You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
fita daga d'akin tana d'aura d'an kwalinta, tana fita ta fara zura itace a murhu ta k'yasta ashana, kafin wutar ta kama Inna dake fitowa daga d'aki tazo ta aje mata shinkafa da kayan miyan da za tayi aiki dasu tana fad'in "gashi nan saura ki munafurceni kamar yanda kika saba."
Kallonta kawai tayi ba tayi magana ba har Inna ta d'auki gyalenta a rataye ta aza a kafad'a ta kalli Raheenat tace "na gaji da wannan ranar tuwon, wallahi daga gobe idan baki shigo gidan nan qarfe sha biyu ba kuma kika d'ora min abinci, to ki sani ba zaki sake zuwa makarantar ba tunda ai dama ba ubanki bane ya biya miki kud'in ba."
Cikin raunin murya Raheenat tace "dan Allah Inna kiyi hak'uri karki hanani, wallahi na miki alk'awarin zan dinga dawowa da wuri, zan nemi izini a gurin malam."
"Aikin banza, shi kuma malam d'in saiya barki kiyi yanda kike so? saboda kece shafaffiya da mai." cewar Farida daga zaune.
Fa'iza ce ta tare da cewar "to kinsan meke tsakaninsu da malam d'in ne, watak'ila akwai karatun da suke na musamman a bayan aji."
A hankali Raheenat ta kalleta tace "Faiza, ka fad'i alkairi ko kayi shiru, hakan bai dace ba ki zargemu a bisa abinda baki gani ba da idonki."
"To waliyiya ustaziya, wato ma zarginku ne ake? to ai kura ba tayi gudu ba d'anta yayi rarrafe." cewar Inna.
Kafin wani yayi magana Inna ta kalli su Farida tace "ni zan shiga wajen Hajia tun jiya rabona da ita."
Cike da izgilanci Fa'iza tace "Inna ki gaida musaki."
Dakk'uwa Inna ta mata tace "shegiya, idan da lafiyarshi k'alau ke kina ganin ba sai nabi duk hanyar da zan biba danna had'aki dashi aure ba."
Farida ce tace "lallai ma Inna, wato ni ko oho ko? ni dake nan kullum ina masa fatan samun sauk'i kodan ya aureni, amma ke kuma kina so ki had'ashi da wacce take masa iskanci."
"Kul!" Inna ta fad'a cikin daka tsawa.
Dorawa tayi da "wallahi karki yarda koda wasa Hajia Luba taji kinawa Abdul fatan samun lafiya, idan ba haka ba kema zaki zama kamarshi, ko kuma ma ya fiki kyan ganuwa."
Tana fad'a ta juya ta bar gidan, duk maganar nan da suke akan kunnuwan Raheenat, tana aikinta tana sake mamakin wannan Hajia Luba to miye matsalarta da samun lafiyar Abdul, watak'ila tana da hannu a rashin lafiyar tasa, wata zuciyar ce ta gargad'eta ta daina zargin haka dan babu kyau tunda bata tabbatar ba.
Tana cikin aikin Sameera ta shigo gidan d'auke da kwanon abinci, ko kallon banza su Farida basu isheta ba, kai tsaye wajen Raheenat ta nufa ta dafa kafad'arta, juyowa tayi cikin dauriyar matsanciyar yunwar da take ji ta kalli Sameera d'in, "my Meera, kece?"
Fuska ba annuri tace mata " karb'i wannan ki tashi kije d'aki ke da Inna kuci , ni zan qarasa miki aikin."
Murmushi kawai Raheenat tayi dan tasan zaiyi wuya ta fita daga gidan nan haka kawai, hannunta ta rik'e tace "Meera, kije ki kaiwa Inna, nima na kusa qarasawa, shinkafa kawai zan zuba."
Cikin d'aga murya Sameera tace "dallah miye haka? kasheki zasuyi ne idan kin tashi daga nan? yunwa fa kike ji."
Farida ce tayi tsal tace "to yunwar ta kasheta mata, ke yarinyar nan fa na lura in dai kika shigo gidan nan saikin nemi tashin hankali, to bari kiji wallahi kin kusa daina shigowa cikin gidan nan."
