Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kai.

Cike da qasaita da isa take magana d'aya bayan d'aya "wannan yarinyar dake zaune a gidanki, ta shiga aikin daba nata ba d'azun, shin ke kika aikota ko kuma gaban kanta ne tayi?"

Shiru ta d'anyi kafin tace "aiko ina jin Raheenat, Hajiata wani abun tayi halan?"

Saida ta sauke numfashi tace " kamar yanda na fad'a miki ta shiga aikin daba nata ba, domin kuwa ta taimakawa Abdul Hakeem da ruwa, kuma ke sanin kanki ne duk wanda ya taimaki Abdul koda da addu'a ne, to yakan samu hukunci daga wajen Hajia Luba."

Cikin washe baki tace "ni kam na sani Hajia, saboda hakan ma yasa kika saka boka ya rufewa duk wani d'an uwanshi baki dan gudun karsu bishi da addu'a."

Sai lokacin kad'ai ta kalleta a wulak'ance, hakan yasa ta kama bakinta tayi shiru, shiru d'akin ya d'auka na 'yan wasu dak'ik'u, mahaifiyar Abdul Hakeem ce ta fito daga kicthen d'in dake gefe dasu d'auke da faranti ta k'awatashi da kayan ciye ciye iri iri ta nufo Hajia Luba dashi, tana zuwa ta sunkuya har qasa ta aje farantin tare da fad'in "Hajia gashi."

Shiru tayi kamar ba zata amsa ba kafin tace "ok, idan kin shiga ciki, saiki d'ora mana tuwon shinkafa da miyar kuka, kisa busashen kifi a ciki shi nake sha'awar naci da dare."

"To Hajia, amma dan Allah ki ban dama zanje na mayar da Abdul Hakeem d'akinshi? nasan yanzu ya 'kosa da zaman can d'in."

Saida ta gama hararanta sama da qasa kafin tace "kije, kuma karki wuce minti uku."

"Na gode Hajia." ta fad'a ta tashi ta fita da sauri, sam ba zaka rabata da mai aiki ba saboda kayan jikinta da gaba d'aya yanayinta.

Tana zuwa ta sameshi kam ya gaji da zama wuri d'aya, abinda ya tayar mata da hankali wanda take da tabbaci saiya d'auketa tsawon lokaci shine, b'ata jikinshi da yayi da bahaya, saida ta goge hawayen dake idonta ta shafi kanshi tace "kayi hak'uri Abdul, nima ba'a son raina na barka nan ba, yanzu ma minti uku aka bani nazo na mayar da kai, gashi kuma ka matsu harka b'ata jikinka."

Qara share qwalla tayi sannan ta tura kujerarsa izuwa b'angarensa, ba laifi baban falo da kuma d'akuna guda uku a ciki sai kicthen da toilet a falon bayan ko wane d'aki akwai toilet d'in, d'akin tsakiya ta shiga dashi anan ne d'akinshi, kai tsaye toilet ta wuce dashi, saida ta cire masa kayan jikinsa ba tare da tana kallon jikinshi ba kafin ta wanke masa jiki, fitowa sukayi ta sake mishi wasu kayan ta fesheshi da turare kafin ta tallaboshi da qyar ta zaunar dashi saman gado, duk abin nan da take masa idonshi rufe dan yakai munzalin da yake jin kunyar mahaifiyarshi duk lokacin da take masa irin wannan d'awainiyar, ganin idonshi rufe yasa ta shafi gefen fuskarshi tace,

"Kayi hak'uri Abdul, wata rana sai labari, ni mahaifiyarka ce kuma ni kad'ai ce zan iya maka wannan hidimar, nasan kana jin kunya amma fa ka sani zaka fi jin kunya idan akace matarka ko wani ne ke maka wannan abun, dan haka kayi hak'uri kaji, ni zan koma na d'ora abincin dare, zanzo na baka abinci sannan na wanke kayan daka b'ata, nasan kana jin yunwa, amma ba'a bani damar da zan baka abincinka ba."

