Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwance na dawo daga gurin aiki wata makaranta
aka turani ta 'yan mata nake koyarwa. Na yi abinci na
gama nayi wanka na kwanta, ya zauna na tashi na
mishi sannu da zuwa, na dire mishi abinci. Yana ci ya
ce, "The only, ina son ki yiwa Fadima taimako daya."
Na ce, "Na me?" Ya ce, "Bata samun bacci don
Rukayya ta fada min cewa zaune suke kwana. To tana
son in dinga kwana gurinta har ta dan
murmure."Zancen ya bani mamaki, sannan na fahimci
cewa makirci ne, amma sai na ce, "Ba komai." Ya ce,
"Dama na san ki baki da matsala." Da dare kuwa ya
tafi, haka-haka har sati uku. Sai dai fa in yana da
matsala ya yi min sammako ko kuma in ina gurin aiki
ya zo ya dauko ni daga baya ya dawo da ni. Ban taba
nuna mishi damuwata ba.
Lamido ya kira shi ya ce, "Ubana an fada min baka
kwana a gidan nan ko?" Ya ce, "Eh, saboda bata samun
bacci ne in bana na." Lamido ya yi murmushi sannan
ya ce, "An fada min kuma tana zuwa hurin aiki ko?"
Abubakar ya ce, "Eh, ai matsalar tata da dare ne."
Lamido ya ce, "To, daga yau na hana, kowacce ka
dinga kwana gidanta a ranar kwananta, kanta aka soma
ciki? An ce ta samu sauki ba shike nan ba?" Abubakar
ya ce, "Shi kenan." Har na soma bacci na ji kwankwasa
kofa, na zo na ce, "Wane ne?" Ya ce, "Ki bude." Na
bude na ganshi na ce, "A'a baka tafi ba?" Ya ce, "Ke ce
kika fada ma Lamido cewa Fadima ta ji sauki amma
ban daina zuwa ba ko?" Na ce, "A'a bani ba ce." Ya ce,
"To wanene?" Na ce, "Ka tambaye shi." Ya ce, "To ni
bana son kai kara, don ban soma zuwa ba sai da
izininki." Na ce, "To gaskiya ba ni bace." Ya ce, "In ma
ke ce din ai yana zuwa kanki, tunda an ce ai haka ciki
ke yi muku." Na yi masa shiru don haushi.
Abinda bai sani ba nima lokacin ina manne da nawa
cikin wata biyu, ina kuma laulayina sai dai bai yarda ni
ba, sai dai amai kuma nafi yin shi da rana, kuma ban
fasa komai ba.
Azumi ya kusanto ya zo ya same ni wai in zo muje
gidan Fadi, zai yi wata shawara, na ce to..........
Cikinta ya fito, amma yanda take tike kugu gami da
turo cikin ko watan haihuwarta ne sai haka, tana yi da
kyar take daga kafa, a dole ga mai ciki shi kuma
kallonta yake yana murmushi, ni sai suka ma bani
dariya. Ya kamata ta zauna yana yi mata sannu, ita ko
sai faman cije-cijen lebe take, na yi 'yar dariya nace,
"Maman twins an fito?" Ta ce, "Umm na fito." Muka
gaisa ya ce, "Dama saboda zuwan azumi ne ina son in
bada sadaka wa kuke ga ya dace in ba?" Fadima ta
dube shi, "Kawai honey ka bamu mana, ni ga ma
sayayyar da ke gabana na kayan baby." Ya dubeni, "Ke
fa?" Na ce, "Ka kai Masallaci ko ka samu mabukata ka
basu tunda Alhamdulillah mu muna cikin wadata." Ya yi
murmushi, "To dama nima tunanina kenan, don haka
zan bai wa masu bukata Zakka, sadaka kuma zan baku
ku bada, ko cikin family dinku ko nawa."ta zobaro baki,
"Kenan shawarata bata yi ba?" Ya ce, "Eh." Ta yunkura,
"To ai da ba'a kirani ba." Ya ce, "Hakkinki na baki da ba
sai na zo ba din, don nasan ita zata iya bani shawara
ta masu ilmi." Kudi ya zube min dubu dari uku da dari
biyar, wai in raba ma masu bukata. A zatonshi zan tafi
da shi gidanmu ne in raba ma dangina, sai na
tambayeshi zuwa kasuwa ya yarda. Ni da Ummi muka
je. Shinkafa kawai na lodo da taliya sai kuma zannuwa,
Ummi ta ce, "Aunty me zaki yi da shi?" Na ce,
"Sadaka." Ta ce, "Don Allah akwai wasu dangin su
Daada dake can wata ruga talakawa ne, jiya ma Abba
ya aika musu da gero da sugar na kunun azumin." Na
ce, "To." Daada din naje na samu na ce, "Sadaka zan
raba ta abinci saboda neman falalar wannan wata, to
ina so in cire na dangi na can Ruga shine nake so ki
cire musu nasu sai na ba makota sauran." Ta ji dadi
sosai, tayi ta shi min albarka, duk da ta san cewa shi
ne ya bamu kudin, ta ce min ya shawarceta, ita ce ma
tace yayi shawara da mu, ta ce ya ban kai dangina ba?
