Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi magun guna
ya sha, suka rubuta mashi wani tare kuma da ya rika
cin abubuwan kara jini tare da shan na kara ruwa
Hashim yaji mamakin ganin shi sharkaf a kwance, ba
wai ciwo bane, a a jikinshi a sanyaye yace, ina kaje tun
dazu? Ya kali Hashim na dan fita na motsa jiki, shine
nagaji. Hashim yace mai makon kayi mana magana
mufita tare? Har nace kodai kaje ka bada jinin ne? Na
tambayi likita yace an siyo jinin. Abubakar ya daure
fuska, in bata jini a kan me? Ko su samu ko kada
susamu ina ruwana? Hashim yace matsalaka kenan kin
fahimta, kana son yarinya har a gidan karuwai ana
dauko mace a aureta bare ita wanan da kadara ta fada
mata. Abubakar yace, kada ka daurewa karya gindi,
wanan ba kaddara bace. Ita kadara ma kanta mace ta
kama karuwanci sanan ace kaddara? Hashim yace, zan
so ka aje wanan kishin ka saurara muyi maganar.
Abubakar yace, amma tuni na fada maka banson jin
ko? Haushi ya kama hashim kada ka so zancenta,
amma ka iya labewa ka lekata ko? Abubakar yace me
zan leka? Hashim yace, zakaga kamar banganka ba ko?
Ya tashi ya nufi dakin Hafsa, lokacin har jinin Abubakar
ya soma diga cikin nata.
AL‘amarin so babu karya acikin shi, amma shi amma
shi kanshi Abubakar yana al‘ajabin irin son da yake ma
Hafsa. Likita ya tabatar bata dauke da cutar kanjamau,
domin tunda abubakar yace ayi mata gwajin (H I V)
hankalinshi yafi da tashi. Kamar jinin take jira, gari na
wayewa ta soma samun sauki, har tana tashi zaune,
kuma har da sallah. Mama da Rahama suna tayi mata
tsiya dama jini kike bukata, gashi har kin gyare. Itama
ta danyi yake, tace Rahama ina wayata? Rahama
tatashi ta balle jakar ta ciro wayar tana cewa. Ke
wayarki da ita da babu duk daya ne. Na dubeta da
alamun karin bayani. Tace, to tun da natafi da wayar
nan babu wanda ya kira ki. Na amsa ba tare da ce
mata uffan ba, sako nasamu kaina da rubutawa.
(ABUBAKAR SADEEQ) NASO IN MUTU SABODA NA
SAN BA ZAN TABA SAMUNKA BA, KA YAFE NI. INA
SO KA SANI CEWA INA MATUKAR SONKA, KUMA HAR
IN KOMA GA ALLAH BA ZAN DAINA SONKA BA. DON
ALLAH KADA KA MANTA DANI, DUK LOKACIN DA KA
TUMONI KA MIN ADU‘A
********
natura masa ne zan katse sakon ashe yariga yaje. A
zatonshi fadi ce, don kullun zata kira shi sau kusan 4
banda tex na kalaman so da kauna tare da bege. Sai
dai shi bai taba jin haka ya burge shi ba ko acikin
ranshi, sai dai bai taba nuna mata bai ji dadi ba. Sai
kusan minti goma sha 2 sanan ya karanta kusan sau 3,
sanan ya yarda ita ce. Yayi ajiyar zuciya sauki ya soma
samuwa kenan.
Da dare yayi yaje ya leka su ta window kamar yan da
ya saba duk dare in hashim ya yi dan bacci sai ya saci
jiki yaje yayi lekensu. Hashim yasha ganin sa, amma
bai taba nuna masa yasan yana zuwa ba. Zaune kan
salaya ya hangeta, hunnuwanta a sama hawaye na ......



Zaharaddeen shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 3-02
Posted by ANaM Dorayi on 10:53 PM, 26-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Hannuwanta a sama hawaye na sauka a kan kumatunta.
Lallai duk wanda ya ganta ya san tana cikin damuwa.