Ganin yaki bud'e ido yasa ta fita ta barshi cike da tausayi, d'akin Hajia ta koma ta samu suna hira qasa qasa ita da Inna, wucewa tayi kicthen yayin da suka ci gaba da hirarsu.

Inna ce tace "aini Hajia wallahi da zaki amince ma, Allah dasai a had'a tsinanniyar yarinyar nan da waccen musakin aure, kinga ni zanyi maganinta ita da uwarta, ke kuma kin qara samun wata 'yar aikin, bauta kawai zata zo tayi."

"Haba Ramatou, ni zan yarda a yiwa Abdul aure a yanzu, miye anfanin hakan to? taimakonsa za tayi ni kuma bana so."

"Hajia ai saikin so zata taimakeshi, da zaran ta shigo gidan kika gindaya mata sharrud'anki da aiyukanta a cikin gidan ai kin gama da ita, ita fa kamar jaka ce shegen aikine da ita."

Shiru ta d'anyi duk da dai bata ga wani anfani a auren ba, amma koba komai zata hukuntata saboda taimakon data masa, kuma zata iya zama mai aikin 'ya'yanta, tunda dama tak'i d'aukar masu aiki mata saboda bata san matsala.


*Muje zuwa tare da*


_Meeraheenat_😘
02/08/2019 à 07:09 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 25 to 30




Bismillahir rahamanir raheem






Inna kuwa ganin shirun na hajiya Luba yayi yawa ne yasa ta ƙara gyara zama cike da makirci ta neman tusa kai tace "
02/08/2019 à 22:19 - ~NANA KHADIJA~😍: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 25 to 30




Bismillahir rahamanir raheem






Inna kuwa ganin shirun na hajiya Luba yayi yawa ne yasa ta ƙara gyara zama cike da makirci da neman tusa kai tace "Hajiya karki saka wani tunani a ranki, babu abinda zai faru insha Allahu, Raheenat bata da damuwa sam, sai yanda kikayi da ita, ina tabbatar miki da cewa baiwa Raheenat zata zamar miki fiye da hajiya maryam ma, kinga a lokacin ne zaki samu damar hukuntata akan laifinta, kuma ma ai ba hakanan zaki ƙyaleta ba in anyi auren, dole zaki gindaya mata sharuɗɗanki kamar yanda nace miki a baya, kuma dole ta bisu ko taƙi ko taso. "


Wani irin murmushi Hajiya Luba tayi, cike da isa ta ƙasaita tace "naji shawararki Ramatou, zan duba nayi shawara akai, abinda na yanke zan sanar dake. "

Cikin jin daɗi Inna tace "Allah yasa muji Alkhairi Hajiyar Allah, uwargida a gidan Alhaji Naseer, Allah yaja da ranki ki daɗe kina zuba mulkinki. "

Murmushin gefen kumatu hajiya Luba tayi tana jin kanta na fasuwa tace "Ramatou ga abin taɓawa nan ki ci."

Ai Inna kamar jira takeyi ta fara aikawa cikinta babu ƙaƙƙautawa, ita kuwa hajiya Luba remote ta ɗauka ta mayar da hankalinta kan tanƙamemen tvn dake manne a falon tana kallo.


**********


Misalin ƙarfe huɗu Sameera ta biyowa Raheenat zuwa makaranta, lokacin da Sameera ta shigo gidan bata samu kowa a tsakar gidan ba, hakan yasa kai tsaye ta shige ɗakinsu Raheenat, gaisawa sukayi da Mama cikin sauri Raheenat ta shirya cikin koɗaɗɗun uniform ɗinta suka fito suka wuce islamiyyar, suna tafe a hanya suna hirarsu har suka isa.

Sun samu har malam ya shiga aji, cikin sauri suka nemi guri suka zauna tare da ciro littafansu, dan yau ba ranar taran latti bane.



