Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

acikin wannan asusun namu na banki馃憞馃憞

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban ta whatsapp shedan biyanku(evidence of payment/Account name)馃憞馃憞

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU馃憞馃憞

聽 0903聽234聽5899

馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎
TEAM----ZAFAFA BIYAR馃敟馃槝馃グ馃槏
10/17/21, 2:10 PM - Aisha Adam: _DALAAL馃馃徏馃挐馃挐_
_(A new world....)_


_漏锔廧AFAFA 2021(next level)_
_(PAID NOVELS/LITTAFAN KUDI NE)_

_庐锔廚ANA-HAFSATUWA_
馃馃徏馃挐


_ FPG:3 _

*SAMEER SA鈥橢D RESIDENCE*

Kalle-kallen layin Dalaal tashiga yi, Kwarai duk da ba mazauniyar kasar bace, Ba zata taba mancewa da tsohon gidan uncle sam ba. Ko kusa bama hanya d鈥檃ya bane. Ko anyi renovating ne? Tai saurin girgiza kanta alamun a鈥檃h! Wani katafaren kofar gidah suka nufa, Da wani jijjigegen gate me nishi na masu kud鈥檌, Suna dosar gate din ya bu鈥檇e da kansa.

鈥淕ida na Uncle Sam?Ba nan ba ina ?鈥�

Dalaal ta tambayi Gali cikin tsananin Mamaki, Gali yai hanzarin gyada kai yana daga hannunsa sama yashiga kwarara bayani yana irgawa da yatsun sa,

鈥淭ab lalle da alamun kin jima baki waiwayo kawun na ki ba, Yo ai Kinga da gidan nan, Da estates din gaban can dana baya du nasa ne, Sannan mun baro wani gidan mai a baya na sam&sons to nasa ne dana yaran sa, kinji uku, Na hud鈥檜 yanada makarantu ga hannun jari da yake dasu a kamfanoni da dama. Ai Allah ya daga uncle d鈥檌nnan naki, arzikin lokaci d鈥檃ya tal aka wayi gari ya zama hamshakin me kudi.鈥�

Dalal ta kad鈥檃 kai, Duk kuwa da bakomai ta tantance ba,

鈥淗em-shark-key...?鈥�
Ta rarraba kalamen tamkar wasu na turanci.

鈥淚na nufin yes the-same, Yes look dangote, Big boy, Kudi many da yawa.鈥�

Murmushi tai kawai ta mayar da kanta gefe tana kallon cikin gidan, Titi ne sosai aka malala shi tun daga gate har gaba d鈥檃yan farfajiyar gidan, Motoci gasunan birjik hadaddu an faffaka su a rumfa. Dai dai kofar da zata sadaka da cikin gidan Kalu driver ya tsaida mota sai da Dalaal tafita, Sannan ya gyara motar ya mayar rumfa, Gali ya dakko mata kayanta suka shigar mata dashi gida.

鈥淲elcome home.. My sweet daughter.鈥�

Cewar uncle sam daya tare ta da sauri, Yana mai bu鈥檇e hannuwan sa. Ya rungumeta yana murmushi.

鈥淯ncle Sam鈥�

鈥淵es! Dearest one. Muje ciki ko..! Ko dai hausar taki tagama tafiya gaba d鈥檃ya.?鈥�

Yi tayi kamar bata gane abunda yake cewa ba, Hakan yasa ya sake darje baki ya shiga yi mata bayani da turanci,

鈥淢uje ciki su Adeel nata jiran zuwan ki har ya gaji da jira ya tafi wajen aiki, Amma sauran yaran na ciki.鈥�

Kada kai tayi, Yana gaba tana biye suka karasa cikin babban parlorn sa. Aunty Nani (Aisha) matar sa ce aciki, Sai yarinya budurwa da saurayi guda d鈥檃ya. Aunt Nanin ce kawai ta tareta da fara鈥檃 banda sauran yaran dake wani kumbure fuska. Bata fuska yayi yana nuna fushin sa a fili dan haka kowannen su ya shiga gaisheta, Amsa su tayi tana mai sake duban Uncle Sam, Cikin harshen turanci take tambayar Sa.

