Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itace yarinyar data fad'o masa a rai a daidai wannan lokacin da yake kallon Abdul shima kuma shi yake kallo, yana tausayawa mahaifinshi rayuwar da yake ciki, yasan abubuwa da dama dangane da rayuwar gidansu, yasan Hajia Luba itace mai alhakin tarwatsa zaman lafiya da farin cikin gidansu, domin kuwa tana fad'a masa haka sai dai ba damar da zai iya koda nunawa, kuma sanin hakane yasa itama take sakin jiki tana fad'a masa duk abinda yazo bakinta ba tare da shakku ba.

***************

Ruwa Inna ta d'auka ta shiga d'akin dashi, durk'usawa tayi zata aje masa yace " ashe Ramatou dama amanata kike ci idan bana gidan nan? akan me zaki min haka Ramatou? wallahi ko kad'an banyi tsammanin haka daga gareki ba"

Cikin sigar makirci tace "dan Allah malam kayi hak'uri, tabbas nayi kuskure amma ba zan sake maimaita kamarsa ba insha Allah."

Shiru yayi ganin haka yasa ta zuba ruwan ta bashi tare da fad'in "fatana dai Allah ya huci zuciyarka, dan kafi kowa sanin ba son ganin b'acin ranka ba nake."

Bashi ruwan tayi ya karb'a yasha sosai kafin yace "ki zuba min ruwa a buta zan wuce masallaci."

"To malam." ta fada tana fita daga d'akin.

Raheenat ce tsaye a bakin rijiyar tana jan ruwa itama zata zuba a buta, harara Inna ta wurga mata tare da fizge gugar a hannunta, bata tsaya ba ta wuce d'aki ta kaiwa Mama ruwan kafin ta fito tayi alwala.


******************

Ganin yanda Abdul d'in ke kallonshi yasa ya tsaya da shafa kanshi da yake yace "ya jikinka Abdul?"

Ko kad'an bai motsa idonshi ba hakan yasa ya sake cewa "baka jin komai?"

Nanma ba wata alama, d'an murmushi yayi yace "akwai tunanin da nake yi a kanka, sai dai ba lallai ne ya yiwu ba, dan akwai tawaya sosai daga d'aya b'angaren, amma duk da haka zan jaraba."

Sai lokacin Abdul ya lumshe idonshi kafin ya sake bud'ewa akan mahaifin nashi, kiran sallah ne yasa mahaifin nashi mik'ewa tare da cewa " ni zan tafi masallaci Abdul, saina dawo."

Bai jira amsarshi ba kai tsaye ya bar gidan ya nufi masallaci dan dama da alwalarshi, had'uwa sukayi da malam Habu suka gaisa sannan suka shiga ciki, haka ma bayan yan idar tare suka fito, a jere suke takawa a hankali suna yar hira sama sama har suka zo k'ofar gidan Alhaji Naseer d'in kafin ya tsayar da malam Habu......

_Kome zai faru?_


*Muje zuwa tare da*

_Meeraheenat_😍
08/08/2019 à 12:23 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 35 to 40



Bismillahir rahamanir raheem








Gyara tsayuwa Alhaji Naseer yayi tare da gyaran murya yace "malam Habu nasan ba kasan meye dalilina na tsayar da kai ba ko. ?"

Shima dai malam Habu gyara nasa tsayuwar yayi yace "gaskiya ban sani ba Alhaji. "

Murmushi Alhaji Naseer yayi yace "magana ne akan yarinyar gidanka. "


Cike da rashin fahimta malam Habu yace "Alhaji ai yaran gidan nawa suna da yawa, wacce a ciki kenan. ?"

Alhaji Naseer yace "ina nufin yarinyar da suke zaune gidanka ita da mahaifiyarta, Raheenat take ne ko wa."


"Ayyo Raheenat kenan, Allah yasa dai ba wani laifi tayi ba. "
Faɗin malam Habu yana kallon fuskar Alhaji Naseer.

Murmurshi Alhaji Naseer yayi yace "a'a ba tayi laifin komai ba, sai ma neman taimakonta da mukeyi. "

"Taimako kuma Alhaji.?"
Malam Habu ya tambaya cike da mamaki.


Alhaji Naseer yace "ƙwarai taimakonta malam Habu, kuma wannan taimakon ba zai samu ba har sai kai ma da taimakawanka. "

Malam Habu yace "wani irin taimakone wannan Alhaji.?"

Wani irin murmushi Alhaji Naseer yayi me ciwo yace "in ba zaka damu ba mu shiga daga ciki sai muyi maganar, dan be kamata ace munyi maganar a nan tsaye ba. "

Malam Habu yace "ba wani damuwa muje Alhaji. "

Nan suka ƙara jerawa zuwa cikin gidan Alhaji Naseer ɗin, basu ya da zango a ko ina ba sai cikin tanƙameme ko ƙawataccen falon Alhaji Naseer, izinin zama yayiwa Malam Babu sannan ya nufi Fridge ya ɗauko masa lemo ya ajiye masa a gabansa sannan shima ya nemi guri ya zauna.


Malam Habu ne ya kalli Alhaji Naseer yace "ina sauraronka Alhaji. "

Nisawa Alhaji Naseer yayi sannan yace "Malam Habu kadai san komai game da lallurar ɗana guda ɗaya tilo dana mallaka a rayuwa ba sai nayi masa bayani ba, yau kimanin shekara goma kenan Abdul-Hakeem yake zaune saman kujera baya iya motsa koda yatsar hannunsa, anyi maganin anyi maganin amma har yau babu wani canji, sanin kanka ne ƙasashen dana fita da Abdul dan neman lafiyarsa ba zasu ƙirgu ba, amma abin mamakim yanda muje haka muke dawowa, maganar gaskiya ba sai na faɗawa kowa ba ansan ina cikin matsanancin damuwa game da ciwonsa, sannan ina matuƙar tausayawa masa, na daɗe ina neman hanyar da Abdul zai samu sausaucin akan ƙuncin da yake ciki amma na kasa, sai shekaran jiya na samu hanyar da na tabbatar Abdul ɗina ko be warke ba zai zauna cikin farin ciki saɓanin yanzu da kullum bana hangen komai a fuskarshi sai ƙunci da baƙin ciki, kuma ba wata hanya bace sai na aura masa Raheenat. "

Da sauri malam Habu ya kalli Alhaji Naseer yace "aura masa Raheenat kuma Alhaji.?"

Ɗan murmushi Alhaji Naseer yayi yace "ƙwarai malam Habu, a shekaran jiya Raheenat ta shigo gidannan ɗibar ruwa, a lokacin Abdul na zaune yana shan iska a farfajiyar gidan nan, basan me ya faru ba, amma mun fito mun iske Raheenat tana bawa Abdul ruwa yana sha, lokaci ɗaya naji yarinyar ta burgeni, daga shigowarta har ta fahimci yana son ruwa alhali ba magana yakeyi ba ? Hakan ne ya tabbatar mun in na aura masa yarinyar zata kula dashi sosai, sannan ni na hango wani abu cikin idanun Abdul game da yarinyar lokacin da take bashi ruwan, malam Habu dan Allah dan annabi ina neman alfarmanka ka bawa ɗana Abdul-Hakeem auren yarinyar nan, ta hakanne kawai mahaifiyarsa zata samu sausauci shima ya samu me kwana tare dashi, na tabbatar Abdul zaiyi farin ciki, duk da nasan kamar cutar da rayuwar yarinyar ne amma ku taimaka ku taimaki yarona, ina ji ajikina aurenta da Abdul zai zamo mana alkhairi dan Allah kuyi min wannan alfarman. "
Ya ƙarasa maganar yana haɗa hannayensa alamar roƙo, ga hawaye da suka cicciko idanunsa.



Shiru malam Habu yayi yana wani tunani, haƙiƙa Raheenat yarinya ce me ilimi, tabbas zata bada gudummuwarta sosai akan Abdul, saboda shi a iya hasashenshi ya gane ciwon Abdul bana asibiti ba ne, sannan ɓangare ɗaya yarinyar tana cikin haɗari a cikin gidansa, dan yasan ba lalene Sadiq ya ƙyaleta ba tunda sheɗan ya riga ya buga masa ganga, yana matuƙar tsoron abinda zaije ya dawo, a halin da ake ciki yanzu aurenta da Abdul wata hanyace ta tsiratar da mutuncinta daga farmakin ɗansa Sadiq, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Alhaji Naseer yace "naji duk abinda kace Alhaji, sai dai karka manta wannan yarinyar marainiya ce, taimakonsu nayi ita da mahaifiyarta, saboda basu da kowa, koda ba zance haka ba dan dangin mahaifin yarinyar suna nan, zumunci ne dai da yanzu ya zama sai addu'a, da zaran aka ce mutum ya faɗi ya mutu to da wahala ka ga ƴan uwansa sun tallafi ƴaƴansa, sai dai abarsu su wulaƙanta, to hakanne suma ya faru dasu Raheenat har Allah ya haɗani dasu na taimakesu na kawosu gidana, bana da iko akan Raheenat, sai dai zan iya taimakawa wajen ganin burinka ya cika."


"Kai, amma malam na gode sosai kuma naji dad'i, Allah ya taimakeka kaima kamar yanda ka taimakeni, Allah ya sanya farin ciki a cikin rayuwarka kamar yanda ka faranta mana, kuma Allah ya saka maka da mafificin alkairinsa."

"Ba komai Alhaji, ai yiwa kaine, yanzu zan samu mahaifiyar yarinyar da maganar, duk yanda mukayi da ita insha Allah za kaji, inhar ta amince nasan zata sadamu da dangin mahaifin yarinyar insha Allah."

"Na gode sosai malam Habu, ba zan tab'a mantawa da wannan taimakon ba a rayuwata ba, sai naji daga gareka."

Mik'ewa malam Habu yayi tare da fad'in "gashi kuma har an fara kiran sallah isha'i."

"Gaskiya ne, kasan lokacin wannan sallolin shi yafi zama tak'aitacce, inaga kawai muje saimu mayar da sallah." cewar Alhaji Naseer

Tare suka koma fita suka tafi masallaci dan gabatar da sallah isha'i, ko da aka idar da sallah suka fito sallama suka ƙarayi wa juna kowa ya nufi gidansa.


***********

Saida Malam Habu ya gama ci abinci sannan ya kalli Inna yace "Ramatou jeki ki kira min Fateema a ɗakinsu. "

Wani kallo Inna tayi masa kafin tace "wacce Fateeman kake nufi malam. ?"

Ba tare da ya kalleta ba yace "Fateema nawa ne a gidan nan Ramatou?"

Cikin jin haushi tace "wai malam Maman Raheenat kake nufin inje in kira maka.?"

Malam Habu cikin ɓacin rai yace "Ramatou bana son jan magana, zaki je ne ki kira min ita ko kuma naje da kaina."

Ganin ransa ya fara ɓaci ne yasa ta miƙe cikin itama nata ɓacin ran ta fice daga ɗakin ba tare da ta ƙara magana ba, ita haushinta ɗaya aikenta da malam yayi ta kira masa Maman Raheenat, yanzu har ita ce za'a aika kiran wancen banzar matar, ko me malam zai faɗa mata ? Abinda Inna take faɗi kenan har ta isa ɗakin su Raheenat, daga ƙofa ta tsaya ta hankaɗe labulan ɗakin ba tare da tayi sallama ba tace "uwar manafunci kizo malam na kiranki, kullum dan salon munafunci kina ƙunshe a ɗaki sai kace daddawa, ko kuma sabuwar amarya, duk munafincinki da karuwancinki wallahi mijina yafi ƙarfinki ki, inma wani abu kike ƙullawa tun wuri ki kwanceshi, dan kishi da Ramatou ba zai miki daɗi ba, banza kawai dangin mayu, marasa asali. "
Tana gama faɗin hakan ta saki labulan ta juya ta koma inda ta fito.

Kallon kallo akeyi tsakanin Mama da Raheenat dake zaune riƙe da al'qur'ani a hannu tana karantawa, kalaman Inna matuƙa sunyi masu zafi, amma ya zasuyi tunda suna zaune a gidansu ne, duk wani abu da zata faɗa musu yanzu dole suyi haƙuri su jure, miƙewa Mama tayi jiki a sanyaye ta ɗauki hijjabinta ta saka ta nufi hanyar fita ɗakin dan jin kiran da Malam Habu keyi mata tare da cewa Raheenat "bari naje nazo ƴar albarka. "

Raheenat bata iya amsa wa Maman nata ba har ta fice daga ɗakin.


Sallama tayi a bakin ƙofar ɗakin Inna, malam Habu ne ya amsa tare da cewa "shigo mana Fateema. "

Buɗa labulan tayi ta shiga tare da ƙara wani sallamar, guri ta samu can gefe ɗaya ta zauna, yayin da Inna take ta aika mata da harara.

Saida ya matsar da kwanukan gabanshi qara tanqwashe qafafunsa yana kallon Mama kafin yace "Fateema dama wata magana ce nake so muyi dake mai mahimmanci, shi yasa nace kizo."

Cikin ladabi kanta qasa tace "to Allah yasa muji alkairi."

Gyara murya yayi yace "kafin na shigo gida makocinmu Alhaji Naseer ya tsayar dani akan wata mata mai mahimmanci, maganar kuwa itace akan 'yarki Raheenat."

Sai lokacin ta kalleshi tace "toh, Raheenat kuma, Allah yasa ba wani abun ba tayi?"

D'an qaramin murmushi yayi yace "a'a Fateema, ba laifi tayi ba, ya sameni ne akan yana so abawa Abdul Hakeem d'ansa auren Raheenat, amma na fad'a masa bana da iko akan haka, kuma nace zan miki magana tunda kece mahaifiyarta."


Tunda yace aure tsakanin Raheenat da Abdul take kallonsa harya gama, da mamaki tace "d'ansa dai dana sani marar lafiya?"

"Eh, shi."

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi amma ba tace komai ba, kallonta ya sake yi a nutse yace "Fateema, wannan fa ba dole bane, idan kinga zaki iya to , idan kinga da tawaya a ciki ma ba za'a miki dole ba tunda 'yarki ce."

Tsal, Inna dake gefe ta karbe da cewa "yo wace tawaya ce a ciki? taimako fa zasuyi su dubi halin da yaron yake ciki, na tabbata da lafiyarsa k'alau dako wannan tunanin ba zata tsaya ba, kuma naga yarinyar da babu wanda yasan asalinta harma an samu babban gida irin wanan suce suna so, amma har a tsaya wani jan aji."

Wani kallo Baba ya mata yace "dan Allah jiramu a waje, maganar fahimta muke."

Da mamaki tace "malam, akan wannan d'in..."

"Nace ki fita ki jiramu." yanda yayi maganar yasa dole ta tashi ta fita tana gunaguni.

Tana fita ya mayar da kallonsa ga Maman Raheenat yace "ina jinki maman Raheenat, me kika yanke."

A cikin nutsuwa ta fara magana "kayi hak'uri Baban Sadik, ina kallonka kamar yaya, zaka iya yanke hukunci a kaina ma bare kuma 'yar dana haifa, amma a gaskiya ina ganin kamar akwai babbar matsala a auren Raheenat da Abdul, domin kuwa shi yana da matsala ita kuma lafiyarta lau, hakan na nufin za'a tauyeta sosai, domin maganar aure ake bawai wacce zata masa aiki ba, ana aurene da saran zama har abada, har abada na nufin har qarshen rayuwa, Raheenat kuma duka yanzu ne ta shiga shekara ta sha bakwai a duniya, idan aka had'ata da Abdul wanda ko magana baya iya yi, sai naga kamar an cutar da ita, amma kayi hak'uri Baban Sadik idan abinda na fad'a bai maka dad'i ba."

_Hmmmmmmm_

*Muje zuwa tare da*

_Meeraheenat_😍
08/08/2019 à 12:23 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```

_Bismillahir_rahaman_rahim._


Page _40 to 45_


"Ba komai Fateema, kuma naji dad'in hangen nesanki wanda ni da mahaifin yaron duk ba muyi ba, tabbas Raheenat zata cutu a zamansu, dan haka ki kwantar da hankalinki kuma ki d'auka maganar nan kamar ba'a tab'a yinta ba, dama nazo miki da maganarne da tunanin samun maslaha tsakanin Raheenat da Sadik, dan d'an yau ka haifeshi ne baka haifi halinshi ba."

Cike da jin dad'i tace "na gode Baban Sadik, Allah ya shige mana gaba, kuma dan Allah ina nemawa Sadik afuwa akan abinda ya faru, kasan yara sai hak'uri."

"Haba Fateema, wane irin yara? wanda yake wa mace wannan maganganun ne za'a kirashi da yaro."

Shiru dai tayi hakan yasa yace "ba komai, zaki iya tafiya."

A nutse ta tashi tana fad'in "a tashi lafiya, saida safe."

Inna ce k'ofar d'akin ta kasa kunne tana jin me suke fad'a, tana ganinta ta harareta tare da tsaki, Mama dai wucewa tayi d'aki ta samu har yanzu Raheenat na karatu, ganin Mama yasa ta rufe ALQUR'ANIN tana fad'in "Mama, lafiya dai ko, ba wani abu bane ya faru?"

Ajiyar zuciya ta sauke tare da cire hijabinta ta aje akan katifa tace "lafiya lau Raheenat, ba wani abu bane, magana kawai mukayi."

Tarbiyar da Raheenat ta samu ba zata barta ta tambayi akan me suka tattauna ba, a hankali ta aje Alqur'anin hannunta ta cire hijabi ta kwanta akan katifar tare da d'aukar littafin Husnul muslim ta fara karantawa, Mama ce ta kwanta gefenta itama tana fad'in "Raheenat kenan, ba kya gajiya da karatu."

Murmushi tayi tace "Mama kenan, ai duk musulmi na qwarai ba zai gaji da karanta abinda zai anfaneshi ba, wannan karatun nafi jin dad'inshi akan komai, yafi d'ebe min kewa da sakani nishad'i."

"Allah ya taimaka, Allah kuma ya miki albarka."

Cike da zumud'i tace "ameen Mamana, na gode."

Bacci ne ya d'auki Mama Raheenat kuma saida ta daina jin motsin bil'adama a kunnenta kafin ta aje littafin tayi addu'ar kwanciya bacci ta shafe jikin Mama duk da a gabanta tayi addu'a, sannan itama ta shafe jikinta ta kwanta.


_Kafin muci gaba, bara muji su waye ne su Raheenat d'in nan_


▶▶▶▶▶▶

Kamar yanda Abdul yayi tunani hakane ta kasance, fitarta daga nan sallah kawai tayi ko wanka ba tayi ba ta shiga gugar kayan Hajia Luba, saida ta gama ta shiga d'akin *Nabeela* domin gyara mata d'akinta, kasancewar itace auta yan uwanta kuma suna qasar waje suna karatu, cikin sauri ta kammala gyaran ta bar d'akin dan bata fatan yarinyar tazo ta sameta ta fad'a mata magana marar dad'i, fitowarta kuma yayi daidai da shigowar Alhaji sun dawo daga masallaci, da sauri Hajia Luba ta tashi ta tarbeshi cikin shirin riga da siket da suka mugun kamata sosai, rumgume juna sukayi kamar yanda ta sama mishi tana masa sannu da zuwa, wucewa tayi kicthen ta d'auko abincinta dana Abdul sannan ta fito, kamar zata wuce sai taga ya kawar da kansa daga barin kallon inda take, sunkuyawa tayi tace "Hajia na gama, ina so zanje b'angarena."

A wulak'ance ta kalleta tana shafar jikin Alhajin tace "kije, kuma ki tabbatar kinyi sammakon tashi gobe."

"To Hajia, insha Allah ba zan makara ba."

Tana fad'a ta tashi ta wuce ba tare data kalleshi ba ko tayi masa magana, tana wucewa yaja tsaki dan jin muryarta yake kamar tana watsa mishi ruwan zafi a jiki, ya tsani ganinta a rayuwa ba kuma yasan rayuwarta a cikin gidanshi, kawai tana zaune ne saboda Hajia Luba ta buk'aci hakan.

B'angarenta ta nufa dake buk'atar gyara sosai ta wuce d'akinta tayi wanka sannan tayi sallah isha'i, tsofaffin kayanta ta saka ko man da zata shafa bata dashi bare turare haka ta nufi d'akin Abdul, kamar dai yanda ta barshi haka ta sameshi, da qyar ta cuccub'ashi ta aza a kujerarshi ta nufi toilet dashi dan tasan zai buk'aci hakan, ai kuwa kamar jira yake ya fara zunduma fitsari, saida ta zuba masa ruwa sannan ta fito dashi, akan kujerar ta bashi abinci sannan ta mayar dashi ta kwantar, zaune take tana shafar kanshi saita fara gyangyad'i, da ido ya kafeta yana so yace taje ta kwanta amma ba hali, langab'owar da kanta yayi har tana neman fad'a masa yasata zabura ta bud'a ido, kallonshi tayi tana murmushi amma ganin kallon da yake mata yasa ta sake shafar kanshi tace "naje na kwanta kake nufi?"

A hankali ya lumshe idon alamar Eh, sumbatar kanshi tayi sannan ta mik'e taja masa zanin rufa tace "saida safe d'ana."

Yana ganin ta kashe masa wutar d'akin ta fita ya maida idonshi ya rufe, kyakyawar yarinyar data bashi ruwa ce ta fito a majigin qwaqwalwarshi, bud'a ido yayi ya fad'a a zuciyarshi *wacece ita*?.

"Ni zan fad'a maka."

"Haba my Meerah, ina ruwanki to? ki bari zai sani da kansa mana." cewar my Heenat.

Turo baki nayi gaba nace "hum, nifa kinsan bana son jira, zaifi kawai ayita ta qare.


_Zamu fara jin asalin labarin gidan Alhaji Naseer, kafin muci gaba_


*Waiwaye, inji bahaushe yace ado na tafiya*




Alhaji Naseer buzu haifaffen najeriya ne cikin garin kano, mahaifinshi Alhaji Musa ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa, ya tara dukiya me yawan gaske, yana da matar aure ɗaya me suna hajiya Rabi, hajiya Rabi buzuwa ce ƴar ƙasar niger, harkan siyasarsa ce ta kaishi can ya aurota, sun haifi yara uku tare, Alhaji Naseer shine babba, sai ƙaninsa me bi masa me Suna Ahmed sai auta Hajara, sun taso cikin gata da tarbiyya, iyayansu suna matuƙar ƙaunarsu, Alhaji Naseer yayi karatunsa tun daga primary har zuwa jami'a duk a cikin garin kano, business ya karanta saboda shine burin mahaifinsa, bayan kammala karatunsa mahaifinsa ya mallaka masa ɗaya daga cikin kampanoninsa, nan shima ya kutsa cikin kasuwanci sosai kuma Allah ya albarkaci kasuwancin nasa, ba'afi shekara biyu ba da kammala karatunsa Allah yayi wa mahaifinsu rasuwa sakamakon jinya da yayi, sunyi kukan rashin mahaifinsu sosai, amma babu yanda suka iya dole suka sakawa zuciyarsu haƙuri suka bisa da addu'a.


Bayan rabon gado ne Alhaji Naseer ya ƙara bunƙasa harkokin kasuwancinsa, sosai Allah ya saka masa nasibi a ciki, ɗan uwansa Ahmed kuwa harkan siyasa ya faɗa gadan-gadan, shima sai Allah ya dafa masa cikin harkokin nasa, ya zamana kula da mahaifiyarsu da ƴar ƙanwarsu ya dawo hannunsu, bayan rasuwar mahaifin nasu da watanni goma sukayi wa ƙanwarsu Hajara aure da wani me kuɗi, haka rayuwar ta ci gaba da tafiya musu cikin nasarori, cikin haka ne Allah ya haɗashi da Lubabatu, soyayya sosai sukayi da Luba wanda har ta kaisu ga aure, lokacin ne shima Ahmed ya mallaki nasa iyalin.


*Wacece Hajiya Luba*


Lubabatu ƴar wani hamshaƙi ne anan kano, mahaifiyarta Hajiya Kilishi macece me ji da kanta tare da son abin duniya, sam bata son wani ya raɓi me gidanta harta da danginsa, duk tabi ta kakkane komai daga ita sai ƴaƴanta, Hajiya Kilishi irin ƴan ɗuniyar matan nan ne, bin bokaye gurin hajiya Kilishi ba'a magana, duk wani damuwa nata to tayi amanna bokaye ne zasuyi mata maganinsa, ta mallake Alhaji Bashir sai yanda tayi dashi, komai ta faɗi ya zaunu babu ja, ta zama itace me jan ragamar gidan gaba ɗaya, Luba ta taso yarinya mara tarbiya, duk abinda takeso shi takeyi, duk wani halayyar mahaifiyarta babu abinda ta bari, tun tana budurwarta take bin bokaye dan samun biyan buƙatarta gurin samari, domin hakaɗin horan mahaifiyarta ce.


Shi yasa kafin shigowarta gidan Alhaji Naseer suka bi duk wani hanya da zai saka ta mallakeshi a hannunta, kuma burinsu ya cika, domin ta samu yanda take so, zamane da soyayya sukeyi tsakaninsu, komai take so Alhaji Naseer nayi mata shi, sam baya son damuwar Lubabatunsa, shekararsu ɗaya da aure Hajiya Luba ta samu ciki, zo kaga murna gurin Alhaji Naseer, ciki na shiga watan haihu ta haifi ƴarta mace, ba haka Luba ta so ba, taso ta haifi namiji ne saboda ya zamo ta mallake gida gaba ɗaya, haka dai ta saka wa zuciyarta haƙuri tare da fatan gaba ta samu ɗa namji, ranar suna na zagayowa yarinya taci suna Rabi'atu sunan mahaifiyar Alhaji Naseer, suna kiranta da Mimie.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya musu sai dai hajiya Luba sam ta kasa samun abinda takeso, saboda bayan haihuwar Rabi'a mata biyu ta sake haifa, Salma da Nabeela, hakan beyi mata daɗi ba amma sai ta saka wa zuciyarta haƙuri ganinta ai ta riga da ta gama mallakar gidan Alhaji Naseer, saboda sai abinda tace tana so ita ɗa ƴaƴanta yakeyi, haka take zuba milkinta yanda yakeso a cikin gidan ba tare da damuwar komai ba, kuma tun daga kan Nabeela haihuwa ya tsaya mata cak.


Ɓangaren Alhaji Naseer kuwa, son samun ɗa namiji ne ya mamaye zuciyarsa, kasancewar kasuwancinsa na ƙara bunƙasa, domin zuwa yanzu ya mallaki kamfanoni zasu kai goma bayan super market's da store's da ya mallaka masu yawa, hakan yasa yake son samun magaji, wanda zai kama masa wasu harkokin nasa, kuma ko bayan ba ransa zai samu magaji.


Mahaifiyarsa ce ta shawarcesa akan me zai hanasa ya ƙara aure ko Allah zai sa ya samu ɗa namiji, yaji daɗin shawarar mahaifiyar nasa, sai dai a inda kizo ke saƙar shine bashi da wata mace da yake so, sannan be san ta inda zaibi ya sanar da Hajiya Luba batun yana son ƙara aure ba, hajiya Rabi lura da tayi da yanayin da ɗan nata yake ciki yasa tace yabar mata komai a hannunta ita zata nema mishi matar aure kuma bata son ya sanar da matarshi batun har sai komai ya kankama, to dama dai tana labarin hajiya Kilishi mahaifiyar Luba da ita kanta Lubar, hakan ne yasa tace karya faɗa mata maganar auren.


Maryam yarinya ce me tarbiya, ta haɗa komai, kyau, hankali, nutsuwa tare da nasaba, iyayanta masu ƙaramin ƙarfi ne, saidai sunfi ƙarfin komai, maƙota suke da gidan Alhaji Musa, wato gidan Hajiya Rabi mahaifiyar Alhaji Naseer.

Hajia Rabi ta gamsu da tarbiyar Maryam hakan yasa ta nemi aurenta a wajen mahaifinta, magana ce tayi qarfi har maza suka shiga ciki, cikin ikon Allah kuma komai ya tafi yanda ake so, Alhaji Naseer yakan fake da zuwa wajen mahaifiyarshi ne sannan yaje wajen Maryam zance, a haka kuma soyayya saita shiga tsakaninsu, saboda Maryam nada hankali sosai kuma

Please Login or Register in order to submit comment