Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni ya kalle shi, sam bamu sani
ba, sai dariyarshi muka ji sannan ya ce...Uncel ashe
kuma kun iya kallon kuda?" shine yayi saurin janye
idanunshi, ya dubi Shadad. Me ka ce? Shadad ya ce, Irin
kallon kudan da yaran ajinmu suke yi, wai kada a kyafta
ido.. Ni kam lumshe ido nayi, bn so shadad ya katse mu
ba, domin ina karanta abubuwa da dama a cikin
yalwatattun idanunshi., Jikana a mace naja filo na sulale
na kwanta, Jim kadan na jiwo wayata sbd jin shigowar
text. Na kalle shi, sbd ganin lambr shi ce mai dauke da
sakon,shima ya dan kalle ni sannan ya maida kanshi ga
Shadad. Na bude sakon,cewa ya yi "KIN YI KYAU."
Murmushi ya su6uce min,dadi mara misltuwa ya rufe ni.
A hankali na dago kai na kalle shi, shima ya dan saci
kallona, sannan ya dauke kai tamkar ba shi ba. Na dinga
kallon kyakkyawar fuskarshi, Shadad na ta krt, bana
zaton ma Uncel din yana tare da shi, don waya yake
dannanwa. Wani sakon ya shigo wai "KALLON FA NA
NAWA NE? na kuma dubn shi, sannan na rubuta cewa.
KALLON SO NE.na tura mishi,ya dago muka hada ido.
Nayi saurin sunkuyar dakai. Ya mike tare da cewa,
"Shadad zo muje." Na dube shi, Ina za ku?" ya ce, Tadi
gurin budurwata." Na tsuke fuska,ya ce "Shadad zaka
gurin Antyn nan me baka ice ream?" Da gudu yasa
takalmi "Za ni Uncel, zata bani da wannan biskt din mai
dadi?" Gabana ya fadi, ko dai gaske ne? nayi shiru raina
6ace . Abubakar yayi murmushi mai sauti, cikin jin dadi
ya ce Zata baka. Suka fice. Na rasa me ke min dadi,
Rahma ta kira ni tana min tsiya,wai miji ya dawo in dai
kokarta in shawo kanshi. Cikin yanayin tausayi na ce,
"Uhm! Wane shawo kai? Mu2min da ke nemn wani
auran? Rahma ta ce, Daina fada min wannan
zancen,tsokanarki kawai yake yi, duka-duka yaushe aka
yi abin? Amma kada in katse ki, menene dalilin da yasa
kika fadi haka?" Na ce, "Tun kafin yace yana sona ina jin
shi yana cewa za shi tadi, su fita shi da Shadad. To yau
ma yana ce ma Shadad za shi gurin Aunty yaro ya hau
murna, har da cewa za'a bashi irin wannan biskit din mai
dadi!" Rahma ta ce, "Kika sani ko wata mai sai da kayan
kanti ce da suke sayayya yake ce mata AUNTY?" Ta ci
gaba, "Ke ko bama haka ba Abubakar ba zai tarki wani
aure yamzun ba, kiyi aiki da hankali mana. Kishi ya rufe
miki ido, baki ga ko ke baki soma cin amarcin ba?" Na yi
murmushi na ce, "Ni ko da har naji haushi." Ta ce, "Don
Allah kiyi amfani da matantakarki ki fizgi mijinki." Na ce,
"To Rahma duk na kasa gane mishi ne, amma yau da
sauki tun da har yaba kwalliyata ya yi." Rahma ta ce, "Ki
yi wadda tafi ta kafin ya dawo, ki ajiye duk wani taurin
kai ko shariya da jan aji, ki zuba basirarki ki samu ki
kwato shi gare ki." Na ce, to na gode.