**********


Sai gurin ƙarfe biyar hajiya Maryam ta kammala girkin da Hajiya Luba ta sanyata ta zuzzuba a kula, ɗauko abincin Abdul-Hakeem tayi sannan ta fito ta duƙa har ƙasa cike da girmamawa tace "na kammala da komai Hajiya, babu wani abu da za'ayi.?"

Cike da isa da wulaƙanci Hajiya Luba tace "babu" ba tare da ta kalli hajiya Maryam ba.

Cikin sanyin murya hajiya Maryam tace "to hajiya zanje na bawa Abdul abinci, nasan yana can yana jirana. "


"Ok, kije, sai dai karki manta akwai gogan kayana da zakiyi, da zaran kin kammala bashi abincin sai kizo kiyi aikinki bana son ɓata time, kinji na faɗa miki. "

Cike da girmamawa tace "to hajiya, insha Allahu bazan ɓata lokaci ba. "
Tana gama faɗin hakan ta fice falon da sauri ta nufi ɓangaren Abdul dan bashi abinci, tasan yanzu ya riga da ya galabaita da yunwa, hawaye ne taji sun tawo mata tayi sauri sa hannu ta sharesu a fili tace "akwai Allah. "


Hajiya Maryam na fita Inna ta kalli hajiya Luba tace "aikinki na kyau hajiyar Allah, gaba ɗaya kishiyarki ta zama baiwarki, gaskiya ke babba ce hajjaju. "

Taɓe baki hajiya Luba tayi tace "an gaya miki Luba ta wasa ce ?, kaɗan daga aikina kenan Ramatou, ace kamarni bacin ƙaddara taya ma za'ace anyi min kishiya, kishiyar ma har tazo ta haihu, haihuwar ma ɗa namiji wanda ni ban haifa ba, ke kanki kinsan ba zan barsu haka ba. "

Murmushi Inna tayi tace "na sani hajiya, kinfi gaban nan, babu wanda zai ja dake ya zauna lafiya, in ko mutum ya zauna lafiya ke kika so, ni bari na zo na koma gida, dama gaisuwa ce nace bari na kawo, naga kwana biyu ban zo na kawo gaisuwa ba. "

Cike da ƙasaita tace "kin kyauta kuwa Ramatou, " jakarta ta ɗauka dake kusanta ta buɗa ta ɗauko 5000 ta miƙawa Inna tace "ga wannan Ramatuo ayi hidimar gida dasu. "

Nan fa Inna ta zube ta dinga zuba godiya, har saida hajiya Luba ta ɗaga mata hannu alamun isa sannan ta dakata, ta miƙe tayi mata sallama ta fito daga gidan ranta fes.


*******


Hajiya Maryam na shiga ɗakin Abdul-hakeem ta iskeshi gar lokacin kwance yanda ta barshi idanunsa lumshe yana hango kyakkyawar fuskar Raheenat lokacin da take bashi ruwa, da sauri ta ƙarasa kusa dashi tana faɗin "yi haƙuri ɗan Mommynsa, ga Mommynka ta dawo baka abinci buɗe idanunka kaji ɗan albarka. "

Buɗe idanun yayi yana kallon Mommyn nasa, wani irin zafi tare da tuƙuƙi ya keji cikin ransa ganin yanda muguwar matar nan ta mayar da Mommynsa ƴar aiki da ƙarfi da yaji, be san sanda hawaye ya zubo masa ba, ganin hawayensa ne yasa hajiya Maryam ruɗewa, cike ta tausayin ɗan nata da ita kanta tace "subhanallahi, Abdul kuka kuma.?"


**********


Biyar da rabi daidai yau aka tashi su Raheenat daga islamiyar, hakan yayiwa Raheenat daɗi sosai, dan zata samu damar kammala aikinta da wuri yau, dan tasan yanzu tana komawa wanke-wanken kwanukan da suka ci abinci nanan na jiranta da kuma gyaran ɗakinsu Farida da na wannan ɗan iskar Sadiq.

Daidai ƙofar gidan su Raheenat Sameera tayiwa Heenat sallama ta wuce gida ita kuma Raheenat ta saka kanta cikin gidan kanta tsaye.