鈥淯ncle dakin dazan kwana fa? Inason na huta.鈥�

鈥淏a zaki ci abinci ba? Har an giggirka miki abubuwa.鈥�

鈥淚na dieting. Sede ruwa da kayan marmari kawai鈥�

鈥淭oh ba matsala, Duk za鈥檃 kawo miki ciki, Ke Hissah tashi ki raka cousin dinki dakin ta.鈥�

Mikewa tai tana zumburar baki tayi gaba, Dalaal na biye da ita a baya tana kalle kallen koina na gidan, Ba wai tsaruwar gidan ce ta burgeta ba, Kawai yana yin habakar arzikinsa ce ta lokaci d鈥檃ya ta bata mamaki kwarai matuka.

鈥淕a dakin nan.. Duk abunda kike buk鈥檃ta ga intercom can a gefen gado.鈥�

鈥淭hank you.鈥�

鈥淯 are not at all welcome.鈥�

鈥淢y pleasure...鈥�

Cewar Dalaal, Ta fada tana murmushin gefen baki. Hissah ta murgud鈥檃 mata baki. Kafin tayi gaba tana zumb鈥檜ro shi.

鈥淎bba!鈥�
Ta kwala masa kira tana cuno baki gaba,

鈥淣a鈥檃m auta...鈥�

鈥淵aushe zata tafi.?鈥�

鈥淲a...?鈥�

鈥淲annan bakuwar mana Abba.. Gaskia bama sonta.鈥�

Cewar Moh (Mohammed) dake tabe baki shima.

鈥淵au naga ja鈥檌ran yara, Akan ku take? Daga zuwanta yau se zancen yaushe zata tafi? Yar uwar kuce nan da kuke gani, Sanda tabar kasar kuna k鈥檃nana. Na gaya muku first cousin d鈥檌nku ce. Kar na soma ji kun sake irin wannan kananun maganganun. Sakarkaru kawai.鈥�

鈥淜ayi ha鈥檏uri Alhaji, Ba saji ne kawai. Amman tun dazu nake ja musu kunne akan ire iren maganganun nan, Su har abada ba wanda zai rab鈥檈 mu, Kwata kwata bakwason baki suzo, Bare wannan yar uwace ta jini, So kuke ku bayyana halin ku itama tayi fushi tatafi Kamar yadda kuke yiwa sauran bak鈥檌 idan sunzo, To bazata sab鈥檜ba. Ke Hissah kece me tsara komai, Don haka ki gaggawar sauya halin ki.鈥�

Haka dai Uncle Sam. Da Aunty Nani su kai ta jan kunnuwan Moh da Hissah akan dabi鈥檃r da suke marar kyau ta munanawa bak鈥檕. Uncle sam ya kar鈥檏are da,

鈥淜uma Dalaal nan gidan su ne, 鈥榊a ce Kamar yadda kuke 鈥榶aya acikin gidan nan, Karku kuskura naji an kawo karar ku, Ko kuma ta yi fushi tace zata koma inda tafito akan haka, Idan haka tafaru to ranar mai raba ni da ku sai Allah. Kun dai ji abubuwan da muka gargade ku akai ko?鈥�

鈥淓h Abba.鈥�

鈥淭oh yayi kyau.鈥�

鈥淗ajjaju muje ki dakkomin takardun nan zan wuce dasu office.鈥�

Mikewa su Kayi suka tafi, Parlor ya zama daga Moh sai Hissah,

鈥淜aji abubuwan da Abba ke fada? Dagaske ne ko kuwa kunnuwa na ne?鈥�

鈥淲allahi nima nayi mamaki sosai.鈥�

鈥淪osai fa, Bai taba nuna fushin sa ba sai yanzu. Ai kuwa sede ya yanka ni gunduwa gunduwa, Dan waccen yarinyar na tabbata ba musulma bace, Kalli kanta ko dankwali babu, Batama jin hausa yar kan uba, Abinci ma dan iyayi wai ta koshi, Mu zata nunawa gayu? Makaryaciya da alama sedata cika cikinta a airport sannan.鈥�

鈥淜ede bari sis, Abba ne da jajibe jajibe, Da can me yasa ta guje shi bata zuwa sai yanzu da yayi kudi? Shine yan uwa suketa tururuwar zuwa. Bakiga kalle kallen da take ba? Shegiya taga gidan daula. Ai kuwa Zata sha zagi da hausa, Har sai ta tsargu. So annoying.鈥�

鈥淣agani.. Irin hate at first sight dinnan na kamu dashi, Allah Yaya ina ganinta naji na tsane ta. Tana wani iyayi, Shegiya bayan nasan kila Abba ne ya dauki dawainiyar kasar wajen data je.鈥�

鈥淓h mana daga gani dama shi ne. Na tsaneta nima, Haka zamuyita musguna mata harta gaji ta tattara kayanta tatafi.鈥�

Haka dai su kayi ta zagin Dalaal suna aibatata. Ita kuwa Dalaal a nata bangaren band鈥檃ki tashige tayi wanka ta tsaftce jikin ta, Tayo alwala hade da tada iqama akan sallayar data ga an shimfida mata da hijabi akai da carbi da alama dai nanne gabas. Tana idarwa tayi addu鈥檕in ta. Knocking kofar akayi alokacin Dalaal na Zaune tana jan carbi,

鈥淵es...Enter.鈥�

鈥淪alamu Alaikum..鈥�

鈥淲a鈥檃lykm Salam.鈥�

Wata yar budurwa ce tashiga ciki dauke da tray kato, Ta ajiye agaban Dalaal.

鈥淕a hi inji Hajia.. Ni kuma sunana Safara鈥檜.鈥�

Kad鈥檃 kai Dalaal tayi mata tana murmushi.

鈥淎kwai wani abun na miki?鈥�

Girgiza kai Dalaal tayi alamun a鈥檃h! Safara鈥檜 ta mike ta mata sallama ta tafi. Dalaal ta sauke zucia tana mai karewa tray din gabanta kallo, Kayan marmari ne a yayyanke an soka fork a gefe, Sai yoghurt me sanyi da ruwan roba guda biyu. Caccakuna tayi tasha fruits din sosai, Tadan debi yoghurt din a kofi karsuce bata shaba tasha, Sai kuma ta dora da ruwa. Sai da taji abincin da taci ya lafa tukun sannan ta haye gado tashiga sharara baccin gajiya....

*SPAIN/MADRID*

Yana kwance akan gadon dakin sa, Kansa a sama yana kallon saman dakin. Da alama ya lula duniyar tunani. Lokaci zuwa lokaci yakan girgiza kansa.

鈥淵a Rabbi..!鈥�

Yaketa maimatawa yana mai cije leben sa. A hankali ya mike ya zauna akan wata kujera mai dauke da teburi, Ya janyo wata fefa fara tas da fensiri ya shiga zana gefen fuskar Dalaal mai dauke da beauty mark. Yanayi yana lumshe idanu, zara zaren gashin Idanun sa masu maiko sai kad鈥檃wa suke. Gashin ta kanannade kalar ja-ja ya shiga zanawa. Ya dau tsawon lokaci a haka kafin ya kammala ya adana shi acikin drawer sa. Tunanin tane dankare acikin kirjin sa wanda ya haddasa masa ciwon kai sosai.

Wayar sace tayi k鈥檃rar shigowar sak鈥檕 ya dauka yana dubawa. Prof. Amelia ce ta sake turo masa sak鈥檕nnin da bata gajiya da turo su.

鈥淣a baka nan da kwanaki k鈥檃lilan, Ka sake tunani akan zance na. Idan ba haka ba za kayi danasani mai tsanani.鈥�

Siririn tsaki yaja yana mai dafe kansa, Lectures yake da, Amman gaba d鈥檃ya yaji bayason zuwa makarantar domin yasan ba zasu 鈥榢arke lafiya da ita ba.

鈥淚nnalillahi wa鈥檌nna ilaihirrajiun.!鈥�

Ya fada a nutse yana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya. Gaba d鈥檃ya ransa a dagule yake. Zuciar sa babu dadi sai zugi take, Kansa na masa matsanancin ciwo, Jiri sai dibar sa yake. Damuwa ce kala kala dankare a kirjin sa. Ya rasa kuma yadda zai sauke shekararriyar damuwar dake dawainiya dashi, Uwa uba ga guda biyu da suka sako shi a gaba yanzu Prof. Amelia da ta Dalaal.

Mikewa yai jikin sa a sanyaye ya sauya kayan jikin sa zuwa wasu. Muk鈥檜llin mota ya dauka ya sauka kasa.

