bazaki tsorata Fadima ba a kyau
" turqashi mu hadu a kashi na "4" na qarshe"
Alhamdulillah.
Wannan shine karshen littafi na "3", godiya ta
musammam ga masoya kuma mabiyan Hausa Novel



Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 4-01
Posted by ANaM Dorayi on 06:21 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Kalmar ta dake ni tamkar saukar aradu jikina yayi sanyi
matuka.Tsam na mike daga gabn madubi na koma gado
na zauna cikin matsanancin kunan rai.Sai naji tamkar
mazaunan nawa ba zasu iya rike ni ba, don haka sai na
kashingida tare da lumshe ido. Duk iya kokarin da nayi
don na tsaida hawayen idona abn d yaci tura,sai da suka
sulalo ta gefen idona, idon haguna kuma hawayen ya
biyo ta karan hancina. Yayi dan murmushi ba shi da
burin da ya wuce yaga 6acin ran Hafsat,duk da son da
yake mata.In ya tuna yanda ta mike tana fada mishi
cewa ita karuwa ce sai ya ji tamkar ya binne kanshi don
takaici. Ya dubi ni Ki tashi mana kin wani kwanta. Na
sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya na ce. Ban san
cewa gasar kyau zamu je ba da ban 6ata lokacina gurin
shirin tafiyar ba., Kaje ka bata Award din da ka tanada
na mika wuya. Ya dan yi shiru. Kila yana nazarin
maganar da na fadane can sai ya fita da cewa in kin
gama ina jiranki a mota in har ina da izinin bada umurni.
Tamkar kada na tashi,amma bani da damar yin haka,dole
na koma gaban mudubi. Jallabiyata na saka baka mai
ratsin ja, tana da tsukakken hannu shima ja, na nade
kaina da dan mayafin, shima yana da ratsin ja. Takalimi
da 'yar post din da na saka duk jajaye ne. Na feshe jikina
da turare, da na kalli madubi sai nayi dan murmushi don
nayi kyau. Zuciyarta ce dai ba dadi sakamakon
maganganun da ya ya6a min. Na isa gefen direba in da
yake zaune cikin sanyin murya na ce, bari nayi ma su
Gwagwal sallama. Ya dago ya dube ni, muka kalli juna
cikin ido. Da sauri na rausayar da kaina gefe tare da
harde hannuwana a kirji, ya ce to kije mana kin tsaya
min kerere. Na dubi shi, "Ai dama umurninka nake jira.
Duk sai da na bi kowa gurinta na ce sai mun dawo,duk
sun ji dadin cewa gurin Fadima zani. Abin da na lura shi
ne, suna son a girmama 'yar uwarsu.Na dawo na shiga
gaba kamar yanda ya bude.Tsararran gida ne mai
matukar kyau, ga furanni masu bn sha' awa, ina biye da
shi hr kyakkyawon falon. Wani dankareren zanen hotonsu
ne yake fuskantarka an jingine shi da bango a kasa.
Kallo daya na yi wa hoton na kauda kai, tamkar jinsin
Larabawa ko Indiya. Ya dube ni ya ce," zauna, bari in
kirata."Ya tafi yana fadin "Sweety.," Tamkar in toshe
dodon kunne na don kishi. Na nutse cikin kujerar ledar
mai kalar siminti. Na dinga bin ko'ina da kallo. Wasu
abubuwan ma bn san su ba, ban ta6a ganinsu ba, daga
karshe na maida kaina ga dankareren TV bangon da
wasu Indiyawa suke ta rawa. Ba rawarsu ce ta birge ni
ba, da har na tsura musu ido,tsabar takaici ne ke cina.
Amma na lallashi zuciyata da cewa tayi hakur, na sani
wata rana dai labari. Hannuwansu sarke da juna suka
fito, kama suke sosai da shi,wani abu yazo ya tokare
kirjina tamkar in rufe su da duka. Wata zuciyar ta ce,
Tashi ki shaketa. Da sauri na ce, "A'uzubillahi
minasshaidaninrrajim" sau 3 sannan na ce, Allah ka yaye
min wannan duhun da ke zuciyata, ka bani ikon yin
dauriya,kasa nafi karfin zuciyata. Suna isowa na mike
tsaye,take naji zuciyata wasai, na saki wata fara'a wadda
bn san ma ina da ita ba,tare da mika mata hannu. Na ce,
Amincin Allah su tabbata a gare ki da rahamominsa da
albarkatunsa. Itama ta miko nata tare da cewa, Amin
kema amincin Allah ya tabbata a gare ki. Muka sarke
hannu.Sannan muka saki na zauna itama ta zauna, ta ce,
kullum ina son ki zo mu gaisa. Na ce"To ai yau gani
nazo." Ta mike ta nufi gurin da nafi zaton kicin ne, shi
kuma ya dauki remote yana canje-canjen tasha. Ya kuma
ajiye ya nufi dakinshi, ta iso da kofin tare da kwalin jus a
hannu fara'arta dai ba sosai ba. Ta dora kan stool ta
dauko shi ta kawo gabana,sannan ta zauna. Na dauki
kofin na jingina da kujerar ina kur6a ina kallon TV.Ta
mike ta nufin ciki,dakin da ya shiga nan ta nufa. Dakin
shi kenan,suka bar ni nan zaune. Tuni na dire kofin jus
din don sai naji ya daina zakin sai daci, don tsabar
takaici. Kusan minti 10 sannan ta fito shima haka. Ta
shiga dakinta shi kuma ya nufo gurina, na kalli agogon
bangon falon wanda hoton sune a jiki. Na ce, Tunda mun
gaisa zan tafi gida."Ya dube ni "Nan ma gida ne. "Yar
aikinta ta soma jera abnci kan dinning. Ta fito ta iso
gurinmu "Honey kuzo muci abnci." Ya dube ni " tashi
muci abnci . Na ce Tuni naci abnci. Ta ce, Ai kam ba ki
isa ba, dole sai kin ci. Ni da ita muka jeru,

Please Login or Register in order to submit comment