Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koda ta motsa yatsarshi, yayin da aka suka rufe bakunan mutane daga yi musu addu'a, tayi nasarar mayar da Maryam yar aikinta, kuma an sakawa Alhaji Naseer tsanarta fiye da komai, a lokacin kawai lafiya yake nemawa Abdul Hakeem gari gari qasa qasa, amma shiru babu labari daga hakan komai ya tab'arb'are, bawai dangi na nesa ba ko Hajia Maryam da Alhaji Naseer babu wanda ya tab'a cewa Allah ya bashi lafiya, bare kuma dangi na nesa dana kusa, d'aid'aikun mutane kad'ai ke iya mishi addu'a wanda ansan ba kullum zasu mishi ba, kuma a lokacin sai Hajia Luba ta fara sakin baki a gaban Abdul Hakeem, dan akwai wata rana ta shiga d'akin tare da Alhaji da nufin ganinshi, kwance yake kamar yanda yake tunda larurar ta sameshi, Alhaji ne ya fara fita bayan mishi magana kafin ta matso tana kallonshi tana dariya tace,

"Yaron babanshi kenan ana kwance, toya kake ji a halin yanzu? humm, kayi hak'uri duk da dai nasan ba laifinka bane, amma mahaifiyarka taja maka, domin kuwa ta had'a hanya dani har takai ga kaiwa wajen dani kad'ai keda ikon kaiwa can, kasan inane wannan wajen?" ta tambaya cike da iskanci.

Murmushi tayi ba tare da kunya ba tace "ina nufin ta bari mahaifinka yayi anfani da kanshi a wajenta kamar yanda yake yi a wajena, alhalin nayi alk'awari ni kad'ai zan zama tashi, wannan shiya janyo maka kwanciya anan kamar gawa, kuma za kaci gaba da zama a haka har lokacin da mala'ikan d'aukan rai zai sameka, idan kaje lahira kuma ka had'u da yan matan aljanna, toka fad'a musu Alhaji Naseer mijin Hajia Luba, nata ne ita kad'ai ba zata iya sharing d'inshi da wata ba, ka gane.?"


Daga haka Abdul Hakeem ya fara rayuwar k'unci da takaici, fatan Allah ya baka lafiya Abdul😭....




*Bara muji asalin Raheenat*




Malam Muhammadu da Rasheeda ƴan asalin garin agadaz ne dake ƙasar niger, talauci da rashin qwqwaran abinyi ne ya fito dasu daga garinsu zuwa Maradi, inda Muhammadu ya samu aiki a gidan wani Alhaji yana masa aikin gadi, da kanshi ya basu wani fili a cikin filayen da yake dasu a cikin unguwar *Ali d'an sofo*, da qyar malam Muhammadu ya samu ya tayar musu da bukka a tsakiyar filin, a lokacin Fateema nada shekara biyu ne a duniya, a haka suka fara rayuwarsu a wannan yar bukka , kasancewar Alhaji mutum ne ba mai zama ba yasa suke shan wahala ko wajen samun abinda zasu ci.


*Shekararsu d'aya* a garin Maradi suna paputuka, ta yanda har Rasheeda saida ta fara shiga gidajen masu kud'i, wani wurin ta kanyi dace a bata wankin kaya wani wurin kuma sai dai a bata hak'uri ta dawo, wani mak'ocinsu mai sunan *Salisu* ne ya bawa Muhammadu shawarar ko zai fara fita *Nigeria* domin samun abinda zai rufawa kai asiri, da wannan shawarar sukayi anfani ya shirya tsaf kuma ya tafi, cikin ikon ubangiji sai sana'ar lebarenci ta karb'eshi, *wata biyu* yayi acan ya dawo, ya samu iyalenshi sun jikkata sosai saboda rashin abinci da kayan masarufi, a lokacin kuma Alhaji ya dawo daga wata tafiya saiya sallameshi tunda yaga ba niyyar zamane dashi ba a waje d'aya, hakan yaba Muhammadu damar sake komawa garin *Kano* domin nema....


