Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce wannan a gidan nan, kaima fa d'an gidan nan ne."

Hannunshi ta rik'e tayi hanyar wajen cin abincin dashi tana fad'in "muje ga abinci an gama kuci."

Umar Faruk dai kanshi na qasa ya kasa kallonta sai Abbakar dake kallon falon irin tsari da dukiyar da aka zuba, da kanta taja mishi kujera ya zauna ita kuma mai aiki taja mata ta zauna, Khairat ma da Mammie duka sun zauna, Biba da Saude ne suka bud'a kwanukan suka fara zuba musu abincin, suna gamawa suka koma mafakarsu su kuma suka fara cin abincin.

Ba ruwan Khairat haka kawai take jin son Umar Faruk na gaskiyar na shirgarta, da kanta take d'ibar abincin tana saka mishi a baki saboda taga baya ci, haka yasa ya fara diba kad'an kad'an yana ci, Khairat d'in da Mammie kuma hira suke sosai irin na kaka da jika , Abbakar dai kallon ikon Allah yake yana qara ganin girman Khairat, dan inba mai hak'uri ba babu ta yanda za ace kana rayuwa cikin wannan daular kamar a masarauta, abinci ma na rana kana cin kusan kala uku zuwa hud'u amma ka yarda ka fara rayuwa a gida kamar nasu, haka ma a wajen Umar Faruk abinda yake rayawa kenan a zuciyarshi tare da sake jaddada irin taushin zuciyar Khairat, lallai baka sanin asalin mutum saika zauna dashi sannan zaka fahimceshi.

Suna kammalawa kafin su tashi Mamie ta kalli Khairat tace "ki tashi kije ki shirya kizo ku tafi."

A shagwab'e ta kalli Mamie tace "to Mamie."

Umar Faruk ne yace "a'a Mama, ku barta kawai ta zauna, naga kunyi kewarta sosai, idan na taso daga aiki zan biyo saina d'auketa."

Cike da farin ciki ta kalleshi tace "da gaske baby? gaskiya naji dad'i."

Mak'ale wuyanshi tayi tare da janyoshi kusanta ta sumbaci kumatunshi tare da fad'in "na gode baby."

Mammie dake kusan Khairat ce ta zura hannu ta kama kumatunshi tace "yaron kirki, gaskiya ka kyauta, dan dama muna so muyi shirye shiryen tafiyarmu a gabanta."

Ture hannunta Khairat tayi tana fad'in "kuma shine saikin tab'a min miji , nifa bana son haka."

"Allah sarki, yo mijinki ko mijina? kaji min yarinya kai, kawai dan na ara mikishi saiki wani zak'e dayawa."

Kallon Umar Faruk tayi ta kalli Mammie tace "zak'ewa ma nake? to ai mijin naki ne ke rawar qafa a kaina."

"Kaji wani d'aurin duniya kuma, to nidai ban gani ba, kuma nasan yafi sona."

"To ai gashi nan ki tambayeshi kiji." Khairat ta fad'a tana nunashi da hannu

"Ba buk'ata, danni zai zab'a, bana so kiji kunya a gaban mutane."


Cikin taushin murya cike da jin kunya Umar Faruk yace " gaskiya ne, za tasha a wajenki."

Mammie kam bushewa tayi da dariya had'e da yiwa Khairat gwalo, turo baki tayi tana kallon Umar Faruk, shi kam kasa kallonta yayi saboda wutar tartsatsin da yake ji a kanta, haka suka mik'e gaba d'ayansu zasu tafi, bayan sunyi sallama Mammie tace "nasan dai sai mun had'u a lokacin tafiyarmu ko?

"Insha Allah." ya fad'a kawai.

"To Allah ya nuna mana."

"Ameen." suka amsa.

A hankali Khairat ta taka musu har zuwa k'ofar d'aki sannan suka tsaya, sumbatar bakinshi tayi tare da kumatunshi kafin ta kalleshi tace "Allah ya tsare, saika zo."