Karo kawai taji tayi da mutum ba tare da taji zuwansa ba, da sauri ta ɗago kanta dan ganin wanene, aiko sai ta sauke idanunta kan Sadiq da yake tsaye yana binta da wani mayen kallo yana lashe laɓɓa......

Ja tayi da baya amma saiya rik'o hijabinta yana janyota, duk da Raheenat nada hak'uri, amma ba zata iya zuba ido aci mutuncinta ba ta hanyar keta mata haddi ko kuma muzanta mahaifiyarta, hakan yasa tayi k'arfin halin fizge hijabinta daga gareshi tana fad'in "haba yah Sadik, wai me yasa ne kake haka? me yasa ba zaka duba girma da darajar yaya da nake baka ba? kai kullum burinka ka zubar min da mutunci."

Sake kashe mata ido yayi yana ci gaba da lashe labb'anshi harda d'an tsizawa yake kafin yace "matsalata dake kenan, wannan gidadancin naki, bansan yaushe zaki waye ba?"

A hassale tace "in dai abinda kake nema a guna ne na hanaka shine wayewa, to ka sani har abada ba zan tab'a wayewa ba, zanci gada da zama a cikin wannan duhun kai, dan shine kad'ai zaisa na tsira da mutunci na."

"Ai kuwa kota k'arfi saina rabaki da mutuncin, dan banga anfanin da kuke mana a gida ba, kufa kamar bayi ne a garemu, kinga kuwa dole kuyi abinda muke so."

"Ba dole, kamar yanda mu ba bayi bane, kuma Allah shine zai tayani kare mutunci na daga ire irenku marasa tsoronshi."

Matsowa yayi kusanta tare da zura hannu yana shirin rik'o k'ugunta, ganin abinda yake shirin yi yasa tayi saurin tureshi da iya k'arfinta harya kusan faduwa tare da kaiwa bango karo, zafi yaji sosai hakan yasa yana d'agowa ya wanketa da wani bazawarin mari, qara ta fasa mai k'arfi saboda yanda taji marin, kafin ta dawo hayyacinta ta kuma jin wani sabon marin, duk'ewa tayi a wajen ta fashe da kuka sosai.

Mama dake zaune a d'aki tun a marin farko taji gabanta ya fad'i, da sauri ta mik'e tsaye jin qarar Raheenat kuma ya tabbatar mata da wani abu ya samu 'yarta, amma tunda cikin gidan ne ba yanda za tayi daya wuce taja baki tayi shiru.


Inna dake fitowa daga ban d'aki duk taji meya faru, kuma taji laifin na d'anta ne, amma saita rufe ido ta shigo soron ta samesu, "meya faru, meka mata Sadik?"

Jin muryar Inna yasa Raheenat mikewa da k'arfin gwiwa ta fara cewa "Inna, yah Sadik ne yake min maganar banza, kuma ba tun yau ba ya jima yana haka, na fad'a mishi ya daina amma yak'i, shine yanzu....."

"Ke dallah rufe min baki." wannan tsawar ce tasa tayi shiru kamar an d'auke wuta.

Kafinta ankara ta finciko hijabinta bata tsaya da ita ko ina ba sai tsakar gidan,
Inna ce ta ci gaba da cewa "ke har kina da wani abinda Sadik zai dinga bibiyarki? wacece ke da zakiwa d'ana qazafi? kenan yanzu abun naku ma harda sharri a ciki? to bari kuji daga ke har bakar uwar taki , wallahi kika sake shiga hanyar d'ana saina wulak'antaki, haka kawai saboda jaraba kin tsotsa a nono shine kike bibiyar Sadik."

Cikin kuka Raheenat tace "wallahi Inna ba qar...."

"Kenan ni kike so kice na nemiki? to me zanyi dake? mata sun qare a duniyar ne da zan rasa wacce zan nema saike?" Sadik ne ya katse.

Share hawayenta tayi tace "naji, tunda haka kace, kaje akwai Allah kuma shi zai mana sakayya , amma idan har kai d'an halak ne Sadik karka sake nemana."