Na ce, "Da ku da dangina Daada ai duk daya ne ba
wani bambanci." Ta ce, "Allah ya shi min albarka. Ta
cire musu sannan na saka 'yan samarin gida mua yi ta
mika wa makotanmu wadanda ke da karamin karfi.
Dama kananan buhuna ne. Lamido har kofata ya zo
yayi min godiya tare da shi min albarka. Abubakar
kuwa da ya dawo ya ga makota na ta mai godiya tare
da addu'a sai kuwa kanshi ya daure, da yai zaton geron
da Lamido ya raba ne, sai da ya je gurin Lamidon shi
ne ya bashi labarin abin da nayi sannan ya ce, "Ka rike
matarka hannu 2, don ka samu macen da babu irinta
cikin yaranmu, Allah ya azurta ku da Yara masu
albarka." Abubakar rungume ni yayi tare da min godiya
na ce, "Allah shi ne abin godiya." Ashe zakkar shi can
ya kai ma su Babana bayan ya dibar ma Innarmu.
Shima bai fada min ba sai da Ya Umar ya kira ni ya
fada min wai mijina ya kawo wa Baba zakkar kudi naira
miliyan 2, Inna dubu dari biyar, in masa godiya sannan
yana son mu yi shawarar abinda za'a siya. Na ce,
"Yaya Umar ku nemi dan madaidaicin gida ka sai ma
Baba kawai." Ya ce, "Nima haka na ce, kuma shima
Baba zai so hakan. Allah ya saka masa da alheri." Na
ce, "Amin.
Kuka na saka da muka gama wayar, ban san ko kukan
me nake yi ba, na farin ciki ne? na son mijina ne? na
barin iyayena baya ne? Oho. Inna ma ta kirani ta ce in
masa godiya na ce to.
Da ya dawo kuka na sa tare da rungume shi, ya rude
ya firgice yana tambayata, "Me ya faru D Only? Wa ya
taba ki?" Na ce, "Ba kowa, na gode da taimakon da ka
yiwa Iyayena, Allah ya saka makada alkhairi, Allah ya
kara budi, ya tsare ka daga dukkan sharrin abin ki, ya
kuma bani ikon binka sau da kafa." Ya shafa kaina,
"Amin Masoyiyata, game da batun Zakka kuwa ba sai
kin min godiya ba hakki ne na Allah na cire." Na ce,
"To da ka cire din da kaga dama ai wani zaaka ba." Ya
ce, "To shike nan." Da dare muna kwance ya ce, "Wai
ya za'ayi da sayan kayan Sallanku? Kudin zan baku
kuje kasuwa ku siyo?" Na ce, "A'a da kai zamu je
saboda ka zaba mana son ranka." Ya ce, "Bari sai na ji
ra'ayin Fadima." Ya janyo wayarsa ya kirata, "Sweet
heart." Ta amsa da, "Na'am Sweet honey." Ina jin
muryarta, don ina jikinsa ya ce, "Gobe zaku shirya ne
mu shiga kasuwa tunda bani da aiki?" Ta ce, "To, daga
nan sai mu siyo kayan Babys din tunda an ce mace da
namiji ne?" Ya ce, "To sai ki shirya zamu shigo wuraren
11am saboda kada ki sha rana ko?" Ta ce, "To Honey
sai kun zo." Ya ce, "Yauwa, ki shafa min Babys." Suna
yin sallama na kankame shi, "Yan biyu zamu samu?" Ya
ce, "Eh, dazun da ta dawo asibiti take fada min wai an
ce 'yan biyu ne mace da namiji." Na ce, "Kai na yi farin
ciki, ina son twins shi ne baka min albishir ba?" Ya ce,
"Na same ki kina kuka yaya zan tuna da maganar 'yan
biyu?" Na ce, "Allah ya sauke mana ita lafiya." Ya ce,
"Amin, kema Allah ya baki ina son in ga kin haihu, duk
wannan dina har yanzun ba ciki, ko dai zamu je asibiti
ne?" Na ce, "Haba dai, duka yaushe aka yi abin? Ko fa
shekara banyi ba." Ya ce, "Don Allah ki daina zancan
nan, yara nake so sosai, yanzun kin ga zan fara da biyu
na zo daidai da Kanina Usman, in kin haihu ko da daya
ne kin ga na fishi ko? Balle ma kema biyun zan baki."