Su Mamie dake hangensu yasa ya d'an shafi fuskarta kawai yayi gaba, suna fita suka d'auki hanya saida ya aje Abbakar gida ko shiga baiyi ba ya juya ma'aikata dan lokaci yayi sosai, sai dai zuciyarshi ta qara narkewa da tsananin son Khairat, haka ya koma duk baijin dad'in aikin saboda manyan kayan dake jikinshi, ga kuma motsi da k'amshin Khairat daya isheshi duk sanda ya motsa, ji yake kamar tana jikinshi ko kuma tana sumbatartashi, a haka dai ya gama aikin a daddafe har aka tashi.


Bai wuce gida ba har saida ya tsaya ya siyawa Zuby kayan data buk'ata kafin ya wuce gida, yana isa ana kiran sallah magrib hakan yasa yana shiga d'akinta ya aje mata kayan ya fito yayi alwala cikin gaggawa ya tafi masallaci, bai dawo gidan ba har saida akayi sallah isha'i saboda lokacin qurarre ne kuma suna tare da Ishaq suna hira, suna gamawa ya shigo gidan saida ya fara shiga wajen Baba suka gaisa kafin ya shiga d'akin Mama da sauran iyayen, yana fitowa ya wuce d'akin Zuby.

Ya samu tana nad'e sallayar da tayi sallah, abinda ya qona masa rai da haushi shine, d'akin dai tsaf dashi sai kamshin turaren wuta amma kayan jikinta, tun atamfar safe ce daya fita ya barta da ita ya kuma dawo ya sameta da ita, kuma yanzu ma ita dai ce, ya d'auka kafin ya dawo daga masallaci zai samu ta canza, amma ina alamu dai na ba tayi wanka ba tun na safe, zaune yayi a kukerar robar dake fuskantar gadon ya kalleta fuska ba yabo ba fallasa yace, cike da ladabi tace "sannu da zuwa."

"Yawwa, sannu? ya gida?"

"An gode Allah."

Aje sallayar tayi ta tsaya tana kallonshi, a d'an dak'ile yace "zauna mana."

Zaune tayi bakin gadon tana kallonshi shima wuyanta yake kallo dake tsattsafo da zufa , a shak'e yace "kin duba kayan?"

"Eh yah, na duba."

"To miye babu a ciki?"

Cikin sanyin murya tace "eh to, kusan abinda babu kad'an ne gaskiya."

Da d'an k'arfi yace "to yanzu kamar nawa zai isheki ki siyo abinda babun?"

Nanma a ladabce tace "eh to, ko nawa ka bayar ma zai isa."

D'aga gira yayi sama ya d'an zame daga kan kujerar yasa hannu aljihu ya fito da kud'i, jikka biyar biyar guda biyu ya bata yace "gashi, sai kiyi manage dashi dan kinsan nauyi dayawa ne a kaina."

"An gode Allah ya saka da alkairi." ta fad'a a sanyaye.

Sauran canjin ya mayar aljihu kafin ya sake gyara zama ya kalleta sosai yace "ina son yin wata muhimmiyar magana dake, ina fatan zaki bani hankalinki kuma ki fahimceni?"

"Ina ji yah Umar."

"Zubeida, akwai wani babban taro da aka shirya a Germany, taro ne na manyan mutane wanda zai had'a da iyalensu, mahaifin Khairat na d'aya daga ciki, kuma ya gayyaceni a matsayina na surukinsa, tafiyar zata iya d'aukanmu kwana biyu zuwa uku, shi yasa nake neman alfarmarki kwanan d'ayan, domin zai iya yiwuwa na shiga cikin kwananki domin kinsan tafiyar hali, kosu Mama basu sani ba domin ina so na kammala daku iyalina, ina fatan zaki min wannan alfarmar ki bani kwananki d'aya tak."

Cikin mamakin kalamansa tace "tafiya kuma, har qasar waje, amma kuma kai yaya ka amince ka tafi? ba ka tsoron ko wani abu aka shirya maka."

"Me kuma za'a shirya min? tare fa da Khairat zamu tafi."