Maman rahama tana gefe kan tabarma tana bacci tamkar
yashiga yaga me tak ma kuka? Menene matsalar ta? Ba
shi da mai bashi amsa, haka ya cigaba da tsayuwa yana
kalonta har ta gama ta jin gina da bango, fiskarta na
kalon saitin window din. Da zata kula sosai zata
hangoshi, amma batayi tunanin da mitinin da zai fito
cikin sulisin daren ya zi ya tsaya ba. Yana kalon ta,
tadago ido sama alamun tana tunani, bakinta kuwa yana
motsi, ga alamu istigifari takeyi. Wayarta tana gefenta,
ya koma ya jin gina da bango, ya curo wayarshi yana
karanta sakonta. Nan take ya rubuta karya kike bakya
sona, kuma daka ki kara min tex. Ni kuma bana sonki, ba
zan aureki ba. Da ya tura sai ya koma leketa, da sauri ta
dauki wayar, ganin labar shi tayi dan mur mushi, amma
da ta gama karanta dan sakon sai yaga ta toshe baki da
da hannunta tana kuka tare da sake daga hannunta
sama tana fada ma Allah. Ya jingina da bango tare da
rintse ido. Hakika tana son shi, to me yasa ta fada mishi
ita karuwa ce a gaban Hashim? Sam baiji takun sawo ba.
Ya de idanun shi a hankali yana me fatan ace hafsa
ce,ganin hashim yasa shi yin kame-kame don baya so su
fahimci har yanzu yana sonta. Hashim yace, mr. Man ka
amince haryanzu kana son Hafsa, kulun ina jin fitarka
kana zuwa lekenta. Aure a gurinka yake in ba zaka
saurari ainihin kaddarar da ta hau kanta ba, to ka amince
muje gurin iyayenta don tautana batun aurenka.
Abubakar ya nufi dakinshi yasan dare ne kila tana ji.
Hashim ya biyo bayan shi suka zauna suna fiskantar juna
Hashim yace, na fada maka Rahama ta fada muna
komai. Ta tabatar muna fyade akayi mata. Yace, agaban
Rahama akayi? Ni dai kawai ina sonta zan aureta.
Sannan ina son kai ka rufa min wanan asirin, mubar shi a
tataba aure, don Allah kada ka bari dangi suji zancen
nan, amana na baka. Abu na gaba kuma muje gurin
iyayenta kafin mu koma gida. Hashim yace, haba nawan,
yaya ma ba zan rufa wanan asirin ba? Koda ban santaba
ai zan rufa mata, balantana kaddara ce ta sameta. Zuwa
washegari na kara samun sauki, har da wanka ina canja
kaya. Wayar Rahama tayi kara, tace min tana zuwa,
Sagir yana kiranta, tana zaton yana harabar asibiti. Nace,
to. Su 3 ta samesu cike da murmushi tace, Abubakar jiki
yayi kyau. Yace, wlh gashi ma an sallame ni. Hashin
yace, Rahama dama muna so ne kiyi mana cikkaken
kwatancen inda zamu samu iyayen Hafsa. Rahama tayi
shuru tana dan nazari, can tace ni dai a kwatancen da
tamun acikin labarin da tabani, ta ce mun a kaduna,
sunan unguwarsu rigasa. Layi kuma ko abuja road tace
min? Na dai manta. Sagir yace, ni anawa ganin Abubakar
ka bari ta kara samun sauki sai aje gaba daya da ita.
Hashin yace, shinema zaifi zuwa da sauki. Abubakar
yace, a a, ina da nawa dalilin zaku fahinci nufina daga
baya. Rahama abinda nake so kafin gobe ki dan
tambayeta cikin dabaru muji koda sunan layinsu. Rahama
tace to.
Ina kwance da wayan rahama a hannuna ina kalon
hotona, yawanci duk hotunan bikin ta ne tasa a ciki. Na
tsaida ido na a kan hoton abubakar me yasa ban fada
mashi gaskiyar lamarina ba?Me yasa nace mashi ni
karuwa ce, alhalin nasan wanan mumunan sunan da na
kira kaina dashi zai iya bina? Ko dayake inma ban fada
mishiba zaiji a wani gurin, cewa nayi ciki na gudu, tunda
babu wanda yasan cewa fyade akayi min. Wasuma zasu
ce masa ni karuwa ce. Amma da yaji abakina fa? Ko da
ya sake ji a wani gurin bazai ji komai ba. Rahama ta ka
tsemin tunani da cewa, hafsat ki tuna min kwatancen
layin ku, wai in kai shadad. Na dubeta banyi maki
kwatancen layin mu ba? Tace, kince abuja road, nace
Allah to ban san nace ba. Rahama tace, har sunan layin
kika ce ko me? Gidan wanene? Atake layinmu ya
bayyana a idona, ban san na furta gidan 12 layi na 3,
wasu suce gidan yawa. Na kali Rahama ina tuno rayuwar
da nayi a wanan gidan, ina kewar gidan ina burin in sake
zuwa gidan. Rahama tace mai zai hana in kin sami sauki
muje? Nayi kokarin in tare hawayena, amma ba zasu
tsaya ba saboda girman bakin cikin dake zuciyata. Nace
rahama lokacin zuwa na gida baiyi ba, tace saboda me?
Na sha fada maki abaya sai na kama aiki ko na sami
mijin aure. Rahama tace, yaushe har kika saki fuska bare
ki samu mijin aure? Taci gaba. Ba ma wanan ba, me
yasa kika cewa abubakar ke karuwa ce? Nace, Rahama
duk wanda zai aureni sai ya nemi asalina, kuma na
tabbata duk wanda yaje unguwarmu don neman labarina
za a fada mishi na shiga duniyar karuwanci,nakuma tafi
da cikin shege, wanene ma yasan munnir fyade yayi
min? Bale ma a dan kare ni? Shiyasa na fadi haka.
Rahama tace, kamata yayi ki bashi asalin labarin abinda
ya faru yanda zai fahimta, in sha Allahu zaya taimaka
miki. Nace nifa kinsan Allah rahama? Bana son
amaimaita min na baya, naga babu wata hanya da zan
kori Abubakar da ya wuce in fada mishi hakan dan ya
rabu dani. Duk da yanzu ina na damar hakan. Na dubeta
sosai yanzu bana jin kunyar in furta ina son Abubakar,
don bansan ina sonsa ba sai yanzu da na koreshi.
Rahama tace kila kiga ya dawo, amma in yazo kada ki
kuma kuskuren da kikayi a baya. Nace, Rhama na rokonki
dakada kimin karya don hankalina ya kwanta, na tabata
ko Abubakar yana shaye shaye ba zai dawo gareni ba.
Tuni na dangana dashi, tun ranar da na tura mashi wani
sako da dadare, kin ga amasar da ya bani nan acikin
wayata. Na sauke ajiyar zuciya tare da share wani
hawaye da ya biyo kan karan hancina yayi min dan
maimayi. Rahama na gane kuskurena da nasani nabi
innata nasan ba zan tozarta ba, zasuyi hakuri dangin
uwata zasu rikeni da ko na hadu da Abubakar bazanji
komai ba. Lallai barin gaban iyaye matsala ce katuwa.
