Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matsala gurin hajiya Luba, da idanunsa yabi Momyn nasa cike da tausayin rayuwarsu, haƙiƙa yana matuƙar tausayawa Momynsa saboda irin wahalar da take sha cikin gidan, wai kuma a hakan gidan mijinta ne, amma marabarta da ƴar aiki babu.



Kai tsaye katafaren kitchen ɗin hajiya Luba ta nufa domin ɗaura break fast, cikin sauri takeyi komai har ta kammala, kai tsaye dining table ta nufa ta fara jeresu, tana cikin jerawa su hakima hajiya Luba aka fito hannunta sarke cikin na Alhaji Naseer, cikin rawar jiki hajiya Maryam ta zube tana faɗin "barka da fitowa hajiya. "

Sai da ta zauna tukunna cikin ya tsina da wulaƙanci tace "me kika girka ne.?"

Cikin rawar baki tace "ruwan zafi ne, sai doya dana suya cikin kwai na haɗa da farfesun kan saniya. "

"Ok, kiyi saving namu"
Ta faɗi kamar ba taso, shiko alhaji Naseer ko kallo bata isheshi ba.



Hajiya maryam cikin sanyin jiki dajin ita ba komai bace a gidan sai ƙasƙantacciya ta fara saving nasu tana riƙe hawayen dake ƙoƙarin zubo mata, tana gamawa tabar gurin cikin sauri domin wani irin kuka ne ta tawo mata da ƙarfi.


Kitchen ta shige taci kukanta ta ƙoshi sannan ta ɗauki kular abincin nasu ta nufi ɓangaren Abdul-Hakeem, zuciyarya nayi mata ƙuna tare da raɗaɗi.


************


Raheenat kuwa kamar yanda ya zame mata jiki tana cire uniform ɗinta fitowa tayi ta fara ƙoƙarin ɗaura masu girkin rana tare da taimakok su Farida, sosai yau ta samu sausaucin aikin saboda tayen da ta samu gurinsu Farida, shi yasa take son ace Baba na gari kodan samun sauƙinta, domin kuwa duk wani hantara da tijara rageshi sukeyi.



Haka dai rayuwar ta ci gaba da tafiya ta ko wani ɓangare cike da ƙuncin rayuwa, ba ga Raheenat ɗin ba ba ga hajiya Maryam da ɗanta ba, suko iyayan gayyar babu abinda yayi musu zafi dangane da rayuwa, cikin karensu kawai sukeyi babu babbaka, Raheenat ta samu sauƙi sosai gurin Sadiq, domin tun daga ranar da Baba ya bigeshi be ƙara taranta da wata maganar banza ɓa, dan yana matuƙar tsoran Babansa.



Yau ta kama juma'a babu islamiyya, Inna ce take ƙwalawa Raheenat kira kamar zata tashi gidan, da sauri Raheenat ta fito daga ɗakin nasu tana faɗin "na'am Inna gani. ".

Wani mugun harara Inna ta jefa mata tace "in kinga dama ki ɗauki botikin nan kije gidan Alhaji Naseer buzu ki ɗebo min ruwa. "
Tayi maganar tana nuni da botikin gabanta.


Juyawa ɗaki Raheenat tayi ta ɗauko hijjabinta sannan ta fito ta ɗauki botikin ta nufi gidan Alhaji Naseer buzu cike da fata da burin ganin Abdul-Hakeem, abin mamaki malamin islamiyyarsu ne ta gaji a k'ofar gidan Alhaji Naseer tare dashi suna hira, cike da nutsuwa ta sunkuya tana dafe da bokitin ta gaishesu, amsawa sukayi cikin sakin fuska da yabawa da tarbiyar yarinyar, mik'ewa tayi ta shiga cikin gidan bayan sun gaisa da mai gadin, kalle kalle take tana so taga ta inda zata hango bawan Allah Abdul Hakeem amma shiru, dole ta d'ibi ruwan ta fito ba tare data gansa ba, saida ta sake cewa malaminsu "sai anjima malam." kafinta wuce.

Abinda bata sani Abdul Hakeem na hangenta ta madubin daya lullub'e qofar falonshi, yanda take kalle kalle shima kallonta yake kamar ya tashi ya mata magana, yana kallo harta fita daga gidan yana jin ba dad'i.....