"Darammm." taji gabanta ya fad'i, cike da kasa b'oye abinda ke ranta ta mik'e tsaye tace "uhum, yanzu naji magana, kace dai tare da karuwarka zaku tafi, wato harta bud'e maka idon da har kake tunanin fara biyarta a duk inda tayi ko? yah Umar wai yaushe ka zama haka ne? gaba d'aya ka canza kamar ba kai ba, to wallahi in dai izinina ne ake nema ban yarda ba."

Wata wawura daya ma hannunta har yayi qara cikin d'aga murya yace "Zubeida , akan miye ina magana dake har zaki mik'e tsaye kina min ihu, rainani ne ki kayi kome, me yasa zaki d'aga muryarki akan tawa? wai tambaya ma kike yaushe na canza? to a ranar da kika canza na canza nima, akan miye zan zaunar dake ina miki magana cikin nutsuwa ke kuma zaki d'aga min hankali, waye ya koyar dake wannan d'abi'ar? nace waye yace kizo nan ki dinga min abinda ranki yake so, waye." ya qarashe da d'aga murya tare da hankad'ata saman gado.

D'orawa yayi da "kina tunanin izininki nake nema? to baki fahimta daidai ba, ni alfarma na nema kimin ta kwana d'aya wanda shima qila waqala na yishi a can, da har zaki wani ce wai baki yarda ba, to karki yarda mana saime? naga idan zamanki nake a gidan."

"Ba dai alfarmar dana nema bace har tasa kika min haka, to bari ki gani yanzu zanyi maganin abin."

Wayarshi ya ciro daga aljihu ya danna kira, daga d'aya b'angaren ana d'auka cike da karsashi da kashe murya tace "hello baby."

Saida ya lumshe ido saboda yanda yaji har tsikar jikinshi ta tashi, saita nutsuwarsa yayi tare da sauke ajiyar zuciya kafin yace "hello, ya kike?"

Cikin shagwab'a da wata shegiyar kissa tace "ba dad'i, ka tafi ka barni inata jiranka, duk da ina kewar gida amma har kasa naji gidan ya gundureni saboda kayi nesa dani, a gaskiya Faruk sai yanzu nake qara tabbatarwa cewa soyayya *had'in Allah ce*, yanzu fad'a min yaushe zaka taho?"

Baisan sanda wani basaraken murmushi ya sub'uce masa ba, a hankali ya furta "zanzo, yanzu fad'a min tafiyar nan da zamuyi, kina ganin zamu iya dawowa a kwana biyu?"

"Eh baby , dan a ranar da za muje ma a ranar za'a gabatar da taron, kawai dai akwai gajiyar tafiya da kuma ganin gari da zai iya kaimu kwana ukun."

Yanda muryarta ke fita yasa yasa hannunshi yana shafar saitin zuciyarsa da yake jin bugunta yana canzawa , cikin basarwa yace "to a kwana biyu nake so mu dawo, ki shirya zanzo d'aukarki yanzu."

Cike da zumud'i da qwarin murya danta daki dodon kunnensa tace "an gama ranka shi dad'e."

Kashe wayar yayi ya maida kallonsa ga Zuby dake zaune tana sauraranshi, kallon sama da qasa ya mata yace "wai duk wanda ya samu dama ba zai tsaya wasa ba sai k'ok'arin ya dama damarsa, to in dan kwana d'aya ne ki rik'e na yafe miki bana buk'ata, zan tafi a ranar da kwanan Khairat zai zagayo, naga kuma mai hanani abinda naga dama."

Wucewa yayi ya barta a zaune yana fad'in "aikin banza kawai, yara da zaran sun ganka ba kaya a jikinka saisu nemi su rainaka."

Yana fita d'akin Khairat ya nufa ya bud'e da makullan wajensa ya shiga, kayansa ya cire ya shiga wanka, bai jima ba ya fito ya shirya cikin qananun kaya yayi wanka da turare kafin ya d'auki makullin mashin d'inshi dan dashi yake so ya d'auko gimbiyar.

_Yaufa my Khairat utu utu zata hau._😁


*****************


Duk da yaso ta fito amma saida tasa ya sake shiga ciki ya gaishe dasu Mamie kafin ta fito, cak ta tsaya saboda ganin Dream a maimakon Renge rover😂, matsowa tayi kusanshi tace "baby, ina motar take?"