Dambun shinkafa na mishi wanda na cuda shi da nama,
karas da kabeji gami da koren wake. Gida ya dime da
kamshi, na hada mishi jus din kokumba da abarba da
kwakwa, na nike su a blender na tace, na saka kankara
da flavour. Bayan na kammala na je na tsala wanka tare
da yin Sallar Magriba, nayi shafa, wata jar atamfa (java)
na saka mai fulawa blue, na gyare gidan tsaf na yi
shimfida a tsakar gida na jera masa, na kunna masa
turaren wuta ko ina ya dauki kamshi.Shi da Shadad
kawai suke 'yan zantukansu, ko nace yake taya shi
shirme. Kusan goma saura ta ce, "To Madam ni zan tafi
na kwanta." Muka yi masa rakiya, na yi Sallar Isha'i tare
da Shafa'i da wutiri na kwanta, zan soma addu'a sai naji
shigowar sako, wanda na zata shine wato Abubakar. Na
bude, cewa yayi, "Ban taba cika ciki irin na yau ba,
abincinki yayi dadi, zan zo in miki kyauta kuma ina son ki
zabi abin da zan baki." Na yi murmushi na lumshe ido,
zuciyata tana wassafo burina, na rubuta cewa, "Duk abin
da ka zaba min da zaka barni ma sai in ce yaba min din
da kayi ma kyaute ce a gurina." Da ya karanta sai ya ji
dadin lafazin, don haka sai ya sake rubuto cewa, "In sai
miki turare? Ko in canza miki waya? Ko kin fi son in
canza miki wani gida kafo mai tsarin zamani? Don
lafazinki yasa naji cewa dole ne ma in miki kyauta." Na
yi shiru ina nazari, wato Abubakar yana so na dinga nuna
kulawa gare shi, in ko haka ne zan yi ta nuna kulawata a
gurinsa, sai na rubuta cewa, "Duk wannan basu yi min
ba, tunda kace in zaba aba abu daya nake so, ka yarje
min in fada?" Da sauri amsarsa ta shigo ya ce, "Eh, fadi."
"Son ka da kulawarka kurum nake so, in zan samu sun fi
duk wani abu na kawa ko na dadi da zaka bani." Ya yi
shiru yana maimaita zantukan, sai kurun na ji kira, na
daga tare da yin sallama kasa yanda ko wani na kusa da
ni ba zaya ji ba, ya amsa min sallama shima cikin wani
sauti mai nuna cewa muryata ta ratsa shi ya ce,
"Hafsah!" Cikin wani irin sauti ya kirani, har yatsana naji
nima nace, "Sadiq!" Ya ci gaba, "Ni naki ne, sona ke
kadai yake naci, kuma zan kula dake, wannan kawai kike
so?" Na saki ajiyar zuciya, "Wannan kawai shine burina,
na gode." Ya ce, "Nima na gode. Ki yi bacci..........


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 4-03
Posted by ANaM Dorayi on 06:39 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Ki yi bacci mai dadi tare da yin mafarkina." Na ce,
"Kullum cikin yin mafarkina ni ke, ina sonka sosai." Na
kashe wayar don jin nauyin furucina, na dauki filo na
rungume na lumshe ido ina tuno fuskarshi.
Shima a nashe gefen ma filon ya manna a kirji yana jin
dadi. Nan take kuma sai wata zuciyar ta ce masa,
"Yanzu kai saboda yarinyar da ta tabbatar maka da cewa
ita karuwa ce ka ke wannan?" Nan take kuma sai ya saki
tsaki tare da yin jifa da filon, zuciyarshi ta ci gaba da
wassafo mishi cewa, "Ba wani son da take maka, wanda
take so shi daya ne, tunda har ta bashi kanta. Kila ma
da zai dawo yanzun da ta nemi ka barta ta koma
gurinshi." Take ya nemi farin cikinsa ya rasa.
Lokuta da dama wannan tunanin ke sa shi jin haushin
Hafsah.......
A zato na zai shigo da wuri, don haka na shirya masa
abin kari, sai ga sakon shi ya shigo, "Madam ki yi hakuri,
kila ki zaci zan shigo, zan duba ma Dada wasu daga
cikin (super market) dinta. Idan mun gama da wuri zan
zo da wuri, in bamu gama ba ki dubi hanyata da rana.
