Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana da barkwanci, Alhaji Naseer kuma yana samun farin ciki da annashuwa idan yana tare da ita, a haka har lokaci ya matso ya rage saura kwana biyar, fargaba da tashin hankali Alhaji Naseer ya shiga a wannan lokacin saboda baisan ta yanda zai fad'awa Hajia Luba maganar auren ba.

Yau ta kama ranar *juma'a* kwana biyu ya rage d'aurin aure, Alhaji Naseer ne ya zaune a bakin gado yana kallon Hajia Luba dake tsefe kai a gaban madubi cikin shirin kwanciya bacci, saida ta qarasa ta taso cikin kwarkwasa ta zauna akan cinyarshi, duk da ta fara rikitashi da kalar salonta haka ya saita kanshi ya rik'e hannunta ya fara magana murya na rawa, dan harga Allah yana jin shakkarta...


*Muje zuwa tare da*


_Meeraheenat_😍
21/08/2019 à 06:21 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```

_Bismillahi_rahaman_rahim._

*We Luv you*😍

Page _45 to 50_


"Hajiata, ina d'an son magana dake idan babu damuwa."

"Ina jinka Alhajina, ai yanzu lokacinka ne."

Gyara murya yayi yana jin bugun zuciyarshi na qara tsananta bugawa yace "dama ba wata magana bace sai...um...sai.."

"Haba Alhaji, ya kuma ka kasa fad'a? ina jinka mana."

Sake matse hannunta yayi yace "kinsan yanzu a rayuwar nan duk maison ya gama da duniya lafiya, to hak'ik'a sai yabi iyayenshi sannan zaiga daidai, kuma kinsan ace bin na gaba bin Allah, to a gaskiyar magana akwai wani hukunci da Hajia ta yanke a kaina wanda na kasa musa mata."

Tunda taji yace Hajia ta b'ata rai, dan tasan matar ba sonta take ba, a daqile tace "ka fito kamin bayani yanda zan fahimta."

Saida ya dauke idonshi daga ganinta yace "dama akwai wata yarinyar mak'otanta ce Maryam, to ta gamsu da nutsuwa da tarbiyarta, shine dai ta nema min aurenta, yanzu haka maganar da nake miki jibi ne d'aurin auren insha Allah."

A wulak'ance tace "me, aure fa naji kace, da gaske kake ko wasa?"

Ba tare daya kalleta ba yace "da gaske mana, ya zan miki maganar aure da wasa? bayan nasan ba kya so."

Tabb',zunbur ta mik'e daga kan cinyarshi kamar mahaukaciya tace "jar uban can, kishiya wai kake nufi, ni Hajia Luba ce kake tunanin had'awa da wata mace a doran duniya? to bari kaji, ko a lahira wallahi ni kad'ai zan zauna da kai bare a duniyar nan, gidan nan nawa ne ni kad'ai banga wacce ta isa ta shigo da sunan kishiyata ba wallahi, babu wacce ta isa ta shigo gidan nan harta had'a kafad'a dani wajen tarayya da kai, wallahi gidan nan nawa ne daga ni sai 'ya'yana, ina nan kuma zanga 'yar iskar fitsararra marar kunyar da zata shigo min gida, wallahi saina halakata ko 'yar gidan uban wacece, kai ka sani kuma kasan wacece ni, nafi k'arfin wannan tozarcin da kake neman yimin, ko gidanmu mahaifiyata kad'ai na gani tana rayuwarta, saini zanzo na had'a gida da wata banza wai a matsayin kishiyata, to mu zuba mu gani d'an halak ka fasa, zanga wacce ta isa ta shigo gidan harta wanke qafa tasa kayan bacci taje turakarka da sunan ta kai maka kwananta, wallahi zan maimaita maka, sai nayi ajalin kowace 'yar iska ce, aikin banza kawai."

A sanyaye ya mike tsaye shima yace " haba mamar Nabeela, ya kamata ki gane shifa aure nufin Allah, idan har Allah ya nufeka da qarawa to ba makawa sai kayi, kuma k...."