Gemunshi ya tattaro ya had'e guri d'aya yana murmushi, a tunaninta so yake ya gwada soyayyar da take fad'in tana masa shi yasa ya taho da mashin d'in, ba zata bari shirinta ya watse ba dan haka ta saki murmushi ta rumgumeshi taré da sumbatar kumatunshi kafin tace,

"Karo na farko a rayuwata zan hau mashin, a gaskiya soyayya za tayi dad'i akan mashin."

Cikin dariya ya fara qoqarin hawa yana fad'in "saima kin hau zaki tabbatar."

Rik'e rigarsa tayi tace "ka taimaka min na hau kafin ka hau."

Hannun damansa ya mika mata ta rik'e sannan ta tattare rigarta kafin ta hau, yana hawa ya tayar suka d'auki hanya, tintserewa tayi da dariya ta fara masa cakulkuli tana fad'in,

"Ashe haka mashin yake? gaskiya daga yau ba zan sake hawa mota ba, nima mashin zan siya sabo."

"Ke ke, dan Allah ki bari, za kisa mu fad'i fa, ki bari mana, hhhhhhh." ya qarashe da dariya.

Saida suka hau titi kad'ai ta rabu dashi amma fa tana makale a bayanshi tayi luf kamar mai bacci, surutu kawai take zuba masa shi dai nishadi da farin ciki ma ya hanashi magana, da sauri ta nuna masa wata babban restaurant da zasu wuce ta gabanta tace ai saiya tsaya sunci abinci.

"Dan Allah me zamu tsaya muyi anan? idan yunwa kike ji muke gida sai kisa Ruk'ayya ta dafa miki duk abinda kike so." cewar Umar Faruk.

Cikin raha tace "a'a ni bana jin yunwa , kawai zamu je ne a matsayin masoya kuma muci abinci."

"Um um , nifa bana son shiga irin guraren nan." ya fad'a cikin shagwab'a.

"Ai tare zamu shiga, in dai kana sona kawai muje."

Saida ya rank'wafo bayanta ya kwantota yace "an gama ranki shi dad'e."

Tsayawa yayi kamar yanda take so suka shiga babban restaurant d'in, d'aya daga cikin ma'aikatan ne suka tarbesu da kyakyawar mu'amula har suka samar musu da wajen zama, ana aka basu takardar da zasu duba abinda suke so, Khairat ce ta zaba Umar Faruk kuma yace abinda take so shi zaici, cikin k'ank'anin lokaci aka wadata gabansu da kayan tab'awa, suna ci suna hira kamar masoyan tun a ranar farko, suna daf da gamawa ma'aikacin ya dawo ya basu bill d'insu, ganin kudin da zasu biya yasa Khairat kallon Umar Faruk, shima kallonta yayi saita bawa ma'aikacin takardar ta nuna Umar Faruk tace "kaba baby zai biya." tana fad'a ta bud'a post d'inta ta d'auko kud'i ko dubawa ba tayi ba cikin dubara ba tare da kowa ya gani ba.

Nufa wajen Umar Faruk ma'aikacin yayi amma sai Khairat ta rigashi isa ta sunkuya kamar ta mishi sumba ta kamo hannunshi ta dank'a masa kud'in kafin ta dago ta kalli ma'aikacin cikin harshen frensh tace "dan Allah ina zan samu douche?"

Kwatanta mata yayi ta nufi wajen Umar Faruk kuma ya kalli a hannunshi yaga kud'i, karb'ar takardar bill d'in yayi sai yaga kud'in da aka rubuta ko kasheshi za ayi ba zai iya biyansu ba, sai lokacin ya fahimci abinda Khairat tayi, murmushi kawai yayi yayi kamar ya fito da kud'in daga aljihunshi ya bawa ma'aikacin, godiya yayi ya wuce Umar Faruk kuma ya maida kallonshi ta inda habibiyar zata fito.

Ai kuwa sai gata dama ba abinda taje tayi kawai dan tabar wurin ne, tana zuwa ya mik'e itama post d'inta ta d'auka sannan suka wuce, suna fita waje ya kalleta yace "me yasa zaki biya? bayan nine ya dace na biya."