Ina fata kina cikin koshin lafiya?" Lallai Abubakar zai
cika alkawarinsa na kula da ni, to nima Insha Allah zan
kula da shi. Na bashi amsa da cewa, "Lafiya lau (Hayate)
rayuwata, Allah ya sa ka gama abubuwan da zaka yi
lafiya, ya kawo min kai cikin kwanciyar hankali."..
Duk da cewa har Abubakar ya bar Kano babu wata
mu'amala ta auratayya da ta hada mu, ban damu ba
saboda ya nuna kulawarsa gare ni. Ya bani kudi, ya
canza min waya zuwa (BB), ya kara min abinci. Haka
nan ko da ya tafi ya kan kira ni sau 3 a kullum, nima
kullum na ke kiran Mahaifanshi da safe in gaishe su,
haka nan Lamido da Matanshi kullum sai na kira su cikin
girmamawa na gaishe su har muka kammala Jarabawa.
Lokacin yayi tafiya zuwa India akan harkokinsa, na ce
mishi, "Tunda muna hutu har da Shadad ina son inje
Kaduna da Funtuwa da Malumfashi." Ya ce shi kam bai
yarda in je Kaduna ba, amma in je Funtuwa gurin Inna in
kwana 2, Malumfashi kwana 2. Sagir zai sani jirgi in
wuce Yola. Na ce masa, "To na gode." Don na lura baya
son gayya.
Washegari Sagir ya zo ya bani kudi dubu talatin, wai inyi
tsaraba in ji mijina. Na yi godiya shima na tura masa da
sakon godiya, sannan na ce, "Ko zan iya zuwa kasuwa
mu yo musu tsaraba?" Ya ce, "Ki je amma ga sharudda
na, ki saka katon hijabi, sannan ki kausasa murya yayin
cinikayya da maza." Dariya sosai na yi, sannan na tura
masa cewa, "Zan kiyaye Insha Allahu."
Innarmu ta yi murna sosai da ganina, mun yi hira sosai
mijinta da 'Ya'yanshi ma sun nuna jin dadinsu da zuwana
tamkar sun sanni. Na bata tsarabar ta, kwanana biyu na
wuce Malumfashi, daga can na dawo Kano. Sagir da
Rahma suka sani a jirgi sai Yola. Hashim ne na samu
yana jirana ni da Shadad, masu aiki ne suka taya ni
gyaran sashen. Daga nan na fitar ma da 'yan gida
tsarabarsu. Washegari da muka yi waya na ce masa,
"Zan je gidan su Dada." Suma na kai musu tsarabar su
Sabulai, turarurruka da 'yan kunnaye. Ummi kuma na sai
mata wata doguwar riga mai kyau, tayi ta tsalle tana
rungumeni, Rukayya kam sai fushi da harare-harare.
Ban so jikina ba na amshi Dada da girki, dama ita da
Rukayya ne, da kyar ta barni, Rukayya na ganin Daada ta
fita itama sai ta bita, ta ce, "Koma mana ku gama." Ta
ce, "Toh!" Da ta dawo sai ta samu guri tayi zamanta tana
latse-latsen wayarta. Ummi ta shigo, "Aunty yaronki yayi
bacci." Na ce to. Ta ga ina yanka albasa ta amsa.
Shinkafa ce fara da miya, kuma ba mai yawa bace tunda
basu da yawa a gidan, nan da nan muka kammala. Lallai
girki hannu ne ba cika kayan miya ba ne, to duk abin da
suke sawa suka bani amma sai gashi suna ta santi, illa
Rukayya da takici wai ita sai dai ta dafa Indomie. Daada
kuma ta ce bata isa ba. Na kai har bayan la'asar sannan
na shirya muka koma. Daada da Abba sunata shimin
albarka. Ai hutun nan na saki jiki cikin dangin mijina don
jan su nake jikina, na kuma saki hannuna, kyauta tana sa
dangin miji su soka.Wata rana matar wani wansu ta
haihu,ya kaira ni na fada mishi, yace duk abin da ya faru
nan ckn danginsa to inje.ummi ce taxo muka je
barka,ranar suna ma ita ce taxo kafin na shirya na bata
kudi ta siyo min kayan baby na hada da turmin xani na
shirya muka je.Mai jego tana ta godia,duk wanda yaxo
sai a ce ga kayan barka da Amaryar hamma ta nbata,sai
godiay ake min.can muna shirin tafia sai ga Fadima ta
shigo cikin isa da jin kai,da muka hada ido sai na fadada
fara'ata,duk da cewa gabana ya fadi.Itama nata gaban
ya fad, in anyi la'akari da aynda nan da nan ta canxa.ta
zauna can kusa da yan'uwansu,huk da haka na bita na
gaisheta,da kyar ta amsa ba tare da ta kalle ni ba kuma
ciki-ciki.Sai yatsina taka tana harare-harare,ni dai sai
mana mike nayi musu sallama na fita na kira Ummi muka
tafi.Duk wata kulawa Abubakar yana bani,ko da ya dawo
gidana ya sauka,gadona ne kurum baya kwana.Ni kuma
ban taba nuna mishi ba,du da cewa hakan yana
damuna,hutuna ya kare ya maida ni Kano.Ya siya min
gado da sauran abubuwan bukata,ya kuma yimin
alkwarin cewa in yaxo xaya dinga koya min mota saboda
ya saya min don xuwa mkrtn.duk da cewa karatun nawa
karashe ne kowa ya ganni sai yace nayi kyau
Wata rana Umar ya kira ni yace jikin Baba ya tashi,
yanxu haka suna asibitin Dutse.A rude an kira Abubakar
a ways, yace in jira shi yaxo gobe muje, sai nasa masa
kuka tare da cewa yayi hkr in je yau.Ina ta rokonshi yace
shi dama baya son motar haya ne, amma in tafi in kuma
kula da kaina,tare da shadad muka tafi,Baba yana jin
jiki,na yi ta kuka su Babasuna ta bani hkr,wai ai jkn ma
da sauki.WashegariAbubakar ya iso,nan take ya kira
liktansu don suna da asibiti nan kaduna.Cikin awa guda
aka canza masa asibiti.Masha Allah, zuwa washegari jiki
yayi kyau. ABUBAKAR YA XUBE MIN KUDI MASU dama
sannan,ya tafi.baba dasu Baabah sai godia.
Na zo na zuna ina tunanin dame xan saka ma Abubakar,
abubuwan da yake min? gashi yaki ya bani dama in nuna
masa irin dumbin son da nake masa. na fito dga asibitin
ina rike da hannu shadad muna jiran mashin don xuwa
gidan Umar. Wata dirkekiyar mota ta tsaya gabana, nan
nan na hade rai tare da cewa yan'iskan mutane ba dama
suga mutum su kyale. kofofin motar suka bude a lkcn
guda,sai kawai naga Munnir. nan take wani irin bacin rai
ya xiyarce ni. Yace"Hafsy manya" nace cikin ihu kai!kai!