"Kuma me?" ta katseshi cikin d'aga murya.

"Aiba wani abinda zaka fad'a min, kuma kamar yanda na fad'a maka, ina nan ina zaman jira naga shed'aniyar da zata shigo min gida, wallahi zanyi maganinku daga kai har ita Hajiar data kitsa maka maganar k'ara auren cikin qwaqwalwa."

Tana fad'a ta fita ta bar d'akin ta koma b'angarenta kamar za tayi hauka, shi kuma hanakalinshi ne ya tashi ganin ran Hajia Luba ya 'bace kuma ta sanadiyarshi, b'angarenta yaje ya fara buga k'ofa amma ko jinshi ba tayi saboda tana can bedroom d'inta, haka ya gaji ya koma nashi ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka dai gari ya waye ba tare da dukansu sun rintsa ba, yana dawowa daga sallah asuba ma part d'inta ya koma yaci gaba da bugawa, a lokacin kuma tana shiryawa dan tafiya wajen wanda take ganin zai mata maganin matsalarta, shiru tayi bata kulashi ba saida taji ya daina bugawa sannan ta d'auko makullin mota da jakarta tare da waya ta fito, saida ta farawa mai gadi magana akan ya bud'e mata gate a hankali dan bata so Alhaji yaji fitarta sannan ta shiga mota, cikin sauri ta fita daga gidan cikin wannan duhun asuba ta kama hanyar wani qaramin qauye dake kusa dasu.


Zaune take a gaban mutumin kai da gani ba sai an fad'a ba kasan mushriki ne ajin farko saboda shigar dake jikinshi, cikin fitar hayyaci da b'acin rai Hajia Luba tace "boka *bandaru*, wannan ma ai maganar banza ce, ya za kace wannan aikin yafi qarfinka, yaune muka fara aiki dakai? naga kayi aikin da yafi wannan ma wahala, to me yasa ba zaka hanashi qara auren nan ba? akwai matsala babba inhar yayi auren nan, dan ina tunanin saboda tsayawar da haihuwa tamin ne yasa mahaifiyarshi tasa ya qara auren nan, kuma kaga akwai yiwuwar matar da zai aura tazo ta haifa masa d'a namiji, haka kuma ta faru wallahi zan iya kashe Alhaji ma baki d'aya, dan ba zan yarda ina ji ina gani ba wata tazo ta qwace gidan nan, alhalin ina tare dashi arzik'inshi ya qara bunk'asa."

A tsawace bokan yace "ke Luba!, ba'a daga mana murya anan, kuma kamar yanda na fad'a miki, wannan auren da mijinki tabbatancen aure ne kuma rubutacce, ba zamu iya ruguzashi ba saboda dole saiya faru, dan haka ki tashi ki koma gidanki ki jira amaryarki, idan kina buk'atar wani abu bayan auren kin dawo, duk da dai yarinyar akwai addini, amma ba za'a rasa yanda za ayi ba."




Jin abinda Boka yace ne yasa hajiya Luba cewa "Allah ya wuce zuciyar boka Bandaru, dole ne ma in dawo ai, domin wallahi bazan taɓa barinsu suyi farin ciki ba. "

Wata irin dariya boka yayi yace "shegiya Luba, ai nasan halinki bakya da imani, tashi kije sai kin sake dawowa."

Miƙewa tayi jiki a sanyaye ta fice daga cikin ƴar bukkar nashi tana jera masa kikarari har ta fita.



Koda hajiya Luba ta koma gida ɓangarenta ta shiga ta fara zirga-zirga hankalinta a matuƙar tashe, "yanzu dole sai anyi auren nan, ta yaya ni Luba zan zauna da kishiya ? Ina! ba zai yiwu ba. "
Ta faɗa da ƙarfi tare da buga hannunta jikin ba bangon ɗakin.