Na ce, "Oh! Kai ne ma kake badawa?" Ya ce, "Allah ne
zai bani ni kuma in baki." Na ce, "Dama kun gaji 'yan
biyu ne?" Ya ce, "A family ni zan fara, shi yasa kowa ke
doki, jiya kinga yanda 'yan uwa ke murna?" Na ce, "Ai
abin so ne, Allah ya bamu masu albarka." Har zuciyata
na taya shi murnna.
Katon super market muka shiga, gefen zannuwa, lesuka
da shaddoji zuwa yaduka, ya ce mu zaba, na ce, "A'a
ka zabo mana." Sai cewa Fadima ta yi, "Ni zan zabi
abina." Na ce, "To ni ka zabo min." Duk wanda ya miko
min ko bata kamfanin ba amsa nake in ce yayi kyau. Ya
ce, "To dama atamfa ce nake da irin wadda nike so,
amma sauran zabi." Da muka gama sai na zabar wa
Ummi atamfa da Shadda da leshi Rukayya ma haka.
Daada kuwa yawan namu na daukar mata, ya bini da
kallo itama haka ya ce, "Wannan fa?" Na ce, "Na su
Daada ne, ta ce, "Su Daada ne za'a sai ma kaya?" Ya
ce, "Shi ne ai, su Daada da ke da super market zuwa fa
zasu yi kawai su zaba...........".......


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 4-06
Posted by ANaM Dorayi on 05:20 AM, 29-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Na ce, "Za ka biya ko in biya?" Na fada cikin daure
fuska, ya ce, "A'a zan biya in basu amsa ba sai kin san
yanda zaki yi da su." Fadima ta ce, "Neman gindin
zama." Ban ko kalle ta ba shima bai ce komai ba. Da
muka isa gurin da ta sai Shaddoji da Yaduka sai na dibar
ma Abba, ya ce, "Dama kin daina wahala na fa san ba
zasu amsa ba." Don haushi ban kuma tanka su ba, don
Fadi sai dariya take yi, ban fasa dibar musu ba, har
turaruka na dibarma Abba, su kuma kayan shafa. Ita
kuma muna zuwa gurin kayan Babys nan tayi ta jida,
kowanne bibbiyu ni ko nayi ta taya ta. Da muka je gurin
takalma da jaka na zaba musu. Da zai sai nashi na zaba
ma Abba har huluna ya ce, "Ke baki san lambar takalma
ka kina ta diba har da hula." Na ce, "Ido ba mudu ba ya
san kima." Ita kuma ta ce, "In da rabon ka tafka asarar
kudi ai shi kena." Ni sai na sharesu kawai na ci gaba da
lamurana.Mun dawo gida cike da lodin kaya, but din
mota shake, kujerar baya shake, da kyar na dan samu
gurin rabawa. Dama hakima ta gaje gidan gaba, ita muka
soma saukewa sannan muka wuce gida. Muka yi ta jidar
kaya zuwa ciki, har lokacin fuskata daure saboda yanda
yayi ta gwasale ni, don kawai na ce ya sayawa Iyayenshi
kaya. Ba gidan zai sha ruwa ba yau, don haka ina yin
sallah na kwanta sai bacci, ban san lokacin da ya tafi ba
ma ni. Sai da ya dawo Asham sannan ya biyo gurina, ya
samu ina sallar Asham din nima, ya zauna yana kallona.