mallam kada ka akra kiran sunana. naja hannun shadad
muka yi gaba, ya biyo ni. Ki tsaya ina so ne muyi mgnr
dana? Cak!na tsaya tare dayi mishi wani mugun
kallo."Ba ka da daa gurina, ka fita hanyata in ko ba haka
ba xaka hadu da nadama. Na tare dan mashin muka hau
ba tare da an fada masa in da xanje ba. Dare muna
gidansu baaba sai gashi da Mom dinsa da dadynsa,muna
cin abinci da sakina itama taxo tana jiran mijinta xai xo
ya dauke ta da mashin... Raina ya baci,suka gaisa da
mutan gida. Mom tace "Don Allah Hafsa nake nema,
nace gani. Sakina ta bata kujera
Ta kure shadad da ido,da kyar na amsa gaisuwar da take
min,tace "ikon Allah!! Lallai wannan yaron Munnir
ne,kamannin har ya baci."Ta dube ni"yar nan nazo ne mu
daidaita, wannan yaron dai jikana ne, "cikn daga murya
na ce "Dana ba jikanki ba ne. na fasa kuka nan mutanen
gida suka taru nace "ki fitar mana daga gida.na daga
waya na kira yaya umar, sai ga shi ban taba ganin
fadansa ba irin na ranar.ya ce sun san dansu ne can da
ba su xo ba sai yanxu?nan fa itama Mom ta shiga
masifa har waje,Munnir wai shi sai ya shigo gidanmu ya
dauki dansa. Umar ya ce, shigo mu rusa maka kai, dan
iska mara kunya"kai, ranar naga tashin hnkl shi kanshi
shadad din ma kuka yake, ganin ina yi.Na kira Abubakar
ina kuka na fada masa cewa sun xo wai xasu dauke
shadad. Yace "xa suyi me?to kan me?na ce nima ban
sani ba, yayi shiru can yace "xan shigo gobe. Washegari
ko asibiti na kasa xuwa, sai kusan sha biyu Abubakar ya
iso.lkcn kuwa Munnir suna waje tare da Umar,wai ko a
ba su yaro ku su kai kara kotu,kuma su dauki
lauya.Abubakar ya kalli Munnir tsaf,nan take ya ji ya
tsane shi.ko shakka babu wannan shine Baban
shadad.Ya ce " kan wane dalili kake son a baka
yaro?"yayi mishi wani duba,sannan kai tsaye yace, Dana
ne"Abubakar yace "ka taba aurenta ne?ya ce ai kowa
yasan cewa budurwata ce a da. Ran abubakar ya sake
baci,ya ce"don kawai tana budurwarka a da yanxun sai
kazo kce danta naka ne?yace ita tasan komai ai.Umar
yace to sai dai in ku ku kai karan mu amma babu wanda
xai baku yaro.Abubakar yace ina Hafsat din? Umar yace
tana ciki.ya shiga gidan ranshi a bace,ya same ni dakin
baabah. Cikin fushi yace"wannan kadan kika gani kin
xabi son xuciyarki kin bar tafarkin Allah, dole kiga
kaico.Sai ma wani ya sake xuwa yace shima dansa ne
tunda kin xama bola mai dibar sharar kowa, ba ki san
adadin maxan daki ka bi ba a rayuwarki."Namike tare da
fashewa da kuka na ce,"sam ni babu wani namiji dana
taba bi a rayuwata, ko shima fyade ya min ai shi ya
sani."Ya ce to da bakinki kika sanar dani cewa ke
karuwa ce kuma a yawonki ne na karuwanci kika yin
ciki,ko ba haka kika ce ba? Na ce "Ni fana fadi haka ne
saboda kawai saboda ina son ka barni.Ya ce"ke dai kika
sani,wanda bai ji maganar iyayen shi ba ai dole ne yayi
nadama in ko ba haba ba ni ba da aure na ba xa'a je
kotu,sai ki tattara dansu ki basu.Na xube gwiwa biyu a
gaban shi tare da rike kafafunshi na ce"Don Allah ka
taimake ni,in na bashi yarona ya cuce ni,ya toxarta ni a
baya. Abubakar xan yarda in ka rabu dani saboda ya
xama ajalina akan in ba da yarona. Ya fita fuu a fusace
,kamar minti 15 ya dawo ya dauki shadad ya fita. Na bi
shi da gudu har gurin motar Yaya Umar, nace "Ina xaku
dashi?Yaya Umar bai tanka ni ba,sai Abubakar da yace
ckn fushi.koma ciki ki jira,duk ranar da kika koyi magana
sai ki kira wayata,yaron kuma xan kai shi gurin uban
nashi,in yaso kije ki dauko shi.Umar yaja mota suka
tafi.Kai tsaye kano suka nufa,gidan Raham suka kai
shi,sannan Umar ya dawo ,ni ko ina nan sai kuka nike
mutanen suna bani hkr,wasu na cewa,in hkr mana,muna
huta lkc da abin ya faru baabah taje gurin Babah a
asibiti. Da ta dawo kuma sai ta same ni ckn kuka da
tashin hnkl,nace"Umar da Abubakar mijina sun dauki
Shadad sun kai ma Munnir. Baabah tace kiyi hkr,ki kuma
gode ma Allah,dmn wannan wata mafita ce ya baki. kin
san hatsarin ba yanxun bane,sai nan gaba yaro yayi
girma sai ya tsare ki ina babanshi,me xa ki ce mashi?