Bawai Inna da Sadik ba, ita kanta Raheenat saida ta fad'a tayi mamakin kanta, Inna ce tayi kanta ba tare da tunanin komai ba ta fara kai mata duka tana fad'in "Raheenat ni? ni Raheenat kike shegantar min da yaro kuma a gabana, ke yanzu Sadik ne zaki kalla har kice in d'an halak ne shi? yau saina ci ubanki, koda yake bama uban gareki ba, sai naci uwarki a gidan nan."

Haka take fad'a tana dukanta, kuka da ihu kawai Raheenat keyi yayin da su Farida ke tsaye suna kallo suna mata dariya, shima Sadik d'in haka sai yake jin inama shine ke dukanta saboda yanda take shigewa jikin Inna, kamar daga sama sukaji sallamar da tasa Inna tsayawa cak yaran kuma kowa yasha jinin jikinshi.. .
05/08/2019 à 19:47 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*



```Muna godiya gareku makaranta wannan litttafin, haƙiƙa muna jin daɗin comment ɗinku, yana sanya mu nishaɗi sosai, har ma my meera take ce min my heenat anya ko baza mu ƙara musu yawan typing ba ko dan mu saka su nishaɗi suma kamar yanda suke saka mu ? Murmushi nayi kawai nace my meera duk yanda kika ce haka za'ayi😊, to fans ku huta kawai kuji daɗinku muna yinku sosai sosai, ku ci gaba da sambaɗa mana comment mu kuma zamu ci gaba da sambaɗo muku typing da yardan me duka🥰```



DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```


30 to 35



Bismillahir rahamanir raheem






Ƙara lumshe idanunsa yayi, hakan yasa wasu hawayen saukowa, a hankali hajiya Maryam ta saka tafin hannunta ta fara goge masa hawayen itama idanunta cike da ƙwalla, magana ta fara cikin sanyin murya tace "kayi haƙuri Abdul, haƙiƙa *komai yayi farko* to yana da ƙarshe, ina me tabbatar maka kamai zai zama tarihi watarana, nasan me kakeyiwa hawaye, to ka sani Allah yana sane da halin da muke ciki kuma ba zai barmu hakanan ba, ina ji a jikina zaka samu lafiya nan ba da daɗewa ba, ina ji ajikina Abdul ka kusa takawa da ƙafafunka, ka kusa buɗe baki kayi min magana da daddaɗan muryar nan naka me daɗin sauraro, dan Allah kabar kuka, bana son ganin hawayenka ko ƙanƙani, hakan na ɗaga min hankali, nasan Abdul ɗina ba rago bane jarumi ne, jarumi kuwa ba'a sanshi da saurin karaya ba. "

Kamar saukar ruwan sama da ɗaukewarsa haka hawayen Abdul suka ɗauke nan take, kalaman Mummynsa ba ƙaramin daɗi sukayi masa ba, sai dai baya da damar nuna mata hakan, ko murmushi baya da ikon yinsa wanda zai iya nuna mata yana farin ciki, idanunsa ne kaɗai suke iya fahimtar da ita farin cikinsa da baƙin cikinsa, kuma ta cikinsu ne kaɗai take iya gano abinda yake buƙata.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin yabar kukan, taimaka masa tayi ta zaunar dashi sosai sannan ta buɗe kular abincinsa ta ɗebo da hannayenta ta nufi bakinsa dashi.

Cikin hikima take bashi abincin, wani na shiga wani na fitowa, a haka ta kammala bashi abincin sannan ta bashi ruwa yasha, goge masa bakinsa tayi sannan ta miƙewa tayi ta nufi toilet domin wanke kayan da ya ɓata ɗazun.

Abudul-Hakeem yana ganin shigewar Mummynsa toilet ɗin ya mayar da idanunsa ya rufe ruf, fuskar Raheenat yaƙi barin ƙwak'walwarsa, yanzu ma da ya rufe ido ita yake hangowa, wacece ita ? shine tambayar da yake yi a zuciyarshi.



***********




"Subhanallahi! me nake gani haka Innar su Sadiq?" malam Habu ya faɗa yana ƙarasa shigowa cikin gidan.

Kame-kame Inna ta farayi saboda bata san me zata faɗi ba, gashi sam ba tayi tsammanin dawowan Malam Habu a wannan lokacin ba saboda balaguro ya tafi.

Cikin ɓacin rai ya zo ya ɗago Raheenat da take duƙe ƙasa tana kuka ya kalli Inna yace "yanzu Ramatou me yarinyar nan tayi miki ne kike mata irin wannan dukan na rashin imani ?, budurwa irin wannan kome za tayi miki ya dace ace kin kamata kina bugu haka, saboda Allah ke kin ga dacewan abinda ki kayi ?, wallahi Ramatou kiji tsoran Allah, ki sani zaki mutu. "

Kallon su Farida yayi cikin tsawa yace "ku ɓacen da gani anan gurin sakarkarun banza kawai shashashai. "

Aiko a guje sukayi ɗakinsu saboda suna matuƙar tsoron Babansu, Inna kuwa kasa magana tayi domin duk iskancinta tana shakkar me gidan nata.

Kallonsa ya mayar kan Raheenat da har lokacin take kuka cike da tausayawa yace " kiyi hak'uri kinji Raheenat, ina mahaifiyarki take?"

Da hannu kawai ta nuna masa d'akin nasu alamar tana nan, kama hannunta yayi suka nufi d'akin nasu yana hararan Inna dake d'arare har yanzu.

Tsaye suka samu Mama k'ofar d'akin tana hawaye, tana jin shigowarsu tayi saurin k'arasawa wajen yar katifarsu ta zaune tana share hawaye, kallonta yake harya karasa wajenta ya zaunar da Raheenat kusanta shi kuma ya tsugunna yana ci gaba da kallonta, "dama kina cikin gidan take dukanta haka? kuma kina ji kin kasa komai."

Shiru tayi kanta qasa, sake magana yayi " *Fateema* dake nake, me yasa za kiyi shiru kina gani tana neman sabauta miki 'ya? ko bake kika haifeta ba baici ace kinyi magana ba."

"Sannu da zuwa malam, anzo lafiya?" shine abinda Mama ta fad'a.

Kasancewarshi mai zafin zuciya yasa ya d'anyi qaramin tsaki ya mayar da kallonsa ga Raheenat, cikin muryar tuhuma yace "me yasa ki kayi haka Raheenat?"

A matuk'ar tsorace ta kalleshi ganin yanda yake kallonta yasa ta tsorata sosai, cikin kuka tace "wallahi Baba bana da laifi, laifin yah Sadik ne, shine yake min maganarrr...."

Kallon da Mama ta mata yasa tayi cak da maganarta, fuska a had'e ya kalli Mama kafin ya mayar da kallonshi ga Raheenat yace "ki fad'a min ina jinki, meya faru tsakaninki da Sadik?"

Saida ta had'e yawu ta kalli Mama da kanta ke qasa kafin tace "tunda muka zo nan yah Sadik yake yawan yimin maganganun banza, kullum ina fad'a masa ya daina amma baya ji, yanzu har takai yana cewa kota k'arfi ne saiya....."

Sai kuma tayi shiru saboda nauyin maganar, a fusace Baba ya tashi bai tsaya ko ina ba sai d'akinsu Sadik, Sadik na kwance akan qaramin gadonshi yana danna wayarshi bai ankara ba yaji saukar wani mahaukacin dundu a bayanshi, wata irin qara yayi mai kamar amai tare da yunk'urawa ya tashi zaune yana kallon mahaifin nashi da kana gani kasan sai dai Allah ya gyara kawai.