*Muje zuwa tare da*



Meeraheenat😘
24/08/2019 à 11:51 - ~NANA KHADIJA~😍: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITTEN*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 65 to 70




Lumshe idonsa yayi yana jin wani irin ɗaci a zuciyarsa, fata yakeyi Allah ya bashi lafiya shima ya miƙe kamar kowa, wannan wani irin rayuwa ce, mutum ko yana son abu baya da bakin da zai faɗa, ko da yake ya ɗauki hakan a matsayin kaddararsa ce.



Alhaji Naseer ne ya dubi Malam Saminu da murmushi a fuskarshi yace "ɗalibarka ce itama kenan.?"

Murnushi Malam Saminu yayi yace "eh, Raheenat ba, yarinyar akwai nutsuwa ga tarbiya data samu daga gida. "


Ɗan ɓata fuska Alhaji Naseer yayi yace "ai kwanakin baya naso nemawa ɗana Abdul aurenta saboda yabawa da tarbiyar nata da nayi, amma saidai babu nasara. "

Kallonsa Malam Saminu yayi sosai yace "wai kana nufin Abdul-Hakeem. ?"

Ɗaga kansa Alhaji Naseer yayi yace "banda abinka Malam ina da wani ɗanne bayan shi. "

"To amma me ya hana abin yiwuwa.?" cewar Malam Saminu.

Ɗan shiru Alhaji Naseer yayi kafin ya gyara zama yace "ka gane ne Malam, wato dai kwanakin baya ne na fito.....nan ya bawa Malam Saminu labarin duk abinda ya faruwa tun daga lokacin da Raheenat ta bawa Abdul ruwa zuwa maganarsu da Malam Habu, da shi abinda Malam Habun yazo ya sanar dashi na rashin amincewar mahaifiyar yarinyar, kafin ya ɗaura da cewa "sam abin beyi min daɗi ba da Mamanta taƙi amincewa, nasan dai tabbas akwai cutarwa ga yarinyar amma taimaka min zasuyi, dan ina saka ran Abdul zai tashi nan bada daɗewa ba, amma babu yanda na iya na haƙura. "


Nisawa Malam Saminu yayi yace "gaskiya ne Alhaji ba ko wacce uwa ce zata so ganin ƴarta cikin wahala ba, shi aure ana yinsa ne domin bautar Allah da kuma jin daɗi, amma a yanzu duk wacce zata auri Abdul to tabbas sai ta wahalta masa, to kaga ko ba ko wacce uwa ce zata yarda da hakan ba, saidai karka damu, zan tayaka da addu'a, insha Allahu in akwai aure tsakanin Raheenat da Abdul komai zai zamo mana cikin sauƙi. "

Cike da jin daɗi Alhaji Naseer ya dinga zubawa malam Saminu godiya, nan sukayi sallama malam Saminu ya tafi shi kuma ya shige gida.


Alhaji Naseer sun haɗu ne da Malam Saminu ta hanyar wani abokinsa da yayi masa hanya akan shi Malam Saminun zai taimaka masa akan ciwon Abdul ɗin, dududu ba afi sati biyu ba da haɗuwar nasu, yanzun ma yazo ganin Abdul ɗin ne, saboda be taɓa ganinsa ba sai labarin ciwon nasa da Alhaji Naseer yake bashi, duk da ya fara bada wani taimako a ringa bawa Abdul hakan be samu ba saboda hajiya Luba ta hana, da yake komai sai Alhaji Naseer ya faɗa mata, to yana faɗa mata ta rinƙa faɗa tace sam ba malamin gaskiya bane kar ya yarda ya bawa ɗansa duk wani magani da zai bashi, to hakanne ta kasance ba abawa Abdul magani ko ɗaya ba cikin wanda Malam Saminu ya bayar, sai dai shi Alhaji Naseer har cikin ransa ya gamsu da Malam Saminu, shi yasa ma ya kasa rabuwa dashi, kallo ɗaya Malam Saminu yayiwa Abdul ya gane akwai sihiri a jikinsa, yanzu ma tsayuwar da Raheenat ta gansu sunayi akan lallurar tashi suke tattaunawa.



_Wannan kenan_




*********


*Bayan kwana biyu*




Malam Saminu ne yayi kiran Raheenat office ɗinsa bayan tashi daga makaranta, da sallama ta shiga office ɗin kanta a ƙasa, nuna mata kujera Malam yayi yace ta zauna, zama tayi kamar yanda ya umurceta gabanta na faɗuwa dan zatonta wani laifi tayi.