Alhaji Naseer kuwa jin hajiya Luba taƙi buɗe ƙofar hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba, dan ya tsani ɓacin ran Hajiya Luba ko ƙanƙani, komawa part ɗinsa yayi ya zauna ya rasa me zaiyi, da zai iya da ya fasa auren nan dan farin cikin hajiya Luba, sai dai baya jin zai iya fasa auren nan, yana jin son Maryam sosai a ranshi, ta yanda yake ji inda yabarta zai shiga cikin wani hali, daɗin daɗawa yana matuƙar son samun ɗa namiji, duk da baya da tabbacin samun ɗa namijin in anyi auren.

Miƙewa yayi ya ƙara fitowa zuwa part ɗin nata ko zaiyi sa'a ta buɗe, cikin sa'a yana tura ƙofar part ɗin nata yajita a buɗe.

Cikin sanɗa ya shiga kamar mara gaskiyya, kai tsaye ɗakinta ya nufa, a hankali ya turo ƙofar ɗakin ya shiga da sallama, a tsaye ya sameta tana takai da kawo har yanzu, kamar me safa da marwa, suna haɗa ido dashi tace "Naseer ka fita min daga ɗaki bana son ganinka, wallahi na tsaneka maci amana kawai. "

Rintse ido Alhaji Naseer yayi ya taka a hankali kusa da ita ya rungumota jikinsa, fisge-fisge takeyi tana son ƙwace kanta daga jikinsa shi kuma yaƙi bata damar hakan, cikin kunninta yake taɗa maya "ki nutsu hajiyata, dan Allah ki tsaya ki saurareni nayi miki bayani, kamar yanda nace miki ne ba laifina bane, hajiyace kawai ta neman min auren, kuma sanin kanki me ba na iya musu da hajiyarmu, amma ke kanki kin sani ke kaɗai ce macen da nakeso kuma nake burin zama da ita, sanin kanki ne kece farin cikina, bana son ɓacin ranki ko kaɗan, to ta yaya kike tsammanin zan nemi auren wata macen alhali kina tare dani, ki yarda dani Luba ba a san raina za'ayi auren nan ba. "

Waɗannan kalaman na Alhaji Naseer ne ya dakatar da hajiya Luba daga ƙoƙarin raba jikinsa da nata, haƙiƙa tasan ko wani kalmar nasa ba gaskiya bane wani gaskiya ne, amma yanda take jin zuciyarta ba ta jin zata iya haƙurin ganin mijinta da wata mace, yanzu mafitarta ɗaya ce kawai ta kwantar da kanta ga Alhaji ta nuna masa komai ya wuce, daga baya tazo ta ɗauki matakin da ya dace akan tsinanniyar yarinyar da zata shigo mata gida, ba ita kaɗai ba har hajiyar sai ta ɗauki mataki akanta dan taga matar na neman shiga rayuwarta sosai.

A hankali ta raba jikinsa da nata cikin taushin murya tace "ok Alhajina, na yarda da abinda ka fad'a kuma na gamsu, fatana yanzu kawai Allah ya bamu zaman lafiya, kai kuma Allah ya baka ikon yi mana adalci."

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "my Hajiata, i really proud of you, that why i like you."


Daga ranar Hajia Luba ta fara nuna masa kamar ba komai, har aka daura auren Alhaji Naseer da Maryam......


*Muje zuwa tare da*


_Meeraheenat_😍


_Barka da sallah yan uwa🤝 Allah ya maimaita mana_
21/08/2019 à 06:21 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*


*MUNA BAKU HAƘURI MASOYAN WANNAN LITTAFI DA RASHIN POSTING AKAI AKAI DA BA BAYI YANZU, HAKAN NA FARUWA NE SAKAMAKON WASU UZIRI DA SUKA SHA MANA KAI MU DUKA, KU ƘARA HAƘURI INSHA ALLAHU KOMAI ZAI DAIDAITA NAN BADA DAƊEWA BA, MEERAHEENAT SUNA YI MUKU FATAN ALKHAIRI.*



DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page _50 to 55_




Bismillahir rahamanir raheem




Daran da aka kawo amarya ƙiri-ƙiri hajiya Luba ta hana Alhaji Naseer shiga ɓangaren amarya ta tilasta masa kwana anata ɓangaren, amarya kuwa tana can tana jiran ango babu ango babu labarinsa, haka ta gaji da jira har bacci ya kwasheta, haka aka ɗibi kwanaki huɗu da ɗaura auren nan amma hajiya Luba sam taƙi bada wani ƙofa da Alhaji Naseer zai keɓe da amaryarsa, gaba ɗaya tabi ta kankane komai, Maryam amarya ta shiga damuwa matuƙa ganin an kawota gidan mijinta amma ganin mijin yayi mata wahala, shi kanshi Alhaji Naseer cikin damuwar yake, yana matuƙar so ya keɓe da amaryarsa amma sarautar matar ta hanasa.