鈥淢aa! Na tafu sch.鈥�

鈥淭oh adawo lapia, Allah yabada sa鈥檃 da nasara.鈥�

鈥淎meen Ameen.鈥�

Ficewa yai da sauri yana kallon agogon hannun sa. Ya shiga mota ya dauki hanyar makaranta. Kansa tsaye ya wuce aji. Ranar dai sukuku suka kammala lectures, Duk baya mayar da hankali. Har yai hanyar motar sa wani abokin karatun sa yace yaje Prof. Amelia na kiran sa. Ba yadda ya iya haka ya juya, Yana daga kai ya hangota ta saman barandar ofisoshin sama na malamai.

Tana ganin ya taho ta koma ta zauna, Ta 鈥榖abballe botiran gaban rigarta, kana hango komai na halittar jikin ta kasancewar rigar shara-shara ce iya cinya. Yana shiga cikin office din ta mike da sauri zata rungume shi yaja baya da sauri har yana tunkude flower vase. Cikin harshen Spanish ta shiga mana ahankali kasa kasa tana jujjuya jikinta. Yana tsaye tamkar gunki Ita kuma tana magana tana zagaye shi,

鈥淪hin meye laifi na da bazaka bani had鈥檌n Kai ba? Se kace ba wayayye ba. Rana d鈥檃ya kacal nace ba wai kwanaki zamu diba ba. Please Hafez... Ka duba magana ta.鈥�

Yadda take magana, Gashi hannun ta d鈥檃ya na shafar gadon bayan sa yasa Hafez sauke wata ajiyar zuciya. Dak鈥檡ar ya matsa baya yana girgiza kai,

鈥淒an Allah ma鈥檃m ki kyale ni, Ki fita daga rayuwata, Bazan taba aikata abinda kike so ba, Ni musulmi ne. Kuma addinin mu ya mana hani da haka inde ba matar ka ta sunnah ba daka aura ta hanyar aure...鈥�

鈥淗aka ka zaba? To shikenan inde haka ka zaba, Zan yi sanadiyyar barin ka makarantar nan, Kuma kowacce 鈥榢asa zakaje senaga inda karfina ya kare don kuwa bazaka cigaba ba. Ka yadda?鈥�

鈥淣a yadda...鈥�
Ya fada a dan tsawace yana sakin tsaki.

Botiran gaban rigarta ta shiga budewa gaba d鈥檃ya, Saman kirjin ta ya fito sosai , Hafez ya runtse ido da sauri yana istigfari,

鈥淶an baka dama... Ka bani ha鈥檇in kai na minti 30 kawai a office dinnan, Z鈥�

Ai be bari ta karasa fada ba da karfin gaske ya fincike jikin sa ya fita da sauri yana mai bugo mata kofar office din. Kansa tsaye ya koma gida a firgice, Kuka kawai yake a daki, Saboda tsananin tashin hankalin dayake ciki, Hasheesh ya dakko a gefen drawer sa ya nannade ta yana shaka. Sai daya ji shi a sama sosai tukun sannan ya kwanta a gado. Haka ya wuni cir cikin maye akan gado. Yanata magana a baibaice. Cikin haka Prof. Basheer ya shiga ya same shi, Hafez din na kwance Yana magana ahankali,

鈥淜izo gare ni... Karki guje ni, Kwakwalwa ta takasa manta ki, Idanuwana sun gaza nuna min hotan kyakkyawar fuskar ki. Zuciyata kullum cikin muradin son sake ganin ki take.. Primer amor!!!(first love)鈥�

Prof Basheer yai shiru yana sauraron maganganun da Hafez ke cewa. Har zai futa ya sake jiyo shi,

鈥淏azan iya zina ba... Ki dena bibiyata.. Ki fita daga rayuwata..鈥�

Dawowa yai yana kallon Hafez din yana girgiza kansa cikin takaici, Jimami, Da kuma tsantsar bacin rai. Dube dube ya farayi na inda zai hango abubuwan mayen, Yana bude drawer ya hango su, Taba, Hasheesh, Da kwalaben giya guda biyu manya manya masu tsada. Daukan su yai gaba ki d鈥檃ya ya kai motar sa ya ajiye. Ya koma cikin gida.

鈥淒ear Lapia?鈥�

鈥淟apia lou habibty, Kawai dai yau ba sai gobe ba, Zan sake mayar da Hafez asibiti. Zurfin cikin sa yayi yawa tun yana 鈥榢ankani. Na kasa gane abinda ke cikin zuciar sa, Kinga sanadiyyar haka ya ha鈥檇u da ciwo, Ga kuma shaye shaye daya fara yanzu daban san inda ya koyo ba.鈥�

Haj Ziyadah ta nemi waje ta zauna tana mai zabga tagumi, Idanun ta sun kawo ruwa zata fara zubar da hawaye.