Na idar na gama addu'a ya taya ni shafawa na dube shi,
"Sannu da zuwa." Ya ce, "Yauwa, na zo ne inga ko kin
huce, naga yau an yi bacci an share ni." Na ce, "Ai bani
fushi da kai Mr Cool." Ya yi murmushi na ce, "To yanzun
dai sai na dauko maka ka kai musu." Ya ce, "Sai dai ki
zo muje tare, dan kuwa ba za'a sace min gwiwa ni daya
ba.Na mike na dauko hijabi zan sa ya ce, "Zo nan." Na
zo ya dubeni sama da kasa, "Wai wanna kibar fa? Sama
da kasa duk kin cika?" Na shafi kumatunshi na ce, "Ka
iya kiwo ne." Na mika mishi ledar dan in bagarar da
maganar, "Ga wannan mu je." Ni kaina na san cewa na yi
kiba, cikina a kirji da hips ya tsaya, marata ba me cewa
ina da cikin wata biyar da 'yan kwanaki. Duk a falo muka
same su suna kallon Tafsir din Sheikh Amin Daurawa, na
zube na gaishe da Daada da Abba, Ummi da murna ta
hawo jikina, Daada na mata fada da fillanci. Rukayya ta
tabe baki ta gaisheni a dakile. Abba ya ce, "Daga gida ku
ke?" Na ce, Eh! Ya ce, "To sai ki basu." Na ciro ledar
Daada na yunkura naje gabanta na ce, "Gashi in ji shi."
Dama bana iya kiran sunanshi a gaban Iyayenshi. Ta ce,
"Me muka samu?" Na ce, "Kayan sallah ne ba yawa." Na
mika ma Ummi da na Rukayya sai suka hau murna,
Rukayya ta daga kai ta ce, "Hamma ya aka yi kasan
kalolin da muke so? Ni komai ja Ummi komai pink." Ya
kalleni, Daada ma sai murna take yi tana fadin, "Allah ya
shi maka albarka ya baka zuri'a ta gari wadanda suma
zasu fita hakkinka." Ya dube ni na kauda kai ina fadin,
"Amin Daada." Na mika ma Abba nashi wanda ke
kallonmu yana dariya tare da fadin, "Masha Allah." Ya
ce, "Har da ni? Ikon Allah Abubakar an yi hankali." Muka
sa dariya. Bayan an nutsu ya ce, "Wato Hamma abin da
yasa kaji na ce ashe kayi hankali shi ne, ka sani duk
kudinmu muna da hakki a kanka, kuma na gode Allah ya
kara budi." Muka ce Amin. Ya ce, "Ni fa da har ba zan
sai muku ba naga kuna saidawa." Daada ta ce, "Don
muna saidawa shi kenan bazaka fita hakkinmu ba?" Ya
kalle ni, nayi maza na kauda kai don bana son ya ce
nice. Abba ya ce, "Bari Usman ya zo ya kai ma telana
su, don da su zan je Idi in Allah yasa mun kai lokacin."
Haka suka yi ta shi mishi albarka, tare da yi masa fatan
samun zuri'a tagari. Da zamu tafi Rukayya har mota,
Rukayya ta ce, "Hamma Allah ya kawo mana 'yan biyu
lafiya..." Muka ce Amin. Har lokacin wani gani-gani take
min suka juya. Ko nisa ba suyi ba ya wani kankame ni ya
rungumeni ya ce, "Na gode D Only, na gode da sani a
hanya da kika yi, ni a zatona tunda iyayena suna dashi
fiye da ni ba sai nayi musu wata hidima na sai dai in ma
danginsu marasa shi daga ciki." Na ce, "Ko sune suke
kera kudi wajibi ne ka basu hakkinsu, yi musu biyayya na
san kana yi, yi musu alheri kai har abinci ya kamata ace
duk wata kana sai musu ko buhu dai-dai ne." Ya ce, "Zan
soma daga wannan watan Insha Allah, kai yau naji dadi
ashe haka mutum ke samun farin ciki in ya faranta ma
Iyayenshi?" Na ce, "Sosai ma kuwa.Ya ce, "Na gode
Allah da ya bani mace ta gari, yanzun fada min bayan su
ko akwai wadanda ya dace in sai ma kayan Sallar?" Na
ce, "Su Lamido da duk kanne da yayin Babanka, ka sai
musu kowa wanda ya dace da shi zasu ji dadi."ya ce,
"To gobe zamu koma kasuwa kenan." Haka ya kaini gida
yana ta shi min albarka, sannan ya tafi gidan Fadima ya
kwana.