*Muje zuwa tare da*


_Meeraheenat_😍
21/08/2019 à 06:21 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITING*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```


_Bismillahir rahamanir rahim._




Page _55 to 60_




Domin neman halalinsa, be bar ƙasar niger ba sai tare da matarsa da ƴarsu guda ɗaya wato Fateema, koda suka iso garin Kano sunsha wahala matuƙa kafin ya samar musu gidan hayan da zasu zauna shi da iyalinsa, gida ne irin ginin ƙasar nan me ɗauke da d'akuna kusan goma cikinsa, haka dai suke rayuwa cikin gidan yana fita yana leburancinsa domin samarwa kansu abinda za suci, haka rayuwa take tafiya musu cikin rufin asiri domin kam babu laifi yana samu, rayuwa ba fara yi musu zafi ba sai lokacin da ƴarsu Fateema ta shekara biyar a duniya, a lokacin ne komai ya kwaɓe wa malam Muhammadu, ko ya fita da ƙyar yake iya samo abinda zasu ci, wata rana ma yanda ya fita haka zai dawo, suna cikin wannan hali na ƙangi da talauci ne Allah ya haɗashi da wani Alhaji, Alhaji Isma'il mutum ne me son mutane da tausayawa na ƙasa dashi, ranar Malam Muhammadu ya fita neman abinda za suci shi da iyalansa ne, domin tun ranar jiya rabonsu da abinci, ga ɗiyarsu Fateema sai kukan yunwa takeyi, kuma cikin gidan nasu babu wanda yaga Allah ya jefesu da ko lomar abinci ne, a cewarsu kowa ta kansa yakeyi, yayi yawon amma be samu komai ba, ga rana ta take hakan ne ya tilas ta masa samun guri a jikin wani katon gida ya zauna yana hutawa, yana zaune ya shiga duniyar tunani be san sanda hawaye yake zuba masa ba, tausaya wa kansu yakeyi da *Halin rayuwar* da suka tsinci kansu a ciki, ko'ina babu sauƙi, be san da zuwan mutum ba saboda yayi zurfi cikin tunani kawai sai jin magana yayi, da sauri ya ɗago da kansa yana kallon Alhajin dake tsaye.

Cikin taushin murya Alhaji Isma'il yace "bawan Allah kai ko me yayi zafi haka da zaka zo cikin rana ka zauna kana hawaye, komai yayi zafi maganinsa Allah ne. "

Wasu hawayen ne suka tawowa Malam Muhammadu, cikin muryar kuka yace "ba zaka gane bane Alhaji tunda kai Allah yayi maka ni'ima, tun jiya kamar iwar haka rabonmu da abinci ni da iyali, nayi biɗar nayi biɗar ban samu ba, har kwasan bola na nemi a bani abin ya gagara, dako nan ma cikin kasuwa na gaza samunshi, yanzu haka ƴarmu ƴar shekara biyar na can tana kuka babu abinda zata ci, to ka faɗa min in banyi kuka ba me ka keso nayi. "

Ya ƙarasa maganar wasu hawayen na zubo masa, cikin matuƙar tausayawa Alhaji Isma'il ya duƙa gabansa yace "kayi haƙuri kabar kuka dan Allah, zaka iya gadi.?"

Washe baki malam Muhammadu yayi cikin farin ciki yace "me zai hanani ni kuwa, wallahi zan iya. "

Murmushi Alhaji Isma'il yayi yace "masha Allah, dama ina neman me gadi saboda me gadina yayi tafiya, yanzu bari na shiga gida na kawo maka abincin da zakaje kuci da iyalanka kafin gobe sai kazo ka fara gudanar da aiki. "

Cikin tsananin farin ciki malam Muhammadu ya dinga zubawa Alhaji Isma'il godiya, miƙewa Alhaji yayi ya shige wannan gidan, be daɗe ba sai gashi ya fito da ƙaton kula a hannunsa, meƙawa Malam Muhammadu yayi yace "gashi ko, haka kawai naji na yarda dakai, shi yasa ma har nayi maka tayin gadin gidana, ina fatan zaka zama me amana. "

"Insha Allahu Alhaji zaka sameni fiye da tsammaninka, nagode, nagode, Allah ya jiƙan mahaifa. "

Nan dai Malam Muhammadu ya dinga zuba ma Alhaji Isma'il godiya kafin ya miƙe ya nufi hanyar gida zuciyarsa cike da farin ciki.


Koda ya koma yake faɗawa Rashida yanda sukayi da Alhaji tayi farin ciki sosai, tun daga wannan rana malam Muhammadu ya fara gadi a gidan Alhaji Isma'il, alhamdulillahi rayuwa tayi musu daɗi, domin kullum sai hajiya juwairiyya ta bashi abinci tare da kaya ya kaiwa iyalanshi, mace me kirki kenan da sanin ya kamata, da tafiya yayi tafiya ma sai Alhaji Isma'il yace ya ɗauko matarshi ya dawo da ita gidan, nan ya basu ɗaki a b/q na gidan, rayuwa sukeyi cikin mutunta juna tsakanin hajiya Juwairiyya da Rashida, kasancewar Allah be bawa hajiya Juwairiyya haihuwa ba yasa ta ɗauki Fateema kamar ƴar da ta haifa, ya zamana Fateema ta koma hannunta, makaranta me kyau ta nema wa yarinyar ta sanyata tare da taimakon Alhaji Isma'il, duk wani gata sunayiwa Fateema kai kace su ne suka haifeta, hakanne ya ƙara musu matsayi da ƙima a idanun Malam Muhammadu da Rashida, ko tsinke Rasheeda bata bari hajiya ta ɗaga, ta ɗauke mata komai ita takeyi mata, zaman nasu dai gwanin sha'awa.


Fateema na girma kyawunta na ƙara fitowa, Allah ya sakawa Fateema son karatu sosai, shi yasa ta mayar da hankalinta ga karatu ba na bokon ba bana islamiyyar ba, hajiya Juwairiyya tana son Fateema sosai, bata son damuwar yarinyar, shi yasa itama Fateemar take sonta, komai Momy wani lokacin har mantawa takeyi da cewa Rashida ce mahaifiyarta, shekarar Fateema goma sha biyu a duniya Allah yayiwa malam Muhammadu rasuwa, sakamakon mota da ta bigeshi ya fita yiwa hajiya cefane, ranar me zuwa mata cefanan ne be zo ba ta fito tana neman ɗan aika, abinka da tsausayi da ƙarar kwana yace ta kawo yaje mata, yaje yayo cefenan zai dawo mota ta bankeshi, ko shurawa beyi ba a gurin, sai gawarshi aka kawo musu..

Rashida ta shiga tashin hankali da ba zai iya misaltuwa ba, haka Fateema duk da qaranci shekaru amma tasan tayi rashin mahaifi , shi kanshi Alhaji Isma'il yaji mutuwar kamar d'an uwanshi ne ya rasa, uwa uba kuma Juwairiya da take gani kamar silarta ne, damuwa da tunani ne sukayi tasiri a gurin Rashida sosai, wanda harya janyo mata matsanancin hawan jini, Juwairiya da mai gidanta na iya qoqarinsu wajen ganin sun bawa Rashida kukala, amma ina haka Allah ya tsara, ranar itama tana fitowa daga d'aki tayi alwala zata koma kawai ta fad'i qasa, Fateema dake rik'e da littafin karatunta ce tayi saurin ajewa takai mata d'auki, anyi sa'a Alhaji na gida suka kaita asibiti, har an rubuta magungunan da zai siyo kuma ya tafi siyowa koda ya dawo babu Rashida itama ta cika.

Fateema na jin haka ta yanki jiki ta fad'i sumammiya, kwananta biyu kamin tasan inda kanta yake, haka itama dai suka dinga jimaminta yayin da kullum mutuwar ke dawo musu sabuwa , saboda ganin Fateema cikin damuwa, gaba d'aya yarinyar saita fita a hayyacinta duk da irin kulawar da take samu, karatunta ma saiya zamana tana saku-saku dashi, dan tunani da kuka yafi yawa a cikin al'amuranta, Alhaji kuma na nuna damuwarshi akan haka, kullum cikin janta a jiki yake yana rarrashi, yau da gobe sai Allah sai shed'an ya farawa Juwairiya hud'uba akan cewar ai Alhaji zai iya cewa yana son auren Fateema, a lokacin saita fara canzawa Fateema, amma abin baiyi nisa ba Allah ya turo mata *Abdullahi*.


Tana da shekara *goma sha biyar* a lokacin suka had'u da Abdullahi, kuma yaron Alhaji Isma'il ne da yake aike, koda ya nuna sha'awar aurenta Fateema ta amince, dan a lokacin ta fara jin d'acin zaman gidan, da taimakon Alhaji akayi komai aka gama, duk da yaso yarinyar tayi karatu, amma tunda tace tana sonshi kuma tana son aure babu yanda ya iya, lokacin har ta kammala secondry ɗinta, cikin wata shida aka d'aura musu aure suka tare a unguwar sabon gari tare da mahaifiyarshi da qannanshi uku maza mata biyu, sosai Alhaji ya mata bajinta, dan saida ya cika mata d'akinta maqil da kaya masu kyau da tsada, qarancin shekarunta yasa ta kasa amincewa dashi da wuri har saida yayi hak'urin wasu kwanaki, ranar ma da dubara da wayo ya samu ya mayar da ita babbar mace, kasancewarshi shima matashi yasa suke matuqar qaunar junansu da kuma nunawa juna soyayya, sai dai hakan kuma yasa mahaifiyarshi ta fara saka musu ido tare da nunawa Fateema tsangwama.

Fateema kuma na hak'uri sosai kuma bata fad'a mishi duk abinda zasu mata, dan har qannanshi basu raga mata ba, wani lokaci har dukanta mahaifiyarshi keyi amma bata tab'a koda tunanin fad'a masa ba, ranar kuma mahaifiyarshi da qannanshi mata su biyu suna dukanta ya shigo gidan, nanya taimaka mata tashi ya kuma tambayi dalilin dukan, mahaifiyar ce ta fad'a mishi waita rainata, haushi ne yasa ya kama qannanshi suma ya dakesu dansu kiyaye gaba, amma furucin da suka fito daga bakin mahaifiyarshi sam ba dad'i, kuma a ranar tace ta cire hannu a al'amuranshi, tun daga ranar hankalin Fateema ya kasa kwanciya take lallab'ar mahaifiyarshi data yafe mishi, shima haka yake bata hak'uri amma sam tace bata bashi, wata uku kuma cikin *Raheenat* ya bayyana a jikin Fateema, kasancewar cikin bamai wahala da matsanancin laulayi bane yasa bata san tana d'auke dashi ba, Abdullahi ne ya fara ganewa daga ranar kuma salon tarairayarta ya canza, kulawa sosai take samu ita da abinda ke cikinta, matsalar d'aya mahaifiyarshi da bata shiga sabgarsu, a haka dai har cikin ya shiga watan haihuwa.


Ranar *Laraba* aka haifi Raheenat, santaleliyar yarinya wacce ta d'auko uwa da uba , koba komai Mama tayi farin cikin ganin yarinyar, duk da bata musu magana ba amma dai ta kula da yarinyar yanda ya kamata, duk wani abu da uba zaiyi Abdullahi yayi wa Fateema da 'yarta shi bakin gwalgwado, sai dai ance _ALLAH baya barin wani dan wani yaji dad'i_, washe garin ranar da akayi sunan Raheenat a ranar shima ya koma ga ubangiji, kafin ya fita haka kawai yake ji wata sabuwar qaunar iyalinshi na qara mamayeshi, harya fita ya dawo ya d'auki Raheenat yana mata wasa, kallonshi Fateema tayi tace "anya kuwa zaka fita yau?"

Kallonta yayi shima yace "aida zan samu Alhaji yace na zauna gida, wallahi dana ji dad'i matuqa."

Murmushi kawai tayi taci gaba da ninke kayanta, bata ankara ba taji ya rumgumeta ta baya yana sumbatarta , nok'ewa ta farayi gabanta na fad'uwa dan tana gudun yace zai zarce daga haka, tunda tana cikin jinin bik'i, da qyar ta samu ya rabu da ita kafin yace "ba zaki barni na rage zafi ba ko, ke kad'ai fa gareni."

"Kayi hak'uri, naji ana cewa sai anyi arba'in."

"Ke wannan fa al'ada ce ba addini ba, taya zan iya hak'ura har wannan lokacin? kema kin sani ai."

Raheenat ce tayi kuka yasa ta d'auketa tasa masa nono a baki, durk'usawa yayi yana kallonsu cike da so da qauna, cike da kunya Fateema ta kalleshi tace "ka tashi ka fita mana, rana fa takewa take."

Mik'ewa yayi yana fad'in "to na tashi, tunda baki so ina kallonku."

Kafin tayi magana kuma ya sumbaci goshinta tare da cewa "ina godiya a gareki abisa wannan babbar kyautar."

Sumbatar Raheenat yayi dake tsotsar nononta ido rufe, kafin ya fita yana kallonsu itama tana kallonshi, awa d'aya da fitarshi labarin mutuwarshi ta samesu, wanda yake tare dasu ne sukace yadai ce musu kanshi na ciwo, daga nan kuma sai yace zaije ya sha magani ya ɗan kwanta, to kwanciyar da be tashi ba kenan.


Fateema tayi kuka kamar hawayenta zasu ƙare, ta shiga matsanancin damuwa, Abdullahi shi kaɗai ya rage mata wanda take kallo taji daɗi, wanda in tayi kuka yake share mata hawayenta, yau gashi shima wanda ya fita sonshi ya ɗauke abinsa, yanzu ƴarta guda ɗaya tilo ita kaɗai ce danginta kuma sanyin idaniyarta.

Haka akayi zaman makokin Abdullahi aka ƙare, mahaifiyarsa kanta tayi kukan rashin ɗan nata me tsananin biyayya a gareta, ta kuma yi nadamar abinda ta dinga yi masa lokacin rayuwarsa, bayan kwana arba'in da mutuwar Abdullahi komai ya ƙara taɓarɓarewa Fateema, domin kuwa sam bata jin daɗin zama da uwar mijin nata da ƴan uwansa, abincin da zata ci kanshi basa bata sai tayi wankau ko daka wani lokacin take samu ta ci, haka dai zaman nasu ya dinga gudana, Fateema duk tabi ta fita a hayyacinta, wahala da rashin abinci duk ya galaɓaitar da ita, lokacin da ta fita takaba taje gidan Alhaji Isma'il neman taimako gurin hajiya Juwairiya, ƙiri-ƙiri ta koreta a gidan, tare da mata gargaɗin kar ta ƙara ganin ƙafarta ako ƙofar gidan ne, sai ka rantse bata taɓa sanin Fateema ba a rayuwarta, kuma wai duk hakan akan kishin mijinta ne wai kar Fateema ta aureshi, ko kuma shi yace yana so, domin Allah yayi wa Fateema kyau.


_Hnmm, shaiɗan kenan me raya mana abubuwan da be kamata ba, yanzu dai duk kirki irin na hajiya Juwairiya shaiɗan yy galaba akanta, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyarmu, ya karemu daga sharrin shaiɗani ameeen._



Tun daga wannan rana rayuwa ta ƙarayiwa Fateema ƙunci ita da jaririyarta ƴar wata biyar, ta shiga *ƙangin rayuwa* wanda Allah ne kawai zai fitar da ita, ga babu dangin uwa bare na uba a gari, yanzu ita ko wuƙa aka sanya mata a wuya ba zata iya kai kanta agadaz ba balle ta nuna danginta.





Muje zuwa tare da Meeraheenat😘
22/08/2019 à 21:16 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITTEN*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```
23/08/2019 à 12:47 - ~NANA KHADIJA~😍: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑



*STORY AND WRITIN*


*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*




DEDICATED TO ALAWIYYA❤




*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```

_Bismillahi_rahaman_rahim._



Page _60 to 65_



Haka rayuwar take tafiya musu ba dad'in yau bana gobe, abin tashin hankalin shine tattara komai da mahaifiyarshi tayi wanda ya mallaka ta rik'e, yanzu haka daga cikin gadon ne take siyan kayan tana tafiya qauye tana siyarwa, idan kuma tayi wannan tafiya komai yafi qara lalacewa, dan tana bawa yaranta kud'in abinci ne, ita kuma ko oho haka ma jikanyarta, tun daga ranar da zata tafi harta dawo ita zata dinga neman abinda zata ci ita da 'yarta, a sannu sannu sai watanni suke shud'e aka fara lissafa shekaru.

*Bayan shekara biyar* Raheenat tayi wayo, kyakyawan yarinya mai kama da mahaifiyarta a fuska, amma a suffa mahaifinta ne sak hatta yatsun qafa dana hannayenta, lallausan hanaye da tsayi, Fateema ta dage sosai har saida ta sata boko da islamiyya, kuma sosai ake ganin ci gaba a karatun yarinyar, a lokacin Fateema ba abinda ba tayi na sana'a danta taimaki 'yarta da kanta, kullum qannan Abdullahi da mahaifiyarsu goranta mata suke akan ta tafi ta basu gida, da farko tace zaman Raheenat take dan bata san inda zata je da ita ba, amma da abin yayi yawa sai tace to subata gadon Raheenat zata tafi, koba komai zata gina rayuwar yarta dashi, daga lokacin sai suka daina maganar, dan insun matsa magana zata iya girma.


A haka aka sake shanye wasu shekarun, Raheenat nada *shekara koma sha biyar* ranar kakarta ta tafi qauye, wannan tafiyar da tayi bata dawo ba tsawon lokaci, kasancewar kuma duka qannan mahaifinta sunyi aure kuma dama babu wanda suke gani idan ba kakarta kenan ba, hakan yasa basu damu ba dan dama ba taimakonsu suke ba inba baqar magana zasu fad'a musu.

Rana tsaka wani Alhaji ya sallamo gidan, Mama ce ta fita ta ganshi nan yake fad'a mata wai ya siyi gidan wajen mahaifiyar Abdullahi, notice ya basu na kwana uku akan subar gidan, d'aurewar kai da Mama ta samu yasa tama kasa maganar da Raheenat, a daren ranar da washe gari mutumin zaizo sam Mama bata rintsa ba, da safe kuwa Raheenat na shirin tafiya islamiyya mutumin yayi sallama, tsoro da fargaba yasa Mama yin shiru tak'i amsawa, shi kuma daba mutunci ne dashi ba yasa yaran da yazo dasu suka shiga gidan, cike da wulaqanci suka dinga fito musu da kayansu suna watsi dasu akan hanya, Mama tayi magiya tayi kuka ita da Raheenat amma ko jinsu basuyi ba, mutane kuma na kallo babu mai *zuciyar taimako*, tofa ana hakane Allah ya kawo Malam Habu wajen yaga wannan cin zarafi, daga nan ya d'aukesu ya tafi dasu gidanshi har suke zaune cikin wannan tsangwamar ta Inna.



*Cigaban labari*


Kamar kullum Raheenat bata kwanta ba ta fara shirya abin karyawa, sai dai ba tayi mamakin ganin su Farida a wajen ba har suna kama mata tunda Babansu yana nan, duk da ba wani aiki sukayi ba saida suka gama a tare sannan ta shiga wanka tayi shirin islamiyya, haka suma su Farida shirin islamiyya sukayi tunda mahaifinsu nanan dole yau zasu tafi ko basu so.

Baba na d'aki zaune yana karyawa Inna na gefenshi yaran suka shigo da sallama, amsawa sukayi a tare suka durk'usa suka gaisheshi, amsawa yayi tare da d'orawa "har kun gama shiri kenan?"

"Eh Baba." suka amsa.

"To a tashi a tafi, Allah ya tsare ya kiyaye."

"Ameen Baba." suka fad'a tare da fita daga d'akin.

Raheenat ma ta gama shiri ta kalli Mama tace "uwa mai dad'i ni zan wuce."

Da murmushi Mama tace "yarinyar da tafi ta kowa har za'a tafi?"

Rumgumo wuyan Mama tayi tana dariya tace "zaki fasa min kaina fa."

"Ni kike nema ki fasa min nawa." Mama ta fad'a cikin dariya itama, sumbatar kumatun Mamanta tayi tace "saina dawo Mama, ki kula da kanki."

"Zanyi 'yata, Allah ya tsare minke da tsarewarsa."

"Ameen Mamana."

Ta fad'a ta fita, saida ta tsaya qofar d'akin Inna tayi sallama Baba ya amsa, shiga tayi kanta qasa cike da ladabi ta gaishesu, Baba kad'ai ya amsa banda Inna dake hararanta kamar idonta zasu fad'o qasa, addu'a Baba ya mata sannan ta tashi ta wuce itama, cikin sa'a kuma sai suka had'u da Sameera itama zata wuce, gaisawa sukayi sannan suka rankaya tare.


Bayan an taso ma tare suka tawo, suna jiyo su Farida ta bayansu suna aika musu da zagi amma ko su kulasu, sai ma suka mai dasu mahaukata, a haka har suka ƙaraso ƙofar gidan, sallama Sameera da Raheena sukayi sannan Raheenat ta shige gida ɗauke da sallama a bakinta su Farida na mara mata baya.



*************


Kamar kullum dai hajiya Maryam tana tashi salla ta gabatar sannan ta nufi ɓangaren Abdul da sauri dan ganin yanda ya kwana, tana shiga ta sameshi kwance yanda ta barshi jiya idanunsa a lumshe, sai dai ta tabbatar ba bacci yakeyi ba, shafa kanshi tayi cike da tausayinsa tace "barka da tashi ɗan albarka. "

Buɗe idanunsa yayi ya kalleta sannan ya mayar ya rufe, cikin taushin murya tace "bari na taimaka maka na kaika toilet Abdul, nasan zaka buƙaci hakan. "

Tana gama faɗin hakan ta ɗauko wheel chair ɗinsa ta aje a gefen gadon, nan ta fara ƙokarin cicciɓansa, daƙyar ta ɗaurasa saman keken tana nishi, turashi tayi a hankali ta nufi toilet ɗin dashi.


Da taimakonta dai yayi fitsari tayi masa tsarki sannan ta kuma gunguro sa suka fito, kuskure ɗaya hajiya Maryam takeyi a cikin jinyar Abdul Hakeem, kuskuren kuwa shine ba ko yaushe ne take ɗaura masa alola tace yayi sallah a cikin zuciyarsa ba, wanda muke ganin hakan babban kuskure ne, Abdul sallah be ɗauke a kansa ba, saboda yana cikin hankalinsa yana iya jin duk wani abu da za'a faɗa yana kuma gani, saidai kawai ba zai iya motsa duk wata gaɓa na jikinsa bane, kunga kuwa ai zai iya yin sallah a cikin zuciyarsa matuƙar aka ɗaura masa alola, to Hajiya Maryam ba ko yaushe ne take hakan ba sai ya ɗauro.

Shafa kansa tayi tace "ɗan gidan Momynsa ni bari naje na haɗa abin kari kar hajiya ta jini shiru, zan barka saman kujeran nasan zaka fi buƙatar hakan tunda ka kwana kwance, ko na kaika falo ne na kunna maka tv ya ɗebe maka kewa.?"

Lumshe ido yayi ya buɗe, hakan yasa ta fahimci eh yake nufi, gungurosa tayi ta ajiye a falo sannan ta kunna masa tv, tashar sunna tv ta kama masa sannan ta fice daga falon da sauri sabida gudun samun

Please Login or Register in order to submit comment