Kwalar rigarshi ya cabko ya fito dashi tsakar gidan yayi wurgi dashi ya zube qasa, cikin zafin nama ya d'auki d'aya daga cikin icen da Raheenat tayi d'ori ya kai masa duka a jiki yana fad'in "ni Sadik? ni? ni zaka zubarwa da mutumci a idon duniya? ni zaka zubarwa da mutumci a cikin unguwa? akan me zaka dinga yiwa marainiyar Allah maganar banza, rashin imani da gurb'acewar tarbiyarka har yakai haka dama? tirr , nayi bak'in cikin wannan ranar, Sadik yau d'in nan kasa naji ina nadamar haihuwarka da nayi, ina ma b'arinkkk."

Inna ce ta fito daga d'akin tana fad'in "a'a malam, akan me zaka dinga aibata d'anka akan wasu bare banzaye? saboda kawai sun fad'a maka qarya da gaskiya, a gaskiya bai dace ba ai kamata yayi ka tarasu kaji meya faru."

"Ke Ramatou, wallahi ki fita idona in rufe, ki kiyayeni fa, ki bari na gama dashi zanzo kanki, zanji dalilin dukanta da kike kamar jaka." duk yayi maganar ne yana nunata da icen hannunshi.

Komawa yayi kan Sadik ya d'aga iccen zai sake gabza masa yayi saurin rik'ewa yana neman afuwar Baba "dan Allah Baba kayi hak'uri ka yafe min na tuba, na tuba wallahi ba zan sake ba daga yau, ka yafe min dan Allah Baba wallahi ba zan sake ba."

Fizge iccen yayi amma yaji ya rik'e gam , da hannu ya nunasa yace "zaka gane dani kake magana, ka kuma shirya dan babu abinda zai hana na maka aure tunda na fahimci burinka shine ka tozartani."

Yana fad'a ya shiga d'akin Inna badan ransa naso ba sai dai kawai shine kawai d'akin da zai iya shiga, dan d'akin nashi shine ya kwashe kayanshi ya bawa su Raheenat suka zauna, Sadik ma tashi yayi cike da kunya da takaicin zafin rai irin na mahaifinsu , da girmanshi da komai ace ana dukanshi, ai sam bai kamata ba kuma ma saboda wata banzar yarinya.

_Koma meye kai kaja, dan ubannn..._

_Ohhh, my Heenat, me yasa zaki hanani na qarasa? da kin barni na nuna mishi_😏

******************


Hajia Maryam ce ta fito daga toilet tana goge hannayenta da hijabinta ta tunkaro wajen Abdul Hakeem, sunkuyawa tayi ta shafi fuskarshi tana murmushi tace "d'an albarka ana kwance, toni na gama zanje na d'anyi wanka dan magriba ta gabato, gaji sosai Abdul, amma dai zan dawo kafin na kwanta kaji."

Duk da mahaifiyarshi ce amma yasan ba gaskiya ta fad'a masa ba, yasan dole akwai wani aiki dake gabanta yanzun haka, d'an lumshe ido yayi alamar to kafin ta sake sakin murmushi tace "da kyau yaron Mamanshi."

D'agawa tayi ta juya zata fita taji an bud'o k'ofar d'akin, mahaifin Abdul Hakeem ne hakan kuma yasa gabanta ya tsinke ya fad'i tare da yin qasa da kanta lokaci d'aya alamar tsoro da fargaba ya rufeta, kanshi tsaye ya wuce wajen Abdul Hakeem ko kallonta baiyi ba dan inya kalleta ranshi ne zai b'ace, kuma da yasan zai sameta da bai shigo ba yanzun.

Tana ganin ya zaune kusan Abdul Hakeem tare da shafa kansa tayi wuf ta fita daga d'akin, kallon Abdul yake sosai ba tare da yace komai ba, yana jin soyayyar d'an nashi qwaya d'aya tak daya mallaka a duniya, kullum ya sauke idonshi a kan d'ansa saiya sake jin burin samun magaji , yana ganin da Abdul yana da lafiya da yanzu shike kula da kusan kashi biyu daga cikin uku na harkokinshi, amma kash larura ta masa cikas , *Raheenat*,

Please Login or Register in order to submit comment