Rahama tace, ita dama mace guri 3 yakamata ta
kasance, in bata gidan ubanta to a sameta a dakin
mijinta. Idanto ya kasance baki can to a sameki a kabari,
ta cigaba da cewa, duk inda mace take a sameta a
karkashin wani uba ko miji, ko wa, ko kani, ko daki. Idan
aka sami mace bata kar kashin ko 1, lallai ba wanda zai
ganta da kima ko daraja. Kare da doki suna iya kawo
maki hari tunda ke yar kanki ce, don haka duk lokacin da
Allah ya kawo maki miji to kiyi aure zafin da kika dauka
kan maza ba inda zaya kaiki, tunda sune a bokan
rayuwa.Rahama tayi wa abubakar text din kwatancen da
na ambata cikin hiran mu don haka washegari suka
dunguma suka nufi kaduna har da sagir inata yi wa
rahama mitar sallama in likita yazo ta fada mishi saboda
sagir na kashe kudi wanda a zatona shine me kashewa
ta ce min in nutsu in warware tas,sun isa kaduna
shekaru masu yawa bai tsaya a garin kaduna ba tun
daya bar ta sai de ya wuce ta a mota tambaya suka yi
aka nuna musu rigasa haka ma abuja road sai dai sun
sha wahala da ta sama suka yi mamakon ta kasa sun
shiga layi na ukusun tambaya gidan yawa amma babu shi
sun zaga sun gaji har sun fita daga abuja road sun fada
makarfi road
Abubakar ya ce mu dai koma kan abuja raod din mu sake
yin tambaya daga bisani suka yi tambaya a wani
masallaci da ke layin na ukun bayan sun idar da sallah
nan mutane suka basu shawaran suje ta kasa Ikon Allah
suna shiga layi na uku Abubakar ya gane gidan su Hafsa
domin tsawon shekaru gidan yana nan yanda yake baa
kara komai ba saidema kara lalacewan da yayi suka
tsaya kusa da gidan yara nata wasa a kofar gidan cikin
kasa sagir yace kana da tabbacin cewa nan ne gidan
yaya ma akayi ka sani abubakar yace nazo shekaru da
dama bayan fitowar yarinya daga gidan yasa su yin
shuru yar doguwa marar jiki tana sanye da doguwar riga
ta farin yadi da kore kalar tutar nigeria gadukkan yan
kaduna duk wanda ya ganshi yasan cewa yadi ne na
makarantar primary ta gwamnati tana rataye da yar jaka
ta buhu mai dauke da littattafanta na makaranta kafarta
sanye cikin sandal na roba wanda igiyoyinsa suka
ciccire,Abubakar gabanshi ya fadi, tamkar hafsat a
shekarun baya. Yace yanmata zo mu tambaye ki mana.
Ta tsaya nesa dasu, abubakar yace nan nan gidan su
hafsat? Ta maimaita sunan hafsat? Yace, eh. Tayi shuru
tana son tunano wacece hafsat a cikin gifan nan? Ta
dubeshi karama ce? Yace, baba ce, suman mamanta
inna ta zaro ido inna? Yace eh. Duk yan dakinsu suna da
labarin hafsa yayarsu, duk da itace karama kwarai a
lokacin da abubuwan suka faru ba zata mance da sunan
hafsa ba. Sai dai kamanin hafsat sun bace mata. Inna
kuwa ai uwarsu ce, wace babansu ya kora sanadin abin
kunyar da akace hafsat tayi. Ta dubeshi tace, hafsat
bata nan, hakama inna. Yace, ina suka je? Cikin kagara
tace, nima ban sani ba. Inna dai tana funtuwa. Yace, to
baba fa? Ta nuna gida da yatsa, yana ciki bashi da lafiya,
sagir yasa baki. Kice masa yana da baki. Tace, saidaifa
ku shiga, don baya iya fitowa. Hashim yace, to fada
masa sai mu shiga. Tana juyawa, sagir yace, wanan
yarinyar tana matukar kama da hafsa. Abubakar yace,
donma baka santa tana karama ba, da cewa zakayi
itace. Tafito tace, yace in shugo daku. Suka rufe mator
suka bita. Lallai gidan yawa ta sunan nanshi inji sagir.
Kansu a kasa saboda yawan matan gidan da yaransu,
wasu kuma suna wasu ayyukan. Sun dan gaisa da
wadanda suke bakin hanyar zuwa dakin, yarinyar da ta
shugo da tabarma ta shinfida musu a gefe suka
zazzauna suna fuskantar tsohon. Yana kwance kan
tsohuwar katifar shi, wadda ta lakume. Suka gaisa, dakin
yayi shuru lokacin yarinyar ta kara dawowa da kwanan
sha na silba mai dauke da ruwa ta dire masu. Baba yace,
kai cema babarku ga baki. Itama ta shugo su gai sa.
Baba yace, kin shaida su? Tace, a a yace samari daga
ina? Abubakar ya zunguri sagir, nan take sagir
yace."Baba mu baki ne daga Kano."
Baba yace, "Kano gurin wa kenan?" Ya ce, "Ba za ka
shaida mu ba, ni sunana Sagirn wannan kuma Abubakar.
Sai kuma wannan Hashim." Sagir yayi dan shiru saboda
tunanin ta inda zai fara maganar.
Can ya ce, "Wato Baba za ku ji mamakin cewa mun zo
neman auren Hafsat ne."
Baba ya yunkura ya zauna wanda baisan lokacin da yayi
hakan ba, domin in zai irin wannan zaman sai an kama
shi.
Ya ce, "Hafsatuna?" Hashim ya ce "Ita" A rude Baba ya
ce, "A ina kuka ganta? Don Allah ku fada min, kun ganta
ne?"
Tausayi da kaunar tsohon ya ratsa zuciyar Abubakar, ya
ce "kada ka damu Baba, Hafsat tana nan lafiya."
Ya ce "Alhamdulillah, Allah yasa ba irin mafarkin da na
saba yi bane, tare kuke da iata?
Hashim ya ce "Ba mafarki bane Baba, kuma ba tare
muke ba." Ya nuna Abubakar. "Ga mai sonta da Aure
nan, mun zo ne mu sanar da kai magabatanmu za su zo.
Sai dai matsalar da muke tunani kada su zo kuma wani
ya basu labarin cewa ta bar gida. Kila sanadin hakan
iyayen mu suki amincewa."
Baba ya ce "Wannan ba matsala ba ce, in sha Allahu,
Amma kafin nan ina son Hafsat ta zo gida, yarinya tafi
daraja idan tana gaban mahaifanta."suka ce To Insha
Allah za su kawota, ko kuma su tafi da wani ya ga inda
take.
Baaba ta ce, "Kai amma wannan abu ya yi dadi, amma
ku jira wanta yanzu sai ku gaisa, batun zuwa kuwa nice
zan biku, ko kuma muje tare da Umar wansu din." Suka
ce A kira shi. Sagir ne ya dauki lambar, bugu daya ta
shiga ya dauka tare da Sallama, Sagir ya amsa ya ce,
"Mu baki ne daga Kano, gamu nan gurin Mahaifinku,
zamu samu ganinka?" Ya ce, "Lafiya?" Sagir ya ce,
"Lafiya lau." Umar ya ce, "To gani nan zuwa, zan shigo
layin da fasinja." Sagir ya ce, "To."Suna zuwa kan layin
Umar ya cema kwandastansa ya kara dasu shi zai shiga
gida, ya basu hannu suka gaisa sannan ya yiwa Baba
sannu da Jiki. Cikin doki Baba ya ce, "Jiki da sauki, sun
zo ne da labari akan Hafsatuna, abin dadi har da mai son
aurenta, gashi nan tsakiya." Da tsananin mamaki ya ce,
"Da gaske kun ga Hafsa? Allahu Akbar!!! dama tana
raye?" Sagir ya ce, "Tana raye." Umar ya ce, "Ikon Allah!"
Baba ya yiwa Umar bayanin komai da yanda suka yi.
Umar ya ce, "Baaba ki zauna ni zan je naga inda take
kafin, in yaso kwaje daga baya." Baba ya ce, "Haka ma
yayi Umar." Umar ya ce, "Shawarata anan ko za a ce
bakin suje can Funtua wajen Inna a karbi auren?" Sai
Baba ya ce, "Ba komai nan ma yayi Umar. Allah shine
mai yanda ya so."Umar ya shiga motarsu, inda suka je
gidanshi suka ci suka sha, sun huta sosai, sai karfe 5
suka ce zasu tafi.
Abubakar ya kasa hakuri ya ce, "Yarinyar can tana kama
da Hafsa." Umar ya ce, "Ummi, 'yar autarmu ce." Ya ce,
"Masha Allah." Duk yaga sauran kannanta yanzun saura
Inna, suna gidanma Umar ya kira wayarta, bayan sun
gaisa ne yake fada mata cewa cewa Wadansu bayin
Allah ne suka zo da labarin Hafsatu, cikinsu har da
wanda zai aureta. Cikin tsananin mamaki ta ce, "Da
gaske kake?" Ya ce, "Gasu nan ma." Ta ce, "Harda
Hafsat din?" Ya ce, "A'a, zan dai bisu muje in ga gurin da
take." Ta ce, "Ko zaku biyo mu je?" Ya ce, "Kada ki
damu Innarmu ni kadai na isa, tunda gida zata dawo."
Inna ta ce, "To."Biyar da rabi suka dauki hanyar Kano su
4 ne. Suna hira a nan Umar ya samu wadan su labaran
game da Hafsat, nan ne ya ji cewa bata san sun zo ba,
bata da lafiya don haka ya ce, "To in mun je ku bari in
fara shiga."Kusan karfe 8 suka iso Kano, sai da suka yi
Sallar Isha'i sannan suka isa gidansu Rahma. Tana ganin
Umar ta gane dan'uwan Hafsa ne, saboda kama ta jini.
Da sun ce a bari sai da safe a je gurinta, Umar ya ce shi
kam yanzun yake son zuwa. Dole suka tafi, daga bakin
kofa suka tsaya Umar ya shiga da sallama.Mama tana
sallar Isha'i, ni kuma ina bakin gado. Ina jin a jikina
tamkar wani bakon al'amari zai same ni. Muryar Yaya
Umar ta katse ni, da sauri na dubi kofar, zumbur na mike
tsaye jikina yana kyarma na ce da sauri, "Yaya Umar!
Yaya Umar kai ne ko mafarki ne?" Ya yi murmushi, "Ni ne
Hafsa." Na zuba masa ido, ya sake zama magidanci, ya
tako ya rike hannuna, na ce, "Kai da wane ne? Wa yace
maka ina nan?" Ya zaunar da ni a bakin gado ya ja kujera
ya zauna dai dai lokacin da Mama ta idar da Sallah.Na
ce, "Mama ga Yayana Umar." Ta juyo suka gaisa, su
Sagirr suka shigo har da Abubakar. Shi na zuba ma ido
tamkar wadda na warke makanta. Shi kuwa ya hade rai
kamar wanda zai fadi sakon tashin bom.
Mama kadai ya gaisar, bai kalli inda nike ba ya ci gaba
da karanta wata takarda da aka lika a jikin bango, ta
masu gargadin ciwon kanjamau. Hankalina ba ya tare da
su, don haka ban san me suke tattaunawa ba, yau wane
irin mafarki nake yi? Ga Yaya Umar ga Abubakar?
Mutumin da na cire rai da sake ganin shi, ya dawo ne?
Ko kuma daman yana nan? Ashe wai a fili nayi zancen,
sai na ji Sagir ya ce, "Wa?" Na dube su cike da damuwa
ina zare ido. Na kalli Abubakar, "Don Allah ku fadi min
ina mafarki ne?" Sagir ya ce, "Hafsa mune muka zo da
Umar." "Kun je gidanmu ne? Wa ya kaiku?"Nan take na
mike don watsa ruwa na fito na jawo jakar Rahma na
murza hoda. Ta ce, "Iye! Har da su hoda? Kina son birge
Abubakar." Na ce, "Ina ruwana da shi?" Mama ta ce,
"Sauki ya samu ta 'ki saka hoda? Har da kwalli radau
kayanki." Na ce to. Sannan na ce Rahma ta dan hada
min tea.