Sunkuyawa Sameera tayi ta aje kwanon hannunta ta dago, Raheenat da tasan meye zai faru tayi saurin tashi daga kujerarta ta rik'e Sameera sosai tana magana qasa qasa tace "pls my Meera, kar kiyi dan Allah rabu dasu, ki shiga ciki ki bawa Inna abinci, ni idan na gama zanci."
Cikin tsawa da masifa Sameera tace "dallah ki sake my Heenat, ki bari na nuna musu da banbanci tsakanin Meera da Heenat, 'yan iska kawai da kuka raina mutane."
"A'a Meera na rok'eki dan Allah, in dai har zan iya fad'a miki kiji to kiyi abinda nace, in kuma ban isa ba to ki nuna min yanzun nan." cewar Raheenat cikin rarrashi.
Fincike kanta tayi daga rik'on data mata ta sunkuya ta d'auki kwanon rai bace ta d'ago ta kalli Farida tace "wallahi kinci albarkacin masu albarkaci, badan haka ba, da kin gane shayi zalla ruwa ne."
A hassale ta shiga d'akin nasu ta samu Mama a tsaye kuma da alama taji me yake faruwa, kawai dai bata fita bane dan tana zuwa za ace ta shigar musu,
*muje zuwa tare da*
_Meeraheenat_😍
28/07/2019 à 14:18 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*STORY AND WRITING*
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*
*DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DA YA BAMU IKON RUBUTA WANNAN LITTAFIN NAMU, TSIRA DA AMINCI SU ƘARA TABBATA GA ANNABINMU FARKON ƘAGA ƘARSHEN AIKA WATO ANNABI MUHAMMADU S.A.W*
```WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARRAN LABARI NE, ƘIRƘIRAR RAHEENAT CE DA SAMEERA DAN HAKA A GUJI JUYA MANA SHI TA KO WANI IRIN SIGA, DUK WANDA LABARINMU YAYI DAIDAI DA RAYUWARSA TO AKASI AKA SAMU👏```
_WANNAN LITTAFIN ƊUNGURUGUM ƊINSA SADAUKARWA CE GAREKI ALAWIYYA, HAƘIKA KINA NUNAWA RAHEENAT DA SAMEERA SOYAYYA, BAMU TA KAMARKI A DUK FANS ƊINMU, SHI YASA MA MUKA BAKI LITTAFIN GABA ƊAYANSA, IN KIKA CE BABU WANDA ZAI KARANTA YA ZAUNU, DOMIN GIRMANKI NE, KI HUTA KAWAI KIJI DAƊINKI MY LOVELY SISTER RAHEENAT DA SAMEERAT SUNA SONKI HAR CIKIN ƘALBINSU❤ LOVE YOU TO ALL MY HEART❤🌹_
*JINJINA IRIN TA BAN GIRMA GAREKU ƳAN ƘUNGIYARMU, HAƘIƘA MUNA MATUƘAR JIN DAƊIN ZAMA CIKINKU, GIDANMU YA AMSA SUNANSA GIDAN ZAMAN LAFIYA DA AMANA KAMAR YANDA MUKA KIRASHI. HAƘIƘA KU ƊIN MUTANE NE MASU KARAMCI DA SANIN YA KAMATA, KU HUTA KAWAI KUJI DAƊINKU RAHEENA DA SAMEERA SUNA YI MUKU FATAN ALKHAIRI💘🌹❤*
*GAISUWA TABAN GIRMA GAREKI SHUGABA KUMA AINTƳNMU WATO AUNTY AISHAN UMMU, HAƘIƘA KECE GINSHIƘIN KAFUWAR ƘUNGIYARMU. KIN KASANCE SHUGABA TA GARI GAREMU, MUNA JINJINA MIKI👍 KI HUTA KAWAI AUNTYNMU RAHEENAT DA SAMEERA NA YINKI, FATAN ALKHAIRI DAKE DA ZURI'ARKI ALLAH YAJA DA KAWANKI❤*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```
Page 1 to 5
" *Raheenat*! *Raheenat*!! , wai baki jina ne ? matsiyaciyar yarinya kawai. "
Cewar matar dake tsaye bakin murhu, wata matashiyar yarinyar da ba zata gaza shekara sha shida zuwa sha bakwai ba ta fito daga wani d'aki tana d'aura d'an kwali, abun mamaki a tare da ita shine duk da kyawun halittarta amma kayan jikinta sai hamdala, doguwar riga ce ta shadda, amma fa tasha jiki sosai duk da kalarta bleue ce, amma har tayi fari fari saboda tsabar wahala, durk'usawa tayi alamar girmamawa tace "Inna gani."