"Ni kuma? biyan me?"

Kallonta yayi yaga raina masa wayo kawai za tayi dan haka yace "daga yau bana so ki sake shiga aikin daba naki ba, wannan ba huruminki bane, yin hakan kamar kina nuna ba zan iya d'aukar nauyinki bane."

Saida suka hau mashin d'in tace "duk da bana da ilimin addini, amma nasan abune mai kyau mata ta taimakawa mijinta, nice nace muzo nan badan kana so ba, taya zan bari kayi asarar mak'odan kud'ad'e har haka."

Jin yayi shiru yasa ta bishi da wata kissar ta hanyar rumgumeshi ta baya tana sauke numfashi tace "kayi hak'uri to idan ranka ya b'ace, zan kiyaye anan gaba, amma ban maka alk'awari ba."

Hannu ya zura ya shafi fuskarta yace "Allah ya miki albarka."

Da sauri ta d'aga daga jikinshi cikin daga murya kamar ta manta inda suke tace "wayyo Allah, yau mijina ne yake saka min albarka, gaskiya na gode baby, dan Allah kayi min alk'awarin kullum zaka dinga saka min albarka, kaji?"

"Nayi alk'awari." ya fad'a yana rik'e hannunta dake kan cinyarshi.

A haka suka kai gida cikin nishad'i da farin ciki, saida suka shiga wanka suka fito kafin ya saka doguwar riga ya shiga yiwa iyayensu saida safe, d'akin Zuby ne ya shiga qarshe ya tarar da ita kwance tana chat a wayarta, ko kallonshi ba tayi ba saboda ta nuna masa ranta a b'ace yake, shi kuma domin ya nuna mata yana farin ciki sai yace "ni zanje na kwanta, ina fatan dai ba wani abu ko?"

"Um um." ta fad'a a cikin mak'oshi.

"Ok, saida safe to." yana fad'a ya wuce ya barta, ta d'auka zai rarrasheta ne koya tsaya tab'a jikinta, hakan kuma ya mata zafi sosai dan haka ma ta fara matso wasu hawaye masu zafi.

Shi kam yana komawa can Khairat tasa ya manta da wata Zuby soyayya da salo ta dinga kasheshi dasu, har saida ya goge hawayen dake idonshi ya k'amk'ameta sosai yace "dan Allah Khairat ki bani dama na shiga rayuwarki shiga ta har abada, Khairat ki amince ki bani kanki mana ta hakane kad'ai zamu sake zama d'aya, dan Allah Khairat ki taimakeni , ina kusa da kaiwa k'adamin da ba zan iya rik'e kaina ba, ki taimaka ki bani kanki kafin kwananki ya qare daga gobe."

Shiru tayi a qirjinshi dan sam ta manta da wani rabon kwana, basarwa tayi ta fara shafar kanshi tana fad'in "kayi hak'uri baby zan baka, d'an lokaci kad'an zaka qaramin."

"Yana iya to , dole nayi hak'uri, na riga dana saba da wannan jikin naki Khairat da salonki , zaiyi yuwa na iya *rayuwa ba tare dake ba*." duk yayi maganar nan yana shafar qirjinta kamar zai ciresu.

Ita kam wani murmushin gefen labb'a ta masa dan kuwa hak'arta ta cinma ruwa, kuma ko iya haka aka tsaya, to tayi nasara akan Umar Faruk.

_Me kuka ce ne my fan's.???_
02/08/2019 à 06:55 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 20 to 25



_Bismillahir rahamanir raheem_




A jiye kwanan abincin tayi sannan ta zauna tana ci gaba da cika tana batsewa, dan ita taso Raheenat ta barta taci uwarsu Farida, ita sam ta rasa wani irin sanyin hali ne ke ga Raheenat ayi tacin mutumcinta ba zata iya ramawa ba, ita fa bata iya juran irin wannan rashin mutumcin da rashin imanin wallahi, murmushi Mama tayi taje ta zauna gefen yaƙunanniyar katifarsu tana kallon Sameera, a hankali ta buɗe baki tace "ƴata me yasa kike son biye wa su Farida ne kuna rigima, su fa dama burinsu kenan, dan ba sabon abu bane a gurinsu, dan Allah ki rinƙa tausar zuciyarki kinji ƴata. "