鈥淒an Allah kakki zubar masa da hawaye, Kawai tashi zamuyi tsaye dole ya fa鈥檇i damuwar sa. Akwai abunda ke masa radadi a zuciya..鈥�

鈥淜ana tunanin y....鈥�

鈥淎h karma ki kawo wannan zancen Habibty, Be shafi wannan ba, Naji yana ambatan wata tazo gare shi, Da kuma yana fatan wata ta futa a rayuwar sa. Ina tunanin mata ne biyu mabanbanta..鈥�

鈥淵anzu ya kake ganin za鈥檃i?鈥�

鈥淎sibiti zan mayar da shi na kwakwalwa.鈥�

鈥淲anda ka Kai shi ya dawo be gaya musu komai ba?鈥�

鈥淓h nan... Duk garin nan ai nanne suke da manyan specialist.鈥�

鈥淭oh Allah ya kawo karshen koma menene dake damun sa.鈥�

鈥淎meen..鈥�

Sama prof. Basheer ya haye. Dakin Hafez ya shiga ya riko shi suka sauka kasa.

鈥淎hh papa...Papa ya hidima? Wai ba zaka gayamun gaskiyar al鈥檃mari ba.?鈥�

鈥淎l鈥檃marin me Hafez?鈥�

Hafez ya karkada hannuwan sa yana jijjiga kai,

鈥淎l鈥檃marin..... Au na manta fa. Al鈥檃marin cheese burger mana.鈥�

Prof Basheer ya sauke zuciya kawai yana mai sake riko kafa鈥檇ar Hafez ya futar dashi waje ya shigar dashi cikin mota, Haj Ziyadah nata kwararar ambaliyar hawaye, Tana tsaye har Prof Basheer ya zura mukulli yaja motar. Sannan ta koma gidah, Kai tsaye ya wuce dasu asibitin su Dr. Fabio, Suna zuwa ma鈥檃ikata suka rirrike hafez suka shigar dashi cikin asibitin. D鈥檃ki sosai na marasa hankali aka kai shi aka bashi gado... Dr. Fabio da kansa ya masa allurori, Duk kudin komai da yakamata na duba lapiar Hafez har warkewar sa prof basheer ya biya. Bacci Sosai Hafez ya shiga yi sakamakon allurorin baccin da aka dirka masa, Bai farka ba sai washegari.

*KANO......*

**JUSTICE SAIFUDDEEN IBRAHIM SANDAMU ESTATE**

*_鈽� AL-茦IBLA_*馃挊
_Na Safiyya Huguma_

*_鈽� MABU茒IN ZUCIYA_*馃挅
_Hafsat Rano_

*_鈽� DALAAL_*馃挐
_Na Miss xoxo_

*_鈽� UBAYD MALEEK_*馃挀
_Na Mamu gee_

*_鈽� MAKAUNIYAR 茦ADDARA_*馃挃
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nisha蓷i馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka馃憞馃徎馃拑馃徎

茒aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu蓷u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki馃憞馃憞

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban ta whatsapp shedan biyanku(evidence of payment/Account name)馃憞馃憞

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU馃憞馃憞

聽 0903聽234聽5899

馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎
TEAM----ZAFAFA BIYAR馃敟馃槝馃グ馃槏
10/17/21, 2:10 PM - Aisha Adam: _DALAAL馃馃徏馃挐馃挐_
_(A new world....)_


_漏锔廧AFAFA 2021(next level)_
_(PAID NOVELS/LITTAFAN KUDI NE)_

_庐锔廚ANA-HAFSATUWA_
馃馃徏馃挐


_ FPG:4_

***ATTORNEY GENERAL SAIFUDDEEN IBRAHIM SANDAMU STREET**

*Wani* katafaren gidah ne mai dauke da gidaje masu bene aciki, Tsararru irin na zamani kirar 3D, Wanda turawa ke kira da estates. Kallo d鈥檃ya za kai masa gidane na masu hannu da shuni, Saboda yanayin yadda aka kashe ku鈥檇i wajen zuba ginin sa, Uwa uba hade da dandazon masu tsaron dake zazzaune a kofar gidan. A farkon layin zaka ci karo da 鈥榢aton allo (sign board/placard) an rubuta da manyan baki (ATTORNEY GEN. SAIFUDDEEN IBRAHIM SANDAMU STREET). Duk wata haduwa dai ta gidan duniya to wannan gida yayi. Har ya zarce tunanin mai karatu. Sai dai muce Masha Allah kawai.