"Raheenat me yasa hankalinki baya kwantawa idan ba ji kikayi ina kwaroroton daga muryata a kanki ba ?, Ke kurma ce da kira d'aya biyu duk bai isa yasa kiji ba.?"
A ladabce tace "kiyi hak'uri Inna, wallahi tun kira na farko naji kuma na taso, to d'an kwalina ne na tsaya nema...."
"Rufe min baki dallah, yau aka fara ne bare na yarda dake? ni dallah d'auki abincin *Sadik* gashi nan ki kai masa d'akinsa."
D'ago ido tayi ta kalleta, a sanyaye ta tashi tsaye tace "bara na d'auko hijab."
"Ke!"
Ta dasa mata tsawa, a tsorace ta zabura ta juyo tana kallonta, "ke awa da har zan aikeki kice wai sai kin d'auko wani banzan hijabi, wata tsiyace a jikin naki da za'a kalla? dubeki fa."
Ta karasa maganar da nunata da hannu, a hankali ta sunkuya ta d'auki kwanan ta nufi d'akinsu Sadik d'in ba dan ranta na so ba, sallama tayi tun kofar d'akin amma shiru babu amsa duk da tana jin hayaniyarsu, "sallama alaikum."
Ta sake wata sallamar, muryar Sadik d'in ce yace "ki shigo mana."
Bud'a labulen d'akin tayi tare da sake wata sallamar, bata yarda ta had'a ido da kowa dake d'akin ba harta aje kwanan, ta juyo zata fita taji an rik'e hannunta, wata irin tsinkewa ne gabanta yayi ya fad'i ga tsoro daya bayyana a tare da ita, juyowa tayi a hankali cikin rawar murya tace "dan...dan...Allah...yah Sadik ka..... sake min hannuna na tafi."
Cikin wata dariya matashin saurayin yace "Raheenat na gaji da wannan jiran, me zai hana ki bani abinda nake so a wuce wurin kawai? kefa ba yarinya ba ce nima kuma haka, amma sai ki dinga yin abu kamar wata marar ilimi kuma yar qauye."
Mutsu mutsun ƙwatar hannunta kawai take amma ba tace komai ba, sake rik'e hannun yayi gam yace "Raheenat, ki amince da buk'atata mana, ni kuma na miki alk'awarin zanyi miki duk abinda kike so, wallahi za kiji dad'in rayuwarki, kuma zan saka Inna ta daina miki duk abinda take miki, kinji?"
Ba tare data daina ƙoƙarin kwatar hannunta ba ta kawar da kanta gefe ta rufe ido tace "dan Allah ka sakeni, na fad'a maka ba zaka tab'a samun abinda kake so ba daga gareni, rayuwar da muke ciki bata kai na salwantar da mutuncina ba."
Sakin hannunta yayi ya nunata da yatsa yace "kiji nan da kyau, ni kuma saina nuna miki nafi k'arfinki, wallahi saina sameki tunda har na k'wallafa rai a kanki, ko kina so ko baki so saina cinma burina, koda kuwa hakan yana nufin numfashinki na qarshe."
Jin haka yasa ta kalleshi da mamaki amma ba tace ƙala ba ta juya ta bar d'akin, ƙannanshi dake kallon ikon Allah d'ayan ne yace "dan Allah yah Sadik ka fita harkar yarinyar nan, karfa kaje kayi wani abinda za kasa kanka a matsala damu ma."
Hannu ya d'ora akan bakinshi yana kallon *Nuhu* yace "yimin shiru da bakinka, ba matsalarka bace, idan kuma nasa kaina bance kowa ya shiga ba."