Don haka kiyi hkr,wannan ma wanke ki ne Allah yayi.Na
nisa."ni kam baabah ba xan fa yarda ba,ni kadai nasan
halin da na shiga tun daga lkcn da Munnir yayi min fyade
har xuwa yanxun,in na bashi yarona yaci bulus. Ta ce "to
me xa kiyi?kina ganin kin fisu tunani ne?kada ki manta
mijinki ne fa da wanki."na hada kai da gwiwa ina kuka
tace."bana son ki sake yin wani abu da za a ce baki
kyauta ba,ko yan'uwanki suyi fushi dake..."Yanxun ya ya
xanyi"Na katse ta, ta ce "ki nutsu ki bisu,duk yanda suke
so.Na ce, shi kenan" Na kira Innarmu na fada mata
komai game da abin dake faruwa,har xuwa abin da
Baabah ta ce.Innarmu ta ce."Ki kwantar da hnklinki
shawarar da Baabarki ta bada ita ce ya kamata ki
bi,sannan ki tuna cewa mahiafinki yana kwance a gadon
asibiti kada ki kara masa wata damuwar."Na ce "to shi
kenan,na hakura.Da dare kuma guraren 9pm,na kira
Rahma ashe lkcn suna tare dasu Abubakar shadad kuwa
yayi bacci.
Tace, gata ta kira, yace kada ki nuna mata cewa mun
xo.Bayan mun gaisa ta ce"Ya jikin baba?na ce da suki
sosai.Ta ce "ya ya naji muryarki wat iri? "na ce Um! sai
kuka tace lfy?nace Munnir yana son kashe ni da
raina.Kinsan yanxun ya kunna min wuta wai in ba shi
dan shi? su kuma Umar da Abubakr dina suka dauke shi
suk kai shi.Ta ce " To yanxun yaya xa kiyi?na ce "Rahma
ba ni da abin yi daya wuce addu'a in xura musu ido.Tace
"hakn in kika yi shine abin da yafi dacewa."na ce
"Um,wai Abubakar ha da cewa ban iya magana ba.Wai in
xauna a gida in na koyi magana in kira shi a waya,wai da
gaske ne Rahma don Allah ban iya magana ba?Ta ce "to
kila shi ne kika sakr ma magana son ranki "na ce
"Rahma xan iya rantse miki cewa ban taba sa'in sa d
ashi ba tunda na aure shi. Ta ce. To ki lallaba shi sai ya
fada miki maganr da kika fada masa mara dadi.Na sauke
ajiyar xuciya."shi kenan na gode.Na koma na
kwanta.Bayan na yanke ma kaina hukuncin cewa ba xan
kira wayarshi ba har sai lkcn daya neme ni.Sam daren
ban runtsa ba,washegari jkn Babah yayi sauki,aka
sallamo shi ya dawo.Can kusan karfe 4 aka yi
sallama,mun xata masu duba baba ne,ashe wai kara
iyayen munnir suka kai kotu.Tirkashi!Sai lkcn baba yaji
komai, na kira Yaya Umar na ce "To gashi sun yi kararmu
to ta me bayan kun basu dansu?ya Umar ya ce kara
kuma?na ce kwarai kuwa,ga magatakardar babban kotu
yaxo.Ya ce"Ina xuwa ya kira Abubakar lkcn ya koma
Yola,bai ko hutu ba don saukar shi kenan,ya ce to
yanxun ranar yaushe ne shiga kotun?Umar yace
"Monday"Abubakrya ce . to xan xo jibi da lauyana."Umar
ne ya fada wa Innarmu komai,itama tace tana xuwa.Inna
wanka najiyo muryar Abubakar suna gaisawa da mutan
gida.Sannan ya shiga gurin Babanmu , na tashi na dan
kintsa jikina,ya ce ya shigo suka gaisa da Baba sannan
ya koma gurin Baaba suna tattauna batun rikicin.N
ashigo na xauna gaida shi,ba tare da na dube shi ba,ya
amsa sannan ya tambayi jkn baba, na ce yaji sauki.Daga
nan yace ,to nazo da lauyana xumu kwana nan tunda
ance gobe ne shari'ar ko/na ce eh!ya ce ki shirya yanxun
muje yayi miki tambayoyi.Ya dubi baba ya ce,Baba ayi