**** Da sauri masu gadi suka bude gate, Tun kafin motar justice ta 鈥榢aro sun jiyo horn dinta, Driver ya shige da motar cikin wawakeken harabar gidan, Ya ajiye motar a ma鈥檃danar ta. Sannan ya futo ya budewa attorney kofa ya fito. Sanye yake cikin kayan lauyoyi (attorney gen) Ya rike bench wig dinsa a hannun dama, Yana tafe yana amsa waya, Ma鈥檃ikatan gidan sai zubewa suke suna gaishe shi yana mai 鈥榙aga musu hannu. Kai tsaye ya shige cikin sashen Hajia Bintah (uwargidan sa).

Yana shiga ta tare shi da sauri, Ta amshi kayan hannun sa. Ta shige dakin sa dake 鈥榢asa, Mai dauke da babban parlour da dakuna guda biyu.

鈥淪annu da zuwa Alhaji..鈥�

鈥淵auwa Hajia...鈥�

Ya fada a hankali yana tari, Da sauri ta dakko ruwa a gefe acikin kayan abincin da aka shirya masa ta tsiyaya masa a kofi. Ta mika masa,

鈥淕ashi Alhaji..鈥�

Karba yai ya kurbe, Har lokacin da waya a kunnen sa, Sai daya dau lokaci sannan ya katse kiran.

鈥淪annu da zuwa Alhaji.. Ga abinci ka sakko ka ci, Ko ruwa zaka fara watsawa? Gashi nan na sirka a bandaki.鈥�

鈥淣agode Hajia, Bara na fara cin abincin, Duk ina yaran basu dawo ba ne.?鈥�

鈥淗afez bai dawo ba, Nasan dai yana hanyar dawowa, Batoul da Ayaah na Islamiyya, Na鈥檈em kuma ya dawo ya sake fita. Farouk kuma ya dawo yana bangaren su.鈥�

鈥淢asha Allah! Toh bara na fara cin abincin ko?鈥�

鈥淭oh Alhaji..鈥�

Jajjanyo kulolin abincin tayi ta sanya agaban sa. Ta shiga zuzzuba masa kowanne a inda ya dace, Yai basmala yana mai jan abincin gaban sa.

鈥淢u ci ko?鈥�

鈥淣a ci Alhaji tun dazu.鈥�

Sosai ya shiga ci, Sai dayaci ya koshi sannan yai hamdalah. Yana mai yaba dad鈥檌n abincin, Ya mike ya shige dakin sa. Ya tsaftace jikin sa sosai ya sauya kaya cikin jallabiya. Lokacin sallar la鈥檃sar ya kusa. Don haka ya fito zai zazzagaya zuwa sauran sashen kamar yadda yake ko yaushe. Yana fitowa daga dakin sa ya hango shi ya dawo shima Sanye cikin kayan lauyoyi. Zubewa yai a kasa yana gaida shi,

鈥淏aba barka da rana, An dawo lapia?鈥�

鈥淟apia kalau Habeebullah! Ya aiki?鈥�

鈥淎lhamdulillah Baba! Ya jikin naka?鈥�

鈥淒a sauki Alhamdulillah.鈥�

Habeebullah bai mike daga tsugunnon da yake ba sai da mahaifin nasa ya fita. Kai tsaye attorney gen saifuddeen ya nufi sashen Haj Naja鈥檃tu (Amaryar sa) yana tafe yana jan carbi. Ya shige ciki bakin sa dauke da sallama,

鈥淲aalykm Salam! Alhaji barka da zuwa.鈥�

鈥淏arkan mu hajjaju..鈥�

鈥淎n dawo kalau? Allah ya temaka.鈥�

鈥淎lhamdulillah, Aamin Yaa rabbi.鈥�

Kitchen ta shiga ta dakko fura da nono me sanyi ta ajiye masa.