Washegari mun shiga kasuwa harda list din mutanen don
kada a manta, lallai kudi sun mutu a ranar, alheri sai
bawa ya dage, amma in kayi dadi ka ke ji, shi kuma
wanda ka wa yana jin dadi. Ya ce, "To wanene zai kai
musu?" Na ce, "Ka samu Hashim ka ware rana kayi ta
kai musu." Da suka dawo kuwa Hashim sai labarin yanda
Iyayen suka yi ta murna da godiya ya ce Abbanshi, Sarki
kenan, har gori ya mishi ya ce, "Hashim kalubalenka, sai
ayi koyi da Hamma." Na yi murmushi, na san kowa zai
yaba don kaya ne na alfarma da takalma da hula.
Hashim ya ce, "Allah ya nufe ni nima." Ranar ma godiya
yayi ta min, su Lamido ma suna ta shi masa albarka,
wanda ma baya nan in ya dawo gida ya gani sai ya kira
waya yana sa albarka. Allah kasa mu dace amin.
Saura sati biyu Sallah Abubakar ya ce min yana son ni
da shi mu tafi Umara, don haka ma in tashi muje inyi
fasfot. Na ce, "A'a da Fadi ya dace kuje." Ya ce, "Ba
zata iya zuwa ba." Na ce, "Ina tsoron abin da zai ja min
bakin jini cikin zuri'arku, amma ka je ka shawarci
Daada." Ya ce, "Shi kenan" Ko da ya samu Daada da
batun sai ta ce mishi ya bari mun je aikin Hajji
dukkanmu, kada ya zama abin tsegumi ace ya kai bare,
amma Hajji kafin lokacin ta haihu. Ya dawo ya ce min
bakinku yazo daya da Daada. Na ce, "Ka gani ko? In kaje
ka samu a addu'a." Ya ce, "Wannab ba sai kin roka ba.
Ni dai na so inje da ke ne saboda mu dan shakata." Na
ce, "Wata rana zamu shakata. Koda yanzun ma ai mun
sha iska." Ya yi 'yar dariya.da xai tafi ya bar ma kowa
komai, na ce xan je kaduna da salla, ya ce a'a in bari ya
dawo ma je tare na ce to.su Ummina sun xo min da salla
har da Yaya Umar, nayi murna sosai kwanansu 2 suka
tafi da Shadad, na ce su bar min Ummi in xamu xo sai
mu xo da ita. Bayan sallah da kwana 3 xaya dawo,nasan
kuma gidana xaya sauka, domin yana fada min irin yadda
yayi missing dina,ko na ce muka yi missing din juna.Tun
safe na soma shirya masa girki kala-kala da abin sha, jus
nayi mas kusan kala 3 n akuma hada nawa hadin mai
kyau nayi ta sha tun safe.misalin 3 ina tsaye gaban
madubi nayi adona ckn 1 daga ckn atamfofin daya siya
min,sam banji shigowarsa ba,sai dai ji nayi an rungeme
ni ta baya kamshin turarensa yasa na gane mijina ne.da
sauri na juyo muka makale juna cikn murna, ya sumbaci
lebunana, sannan ya ce bari mu isa gidan Fadi, sai in
dawo. In na xauna ba xan iya tafiya ba.xamu wuce ne da
Hashim daya dauko ni naga ba xan iya wucewa ban
ganki ba,na ce to in ka san ba xa ka dawo ba to ka wuce
da abinci.Cikin marairaita nayi maganar,ya shafi
kumatuna. kada ki damu d only yanxun xan dawo naji
gidan na kamshi na ce to "Da sauri ya shige mota suka
tafi.kafin ya dawo na kara gyara gidan, na canza kaya
doguwar rigar leshi nasa mai kalar sky blue, su hudu
suka shigo duk da Hashim.na jera musu abinci da na sha,
in adaga daki ina jiyo su suna santi.Hashim ya ce,
Hamma gaskiya xan kullo ma Hafsat kawance da Shatu,
ina son taxo ta koyi kalolin girkin nan, Dayan ya ce na
riga ka a xuci ka riga ni a baki, shi ko dayn ba shi da
mata, cewa yayi xaya kawo budurwanchi ta yi hadda.shi