➡➡➡➡➡➡➡
Tana shiga d'akin nasu ta fara canza kayanta izuwa na islamiyya, riga da wando ne da hijab, amma wandon har yana neman ya d'age mata gashi sunyi wani sid'ik dasu kayan, musamman hijab da saman kanshi yayi fari tas ga wasu qananan hudodi akan alamar zafin rana ta kusa kasheshi, haka ma 'yar doguwar rigar dake bakin gwiwa ita kam a mazaunin duk ta tumurmushe sai wani k'aton d'inki da akayi a wajen, ba komai a d'akin sai kayan jikinsu da kuma katifar baccinsu, kyakkyawa kuma matashiyar matar dake zaune a bakin katifar ce ta lura da yanayinta dan haka ta d'anyi murmushi tace "tunda naji tace ki kaiwa Sadik abinci, nasan shine silar wannan shirun naki."
Da sauri ta tsaya daga saka hijab d'in ta nufo matar ta durk'usa gabanta ta rik'e hannayenta tace " *Mama*, dan Allah mubar gidan nan, wallahi ina jin tsoron Sadik, ya fara bani tsoro Mama."
Jaye hannunta tayi ta dafa kafad'arta tace "muje ina Raheenat ? Na d'auka nan ma da muke taimakonmu ne akayi, kuma kinsan komai, toya kike so muyi?"
Kamar zata fashe da kuka tace "Mama za'a sake taimaka mana, amma dan Allah mubar gidan nan dan komai zai iya faruwa, Sadik ba imanine dashi ba."
Kai matar ta girgiza tace "a wannan duniya tamu da taimako yayi wuya, taya kike tunanin da mun fita daga nan za'a taimaka mana, Raheenat nasha fad'a miki cewar ki kwantar da hankalinki, wallahi Sadik ko waninshi basu isa su cutar dake ba, saboda kina tare da addu'ata, dan haka haka Allah ba zai bawa duk wani mai
ƙoƙarin son yaga ya cutar dake nasara ba, dan haka tashi ki shirya lokaci na tafiya."
Rumgume mahaifiyar tata tayi tace "shi yasa nake alfahari dake Mamana, har kinsa naji zuciyata ta washe."
Murmushi tayi itama tace "nima ina alfahari dake 'yata, tashi ki shirya to."
Qarasa shirin tayi ta d'auki wata irin bak'ar jaka da duk ta yamutsu ta kece ta rataya a kafad'a sannan ta dawo gaban mahaifiyartata ta sunkuya tace "Mama kimin addu'a tare dasa albarka?"
Kanta ta dafa tace "Allah ya miki albarka Raheenat, Allah ya kaiki lafiya ya dawo min dake lafiya, ya baki ilimi me albarka wanda zai amfani al'umma, Allah ya tsareki daga duk wani abun cutarwa ko sharri, ubangiji ya rufe idon mak'iya daga ganin kyakyawar 'yata."
Ta k'arashe maganar da kama kumatunta, dariya dukansu sukayi kafin tace "na gode Mama, ina miki fatan zama cikin aminci har izuwa lokacin da zan dawo gida."
Daga haka sukayi sallama ta fito ta kama hanyar islamiyyarsu, tana tafe tana tilarwar karatu a kai saboda mahardaciyar ALQUR'ANI ce.
Da isarta ta taras har Sameera ƙawarta ta rigata zuwa, zama tayi kusa da Sameerar tana faɗin "yau kin rigani zuwa Sam. "
Murmushi Sameera tayi tace "nima ɗin yanzun nan na shigo, naso shigowa gidanku sai kuma nace ƙila kin wuce tun ɗazun. "
Littafin Hallul masa'i Raheenat ta ciro cikin jakarta ta fara ƙokarin dubawa domin shine darasinsu na farko a yau tana cewa "wallahi kin ganni sai yanzu. "
Sameera bata ƙara cewa komai ba sai ga malam ya shigo ajin, nan itama ta ɗauki littafinta dake kan tebur ɗinsu tana buɗawa, ba tare da ɓata lokaci ba malamin ya fara gabatar musu da abinda ya kawo shi, nan duk ajin suka nutsu suna sauraronsa.
Ƙarfe shida daidai aka tashesu daga makarantar, jerowa Raheenat da Sameera sukayi zuwa gida, domin unguwarsu ɗaya, duk da cewa Raheenat basu wani daɗe da zuwa unguwar ba.