Wani nannauyar numfashi Sameera ta sauke ta kalli Mama idanunta cike da ƙwalla tace "Mama ba zan iya juran ganin ana wulaƙantaku nayi shiru ba, Mama sufa sam basu da imani, ace tun safe baka ci komai ba a cikinka, sun kuma san kuna jin yunwar nan amma su sam babu ruwansu, kuma dan rashin tausayi da imani ba zasu bar Raheenat ta huta ba sai sun haɗata da aikin da yafi ƙarfinta, da wanne za taji Mama ? Da yunwar dake damunta ko kuma da aikin da suke sakata, gaskiya Mama ba zan iya yin shiru ba ina kallon wannan rashin imanin. "

Murmushi Mama ta kumayi tana jinjina irin soyayyar da Sameera takeyiwa Raheenat tace "to bacin abinki Sameera maganar naki zai hanasu yin abinda sukeyi ne, yau ne kika fara nuna ɓacin ranki a akan hakan, kuma sun bar abinda sukeyi, ina ce ma sai wanda ya ƙaru ? Sameera ya zamar mana dole muyi haƙuri da duk wani abinda zasuyi mana saboda muna cikin gidansu ne. "

Kamar Sameera zatayi kuka tace "to Mama dan kuna gidansu sai aka ce su wulaƙantaku, ku bar musu gidan mana, wallahi mutanen nan basu da imani da tausayi ko ƙanƙani. "

Mama tace "mu bar musu gidansu muje ina Sameera, kin ko san irin wahalar da muka sha kafin mu samu nan ɗin ma?, kina sane da *Halin Rayuwar* da muke ciki a wannan zamani namu, taimako yayi ƙaranci, rayuwar ya zama ramin kura, kowa daga shi sai ƴaƴansa, Sameera ki bar faɗin mu bar gidan nan dan bamu da inda za muje in muka bar nan ɗin."

Sameera tace "wallahi Mama da da ɗaki a gidanmu da na roƙi Babana ya baku, to babu ɗaki shi yasa, amma insha Allahu komai ya kusan zama tarihi. "

Murmushi Mama tayi cike da ƙaunar yarinyar tace "to Allah yasa ƴata. "

Janyo kwanar abincin Sameera tayi tace "yauwa Mama sauko ki ci abinci kafin Raheenat ta ƙarasa aikin ta zo. "


Cikin jin daɗi Mama tace "Sameera ba dai zaki bar wahalar da kanki ba ko akan kawo mana abinci. "

Turo baki Sameera tayi tace "Mama meya abin wahala a cikin kawo muku abinci, dan Allah kibar cewa haka, yanzu dai dan Allah zo ki ci. "
Ta ƙarasa maganar tana buɗa ƙwanan abincin.

Riƙe hannunta Mama tayi tace "rufe ƴata, bari Raheenat tazo sai muci tare, nasan ta fini jin yunwa. "


Cike da matuƙar tausayinsu Sameera take kallon Mama, wannan soyayya tsakanin uwa da ɗiyartan yana burgeta, da wahala kaga ɗaya ya saka wani abu a bakinsa ba tare da ya tabbatar ɗayan ya ci ba, bata ƙara wani maganar ba sai ga Raheenat ta shigo ɗakin, daƙyar sallamar ma ta fito saboda yunwar da takeji, har wani jiri-jiri take gani, da kallo suke binta har tazo ta zauna kusa da Mama, Mama ba tayi wani magana ba ta janyo kwanan abincin ta buɗe tare da turawa gaban Raheenat, ɗago ido Raheenat tayi ta kalli Mama, Mama tasan ma'anar kallon hakan yasa ta saka hannunta tare da yin bismillah ta ɗibo loma, itama Raheenat ɗin sai ta saka hannu tare da bismillar suka fara cin abincin, ƙwallar da ya ciko idanun Sameera ta saka hannu ta share tana ci gaba da kallonsu, miƙewa tayi tsam ta ɗebo musu ruwa a randa tazo ta ajiye musu a gabansu sannan ta koma ta zauna.