Lokacin da Sagir ya isa masaukin nasu, ya same su suna
karyawa, hira suke yi inda Umar ya basu labarin barin
Hafsa gida, ya ce kowa ya sha mamakin faruwar
matsalar saboda Hafsa nitsatstsiya ce, ko yawace-
yawacen nan na 'yan mata bata yi, bata ma da kawaye,
son bokonta ne yasa wannan saurayin ya yaudareta har
ya kai ga yi mata ciki, kasan mata da karamar
kwakwalwa, idan saurayi na kashe musu kudi babu wuya
an yaudaresu. Hashim ya ce, "Labarin da Rahma ta
bamu fyade yayi mata shi saurayin." Umar ya ce, "Ta
yiwu haka ne, don lokacin da abun ya bayyana Babanmu
bai kwantar da hankali an ji yadda lamuran suka faru ba,
kawai ya kore su ne."
Abubakar ya ce, "Ta bakin Umar ne mace idan tana son
namiji ta hadu da Shaidani, to ba zata yi wuyar bada kai
ba." Sagir ya ce, "To duk dai komai ya wuce. Allah ya
tsare mana zuri'a kuma ya rabamu da rudin shaidan."
Ameen ya Rabbi, suka amsa.
Ran Abubakar fa a bace yake amma bai nuna ba, a nashi
ganin ba wani fyade, ita dai dan tana son shine taje don
sakarci ta bashi kanta, har saida yayi mata ciki sannan
za tace yayi mata fyade, dan ta kare kanta ne kawai, wa
ma yasan adadin kwanciyar da tayi da shi. Ya ja
tsaki.Sun shigo ina shan tea, na ajiye ina kallon Yaya
Umar na ce, "Ina kwananku?" Suka amsa amma ban da
Abubakar wanda ke latsa wayarshi, a raina na ce,
"Mutumin nan fa har yanzu bai huce ba." Na dubi Yaya
Umar na ce, "Ina Baba da su Baaba?" Ya ce, "Suna nan...

Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 3-03
Posted by ANaM Dorayi on 09:35 PM, 27-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Ya ce, "Suna nan, Baba ne dai ba lafiya, ya fi shekara
baya fita." Idanuna suka ciko da kwalla na ce, "Allah ina
zaton halin da na saka su a ciki ne ya sa shi rashin
lafiya." Umar ya ce, "A'a lalura ce kawai." Na ce, "Ina
Ummi?" Ya ce, "Ummi ta yi tsawo, sai kin ganta." Na ce,
"Inna fa?" Ya ce, "Inna tana Funtua." Na tsura mishi ido,
"Me take yi a can? Ko suna da dangi ne?" Ya ce, "A'a,
tayi aure can da Yaranta ma 2." Nan take na dafe kirji,
kuka ya kuma kwace min na ce, "Ban yiwa Iyaye na
adalci ba, sun soni, sun min dukkan abinda iyaye kewa
dansu daidai karfi, amma ni sai na tarwatsa su." Yaya
Umar ya ce, "Komai mukaddarine kada ki damu." Tsaki
Abubakar yayi tare da tabe baki, ni dai na kauda kaina
gefe.
Likita ya shigo a nata 'yan hirarraki ya bani sallama.
Daga nan Sagir ya kwashemu mu 6 banda Abubakar, don
yace muje kawai, muka fice zuwa gidana.
Mama dama ita bata shiga ba gidansu ta wuce, sai ga
Shadad ya rugo da gudu, Mama ta ce mishi na dawo
shine ya taho. Mama tana barinshi gida ne saboda rigima
da yake yi a asibiti, ya fada jikina yana min oyoyo Aunty.
Umar ya zuba mishi ido, shi kam sai yanzu ya tuna fa
ashe da ciki na bar gida, ya ce, "Dan da kika haifa
kenan?"nace shine, sunansa shadad, idanuna suka soma
kawo ruwa, nace jeka gurin kawunka, yamike yaje gurin
umar, umar yace tabbas wannan dan munnir ne, kamarsu
ta baci, kinga ko dolensa ya amshi danshi, nace ai yaya
wlh baxan bashi yaron nanba, koshi ya bukata, inkuma
kunsan zakuce in kaishine tobazan koma gdaba, daganan
gabama zanci.... da sauri umar yace, toshikenan anbar
maganar, kusan karfe 1 har sagir da hashim sunyi mana
sallama, sai kuma gasu sun shigo da kayan abinci,
karamin buhun shinkafa ne da taliya, sagir ya mikoma
rahma kudi batare da yayi mata mgn ba, yafita. sannan
ya kirata a waya, wai tabani inji abbkr ne, amma tace inji
sagir, rahma kuwa tabani tace inji sagir, nace kaiba zan
amsaba kashe kudin yayi yawa, dubi kwanciyata a
asbitifa, tace a'a asbitinki ina ganin hashim ne, na amsa
tare da cewa, ko wanene ma dai nagode.Rahma ce
tadafa mana abinci mukaci, misalin karfe 3 yaya umar
yashirya tafia kd, nace yasakebi ta gidansu maman
rahma yayi mata godia, don tun bayan fitarsu sagir na
bashi labarin komai, tundaga tafiyata har iyanzu har
tsakanina da munnir ban boye masa komaiba, yacemin
yana ganin munnir shima a wata jibgegiyar mota lkc
zuwa lkc, yafadamin dukkanin abubuwan da suka faru
bayan barina gda, nayi kuka sosai, yace karna damu
komai yafaru da mumini daga Allah ne, kuma sakayya
tana nan tafe tsakanina da munnir, insha Allah sai kowa
yagane fyade ya miki, nidashi da rahma mukaje gdansu
mama inda yayi mata godia bisa godiya bisa rkon
datayimin, yayi addu'a ga likita hindu wadda tamin gata,
munayi masa rakiya saiga sagir da abbkr, yace da umar
yadan jirashi.suka shigo gurin rahma ashe sallama yayo
mata, suka kira umar gefe sukayi sallama dashi, sannan
abubakar yabashi kudi tare da tabbatar mishi da cewa
tsakanin gobe zuwa jibi iyayensa zasuzo, don haka
yasanar dasu, bansan mesuke tattaunawaba, yazo dai
yacemin zasu saukeshi a gareji, nace to saimunyi waya,
don nakarbi lambarshi, yasoma yakira inna muyi mgn
nace mishi a'a baxan iya mgn awayaba, washe gari naje
skul, ashe na danji sauki, kuma yanzun na rage kuncin
zucia kamar da, ina zaune ina krt wata baiwar Allah
tayimin sallama, nakalleta tanamin murmushi tare da
sallama, na amsa mata nima cikin sakin fuska, tace
nadaina ganinki kwana 2 lfy, naga kindan rame, nace
banda lfy ne, har na kwanta asbiti, taxauna tare da cewa
eyya, Allah yasauwake, saita danyi shiru daga baya kuma
tacemin sunana sa'adatu sulymn, kekumafa? nace
sunana hafsa, tacemin inaso muzama kawaye inba
damuwa, nace bakomai, mun danyi hira, sannan tatafi,
abinda yafi cizon raina yanzu a wane matsayi abk ya
ajiyeni? da nayi zaton yabarni har abada, amma sai gashi
yazo asbiti, duk dabaimin mgn ba, kuma naganshi a
layinmu yazo gidan mama yakira yaya umar, kenan har
yanzu yana sona? bari in isa gda in kirashi, ta gidan
rahma nabiya, ban boye mata komaiba abinda ke raina,
itama ta amince da cewa inkirashi mu gaisa na masa
godia, donfa gaskia shine ya nauki nauyin asbitinki, tace,
hatta jinin da aka karamin nashine yabada, amma baisan
cewa su sagir sun saniba, tace keko shinkafar nan da
kudin nan shine yakawo nace sagir ne don kada kiki
karba, bayan tayi shiru, sai kuma takara da cewa, abk
yana sonki, matsalar karuwancin dakika dorawa kankine,
kinsan maxa sunada kishi, kuma gaskia yana kishinki,
yakuma ki sauraron kowa cikinsu sagir

Please Login or Register in order to submit comment