鈥淎lhaji ga fura鈥�

鈥淕odia nake hajjaju.鈥�

A nutse ya shiga shan furar yana yaba da鈥檇in da tayi, Bai wani jima sosai ba yai mata sallama ya tafi. Yaje sashen Haj Iklima matar sa ta 2. Nan ma suka gaisa sannan ya mike, Ya Zazzagaya sauran sashen har na masu aiki ya tabbatar kowa da komai yana cikin koshin lapia. Sannan ya wuce masallaci dake cikin gidan, Nan ya shiga ya fara karatun al鈥檘urani har lokacin sallah ya gabato sukayi sallah, Sannan ya dau mota ya tafi majalisar su.

*Attorney gen. Saiffuddeen Ibrahim Sandamu, Dattijone kamili masanin ilimin shari鈥檃, mai matakin sharia babba na jihar kano, Yana da mata 3 da yara 7, Matar sa ta farko da bata gidan a halin yanzu tana da yaro d鈥檃ya mai suna Habeebullah wanda shima lawyer ne a karkashin chamber mahaifin sa, Shine babban 鈥榙a ga Alhaji saifuddeen, Sai yara 4 wanda duk uwargidan sa ce ta haife su, Na鈥檈em shine babba, Likita ne a babban asibitin kwararru dake kano, Sai Ayah tana jami鈥檃, Sai Farouk shi kuma yana aiki a banki, Sai autar su Batoul. Wannan duk 鈥榶ayan Haj Binta ne uwargidan sa, Itama yar dattijuwa ce wadda ya aura bayan ya rabu da matar sa farko. Sai Haj ikhlima mai yara yan biyu duk mata suna jami鈥檃 Nasrean da Aliyah, Sai Haj Naja鈥檃tu wadda bata taba haihuwa a gidan ba, A bazawara ya aure ta tana da 鈥榶a mace da mijinta na farko wanda ya rasu. 鈥榊ar tata mai suna DALAAL, Ba a hannun ta take ba tun bayan rasuwar sa. Takanzo dai tayi hutu awajenta tun kafin ta auri Alhaji Saiffuddeen.

****SPAIN/MADRID****

Yana farkawa yaci karo da 鈥榢wala-kwalan gilasan Dr. Fabio ya zuba masa kallo Kamar zai cinye shi, Da sauri Hafez ya mike yana kalle kalle,

鈥淢e nake anan Dr.?鈥�

鈥淜ana asibiti ne..鈥�

鈥淢eya faru aka kawo ni nan?鈥�

鈥淏aka tuna komai ba?鈥�

Kad鈥檃 Kai Hafez yai yana girgiza kansa, Da sauri ya sake cewa dashi,

鈥淜arfe nawa?鈥�

鈥淕oma..鈥�

鈥淣a dare? Har dare yayi haka?鈥�

鈥淲ane dare? Na safiya dai, Kwanan ka daya anan.鈥�

Ai Hafez bai jira Dr. Fabio ya sake magana ba ya fisge karin ruwar dake hannun sa, Bandaki ya shige da sauri yai wanka hade da yin alwala, Ya samu waje mai tsafta ya shiga jera sallolin da suka wuce shi, Ya nemi gafarar Allah abisa abubuwan daya aikata. Yana idarwa ya mike har yakai hannunsa kofa ya jita a rufe,

鈥淏udemin na fita...鈥�

鈥淜a fita Ina? Ai babu inda zaka je sai ka warware mana damuwar ka.鈥�

鈥淏abu abinda yake damu na..鈥�

鈥淢eyasa kake shaye-shaye?鈥�

鈥淏ana shaye-shaye.鈥�

鈥淎bunda kayi kenan, Hankalin ka ya bar jikin ka, Shi yasa aka kawo ka nan.鈥�

Jujjuya kansa Hafez yai ya zura aljihun sa zai dakko wayar sa yaji wayam.

鈥淚na waya ta?鈥�

鈥淭ana wajen mu.. Mahaifin ka yace karmu baka sai ka samu lapia.鈥�

Takaici, Da 鈥榢ololuwar bakin cikin kalamen Dr. Fabio ne suka sashi dukan karfen gado da k鈥檃rfi, Ya ja tsaki. Zagaye dakin ya shiga yi yana mai karanta dik wani hoto daya gani mai dauke da rubutu. Can k鈥檃rshen kusurwar dakin ya hango wasu hotuna na likitocin asibitin gaba d鈥檃ya Kowanne da sunan sa ajiki. Ahankali ya shiga kallon kowannen su har yazo kan na Dalaal, Ya tsura mata idanu tamkar ita ce yake gani dagaske.

鈥淒r. Fabio wacece wannan?l鈥�

Dr Fabio ya mike ya karasa kusa da hotan Dalaal da Hafez ke nuna masa,

鈥淒ALAAL...!l鈥�

鈥淪unanta kenan..?鈥�

鈥淓h..鈥�

鈥淜o zan iya ganin hotan gefen fuskar ta..?鈥�

鈥淚t鈥檚 confidential..鈥�

Murmushi Hafez yayi, Jin Dr. Fabio ya rama abinda ya masa rannan.

鈥淒an Allah Dr...鈥�

Hafez ya fada a hankali yana mai kalle hotan Dalaal, Gaba d鈥檃ya yanayin gashin ta da hasken fatar ta iri d鈥檃ya ne da na yar budurwar data cece shi. Ahankali can kasan zuciar sa yace,

鈥淎 beautiful lady, who has light colored hair..鈥�

鈥淒ALAAL kenan, Kyakkyawar budurwa, Tushen Nigeria da Lebanese...鈥�

Dr Fabio ya bashi amsa yana murmushi, Ai gaba d鈥檃ya jikin Hafez sai ya dauki rawa kamar mazugi. Kwakwalwar sa tashiga tariyo masa amsar da dayan likitan ya bashi akan Dalaal, Cewar tace musu sauri take zatai tafiya ne. Dama kuma likita ce. Kenan a asibitin su Dr. Fabio take...

鈥淎lhamdulillah...鈥�
ya furta cikin farin ciki yana mai dashe bakin sa.

鈥淵a akai Hafez?鈥�

鈥淒r. Fabio, Na yadda zan amsa duk abunda kukace nayi, Amman in return zaka gayamun komai akan Dalaal.. Ka yadda?鈥�

鈥淎greed....!( Na amince)...鈥�


<><><><><>

**DALAAL**

Dalaal bata farka ba sai da aka kira sallar la'asar ta dinga juye-juye a kan gado baccin yaki ci gaba, ta tashi tana mik'a tare da jujjuyawa da alama jikin take son ya yi mata normal. Toilet ta shiga tayo alwala tana fitowa ta tayar da sallah, bayan ta idar tabi jikinta da addu'o'i sannan ta cire hijabin tana ninkewa taji an bude kofar dakin an shigo. Kallan kallo suka tsaya yiwa juna tamkar masu yin wani nazari, can Dalaal taci gaba da ninkin tana cewa.

鈥淏abu sallama?鈥�

Mamakin tambayar yasa shi sakin baki.

Tsaye take cikin riga da wando jeans gashin kanta ya barbazo gashi kuma ja bata da maraba da arniya sai dai idan ka kalli goshinta wajan farkon fitowar gashi zaka ga bakin sallah, gashi kuma yaga sallaya harma ga hijabi nan tana ninkewa, sai dai duk da haka zuciyarsa bata yarda cewa ita bace.

鈥淚na Dalaal take?鈥�

Yana dan waige waige ko zai ga wata ta fito.

鈥淕ani.鈥�

Ta bashi amsa tana rike kugunta.

鈥淜ece Dalaal din.?鈥�

Tayi banza dashi ganin sai yi mata tambaya daya yake yi, ta dauki iPad din ta tare da hayewa tsakiyar gado taci gaba da harkarta.

鈥淪una na Adeel, nine babba a gidan nan Abba yace kinzo shi yasa na zo na ganki.鈥�

鈥淣agode.鈥�

Duk maganar da suke yi suna yi ne cikin harshen turanci, dan shi Adeel beyi zaton tasan zo ba da hausa shi yasa beyi gigin yi mata ba. Ganin taci gaba da danne-dannenta yasa Adeel sake kallonta ganin yadda rigar jikinta tayi mata kyau, kamar ba zai tafi ba sai kuma ya juya ya kama handle din yaji tace masa.

鈥淯ncle Sam yana parlor ne?鈥�

Ya juyo ya kalleta yaga shi take kallo tana jiran jin amsa daga bakinsa, ya saki wani munafikim murmushi tare da cewa.

鈥淜i fito ki gani mana.鈥�

Dalaal ta daga masa kai kawai alamar zata fito taci gaba da harkar gabanta. Lallai yarinyar nan tazo da girman kai, daman haka turawan suke yi ko kuwa dai nata salon wulakancin kenan? Adeel ya koma

Please Login or Register in order to submit comment