Murmushi Raheenat tayi tace "mun gode my meera, Allah ya biyaki da gidan aljanna, yanda kike jin tausayinmu ubangiji kema yaji tausayinki. "

Itama murmushi Sameerar tayi tace "ameen ameen my Heenat, karki damu matuƙar muna tare to sai inda ƙarfina ya ƙare gurin taimakonku. "


Murmushi kawai Raheenat tayi ta ci gaba da cin abincin, suna kammalawa ta ɗauki ruwa tasha tace "Alhamdulillahi. "

Tana faɗin hakan ta miƙe da sauri ta nufi hanyar fita daga ɗakin.

Sameera ce tace "ina zaki kuma my Heenat.?"

Bata juyo ba tace "abincin zan duba ko ya ƙarasa dahuwa. "

Itama Sameera miƙewa tayi tabi bayan ƙawar nata suka fice.



Har lokacin su Farida na zaune suna aikin matsar waya, ko kallon inda suke Sameera ba tayi ba danji takeyi kamar taje ta rufesu da duka ko taji sanyi a ranta, nan ta taimaka wa Raheenat suka sauke tukunyar daga kan murhu domin shinkafar ta tsanye, ganin Inna har lokacin bata shigo daga gidan Alhaji Naseer buzu bane yasa Raheenat ta kalli Farida cikin sanyin murya tace "Farida na gama abincin. "

Ba tare da Farida ta ɗago ta kalleta ba tace "to dangin yunwa kije ki ɗauko kwananku na zuba muku ke da munafukar uwarki. "

Rintse ido Raheenat tayi cikin jin zafin kalaman Farida tace "Farida ki iya bakinki akan mahaifiyata, wallahi ina iya juran komai amma banda cin mutumcin mahaifiyata. "

Tana gama faɗin hakan ta nufi hanyar ɗakinsu tana share hawayenta, Farida kuwa cikin ɗaga murya tace "naƙi in iya bakin nawa, dukana zakiyi ne Raheenat, nace dukana zakiyi, ai da kin tsaya kin saka min hannu shine zansan ranki ya ɓaci da kalamai na, banza kawai dangin mayu. " ran Sameera fa in yayi dubu to ya ɓace, cikin fusata take kallon Farida, wallahi taci darajar Mama tayi mata magana yau da zai ta koyawa Farida hankali a gidan nan, sai dai kome zai faru ya faru, amma ta ɗauki alƙwari a ranta sai ta koyawa Farida hankali ko ba yau ba.

Raheenat ce ta fito ɗauke ɗa kwano a hannu ba tare da ta kalli Faridar ba tace "gashi."

Dariya Fa'iza tayi tace "gashi dai duk gorin da za'ayi muku bakwa zuciya da abincin kuce baza ku ci ba. "

Farida ta amshe da cewa "to su mayi zuciyar ai sune zasu zauna da yunwar ba wani ba. "

Raheenat dai ba tace komai ba har Faridar ta taso ta zuba mata abincin tare da ɗaukar tukunyar ta nufi ɗakin Inna dashi, itama ɗaukar nasu tayi takai ɗaki sannan ta dawo ta haɗa wanke wanke Sameera ta tayata suka wanke, sai da Sameera ta tabbatar ta gama aikinta a wannan lokacin sannan tayi masu sallama ta tafi gida tare da cewa zata biyo mata islamiyya in ta shiryo...

****************

Koda Inna ta shiga gidan kai tsaye b'angaren Hajia Luba ta nufa kamar yanda ta saba, ta sameta akan lumtsumemiyar kujera 3 seater tana waya, qasa ta zauna kusa da qafafun Hajia Luba kamar yanda take kullum tana kallonta tana murmushi tana ji kamar Allah ya ara mata lokaci itama ta dama wannan damar, saida ta d'auki kusan minti ashirin kafin ta gama wayar kuma duk maganar kud'i ce take kafin ta kashe wayar, ba tare data kalleta ba tace "Ramatou."

"Na'am Hajiata." ta fad'a tana sunkuyar

Please Login or Register in order to submit comment