Gyaran murya Malam Saminu yayi yace "Raheenat dama kina shiga gidan Alhaji Naseer ne.?"

Ɗagowa tayi ta kalleshi tace "eh malam ina shiga, amma ruwa ne kawai nake zuwa ɗibowa, shima ba ko yaushe bane. "

Cikin gamsuwa da bayaninta yace "kinsan Abdul-Hakeem ne.?"

Girgiza kanta tayi tace "eh, amma so ɗaya na taɓa ganinshi. "

Ɗan murnushi yayi yace "kenan baki san taimakon da mahaifinsa ya nema a gurinki ba.?"


Cike da mamaki Raheenat ta kalli Malam tace "taimako! A gurina kuma, wani irin taimako ne ni kuma Alhaji Naseer zai nima a gurina ? Ni bansan komai ba wallahi malam. "

Gyara zamanshi Malam yayi yace "kenan mahaifiyarki bata faɗa miki komai ba. "

"Ni bata faɗa min komai ba Malam "
Raheenat ta faɗi hankalinta a ɗan tashe.

"Kwantar da hankalinki Raheenat ba wani abu bane, dama aurenki ya nema a bawa ɗansa Abdul. "

Waro ido tayi tare da dafe ƙirji tace "aurena kuma, ni Raheenat akeso na auri Abdul-Hakeem, kuma malam kace mahaifiyyata ta sani.?"

Ɗaga mata kai yayi yace "ta sani. "

"Kuma ta yarda.?"


Murmushi Malam Saminu yayi ya fara mata bayanin duk yanda sukayi da Alhaji Naseer har abinda mahaifiyarta tace kafin ya ɗaura da cewa "Raheenat ni a ganina taimako zakiyi tare da *Jihadi*, saboda na gano lallurar yaron akwai sihiri cikinsa, kuma ina ji ajikina aurenki dashi Alkhairi ne, Raheenat nasan ke malama ce, zaki bada gudunmuwarki sosai gurin samun lafiyarshi, na fahimci wani abu da yake faruwa a cikin gidan Alhaji Naseer tun lokacin da yazo gurina neman taimako, kuma wannan abin da yardan Allah zai zo ƙarshe sanadin shigarki gidan, saidai bansan ta yaya al'amuran zasu kasance ba, Raheeenat ina so ki bani nan da kwanaki uku zan ƙarayi miki istihara akan al'amarin, abinda na gani zan sanar dake, kema kuma ya kamata kiyi istiharar nan da kwanakin sai ki faɗa min me kika gani. "

Jiki a matuƙar sanyaye Raheenat tace "to malam, insha Allahu zanyi yanda akace, Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi. "

"Ameen ameen" cewar Malam Saminu, kafin ya ƙara da cewa "zaki iya tafiya, amma karki saka wani damuwa a ranki fa. "

Murmushi tayi tace "kar ka damu Malam babu komai wallahi. "

Shima murmushin yayi mata yace "kina da zuciya me kyau Raheenat, nasan Allah ba zai taɓa bari ki wulaƙanta ba. "

Raheenat cike da jin daɗi tace "nagode Malam. "

Nan tayi masa sallama ta fito daga office ɗin, bakin office ɗin ta iske Sameera na jiranta, murmushi suka sakarwa juna sannan Sameera tace "my heenat ina fatan ba wani laifi kikayi ba. "

Tafiya Raheenat tayi tace "karki damu my Meera tamabayata kawai yayi, kisan rannan nace miki na haɗu dashi a gidan Alhaji Naseer ai. "

Bayanta Sameera ta biyo suna tafiya tace "ok har naji sanyi, kinsan ko kaɗan bana son naji ance kinyi wani abu barar daɗi. "

Murmushi Raheenat tayi ta kamo hannu Sameera ta riƙe tace "na yarda Allah ne me haɗa bayinsa my Meera, kina nuna min soyayya wacce ko ƴan uwa jini ɗaya muke sai haka, nagode da soyayyarki Allah ya barmu tare har mutuwa, ya kau da idon maƙiya a kanmu. "

"Ameen ameen my Heenat. "
Cewar Sameera tana murmushi.


Haka suka ci gaba da tafiya suna hirarsu har suka zo inda zasu rabu Sameera ta nufi gidansu ita kuma ta shige nasu.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment