Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```

_Bismillahir- rahamanir-rahim_


Page _10 to 15_


Daga k'ofar d'akin tayi sallama kamar yanda aka gindaya mata tsayawa nan, Inna ce ta fito cikin jin haushi tana zuwa ta tsaya ta qare hararanta tas kafin tace "jaraba, to ina wajen da zan zuba miki? ko kuma zanina kike so na zuba miki a ciki?"

"A'a Inna." ta fad'a tare da juyawa ta nufi d'akinsu, wata qaramar mod'a ta dauka wacce ta zama ta zuba musu kokon sannan ta fito duk Mama na kallonta, tana zuwa ta aje mod'ar Inna kuma ta d'auki babban ludayin ta zuba mata biyu dashi.

_Ikon Allah, duk da qarantar modar amma ba za'a cikata ba._

Tana zuba mata ta d'auki bokiyin tayi d'akinta dashi ita kuma ta d'auka tayi nasu d'akin, tun kafin ta shiga d'akin wata dubara ta fad'o mata a rai, dan haka ta canza yanayinta kamar mai gaggawa ta shiga d'akin, da sauri ta qarasa gurin Mama ta aje modar tana fad'in "Mama ga kokonki kisha, ni zan wuce islamiyya."

Bata jira me za tace ba ta nufi wajen tsohon uniform d'inta ta fara sakawa, harta gama bata kalli Mama ba sai dai Mama ita take kallo, "Raheenat kizo kisha kokan mana karya huce." cewar Mama.

"Mama kisha, Sameera na jirana a waje zamu wuce, idan naje zan samu wani abu naci." duk tayi maganar ne tana saka hijab d'inta da d'aukar jakarta.

Kafin Mama tayi wata magana kuma ta durk'usa gabanta ta sunkuyar da kanta tace "Mama sa albarkarki."

Cikin murmushi Mama ta dafa kanta tace "albarkata na tare dake 'yar albarka, kina cikin kariyar ubangiji har kije ki dawo."

Yatsu biyu ta saka taja kumatun mahaifiyarta ta tana dariya tace "uwa mai dad'in zama uwa abar alfahari, na gode Allah daya bani ke, nafi kowa sa'a."

"Nima ina alfahari da samunki yarinyar kirki."

Tashi tayi a sukwane tare da sumbatar kumatun mamanta tace "ina sonki Mamana."

"Ina sonki, Allah ya tsare saikin dawo." Mama ta fad'a saboda harta kusan fita daga d'akin.

Girgiza kai Mama tayi tare da share wasu wahalallin qwalla, tasan babu abinda zata samu taci, hakan yasa ta d'auki modar ta samu wani d'an murfi ta rufe da tunanin aje mata harta dawo, tashi tayi ta fito daga d'akin dan ganin meke wakana a wajen, dan tasan Raheenat bata so saboda rashin mutuncin Inna, haka yasa tace ta dinga zamanta a d'aki.

Ai kuwa Inna ce ta fito daga d'aki bayan su Farida sun tafi school, ganinta yasa tayi saurin juyawa zata koma d'aki amma sai Inna tace "dakata mana, ai saiki fito kisha iska, wato munafirci da kinibibi baya tashi sai mai gidan na nan, idan kuma baya nan saiki wuni baki lek'o tsakar gida ba."

Shiru dai tayi ita kuma ta qara da "an daiji haushi, kilaki kawai, waiku kun b'ige da neman taimako, ba gaira ba dalili kin d'orawa mijina nauyin daba nashi ba, a banza sai ciyar daku yake ba lada ba zunubi."

"Allah ya baki hak'uri, muma rayuwa ce tasa har muka zauna tare daku."

"Uhum, da anyi magana sai kice rayuwa rayuwa, kamar ku kad'ai ne a cikin *K'angin rayuwa*, bayan akwai wanda suka fiku shiga wani hali a cikin rayuwar."

"Humm, ai kuwa duk wanda ya fimu matsi da k'uncin rayuwa, to ki sani baya numfashi, yana cikin k'abarinsa da munanan ayyukansa."

Juyawa tayi zata koma ciki tace "aikin banza aikin wofi, in har gaske ne me zai hana ki sada yarinyar nan da dangin ubantan in har ya mutu da gaske, ai da gani ba sai kin fad'a ba cewar a yawon ta zubar kika samu wannan 'yar, hakan yasa ma kowa ya gujeku, kuma kamar yanda kika sameta ta hanyar da bata dace ba, to ki shirya itama saita samo miki d'an dakan kuka, wallahi saikin goyi d'an shege a bayanki."

Zafin da kalaman suka mata yasa ta qarasa shiga da gudu d'akin tana zubar da hawaye, in banda sauyin rayuwa har ace ana sheganta mata 'yar data haifa ta hanyar sunna, lallai yau za taji maganar Raheenat ba zata sake fita ba in dai bada wani dalili ba, dan zuciyarta ba zata iya d'aukar bak'ak'en maganganu akan 'yarta ba.



***************



Hajiya Maryam ce take gunguro ɗanta Abdul-Heema saman kekensa zuwa farfajiyar gidan domin yasha iska, daidai gurin wani ɗan madaidaicin gurin hutawa da aka ƙawata shi da fararen kujeru kusa da gurin adana motocin gidan ta ajiyesa, kallonsa tayi da murmushi a fuskarta tace "to Abdul ni zan koma ciki na ƙarasa aiyuka. "

Da ido ya bi mahaifiyar nasa kawai, tasan ba zai iya magana ba amma tana da tabbacin yaji abinda ta faɗa, juya kawai tayi ta koma ciki ta barsa a gurin yana shan iskar da take kaɗawa me daɗi.


Lumshe ido yayi wanda su kaɗai ne suke motsawa a jikinsa ya buɗesu fes a akan wasu tsintsaye da suke saman bishiyoyin fulawar da aka ƙawata gidan nasu dashi, da ganin yanda yake kallonsu zaka fahimci yana cikin nishad'i.

Shekarunsa ba zasu gaza ashirin da hud'u ba zuwa da biyar, kana ganinshi zaka fahimci hutu ya ratsashi sosai saboda tattausa kuma lallausar fatar jikinshi wacce ke shek'i da kyali , sumar kanshi dake bak'a sid'ik ta qara fito da farin fatarshi, ga kuma sajen daya sake k'awata fuskarshi, tako ina dai Abdul-Hakeem ya had'u, nak'asunshi d'aya tak shine, *ido ne kad'ai ke motsi a jikinshi*.

Wata rantsetsiyar matace ta fito daga wani katafaran b'angaren da duk gidan ba b'angare mai kyau kamarshi, suturarta da sauran kayan adon dake jikinta zasu fahimtar da kai tana fad'a aji a gidan kuma dukiya ta kwanta mata sosai, wani b'angaren ta tunkara amma ganin Abdul zaune yasa ta tunkari wajenshi, da takon k'asaita ta isa ta tsaya gabanshi tana murmushi, giftawar wata ma'aikaciyar gidan yasa ta dafa kanshi tare da d'an rank'wafawa tana murmushi tace,

"Yadai musaki, an fito shan iska ne? To yayi kyau, aci gaba da zama a haka har lokacin da zaka qarasa inda ya dace."

Har zata wuce kuma tace "ehem, nasan kana jin haushina, amma hak'uri ya zama dole, nima hak'uri nake da nake iya jurar kallonka kai da tsinanniyar mahaifiyarka a gidan nan, amma komai ya kusan zuwa qarshe kamar yanda boka ya fad'a min."

Kumatunshi ta shafa ta sake sakin wani murmushin tace "see you my son."

Tana wucewa ya lumshe idonshi da sukayi jawur yana so ya zubar da hawaye amma ya kasa, hakika matar na bala'in kasheshi da bak'in ciki, amma ba yanda ya iya, ko alama ba zai iya yima wani ba bare kuma a fahimceshi, yasan abubuwa da dama a tare da ita saboda tana wayan sakin baki a gabanshi saboda tunaninta dashi da gawa duk d'aya, sai dai komai na cikin kanshi kuma yana mayar mata da martani a zuciyarshi, lafiya kawai yake fatan samu ya rabata da mahaifinshi.


*****************


Da qyar Raheenat ta kai kanta islamiyya saboda azababbiyar yunwa, amma fa babu abinda ta fahimta a game da karatun da aka musu, suna tashi suka d'auko hanya ita da Sameera, fahimtar halin da take ciki da tayi yasa Sameera cewa "my Heenat, kizo muje gida idan muka ci abinci saiki wuce gida."

Tana girgiza kai cikin tsananin yunwa tace "a'a my Meera, ki barshi kawai zanje gida, aiki na jira a gida idan na makara zansha masifar Inna ne kawai."

"A hakan za kiyi wani aiki? To ai bana ganin zaki iya moruwa a haka, kinga kizo muje dan Allah, idan masifarta kike gudu ni zanje mu tafi tare gidan."

"Wato ke uwar masifa ko?" cewar Raheenat.

"Ba haka bane, kawai zan kama miki aikin ne."

Qarasawa da sukayi inda zasu rabu yasa suka tsaya, kafadarta Raheenat ta dafa tace "karki damu my Meera, idan naje nasan ba zan rasa abinda zanci ba."

Cikin jin haushi Sameera tace "me zaki samu kici, a ina ne zaki samu abinda zaki ci d'in, wanda ko abincin da ake baku ba isarku yake ba, taya kike tunanin samun wanda zaki ci yanzu?"

Dafe cikinta tayi tace "my Meera, idan har baki so na shiga matsala, to dan Allah kiyi hak'uri ki barni, na fad'a miki zan samu abinda zanci."

Tsaki Sameera tayi ta nufi hanyar nasu gidan dake kallon nasu Raheenat d'in zuciyarta na k'una , itama hanyar gidan ta nufa tana murmushi dan tafi kowa sanin halin aminiyarta ta, hakan yasa bata cika son tana zuwa gidan ba, in har taje sai an samu matsala ko dai tsakaninta da Inna kosu Farida.

"Sallamu alai..." bata qarasa ba taji an jefo mata bokiti a qirji ana fad'in "saiki d'ebo mana ruwa tunda kin dawo daga gantalin."

Sai lokacin ta kalli Farida ce ke maganar, za tayi magana kuma saita dafe cikinta saboda kukan da yake, Inna ce ta fito daga d'akin tana fad'in "wai har yanzu bata dawo ba?"

Jin haka yasa tayi saurin cire jakarta ta aje a qasa gefen tabarmar dasu Faiza dake latsar waya, d'aukar bokitin tayi zata fita Inna tace "kuma kiyi sauri ki dawo kizo ki d'ora mana abinci."

Juyawa tayi ko ganin gabanta ba tayi da kyau sai sharar qwalla take, duk da rijiyar dake akwai a cikin gidan, amma idan suka niyyar muzguna mata sai suce saita d'ebo ruwa a panpo a gidan *Alhaji Naseer Buzu*.

Tana zuwa mai gadin ya bud'e mata gate d'in yana fad'in "Raheenat d'iban ruwa aka zo?"

"Eh Baba, ina kwana?"

"Lafiya lau, halan tasowarki kenan daga islamiyya na ganki da uniform?"

"Eh Baba." ta fad'a tana wucewa cikin gidan.

Aje bokitin tayi a bakin panpon dake kusa da wajen ajiyar motoci, kan panpon ta rik'e hannu d'aya kuma ta dafe 'kugu saboda bala'in yunwa dake cinta.

D'an kalle kalle ta shiga yi har idonta suka sauka akan idon Abdul daya kafe ruwan dake zuba da ido....


_Meeraheenat_😍
28/07/2019 à 14:18 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




_GAISUWA GAREKU MASOYA, HAƘIƘA MUNA JIN DAƊIN COMMENT ƊINKU AKAN WANNAN NOVEL ƊIN, KU SANI MEERAHEENAT SUNA YINKU IRIN SOSAI SOSAI ƊINNAN FA😉💘_



DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



*Bismillahir-rahamanir-rahim*



Page 15 to 20






Yana ji a ransa ina ma lafiyarsa ƙalau da ya tafi a sukwane yasha ruwan nan sha ba na wasa ba, saboda irin matsanancin ƙishir ruwan da yake ji, saidai kash ba zai iya ko motsa ƙafarsa ba balle ya miƙe, kallonsa Raheenat takeyi sosai a ranta tana yabawa da kyaunsa, duk shigowarta da takeyi gidan ɗiban ruwa bata taɓa ganinsa ba, amma tasan babu shakka wannan kyakkyawar matashin saurayin shine Abdul-Hakeem ɗa ɗaya tilo ga Alhaji Naseer buzu wanda take jin labarin rashin lafiyarsa a cikin unguwa, wani lokacin kuma a bakin su Farida in suna hira labarinsa, ganin da tayi shi Abdul-Hakeem sam ba ita yake kallo ba ruwan da yake zuba a panpon ya tsurawa ido yasa tayi tunanin ko ruwan yake son sha ne, kau da idanta daga kallonsa tayi ta fara neman abinda zata ɗiba ruwan ta bashi yasha, ganin babu wani mazubi a kusa yasa ta nufi bakin get gurin Baba megadi da sauri dan samun kofi.

Baba na zaune kan bencinsa da ƴar redionsa a hannu ya yana saurara yaga Raheenat ta nufo inda yake, murmushi yayi yace "ƴata Raheenat ya akayi ne banga kin ɗebo ruwan ba.?"

Murmushi Raheenat tayi tace "Baba kofi nake son ka taimaka min dashi na tara ruwa nasha. "

Miƙewa Baba yayi ya shiga ɗakinsa ya ɗauko mata kofi yana faɗin "ayya kice ƙishi kika ji. "

Raheenat dai bata tsaya bashi amsa ba ta koma gurin ponpon da sauri tara ruwan a kofin sannan ta nufi gurin Abdul-Hakeem, da zuwanta ta kafa masa ruwan a baki tana faɗin "nasan duk yanda akayi kishi kake ji tunda naga kana kallon ruwan. "


Nan Abdul-Hakeem ya kama shan ruwan babu ƙaƙƙautawa, domin kishin yake ji sosai.



Hajiya Luba ce wacce dama ɓangaren mahaifin Abdul-Hakeem ta shiga sai gashi sun fito tare dashi suna hira cikin nishaɗi, karaf idanunsu ya sauka kan Raheenat wacce ke bawa Abdul-Hakeem ruwa, nan take annurin fuskar hajiya Luba ya ɗauke haushin Raheenat da tsanarta taji nan take, shiko Alhaji Naseer abin birgesa yayi yaji yarinyar ta shiga ransa, hajiya Luba kuwa a ranta take faɗin "akan me wannan yarinyar zata shiga hurumin da ba nata ba, akan me zata taimaka masa, me yasa ba ta bari ƙishir ruwan ya galabaitashi koma ya kasheshi kafin waccen shashashar uwar tashi ta zo ta bashi ruwan ba, lallai wannan yarinyar ta shiga al'amarinna, ya kuma zama ɗole ta ɗauki matakin da ya dace a kanta, dole ne ma na hukuntata. "

Muryar Alhaji Naseer ne ya katse mata tunaninta taji yana cewa "hajiya kinga wani abin burgewa, gaskiya yarinyar ta samu nagartacciyar tarbiya, wallahi naji ta birgeni sosai, yanzu daga shigowarta har ta fahimci Abdul na son shan ruwa. "

Saurin wayancewa tayi ta saki murmushin da bai kai zuci ba tace "Raheenat kenan ai tafi da haka, gaskiya nima ta burgeni matuƙa, gaskiya kam ta samu tarbiyya sosai wajen mahaifiyarta" cikin suɓutar baki tare da nuna ita ɗin tana tausayinsa, ta ɗaura da cewa "ni har nayi wa ɗana sha'awarta, ina ma ace zaka nemawa Abdul-Hakeem aurenta, kaga ko ba komai mahaifiyarsa zata samu sausacin wasu abubuwa, dan gaskiya akwai abinda ya kamata yanzu ace matarsa ce zatayi masa, kamar wanka, wankin ba hayanshi da fitsari dan akwai nauyi matuƙa mahaifiyarka nayi maka irin waɗannan abubabuwa, matarshi ce kawai zatayi masa ba tare da jin nauyi ba. "

"Kin santa dama?" ya tambayeta.

A kakkauce tace masa "eh , ai yar gidan malam Habu ce wacce suke zaune a gidanshi."

Wani basaraken murmushi Alhaji Naseer yayi ya ƙara kai kallonsa ga Raheenat wacce ta gama bawa Abdul ruwan, kuma tas ya shanye sai kofin, har ranshi yaji daɗin maganar Hajiya Luba tare da ƙudurawa a ranshi zai nemi iyayan yarinyar ya nemawa Abdul auren Raheenat domin yanayin yarinyar kaɗai da ya gani yasan zatayi hankali sannan zata kula da ɗansa sosai, sai dai ko da wasa be nunawa Hajiya Luba ya ɗauki shawararta ba, dan haka kawai yaji baya son sanar da ita amincewarshi akan batun.


Ita kuwa Hajiya Luba dariyar mugunta tayi ganin Alhaji Naseer bece komai ba, a ranta tace "aikin banza, wacce macen ce zata yarda ta auri masaki ta zo tayi zaman bauta, to koni naji wacce ta yarda wallahi sai nayi yanda zanyi na hana abin faruwa, domin ba zan yarda Abdul-Hakeem ya samu kulawa ba, nafi son naga yana wahala kafin ranar da zai margaya. "



Shiko Abdul-Hakeem da ido yakeyiwa Raheenat alamu da ya gode ta hanyar lumshesu, murmushi kawai ta sakar masa taje ta ɗauki ruwanta ta ɗaura akai ta nufi get, da kallo Abdul ya bita har ta ɓacewa ganinsa, sai da ta bawa Baba kofinsa sannan ta fice daga gidan zuciyarta cike da tausayin Abdul-Hakeem, tana tafe tana cewa a ranta "ikon Allah kenan, mutum da ransa amma marabarsa da matatce kawai numfashi, ko wannan ya isa ya ƙara mana imani, mutum ba a bakin komai yake ba, lokaci ƙanƙani Allah zai iya sauya maka halitta ka zama wani abu daban, wannan ba komai bane a gurinsa, gashi dai ina ganin babu wanda ya kaimu shiga k'unci da *K'angin rayuwa*, amma da gani wannan ya fimu, dan babbar kyautar da ubangiji zaima bawansa bayan ya bashi addinin musulunci shine ya bashi lafiyar da zai bauta masa da ita."


*************


Tana shiga gidan ta ajiye ruwan, ko sauraren masifar da Fa'iza takeyi mata na ta daɗe ba tayi ba ta shigewarta ɗakinsu da sauri domin cire uniform ɗinta tazo ta ɗaura girkin rana.


Zaune ta iske Mama akan sallaya da alama kiran sallah azahar take jira, "sannu Mama." ta fad'a cikin hanzari tana cire kayan jikinta.

"Sannu Raheenat, har kin d'ebo ruwan ne?" cewar Mama.

Doguwar rigar jiya ce ta zura a jikinta tana fad'in "eh Mama na d'ebo, zanje ne na d'ora girki rana nayi."

Tana fad'a ta fita daga d'akin tana d'aura d'an kwalinta, tana fita ta fara zura itace a murhu ta k'yasta ashana, kafin wutar ta kama Inna dake fitowa daga d'aki tazo ta aje mata shinkafa da kayan miyan da za tayi aiki dasu tana fad'in "gashi nan saura ki munafurceni kamar yanda kika saba."

Kallonta kawai tayi ba tayi magana ba har Inna ta d'auki gyalenta a rataye ta aza a kafad'a ta kalli Raheenat tace "na gaji da wannan ranar tuwon, wallahi daga gobe idan baki shigo gidan nan qarfe sha biyu ba kuma kika d'ora min abinci, to ki sani ba zaki sake zuwa makarantar ba tunda ai dama ba ubanki bane ya biya miki kud'in ba."

Cikin raunin murya Raheenat tace "dan Allah Inna kiyi hak'uri karki hanani, wallahi na miki alk'awarin zan dinga dawowa da wuri, zan nemi izini a gurin malam."

"Aikin banza, shi kuma malam d'in saiya barki kiyi yanda kike so? saboda kece shafaffiya da mai." cewar Farida daga zaune.

Fa'iza ce ta tare da cewar "to kinsan meke tsakaninsu da malam d'in ne, watak'ila akwai karatun da suke na musamman a bayan aji."

A hankali Raheenat ta kalleta tace "Faiza, ka fad'i alkairi ko kayi shiru, hakan bai dace ba ki zargemu a bisa abinda baki gani ba da idonki."

"To waliyiya ustaziya, wato ma zarginku ne ake? to ai kura ba tayi gudu ba d'anta yayi rarrafe." cewar Inna.

Kafin wani yayi magana Inna ta kalli su Farida tace "ni zan shiga wajen Hajia tun jiya rabona da ita."

Cike da izgilanci Fa'iza tace "Inna ki gaida musaki."

Dakk'uwa Inna ta mata tace "shegiya, idan da lafiyarshi k'alau ke kina ganin ba sai nabi duk hanyar da zan biba danna had'aki dashi aure ba."

Farida ce tace "lallai ma Inna, wato ni ko oho ko? ni dake nan kullum ina masa fatan samun sauk'i kodan ya aureni, amma ke kuma kina so ki had'ashi da wacce take masa iskanci."

"Kul!" Inna ta fad'a cikin daka tsawa.

Dorawa tayi da "wallahi karki yarda koda wasa Hajia Luba taji kinawa Abdul fatan samun lafiya, idan ba haka ba kema zaki zama kamarshi, ko kuma ma ya fiki kyan ganuwa."

Tana fad'a ta juya ta bar gidan, duk maganar nan da suke akan kunnuwan Raheenat, tana aikinta tana sake mamakin wannan Hajia Luba to miye matsalarta da samun lafiyar Abdul, watak'ila tana da hannu a rashin lafiyar tasa, wata zuciyar ce ta gargad'eta ta daina zargin haka dan babu kyau tunda bata tabbatar ba.

Tana cikin aikin Sameera ta shigo gidan d'auke da kwanon abinci, ko kallon banza su Farida basu isheta ba, kai tsaye wajen Raheenat ta nufa ta dafa kafad'arta, juyowa tayi cikin dauriyar matsanciyar yunwar da take ji ta kalli Sameera d'in, "my Meera, kece?"

Fuska ba annuri tace mata " karb'i wannan ki tashi kije d'aki ke da Inna kuci , ni zan qarasa miki aikin."

Murmushi kawai Raheenat tayi dan tasan zaiyi wuya ta fita daga gidan nan haka kawai, hannunta ta rik'e tace "Meera, kije ki kaiwa Inna, nima na kusa qarasawa, shinkafa kawai zan zuba."

Cikin d'aga murya Sameera tace "dallah miye haka? kasheki zasuyi ne idan kin tashi daga nan? yunwa fa kike ji."

Farida ce tayi tsal tace "to yunwar ta kasheta mata, ke yarinyar nan fa na lura in dai kika shigo gidan nan saikin nemi tashin hankali, to bari kiji wallahi kin kusa daina shigowa cikin gidan nan."

Sunkuyawa Sameera tayi ta aje kwanon hannunta ta dago, Raheenat da tasan meye zai faru tayi saurin tashi daga kujerarta ta rik'e Sameera sosai tana magana qasa qasa tace "pls my Meera, kar kiyi dan Allah rabu dasu, ki shiga ciki ki bawa Inna abinci, ni idan na gama zanci."

Cikin tsawa da masifa Sameera tace "dallah ki sake my Heenat, ki bari na nuna musu da banbanci tsakanin Meera da Heenat, 'yan iska kawai da kuka raina mutane."

"A'a Meera na rok'eki dan Allah, in dai har zan iya fad'a miki kiji to kiyi abinda nace, in kuma ban isa ba to ki nuna min yanzun nan." cewar Raheenat cikin rarrashi.

Fincike kanta tayi daga rik'on data mata ta sunkuya ta d'auki kwanon rai bace ta d'ago ta kalli Farida tace "wallahi kinci albarkacin masu albarkaci, badan haka ba, da kin gane shayi zalla ruwa ne."

A hassale ta shiga d'akin nasu ta samu Mama a tsaye kuma da alama taji me yake faruwa, kawai dai bata fita bane dan tana zuwa za ace ta shigar musu,


*muje zuwa tare da*

_Meeraheenat_😍
29/07/2019 à 13:11 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


_Bismmilahir-rahman-rahim_


3⃣2⃣


Wanka ya shiga ba tare da sun kula juna ba, saida ya shiga sannan ta tuna da tsarinta, tashi tayi yanzu ma ta fito mashi da wata watsetsiyar shadda fara qal da alama bai tab'a sakata ba, takalma agogo ta fito dasu tare da hula bak'ak'e, tana gamawa ya shigo yana tsane ruwan jikinshi, karb'ar towel d'in tayi ta fara goge masa shi kuma yana kallonta yana tunanin kodai tana da aljanu, a haka ta gama shiryashi tsaf dashi yau ma ta d'aukesu selfie sannan ya fita zuwa masallaci, harya fita ya kuma dawowa yace "wannan shirin fa na miye?"

"Ba amaryarka zata zo ba anjima." ta fad'a tana kunburo baki.

Murmushi kawai yayi ya fita zuciyarshi na qara kamuwa da qaunarta, ana kiran sallah itama tayi sallah sannan ta shiga wanka ta shirya cikin riga da siket masu shegen kyau na kantie sun fito mata da komai a fili, kwalliya tayi sosai tana gamawa kuma ta mayar da sallah isha'i da ake kiran, harta gama ta zauna akan kujera amma bai dawo ba, ranta na tafarfasa haushi ya gama isarta tunaninta ko yana can da motarta ma ya tafi d'aukar figaggiyar amaryarshi.


***************

Tanti Ma'u ce ta tisa Zuby gaba ta bata wani kullin magani tace "wannan wanka za kiyi dashi na tsawon kwana uku, wannan kuma kisan hanyar da za kibi Umar Faruk yaci a abinci, wannan kuma na tsinnaniyar matarshi ce, a abinsha zaki zuba matashi."

"Amma Mama duk na miye wannan? nifa tsoro nake ji."

"Ke can dallah, wannan da kinyi aiki dashi, to ke zai dinga gani da daraja , ita kuma ta fita a ranshi, wannan kuma idan yaci a abinci, to zaki malleshi ne sai yanda ki kayi dashi, wannan kuma da tasha ita kuma, to ba haihuwa a gidan Umar Faruk har saita mutu."

"Yawwa Mama na gode sosai, zanyi maganin shegiyar."

***************


Umar Faruk kuma yana can ya tura abokananshi d'aukar Zuby amma yana k'ofar gida tare da Ishaq, ana cikin haka an kawo amarya suka hallaro, nanfa aka fara hayaniya aka shiga da amarya aka bud'e d'akinta aka zurata ciki, saida aka gama bidi'o'i da kwanjil kwanjil sannan mutane aka fara watsewa, anan yan uwan Zuby suka sake bata wasu sinadaran na yak'ar Khairat danta cinye gida, yayin da Zabba'u take addu'ar Allah ya had'ata da Khairat a tsakar gida ta rama marinta.

Ganin har zasu tafi bata fito ba yasa suka dinga d'ura mata ashar suna habaici iri iri had'e da kiranta karuwa, to nidai lek'awa nayi d'akin Khairat d'in naga tana jinsu kuma tayi shiru.

😂 _Kun sanfa mutuniyar akwai son casu, can na hangota kwance akan kujera ta danne kunnuwa da

Please Login or Register in order to submit comment