kuma Abubakar sai murna da cika baki. fadi ya ke
"Matata yar baiwa ce, duk abubuwanta cikin ilimi ne da
daraja girkin Hafsat daban ce.Amma fa ba xa ku takura
min mata ba, da Ummi taxo tana kwashe kayan bayan
sun gama,Hashim ya ce ko dai xan tsaya nan ne Hamma
ka tsaya min a bani wannan in kiwatat?Abubakar ya ce
"Katon banxa wa xai baka?suka sa daria.Misalin karfe
tara saura muna ta shirin kwanciya, Fadi ta kira shi ya
daga ta ce"sweet hrt ba nan ka ke ba?ya ce "In ji wa?ta
ce Eh!! mana yi lassafi.Ni dai wlhy kada ma ka ce xaka
kwana can, don ba xan yafe ba.Duk ina jin su, kuma ba
gidanta xai sauka ba, saboda randa xai dawo gidana ya
tafi.Na ce to koma can din , ya ce ba xan koma ba, tana
xaton ban san me nake yi ba?ya share ta muka ci
soyayyarmu, dama mun yi rashin juna.Wata juma'a
misalin 3 muna cikin bacci wayarsa ta soma kuka, ni ce
na farka na daga.Sweet hrt na gnai a jiki na daga, Muryar
Goggo Jami naji tace, "Ina Hamma din?N ace "yana
bacci "Ta ce to tashe shi Fadi bata da lfy shi bacci ma
yake?a raina nace kada yayi? Namatsa kusa dashi na
shafa fuskarshi, ya rike hannuna zuwa kirjinshi, nayi
masa rada cikin kunne.
Mr Cool ka tashi yau twins zasu fito, Fadi zata haihu."
Firgigit! Ya mike ya zura jallabiyya ya dauki key din
mota.
Na ce yanzun zaka fita?" Ka bari a kira Sallah."
Ya ce ba komai kada ki damu, na ce to Allah ya raba su
lafiya." Ya ce "Ameen the only."
Takwas na safe na kira shi, ya ce har yanzu dai shiru, na
ce gani nan.
Na isa gurin na samu 'yan gidan su, sai su Rukayya. Shi
kuma can na hange shi tare da su Hashim da Usman
kaninshi.
Na gaida su Goggo Jamin, sannan na nufi gurinshi.
Rukayya harda cewa 'yan biyun nan suna ba mamansu
wahala, Allah yasa kada zuwan wasu yasa abin ya sake
rikicewa.
Wata da ban san ko wacece ba, ta ce ai mun rike Allah,
kuma sai ta sauka lafiya da izininshi.
Ban da lokacinsu bare amsarsu, don nasan dani suke,
gurin mijina ma ni na nufa.
na dube shi har yanzu ko? Na yi maganar ne cikin nuna
tausayawa da tausasa murya.
Ya ce, wallahi, na matso na kama hannunshi na dama na
matsa kadan. Ka da ka damu samu ruwa a tofa mata
addu'a, In shaa Allah zata sauka lafiya.
Goran Ruwa ya kawo na karanta mata, YA HAYYU YA
KAYYUM, YA ZULJALALU WAL IKRAM, BIRAHMATIKA
ASTAGISU, sau bakwai na ce ya bata tasha.
Da kanshi ya kaimata tasha, ya fito, ko minti ashirin ba a
yi ba Nurse ta fito da murna tana fadawa su Goggo Jami
ta sauka.
Kawai sai naji mutum ya rungume ni a bainar jama'a
yana fadin "Alhamdulillah." Usman ya ce "Aunty na Allah
ya amshi Addu'armu, sai dai kuma me? Maimakon biyu
sai aka fito mana da yarinya katuwa mai kyau.
Sai kace mamanta tayi kaki, aka amsa da murna ana
cewa ina dayan? Wannan ce Hassana kenan.Nurse ta ce
ai daya ce, ita kenan aka haifa. Yanzun haka mai jegon
ana gyara mata jiki.
Gaba daya sai naga jikinsu yayai sanyi, har shi kanshi
angon karnin. Usman ya ce amma 'yan asibitin nan sun
cika shegiyar karya, shine suka ce biyu?
Doctor ya fito, su Hashim suka bishi suna tambayarshi,
"dama daya ne? Ya eh ai dama daya ce duk scanning
dinta bai taba nuna biyu ba, wa ya ce biyu ne?
Abubakar ya ce "ita ce" likita yayi tsaki ya ce "haka
wasu matan suke yi ban san amfanin hakan ba, alhalin
sun san cewa akwai ranar irin wannan da za a kure su.
Ya dafa kafadar Abubakar "kada ka damu, ka yiwa 'yarka
addu'a Allah yasa mai albarka ce."
Duka suka ce "Ameen" Masu habaici da rawar kai kowa
dai baki tsuu, shiru kake ji. Kullum nake zuwa gidan mai
jego har ana jibi suna.
Ranar da ya kawo mata zannuwan fitar suna ta ce basu
yi mata ba, ranar ce ya amayar mata da takaicinshi a
gaban 'yan koran nata.
Ya ce "ki bini a sannu, banza makaryaciya, zan
maganinki, kuma in na dawo baki dauki kayan nan ba sun
zama ba rabonki ba.
Ki sani ko bari kika yi zan so shi, bare dan mutum. To
meye ribar karyar da kika yi kika sa muma muka yi?
Mutuncin ki ya zube a gurina da sauran mutane. Sannan
baki isa ki juya ni ba, kinfi kowa sanina.
Zata yi magana ta rike kugu, ya ce yi min shiru, in kin
furta wata magana zan bata maki yanzun nan.
Ta yi tsit, ya fice. Nan ta shiga kuka suna bata hakuri,
Rukayya tana cewa sai ta fadawa Dada da Abba.
Yarinya taci suna Nana Fiddausi, in da ni kuma na
shiryawa Abubakar kalolin girki kusan bakwai da kayan
drinks.
Suka yi walima, Ummi da kanwata Ummi sune yan taya
aiki.
Bayan suna da sati daya muka je Kaduna don maida
Ummi tare da dauko Shadad daga gurin babanshi.
Har da Umminsu ta mana rakiya don sun kulla kawance
da Umminmu,saboda xaman mota sai kafafuna suka
kumbura,sannan nayi ta shar amai,duk Abubakr ya rude
hankalinsa ya tashi.kafin kace haka na kwana
shrkaf.muna isa kaduna asibitin Garkuwa ya wuce dani,
da gudu-gudu aka kawo gadon tura mara lafiya aka yi
ciki dani,likitan yana duba ni yana mishi tambayoyi,tana
da ciki ne?ya ce kai bana xatao, sai dai ko in yanxun.
likitan ya maida allurar da yayi niyar yi min ya aje,yasa
aka tura ni xuwa dakin scanning, kusan min 30 aka fito
dani yaxo ya dauko ruwa aka yi wasu allurai a ciki,
sannan aka dora ni ,ana da nan bacci yayi gaba
dani,likitan ya kalle shi"matarka tana da ciki kusan
wata 5 ko ma fi,sai in ta farka nayi mata wasu
tambayoyi tukunna. Abubakr ya tsura mishi ido,kace
tana da ciki wata 5? likitan ya ce kila ma ya fi.
Abubakar dai yayi shiru,amma ba don ya yarda ba, ya
kira Umar ya fada masa kusan minti 30 suka iso dasu
Baabah.Sannan ban tashi ba, ya ce don Allah yaya
umar ya kai su Ummi gida don suna ta kuka,kujera
Abubakr yaja ya xauna ya rike min hannu su Baabah
sai waje suka fita don kunyar yanda ya tasa ni gaba
kamr xai cinye ni.ya kira su Hashim ya fada mishi su
Daada ma ya sanar da su,kusan wa daya na farka.Da
sauri ya tashi yasa hannunshi a kuskata, yana cewa
"Sannu Hafsat sannu.Na ce yauwa Na yunkura xan
tashi ya kama ni na xauna ya xauna gefen gado. Ina ne
ke miki ciwo yanxun?nace "Ba ko ina yunwa nike ji,
bakina ya cika da miyau,na ce xan xubar "ya miko min
wata yar tasa sannan yace bari in kira likitan.Da sauri
ya fita ya ce ma su Baabah na farka, suk shigo suna
min sannu, na amsa na ce ni babu gurin da ke min
ciwo,yunwa kawai nake ji (dama cin abinci a gurina tun
dana samu cikin nan kmr gara)suka shigo da likitan aka
ce su fita Abubakar kuwa xama yayi kusa dani likitan
ya ce "Madam

Please Login or Register in order to submit comment