Tafe suke suna hirar karatunsu, faɗin wahalar littafan da aka sanya musu yanzun sukeyi, Raheenat ce tace "ni fa duk wahalarsu be dameni ba tunda ina fahimta, kuma akwai karuwa sosai a cikinsu, abinda yafi burgeni ma shine ayoyin alqur'anin da suke cikin littafan. "
Murmushi Sameera tayi tace "akwai fa ƙaruwa wallahi, fata dai Allah ya amfanar damu abinda muke karanta. "
"Ameen dai" cewar Raheenat, wanda faɗin hakan kuma yayi daidai da zuwa ƙofar gidansu.
Sallama sukayiwa juna Sameera tayi gaba dan gidansu na gaban nasu Raheenat ne, shiga gidan Raheenat tayi da sallama a bakinta, Inna dake zaune tare da ƴaƴanta mata ko su ɗago su kalli Raheenat ba suyi ba balle ta saka ran su amsa sallamar da tayi, nufar hanyar ɗakinsu tayi cikin sanyin jiki, daidai ta buɗe labulan ɗakin nasu ta jiyo muryar Inna na cewa "ki shiga ki cire uniform ɗin ki zo ga wanke-wanke nan na jiranki, ki gama kuma ki share gidan gaba ɗaya, sannan ɗakin su Farida ma nason gyara, saura ki shiga ki ƙi fitowa da wuri, dan nasan munafukar uwar nan taki in ta sakaki a ɗaki babu abinda takeyi miki sai huɗubar tsiya. "
Lumshe ido Raheenat tayi ta buɗe cike da jin ɗacin kalamar Inna akan Mamanta, cikin mutuwar jiki tace "to Inna"
Tana faɗin haka ta ƙarasa shigewa cikin ɗakin nasu da sallama a bakinta.
Mama dake zaune ne ta amsa mata cikin sakin fuska tace "ƴar albarka kin dawo. ?"
Murmushi Raheenat ta saki wanda saida duka kumatunta suka lotsa ta ƙarasa kusa da Maman nata ta zauna tana faɗin "eh na dawo Mamana, ina fatan dai kina cikin ƙoshin lafiya kamar yanda na barki.?"
Murmushin jin daɗi Mama tayi tace "lafiya ƙalau nake ƴar Mamanta, saboda lafiya ma zan iya zuwa makka da gudu in dawo."
Dariyar da bata shirya ba Raheenat ta saki tare da miƙewa ta fara ƙoƙarin cire uniform ɗinta dan zuwa gabatar da aikin da Inna tace suna jiranta, kafin yanzu a fara mata tijara ita da Mamanta, tana cewa "haka nakeso ai Mamana, Allah ya kara miki lafiya.?"
Ameen Mama tace tana kallon ƴar tata cike da so da ƙauna, a kullum tafi son taga ƴa nata tana farin ciki, sam bata son ganin damuwa a fuskar ɗiyartata kamar yanda itama Raheenat bata son ganin damuwar Mamanta wacce ita kaɗai ce gareta.
Muje zuwa tare da meeraheenat🥰
More comment more typing😁
28/07/2019 à 14:18 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*STORY AND WRITING*
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```
*Bismilallahi-rahamanir-rahim.*
Page _5 to 10_
Shara ta fara saboda ba taso magriba tayi tana sharar, tana karasawa kuma ta had'a kwanuka ta wanke, ruwan wanke wanken ta had'a ta fita zubarwa a waje, bata an karaba a cikin soro ta had'u da mutum har ruwan suka zuba sosai, muryar Farida kawai taji tace "kutumar uba, yau ana shirin yinta."
Sai kawai ta shak'o wuyanta tayi yarb'i da ita tare da rufa mata baya ta fara shirgarta tana fad'in "marar mutunci, ke yanzu ni zaki jika da ruwa in ba iskanci ba? turoki akai ko?"
Saurayin da suke tare dashi ne a soron ya rik'e Farida yasa hannu ya tallabo Raheenat yana fad'in "haba ke kuwa ya isa haka, ruwane fa ba wani abu ba."
"Ruwa ne ba wani abu ba? ruwan wanke wake ne fa, wallahi da gangan tayi munafukar, saboda kawai ita bata da saurayi." duk tayi maganar ne a hassale.
Raheenat da share hawaye kawai take tace "dan Allah kuyi hak'uri, wallahi ban kula bane, sam ba'a ganin mutum shi yasa."
Wani duka ta sake kai mata a fuska hakan yasa ta zube qasa ta dafe wajen saboda zafin da taji, qafa tasa ta harbeta tana fad'in "zaki tashi ki wuce ko saina illataki, banza kawai."
Tana zubar da hawaye ta tashi ta fita ta zubar da ruwa ta dawo, koda zata wuce ma saida ta sake dangwararta a baya tana fad'in "shegiya kawai."
Tana aje bokitin ta nufi d'akinsu Farida danta gyara kamar yanda aka ce, nanta fara da gayaran shibfidarsu dake kamar ta mahaukata saboda basa iya gyarawa, sannan tayi goge goge tayi shara, saida ta saka turaren tsintsiya sannan ta bar d'akin shi kanshi yana samun nutsuwa.
Ta fito kenan zata nufi d'akinsu Inna dake zaune ta kirata, karasawa tayi jiki a sanyaye ta tsugunna, saida ta gama kallonta tace "d'akinsu Sadik zaki je ki share musu, tunda rana ya fad'a min na fad'a miki amma na manta."
Hawayen da suka taho matane ta mayar dasu kafin tace "Inna dan Allah ki taimaka ki bani abinci na kaiwa Mama, wallahi nasan tana jin yunwa."
Kujerar dake kusa da ita yar tsugunno ta dauka, ba tare da tausayi ko tunani ba ta kuwa gabza mata ita, kasancewar ta kare kanta hakan yasa ta sauka a hannunta, rintse ido tayi sosai tuni hawaye suka b'alle mata, masifa Inna ta fara "marar kunya fitsararriya, yarinya sai iya shege da kinibibi, ni har in saki abu amma ba za kiyi ba saikin kawo min uzurinki, wallahi dani dake nan a gidan, kuma bari shi wanda ya kawoku gidan ya dawo kiga yanda za muyi dashi."
Raheenat kam tuni ta shige d'akinsu Sadik ta fara gyara musu shinfida , tana gamawa tayi shara sannan ta musu turare, fita tayi ta maida kofar ta kara musu ita sannan ta koma wajen Inna, dan dama bata basu abinci har sai ta tabbatar Raheenat ta gama musu aikin da duk yasha gabansu sannan, tun kafin tayi magana ta d'auko wani yamushashen kwano ta dangwaro mata har miyar kukan na fallatsuwa k'asa.
Dauka tayi ta nufi d'akin nasu inda Mama take, da sallama ta shiga d'akin Mama ta amsa tana aje carbin dake hannunta.
Ajiye kwanan abincin tayi gaban Mama sannan ta zauna itama, kallon ƴar nata Mama tayi cike ta tausayi tace "sannu da aiki Raheenat. "
Murmushi ta saki tace "wani aiki Mama, ba wani wahala fa, ga abinci nan ciki Mama nasan kina jin yunwa sosai. "
Kallonta Mama tayi sosai sannan ta kalli kwanan tuwon da yake can ƙasar kwano tace "kefa Raheenat.?"
Murmushi ta kuma tace "ni bana jin yunwa Mama, kedai kawai kici. "
Mama tace "nima bana jin yunwan bazan ci ba. "
Waro fararen idonta tayi tace "dan Allah Mama ki ci, wallahi nasan kina jin yunwa. "
Kallonta Mama tayi tace "bazan ci ba har sai kema zaki ci, Raheenat ta yaya kike tunanin zan iya cin abinci ke baki ci ba. ?"
Raheenat tace "to Mama zanci shikenan.?"
Murmushi Mama tayi tace "eh shikenan mu ci. "
Itama murmushi tayi ta gyara zamanta suka fara cin tuwan.
Sun kusa ƙarasawa Mama ta cire hannunta badan ta ƙoshi ba saidan tabar wa ƴarta ta ƙarasa duk da tasan itama ɗin ba ƙoshin zatayi ba, domin tuwan ko mutum ɗaya yaci shi kaɗai ba ƙoshi zaiyi ba, ɗago kai Raheenat tayi ta kalli Maman nata, murmushi Mama ta sakar mata tace "Alhamdulillahi. "
Raheenat ba tace komai ba ta maida kanta ta ƙarasa cinye sauran sannan tayi hamdala ta miƙe ta ɗibowa Mama ruwan sha cikin wata tsohuwar randar dake ɗakin.
Saida Mama tasha ta wanke hannunta sannan itama tasha ruwan ta miƙe ta fice daga ɗakin ɗauke da kwanan a hannu.
Wanke kwanan tayi taje ta ajiye a majiyarsa sannan ta ɗauki buta ta nufi rijiya taja ruwa, bayi ta shiga tayi tsarki sannan ta duƙa ta ɗaura alola, saboda kiran sallah da aka fara a masallatan dake unguwar.
Bayan ta idar da alolan ƙara cika butan tayi da ruwa ta nufi ɗakin nasu dashi, bakin ƙofa ta samu Mama na shirin fitowa itama dan ɗaura alolar, miƙawa Mama butan tayi ita kuma ta shige ɗakin domin yin sallar.
Sai da sukayi isha'i tare da shafa'i da wuturi sannan suka tashi daga kan sallaya, memakon kwanciya bacci sai Raheenat ta ɗauko littafanta ta fara muraji'a, saida ta tabbatar da iya duk karatun da akayi masu yau sannan ta mayar da littafai cikin jaka ta ajiye, bata tsaya nan ba ta fara rero ƙira'ar karatun al'qur'ani cikin daddaɗar muryarta me daɗin sauraro, kamar yanda muka ce muku Raheenat hafizace, dan haka ta ɗinga rero karatu babu tsayawa saida ta karanto surori har uku, sannan tayi addu'ar kwanciya bacci ta kwanta, zuwa lokacin tuni Mama ta daɗe dayin bacci.
*************
Washe gari tana yin sallah ko tsayawa azkar ɗin safiya ba tayi ba ta fito ta fara ƙoƙarin hura wuta, wanda tasan dama aikinta ne, daƙyar ta samu wutar ta kama mata sannan ta ɗaura ruwan koko, bata tsaya ba ta fara haɗa wanke-wanken da akaci da daran jiya ta wankesu tas, tana kammalawa ta ɗauki tsintsiya ya share gidan ƙyal, daidai kammala sharar ruwan da ta ɗaura ya tafasa.
Nufar ɗakin Inna tayi domin amso ƙullun da zata dama, sallama tayi bakin ƙofar ɗakin har daki uku amma ba'a amsa mata ba, ta buɗe baki kenan zatayi na huɗun kenan sai ga Inna ta fito cikin hargowa tana faɗin "dan jaraba kana bacci ma sai an addabeka, tsaban baƙin ciki ba za'a barka kayi bacci ka huta ba, wannan masifa har ina," mttsss taja godon tsaki.
Raheenat dai dake tsaye haɗiye wani mugun yawo tayi ta duƙa har ƙasa tace "ina kwana Inna."
Wani mugun harara Inna ta wurga mata tace "daba kwana ba zaki ganni ne uwar kinibibi, meye kika zo da wani sassafen nan ki na ƙwaɗa min sallama.?"
Cikin sanyin murya Raheenat tace "dama kamu nazo amsa na dama koko. "
Kallonta takai ga murhun wanda yake ci ganga-ganga da alamu ruwan tukunyar ya daɗe ta tafasa sannan ta juya a fusace ta shige ɗaki ta ɗauko botikin kamun ta dangwarawa Raheenat a gaba tace "gashinan kije ki dama gangin jaraba kawai. "
Ɗauka kwai Raheenat tayi ba tare da yace komai ba ta nufi bakin murhun dan dama kokon, domin inda sabo ta saba da irin hakan.
My meera ce ta kalleni idanu cike da ƙwalla tace "my heenat ina matuƙar tausayawa takwarar nan taki wallahi. "
Nace "hmmm, my meera tausayi ma ai na gaba. "
My meera tace "kice na tanadi hawayen zubarwa kenan.?"
Dariya nayi nace "da yake ka tausayi yayi miki yawa ba."
My meera tace "ba zaki gane bane my heenat. "
Dariya nayi nace "tunda ke kin gane ai kamar Raheenat ta gane ne. "
Raheenat tana kammala dama kokon ta mayar masu Farida da ruwan wanka akan wutan cikin wata ƙatuwar tukunya, ɗaukar kokon tayi wacce tafi rabin kafilas (babban farin roban fanti) ta nufi ɗakin Inna dashi.
Muje zuwa🥰
Meeraheenat ne💋
28/07/2019 à 14:18 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
Book Chapters
Chapter 22
Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30