Yau ma zaune suke a falonshi hajiya Luba duk tabi ta kanenayeshi, kusan rabin jikinta yana jikinshi sai faman zuba masa shagwaɓa takeyi kamar wata karamar yarinya, shafo fuskarshi tayi cikin kissa tace "Alhajina ina so kayi min wani alƙawari ne dan Allah. "

Kallonta yayi cikin sakin fuska yace "ina jinki hajiyata, faɗi ko wani irin alƙawari ne ni me yi miki shine. "

Ƙara lanƙwashe murya tayi cikin salon makirci tace "alƙawari nakeso kayi min ba zaka taɓa kusantar amaryarka ba, kaga kai kanka ba sonta kakeyi ba dole akayi maka ka aureta, ni kuma sam ba nason sharing ɗinka da wata macen, wallahi Alhaji zan iya mutuwa duk randa ka kusanci wata mace bani ba, dan Allah kayi min wannan alƙawarin ba zaka taɓa kusantarta ba Alhajina."
Ta ƙarasa maganar cikin salon makirci da kitihi tana wani shafa jikinsa tare da kashe masa idanuwa.

Salon da takeyiwa Alhaji Naseer gaba ɗaya ta rikitashi ya fara fita a haiyacinsa, cikin wani irin amon murya wanda kana jinsa kasan yana cikin matukar sha'awa yace "amma hajiyata bakya ganin hakan zai zamo cutarwa ga ita yarinyar, amanace ita ɗin aka bani fa, ina naci amanarta Allah fa ba zai barni ba. "


Ɗan haɗe rai hajiya Luba tayi tace "me kake nufi Alhaji, kar dai kace min ka fara son yarinyar ne.?"


Cikin in ina yace "a'a hajiyata ba haka nake nufi ba, amma kin...."


Katseshi tayi kafin ya ƙarasa tace "amma me Alhaji, nufinka dai yanzu ba zaka iya min alƙawarin ba kenan ?, hmmmm, ai sai yanzu na ganoka Alhaji, wato dai kana son yarinyar kuma kana son kusantanta, hakan ne yasa ba zaka iya yimin alƙwari ba ko.?"
Tayi maganar tana tsaresa da idanunta.

Janyota yayi jikinsa ya rungume cikin sanyin murya yace "ba haka nake nufi ba hajiyata, sanin kanki ne ke kaɗai kin isheni ba sai na haɗaki da wata ba, abinda ina so ne ki gane shine Maryam amana ce aka bani, be kamata ace na watsar da amanar ba tun kafin akai ko'ina, dan Allah zai iya kamani da laifin cutar da ita."

Shafa ƙirjinsa ta fara cikin wani irin salo, gaba ɗaya riga ta rikita Alhajin cikin raɗa raɗa tace "indai da gaske baka sonta wannan hanya shine kawai mafita Alhajina, kaga ita kanta in taga baka kulata ba zata zauna ba, da kanta zata nemi takardanta, kaga shikenan sai ka sallameta mu ci gaba da zamanmu mu kaɗai kamar yanda muke ada. "

Cikin fitar haiyaci Alhaji Naseer yace "shikenan Hajiyata, duk yanda kika ce haka za'ayi."

Cike dajin daɗi hajiya Luba ta ci gaba dayiwa Alhaji wani irin salo tare da raɗa masa a kunni cewa "shi yasa nake sonka Alhajina. "
Daga nan kuma komai ya kwance musu suka lula wata duniyar.




Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya musu har aka samu tsawon sati uku da kawo Maryam gidan amma hajiya Luba ta hana Alhaji Naseer shiga ɓangarenta ya dubata ma balle ayi wani maganar haƙƙinta na aure, zuwa lokacin kuwa hankalim Alhaji Naseer in yayi dubu to ya tashi, ya rasa hanyar da zaibi ya ga amaryarsa, idon hajiya Luba na kansa gaba ɗaya, ga wani sabon tsoranta da gudun ɓacin ranta da ya keji yanzu , ɓangaren Maryam ko tayi kuka har ta gaji, ta rasa wani irin jarabawa ce wannan, da farko dai ta shiga cikin damuwa tare da tunanin me Alhaji Naseer yake nufi da ita, dama ba sonta yakeyi bane ya aureta, ko dama ya aureta ne dan ya wulaƙantata ? Amma sai zarginsa da ƙudirin da tayi akansa duk randa yazo gareta ya kau a lokacin da ta samu baƙuncin hajiya Luba cikin falonta, ranar tana zauna ta rafka tagumi tana hawaye tare da tunanin halin da take ciki hajiya Luba ta shigo, bayan ta gama ƙare mata kallo ita da falon nata a wulaƙance ta fara mata gargaɗi akan mijinsu, tare da yi mata ikirari da cewa Alhaji nata ne ita kaɗai, babu wacce ta isa ta shigo tsakaninsu, sannan ta ƙara da ce mata ita take da iko dashi, sai abinda tace yayi yakeyi, dan haka ta saka a ranta tazo mata bautane kawai nan da ɗan lokaci ƙanƙani, amma ba zaman aure ba, domin Alhaji baya da wata mata bayan ita kaɗai, nan dai ta gama yi mata tijara kafin ta fice tabar Maryam na rusar kuka, tun daga wannan rana Maryam ta dage gurin miƙawa Allah kukanta, Allah maji roƙon bayinsa, cikin satin wani biki ya tasowa Hajiya Luba na ƴar aminiyarta dake Kaduna, nan ta fara shirin tafiya, ranar da zata tafi haka ta dinga yiwa Alhaji gargaɗi kan kar yaje ga Maryam, shidai da to yake amsa mata har sukayi sallama direba ya jata suka kama hanyar Kaduna, ai Alhaji Naseer kamar jira yakeyi da saurinsa ya juya ya nufi ɓangaren Maryamu.


Kwance ya sameta saman kujera three seater hannunta riƙe da carbi tana ja yayin da idanunta suke a lumshe, wani irin tausayinta ne yaji ta taso masa tun daga ƙasan ransa, da ɗan sassarfa ya ƙarasa kusa da ita.

Saida taji tsoro saboda jin an tab'ata, a zabure ta tashi har d'an kwalinta ya zame ya fad'i, ido tsaye take kalleshi ba ko k'yabtawa, qasa yayi da nashi idon yana tunanin abinda zaice mata, da qyar ya fara da "Maryam kina lafiya?"

Wasu ƙwalla ne taji sun zubo mata, dakewa tayi tace "abinda kazo tambaya kenan.?"

Da sauri ya kama hannunta yana matsawa alamar rarrashi yana fad'in "Maryam, dan Allah kiyi hak'uri ki gafarceni, nasan ni mai laifine a gareki, amma dan Allah ki taimaka ki yafe min, wallahi nima ba'a son raina bane, kullum ina tunaninki kuma da tunaninki nake wuni, amma na kasa samun damar da zan iya zuwa inda kike, Maryam ki gafarta min dan girman Allah, wallahi idan baki yafe min ba zan shiga tashin hankali, kuma kema kinsan haka a matsayinki na mai ilimi."

Kallonta yake yana jiran yaji me za tace, ita kam tayi qasa da idonta kuka ne ya qwace mata, hankalinshi ne tashi dan haka ya matso kusa da ita ya rumgumota jikinshi ya fara rarrashi, da qyar ya samu ta tsagaita da kukan kafin yace "yanzu fad'a min me kike so?"

Cikin shashek'ar kuka tace "yanzu dai yunwa nake ji, kasa mamin abinci naci."

Cike da kunya ya d'an cije lips d'inshi yana satar kallonta, ace matarshi tana zama da yunwa saboda rashin abinci, duk da yana da dukiyar da zai iya ciyar da milyoyin mutane, murya qasa qasa yace "dama wai baki cin komai?"

Cikin muryar kuka tace "akwai cincin da mahaifiyata tasa aka kawo min shine nake ci, kuma ina ina da yan kud'i a jikina ina siyan wani abu, amma tun jiya komai nawa ya qare har yanzu banci komai ba."

Wani irin tausayinta ne ya sake ji, rumgumeta yayi sosai a jikinshi baisan lokacin da qwalla ta matso mishi ba a ido, sakinta yayi yana goge qwallan yana fad'in "bara na samo miki abinda zaki ci, kiyi hak'uri kinji Maryam d'ina."

B'angaren Hajia Luba ya nufa, cikin qanqanin lokaci sai gashi da kayan ciye ciye, nan ya zube mata gabanta ta fara ci, saida ta qoshi tayi hamdala kafin ta tashi ta d'auke kwanukan, duk lokacin idon Alhaji Naseer na kanta, a lokacin kuma yaji wata yana buk'atar matarshi a kusa dashi.

A wunin ranar dai tare sukayi shi yana riritata kamar qwai , gashi dama masu aiki basu zo ba kuma Hajia Luba ta tafi da yaran duka , sallah kawai ke fitar dashi kuma kuma da yayi zai dawo haka har isha'i ta samesu, koda yayi sallah isha'i da kanshi yaje ya siyo kaza guda biyu😋 da lemunmuka masu sanyi sannan ya dawo, saida sukayi sallah ya mata tambayoyi akan addininta ,duk da Maryam ta nuna tsoro da fargaba, amma cikin dubara da siyasa Alhaji Naseer ya mayar da ita babbar mace, wannan dare kuma ya shiga cikin tarihin rayuwarsu , dare ne da Alhaji Naseer ba zai tab'a mantawa dashi ba.

A kwana ukun da Hajia Luba tayi bata nan, sosai Alhaji ya gurji amarcinshi da Maryam, amma ranar da Hajia Luba ta diro daga ranar kuma komai ya lalace ya koma kamar farko, al'amura basu sake watsewa ba saida Maryam ta fara laulayi, Hajia Luba ta sani ne ta hanyar 'yar aikinta lokacin da taga Maryam nacin d'ata, saida ta mata kallon qwqwaf sannan taje ta fad'awa Luba, nanfa hankali ya tashi a take ta nufi wajen boka danya tabbatar mata, ya kuma tabbatar mata anan ta nemi a lalatashi, amma saiya fad'a mata tana cikin kariyar ubangiji ba zai iya musu komai ba, amma ya bata shawara ta jira harta haihu sai a kashe d'an, da wannan ne yasa ta kwantar da hankalinta harta haihu, a lokacin da Alhaji yaji tana da ciki yayi farin ciki, amma bai bari Hajia Luba taji ba, dan a tunaninshi bata sani ba kuma baya so ta sani, da taimakon mahaifiyarshi Maryam ta dinga rainon cikin Abdul Hakeem.

Lokacin mahaifiyar Hajia Luba ta dawo daga qasar waje wajen harkokinta, nanfa tace ai Luba tayi wasa sosai, data fad'a mata yanda boka yace sai tace sam bata yarda ba, nanta d'auketa suka je wanjen wani bokan, duk da basuyi nasarar fitar da cikin ba, amma sunyi nasarar saka Maryam shan wahala, har saida ta fita daga hayyacinta ta rasa gane wacece ita, kuma sunyi sihirin da har abada ba zata sake haihuwa ba, yan uwa da iyaye aka dage wajen addu'a har lokacin haihuwarta yayi, saida Maryam tayi kwana goma sha biyu tana nak'udar Abdul Hakeem, gashi dai haihuwa kusa kuma zata iya haihuwa da kanta, amma sam ta kasa haihuwar sai azaba da wahala da take sha, da qyar take samun baccin minti biyar zuwa goma, da qyar da taimakon Allah da taimakon addu'a aka samu ta haifi Abdul Hakeem, haihuwar d'a namiji shine silar faruwar lalacewar komai, Alhaji Naseer dai yayi farin ciki kamar zai kasheshi haka ma mahaifiyarshi, amma a b'angaren Hajia Luba da mahaifiyarta kamar bak'in ciki ne zai kashesu.


Anyi hidima, kuma irin hidimar da Alhaji yayi yasa Hajia Luba ta qara tunzura , mataki na qarshe suka d'auka akan wannan al'amarin, dan kuwa kafin Maryam tayi arba'in mahaifiyar Alhaji Naseer Allah ya mata rasuwa itama, Maryam tafi kowa jin mutuwar, domin kuwa itace ke taimaka mata akan komai, abubuwa sun qara had'e mata ta yanda ko abinda zata ci wani lokaci yakan bata wahala, dan saita d'auki wata d'aya ba taga Alhaji Naseer da idonta ba, musamman idan baya gari ma saita d'auki wata kusan biyu, ga tsangwamar yaran Luba da suka rainata kamar ba matar mahaifinsu ba.


Duk da baya kula Maryam amma baya hana ya aiko ya amsar mishi Abdul Hakeem, yana matuk'ar son yaran, da wannan kad'ai take jin dad'i saboda soyayyar da yakewa yaron, amma duk da haka ba'a barsu ba, bayan *shekara goma sha biyar*, abubuwa sun faru marasa dad'i kuma su sukafi yawa a b'angaren Maryam, yana daga cikin rashin kulawar da yake nuna ma Maryam rashin zuwanta qasa mai tsarki, hakan kuma ya tab'a qaninshi Ahmad sosai, ba tare da shawarar Alhaji Naseer ba yabiya mata kujerar makka, amma hakan baiwa Alhaji Naseer dad'i ba musamman da Hajia Luba ta qara zugashi, sosai sukayi fad'a da d'an uwanshi har yace ya fita harkar iyalinshi, duk da bai fita harkar iyalin nashi ba amma dai ya rage zuwa inda suke, saidai Maryam ta samu nasarar tafiya ɗakin Allah ta sauke farali, daga lokacin ta tashi daga Maryam zuwa Hajiya Maryam.


Abdul Hakeem an girma, kuma Allah ya bawa yaron qwaqwalwa sosai, yakan hardace komai cikin sauk'i, kuma a lokacin sai mahaifinshi ya fara janshi a jiki sosai wajen harkokinshi, daya taso daga school ko islamiyya Alhaji Naseer zaice ya sameshi office, harta kai ta kawo Alhaji Naseer idan zaiyi tafiya saiya tafi da Abdul Hakeem, hakan ba qaramin tab'a Luba yake ba, Abdul Hakeem yana kallon irin rashin adalcin da mahaifinshi ke nunawa tsakanin mahaifiyarshi da mahaifiyarsu Mimie, haka baya masa dad'i amma babu yanda ya iya, sai dai ya tsani Hajia Luba sosai, baya ko qaunar ganinta dan yana ji a jikinshi ba mutuniyar kirki bace, hakan yasa ko gaisheta zaiyi sai dai ya gaisheta kamar mai ciwon baki, kuma da abinda yake samu ne wajen mahaifinshi yake yiwa mahaifiarshi abubuwan buk'atar rayuwa, ranar da hajiya Luba ta kusa mutuwa saboda bak'in ciki itace ranar da Abdul Hakeem ya kawo result d'inshi kuma yayi kyau, a lokacin Alhaji Naseer ya fara mishi tanadin shiga jami'a tare da kyautar tartsetsen gida da kuma mota da zai fara tafiya da ita school, koda ta fad'awa mahaifiyarta nan suka shirya domin zuwa d'aukar mataki.

A wannan karon sunyi nasara sosai, anyi nasarar nakasa Abdul Hakeem ta yanda aka hanashi

Please Login or Register in order to submit comment