mata fada ta fada mishi gaskiya,dmn da ita ce xa'a
yanke miki duk wani hukunci.Baba yace."kwarai kuwa in
kin fadi gaskiya to kin hutar da kanki,kin hutar da
kowa,Allah ya ba da sa'a.Muka fita xuwa mota,lauyan ba
xai wuce sa'anshi ba,baki mai yar'kiba kadan,yana amsa
suna Barista murtala.In da suka yi masauki nan muka je,
amma gurin shakatawar muka zauna.lauya Murtala yace
in fada mishi sunana,na fada mishi.Daga nan ya tambaye
ni tarihina,Abubakar na xaune na xayyana ma lauyan
komai,tun daga haduwata da Munir har xuwa yau.Lauya
Murtala yace "kin tabbata haka ne?Na ce ko ckn bacci
ka tashe ni xan maimaita maka wannan don ba xan
manta da wannan bakin tarihin nawa bah.Abubakar ya
ce?Kada dai ki fada man karya,don ke baki iya magana
ba.ya ci gaba da cewa."yaya batun xagawa duniya da
kika yi?Na ce,"banje ko ina ba,kuma ban da shi da ya
min fydae ban taba hulda da kowane namiji ba.Ya ce "in
har hak ne fyade yayi mata barista sai in ga kamr
shari'ar xata yi sauki ko?Murtala yace "inshaAllau in an
gam matsalar yaron sai tayi karan cewa fyden da ya
mata,tana son abi mata hakkinta,tunda nasan dole xai
amsa laifinsa.Bayan gama gabatar da shari'ar a ranar
litinin din da muka gurfana a gaban kotu lauyoyi suka
fito,lauyan shi ne yafi bani mamaki, yanda ya kuke kan
cewa a ba shi danshi xai biya duk abin da aka kashe.ni
dama koda aka tambaye ni dans ne?na ce dan shi ne,ban
bata lokaci ba.Lauyana ya bukaci in ba da labarin
dangantakata da munir,mijina ne?na vce a'a saurayina ne
,ya ce to saurayinki ya ya aka yi kuka haihu har ma ki ka
hana shi danshi?ya dubi Alkalin ya amince nan na
xayyano komai har xuwa yau.Jama'a da dama sun xubar
da hawaye don tausayin min aka tamabyi munir shima
bai bata lokaci ba ya amsa da cewa tabbas fyade ne
yayi min.kuma duk abin da na fada haaka ne,sai dai shi
bai san cewa na shiga wani hali ba,sannan ko nawa na
kashe wa dan xai biya ni.nan dai lauyoyi suka yi ta
kafsawa,daga bisani na ce ina son a bi min hakkina na
fyaden da yayi min .nan Alkali ya daga kara xuwa sati
biyu masu xuwa,kuma ranar ne za'a yanke hukunci,haka
muma Alakli ya bukaci a xo da yaron.Muka fito
,Abubakar sai kallona yake yi tamakr yau ya soma
ganina,ya ce Umar ya wuce da su Innarmu saboda shi
xai tafi tare da lauyan,don in sake mishi karin
bayani.Tunda muka xo daidai dakunan su Barista Murtala
ya shige nashi,ya rike hannuna xuwa ckn nashi
masaukin.tsakiyar dakin ya tsayar dani ya rike
hannuwana tare da kallon fuskata ckn matsanancin
tausayi ya ce min."Hafsat me ya hana ki sanar dani
ainahin abin da ya faru ki ka sa ni ckn kunci nima ni
dinga kuntata miki? Na tsura ma fuskarshi ido."Abubakar
a lkcn na furta maka haka ne don kawai ka rabu da
ni,sam ban san xa ka zama makusancina ba,lkcn bana
bukatar wanda xai kusanto ni da gida,ban san lamura
xasu xo da sauki haka ba,ya manna ni a kirjinsa, lokaci
guda muka sauke ajiyar zuciya, ya ce ki yafe ni, na
nisance kine saboda in ina tuna cewa bansan adadin
mazan da kika yi hulda dasu ba, ga kuma kishin ki mai
wahalar dani......

Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 4-04
Posted by ANaM Dorayi on 05:15 AM, 29-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Na soma kukan farin ciki.
"Na yafe maka, dama kuma ni ko kusa ban rike ka da
komai ba, saboda ba duka namiji ne ne zaiji furucin da
nayi ma kaina lakabi da shi ba, sannan ya saurare ni, sai
sadauki, jarumi irinka mai taimako don Allah."
Na sake kwantar da kaina a kirjinsa, na ce "Nima ka yafe
min bata maka ran da nayi."
Ya dago fuskata, ya sumbaci goshi na, sannan ya
tsurawa kwayar idona nasa idon.
"Na yafe maki, sannan ya sake maida ni kirjinsa da wani
kalar salon nuna soyayya.
Wayar shi ce ta katse ni, sanda muka yi nisa cikin wata
duniya muka sake ajiyar zuciya, sannan yasa hannu ya
zaro wayar a aljihu.
Ni kuma na zauna, zuciyata kuwa farin ciki ne maras
misaltuwa. Ya daga wayar, mahaifinshi ne suka yi
magana cikin fillanci na tsahon minti goma sannan
suka yi sallama.
Ya zo ya zauna kusa dani, sannan ya kira Sagir ya
bashi labarin yadda shari'a ta kaya, sannan ya ce zama
na gaba ya zo da Shadad.
Suka yi sallama, ya ce "To mu fa zamu wuce ne,
yanzun haka Abba na jira na saboda tafiyar dake gaban
mu zuwa Pakistan."
Na ce "To ni in zauna a nan?" Ya ce "Kano za ki koma,
ki kwantar da hankalinki, In Shaa Allahu za a bi maki
hakkinki, domin na kula Alkalin yana da kokarin
kamanta gaskiya."
Ya ce, "Amma fa ki barshi gurin sagir kada a zo a
dauke shi, na ce to" ya soma hada kayan shi ina taya
shi har muka gama.
Ya rike hannuwana, "Ko in raka ki Kanon ne?" Na ce
"A'a, ka ta fi kiran Abba din."
Sai da suka kaini gida, ya cika ni da kudi, sannan ya
roki Umar da cewa ya kaini gida baya son na shiga
motar haya.
Su Baba ma yayi masu alkhairi, sannan ya tafi.
Abinda yayi wa zuciyata dadi, yanda na samu mutan
gida suna tattaunawa akan shari'armu.
Wasu sunje kenan ku yau sunji da kunnan su cewa
Munir fyade yayi min.
Ade ta dube ni, "Hafsat ina maki murna, Allah ya dora
ki a kan shi." Na ce "Ai dama gaskiya tana halinta
komai daren dadewa.
Sannan masu zagina da masu cewa nayo ciki SANADIN
BOKO duk na barsu da Allah."
Asabe ta ce "Ba a yi haka ba Hafsat, zance na gaskiya
ko mu gidan nan ba wanda bai yi da ke ba,

Please Login or Register in order to submit comment